Showing 60001 words to 63000 words out of 116224 words

Chapter 21 - Maciji ne book 1

28 Aug 2024

25298

kuma?
Tsabar rawar da jikinta yakeyi bata san lokacin data buge wani flower vase dake ajiye agefenta ba ,ya fadi kasa ,jikake toshshs!! Ya fashe .

Cikin tsoro da tazana fattu ,tayi sauri buya ajikin ƙofa tare da runtse idanunta.
Ammi kuwa da sauri ta taso Dan ganin waye yayi mata labe ,har yaji sirri ta.

Da mugun ƙarfi aka fizgi fattu akayi waje da ita ,buɗe baki fattu tayi da nufin kurma ihu,taji an toshe mata bakinta.....


Waye ya dauke fattu?
Me zai faru nan gaba?
Muje zuwa anty mammy ce

Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[30/08 14:58] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 63/64




_______________Jikin nanny ne yayi sanyi sosai,ganin Adeeb atsaye,kuma ya gansu tare da amma,tasan yanzu kam kome zata faɗa masa ,bazai taba yarda da ita ba.ahankali take takawa zuwa gareshi,gaba ɗaya jikinta ba kwari,
Shikuwa Adeeb yana tsaye ya kafeta da Mayun idanunsa ,masu sanya mutum yaji shi cikin tsoro da fargaba.
Nanny Tana karasowa tace "magajin fada ,fushi kake dani ko"?
Ta fada cikin sanyi murya da mutuwar jiki.

Lumshe ido Adeeb yayi ,zuciyarsa na masa zafi yana mamakin abinda nanny tayi masa,ace wai nanny ta hada kai da maƙiyarsa tana tayata ƙoƙarin cutar dashi,matar daya ɗauka matsayin uwa ?mutum kenan.
"Ko kaɗan nanny bana fushi dake,kawai ina godiya ga Allah ne ,daya nunamin gaskiya ,na gane irin mutanen da nake tare dasu,na daukeki tamkar mahaifiyata nanny,Amma bansan nayi babban kuskuren yin hakan ba,dan Allah kiyi haƙuri"ya faɗa yana mai haɗe hannayensa guri ɗaya alamun neman afuwa.

Sosai nanny kejin ciwo cikin ranta ,damuwa da taraddadi sun cika mata zuciya,dama tayi wannan tunanin,tasan idan har Adeeb ya gansu tare da amma ,to shikenan,kuma kome zata faɗa masa bazai yarda da ita ba,amma Allah shine shaida bata da nufin cutar da Adeeb ko kaɗan.

"Magajin fada wllh abinda kake zargi ba haka bane ,kada ganina tare da amma yasa maka kokwanto akaina, wllh nima Ina jinka tamkar tareeƙ bazan taɓa cutar dakaiba magajin fada.
Nanny ta faɗa cike da damuwa aranta.
Girgiza kai kawai Adeeb yayi tare da barin gurin,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa .
Kallonsa kawai nanny keyi,tana fatan Allah yasa ya gane gaskiya cikin sauri kafin komai ya daɗa lalacewa.

Ba kowa cikin falon ammi,sai ƙamshi dake tashi ta ko'ina ,dan ammi akwai son kamshi,kai tsaye ya nufi dakin kwananta, nocking yayi amma shiru,hakan yasa shi shiga cikin dakin kai tsaye.saidai nan ma ba kowa cikin dakin.

