Showing 114001 words to 116224 words out of 116224 words
fara fadin"maraba lalle baiwar Allah,daga ina?wa kike nema kodai gidan mai gari kike nema?"gwogwgo hansai ta fada cikin rawar jiki tana kallon fattu.
Dariya fattu tayi tana kallon gwogwgo Hansai,duk ta rame tayi baki sosai gashi ta tsufa,kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin wahalar rayuwa.
"Gwogwgo,baki ganeni ba ?nice fa,nice fattun baffa"fattu ta faɗa tana kama hannun gwogwgo Hansai ba tare da gyama ba.
Galala gwogwgo tayi tana kallon fattu,cike da ƙaryata abinda fattun ta fada,saidai kuma wa yasan fattun awani guri?bare yazo yayi mata wasa.cikin rawar murya tace "fa....t.t.tu,kece haka ?kece kika zama kamar balarabi?ina kika je kika zama mai kudi haka?ta fada tana shashshafa fattu.
Dariya fattu tayi kafin tace" nice gwogwgo tare muke da iyayena fa da hammana,suna waje bari nace su shigo,wai ina baffana ne tunda na shigo nake nemansa"fattu ta faɗa cike da doki tana nufar waje.
Lokacin da ta fita atsaye ta tarar da itayenta da Adeeb,mutanen garin sun zagayesu suna kallonsu da shafa motar da suka fito daga ciki.
Bata damu da mutanen gurinba tacewa su Adeeb su shigo.
Murna take sosai kamar wacce akayiwa bushara da gidan aljanna.
Gwogwgo Hansai jiki na rawa ta shimfida musu wata rubabbiyar tabarmar kaba.ko kaɗan basu nuna mata gyamaba suka zauna.
Bayan gaishe gaishene, gwogwgo tayi ta kuka tana bawa fattu hakuri,itadai fattu burinta daya taji ina baffanta yake.
Nan gwogwgo Hansai ta sanar da ita duk abinda ya faru da baffa,ranar da suka bar garin.
Kuka sosai fattu ta sanya,tana jin wani irin kunci cikin zuciyarta,ina zata ga baffa?mutumin daya tallafi rayuwarta ,ya bata kulawa,wayyo Allah.haka fattu tayi ta kuka,ajikin Adeeb yana rarrashinta.
Gwogwgo Hansai cikin nadama take faɗin"bayan tafiyar malam,gaba ɗaya lamari ya lalace garin nan,kowa abinda yake so shi yakeyi,haka inaji ina gani,yarana mata sukayi cikin shege,yanzu haka bansan duniyar da suka shiga ba,shima namijin tuni ya zama rikakken barawo,yayiwa yar mutane fyade shine ya gudu,ya bar rugar nan.mai gari yana nan ya zama gurgu,jauro kuwa abarsa ta lalace har yanzu bata da amfani,haka haroji yana na da fuska kamar ta dodo,saidai yaje Bara cikin gari,dan Allah fattu ki yafe mana ,nasan hakkinkine ke bibiyarmu"gwogwgo Hansai ta fada cikin kuka.
Haushin ta sosai Adeeb yakeji,dan yasan kadan daga cikin mugayen halayenta.
Tashi sukayi domin barin rugar,dan bawani amfanin zamansu,tunda wanda suka zo gurinsa baya nan.
Kudi mai yawa sultan habib ya bawa gwogwgo hansai,sai murna take tana godiya,haka ya tabawa mutanen kauyen ma kafin suka bar garin.
Kuka sosai fattu keyi ajikin Adeeb,ta shiga damuwa mai tarin yawa,haka yayi ta rarrashinta,har suka iso cikin garin jos.
Wata babbar motace tayi faci akan tsakiyar kwalta,hakan ya haddasa go slow agurin,suna tsaye cikin mota,masu bara sai zuwa suke suna Bara.
