Showing 78001 words to 81000 words out of 116224 words

Chapter 27 - Maciji ne book 1

28 Aug 2024

25318

kansa abin yana damunsa,.
Haka ma Adeeb yana jin ciwon abinda yayiwa ɗan uwan nashi,saidai koma menene shiyajawa kansa.kuma hakan bai hana shi neman masa magani ba .

Shaikh lateef ya bawa Adeeb magungunan da zai rinka amfani dashi,kuma yana amfani dasu yadda ya kamata.zamu iya cewa yanzu abubuwa sun dan lafa agidan.

Yanzu haka fattu ana mata lesson kullum ,zakuyi mamakin yadda fattu ta iya Yaren larabci sosai,tana ji kuma tana iya mayarwa, dan fattu akwai ƙwaƙwalwa,shikansa mai mata lesson yana mamakin hazaka irin ta fattu.
Adeeb kullum yana kara nuna mata abubuwan da bata game ba.tayi kyau sosai ta goge idan ka ganta bazaka taba cewa itace ba.
Kullum saisunyi waya da sarauniya suhaimat,sun shaku da juna sosai.

Gimbiya Zulaihat ma tana nan tana nata shirin,dan yanzu kam tana ganin fattu na neman zama wata abar alfahari agidan,dan ta kereta ta ko ina,Shegiyar yarinya kyau kamar yar aljanu.

Wannan kenan.

Ammice zaune ƙaton falonta tana waya,dawowarta kenan daga gurin mai martaba,tana masa maganar ya dace ace zuwa yanzu Adeeb yayi aure ,dan shekaru na tafi kuma shine magajin fada.
Dan haka abie yace ta zaba masa matar da zai aura ,tunda itace amminsa ,kuma yasan Adeeb bazaiki zabin ammin nashi ba.tun da dai shi ba kula yan mata yake ba.
Cikin farin ciki kuwa ammi ta dawo ɗakinta ta kira kawarta.

"Ƙawata ,albishirinki?
Ammi ta fada cikin ɗoki.
Bansan me akace mata ba ta dayan bangaren naji dai taci gaba da cewa"ai mai martaba ya bani damar zabawa Adeeb matar da zai aura,kuma ba kowa na zaba masaba face yar wajenki,maryam.kinga mun sami hanya cikin ruwan sanyi,da zamu cika burinmu akansa" ta fada cikin doki tana murmushi.

Shiru na ɗan wani lokaci kafin taci gaba"ki rabu dashi, kawai ,nasan barazana ce yake min,amma kinsan bazan taɓa yarda Zulaihat ta auri Adeeb ba,dan kuwa ubanta zatayi wa aiki ba muba,
Batun yarinyar da yazo da ita kuwa,na boye duk wata hanya danasan zai gane suwaye iyayenta na asali,kuma nasanya boka ya hana uwarta zuwa gasar nan ma gaba daya , Kinga har abada bazasu taba haduwa da junaba.
Abu na gaba da zamuyi shine ,da zarar anyi auren nan,zamu sa ta kashe dan banza kowa ma ya huta, zan san yadda zanyi in shawo kan wancan mugun ya yarda ayi auren saimu kashe Adeeb din"

Shiru ammi tayi tare da sauraron abinda ake fadi aɗaya bangaren.
Kafin taci gaba"wllh ƙawata Ni kaina yarinyar nan na tsaneta ,bana don ganinta,Aduk lokacin dana ganta fuskar uwarta nake gani ,kuma ina tunano abinda ya faru abaya,dan haka itama kawar da ita zanyi kowa ya huta ,duk dana ɗauke sarƙar nan Tata,amma na nemeta na rasa ,kuma banganta awuyan yarinyar ba,dan haka ina tunanin bata koma gareta ba,ƙila dai nice na sauya mata gurin ajiya na manta"
Shiru ammi ta sake yi ,kafin tace shikenan sai kinzo ma karasa maganar.
Jikin fattu banda rawa da bari ba abinda yake ,zuciyarta sai neman tarwatsewa take , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!wanann wace irin masifa ce haka,yanzu ammi tasan su waye iyayena dama ?kenan kashe Hamma zasuyi?me hakan ke nufi? kenan ammi ba itace mahaifiyar Adeeb ba?dan kuwa tasan ba ta yadda za'ayi uwa tayi yunkurin kashe ɗan ta, wai meke faruwa ne?wannan ɗin wane irin badakala ce kuma?
Tsabar rawar da jikinta yakeyi bata san lokacin data buge wani flower vase dake ajiye agefenta ba ,ya fadi kasa ,jikake toshshs!! Ya fashe .