Harya juya zai fice ,sai kuma zuciyarsa ta raya masa ya duba wanann akwatin da yaji ammi na magana akanta.
Dan haka juyowa yayi yana karewa dakin kallo.
Ahankali yake duba dakin dan neman wannan akwatin,amma yayi iyakar dubansa bai ganta ba.
Harya hakura sai kuma ya hango wata akwati mai kyau da ɗaukar ido,yasan akwatin Dan acikinta ammi ke ajiye kwalakwalanta ,dan haka sai yayi tunanin ba komai cikinta, har ya juya da nufin barin dakin,sai kuma zuciyarsa ta kwadaitu da son duba akwatin .
Dan haka ahankali ya zauna tare da ɗauko akwatin, danna lanbobin bude akwatin yayi,dan kuwa tuni yasansu, aikuwa saiga akwati ta bude,gwalagwalai ne acikinta iya ganin ka ,masu kyau da ɗaukar hankali,kallo ɗaya zaka musu kasan an zubar da maƙudan kudade wajen mallakar sarkokin.
Dubawa yayi tayi amma baiga komai aciki ba,sai wani dan karamin akwati mai kyau da ya gani,kallon akwatin yake da mamakin meye acikinsa aka wareshi ?lallai yana son ganin abinda ke ciki.dan haka hannu Ya mika tare da ɗauko akwatin ya bude.

Mamaki ,al'ajabi ruɗu da kuma faduwar gaba sune suka ziyarci zuciyar Adeeb,sakamakon ganin sarƙar nan ta Hulwa data bace ,cikin wannan akwatin,
Me yakawo sarkar Hulwa cikin kayan ammi?har akayi mata adana ta musamman?me hakan ke nufi,shidai yasan ammi tana da sarkokin da suka ninka kudin wannan bare yayi tunanin ta daukene dan bata da mai tsada kamar wannan ,to me hakan ke nufi kenan?innalillahi meke faruwa ne acikin gidan nan?kodai akwai Abinda ammin nashi ke kullawa da gaske ? Wayyo ina zaisa kansa ?dawa ya kamata ya yarda ne cikin fadar nan? Dauko sarƙar yayi cikin sauri ya maida komai inda yake sannan yayi saurin barin dakin na ammi ya koma part dinsa. Zuciyarsa na zafi kamar zata kama da wuta .

Lokacin daya koma part din nasa fattu ta farka,tana zaune tana kuka,tsoro takeji,har lokacin barin ma dataga ita kadaice cikin dakin,ina Hamma ya tafi ya barta?karfa wannan Rashad din ya dawo mata? Gashi wannan innar ma bata dawo ba,wannan tunanin yasata ƙanƙame jikinta tana kuka.

Adeeb kuwa cikin wani irin yanayi na sarewar zuciya ya shigo cikin dakin,abubuwa sunyi masa yawa cikin zuciyarsa,jinsa yake kamar bashiba, kansa banda ciwo ba abinda yake ,wai meke shirin faruwa da rayuwarsa ne ?me hakan ke nufi ?me amminsa ke nufi da ɗauke sarƙar Hulwa?
Kukan hulwar da yaji Yone yasani saurin ƙarasawa cikin dakin.

Tana jin motsi sa ta zabura atsorace tana mai kallon ƙofar dakin.ganin Adeeb ne ya shigo yasata saurin yunkurawa ta mike da gyar tana kuka tare da kallonsa.

Da saurinsa ya ƙaraso inda take ,yana zuwa ya kamo hannunta tare da shafa gefen fuskarta yace "menene kike kuka?inane yake miki ciwo ?ya faɗa cikin mugun sanyin murya ,wanda har saida fattu ta ɗago kanta ta kalleshi,

Idanunsa sunyi jajur sosai jijiyoyin kansa sun fito rudurudu,fuskarsa tayi jajur ,kana gani kasan yana cikin damuwa da tashin hankali.
Cikin kuka fattu ta faɗa ƙirjinsa ta rungumeshi, tana faɗin "tsoro nakeji Hamma ,ko ina ganin ƙaninka nake yana min gizo Hamma" ta fada cikin kuka tana ƙanƙame Adeeb.

Cike da tarin damuwar da baisan menene mafitarta ba shima ya ƙanƙame fattun ajikinsa yana mai lumshe ido da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi,
Ahankali yake faɗin"kiyi haƙuri Hulwa , dagani harke muna cikin damuwa, Hulwa komai bayamin dadi na kasa gane dawa ya kamata in amince cikin fadar nan,Hulwa kowa na fadar nan so yake yaga bayana bansan me na tsare musu ba" Adeeb ya faɗa cikin murya mai tattare da karaya da sarewa.