Wani dattijone cikin shiga ta almajirai,kallo ɗaya zakayi masa kasan yana shan wahala yazo jikin motar su fattu yana Bara,kasancewar gilas din motar irin mai duhun nan ne,yasa na waje baya ganin na ciki.
Fattu ce tayi firgigit tatashi daga jikin Adeeb tana kallon tsohon dake barar.
Wani dan ihu ta sanya tana mai ƙoƙarin buɗe kofar motar.kira take
"Hamma baffana,baffana"tana faɗa cikin rawar jiki tana kokarin buɗe motar.
Da sauri shima Adeeb ya kai kallonsa inda fattun ke nuna masa.
Tabbas baffa ne kuwa.gana ɗaya fattu ta rikice tana kici kici buɗe kofar Amma tsabar farin ciki tama kasa,budewar sai kira take"baffana,baffana"
Hannunta Adeeb ya riko yace "ki nutsu hulwa,karkije kiki ciwo kinji bari muje gurin baffan"ya faɗa yana bude kofar motar.
Da sauri fattu ta fito daga cikin motar ta nufi gurin mutumin da yayi dan gaba dan zuwa wajen wata motar ya sami sadaka.
Da sauri ta kamo hannunsa tana faɗin "baffana kaine,haka ?"cikin azama baffa ya juyo sakamakon jin Muryar da akullum saiyayi kukan rashin ta,kuma duk kuɗin da yake samu na bara tarawa yake,dan yayi ta zaga garuruwa yana neman fattu,yasan watarana zasu hadu.
Jifa yayi da dan buhun dake hannunsa,wanda yake tara kudin barartasa ciki.
"Fattu,kece"baffa ya faɗa cike da shauki.
Kuka fattu keyi tana kallon baffa,kafin ta rungumeshi ajikinta tana kuka.shima baffa kuka yake cike da godewa Allah,yau gashi ga fattunsa,shikenan burinsa ya cika.
Sultan habib,da innar fatyu ma,fitowa sukayi,dan kobasu tambaya ba,sunsan wanna shine baffan fattunsu.
Adeeb kansa saida yaji kwalla ta cika masa ido,dan tausayin tsohon da yadda ya koma.
Horn din da motoci ke musu ne ya dawo dasu cikin hayyacinsu,dan tuni an janye motar data haddasa go slow ɗin,dan haka cikin hanzari suka shige mota dan ba mutane hanya.
Motar su fattu baffa ya shiga,su Sultan ma suka koma cikin tasu ,sannan suka bar gurin.
Kai tsaye gidan da suka sauka suka koma,dan yau suke don komawa Ghana,
Fattu sai murna take daga ga baffanta.
Wanka kawai suka bari baffa yayi,aka bashi wasu kayan ya sanya,kafin suka daga sai Ghana....
Masu karatu bari muyi musu rakiya zuwa ghanar muma.
Ina kuke
Masoya anty mammy?
Albishirinku,ina mai farin cikin sanar daku,sabon littafina mai suna RAINON DAWA,yana nan akan hanya,da zarar mun kammala MACIJINE,hmmmm
Daga jin sunan kinsan ba magana.
Karku bari abaku labari.
Ga mai bukata ,zai iya biyan kudinsa tun yanzu,domin nan da kwana uku zaku fara samun wannan kayataccen labarin na RAINON DAWA.
akan fashi mai sauki,
Normal group 300
Special group 500
Sannan akwai manyan mata dake son atura musu private to kuma ga naku farashi,1000
Dan haka saina jiku,
Acc. No.
Saratu kabir
A.u.b
2215749011
Saiku nuna shadar biya ta wannan no.
08148360851
Saina jiku,masoya.
Show ne your love akan novel ɗi Nan,
😍😍😍🥰🥰🥰🥰
Mrs babi ce💘💘
[30/08 15:01] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din👆🏽
Free book
Page 93/94
_______________Ko a cikin jirgi fattu na kusa da baffanta,wanda yayi tsuru cike da tsoron jirgin,dan kuwa wannan shine karon farko daya hau jirgi.amma haka fattu ke kwantar masa da hankali har suka ƙarasa Ghana.