Cikin tsoro da tazana fattu ,tayi sauri buya ajikin ƙofa tare da runtse idanunta.
Ammi kuwa da sauri ta taso Dan ganin waye yayi mata labe ,har yaji sirri ta.

Da mugun ƙarfi aka fizgi fattu akayi waje da ita ,buɗe baki fattu tayi da nufin kurma ihu,taji an toshe mata bakinta.....


Waye ya dauke fattu?
Me zai faru nan gaba?
Muje zuwa anty mammy ce

Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[30/08 14:58] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 67/68




_______________Da sauri ammi ta taso cikin tashin hankali da fargaba,dan kuwa tabbas tasan wani yaji me take cewa.

Fattu kuwa tsabar ruɗewa da shiga tashin hankali tama rasa ina zata dosa,tsoro ya cika mata zuciya ganin ammi ta nufo inda take ,saidai cikin wannan yanayin ne taji an fizgeta da mugun ƙarfi anyi waje da ita.nan take tsoronta ya kara rubanya.buda baki tayi da nufin kurma ihu ,dan atunaninta masu kashe tan ne suka kamata.saidai gam!aka rufe mata baki,bata yadda zatayi ihu.kuma cikin wani irin sauri mai kama da gudu akayi waje da ita,ta wata hanya da bata nan ta shigo ba.

Ammi kuwa tayi iyakar dubanta ,amma bata ga kowa ba,kuma tabbas tasan anshigo cikin dakin nan,to waye?dan duk ta kora yan aiki can farfajiyar gidan dan tasami damar yin wayarta.
Ko dai Adeeb ne?kai bashi bane ,dan kuwa Adeeb baya zuwa gareta ba tare da yayi sallama ba.toko nanny ce ?kai idan nanny ce zan iya cimma ta kafin ta gudu,wai waye wannan yake son shiga rayuwata ne?waye yake son bakuntar lahira kwana kusa?na rantse da Allah idan na gano ko waye saina hukuntashi, hukunci mai tsanani.yanzu dole mu sake sabon tsari dan wannan kam ya rika ya lalace"ammi ta fada cikin zafin zuciya da kunar rai.

Tana nan tsaye Zulaihat ta shigo dakin ba ko sallama,kawai ammi sai ganin mutum tayi bukut ya shigo cikin falon.guri ta nema ta zauna tare da ƙurawa ammi ido.

Harara ammi ta Banka mata tana tunanin koma dai Zulaihat ɗin ce ta shigo dazu da tasan Zulaihat ba hankali gareta ba?
"Ke Zulaihat kece kika shigomin daki dazu kina Min labe?"ammi ta fada cikin haɗe fuska.

Wani shegen kallon Zulaihat ke jifan ammi dashi,kafin ta fara magana "lallai ma ammi har kina tunanin akwai wanda zan zauna inayiwa labe?to me zan labe naji,bayan duk wani tuggun da ake ƙullawa ina sane dashi,me kuma za'a boyemin ?kinsan Ni bana munafurci kai tsaye nake Abunda naga dama "Zulaihat ta faɗa cikin rashin kunya tana wani juya ido.