Shiru fattu tayi tana sauraron abinda yake fadi,ita fa sam bata fahimci inda zancen sa ya nufa ba,ahankali tace "Hamma ,su waye ke son kamin bayanka"?

"Shiru yayi yana mai kara rungume fattu ajikinsa,dan sosai yake jin nutsuwa na samunsa sakamakon rungumeta da yayi,zuciyarsa tana yi masa sanyi .shafa gashin kanta kawai yake bai ce komai ba.
Kusan minti biyar suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin zareta daga jikinsa ya zaunar da ita abakin gado,kallonta yake ,har zuwa lokacin idanunta basu koma yadda suke ba,akwai kumburi da kuma dan jaa kadan acikinsu.
Hannunta ya kamo cikin nashi ya rike gam-gam yana kallonta.ji yake kamar ita kadai ta rage masa wacce zai fadawa damuwarsa,saidai fattu yarinyace,idan ma ya faɗa mata damuwarsa bazata fahimci me yake nufiba.

Kallonsa fattu tayi itama,tabbas akwai Abinda ke damun hamman nata,ko menene oho."Hamma meke danunka?baka da lafiya ne ?ta fada cikin muryar marasa lafiya ,wadanda suka sha kuka.

Ahankali ya koma kusa da ita ya zauna ,kallonta yayi yace "Hulwa abinda ke damuna yana da yawa,ina cikin wata sarkakiya wacce Allah ne kawai zai fitar dani,bani da wanda zan fadawa damuwata ahalin yanzu,bana son sanar da abie na komai,dan gudun ɓacin ransa,saboda tsoron kar ciwonsa ya tashi,kiyi ta min addu'a kinji hulwatee" Adeeb ya faɗa yana mai riƙe habar fattu tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa.

Cike da tausayawa fattu ke kallon Adeeb,kafin itama ta sanya hannunta akan fuskarsa tana shafa gefen fuskar tashi, kamar yadda yake mata .sannan tace "Hamma zanyi ta maka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, kuma kaima kayi ta addu'a Allah maji rokon bawansa ne ,Allah ya bawa abie lafiya Hamma,amma me zai hana ka sanar da innarka itama ta tayaka addu'a" fattu ta faɗa bayan ta cire hannunta daga kan fuskar Adeeb.

Wata sassanyar ajiyar zuciya Adeeb ya sauke lokacin da fattu ke shafa gefen fuskarsa ,ahankali ya lumshe idanunsa yana jin wani irin sanyi yana Ratsa zuciyarsa.

Ahankali ya bude idonsa lokacin da yaji ta cire hannunta daga kan fuskarsa.kafin yace "Hulwa ammina tana daga cikin mutanen da nake son boyewa damuwata ,ahalin yanzu bazan iya sanar da ita komai daya danganci lamarinaba,ke dai kiyi ta min addu'a kinji"ya faɗa cikin murya mai cike da ban tausayi.

Sosai fattu kejin tausayin hamman nata yana Ratsa zuciyarta.ahankali ta ɗora kanta gafen kafadunsa tare da rungumoshi ta gefe.tayi shiru cike da tunanin meke damun hamman nata.

Ahankali shima ya dora kansa akan nata kan yana jinsa tamkar marayan da bai da kowa.

"Hamma wannan innar bazata dawo ba ko?" Ta fada ahankali idanunta alumshe.

Shima idonsa alumshe yake yana shafa kan fattu ,yace "kina so ganinta ne?
"Daga kai tayi alamun eh sannan tace " eh Hamma ina son ganinta ,ina kaunar ta har cikin raina ,kuma tace daga yau itace inna ta"

Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin yace " Hulwa ita kadai kike kauna ? Ni baki kaunata?ya faɗa ba tare da yasan ya fadi hakan ba .saida ya faɗa sannan ya fahimce me yace .

"A'a Hamma ina ƙaunarka sosai mana,ina sonka,kaidin kamar baffana kake ,bani da kowa saikai, Hamma bana son wani abu ya tab aka ma" ta fada tana ɗago kai tare da kallon Adeeb.

