Showing 111001 words to 114000 words out of 116224 words

Chapter 38 - Maciji ne book 1

28 Aug 2024

25315

can yankin Nigeria,dan ko ganin ka bana sonyi kusa da fadar nan"waziri ya faɗa yana hawaye.

Salati gaba ɗayansu suka dauka,kowa yana Allah wadai da waziri,saboda son zuciya da abin duniya,yake kokarin hallaka dan dan uwansa.
Runtse ido Adeeb yayi cike da kumar zuciya,yama rasa me ya kamata yayi.
Daga bakin ƙofar dakin abie sukaji magana yana faɗin"waziri ka cuceni ka ci amanata ka yaudari soyayya irin ta yan uwan taka,me nayi maka haka da zafi ?kake son ganin bayana?duk irin kulawa da soyayya irin ta yaya da ƙani dana nuna maka,amma yau kaine ke son ganin bayana?kaje dan kanka,duniya zata koya maka hankali,kuma ko yanzu kasan Allah shine ke da iko akan kowa,dan gaka a ƙasa Ni kuma da iyalina muna samanka"abie ya faɗa cikin zubda hawaye yana dafa bango.

Da sauri Adeeb yayi gurinsa tare kamo hannunsa ya zaunar dashi akan kujera.
Cikin kuka waziri ya rarrafo gurin mai martaba yana bashi hakuri,
Suna cikin haka Tareeƙ ya shigo cikin dakin da sauri .
Duk waigawa sukayi suna kallonsa,
Cikin girmamawa yayiwa Sultan sannu da jiki,kafin ya isar musu da saƙon mutuwar Zulaihat .
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,shine abinda Dukansu suka haɗa baki gurin faɗa.
Shikenan Zulaihat ta riga mu gidan gaskiya,Allah ya yafe mata kurakuranta.
Waziri kuwa daskarewa yayi azaune jin labarin mutuwar ɗiyar tasa guda ɗaya tilo,
Ihu ya sanya tare da faduwa agurin yana birgima...


Mu hade anjima.
Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[30/08 15:01] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE 🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 89/90




_______________Waziri kuwa,daskarewa yayi agurin,tsabar shiga ruɗu da yayi,sakamakon jin abinda tareeƙ ke faɗa.
Ihu ya sanya tare da faduwa agurin yana birgima da kuka.shikenan ya rasa yarsa, Zulaihat ta tafi ta barshi,ita kadaice ƴar da ya mallaka a duniya,yanzu gashi sakamakon mugun nufinsa ya rasata.kuka yake sosai cike da tarin nadama da dana sani.

Gaba daya sun ji mutuwar Zulaihat,cike da alhini suka dunguma har waziri,saidai yana karkashin kulawar dakaru,saboda karyayi yunkurin aikata wani abu.

Haka akayiwa Zulaihat wanka,tare da sallar gawarta aka kaita gidanta na gaskiya.sai muce Allah ya yafe mata kurakuranta.

,Kai tsaye daga gurin makoki,kurkuku aka wuce da waziri.
Sukuma suka dawo falon Sultan suka zauna.anan Adeeb ke sanar dasu Queen Suhaimat cewar akwai wanda ya rike fattu,ma'ana wanda ya tsinceta tun tana karama,kuma shine ya raineta harta girma.
Sannan shine mutumin da suka taimakeshi tare da Fattun.dan haka idan ansami nutsuwa yana son zasu tafi da fattu domin dubo halin da yake ciki.

Sultan Habeeb ne yayi gyaran murya kafin yace "ai wannan tafiya damu ya kamata ayi ta,dolene muje musaka masa da abinda yayi mana,dan kuwa ya cancanci yabo da kyautatawa agaremu"
Sultan ya faɗa cike da jinjinawa bawan Allah daya kula masa da ɗiyarsa.

