Showing 18001 words to 21000 words out of 116224 words
daina jin wannan azabar da kuma yanayin dake bibiyar ilahirin jikinsa.
Kusan minti biyar fattu na tsaye kanta aƙasa ,jifa jifa tana share hawayen dake zubowa daga idanunta.aranta kuwa cewa take "wannan hamma wllh baida kirki ,san ba bakinsu ɗaya da macijina ba,dubi yadda nayi masa magana ya wani shareni.
Shikuwa Adeeb yana kwancene yana ci gaba da ambaton sunan Allah,harya samu marar ta kafa masa ,sai wani uban gini dake karo masa agishinsa ,duk da sanyin a.c dake ɗakin hotel ɗin.
Ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya yana ɗan kumshe idanunsa.kafin ya tashi zaune yana mai dafe da kansa.
Ganin ya tashi zaune yasa Fattu ɗan ja da baya,dan ita tsoronsa ma takeji yanzu ,dan wllh da gani masifaffene.
Kallon gefen ta yayi ba tare da ya lalle ta kai tsaye ba,sannan ya ɗan ja tsaki yana mai yamutsa fuska da turo baki,kamar wani mace ,sannan ya miƙe ya shiga bayin ,ruwan wanka ya haɗa mata cikin boket dan yasan ba iya shiga kwamin wannan zata yi ba, sannan ya ɗauki sisi da sabulu ta ajiye mata .ya ratsa makilin acikin sabon burush sannan ya ɗan leƙa cikin ɗakin .tana tsaye kamar gunki ,har lokacin share hawaye take ,kumshe ido yayi yana mai cewa, wannan ta cika kuka ,cikin ransa.
Kafin ya buɗe baki ahankali yace "zo" ya faɗa kamar baya so.badan Allah yasa Fattu mai saurin ji bace da bazata ji me yace ba.
Ahankali take takowa cikin yanayi na tsoro,dan dai tana tsoron masifarsa ne da ba abinda zai sa ta koma wannan ɗakin da ake ruwan jini.
Shiga tayi tare da tsayawa tana kallonsa.jikin sink ya matsa tare da miƙa mata burush ɗin yana mai cewa "oya wash your mouth"
Shiru fattu tayi tana kallonsa tare da kallon burush ɗin data karɓa daga hannunsa.
Kallon ta yayi shima fuska aɗaure yace "wanke baki" ya faɗa cikin ƙosawa ,yana jinjina ƙauyanci irin na fattu wai ko burush bata sani ba.
Ita kuwa fattu kallonsa tayi tare da kallon burush ɗin ,cikin ranta tace ikon Allah ,su nan da wannan abun suke wanke baki,mutuwa saidai hawaye da gishiri.ƙara kallonsa tayi suka haɗa ido,da sauri kowa ya kawar da kansa ,cikin shagwabar da fattu batasan tana da ita ba tace "hamma Ni ban iya wanke baki da wannan ba"ta faɗa tana miƙa masa burush ɗin.
Wani yarrrrr yaji ajikinsa, saboda salon yadda tayi maganar ,saiyaga kamar da gangan take wani abun.harara ya salla mata kafin ya karɓi burush ɗin yace "open your mouth"
Gurun fattu tayi tana kallonsa ba tare da ta buɗe bakin ba.
Runtse ido yayi cikin ciwon rai yace da ɗan ƙarfi"haaaaaa"ya faɗa yana bude dan madaidaicin bakinsa.
Buɗe nata bakin tayi kamar yadda taga yayi, wanda yake nan ɗan mitsitsi kamar gidan tsutsa ,haƙora ta farare tass dasu,ajere reras.
"Masha Allah "Adeeb ya faɗa cikin rashin sanin ya furta hakan.
Saida ya faɗa kafin ya ankare.kallon fattu yayi suka haɗa ido,harara ya watsa mata yana mai cewa"kaki cinyeni da wannan lulu eyes ɗin naki"Adeeb ya faɗa yana mai sanya burush ɗin cikin bakin fattu.