Cikin wani irin farin ciki da jin dadi Adeeb ke kallon fattu,zuciyarsa cike da jin dadi yace "da gaske kike Hulwa?" Ya faɗa cikin murmushi yana kallonta.

Jinjina kai tayi itama cikin murmushi tana kallonsa.

Ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta gamm yana mai lumshe ido , sosai yake jin wani irin. Daɗi da Nutsuwa cikin zuciyarsa.

"Kina son ɓata min shiri ko ?,kisani wllh idan kikayi wani kuskuren dana rasa damata,kema zaki karbi naki hukuncin ,kin sanni kinsan halina,kuma kinsan abinda zan iya aikatawa ,dan haka ki kula da kanki,komai yana ƙoƙarin lalacewa saboda sakacinki,to bazan laminci wannan abinda kike yiba.wllh zan aikaki gurin da duk wanda zai zamenin matsala nake aikawa.akan wannan karagar zan iya batar da kowa"
Wani mutum ne daya lulluɓe ilahirin fuskarsa ke fadin wannan maganar cikin ɓacin rai yana kallon ammi,wacce ke tsaye cikin tsantsar tsoro ,jikinta sai rawa yake cikin tashin hankali tace "dan Allah kayi hakuri ,wllh ina yin iyakar ƙoƙarina akan wannan abun ,kuma aKwai shirin da nake yi ,karka damu ka kara hakuri "ta fada cikin rawar murya,tana kallon mutumin da baka ganin komai bace kwayar idanunsa.

Cikin fushi mutumin ya damƙi wuyan ammi ya hadata da jikin bango yana faɗin"bana son jin komai daga bakin ki kawai ki aikata abinda nace miki ,ki tabbatar ya bar duniyar nan nanda lokaci kankani,zan kawo miki abinda zaki saka mishi acikin abinci,zai mutu kuma ba wanda zai zargi wani abu,idan kuma aka samu kuskure .yayi shiru tare da sakin wuyan ammi wacce ke kakari tana kokarin shekawa.

Tari sosai ammi keyi,lokacin da mutumin ya saki wuyanta sannan yayi tafiyarsa cikin sauri yana ƙara gyara rufin fuskarsa.

Saida ammi ta samu nutsuwa kafin ta bar gurin ,kai tsaye dakinta ta nufa ,gaba ɗaya awahale take,
Bakin gado ta zauna cike da damuwa tana tunani,can dai ta dauko akwatin sarkokinta,abin yayi matuƙar tsorata ta lokacin datayi arba da akwatin sarƙar fattu ba komai acikinta.

Wani dan gajeren ihu ta kwalla cikin tashin hankali,tana dube dube cikin akwatin ,waye ya daukemin sarƙar nan?na shiga ukuna wayyo ni ammi .da sauri suhaimat ta shigo dakin ammi ,dan kuwa taji ihun da ammin ta kwalla."uktee lafiya ?naji kina ihu?suhaimat ta fada cikin damuwa tana rike ammi.

"Ba komai suhaimat na Dan bugene "ammi ta fada cikin tashin hankali.
Kallonta suhaimat keyi cikin rashin yarda da abinda ya fada,amma koma dai menene tunda taki faɗa shikenan .
"To mukam muna ta shiri anjima jirginmu zai tashi .zanje in Kara duba yarinyar can "suhaimat ta fada tana kallon ammi.

"Karkije suhaimat ,karkije,na roƙeki,ki rufamin asiri karkije "ammi ta fada cikin tashin hankali tana kama hannun suhaimat.dan tana tsoron kar ace sarƙar ta koma gurin fattu ne kuma suhaimat ta gani ta gane yarta.

Cike da mamaki suhaimat ke kallon ammi,anya kuwa kalau take?ji yadda ta wani rikice daga cewa zani ganin yarinyar can.
Kai gaskiya akwai wani abu aƙasa.

Cikin hade fuska suhaimat tace "uktee ki fadamin menene dalilinki da baki son na haɗu da yarinyar can?me kike kullawa akanta ?menene hajjarki ? suhaimat ta fada cikin haɗe rai tana kure ammi da ido.

