Showing 3001 words to 6000 words out of 116224 words

Chapter 2 - Maciji ne book 1

28 Aug 2024

25285

sanyata zabura ta miƙe da sauri tana haki,kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta kuma taji duka yana sauƙa ajikinta ta ko ina ,ihu ta fara tana neman taimako amma ba wanda yazo dan taimakon nata,dan baffa yana masallaci kasancewar shine limamin rugar,

"Wayyo Allah na gwogwgo kiyi haƙuri wllh bazan ƙara ba ,tsautsayine yasa na fashe miki bokati, dan Allah kiyi haƙuri gwogwgo"abinda fattu ke daɗi kenan cikin azaba dan ko ina na jikinta ciwo yake mata barin ma hannunta daya kumbura sosai ,alamun tayi targaɗe a hannun kenan.
"Wllh yau saina kasheni Shegiyar yarinya muguwa, kafin baƙin cikinki ya kasheni ,na Tsaneki fattu bana ƙaunar ganinki arayuwata, kinsan nawa nasai bokatin nawa?kika je kika fashemin shi? Murtala huɗu da nairagoma fa na siya,wllh saina daki kuɗina kuma kije duk inda zaki samo min kuɗin bokatina ki samomin dan bazan ɗauki asarar ba"gwogwgo ta faɗa tana haki,kuma bata daina jibgar fattu ba ,kamar ta sami jaka.
"Wayyo gwogwgo dan Allah kimin rai hannuna zai karye, wllh bada gangan na fashe miki bokati ba,macizaine suka biyo ni zasu cinyeni shine na gudu amma bada gangan nayi ba wllh"ta faɗa cikin azaba dan tuni ƙarfinta ya kare ko iya ɗaga hannunta bata yi.

"Allah ya tsine muku keda mashizan shegen yaro karuwa ,ina ruwana da macizai ?dama sun cinyeki kowa ya huta mai baƙin hali marar farin jini har yanzu kin kasa auruwa ,dama shegun macizan sun.......kasa ƙarasa magannarta tayi sakamakon wani ƙaton abu dataji ya faɗo kanta jifff !!!kamar buhun hatsi.

"Wayyo Ni Hansai menene wannan ɗin yake zagayemin jiki?ta faɗa cikin firgici da tashin hankali tana mai jefar da iccen hannunta.aikuwa carab idanunta suka sauka akan ƙaton macijin daya nannaɗeta ko motsi bata iya yi,kuma ya fasa kai a saitin fuskarta sai huci yake yana Filato da harshe.

"Wayyo Allah na Ni hansai yau me zan gani ?na shiga ukuna malam kazo fattu ta min ture maciji zai kasheni ka taimakeni, handi ɗin bonu lalashewa ni yar nan wayyo malam"ta faɗa cin tsantsar tsoro da razani da ƙyar take magana dan ba ƙaramin shaƙar mata jiki macijin yayi ba har wuyanta.

Tsoro,fargaba da tashin hankali sune suka daɗa kashewa Fattu jiki ,dan faɗuwa tayi ƙasa warwas ko motsin kirki bata iya yi,shikenan Tata ta ƙare yana gamawa da gwogwgo tasan kanta zaiyo ,Allah Sarki innarta ,yanzu shikenan zata mutu bataga innarta ba,batasan ya fuskarta take ba ?bare tasan dangin innarta?,amma Gara ta mutumma ta huta da wannan baƙar azabar da take sha agurin gwogwgo.

Shikuwa macijin nan ƙara matse gwogwgo yake sosai ,gaba ɗaya ta fice daga hayyacinta,dan ko magana ma ta kasa ,idanunta sunyi jajur sai nishi take numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa.
Saida macijin nan yaga gwogwgo bata motsi alamun ta suma,kafin ya sake ta ta hanyar janye jikinsa daga gareta.

Da gudu kuma yayi kan fattu wacce ke kwance cikin tashin hankali ganin yadda macijin nan ya kashe gwogwgo.runtse ido tayi da mugun ƙarfi tana salati da sallama da duniya,ko motsin kirki batayi ,dan da kyar take iya jan numfashi ma.