Ahankali yake wanke mata haƙoran nata masu kyau da ɗaukar hankali,yana wanke wa yana kallon fuskarta,ita kuwa ta rufe idanunta ƙam!wani irin takeji bakin nata,gashi abun da shegen zaƙi, anya kuwa ba abin sha bane ya manta yace na wanke baki ne?
Aikuwa wllh saita ɗan sha taji ya faɗinsa yake.Adeeb bai sankara ba kawai yaga ta tattara kumar bakinta ta haɗeye ƙut!
Zaro ido yayi tare da buɗe baki cike da mamaki yace "what!!" Kin shanye kunfar?oh my God" ya faɗa yana zare burush ɗin daga bakinta.
Yace "oya fito dashi"ya faɗa yana zare mata idanu.
Shagwabar fuska fattu tayi kafin tace "ai na shanye zaƙi gareshi" ta faɗa tana mai sunkuyar da kanta.
Girgiza kai kawai Adeeb yayi,baice komai ba ya kunna fanfo yace ta tara ta kuskure bakin,
Hannu ta saka ta tari ruwan sannan ta kuskure bakinta.wani fayau taji bakin nata yayi ,sosai taji yayi mata daɗi ga kamshin strowberry da bakin keyi.
Nuna mata ruwan wanka yayi yace tayi wanka ,yanzu ta fito yana jiranta.
Kai ta daga masa,tana nufar gurin da boket ɗin yake ajiye.
Harya kama handle ɗin kofar sai kuma ya juyo yace "kiyi alwala anan"ya faɗa yana nuna mata jikin sink din tare da ficewa.
Zama yayi abakin gado bayan fito daga toilet ɗin ,haka kawai yaji yana cikin farin ciki,sai murmushin yake,abinda ba al'adar shi bace yawan fara'a.
Fattu kuwa ko minti biyar batayi ba ,sai gata ta fito sanye da Kayan ta data cire .
Kallon ta Adeeb yayi yace " ina kayan dana baki?"
Miƙa masa al'adar tayi tana mai cewa"bazan iya sawa ba harɗe Ni zasu yi"
Kallon ledar yayi sannan ya lalle ta, karba yayi tare da budewa ya zazzage,doguwar rigar baƙa mai dan faɗi sai ɗan kwalin rigar shima baki,kuma yana da girma.wai amma sune bazata iya sawa ba '
"Take it ,ya faɗa cikin hade fuska.
Kallonsa tayi, tare da karɓar ledar,bawai dan ta ji me yace ba ,saidan taga yana miƙa mata ledar .
"Wuce kije kisa"ya faɗa ba alamun wasa afuskarsa.
Juyawa tayi sumi"sumi ta koma toilet ɗin ,amma bata rufe ƙofarba ,ta yadda dataji burum,zata arce.
Haka ta cire kayanta ta sanya wanna doguwar rigar ,masha Allah rigar tayi mata kyau sosai ,saita fito ras da ita.maimaiko ta lulluɓa dan kwalin ,sai kawai ta daura akanta.,sannan ta sanya kayanta wanda ta cire cikin ledar sabon kayan.
Fitowa tayi tana tattare rigar ,dan harga Allah jinta take aharharde,tafi don tsangalallen ,zaninta.
Tana fitowa Adeeb yabi ta da kallon,aransa yana mai yaba irin Khan da tayi ,amma jibi yadda yake wani dage rigar.
"Hamma a ina zanyi sallar?ta faɗa tana kallon gefensa.
Shiru yayi yana kallon ta kafin yace "zo nan"
Cikin tsoro take takowa har zuwa kusa dashi,tana fatan kar yayi mata faɗa irin na ɗazu.
Mikewa yayi tare da zare ɗan kwalin kanta,ya warware shi tare da yi mata rolling irin yadda yaga amminsa da ƙannansa nayi.
Masha Allah ai nan danna fattu ta fito abalarabiya sak, tayi kyau sosai da sosai,kamar ba fattu yar fillo ba.
"Kije can kiyi sallah"ya faɗa yana nuna mata kan dardumar da yayi Sallah shima.
Bayan ta idar da sallar Adeeb yana kallon ta,masha Allah ba wani kuskure cikin sallar Tata,dan fattu tana da ilimin addini sosai.