Zato ido ammi tayi tana kallon suhaimat ,kafin cikin in Ina ta fara magana "su...haim..at ......



Hmmmmm muje zuwa masu karatu.

Mrs babi ce💘💘


Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[30/08 14:58] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din👆🏽

Free book

Page 67/68




_______________Da sauri ammi ta taso cikin tashin hankali da fargaba,dan kuwa tabbas tasan wani yaji me take cewa.

Fattu kuwa tsabar ruɗewa da shiga tashin hankali tama rasa ina zata dosa,tsoro ya cika mata zuciya ganin ammi ta nufo inda take ,saidai cikin wannan yanayin ne taji an fizgeta da mugun ƙarfi anyi waje da ita.nan take tsoronta ya kara rubanya.buda baki tayi da nufin kurma ihu ,dan atunaninta masu kashe tan ne suka kamata.saidai gam!aka rufe mata baki,bata yadda zatayi ihu.kuma cikin wani irin sauri mai kama da gudu akayi waje da ita,ta wata hanya da bata nan ta shigo ba.

Ammi kuwa tayi iyakar dubanta ,amma bata ga kowa ba,kuma tabbas tasan anshigo cikin dakin nan,to waye?dan duk ta kora yan aiki can farfajiyar gidan dan tasami damar yin wayarta.
Ko dai Adeeb ne?kai bashi bane ,dan kuwa Adeeb baya zuwa gareta ba tare da yayi sallama ba.toko nanny ce ?kai idan nanny ce zan iya cimma ta kafin ta gudu,wai waye wannan yake son shiga rayuwata ne?waye yake son bakuntar lahira kwana kusa?na rantse da Allah idan na gano ko waye saina hukuntashi, hukunci mai tsanani.yanzu dole mu sake sabon tsari dan wannan kam ya rika ya lalace"ammi ta fada cikin zafin zuciya da kunar rai.

Tana nan tsaye Zulaihat ta shigo dakin ba ko sallama,kawai ammi sai ganin mutum tayi bukut ya shigo cikin falon.guri ta nema ta zauna tare da ƙurawa ammi ido.

Harara ammi ta Banka mata tana tunanin koma dai Zulaihat ɗin ce ta shigo dazu da tasan Zulaihat ba hankali gareta ba?
"Ke Zulaihat kece kika shigomin daki dazu kina Min labe?"ammi ta fada cikin haɗe fuska.

Wani shegen kallon Zulaihat ke jifan ammi dashi,kafin ta fara magana "lallai ma ammi har kina tunanin akwai wanda zan zauna inayiwa labe?to me zan labe naji,bayan duk wani tuggun da ake ƙullawa ina sane dashi,me kuma za'a boyemin ?kinsan Ni bana munafurci kai tsaye nake Abunda naga dama "Zulaihat ta faɗa cikin rashin kunya tana wani juya ido.

Kallonta ammi tayi cikin tsantsar ɓacin rai da tsanar halayen ta na rashin kunya kafin tace " yanzu kina Min wannan gatsalin kike son na aura miki Dana?to wllh gara ki nutsu Dan bazan yarda ki auri Adeeb da wannan shegen halin naki ba,domin shirme zakiyi tayi mana,idan mun saki aiki"ammi ta fada cikin faɗa -fada.
Wata irin dariya Zulaihat tayi tana kallon ammi kafin tace "Kinga ammi ki daina min tsawa keba uwata bace,ko iyayena lallaɓani suke ,kuma da kike cewa zan bata muku aiki,ku atunaninku idan anyi auren biye muku zanyi in cutar da abin sona,?wllh garama ku nutsu daga ke har daddy na Dan kuwa rungumar mijina zanyi musha soyayya ,kuma duk wanda yayi yunkurin cutar da shi ,wllh saina kashe mutum,kinsan nima na iya dabancin"Zulaihat ta faɗa cikin gadara tana kallon ammi ido cikin ido.