Shikuwa macijin nan yana zuwa gareta ya tsaya saitin fuskarta ya fasa kai yana huci,sai kuma ya fara zagayeta cikin sauri da sassarfa, kafin kuma ya fara hayewa kan ruwan cikinta........

Masu karatu mezai faru da fattu ?

Me macijin nan yake nufi da ita ne?
Anya ma macijin ne shi?

Saimun haɗe next page in Sha Allah taku har kullum anty mammy
Mrs babi💘💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LsrDragdsZn2UMCRLPA7uv


Banda maza Please mata kawai .

By mammy kabeer





🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJINE SHI 🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)




Elegant online writers📚📚


Free book

Page 7/8







________________Ihu jauro ya kurma mai ƙarfin gaske ya faɗi can gefe yana burbura tare da rikan "wayyo haroji jaurota zai cinyemin ka taimakeni zan mutu wayyo maciji "ya ƙarasa faɗa da kyar sakamakon wata danƙa mai ƙarfi da macijin nan yayiwa jauronsa har saida numfashinsa ya ɗauke .


Haroji kuwa ya mugun tsorata ganin halin da jauro ke ciki,ga wannan ƙaton macijin daya kanannadeshi yana ƙoƙarin karya masa ƙasusuwa.

Cikin kiɗima ya rarumo wani ƙaton dutse yayi kan jauro da wannan macijin,yana zuwa baiyi wata wata ba ya ɗaga dutsen ya kwaɗawa macijin nan abayansa.
Aikuwa nan da nan bayan macijin ya fashe jini yayi tsartuwa har kan fuskar haroji,wani ihu haroji ya kwala ,sakamakon sauƙar jinin macijin nan akan fuskarsa ji yayi kamar an watsa masa ruwan batir,nan da nan gurin ya sale kamar wanda ya ƙone sai turiri gurin yake.
Jifa haroji yayi da dutsen hannunsa yana ihu yana faɗin"wayyo Allah idona bana gani wayyo kwayar idona ta zazzage na shiga ukuna "abinda yake daɗi kenan yana ihu da tsalle.
Shikuwa macijin nan silalewa yayi daga jikin jauro ya koma gefe guda tare da kwantar da kansa akasa ,dan kuwa sosai haroji ya kwada masa dutsen nan,kuma da alama ya shige shi .

Gaba ɗayan abinda ke faruwa akan idanun fattu ,tana kwance tana kallon ikon Allah,tabbas zuwa yanzu ta gama yarda cewa macijin nan bashi da biyar cutar da ita ,saima taimakon ta da yake,shin wanene wanan macijin?meye alaƙarta da shi?me yake nema agurinta?anya ma MACIJINE wannan ?kodai aljanine yake zuwa mata asiffar macijin? Wadanna sune tarin tambayoyin da fattu ke yiwa kanta tana daga kwancen wanda bata da amsarsu.

Saidai kuma gaba ɗaya hankalinta ya tashi ganin yadda macijin nan ya kwanta lamo kamar ya mutu.nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta ,cikin dauriya da jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye tana yamutse fuska,hannunta mai ciwon yana riƙe aɗaya mai lafiyar.

Gurin macijin ta nufa gabanta na ci gaba da faɗuwa,dan tsoro take kar ita kuma yayi mata wani abu.tana ƙara sawa ta durƙusa ahankali dai dai inda haroji ya buga masa wannan dutsen ,hannu ta sanya ahankali ,cikin karkarwa jiki ta ɗan shafa gurin ciwon.ai tana ɗora hannunta agurin macijin nan yayi wata irin juyowa tare da fasa kai kamar zai sareta, cikin tsoro da fargaba ta cire hannunta tare da matsawa baya da sauri tana zare ido tana kallon macijin.
Shima yana juyowa yaga fattu ce ,sai ya tsaya yana kallon ta,tare da komawa yadda yake ,wato ya sassauta fusatar da yayi ,kawai ya tsaya yana kallon ta.
Itama kallonsa take cikin tsoro da bugawar zuciya,ahankali macijin ya fara tahowa ,har ya zo gareta ,runtse idanu tayi tana karanta addu'ar Allah ya tsareta.
Ga mamakinta kawai saitaji macijin ya hau kan cinyarta ya kanannaɗe jikinsa ya dora kansa a saman gammon da yayi da jikinsa.

