Showing 54001 words to 57000 words out of 70847 words
Fatima.
Fatima da dama tun da tagansa taji guy din yyi mata, cikin jin kunya ta gudu cikin gida.
Murmushi kabeer yyi yace mun had'u a next tima.
Murmushi su Hafsat sukayi ,sa'ada tace ah lallai su yaya an kamu to ai kawatace sai kai kamun k'afa aguna na shigar da kai gunta.inkuma kaci zalin dina wlh nazugata kurabu.
Murmushi yyi had'e da marairai cewa yace haba y'ar autarmu ai yanxun nadena cin zalinki,muje gobe sai muxo tare gunta xance kinga sai ki shigar da ni sosai.
Sa'ada tace to shikenan Yayana muje.
Nan suka fito ,kabeer nata tsokanar Hafsat.
Awaje suka sami su mommy zasu tafi gida.
Nan Hafsat ta saka rigima ita abarmata mamanta ,dan tanajin kunyar xuwa gidansu sir Aliyu kasancewar shi xata aura da tuni ta bi mamanta acan sun kara gaisawa.
Rarrashinta mommy ta yi tace jibifa mamanku zata dawo kinji inkuma mutafi dke to sai kusake gaisawa.
"Cikin jin kunya tace ah ah."
Sir Aliyu kuwa da ita yake kallo yaso ta bisu amma sai tace wani ah ah.
Nan dai suka shige mota, Hafsat ta saci kallon sir Aliyu taga ya had'a rai yana wani shan kamshi ,juyawa tayi tabi baba cikin gida murna fal aranta da farin cikin.
sukuma su senator suka bakabar anguwa r cikin jin Dadi.
A cikin gida kuwa Laure hankalinta yatashi dan tasan kashinta yabushe ,musammun da ta tuna kalaman baba nacewa duk sadda yaga matarsa saisun rabu.
Hakan yasa ta dauki niyar yau in rana tayi sanyi zataje gun boka dan baza bari hakan yafaru ba dan saitara ba mairo da Mlm aminu kota halin k'ak'a.
"Tana cikin wannan mugun tunanin nata baba da Hafsat suka shigo suna murna,."
Tsaki taja hade da cewa wlh kaji kunya ace mace taje tagama yawon duniyarta ,tayo hayar kaya da mutane shine za'azo a yaudareka ko?
Wata harara mlm aminu ya Aiko mata da ita yace eh naji komai tajeyi bama yawon duniya ba ahaka nake sonta,sannan wad'anda kikace ta dauko haya to iyayan Aliyu ne Wanda zai auri Hafsat inbaki saniba ki sani sai bak'in ciki yakasheki.sannan yace kuma jibi matata zata tare dan gobe za amaida aurenmu,dan haka ayau za'a fara gyara a gidan nan sbd amaryata.
"bejira amsarta yanufi dakinsa."
Ai Laure jitayi kamar yawatsa mata muta ,sbd maganganun sun shigeta.
Hakan yasa ta dauki niyar tatwatsasu kota halin k'ak'a.
Bangaren su sir Aliyu kuwa.....
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿97&98
b'angaren su sir Aliyu kuwa,koda suka isa gida ,duk aka zauna a waiting parlour anahira da farin ciki. "Sir Aliyu da yalura",mama mairo najin nauyinsa dan taki sakin jikin ta ma gaba daya.
Hakan yasa yabar parlourn yakoma part din sa." Aikamar jira kabeer yake yafita".kasancewar kabeer bawata kunya gareshiba,yakalli mommy yace mommy nifa inada mata!gsky azo ayi bikin yaya ko anyi nawa,Allah kuwa dan amatse nak...dakk'uwarda mommy ta yi masa yasashi kasa ida maganar.
"Mairo kuwa y'ar dariya tayi", tace ah ah mommy aibakya hanasaba xonan kagayamun wacece y'ar tawa.mommy ta harareshi tace hmm kedai rabu da marar kunya ,bama kacewa kasami wadda zaka aura,ah ah matarka ma gaba daya.
" dan rashin kunya ko?"sunkuyadda da kai yyi hade da mik'e wa yabar parlourn mairo kuwa sai murmushi take.sa'ada tayi saurin cewa wlh mommy Fatima ce yaya kabeer keso kawar Anty Hafsat.
Cikin sakin fuska mommy ta ce hmm Allah yasa alkhairi, mairo tace ameen.
Sir Aliyu kuwa yanacan yana aikin nasa wato tunanin Hafsat dan ji yake kamar yakoma yasake ganinta,amma daya tuna d'azun ta wani share shi, saiyaji yafasa zuwa ma gunta duk da yasan kunya takeji.
Tashi yyi yafito dan lokacin lunch yyi nan yaje yasami kowa a dining area suna lunch ,ai yana zama mairo ta tashi dg gun.