Baki buɗe ammi ke kallon Zulaihat,lallai yarinyar nan ta wuce yadda suke tunani,Gara ta lallabata,karta jika mata aiki,dan haka cikin dan murmushin yake ammi tace "kai ƴata dadina dake baki san wasa ba,yanzu saiki maida abu gaske,ki kwantar da hankalinki,kinsan nima bazan taɓa bari a cutar min da Adeeb ba, dama nayi tunanin bakinsu ɗaya da mahaifi ki,shiyasa na fadi hakan"ammi ta fada cikin murmushin yaƙe tana hararar Zulaihat ƙasa ƙasa.

"Ato Gara dai mutum ya kula wllh ,dan zan iya komai akan abinda nake so"Zulaihat ta faɗa tana mai gyara zamanta zuwa kwanciya,tare da lumshe idonta kamar zatayi barci.

"Zanyi makaganinki daga ke har uban Maki shegiya"ammi ta fada cikin zuciyarta,tana shigewa daki,cike da tunanin mafita.


Ba'a dire fattu a ko ina ba, sai cikin wani daki mai dan duhu, wanda kana iya ganin mutum ,amma bazakaga fuskarsa kai tsaye ba.
Koda aka direta sam ba'asakar mata baki ba.
Fattu kuwa banda rawa ba abinda jikinta keyi,sai ƙoƙarin cire hannun mutumin take daga bakinta, ammata kasa .

Cikin nutsuwa da kwantar da hankali ya fara magana "ki nutsu ,niba cutar dake zanyi ba,koda na bude miki baki to karkayi ihu "

Cikin hanzari fattu ke jinjina kanta idonta yayi zuru zuru ,burinta kawai tajita free.
Ahankali ya dannan makunnar dake gefensa,nan take dakin yayi haske ta yadda kana iya ganin komai.

Da sauri fattu ta daga idanunta tana kallon mutumin,
"Hamma tareeƙ"ta fada cikin rawar murya,"ka bani tsoro Hamma tareeƙ,meke faruwa cikin gidan nan,wacece ammi ?meye alaƙarta da hammana?fattu ta faɗa cikin muryar kuka tana kallon tareeƙ.

Shima kallonta yake zuciyarsa na masa zafi ,yayi fatan ace Adeeb da kansa yaji wannan maganar ba wani ne yaji ba.
"Ki kwantar da hankali ki fateema,da sannu zaki fahimci komai "
Ya fada tare da ɗauko wayarsa yayi kira.

"Ummee kuzo ina nan cikin dakin baya"haka kawai ya faɗa ya kashe wayar.
Kallonsa fattu keyi jikinta har lokacin rawa yake ,tana cikin shock da zallar mamaki,kujera tareeƙ ya nuna mata tare da cewa"ki zauna anan fateema " jiki ba kwari fattu tabi bango ta zauna aƙasa ba tare da ta hau kan kujerar da tareeƙ ke nuna mata ba.zallar mamakin ammi da al'ajabi ta ke ɗawainiya da fattu,yanzu duk zaman da sukayi dama ammi tasan asalin iyayenta?kuma ita ta sace sarƙarta wacce take matsayin shaidar da zata sadata da iyayenta na asali?amma menene ribar ammi nayin hakan?wane amfani zata samu?lallai dole ta sanar da Hamma wannan maganar .
Bude kofar da akayi ke ya katsar mata da tunaninta ,da sauri cikin tsoro ta kalli bakin ƙofar,nanny ce ta shigo ita da amma.
Da sauri fattu ta mike cikin rawar jiki ta ƙanƙame nanny tare da sakin kuka mai ciwo da radadi," nanny wai zasu kashe min hammana ,kuma nima zata kasheni ,sannan tace tasan asalin iyayena ,amma bazata bari muhadu dasuba.nanny wacece ammi ?meye alaƙarta da hammana,anya kuwa itace ta haifeshi ?fattu ta faɗa tana mai dago kanta tare da kallon nanny.

Cike da tausayin fattu nanny ta riketa ajikinta Tana mai shafa bayanta ,alamun rarrashi,kafin tace "ki kwantar da hankalinki ɗiyata,ba abinda zai sameku da yardar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login