Abinci ya nuna mata yace tayi sauri taci zasu tafi.bata wani ciabincin kirki ba,dan ji tayi sam abincin baiyi mata daɗi ba,tafi son tuwo ko madarar shanu.
Shima bai wani damu ba ,dan yaga bataci abinci ba sosai.tashi yayi yace mata suje .
Yayi gaba tana binsa abaya. Riƙe da rigarta, hannun dayan kuma tana riƙe da ledar kayanta.
Suna fita daga hotel ɗin kai tsaye gurin masu saida waya ya nufa , wata ƙaramar waya ya siya da layi,ba tare da ya tambayi kuɗi su ba ,naga ya bada duka kuɗin nan dake cikin leda,dan dama suna hannunsa,wanan rigar kawai ya cire daga ledar,sosai naga mai saida wayoyin yana ta murna da godiya har kasa ya durƙusa yana godiya.
Haɗa wayar Adeeb yayi tare da sanya layin ,kati ya karɓa gurin mai saida wayar ,aikuwa da sauri ya ɗauki mata na dari biyar ya mika masa.
Wata number naga ya daddana cikin wayar,bayan ya gama sanya katin acikin wayar.
Magana ya farayi cikin harshen larabci,bayan anɗaga wayar daya kira.ni dai ba dan me yake cewa a,saidai naga kamar yana kwatancen inda yake ne.
Bayan ya kammala wayar ne yana ƙoƙarin sanyata cikin Aljihu,kawai yaji mutum yana ƙwaƙwumarsa kamar za'a shige cikin jikinsa.
Da sauri ya kalli gefen hagunsa ,inda tanan yake jin alamun mutum ɗin,aikuwa fattu ya gani tsaye ta kama gefen rigarsa,jikinsa har rawa yake tana ɓoye fuskarta ajikinsa.
Hannunsa ya sanya tare da kamo hannunta ya dawo da ita zuwa gabansa.
Saida ya ɗan harareta kafin yace "menene kuma"ya faɗa cikin salon maganarsa kamar baya so.
Ahankali fattu ta nuna masa wasu matasa kusan su goma da suka tsaya suna kallonsu.tace "waɗan can ne ke kallona "kallon gurin matasan yayi,yaga yadda suka kafesu da idanu,kuma ba akowa suke kallo ba face fattu,nan da nan yaji wani irin ɓaci rai da ciwon zuciya ya turnuƙeshi,
Cikin hanzari ya maida fattu bayansa yana mai hararar matasan nan,zuciyarsa kamar zata fito dan tsabar ɓaci rai.gaba ɗaya yaji gurin yayi masa baƙi kirin,Bama yason tsayuwa agurin, dan haka cikin zafin nama ya fizgi hannun fattu suka fara tafiya daga gurin,mai saida wayoyin yana ta masa godiya da Allah ya kiyaye amma ko sauraransa baiyi ba.
Can wani guri ya koma tare da tsayawa ,shi kaɗai dai huci yake,dan me zasu tsaya suna kallon ta ,shifa saiyaga kamar ma ɗaya ƙirjin fattu yake kallo. Cikin sauri ya juyo tare da kallon fattu tun daga sama har ƙasa.ba wani abu daya bayyana ajikinta ,wanda za'ace shigarta batayi daidai ba ,saidai fa idan ka ƙura mata ido zaka iya gane ba bra ajikinta.
Lallai ke nan bata sanya bra ajikinta?
"Ke meyasa baki saka wannan abun ba kafin kisa rigarnan"
Ya faɗa cikin fushi da bakin rai.
Kallonsa fattu tayi cikin rashin fahimta dan bata gane me yake nufi ba,kawai saita sunkuyar da kanta ƙasa tace "kayi haƙuri Ni banga komaiba inda rigar ba"ta faɗa Muryar har ta fara rawa,alamun zata yi kuka.
Harya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa na ringing,tsaki yayi kafin ya ɗaya call ɗin.
Shiru yayi na tsawon lokaci kafin yace "Yes i sawa them"ya kashe wayar .
Dan fitowa yayi daga gurin dasuke tsayen naga ya ɗaga hannunsa .