Ahankali ta buɗe idanunta tana kallonsa,shima ita yake kallo saidai idanunsa na zubar da hawaye kuma na jini .

Jikinta kawai rawa yake cike take da tsantsar tsoron abinda zai faru .juyawa tayi tana kallon haroji dake ta faman ihu yana yaɗuwa kasa.sannan ta kalli jauro wanda yake kwance ba alamun numfashi atare dashi,ga jauronsa nan tayi wani irin kumbura na ban mamaki sai jini ke zuba .

Tsorone ya ƙara kamata cikin azama ta yunƙura tare da mikewa tsaye, ture macijin tayi daga jikinta ta kwasa da gudu tayi gida tana kuka .
Koda taje gidan, da sanɗa tayi saurin shiga ɗakinta tana kuka,zama tayi akan tabarmarta tare da kife kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka.damuwace fal cikin ranta,wai meke shirin faruwa ne da rayuwarta?wacece mahaifiyarta?waye wannan macijin da yake ɗaukan hukunci akan duk wanda yayi nufin cutar da ita?tanasan sanin wannan macijin waye shi,kokuma waye ya aikoshi gareta.tana cikin kukanta ne kawai taji abu yana hawa jikinta silililili!!! Afirgice ta ɗago kanta tana kallon macijin daya gama hawa jikin nata. kansa ya ɗora akan wuyanta yana fidda wani irin huci ,shiru tayi tana sauraron yadda macijin ke huci,sanan jikinsa yayi wani irin zafi sosai.duk yadda akayi bashi da lafiya ,kuma dukan da haroji yayi masane solar hakan.
Tausayinsane taji yayi mugun kamata,ahankali cikin tsoro ta miƙa hannunta tare da riƙo saitin wuyansa ahankali ta janyoshi, ko motsi baiyi ba bare ya hanata abinda yake yi ɗin.

Akan tabarmar ta ɗorashi tare da ci gaba da kallonsa,cikin muryar kuka tace "bawan Allah kai waye?meke tafe dakai?waya aikoka zuwa gareni?meyasa kake ƙoƙarin daukar mataki akan duk wanda ya zalumceni?dan Allah karka cutar dani, bani da kowa sai baffana,dan Allah kayi tafiyarki ,idan mutanen garin na suka farga da kai zasu kasheka ,bazan so hakan ba dan Allah na roƙeka ka tafi"ta ƙarasa maganar tana haɗa hannunta cikin kuka.

Shidai macijin nan ko motsi baiyi ba sai huci da yake yi sosai,
Ahankali ta kalli gurin da yaji ciwo dazu sai taga gurin yana turiri kuma yayi wani fari fat.shiru tayi tana kallonshi ,yanzu ya zata yi masa ne?dan da alama fa yana jin jikine, data rasa abinyi kawai saita lulluba zanin sallarta ta fara karatun Alqur'ani mai girma.cikin abinda bai wuce sakwan biyar da fara karatunta ba kawai macijin nan ya fara wata irin murmurɗewa yana sauya kala, da farko yayi jajur dashi,sai kuma yazo yayi baƙiƙirin sosai ,wani irin hayaƙi na fita daga jikinsa .
Duk abinda yake sam fattu bata kulaba ,dan ta ɗaga kanta sama ne tana karatun ,kuma idanunta na zubda kwalla.

