Showing 75001 words to 78000 words out of 116224 words
nanny tayi masa,ace wai nanny ta hada kai da maƙiyarsa tana tayata ƙoƙarin cutar dashi,matar daya ɗauka matsayin uwa ?mutum kenan.
"Ko kaɗan nanny bana fushi dake,kawai ina godiya ga Allah ne ,daya nunamin gaskiya ,na gane irin mutanen da nake tare dasu,na daukeki tamkar mahaifiyata nanny,Amma bansan nayi babban kuskuren yin hakan ba,dan Allah kiyi haƙuri"ya faɗa yana mai haɗe hannayensa guri ɗaya alamun neman afuwa.
Sosai nanny kejin ciwo cikin ranta ,damuwa da taraddadi sun cika mata zuciya,dama tayi wannan tunanin,tasan idan har Adeeb ya gansu tare da amma ,to shikenan,kuma kome zata faɗa masa bazai yarda da ita ba,amma Allah shine shaida bata da nufin cutar da Adeeb ko kaɗan.
"Magajin fada wllh abinda kake zargi ba haka bane ,kada ganina tare da amma yasa maka kokwanto akaina, wllh nima Ina jinka tamkar tareeƙ bazan taɓa cutar dakaiba magajin fada.
Nanny ta faɗa cike da damuwa aranta.
Girgiza kai kawai Adeeb yayi tare da barin gurin,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa .
Kallonsa kawai nanny keyi,tana fatan Allah yasa ya gane gaskiya cikin sauri kafin komai ya daɗa lalacewa.
Ba kowa cikin falon ammi,sai ƙamshi dake tashi ta ko'ina ,dan ammi akwai son kamshi,kai tsaye ya nufi dakin kwananta, nocking yayi amma shiru,hakan yasa shi shiga cikin dakin kai tsaye.saidai nan ma ba kowa cikin dakin.
Harya juya zai fice ,sai kuma zuciyarsa ta raya masa ya duba wanann akwatin da yaji ammi na magana akanta.
Dan haka juyowa yayi yana karewa dakin kallo.
Ahankali yake duba dakin dan neman wannan akwatin,amma yayi iyakar dubansa bai ganta ba.
Harya hakura sai kuma ya hango wata akwati mai kyau da ɗaukar ido,yasan akwatin Dan acikinta ammi ke ajiye kwalakwalanta ,dan haka sai yayi tunanin ba komai cikinta, har ya juya da nufin barin dakin,sai kuma zuciyarsa ta kwadaitu da son duba akwatin .
Dan haka ahankali ya zauna tare da ɗauko akwatin, danna lanbobin bude akwatin yayi,dan kuwa tuni yasansu, aikuwa saiga akwati ta bude,gwalagwalai ne acikinta iya ganin ka ,masu kyau da ɗaukar hankali,kallo ɗaya zaka musu kasan an zubar da maƙudan kudade wajen mallakar sarkokin.
Dubawa yayi tayi amma baiga komai aciki ba,sai wani dan karamin akwati mai kyau da ya gani,kallon akwatin yake da mamakin meye acikinsa aka wareshi ?lallai yana son ganin abinda ke ciki.dan haka hannu Ya mika tare da ɗauko akwatin ya bude.
Mamaki ,al'ajabi ruɗu da kuma faduwar gaba sune suka ziyarci zuciyar Adeeb,sakamakon ganin sarƙar nan ta Hulwa data bace ,cikin wannan akwatin,
Me yakawo sarkar Hulwa cikin kayan ammi?har akayi mata adana ta musamman?me hakan ke nufi,shidai yasan ammi tana da sarkokin da suka ninka kudin wannan bare yayi tunanin ta daukene dan bata da mai tsada kamar wannan ,to me hakan ke nufi kenan?innalillahi meke faruwa ne acikin gidan nan?kodai akwai Abinda ammin nashi ke kullawa da gaske ? Wayyo ina zaisa kansa ?dawa ya kamata ya yarda ne cikin fadar nan? Dauko sarƙar yayi cikin sauri ya maida komai inda yake sannan yayi saurin barin dakin na ammi ya koma part dinsa. Zuciyarsa na zafi kamar zata kama da wuta .