Wata tsuleliyar mota naga ta taho gareshi,suuuuuu,baka ko jin ƙagarta,kallon ɗaya zakayiwa motar kasan anɓadda Naira agurin,farking motar tayi agabansa,kafin mai riƙon ya fito cikin sauri yana mai faɗin "your highly well come back sir"mutumin ya faɗa yana mai durƙusawa har kasa gaban Abeed.
Kafadar mutumin Abeed ya dafa tare da miƙar dashi tsaye,sannan ya ɗan rungumeshi yana mai bubbuga bayansa.
"Let go hisham"Abeed ya faɗa yana mai nufar motar ,da sauri wanda aka kira da Hisham ya budewa Adeeb motar ,shikuma ya shiga gidan baya ya zauna.
"Hamma " fattu ta faɗa cikin sauri tana mai ƙarasowa jikin motar ganin ya shige cikin motar yana ƙoƙarin barcinta.
Adeeb kuwa da gangan yayi banza da ita ,intaga dama ta ƙara so ta shiga motar,dan haushinta ya keji sosai ,ai da gangan ta wani tsaya har wasu ba zaune ke ƙare mata kallo.
Hisham ne ya kalli fattu yace "yan mata lafiya kuwa?
Shagwabe fuska fattu tayi tana kallon Adeeb tace "gurin hamma zani gashinan acikin nan"ta faɗa tana nuna mai Adeeb ,wanda ya wani ɗauke kai .
"Yallaɓai this ...
"Let her in"Adeeb ya faɗa cikin katse Hisham .
"Yes sir"Hisham ya faɗa cikin bin umarni,ya kauce daga bakin ƙofar motar yana mai cewa fattu"shiga"
Da saurinta kuwa ta shige kusa da Adeeb ta zauna ,harda sauƙe ajiyar zuciya.
Ahankali ta sanya hannunta tare da riƙe gefen rigar Adeeb ta kalle- kallen motar.banda faɗuwa ba abinda gabanta keyi.
"Yallaɓai where are we going now"
Hisham ya tambaya cikin girmamawa.
"Abuja" Adeeb ya faɗa tare da kwantar da kansa jikin kujera ,ac na ratsa shi ta ko ina.
Nan Hisham ya kunna mota suka cilla sai Abuja.
Ko daga Abuja kuma sai ina ?
Ga dai Hajiya fattu cikin mota mai a.c ana baza idanu.
Muje zuwa ku biyoni sannu kan hankali.
Domin samun wannan littafin daga farko sai ku danna bulun dake kasa 👇🏻👇🏻👇🏻
https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/macijine-shi-page-5-6-hausa-novel.html
Anty mammy ce
Mrs babi💘💘💘🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MICIJI NE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 25/26
https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
________________Tafiya suke cikin motar Ba tare da kowa ya ƙara cewa komai ba,ba abinda ke tashi cikin motar dai sanyi a.c da daddaɗan kamshi, gefe guda kuma ƙira'ar sudais ke tashi cikin suratul mulk.
Gaba daya zuciyoyinsu,sun sami nutsuwa,irin wacce mai sauraron Alƙur'ani ke samun tago mashi da ita.
Adeeb yana kwance cikin kujerar, idanunsa alumshe ,ahankali yake ɗan motsa bakinsa yana bin ƙira'ar,al'adar sa kenan dama shi,inda yana cikin mota ,to karatun alƙur'ani yake sauraro. Yayin da can ƙarƙashin zuciyarsa yake jin wani irin farin ciki da annashuwa,duk da baisan tsawon lokacin daya ɗauka cikin yanayi na wata halittar ba,amma yana ji ajikinsa cewa yayi kewar ahalinsa fiye da yadda yake tunani.ba abinda yake fata da buri irin ace yaganshi kusa da abie da ammi.ko wane yanayi zasu shiga idan suka ganshi?
Tunanin da Adeeb yayi tayi kenan cikin zuciyarsa.hakan ya hana masa fahimtar halin da fattu ke ciki.wato ta takure jikinsa sosai,sai rawar sanyi takeyi, sosai sanyin motar ke damunta, ga wani irin yanayi na kewar baffanta dake taso mata, sosai ta ƙunaci Jikin Adeeb ,aƙoƙarinta na samun gurin da dataji ɗumi.