Shikuwa macijin nan burburwa ya ci gaba dayi yana murɗewa jikinsa na turiri tare da sauya kala.can kuma ya fara wani irin ƙara mai kama da gurnanin zaki.cikin tsoro fattu ta dawo da kanta ƙasa tana kallon macijin , sakamakon wannan sautin ƙara da taji yanayi.sai lokacin hankalinta ya kai kanshi taga abinda ke faruwa.
Tsorone ya kamata ƙarara "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"shikenan ta tabbata wannan ba maciji bane tabbas aljanine ,ko kuma aljanine ya shiga jiki sa,na shiga uku ni fattu ya zanyi da rayuwata?meke shirin faruwa dani" ta faɗa cikin muryar tsoro da shiga ruɗu.
Shikuwa macijin nan tana daina karatun saiya daina burburwar da wanann gurnanin,ahankali kuma jikinsa ya dawo yadda yake . Ya jima kwance lamo kafin ya fara motsi,kansa ya ɗago tare da fasa kan yana kallon fattu,gaba ɗaya idanunsa sun koma baƙiƙirin dasu sannan wasu irin ƙananan layoyi suka bayyana kusan guda uku aƙasan kanshi, sai wani irin motsi suke kamar ya'yan tsutsa.

Karkarwa jikin fattu keyi kamar an saka mata shokin, lamarin ya matukar bata tsoro ,meye wannan ɗin haka suka bayyana jikin macijin nan? Me yasa daga fara karatun Alqur'ani gaba daya ya sauya kama?tabbas akwai wani boyayyen al'amari game da wannan halittar dake gabanta,kuma zata ci gaba da bibiyar macijin nan sannu kan hankali har saita gano menene tattare dashi.

Tana nan maƙale jikin katangar karanta kamar ƙadangaruwa dan tsabar tsoro da shiga shock ,idanunta ƙuri akan macijin ,wanda shima ita yake kallo ,kusan minti biyar suna haka ,taga macijin ya sulale ya bar ɗakin ta wannan hanyar tashi.

Rarraba idanu ta farayi tana dafe da ƙirjinta ,yau kam tana ganin ikon Allah kala kala ,anya kuwa bata janyowa kanta masifa ba?waima meye alaƙarta da wannan halittar ne?ko dai baffanta zata sanarwa halin da ake ciki ne?kai a'a ba yanzu ba tukunna ,ya kamata ta zama jaruma tayi wanann aikin koba komai zata taimaki rayuwar macijin,dan ta fahimci akwai boyayyen al'amari atareda shi.

Su haroji kuwa gaba ɗaya ya fice daga hayyacinsa sai ihu yake yana faɗuwa ƙasa ,ahaka ya nufi gidan lamiɗon garin ,wanda shine mahaifin jauro ,yana ihu yana tumami, har yaje gaban lamiɗo ya faɗi yana "wayyo idanuna ,wayyo fuskata lamiɗo ka taimaka min.

Ruɗewa lamiɗo yayi wanda yake tsaye jikin wata sanuwa yana bata ciyawa, lamiɗo bashi da imani ,azalumine sosai ,kuma mutanen garin suna matuƙar tsoronsa, dan haka yake mulki na zalumci agarina,ganin halinda haroji yake ciki"kai haroji menene hakan ?ina jauro?me yasameka?sune tambayoyin da lamiɗo ya jerowa haroji

Cikin azabar ciwo da fitar hankali haroji yace "jauro ya mutu maciji ya cinye masa jauronsa yana bakin rafi"
Ai dajin wannan batu hankalin lamiɗo ya tashi ,nan da nan yayi kan haroji yana faɗin wane macijin ?me kake cewa ?jauro ya mutu?ƙaryane badai agarina ba ,ba wanda ya isa ya zo garina ya kashe min ɗana."lamiɗo na gama faɗin haka ya kira mazan garin ,ya sanar dasu maza aje bakin rafi ataho da jauro.
Aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauko shi kamar gawa .

Nan da nan lamiɗo ya nemi haroji ya sanar dasu abinda ya faru .
Nan ya sanar dasu iya abinda idanunsa suka gani,dan shima yana cikin mugun halin mutuwa ko rayuwa dan tuni gurin da jinin nan na macijin ya taɓa ajikinsa yayi wani irin kore shar yana zubar da wani yallow ɗin ruwa .