Part guda aka warewa baffa wanda ke dauke da duk wani kayan more rayuwa.baffa ya cika da farin cikin ganin irin rayuwar jin dadin da fattunsa keyi.abinci kala kala aka ajiye masa,har yama rasa wanda zaici.haka fattu keta zuba masa abincin tana tura masa.
Saida ya huta sosai nutsuwarta ta dawo jikinsa, sannan aka taru apart din da aka saukeshi, har Sultan Habib.godiya suka farayiwa baffa,bisa irin taimakon da yayiwa rayuwar yarsu,sannan suka ce suna bukatar yayi zamansa anan gurinsu,tunda bashi da kowa acan Nigeria.
Kuka kawai baffa keyi na gani yadda bayin Allah nan ke karramashi, suna son ya kasance tare dasu,amma wadanda ya taso cikinsu,haka suka koreshi korar kare bayan sun karbe masa dukiya.
Fattu ce ta dan turo baki tana kallon innarta da mahaifinta,kafin tace "Ni gaskiya ban yarda baffana ya zauna anan ba,tare zamu tafi dashi can gida,bana son yayi nesa dani,kuma shima yafi son zama kusa da fattunsa ko baffa"fattu ta faɗa cikin salon shagwabarta.
Murmushi baffa yayi,yace kwarai kuwa fattun baffa,duk inda kike to Nima Ina can koda kuwa cikin dokar dajine"baffa ya faɗa cikin murmushi.
Dariya sukayi suma,kafin mahaifin fattu yace "wato dai zara kin kwace mana baffanki ko?"ya faɗa da murmushi akan fuskarsa.
Dariya fattu tayi kafin tace "Allah ba haka bane daddy nayi kewar baffana,kuma nima inason in kula dashi,kamar yadda ya kula da rayuwata abaya"
Jinjina kai sukayi gaba ɗaya,suna ayyana irin kaunar dake tsakanin fattu da baffanta.
Kafin su bar kasar Ghana saida mahaifin fattu ya mallaka wa baffa kanfaninsa na ƙera takalma da jakunkuna,ya maida sunan sa akan takardun kamfanin,sannan ya bashi gida,wanda idan yazo zai rinka sauka aciki sannan ya damkawa fattu takardun gida dana kamfanin,harda mukullin sabuwar mota yar yayi.
Kuka sosai baffa yayi yana godiya,fattu ma tayi matukar murna sosai.adeeb kam godiya yayiwa Sultan habeeb,haka innar fattuma ba'a barta abaya ba,dinkuna ta sanya aka yiwa baffa,na gani na faɗa, masu kyau da tsada.sosai baffa ke yaba karamcin iyayen fattu,ba abinda zaice saidai Allah ya saka musu da aljanna.
Washe gari kuwa jirginsu ya daga zuwa Misra,fattu harda kukan rabuwa da yan uwanta,haka innarta ta cika ta da kayan gyara kala kala.
Wani ƙayataccen bangare su fattu suka sauka,wanda bayan tafiyarta Ghana ,Adeeb sanya aka kera musu.tsyawa fadar irin tsaruwar da bangaren yayi abune mai matukar wahala.kallo daya zakayiwa gurin kasan an kashe kudade makudai.
Baffama bangare guda aka ware masa inda zai zauna.haka yasha kyaututtukan gurin iyalan Adeeb,sannan shima Adeeb ya ba baffa kanfaninsa na motoci,baffa neman zaucewa yayi da irin wannan kyautukan da ake ta bashi.
Sosai ake girmama baffa cikin fadar,dan kowa yasan shidin waye.
Cikin lokaci kalilan baffa ya wanke yayi fes dashi,masha Allah kyakykyawan bafillatani,yayi kiba ya koma Alhaji sosai.ba jimawa suka shirya shida Adeeb da fattu dasu nanny sukaje suka sauke farali.