Kallonta ammi tayi cikin tsantsar ɓacin rai da tsanar halayen ta na rashin kunya kafin tace " yanzu kina Min wannan gatsalin kike son na aura miki Dana?to wllh gara ki nutsu Dan bazan yarda ki auri Adeeb da wannan shegen halin naki ba,domin shirme zakiyi tayi mana,idan mun saki aiki"ammi ta fada cikin faɗa -fada.
Wata irin dariya Zulaihat tayi tana kallon ammi kafin tace "Kinga ammi ki daina min tsawa keba uwata bace,ko iyayena lallaɓani suke ,kuma da kike cewa zan bata muku aiki,ku atunaninku idan anyi auren biye muku zanyi in cutar da abin sona,?wllh garama ku nutsu daga ke har daddy na Dan kuwa rungumar mijina zanyi musha soyayya ,kuma duk wanda yayi yunkurin cutar da shi ,wllh saina kashe mutum,kinsan nima na iya dabancin"Zulaihat ta faɗa cikin gadara tana kallon ammi ido cikin ido.

Baki buɗe ammi ke kallon Zulaihat,lallai yarinyar nan ta wuce yadda suke tunani,Gara ta lallabata,karta jika mata aiki,dan haka cikin dan murmushin yake ammi tace "kai ƴata dadina dake baki san wasa ba,yanzu saiki maida abu gaske,ki kwantar da hankalinki,kinsan nima bazan taɓa bari a cutar min da Adeeb ba, dama nayi tunanin bakinsu ɗaya da mahaifi ki,shiyasa na fadi hakan"ammi ta fada cikin murmushin yaƙe tana hararar Zulaihat ƙasa ƙasa.

"Ato Gara dai mutum ya kula wllh ,dan zan iya komai akan abinda nake so"Zulaihat ta faɗa tana mai gyara zamanta zuwa kwanciya,tare da lumshe idonta kamar zatayi barci.

"Zanyi makaganinki daga ke har uban Maki shegiya"ammi ta fada cikin zuciyarta,tana shigewa daki,cike da tunanin mafita.


Ba'a dire fattu a ko ina ba, sai cikin wani daki mai dan duhu, wanda kana iya ganin mutum ,amma bazakaga fuskarsa kai tsaye ba.
Koda aka direta sam ba'asakar mata baki ba.
Fattu kuwa banda rawa ba abinda jikinta keyi,sai ƙoƙarin cire hannun mutumin take daga bakinta, ammata kasa .

Cikin nutsuwa da kwantar da hankali ya fara magana "ki nutsu ,niba cutar dake zanyi ba,koda na bude miki baki to karkayi ihu "

Cikin hanzari fattu ke jinjina kanta idonta yayi zuru zuru ,burinta kawai tajita free.
Ahankali ya dannan makunnar dake gefensa,nan take dakin yayi haske ta yadda kana iya ganin komai.

Da sauri fattu ta daga idanunta tana kallon mutumin,
"Hamma tareeƙ"ta fada cikin rawar murya,"ka bani tsoro Hamma tareeƙ,meke faruwa cikin gidan nan,wacece ammi ?meye alaƙarta da hammana?fattu ta faɗa cikin muryar kuka tana kallon tareeƙ.

Shima kallonta yake zuciyarsa na masa zafi ,yayi fatan ace Adeeb da kansa yaji wannan maganar ba wani ne yaji ba.
"Ki kwantar da hankali ki fateema,da sannu zaki fahimci komai "
Ya fada tare da ɗauko wayarsa yayi kira.

"Ummee kuzo ina nan cikin dakin baya"haka kawai ya faɗa ya kashe wayar.
Kallonsa fattu keyi jikinta har lokacin rawa yake ,tana cikin shock da zallar mamaki,kujera tareeƙ ya nuna mata tare da cewa"ki zauna anan fateema " jiki ba kwari fattu tabi bango ta zauna aƙasa ba tare da ta hau kan kujerar da tareeƙ ke nuna mata ba.zallar mamakin ammi da al'ajabi ta ke ɗawainiya da fattu,yanzu duk zaman da sukayi dama ammi tasan asalin iyayenta?kuma ita ta sace sarƙarta wacce take matsayin shaidar da zata sadata da iyayenta na asali?amma menene ribar ammi nayin hakan?wane amfani zata samu?lallai dole ta sanar da Hamma wannan maganar .
Bude kofar da akayi ke ya katsar mata da tunaninta ,da sauri cikin tsoro ta kalli bakin ƙofar,nanny ce ta shigo ita da amma.
Da sauri fattu ta mike cikin rawar jiki ta ƙanƙame nanny tare da sakin kuka mai ciwo da radadi," nanny wai zasu kashe min hammana ,kuma nima zata kasheni ,sannan tace tasan asalin iyayena ,amma bazata bari muhadu dasuba.nanny wacece ammi ?meye alaƙarta da hammana,anya kuwa itace ta haifeshi ?fattu ta faɗa tana mai dago kanta tare da kallon nanny.