Ahankali ta ɗan zakuɗa kadan zuwa jikinsa,ta yadda har kafaɗarta na gugar tasa.kuma har zuwa wannan lokacin tana riƙe da gefen rigarsa.
Shikuwa Adeeb jin anɗan bugeshi ,yasa shi buɗe idanunsa ahankali, ɗan juyowa yayi yana kallon fattu, wacce tayi lugus ajikinsa tana karkarwa.
"Ke matsa daga jikina"ya faɗa cikin salon maganarsa ba tare da ya motsaba.
Da sauri fattu ta ɗan matsa ,daga jikin nashi,dan ita atunaninta dama yayi barcine.
Kallonsa tayi tare da marairaicewa tace "Hamma sanyi nake ji,kodai cikin ƙanƙara muke tafiya"ta faɗa zuciyarta ɗaya,tana ɗan gwabe fuska.
Kallonta yayi tare da harararta yace "dake baki san acikin ƙanƙara muke tafiyaba?ya faɗa cikin gatse.
Zato ido fattu tayi tare da dafe ƙirji,"na shiga ukuna Ni fattu ,dan Allah Hamma kayi min rai,mu canja wata hanyar wllh mutuwa zanyi idan naci gaba da jin sanyin nan"fattu ta faɗa cikin marairaita tana rawar sanyi,gaba ɗaya ta gama tsorata,idanunsa kuwa harya fara kawo ruwa.
Bamza Adeeb yayi da ita tare da maida idonsa ya rufe,wannan gaskiya ɓaci ƙauyencima akwai shirye atattare da ita,kamar ba tare suka shiga motar ba, ko ina taga alamun ƙanƙarama bare tace akanta suke tafiya?
Fattu kuwa ganin ya maida idanunsa ya rufe sai tsoro ya ƙara makata,da sauri ta cusa kanta tsakanin hannunsa da kujera, ta kara ƙanƙame gefen rigarsa tana kuka.
"Wayyo Hamma sanyi nakeji yana shiga cikin ƙashina ,jinina daskarewa yake" fattu ta faɗa cikin kuka,tsakaninta da Allah take kukanta.
Dafe kai Adeeb yayi tare da kallon Hisham yace "switch up that a.c" ya faɗa kamar baya so.
"Ok sir" Hisham ya amsa tare da kashe a.cn yana mamaki,yau yallaɓai ne da kansa yace akashe a.c?
Fattu kuwa ahankali taji ta daina jin sanyi da take ji,dan haka share hawayenta tayi tana mai cewa aranta."anya kuwa Hamma ba so yake ya kaini gurin yan shan jini su tsotsemin jini ba? Ahankali ta dago kanta tana kallon fuskarsa ,shagala fattu tayi da kallon kyakyakywar fuskarsa ,barin ma light pink lips ɗinsa da gashin baki yayi masa ƙawayan,ga gemunsa mai kyau sai sheƙi yake,hanci kuwa kamar wanda aka ɗora masa,gaskiya Hamma akwai kyau ,inama nike da kyansa,aikuwa danasha gayu.
"Ke meye kika ƙuramin ido haka?karki cinyeni" Adeeb ya faɗa yana mai tsare fattu da idanunsa masu tsananin haske.
Dan duk yadda ta ƙuresa da ido yana kallonta ,dan ba duka ya rufe idon nashi ba .
Ɗan zabura fattu tayi ta matsa baya tana soso kai,dan ba ƙaramin kunya taji ba,ashe yana kallonta ta ƙuresa da ido haka? wayyo Allah Ni fattu .ta faɗa cikin ranta tana mai kwantar da kanta jikin kujera cikin kunya.
Tun daga lokacin ba wanda ya ƙarayin magana a cikinsu.
Adeeb yana cikin tunaninsa yaji fattu ta langaɓo kansa,dan dubawa yayi saiyaga ashe ma barci tayi.kafeta yayi da idanuwansa yana kallon zallar kyau irin na fattu,duk da ƙarancin shekarunta ,amma Allah yayi mata baiwar kyau,irin kyanda sai kana kallon mutum kake ƙara ganin kyan nashi .