Shiru falon yayi nadan lokaci kafin Adeeb yayi gyaran murya,yana mai kallon kowa cike jinjina maganar da yake son fadi.
Baisan ya zasu dauki maganar ba.ko zasu yarda da batun aurensa dake kan fattu?duba da yanayin shekarunta.
Dan haka cikin nutsuwa ya fara magana"Abie,uncle da sauran mutanen dake cikin dakin nan,akwai Abinda nake son sanar daku,amma bansan ta yaya zaku fahimci maganar tawaba, saidai nayi hakan ne bada wata manufa ba,saidan kare hakkin addinina.yayi shiru yana da kallon yanayin fuskokinsu,kafin ya maida kallonsa ga fattu,wacce ke jikin mahaifiyarta,ta ɗora kanta akafadun innarta,jikinta yayi mugun sanyi,dan sosai taji mutuwar Zulaihat,dan adam ba abakin komai yake ba,yanzu duba fa dazun nan Zulaihat tana raye,amma yanzu har an kaita makwancinta.Allah kasa mudace.
Haɗa ido sukayi da Adeeb wanda yake kallonta cike da kauna,yana fatan Allah yasa iyayensu su yarda da batun auren dake tsakaninsa da fattu,dan bazai iya rayuwa ahalin yanzu batare da fattu ba.
Fattu ta zama jinin jikinsa,ta zame masa,mahadin rayuwa,kuma farin cikinsa.
"Muna jinka dana, ka fadi abinda ke cikin ranka karka damu,zamu zama masu fahimtar ka"Sultan Habeeb ya faɗa yana mai dafa kafadun Adeeb,dan yana kusa dashi ne.

Jinjina kai Adeeb yayi kafin yaci gaba da faɗin"lokacin da zamu taho kasar nan da Fatima,nayi tunanin haramcin yin tafiya da yarinya mace,wacce ba muharramarka ba,dan haka,nayi shawara da tareeƙ akan cewar,zan auri Fatima in taho da ita amatsayin matata,kuma zata ci gaba da zama matsayin matar tawa,har zuwa lokacin da iyayen ta zasu bayyana.sai In sawwake mata ta koma garesu,lokacin da aka daura auren itama kanta bata sani ba,sannan tareeƙ shine wanda ya zama waliyyinta,shina bawa sadakinta,kafin aka daura mana aure.yayi dan shiru kansa akasa kafin yaci gaba"awancan lokacin nayi aurenne da nufin idan iyayen Fatima suka bayyana zan sawwake mata,saidai kuma ahalin da ake ciki yanzu,bazan iya rabuwa da Fatima ba,ina rokon alfarmar ku barmu, mu rayu tare muci gaba da zama matsayin ma'aurata,domin ina sonta"Adeeb ya kai karshen zancen sa cike da faduwar gaba,yana fatan Allah yasa su amince da batunsa.

Ajiyar zuciya suka sauke dukansu, hakika wannan batun yayi matuƙar daɗaɗa musu rai,domin Adeeb mutum ne wanda duk wasu iyaye zasuyi fatan ya kasance mijin ga yarsu,dan haka ta bangaren su Queen Suhaimat kam,ba wata matsala,dan kallon juna sukayi ita da mijinta cike da jin dadi,suna murmushi.

Abie ma abun yayi masa daɗi,saidai dole abawa yarinyar da iyayenta dama,idan sun amince da batun auren shikenan,sannan itama yarinyar sai sunji ta bakinta idan ta amince shikenan.
Amma ma taji daɗin maganar Adeeb sosai,domin ta jima tana fatan ace,inama Adeeb zai auri fattu,dan ta yaba da hankali da kuma nutsuwar fattu,saidai awancan lokacin ba damar fadin abinda ke cikin ranta.

Abie ne yayi murmushi cike da jin daɗi,kafin ya kalli Sultan Habeeb,ya fara magana"Sultan kaji abinda ɗan nata ya faɗa ko,ina fatan dai zuciyarka tana irin tunani da fatan da nakeyi, dan haka ina jiran jin ta bakinka,kaida mai dakinka"

Murmushi uncle Habeeb yayi kafin yace "ai ranka shi dade,wannan abun yayi min daɗi fiye da yadda kake tsammani,dan haka mudai ba abinda zamuce, sai Allah ya haɗa kansu,ya basu zaman lafiya, sannan ya karesu daga dukkan sharrin abin ki"ya kai zancen sa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Wani irin sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Adeeb, Alhamdullah shikenan iyayen fattu ma sun amince da aurensu, shikenan bashi da wata matsala.
Kallonshi ya kai ga fattu,amma bai sami damar hada ido da itaba,dan kanta na duke,murmushi yayi wato fattu irin matan nan ne masu,kunyar ,hmmm zama ta ware ne ,dan shikam wllh zagewa zaiyi ya koyar da ita salon soyayya kala -kala,dan shi mutum ne mai son soyayya daga matarsa.