Lokacin daya koma part din nasa fattu ta farka,tana zaune tana kuka,tsoro takeji,har lokacin barin ma dataga ita kadaice cikin dakin,ina Hamma ya tafi ya barta?karfa wannan Rashad din ya dawo mata? Gashi wannan innar ma bata dawo ba,wannan tunanin yasata ƙanƙame jikinta tana kuka.
Adeeb kuwa cikin wani irin yanayi na sarewar zuciya ya shigo cikin dakin,abubuwa sunyi masa yawa cikin zuciyarsa,jinsa yake kamar bashiba, kansa banda ciwo ba abinda yake ,wai meke shirin faruwa da rayuwarsa ne ?me hakan ke nufi ?me amminsa ke nufi da ɗauke sarƙar Hulwa?
Kukan hulwar da yaji Yone yasani saurin ƙarasawa cikin dakin.
Tana jin motsi sa ta zabura atsorace tana mai kallon ƙofar dakin.ganin Adeeb ne ya shigo yasata saurin yunkurawa ta mike da gyar tana kuka tare da kallonsa.
Da saurinsa ya ƙaraso inda take ,yana zuwa ya kamo hannunta tare da shafa gefen fuskarta yace "menene kike kuka?inane yake miki ciwo ?ya faɗa cikin mugun sanyin murya ,wanda har saida fattu ta ɗago kanta ta kalleshi,
Idanunsa sunyi jajur sosai jijiyoyin kansa sun fito rudurudu,fuskarsa tayi jajur ,kana gani kasan yana cikin damuwa da tashin hankali.
Cikin kuka fattu ta faɗa ƙirjinsa ta rungumeshi, tana faɗin "tsoro nakeji Hamma ,ko ina ganin ƙaninka nake yana min gizo Hamma" ta fada cikin kuka tana ƙanƙame Adeeb.
Cike da tarin damuwar da baisan menene mafitarta ba shima ya ƙanƙame fattun ajikinsa yana mai lumshe ido da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi,
Ahankali yake faɗin"kiyi haƙuri Hulwa , dagani harke muna cikin damuwa, Hulwa komai bayamin dadi na kasa gane dawa ya kamata in amince cikin fadar nan,Hulwa kowa na fadar nan so yake yaga bayana bansan me na tsare musu ba" Adeeb ya faɗa cikin murya mai tattare da karaya da sarewa.
Shiru fattu tayi tana sauraron abinda yake fadi,ita fa sam bata fahimci inda zancen sa ya nufa ba,ahankali tace "Hamma ,su waye ke son kamin bayanka"?
"Shiru yayi yana mai kara rungume fattu ajikinsa,dan sosai yake jin nutsuwa na samunsa sakamakon rungumeta da yayi,zuciyarsa tana yi masa sanyi .shafa gashin kanta kawai yake bai ce komai ba.
Kusan minti biyar suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin zareta daga jikinsa ya zaunar da ita abakin gado,kallonta yake ,har zuwa lokacin idanunta basu koma yadda suke ba,akwai kumburi da kuma dan jaa kadan acikinsu.
Hannunta ya kamo cikin nashi ya rike gam-gam yana kallonta.ji yake kamar ita kadai ta rage masa wacce zai fadawa damuwarsa,saidai fattu yarinyace,idan ma ya faɗa mata damuwarsa bazata fahimci me yake nufiba.
Kallonsa fattu tayi itama,tabbas akwai Abinda ke damun hamman nata,ko menene oho."Hamma meke danunka?baka da lafiya ne ?ta fada cikin muryar marasa lafiya ,wadanda suka sha kuka.
Ahankali ya koma kusa da ita ya zauna ,kallonta yayi yace "Hulwa abinda ke damuna yana da yawa,ina cikin wata sarkakiya wacce Allah ne kawai zai fitar dani,bani da wanda zan fadawa damuwata ahalin yanzu,bana son sanar da abie na komai,dan gudun ɓacin ransa,saboda tsoron kar ciwonsa ya tashi,kiyi ta min addu'a kinji hulwatee" Adeeb ya faɗa yana mai riƙe habar fattu tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa.