Sun dawo da kwana uku aka shirya gagarumin taron nadin Adeeb matsayin sarki.sannan ranar za'a gudanar da bikinsu shida fattu.
Anyi taro na ban mamaki wanda saida ya girgiza duniya,taron daya hada sarakunan hasashe daban daban,daga turawa,larabawa zuwa hausawa,ba kalar mutanen da babu agurin.
Taro yayi taro,an nada Adeeb matsayin sarkin misra,SULTAN ADEEB MUHAMMAD ASHRAF.
haka aka kammala taro ya tashi lafiya,kuma ranar Adeeb ya mallaka fattu dankareriyar mota mai shegen tsada da kyau,sannan ya mallaka mata kamfaninsa wanda ake hada mayukan shafawa na mata da kayan kwalliya.
Murna dai agurin fattu ba'a cewa komai.
Sati biyu da nada Adeeb matsayin Sarki,fattu ta kama laulayi, wayyo kuzo kuga murna gurin bayin Allah nan,haka nanny ta zage tana kula da fattu,ita da amma,suna bata gata da kulawa sosai,haka uban gayya,dan har kuka yayi lokacin da labarin cikin fattu ya sameshi.kuma yayi mata alƙawarin idan ta haihu ta zabi inda take son zuwa yin karatu.
Cikin fattu nada wata biyar aka yi auren tareeƙ da wata yar uwarsa,rana daya aka daura auren dana Rashad,anyi biki na kece raini,su fattu sune akan komai na biki, zakuyi mamaki yadda fattu ta zama babbar mace,tayi mugun kyau har ta gaji,suna nunawa juna soyayya mai tsafta ita da Adeeb,yayin da suke rainon cikinsu cike da so da kauna.saidai fattu tana da girman ciki,dan yanzu haka inka ganta zaki tunanin cikin yakai wajen watanni bakwai, dan girmansa.
Komai yana tafiya daidai arayuwarsu fattu,basu da wata matsala yanzu,domin suna cikin aminci da kulawar yan uwa,sarauniya suhaimat da Sultan habeeb,sunyi matukar murna da samun cikin fattu,addu'oi kuwa,ba irin wanda fattu bata samu,domin takanas ake biyawamutane makka,dan suke suyi mata addu'a.
Lokacin da cikin fattu ya cika wata tara,ko tashi bata iyayi da kanta,saidai idan Adeeb ya tasheta idan tana zaune ko kwance,amma kasancewarta mai hakuri da kawaici,haka take daurewa tana nuna bata jin wahalar ciki,shikuwa Adeeb tausaya mata yake sosai.
Wata rana da safe suna barci nakuda ta kama fattu,aikuwa,nan da nan likitoci kwarraru,wadanda ke mata awo suka rufu akanta,cikin hikimar ubangiji,fattu ta haifi yaranta takwaye, mace dana miji masu matuƙar kama da Adeeb, kyakykyawa na ban mamaki.
Irin murnar da ahalin nan suka nuna abin ba'a cewa komai,ta ko ina zuwa ake ganin jarirai,ranar suna aka sanya musu sunan baffa dana Nazli,Abubakar,amma ana kiransu da Ameer da ameera.
Fattu ta sami alkairi sosai haihuwar yaran nan.dan motoci ma sun sami sama da guda sha biyar,banda gidaje da tsabar kudi.sai muce Allah ya raya twince.
Bayan suna da sati biyu aka daura auren baffa da nanny,bisa ga amincewarsu,bayan fattu tayi shawara dasu,ba nuna ja suka amince,dan dama sun kamu da son juna.