Hamdala abie yayi kafin yace "tunda yanzu mu Dukansu mun amince da wannan auren,yana da kyau muji ta bakin yarinyar,dan kar'ashiga hakkinta,tunda bada saninta akayi auren ba.dan haka Ƴata karki cuci kanki,ki sanar dani shin kin amince da wannan auren ko kuwa?"abie ya faɗa yana mai kallon fattu,da fatan Allah yasa itama tace ta amince.

Fattu kuwa kunyar duniya ta gama cika mata ciki,ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki,yanzu ta yaya zata amsa muce cewar tana son Hamma?tab !wllh bazata iyaba.
Gaba ɗaya dakin yayi shiru,amsar fattu kawai ake jira,saidai ba alamun fattu zatace wani abu.
Ƙuri !!Adeeb ya kure fattu da ido,karfa Hulwa ta ki amincewa da aurensa?kai baya wannan tunanin, domin yasan Hulwa na sonsa sosai bazata taba kin zama dashi ba.dan haka kallonta yake danjin mezatace.

Ganin fattu ta kasa magana sai kara sunkuyar da kanta take,yasa ammi dafa kafadunta cikin murmushi tace "karki ji tsoro yata,ba wanda zaiyi miki dole,amsarki kawai ake bukata"nan ma dai shiru fattu tayi bata ce komai ba.kunya take ji sosai.
Ajiyar zuciya abie yayi kafin yace "to alamu dai sun nuna Fatima bata amince da wannan auren ba,dan haka habeebee dole kayi hakuri ka sawwake mata"abie ya faɗa yana kallon fattu dan ganin yanayinta.
Aikuwa da sauri ta ɗago kai tana zaro ido waje,cikin muryarta mai kama da shagwaba tace "a'a Abie nifa bance bana sonshi ba,dan Allah karkasa ya sakeni,na amince Nima Ina sonshi"fattu ta faɗa cike da kuruciyarta, idonta akan Adeeb.
Gaba daya saida ta basu dariya,dan dai kawai suna cikin alhinin rashin Zulaihat ne, ya hana su darawa.amma saida suka murmusa.
Ajiyar zuciya Adeeb yayi yana mai kafeta da ido,sosai yake jin tana kara shiga cikin zuciyarsa.

Koda su Sultan zasu koma Ghana,sun bukaci tafiya da fattu, domin ta gana da yan uwanta,sannan ta dan saba dasu,amma ba jimawa zatayi ba tunda da aurenta.

Adeeb ji yayi kamar ya kwalla ihu, dan yasan zai sha wahala zama ba tare da fattu ba,amma ba yadda ya iya dole ya amince,akan idan komai yayi daidai, zaizo sai su wuce Nigeria wajen baffa.
Queen suhaimat kuwa tayi hakanne,dan tana son ta gyara yarta sosai,yadda zata kara martaba agurin Adeeb.
Cikin yanayi na gajiyar jiki da zuciya,ga tarin kewar fattu da Adeeb ya fara tun yanzu,ya mike tare da cewa"Anty bari muje dan ta shirya kayanta"ya faɗa yana kallon fattu,fuska amarairaice.

Kallonsa fattu ma keyi,cike da tausayinsa,dakuma kewarsa,amma dole tabi iyayenta,dan kuwa tana bukatar jin duminsu ajikinta,sannan tana son ta san yan uwanta.

Queen suhaimat ce ta kalli fattu tace "Zara kije ki shirya kayanki maza "ta fada tana shafa kan diyar Tata cike da so da ƙauna.

Mikewa fattu tayi,cike da kunya,tabi bayan Adeeb dan tuni yayi gaba.

Tana fita ta ganshi ya jingina bayansa da jikin bango,idanunsa alumshe.tana zuwa ta tsaya akusa dashi,tare da sanya hannu ta rike hannunsa.ahanakli ya buɗe idonsa tare da saukewa akan kyakykyawar fuskarta.baice komai ba ya rike hannun nata suka nufi part dinsa.