Cike da tausayin fattu nanny ta riketa ajikinta Tana mai shafa bayanta ,alamun rarrashi,kafin tace "ki kwantar da hankalinki ɗiyata,ba abinda zai sameku da yardar Allah,kuma yau zan sanar dake alakar dake tsakanin Adeeb da amminsa" cewar nanny Tana me zaunar da fattu akan kujera.

Amma kuwa tana tsaye ta kafe fattu da idanu,tabbas hasashenta ya tabbata ,dan kuwa ba tun yau take zargin cewa fattu yar sarauniya suhaimat bace,dan kuwa tasha ganin irin sarƙar wuyan Fattu atare da iyalin suhaimat,bayan nan sai kayi duba na tsanake zaka gano tsantsar kamar dake tsakanin fattu da suhaimat ɗin.aikuwa insha Allahu yau ba sai gobe ba zata sanar da fattu wacece ammi.

Cikin kuka fattu ke kallon nanny kafin tace "Dan Allah nanny ki sanar dani ala'akar dake tsakanin hammana da kuma ammi,ko zuciyarta zata sami salama,ji nake kamar zan mutu,banson wani abu ya sami hammana nanny Ina kaunar hammana fiye da yadda nake son kaina idan wani abu ya sameshi wllh mutuwa zanyi"fattu ta faɗa cikin kuka mai ban tausayi.

Hawaye nanny ta goge tana mai kallon fattu kafin tace "In Sha Allahu ba abinda zai sami magajin fada ki kwantar da hankalinki ɗiyata.

Hannun fattu amma ta kamo cikin sanyin murya tace "kiyi shiru ,ki kuma kwantar da hankalinki,dan yau zaki san abubuwan da baki sani ba abaya,dan haka ki adana hawaye ki zai miki amfani nan gaba "cewar amma tana kallon fattu cikin tausayawa.

Share hawayen kuwa fattu tayi tare da kafe nanny da ido,zuciyarta na bugawa kamar ana. Kada ganga.

Ahankali nanny ta fara magana"ammi ba itace asalin wacce ta haifi Adeeb ba,amma itace wacce ta rike shi bayan ta kashe mahaifiyarsa."

Dararararmmmm gaban fattu ya bada sautin karar da saida ta kusan faduwa tana daga zaune.

Ai Ni kaina saida na tsorata na jefar da wayar nan dan tsoron jin abinda nanny zata faɗa .

Muje zuwa masoyan fattu da Adeeb .

Sai mun haɗe anjima in Sha Allahu.

Anty mammy ce

Mrs babi 💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[30/08 14:58] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE 🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)


Elegant online writers📚📚



Free book

Page 69/70




___________Ahankali nanny ta fara magana ,tana cewa"Ammi ba ita bace asalin mahaifiyar Adeeb,amma itace wacce ta rikeshi bayan ta kashe mahaifiyarsa."

Dararrararaammm!!!gaban fattu ya bada ƙara, sakamakon jin maganar nanny datayi kamar saukar aradu,
Da sauri ta dafe gefen kujerar da take kai,dan ji tayi kamar zata faɗi.
Baki buɗe take kallon nanny cike da tsantsar mamaki,cikin rawar murya tace "nanny kina nufin ammi itace ta kashewa Hamma mahaifiyarsa?to amma me yasa Hamma yake mata kallon uwa?me yasa bai dauki mataki akanta ba?"fattu ta faɗa cikin rudani.