Ammi kullum abu sai kara lalacewa yake,hauka take tun ƙarfi,gaba ɗaya ta gama kwarzane jikinta,tananan kamar wata horuwa, tayi ta ihu tana yakushun jikinta.(ai dama ammi hausawa sunce idan zaka gina ramin mugunta ka gina daidai da kai,hakkin rayukan da kika kashema kadai sun isheki)
Waziri ma yana gidan yari,saidai shikam yayi ladama,ya koma ga Allah,kullum yana istugfari.
Yaran fattu sun taso cikin kulawa da soyayya,idan kun gansu gurin fattu,to nono kawai zata basu,dan tuni ta fara karatunta ,tace anan gida zatayi karatu,bazata je ko ina ta bar mijinta ba.
Abin sai son barka,rayuwa tayi musu daɗi,suna zaune cikin kwanciyar hankali,fattu ta buɗe gidajen marayu ajahohin Nigeria sosai,ta taimakawa yan kauyen su,tayi musu makaranta, ga ruwa ya wadata,ta tallafawa mabukata, gaba ɗaya sunyi nadama abinda suka yiwa fattu da baffanta,dan lokacin da baffa yaje basu ganeshi ba,haka gwogwgo hansai tayi ta kuwa wai ya maidata dakinta,dariya kawai yayi tare da bata makudan kudade kafin ya bar kasar.
Amare da angwanye ma suna zaune cikin aminck da soyayya,yayinda ko waccensu ke dauke da yaron ciki,saidai muce Allah ya raba lafiya.
Fattu ce zaune akan kujera tana bawa ameer nono,yayinda Adeeb ke gefenta riƙe da ameera,kallonta yeke cike da ƙauna da sha'awa,yadda take shayar da yaron cikin nutsuwa.
Ajiyar zuciya yayi tare da faɗin "Alhamdullah ,Allah na gode maka kacikani da ni'imarka ta ko ina ,ka bani mace mai hankali da nutsuwa,sannan ka hadamin kan ahalina,ka bani yara kyakykyawa har biyu a lokaci daya,Allah Nagode maka"Adeeb ya faɗa cike da kushu'i yana mai jin dadi cikin ransa.
Murmushi fattu tayi tare da kamo hannunsa tayi kissing, sannan ta Dora kanta akan kafadunsa, tace "Ina sonka mijina kaine farin cikina,kuma rayuwata,Allah ya raya mana yaranmu bisa hanya madaidaiciya"
"Ameen Hulwa ana ahubbikteeer Hulwa anti sururi"ya faɗa yana mai kara rungumeta ita da yaran ajikinsa.
Tammat bi hamdillah.anan na kawo karshen wanna littafi Mai suna MACIJI NE.
Jinjina gareka mijina,na gode da gudunmawarka gareni,Allah ya bamu zaman lafiya,ya raya mana zuri'a.
Much love.
Godiya ta musamman gareki,maman nafi,na gode sosai da gudun mawarki akan wannan littafi.
Gaisuwa gareku macijine fans inq kaunarku.
Jinjina ga elegant online writers,Allah ya hade kanmu.
Ina godiya gareku yan uwana,da addu'ar ku gareni 🫠🫠🫠
Allah ya sa mu amfana da darasin dake cikinsa,muyi watsi da sharrin dake cikinsa.
Allah ka yafe mana kuraruranmu,kasanya imaninmu ya nunku fiye da nada.
Godiya agareku masoyansa ,da kukayi ta bibiyar wannan littafi,tun daga farko har karshe,Allah ya hadamu gidan aljanna.
Sai mun haɗe daku cikin sabon littafina
RAINON DAWA.
Ga mai bukata,zai fita kudinsa kamar haka.
Normal group 300₦
Special group 500₦
Manyan mata masu bukata ta private,kuma ga naku1000₦
Zaku biya ta wannan acc. Din.
Saratu Kabir
U.b.a
2215749011.
Evidence of payment
08148360851
Saina jiku masoya.
Show me You love,
Kuyi payment na wannan littafin.💘💘💘
Kada kusake baku labari.
Saina jikiku.
Takuce har kullum anty mammy.
Mrs babi💘💘