Suna shiga ya janyota jikinsa ya rungume tsam.ahankali yake sauke ajiyar zuciya,idanunsa alumshe.fattu ma lumshe ido tayi cike da jin tsananin so da kaunar Adeeb cikin zuciyarta.

Ahankali ya fara magana"Hulwa komai yazo ƙarshe,Allah ya bayyana mana azzalumai,mun ganesu, yanzu lokacine da nake bukatar kulawar ki da soyayya,saidai kuma gashi zakiyi nisa dani, alokacin da nake tsananin bukatarki kusa dani,Hulwa zanyi kewarki sosai"Adeeb ya faɗa cike da jin kewar fattu sosai yana kara kankameta ajikinsa.

Cike da tausayi fattu tace"Hamma nima fa zanyi kewarka, amma ai ba dadewa zanyi ba,ina son zama tare da iyayena,dan inji dadin da ake ji idan ana tare da su.amma Hamma zanyi kewarka sosai"itama ta faɗa ahankali tana mai ƙara kwantar da kanta cikin faffadan kirjinsa.

Sun jima ahaka,rungume da juna,Adeeb yana ta saukewa fattuhadda, wanda har bata san lokacin da ta biye masa ba itama,duk abinda yayi mata, itama shi take masa.basu rabu da juna ba har saida Adeeb ya samu nutsuwa sosai.kafin suka daure suka rabu da jikin juna,sai lokacin fattu ta fahimci ko kaya babu ajikinsu.kunya ce ta kamata,da sauri ta janyo bargo ta rufe jikinta tare da lumshe idonta.

Murmushi Adeeb yayi yana mai gyara mata gashin kanta daya barbaje,kafin yace "Hulwa meye kuma na rufe ido?nifa bana son wanna kunyar taki,Please ki buɗe ido ki kalleni,kinji?"ya faɗa yana hura mata iska akan idanunta.
Cikin wani irin salon murya mai cike da nishadin soyayya tace "Hamma Ni wllh kunya nakeji,kayi ta gane min jiki"ta faɗa ahankali tana rungumeshi.

Rungumeta shima yayi cike da soyayya kafin yace "hulwata idan ban kalli jikin ba,jikin wa zan kalla?jikinki mallakina ne,shine abinda zan kalla ya debemin kewa dan Allah karki hanani kallon abinda ke sani nutsuwa" ya faɗa cikin salon sa na shagwaba yana ɗan turo baki.

Murmushi fattu tayi tana mai kara cusa kanta akirjinsa,cike da kaunarsa.
Gaba daya sun shagala da nunawa juna soyayya,sun manta da su, Sultan Habib dake jiran fattu,saida wayar Adeeb tayi kara sannan suka farga,kiran Abie ne dan haka cike da kasala ya mika hannu ya daga wayar,
"To Abie gamunan "kawai ya faɗa tare da kallon fattu yace "Hulwa su anty na jiranmu"ya fada kamar zaiyi kuka.

Da sauri fattu ta mike tana zaro ido,wllh sam ta ma manta da batun tafiya Ghana,gaba ɗaya Hamma ya mantar da ita komai da soyayyarsa.
Shagwabe fuska tayi tana mai faɗin"Hamma kaga kasa na manta da su inna suna jirana ko?"ta fada tana nufar toilet da sauri tana tafe tana bubbuga kafa,ciki da tabara.
Lumshe ido Adeeb yayi yana mai faɗin "wayyo hulwata,zaki kasheni da salonki"kafin ya bita toilet din,wanka sukayi tare sannan suka fito,da kansa ya shirya fattu,kafin ya haɗa mata kayan da yasan zata bukata,sannan suka fito.

Haka Adeeb da Hulwa suka rabu cike da kewar juna,Adeeb ji yake kamar yayi kuka.

Tunda fattu ta tafi Ghana,kullum sai su wuni suna waya da Adeeb,sosai yake nuna mata yadda yayi kewarta,ita kuwa tausayinsa duk ya gama kamata,ba abinda yake son ji da gani sama dashi.saidai tayi tararrashinsa,tun tana kunyar fada masa kalamai harta zo ta daina,take zagewa tana nuna masa soyayya.