Ajiyar zuciya nanny tayi kafin tace "saboda bashi da masaniya akan abinda ya faru,kuma ya yarda da ammi fiye da kowa,dan yana mata kallon uwa mahaifiyane,baya tunanin zata taba cutar dashi.ki saurare Ni da kunnen basira ,zaki ji abinda ya faru yanzun nan.

"Sarauniya Nazli,ƴace agurin ƙarin baban mai martaba uwa daya uba daya,wato kenan ita da mai martaba ,yan uwan juna ne ,dan kuwa auren zumunci akayi musu.
Suna kaunar juna matuka bayan anyi auren,suna zamansu lafiya cikin so da aminci, lokacin da akayi auren nasu,iyayen sarauniya Nazli duk sun rasu,hakan yasa take zaune a hannun mahaifiyar mai martaba ,dalilin hankali da nutsuwarta yasa mahaifiyar mai martaba ta zaba masa ita matsayin matar da zai aura inda ranar da aka daura musu aure aka naɗa shi matsayin sarkin misra.

Shekara guda dayin aurensu Allah ya azurtata da zamu yaro , kyakykyawa abin so ga kowa, ranar suna aka rada masa suna adeeb.

Adeeb ya taso cikin so da kauna, agurin iyayensa, da ma duk wani wanda yake fadar nan,yana da matukar hakuri ,hazaka ,ladabi da kuma biyayya.
Nice wacce ke rainon Adeeb ,kasancewar mijina yana aiki acikin fadar nan,shine drivern dake tuka sarki da iyalinsa.
Lokacin ina goyon dana tareeƙ ,dan haka na hadasu duka ina rainonsu,saidai ko da wasa ban taba hada tareeƙ da Adeeb matsayi daya ba,duk lokacin da zanyi musu wani abu saina farayiwa Adeeb,sannan nake yiwa tareek,ko wasa suke yi nakan sanya Adeeb matsayin shugaba ne tareeƙ kuma bafadensa.hakan yasa suka taso cikin kaunar juna da girmamawa,dan kullum nakan nusar da tareeƙ cewar Adeeb ɗan sarkine kai kuma dan bafaden sarkine,dan haka kada ka haɗa kanka da Adeeb .

Sosai shakuwa ta shiga tsakanin Adeeb da tareeƙ,dan kuwa ko gurin sarki Adeeb zaije to dole saida tareeƙ ,kuma tun lokacin ƙuruciya tareeƙ ke kiran Adeeb da yallaɓai.
Muna jin dadin zama da sarauniya Nazli,dan kuwa macece mai matukar girmama dan adam,ba ruwanta da nuna isa ko iko,akan kowa ,tana janmu ajikinta sosai ,hakan yasa kowa ke kaunarta cikin masarautar nan.

Kwatsam batun karin auren mai martaba ya taso,kuma auren zaiyi shine da mata biyu a lokaci daya, dayar ƙánwar abokinsa ce wato amma,dayar kuma yar abokin babansa wato ammi. ko kaɗan sarauniya nazli bata tada hankalinta ba,koda mai martaba ya nuna tayi hakuri,shima bada son ranshi zaiyi auren ba ,nuna masa tayi ma tafi shi farin ciki tayi masu fatan alkairi ,duk da kuwa can ƙasar zuciyarta tana jin kishi da zafin abin aranta,amma haka ta daure ta nuna ba komai.

Bayan anyi bikin mai martaba da matansa guda biyu,da farko ana zaune lafiya kowa na ba kowa girmansa,sai kuma abubuwa suka zo suka fara lalacewa,yau kaji wannan maganar gobe kaji waccan.ammi itace wacce ke haddasa komai,sam bata son zaman lafiya ta cika gutsiri tsoma,amma sarauniya Nazli bata kulata ,dan kuwa lokacin tana fama da laulayin cikinta na biyu.
Amma ce ma ke dan maida mata martani,
Kullum amma na zuwa gurin sarauniya Nazli tana kula da ita, sosai suke zaman lafiya a tsakaninsu ba gutsiri tsoma ko kaɗan,hakan kuwa ba ƙaramin bata ran ammi yake ba ,dan ita burinta kawai ta farraka su.