Cike da tausayawa fattu ke kallon Adeeb,kafin itama ta sanya hannunta akan fuskarsa tana shafa gefen fuskar tashi, kamar yadda yake mata .sannan tace "Hamma zanyi ta maka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, kuma kaima kayi ta addu'a Allah maji rokon bawansa ne ,Allah ya bawa abie lafiya Hamma,amma me zai hana ka sanar da innarka itama ta tayaka addu'a" fattu ta faɗa bayan ta cire hannunta daga kan fuskar Adeeb.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Adeeb ya sauke lokacin da fattu ke shafa gefen fuskarsa ,ahankali ya lumshe idanunsa yana jin wani irin sanyi yana Ratsa zuciyarsa.
Ahankali ya bude idonsa lokacin da yaji ta cire hannunta daga kan fuskarsa.kafin yace "Hulwa ammina tana daga cikin mutanen da nake son boyewa damuwata ,ahalin yanzu bazan iya sanar da ita komai daya danganci lamarinaba,ke dai kiyi ta min addu'a kinji"ya faɗa cikin murya mai cike da ban tausayi.
Sosai fattu kejin tausayin hamman nata yana Ratsa zuciyarta.ahankali ta ɗora kanta gafen kafadunsa tare da rungumoshi ta gefe.tayi shiru cike da tunanin meke damun hamman nata.
Ahankali shima ya dora kansa akan nata kan yana jinsa tamkar marayan da bai da kowa.
"Hamma wannan innar bazata dawo ba ko?" Ta fada ahankali idanunta alumshe.
Shima idonsa alumshe yake yana shafa kan fattu ,yace "kina so ganinta ne?
"Daga kai tayi alamun eh sannan tace " eh Hamma ina son ganinta ,ina kaunar ta har cikin raina ,kuma tace daga yau itace inna ta"
Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin yace " Hulwa ita kadai kike kauna ? Ni baki kaunata?ya faɗa ba tare da yasan ya fadi hakan ba .saida ya faɗa sannan ya fahimce me yace .
"A'a Hamma ina ƙaunarka sosai mana,ina sonka,kaidin kamar baffana kake ,bani da kowa saikai, Hamma bana son wani abu ya tab aka ma" ta fada tana ɗago kai tare da kallon Adeeb.
Cikin wani irin farin ciki da jin dadi Adeeb ke kallon fattu,zuciyarsa cike da jin dadi yace "da gaske kike Hulwa?" Ya faɗa cikin murmushi yana kallonta.
Jinjina kai tayi itama cikin murmushi tana kallonsa.
Ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta gamm yana mai lumshe ido , sosai yake jin wani irin. Daɗi da Nutsuwa cikin zuciyarsa.
"Kina son ɓata min shiri ko ?,kisani wllh idan kikayi wani kuskuren dana rasa damata,kema zaki karbi naki hukuncin ,kin sanni kinsan halina,kuma kinsan abinda zan iya aikatawa ,dan haka ki kula da kanki,komai yana ƙoƙarin lalacewa saboda sakacinki,to bazan laminci wannan abinda kike yiba.wllh zan aikaki gurin da duk wanda zai zamenin matsala nake aikawa.akan wannan karagar zan iya batar da kowa"
Wani mutum ne daya lulluɓe ilahirin fuskarsa ke fadin wannan maganar cikin ɓacin rai yana kallon ammi,wacce ke tsaye cikin tsantsar tsoro ,jikinta sai rawa yake cikin tashin hankali tace "dan Allah kayi hakuri ,wllh ina yin iyakar ƙoƙarina akan wannan abun ,kuma aKwai shirin da nake yi ,karka damu ka kara hakuri "ta fada cikin rawar murya,tana kallon mutumin da baka ganin komai bace kwayar idanunsa.