Gyara mata kwanciyar yayi agefen kafaɗarsa ,duk da yadda yake jinsa atakure,kasancewar kusancinsu yayi yawa ,amma haka ya daure ya barta akan kafaɗar tashi taci gaba da barcinta.
Fattu na cikin barci taji ana dan taffing kumatunta, Ahankali ta buɗe idanunta da sukayi mata nauyi saboda barci.
"Dagani malam duk cin batani da yawun barci ko" Adeeb ya faɗa yana hararar fattu
Wacce ke kif-kifta idanunta tana mai daga masa kafaɗa,kallon kafaɗar tashi tayi,amma ita bata wani ga yawu agurin ba.
Suna fita daga Motar fattu ta gansu kusa da wani ƙaton jet ,Aida sauri ta kamo hannun Adeeb ta rike ƙam cikin nata tana mai zaro ido.
Fizge hannunsa Adeeb yayi yana hararar fattu "stop touching please" ya faɗa yanayin gaba binsa.
Da sauri fattu ta mara masa baya,tana binsa ƙafa ƙafa.tab yaushe zata tsaya kusa da wannan abu mai kama da girman duniya?haka kawai ya fado kanta ta mutu ?
Wani farin Balarabe ne ya fito daga cikin wata ƙofa,dake ɗan nesa da inda jet ɗin ke tsaye.
Da gudu naga ya taho ya ruƙunƙume Adeeb yana sunbatarsa,kuma yana hawaye.
"Habeebi ina ka shiga ?me yasameka?kasan irin tashin hankalin da muka shiga?kowa na gida yana cikin damuwa,abie yana nan akwance ba lafiya tunda aka rasaka"Balarabe ya faɗa cikin harshen larabci.
Murmushi kawai Adeeb yayi yana mai shafa kan wannan balaraben ,sannan yace " where is the imam?
Cikin share hawaye mutum yace "yana ciki kai kawai muke jira.
Kallon fattu Adeeb yayi yace "jirani ana karki biyoni" ya faɗa cikin hade fuska.kafin yayi gaba.
Da sauri fattu ta kamo hannunsa cikin marairaita tace "tsoro nakeji Hamma dan Allah karka gudu ka barni"ta faɗa cikin kwabe fuska.
Zare hannunsa kawai yayi baice komai ba suka shige cikin dakin da wanann balaraben ya fito. Zama fattu tayi akan wata kujera dake gefen ta,da alama kujerar sassaƙata akayi dan zama agurin,tagumi tayi rungume da yan kayanta,tunani take yanzu idan Adeeb ya gudu ya barta anan yazatayi? Gurin wa zata?dan ita dai yadda take ganin garin nan da zungura- zunguran gidajen dake cikin garin ,zaiyo wahala idan ba shan jini akeyicikin gidajen ba.shikenan ba ita ba ƙara ganin baffanta.
Daga kanta tayi ta kalli inda aka daka motar da suka zo cikinta amma watan bataga motar ba,saidai taga wasu tarin motocin can gefe guda arufe da wani abu.
Ƙila duk waɗanda aka kawo su cikin motocin can an shanye musu jininsu.yanzu itama haka za'a shanye nata jinin idan Hamma ya gudu?"wayyo ni fattu naga rayuwa "ta faɗa tana mai leave fuska da waige waige .
Shikuwa Adeeb koda suka shiga ƙofar nan,
Kusan minti talatin suka ɗauka cikin dakin kafin suka fito, ,lokacin fattu hatta fara kuka, tana ganinsa taji wani sanyi cikin ranta,da hanzarin ta ta miƙa tare da nufarsa tana kuka,tana zuwa ta kama hannunsa cikin kuka take cewa"Hamma harba fara kuka ,nayi tunanin gudawa kayi ka barni, anan ado a shanye min jinina, dan Allah Hamma karka ƙara tafiya ka barni" fattu ta faɗa tana mai ɗora kanta akan damtsen hannunsa. Wani irin yanayi na tausayinsa Adeeb yaji yana ratsa zuciyarsa,Allah Sarki,yasan ahalin yanzu bata da wani gata saina Allah saikuma shi,shi kaɗai ta sani,zaiyo