Lokacin da sarauniya Nazli ta zo haihuwa kuwa ,cikin nasara ta haifi yaranta tagwaye duka mata, Masha Allah,karkuzo kuga kyau garin yaran nan,sosai kowa ke murna da samun yan yaran nan,
Adeeb yana bala'in kaunar ya'yan nan,kullum yana kusa dasu yana musu wasa,shida tareeƙ ,wani lokacin hana daukar yaran ma suke,idan za'a daukesu suyi ta kuka kar'a taba musu kannai.kuma daidai lokacin ne amma ta fara laulayi itama.
Sosai mai martaba yake jin dadin zama da matansa ,dan kowa na kokarin kyautata masa.koda labarin cikin amma ya sameshi yayi murna sosai .
Wayyo ai tunda ammi ta kyalla ido ta gano ciki jikin amma,hankalinta yayi magun tashi,ya za'ayi haka ?an aurosu tare amma ita har yanzu ko batan wata bata taba yi ba?ina da sake wllh saita zubar da cikin Nan.shikenan saisuyi ta haihuwa ,su gaje masarautar ita ko oho?
Ba irin abunda ammi batayi ba akan cikin rashad ya zube,amma hakarta bata cimma ruwa ba.

Haka aka haifi Rashad , kyakykyawa dashi ,suna matuƙar kama da Adeeb,Adeeb yana son Rashad fiye da yadda yake san twince husna da haseena,kullum yana tare da Rashad shida tareeƙ ,barci ne kawai ke rabasu.

Hakan yana dagawa ammi hankali,tun daga nan saita fito da sabon salo, wato ta fara jan yaran ajikinta,da farko sam Adeeb bai saki jiki da ammi ba ,dan shi irin yaran nan ne miskilai,idan Kinga dariyarsa to shida tareeƙ ne ko mai martaba da mommansa ,ko kuma ni,sai kuma Rashad da amma .
Saidai yana da yawan kyauta ,yanzun nan zai baka abu yace na kyauta na baka,hakan yasa kowa ke kauanarsa sosai,
Kusan tunda ga lokacin wasu da yawa ke kiransa da magajin fada,ciki kuwa hardanki.ciki kuwa harda Ni.
Amma kasancewar ammi makirar mace ,ta san ta yadda zata ja hankalin mutum ,sai Adeeb ya fara yarda da ita,harta kai ta kawo yana kwana anan bangarenta.daga wannan lokacin ne kuma Adeeb ya fara tsiro da wata halayyar sam baya son Rashad yazo inda yake ,lokacin Rashad yana rarrafe,wai zai bata masa jiki,saidai idan shi yaga dama yayi masa wasa .

Wata rana mijina ya dawo gida hankalinsa atashe,koda na tambayesa lafiya ?meke faruwa?nagansa cikin tashin hankali .nan yake sanar dani cewar ,yau ya kai ammi anguwa ,yana zaune yana jiranta, bata fitina, kawai saiya dan zagaya dan ya ware ƙafarsa ,yana zuwa saitin window yaji tana magana da wani mutum, kuma suna tattaunawa ne akan yadda zasu kawar da Adeeb harda tareeƙ,sannan yaji tana sanar da mutumin cewar aiki yayi kyau,dan yanzu sam Adeeb baya kaunar Rashad,baya son Rashad yazo koda inda yake ne.yanzu abinda take so shine a cire musa mahaifiyarsu daga ransu,ta yadda sai abinda tace suyi zasuyi,
Tana son saita lalata musu tarbiyyar sun zama abin kwatance ,sun haddasawa iyayen su ciwon zuciya sun mutu,kafin ta kawar dasu,inya so ta gaji dukiyar mai martaba ita kadai.

Hankalina yayi matuƙar tashi lokacin dana ji wannan maganar ,nan take na fara kuka ,ya zama dole na sanar da iyayen yaran nan,su kula da ƴaƴansu,
Amma nasan sarauniya Nazli,koda na faɗa mata ,ita macece mai hakuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login