"Murmushi mommy ta yi",tace oh ni kinmaida babana sirikinki dg gani sa har kintashi.
Kallonsa mommy ta yi tace kaje part din ka sa'ada zata kawomaka kaga mamarku najin kunyarka.
" yar dariya yyi yace to natafi".nan sa'ada tayi serving nasa takai masa a part din sa.
Bayan anyi lunch mommy ta saka mai kitsonta ta yarfa ma mairo kananun Kitso dama gata da gashi masha Allah yy kyau sosai sannan akayi mata lalle ja ."aitake mairo ta fito a amarya. "
Sannan mommy ta bada mata sabbin dinkuna ayi mata .
*******************
Washe gari da misalin karfe 12:am aka sake d'aura auren mlm aminu da mairo.
"Ak'ofar gidan senator."
Bayan angama ne senator yakira sir Aliyu yace yaje gidan mlm aminu yaduba girman d'akin da za akai mairo ciki.yaje yasa ayimata jere ,kasancewar sir Aliyu fannin Carpenter yakaranta kuma yanada company.
"nan yace to"
Yaje yadauki mota yyi anguwarsu Hafsat.
Agidan mlm aminu kuwa tun 10nasafe Laure ta tattara duk wasu kud'ad'e nata ta nufi gun boka mai yankan wuk'a.
Shikuma mlm aminu murna shar ,aransa dan haka yasa masu aiki suka rushe d'akin Hafsat aka had'a da wani fili dke kusa da dakin akafara ginawa mairo bed room da parlour.
"Ita kuwa Hafsat tana gidansu Fatima."
Koda Sir Aliyu yazo ,bayan sun gaisa da baba yyi masa bayanin xiwansa,nan suka shiga yaduba komai.
"Bayan yagama ,yaga bega Hafsat ba dukda dama bayaso ta zauna gidan sbd ga masu aiki."
Yanaso yatambayi baba ta na ina ? Amma yanajin kunya .da hakadai sukayi sallama yafita, Dede bakin k'ofar fita daga gidan suka had'u da Hafsat saura kiris tafad'a jikin sa.
Tana ganinsa ta fasa shiga ta sunkuyadda kanta had'e da rufe ido.Ku ra mata mayun idanunsa yyi yanajin wani sabon sonta nashigarsa,jiyake kamar ya janyota jikin sa amma yanaganin rashin dacewar hakan.
"Itakuwa ranta bata yyi",sir Aliyu yyi tafiyarsa da sauri ta bude idonta caraf idonta cikin nasa.da sauri yace my Hafsat meyasa kike guduna?
" cikin sanyin murya tace kayi hkuri yaya "bazan sakeba.
Murmushi yyi yace muje mota mu gaisa ko? bbu musu tabisa ,bayan sun zauna yakalleta yace mekika shirya na bikinki?" Shiru tayi",tana maimaita bikinki a zuciyar ta.catake tabbas bayasona dan da yanasona zai ce bikinmu.
"batare data kallesaba", tace babu abinda na shirya.yace meyasa?
" ahankali tace sbd banshirya aurenba."
da sauri yace bakison auren kome,?tsintar kanta tayi da cewa eh.
Atake yaji mugun fad'uwar gaba had'e da bacin, aziciyarsa yace wato yarinyarnan bata sona kenan.
"Atake idanunsa sukayi jajir atsawace yace ok bakya k'aunata kenan ko? To kije gun Wanda kikeso ni zan tafiya.
" atsorace ta kallesa ganin yanayinsa dan batayi tunanin Wannan y'ar maganar zata b'ata masa rai,atsawace yace get out!
"cikin kuka Hafsat ta fita dg motar".
Shikuwa atsiyace yabar gun,ikon Allah kawai yasa yadawo gida lfy.
gaba daya cikin damuwa sir Aliyu yayini dan ya yarda Hafsat bata sonsa,saidai ya d'au alkawarin sai ya cusa mata sonsa sannan zai nuna mata shima yanasonta.
b'angaren Laure kuwa taje gun boka mai yankan wuka kuma yabata maganin dazata zubawa mairo ta tsallaka ,inta tsallaka to xata haukace,shikuma mlm aminu tazuba masa abinci to zai koma mijin tace.
" cikin murna ",ta nufo gd, kasancewar tana cikin farin ciki yasa tazo tsallaka titi bata lura da kyauba burinta taje gd ta aikata bak'in nufinta.
Atake babbar mota ta bigeta ,had'e da take mata k'afa daya ,atake kafar ta gundule ,cikin tsananin azaba Laure ta suma batasan inda kanta yakeba.
Wanda yakade ta yyi asibiti da ita.
________________
Washe gari byn sallar la'asar sir Aliyu yaje da ma aikatansa suka hau shirya d'aikin mairo kasancewar da dare za a kawota.