Cikin fushi mutumin ya damƙi wuyan ammi ya hadata da jikin bango yana faɗin"bana son jin komai daga bakin ki kawai ki aikata abinda nace miki ,ki tabbatar ya bar duniyar nan nanda lokaci kankani,zan kawo miki abinda zaki saka mishi acikin abinci,zai mutu kuma ba wanda zai zargi wani abu,idan kuma aka samu kuskure .yayi shiru tare da sakin wuyan ammi wacce ke kakari tana kokarin shekawa.
Tari sosai ammi keyi,lokacin da mutumin ya saki wuyanta sannan yayi tafiyarsa cikin sauri yana ƙara gyara rufin fuskarsa.
Saida ammi ta samu nutsuwa kafin ta bar gurin ,kai tsaye dakinta ta nufa ,gaba ɗaya awahale take,
Bakin gado ta zauna cike da damuwa tana tunani,can dai ta dauko akwatin sarkokinta,abin yayi matuƙar tsorata ta lokacin datayi arba da akwatin sarƙar fattu ba komai acikinta.
Wani dan gajeren ihu ta kwalla cikin tashin hankali,tana dube dube cikin akwatin ,waye ya daukemin sarƙar nan?na shiga ukuna wayyo ni ammi .da sauri suhaimat ta shigo dakin ammi ,dan kuwa taji ihun da ammin ta kwalla."uktee lafiya ?naji kina ihu?suhaimat ta fada cikin damuwa tana rike ammi.
"Ba komai suhaimat na Dan bugene "ammi ta fada cikin tashin hankali.
Kallonta suhaimat keyi cikin rashin yarda da abinda ya fada,amma koma dai menene tunda taki faɗa shikenan .
"To mukam muna ta shiri anjima jirginmu zai tashi .zanje in Kara duba yarinyar can "suhaimat ta fada tana kallon ammi.
"Karkije suhaimat ,karkije,na roƙeki,ki rufamin asiri karkije "ammi ta fada cikin tashin hankali tana kama hannun suhaimat.dan tana tsoron kar ace sarƙar ta koma gurin fattu ne kuma suhaimat ta gani ta gane yarta.
Cike da mamaki suhaimat ke kallon ammi,anya kuwa kalau take?ji yadda ta wani rikice daga cewa zani ganin yarinyar can.
Kai gaskiya akwai wani abu aƙasa.
Cikin hade fuska suhaimat tace "uktee ki fadamin menene dalilinki da baki son na haɗu da yarinyar can?me kike kullawa akanta ?menene hajjarki ? suhaimat ta fada cikin haɗe rai tana kure ammi da ido.
Zato ido ammi tayi tana kallon suhaimat ,kafin cikin in Ina ta fara magana "su...haim..at ......
Hmmmmm muje zuwa masu karatu.
Mrs babi ce💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
[30/08 14:58] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 65/66
________________"Ki sanar dani dalilin da yasa baki son zuwana gurin yarinyar nan?
Me alaƙarki da ita ?ko ince me ta tsaremiki uktee?
Sarauniya suhaimat ta fada cikin haɗe fuska ,dan tasan kadan daga aikin ammi ta hanata zuwa gurin fattu.
Zaro ido ammi tayi tana mai kallon suhaimat ,dan sai lokacin ta fahimci tana kokarin bada kanta,cikin in-ina ta fara magana "su...hai..mat,wane dalilin ne zaisa kuwa in hanaki zuwa gurinta?kawai ina gudun ace ko wata munaƙisar muka ƙulla yasa kike ta zarya,kinsan tunda wannan abun ya faru to komai ma laifi zai zama , amma bayan wannan bani da wani dalili"ammi ta fada tana kafe suhaimat da idanu.
Murmushi suhaimat tayi ,kafin tace "Indai dan wannan ne karki damu ,ai kowa yasan Ni likitar matace,kuma ba laifi bane idan naje duba marar lafiya,kuma ma mace"suhaimat ta fada cikin yanayi na rashin damuwa.kafin ta juya ta bar ɗakin.