"Lamiɗo fattu ce ta Turo mana macijin nan ,shine ya kashe jauro"abinda haroji ya faɗa kenan ya sume.

Nan da nan mutanen gurin suka fara maganganu Suna faɗin da "da hansai ta faɗa tace mayyace yarinyar ,tunda har ta fara kashe mutane ba zasu yarda ba sai an hukunta itama.
Ran lamiɗo ya ɓaci sosai ,dan dama yana jin haushi yarinyar da ubanta,ya shirya neman aurenta amma sam taƙi yarda wai karatu take,yanzu kuwa dama tasameshi da zai hukunta su ita da tsohon nata.dan haka cikin bada umarni yace lallai lallai aje ataho da fattu da ubanta .

Nan da nan fusatattun maza suka nufi gidan malam bukar dan aiwatar da ƙudurin lamiɗo........


Masu karatu meke shirin faruwa ne ?

Wane hukuncin lamiɗo zai zartar akansu fattu?

Mai zai far nan gaba?
Muje zuwa yaki ce dai anty mammy

Mrs babi💘💘💘

Share and comments fisabilillah.

More comments
More typing.🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄




MACIJINE 🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)




Elegant online writers📚📚


Page 9/10





__________________Nan da nan fusatattun rugar suka nufi gidan malam bukar ,dan aiwatar da ƙudirin lamiɗo.

Allah Sarki fattu kuwa a wanann lokacin tana ɗakinta cikin jimami da tunanin abinda ta gani yau ɗin nan,haka nan ta tsinci kanta da son sanin menene wannan abubuwan dake motsi aƙasan wuyan maciji? wanda tun daɗewa bata taɓa ganinsu ba sai yau,waya sani ma ko wani akayiwa asiri ajikin macijin ?tabbas zatayi iya ƙoƙarin ta dan ganin ta raba macijin nan da wannan abubuwan ,ta yadda koda wani aka yiwa asiri ta hanyar macijin, to asirin zai karye .sannan tana fargabar gwogwgo ta gano cewar tana gidan kuma bata ɗebo ruwan ba.kuma ahalin da ake ciki yanzu bazata iya komawa rafin nan ba ,.dan ta tsorata dasu jauro .

Hayaniyar mutane ce ta cika gidan nasu fattu ,wanda haka yasa gwogwgo hansai fitowa dole badan ta soba, Dan har lokacin nan ita da yaranta ba wanda yayi sallar asuba.

"Kai su waye haka suka zo suka cika mana gida da ihu kamar ana yaƙi?"cewar gwogwgo hansai tana gyara daurin ƙirjinta dake ƙoƙarin kuncewa bayan ta fito daga ɗakin.
"Aa meye hakan arɗo ?lafiya na Ganku da yawanku kun shigo?ta tambaya lokacin da idanunta ya sauka akan mutanen da suka cika gidan,kusan duk mazan garin ne.

Cikin masifa wanda aka kira da arɗo yace "wllh yau saimun ɗauki mataki akan bukar da fattu ,haka kawai yarinya ta fara kashe mutane ,kuma ta rasa ta kan wa zata fara sai ɗan gidan lamiɗo ?wllh yau sai mun kashe Shegiyar yarinyar nan"ya faɗa yana wani zazzaro idanu kamar zararre.

Eh wllh afito mana da ita kawai mukaita gurin lamiɗo ya bamu izini mu kashe mayya.gaba ɗayan mutanen gurin suka faɗi haka cikin nuna fusata da ƙosawa abasu fattun .