Ba irin gatan da fattu bata ganiba,agurin iyaye da danginta,kowa sonta yake,yana riritata,gyara kuwa tunda suka zo innarta ke fama,an tsuma fattu sosai,ta yadda da kanta wataran take jin tana bukatar Adeeb akusa da ita.
Tayi kyau jikinta ya kara gogewa,kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin jin dadi da annashuwa,komai yaji ajikinta.

Satinta biyu a ghana Adeeb ya kasa daurewa ya shirya kayansa yace ya tafi Ghana.
Amagarkama kuwa,lamarin ammi ya gwabe sosai,dan kuwa zuwa yanzu bai zama lallai ka gane ta ba,wasu abubuwa take tamkar na mahaukata,tayi ta ihu kenan tana faɗin irin abubuwan da ta aikata,ƙafarta ɗaya ta lalace sakamakon ciwon da taji,banda wasu irin kuraje da suke fito mata masu tsananin karni da doyi.haka zatayi ta ihu tana yagunin jikinta.duk wanda yazo inda take,da gyar yake iya tserewa dan kuwa hauka take sosai,tana dukan mutane.hakan yasa aka kulle gurinta,saidai atura mata abinci ta kasan kofa.

Waziri kuwa,an yanke masa hukumcin daurin shekaru arba'in agidan yari, yayi nadama sosai kullum cikin kuka yake da neman gafara.

Rashad kuwa zuwa yanzu jiki alhamdullah,dan sosai yaji sauki walwalarsa ta dawo, Amma ma hankalinta ya kwanta sosai take kula da abie,abin sai godiyar Allah.

Ranar da Adeeb ya sanar da zuwansa Ghana,ba ƙaramin farin ciki fattu tayi ba,murna sosai takeyi har saida innarta ta fahimta,shiri akayi mata na musamman,cikin shiga irin ta ya'yan sarakuna, tayi matukar kyau kamar kasace ta ka gudu,sai ƙamshi take zubawa,gashi tadanyi kina kwanin sha'awa.

Wani kayataccen daki aka sauki Adeeb,ko ina yayi fes sai ƙamshi ke tashi,an jere masa kayan ciye- ciye,amma ko ruwa ya kasa sha,burinsa kawai yayi tozali da hulwarsa.

Wani sihirtaccen kamshine ya bugi hancinsa,wanda ya sanya shi saurin ɗago kai,cikin hanzari ya mike tsaye tare da kafe fattu da lumsassun idanunsa,wadanda ke cike da tarin gajiya da bukatar fattun tare da kewarta.

Murmushi take sakar masa cike da shaukin ganinsa.tana takawa kamar wata tarwada.

Cikin wani irin salo da zaƙuwa Adeeb ya bude mata hannayensa,alamun ta taho gareshi,da sauri ta ƙaraso tare da fadawa jikinsa,shikuma ya mayar da hannunsa ya rungumeta tsammm.


Muje zuwa masu karatu.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[30/08 15:01] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 91/92






_____________Cikin wani irin salo wanda ke nuna tsantsar farin ciki da zaƙuwa,Adeeb ya bude hannayensa,alamun fattu ta taho gareshi.
Da sauri fattu ta ƙaraso gareshi,cikin takunta mai jan hankali,tare da fadawa jikinsa tana murmushi.
Maida hannunsa yayi ya kulle tare da rungume fattu tsamm,ajikinsa.

Atare suka sauke ajiyar zuciya,wacce ke nuna tsantsar kewar juna da sukayi.
Banda ajiyar zuciya ba abinda Adeeb ke saukewa,kamar wanda yayi wasan tsere.
Ahankali cikin murya mai tattare da shauki yace "I miss You so much Hulwa"ya faɗa yana kare matseta akirjinsa,kamar zai maidata cikinsa.
Kusan minti biyar suka dauka ahaka,kafin Adeeb yayi karfin halin ɗago da fattu daga jikinsa yana kallon kyakykyawar fuskarta.gani yake kamar ba fattunsa ba,kamar wanda aka sauya masa ita,tayi kyau matuka,ta kara gogewa kai kace acikin ƙanƙara tare rayuwa.

Fattu ma kallonsa take cike da jin zazzafar kaunarsa na ratsa jini da tsokarta,dan gani tayi yayi mata kyau sosai,ya ɗanyi kiba kaɗan ya kara fari,ga sajen da ya kara ajiye wa yayi matuƙar ƙawata fuskarsa.