Harara ammi ta biya da ita ,kamar idanunta zasu fado ,haushin suhaimat takeji fiye da tunanin mai tunani,wllh badan tana tsoron faruwar wani abu ba ,data gama da suhaimat ,dan itace silar shigar ta ko wace irin damuwa.amma ba komai muje zuwa sannu sannu bata hana zuwa,saidai dade ba'ajeba.
koda sarauniya suhaimat ta koma bangaren Adeeb, kwance ta tarar da fattu adaki, idanunta alumshe kamar mai barci,yayinda Adeeb ke falo yana amsa waya.
Bayan sun gaisa yake sanar da ita fattun tana cikin daki, dan sosai yake jin dadin yadda take kula masa da fattu.
Tana shiga fattu ta buɗe idonta,da sauri sakamakon jin muryarta,dan dama tana kwancen nan, tunaninta Sarauniya suhaimat kawai take.
Da murna ta tashi zaune tana murmushi,tare da kallon suhaimat,
Itama cikin farin ciki ta karasa gareta ta zauna.
Ahankali fattu tace "inna nayi tunanin bazaki dawoba,ina ta tunaninki araina"ta fada fuskarta ɗauke da annuri.
Shafa fuskar fattu tayi kafin tace "ƴata kenan ,tunda nace zan dawo ,ai dole na na dawo naga kaykykyawar fuskar nan taki,ya jikin naki"suhaimat ta fada cikin murmushi.
"Da sauki "cewar fattu.
"Masha Allah,haka ake so ki kula da shan magungunanki kinji"cewar sarauniya suhaimat.
Jinjina kai fattu tayi kafin tace "ina yan biyu "
Murmushi suhaimat tayi kafin tace "suna can suna shiryawa ,Basu san nazo nan ba da kin gansu sun biyoni, dan sun damu dake sosai" ta fada cikin murmushi.
Fattuna murmushin tayi, tana wasa da ƴan yatsunta.
Sun jima suna hira da fattu,duk da tana ɗan jin kunyar sarauniya suhaimat din,amma zakayi mamakin yadda ya sake suke ta hira ,harda dariya .
Anan ne take sanar da ita cewar yau zasu tafi garinsu.
Lokaci guda fattu ta shagwabe fuska kamar zatayi kuka,
"Ayya inna meyasa zaki tafi?dan Allah ki zauna anan,bana son ki tafi "fattu ta faɗa tana mai kallon sarauniya suhaimat.
Ahankali suhaimat ta kamo hannun fattu ta rike cikin nata tana ɗan murmushi,duk da itama sam batason rabuwa da Fattun,amma dan ta kwantar mata da hankali sai tayi murmushi tace"karki damu my princess ai zan rinka zuwa ina ganinki,kuma wataran zance yarima ya kawomin ke muyi hutu,ko bazaki zoba"?ta fada tana kallon fattu.
"Zanzo mana inna dama bana son zama agidan nan tsoron wannan mai kama da hamman nawa nake"ta fada cikin yanayi na damuwa, idanunta har ya kawo kwalla.
Cikin damuwa itama suhaimat ta tallafi kumatun fattu,tana mai cewa"ki kwantar da hankalinki ƴata, ba abinda zai miki kinji,ki daina tsoronsa,yanzu haka yana can akwance cikin halin mutuwa da rayuwa,kuma hammanki yana tare da ke"ta fada cikin salon kwantar da hankali.
Jinjina kai fattu tayi tana mai kallon suhaimat ɗin.
Murmushi suhaimat tayi tana mai kallon wayarta dake ringing ,lokaci ta duba taga harta kara minti biyar akan time ɗin da zasu tafi,dan ma private jet ne.kuma mijinta bai sami halartar gurin ba saboda wani meeting da suke mai muhimmanci.
"To ƴata zan tafi saina ƙara dawowa zan dawo mutafi tare dake ,kinji"suhaimat ta fada tana jin ba dadi cikin ranta,ji take kamar zata rabu da abu mafi muhimmanci arayuwarta.
Ahankali fattu ta daga mata kai, idanunta na zubda kwalla,sam bata son suhaimat ta tafi,"Allah ya tsareku,ya kaiku lafiya inna ,saikin dawo"fattu ta faɗa tana ɗan kwantar da kanta jikin suhaimat.