Wani irin farin ciki da jin daɗine ya kama gwogwgo hansai ,shikenan zata rabu da alaƙaƙai cikin sauƙi Allah yasa akasheta kowa ya huta ,dama su haɗa da bukar ɗin da yake ɗaurewa fattu gindi ,koba komai shanunsa sun zama nata.gwogwgo hansai ta faɗa cikin ranta.kafin ta kalli arɗo da sauran mutanen tace "aikuwa idan aka kasheta an kyauta ,dan nima nan wllh so take ta cinyeni nida yarana, jiya da kyar mukasha data maƙuremin wuya wai saita cinyeni, ku ɗan jira kaɗan yanzu zaku ganta shegiya gantalalliya,banma san inda ta tafiba, dama haka takeyi kullum inta fice yawon iskanci bata dawowa da wuri,tana can gurin maza"gwogwgo hansai ta ƙarasa maganarta tana mai buga hannu acinya.

"Aikuwa yanzu zamuje mu nemota ko ina ta shiga,wasu sutafi bakin rafin wasu sushiga jeji, mukuma zamu jira ana "cewar arɗo kenan yana kafe sandarsa akasa,sannan ya gyara tsayuwarsa.


Duk wannan abunda ke faruwa akan kunnen fattu, tana jin komai ,saidai tashin hankali,firgici tsoro da kuma ruɗewa sun hanata koda yin kwakwkwaran motsine .
Numfashinta ma da ƙyar yake fita tsabar ruɗewa.
Ta shiga uku !shikenan yanzu kasheta za'ayi?laifin me tayi da za'a kasheta?me baffanta yayi ake nemansa shima? Dama jauron mutuwa yayi ? innalillahi !!!yanzu ya zatayi.

Wani kukane ya kubce mata cikin sauri ta toshe bakinta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,ji take dama tana da ikon ɓacewa, tabbas da ba abinda zai hanata ɓacewa ta bar duniyar ma gaba ɗaya.

Ahankali ta miƙe cikin sanɗa ta leƙo da kanta ,ba ƙaramin tsoro tajiba lokacin da taga mutanen da suka zo tafiya da ita.shikena kawai ta mutu,yanzu shikenan bazata cika burinta na ganin innarta ba?wayyo "Allah ka kawomin ɗauki "ta faɗa cikin raunananiyar muryarta mai cike da tsantsar tsoro.

Ahankali ta ƙara leƙo da kanta waje ,cikin rashin Sa'a kuwa sukayi ido huɗu da dan gidan gwogwgo hansai umaru.wanda hayaniyar mutane tasa suma suka farka.

"Laaaah aradu gwogwgo ga fattun can cikin ɗakinta tana leƙowa"ya faɗa yana nuna ɗakin da Fattu ke ciki
.cikin hanzari fattu ta koma cikin ɗakin tana mai runtse idonta ,tare da dafe ƙirjinta."shikenan sun ganni wayyo Allah na baffa,wayyo MACIJINA kana ina kazo ka taimakeni zasu kasheni wayyo ni fattu"fattu ta faɗa tana mai leƙa hanyar nan da macijin Kebi idan zai bar ɗakin nata inya zo kamar Zariya haka take bankada hanyar macijin da hannunta.

"Munafuka ,mayya dama kina ji ana neman ki shine kika ɓuya nan?to fito yau dubunki ta cika ,mutuwa zakiyi wllh saikin bar duniyar nan yau nima na huta da ganinki ,maza arɗo zoka tafi ta ita gata nan"gwogwgo hansai ke faɗin wannan maganar tana daga bakin ƙofar dakin Fattu,dan tun lokacin nan da tasha matsa agurin maciji bata ƙara shiga ɗakin Fattun ba.
Aikuwa kafin ta rufe baki su arɗo sukayo kan Fattu suna janta.

"Wayyo Allah gwogwgo karki bari su tafi dani zasu kasheni ,wllh ban aikata komai ba wayyo Allah na gwogwgo ki taimaka min"abinda Fattu ke faɗi kenan tana miƙawa gwogwgo hannu cikin kuka mai tsanani.

"Ai wllh dana taimakeki gara hannuna ya karye Shegiyar yarinya ,kutafi da ita can ku kashe banza" gwogwgo ta faɗa tana kaɗa hannu irin yadda ake korar kaji ,cikin farin ciki take maganar.

Ihu Fattu keyi tana kuka,amma haka suke janta kamar akuya aƙasa, suna cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login