Ahankali ta kai hannunta tare da shafa gefen fuskarsa,lumshe ido yayi yana mai jin sanyi cikin ransa.cike da son nunawa Adeeb yadda tayi kewarsa ta kai bakinta kan nashi,ta fara kissing dinsa,kawai sai jin bakin fattu yayi cikin nashi.

Ai kamar mayen karfe haka Adeeb ya karbe lips din fattu ya fara sha kamar ya sami lollipop.
Tun abun yana karami har yazama babba,dan sun kasa rabuwa da juna,ganin suna neman faduwa ne yasa su zubewa akan lafiyayyar kujerar dake kusa dasu.adeeb bai bar wannan dama ba ,saida ya kara angoncewa, sosai ya shiga ruɗu da gigita,ɗan jin fattu yayi kamar bai taba ma saninta matsayin ya mace ba,sosai ya nishadantu da ni'imarta,ya rikice mata sosai haka yayi ta sunbatu yana hawaye.albarka kuwa fattu ta shata ba adadi da kyaututtuka kala kala.
Saida suka sami nutsuwa kafin Adeeb ya samu yaci abinci.anan dakin sukayi wanka tare,gaba ɗaya Adeeb ya kara kwarewa fattu,ko yaya tayi motsi hankalinsa na kanta,wani irin so yake mata marar misaltuwa.fattu duk da taji zafi amma haka ta daure bata nunawa Adeeb raki ba.nan suka shantake suna nunawa juna so da kauna,dama tuni Adeeb ya mika gaisuwa ga Sultan Habib da innar fattu.
Dan haka salla ma acikin dakin nan yakeyinta. Fattu kuwa ranar ta yabawa aya zaƙinta,dan ta tabbatar da cewar Adeeb yayi kewarta,kuma shidin jarumi ne na gaske.

Washe gari suka tashi daga Ghana zuwa Nigeria,da tareeƙ akayi tafiyar,dan dama tare suka zo da Adeeb,shiya sauka a masauki na daban.
Kai tsaye a Jos suka sauka,kafin suka nufi kauyen su fattu cikin dalla dallan motocinsu.
fattu da Adeeb cikin mota daya suke,yana rungume da ita ajikinsa,motar su ce agaba,ko kaɗan fattu bata manta hanyar kauyen nasu ba,dan haka tana lura da inda suke nufa.

Sai motar Sultan Habib shida innar fattu dasu zayyad.

Kauyen yana nan inda fattu ta sanshi, ba abinda ya sauya.gidansu ta fara hangowa,cike da doki take nunawa Adeeb gidan"Hamma ga gidanmu can,yanzu zanga baffana,Hamma bazan iya kwatanta irin farin cikin da nake ciki ba"fattu ta faɗa tana rike hannun Adeeb cike da murna idanunta ya cika da kwalla.
Murmushi yayi,dan shima saiya tsinci kansa cikin farin ciki, ganin yadda Hulwarsa ke farin ciki.
"Nima ina farin ciki Hulwa zataga baffanta,saidai anya kuwa zai gane ki?Adeeb ya faɗa yana kallonta da murmushi.
Cikin doki da dariya fattu tace "wllh zai ganeni,ko me nazama na tabbata baffana zai ganeni kuma zaka gani"ta fada daidai lokacin da sukayi facking akofar gidansu fattu.

Da hanzari fattu ta buɗe kofar motar ta fito,bata ko tsaya sauraron Adeeb ba,burinta kawai tayi tozali da baffa.da sallama ta shiga cikin gidan tana rarraba ido dan ganin ta inda zataga baffanta.
Ba kowa cikin tsakar gidan,gaba ɗaya gidan yayi datti,ko ina kazantace cikinsa.jin sallama yasa gwogwgo hansai fitowa daga cikin dakinta,tana ta soshe soshen kwarkwata.
"Waye yau agidan nan nawa?rabon da naji wani yazo gidan nan,harna manta,kodai Hau......maganar gwogwgo hansai ta makale sakamakon ganin wata balarabiyar yarinya da tayi tsaye fuskarta ɗauke da murmushi.
Cikin rawar jiki gwogwgo hansai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login