Rungumeta suhaimat tayi cikin alhinin rabuwa da ita .Adeeb ne ya shigo dakin da sallamarsa,da alama wanka yayi dan ya cire kayan dazu ya sanya riga da wando blue and white yayi matuƙar kyau sosai,sai ƙamshinsa yake kamar kullum.
Kallonsu yayi yadda ko wanne ke zubda kwalla ,lallai lamarin Allah abin kallone,dubi yadda lokaci ɗaya shakuwa ta shiga tsakanin bayin Allahn nan?kamar sunsan juna.murmushi yayi yana kallon suhaimat kafin yace "anty suhaimat har yanzu kina nan da tausayi da kuma saurin kuka " ya faɗa yana kallonta.shikam tun sanin da yayi mata haka bakinta yake ,akwai tausayi da son mutane bata da kyamar dan adam.
Share hawayen idanunta tayi kafin tace "prince wllh da zaka bani yarinyar nan dana tafi da ita can Ghana munyi zaman mu ,dan Allah ya doramin kaunarta cikin raina sosai" ta fada tana shafa kan fattu.
"In baki ita ku tafi?Ni kuma inyi yaya,haka kawai ,ki tafimin da mata?inaaa"Adeeb ya faɗa cikin zuciyarsa.amma zahiri saiyace "karki damu watarana zata zo "
"Allah yasa da gaske kake,yanzu dai kayi mana hoto dan tarihi"sarauniya suhaimat ta fada tana mai janyo fattu jikinta.
Luuuf!! fattu tayi ajikin suhaimat tana mai jin wani irin sanyi acikin zuciyarta.hotuna Adeeb yayi musu kusan kala biyar awayarsa, hakama yayi musu awayar Sarauniya suhaimat ɗin.
Da gyar suka rabu da juna cikin kewa da kaunar juna, fattu sai kuka take ta rungume Adeeb lokacin da suhaimat ta tafi rarrashinta yayi tayi da gyar ya samu tayi barci.
Ammi kuwa sosai taji dadin tafiyar suhaimat,dan hankalinta sam bai kwanta ba ,gani take kamar zata iya gano wani abu game da fattu
Yanzu damuwarta daya shine yadda ,zata bullowa lamarin Adeeb.
Rashad ya farfaɗo ,saidai gaba ɗaya ankasa gane kansa ,dan kullum haka zaka ganshi shiru baya magana saidai kallo,abin yana matukar damun amma,haka zatayi ta kuka tana kallonsa,saidai kawai kaga hawaye yana bin fuskar Rashad din,ya rame sosai,dan baya wani cin abinci,ga karaya ajikinsa ta ko ina likitoci suna ta binciken kwakwalwarsa dan suna tunanin tanan ya sami matsala.saidai muce Allah ya bashi lafiya.
Sam yanzu Adeeb baya kula tareeƙ ,haka zai zo yayi ta bashi haƙuri amma Adeeb bazai ce masa ko ci kankaba.duk da yadda yayi kewar tareeƙ ɗin cikin zuciyarsa.
Abin yana yiwa tareek ciwo ,haka zai je gurin nanny yayi ta kuka ,saidai tabashi hakuri.
Alhamdullah jikin fattu ya warke sosai,dan duk tabon ciwukanta ma babu,sosai shakuwa ta kara shiga tsakaninta da Adeeb,dan kuwa ya dawo da ita bangaren sa gaba ɗaya ,ya siyo mata sabbin kayan sawa ,da duk wani abu datake bukata.
Yayin da gefe guda yake ci gaba da bincikensa akan al'amarin su Nazli da kuma sarƙar nan ta fattu,akan ammi ,saidai har yanzu ya kasa samun wata kwakwkwarar hujja da zai kama ammi da ita .dan haka ya kara yarda cewar hadin bakine na amma da nanny ,suke son hadashi da ammi.
Bangaren rashad kuwa ,abin ba'acewa komai,dan har yanzu yana nan jiya iyau, baya uhhhm bare uhm -uhm .magani ta ko ina yi masa ake ,mai martaba da