" dukda yanajin haushin Hafsat Amma ganin be ganta ba yasa sai yan waige waige yake a cikin gidan amma bata nan".
Gab da zasu tafi ta shigo gidan da yuni foam na islamiya jikinta ,kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa.
"Wani irin tausayinta yaji," tunawa yyi itafa yarinyace abinda aka koya mata dashi zata tashi.
Itakuwa tanaganinsa ta nufo gunsa, inda yake zaune a tsakar gidansu, ta duk'a ta gaishi,fuska ba walwala ya amsa ,"ahankali tace dan Allah yaya kayi hkuri bazan sakeba ."
Murya kasa kasa yace ba komai yawuce goge hawaye nki,bbu musu ta goge.had'e da zama a gefensa cikin yarinta tace yaya yimun murmushi ka mana .
Kallonta yyi yamak'e kafad'a kamar wani yaro,yace um um bazanyiwa wadda bata sona murmushiba.
Shagwabewa tayi ita a dole sai yyi mata mata murmushi ganin ta fara dire dire yasashi jin wani yanayi gakuma masu aiki hakan yasa yyi mata,itama tayi masa so take sukadawo kamar bbu abinda yahad'asu,nan yajata sukaje suka siyo ice cream, cikin motar suketa shan abinsu suna firansu ta masoya har masu aiki suka gama ,dazai tafi yaga Hafsat bata wani nuna damuwa ba zaitafi,hakan yasa yagane dan mama zata dawone,kafin yyi magana har tace masa yaya wai yaushe maman zata dawo?
"Murmushi yyi yace sai nan da sati biyu."
Cikin zaro ido Hafsat ta ce Allah ban yarda,yar dariya yyi yace tsokanarki nake,murmushi tayi tace ainasan mommy bazata bariba ma tafad'a hade da fitowa dg motar tana yima sir Aliyu gwalo,kallonta yyi yanuna kansa yana cewa Niko?
"Murgud'a baki tayi tace eh din".
Kwafa yyi yace hmmmm haba yarinya zaki zo hannuna ai saura 13days bikin,zankamakine, yafad'a hade da Jan motar yyi tafiyarsa,itakuma ta yi shigewarya gd mamakin maganarsa ,tunowa tayi da sex ai atsorace ta rufe bakinta ,afili tace aibama haka yake nufiba yana nufin ya horani ne ai daga gani yaya ba ruwansa.
Ana gama isha'i mummy tarako mairo dakinta,hade dayimata nasiha gakuma sha tara ta arxiki data had'a mata.nan mairo dan Dadi har hawaye tayi tana godiya.
"""" dazasu tafi mommy ta ce mata jibi za'a kawo lefen Hafsat.nan kowa ya watse akabar mairo da Hafsat sunajin dadin ganin juna suka hau firar yaushe gamo.
Koda mlm aminu yadawo beyi mamakin ganin laure bata gidanba dan dama ko fits zatai bata wani tambayarsa.
Hakan yasa yyita hidimar sa da sabbin iyalinsa.
***** ***** *******
Mubarak ne zaune saman motarsa ,dan abbansu yabasu motarsu shida zakiyya ganin sun shiryu.tunani kawai yake dan acikin kwana biyunnan wani mugun son sa'ada yashigesa saidai yana tsoron furtawa duk da kowa yasan yanatsu,amma aganinsa kamar Aliyu bazai yardaba kuma itama sa'ada baza ta soshiba.
Gajiya yyi da zaman can ya yanke shawarar xuwa gidan yaga ,sa'ada koxaiji sanyi aransa.
Part dinsa ya wuce yadauki babban wanka, yafito cikin dark blue in suit yasharce gashin kansa da sajensa yafeshe jikin sa da turare yafito dg part din sa.
"Awaiting parlour yaga mommy nsu zaune ", da sauri ta kallesa tace my son sai ina ?naga kasha gayu haka.
Cikin jin kunya yace mommy kiyimun addua zance zanje ,Allah yasa yarinyar tasoni,dan yau nike so ingabatar da kaina gunta.
Jikin jin dad'in takusa samun suruka tace to my son insha Allah ma zata soka dan yadda kake haka babu yarinyar dazakace kanaso tak'ika .
Murmushi yyi yace mommy aibadole ne saika birge kowa bace,yafad'a hade da ficewa dg gidan yanufi gidansu sir Aliyu....
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿99&100
Bayan mubarak yyi parking, yashige ciki.mummy yasamu zaune aparlour nan takarbesa cikin sakin fuska bayan sun gaisa yyi shiru kansa aduk'e."tunani mommy keyi",na dalilin zuwansa duk da tasan yanzun sun natsu sosai sai ranta yabata k'ila zumunci yazo.jin shirun tayi yawa yasa ta kallesa tace yayadai mubakar? naga kayi shiru kak'i magana.
"Cikin jin kuny a " ,had'e da Sosa kai yace ba komai mommy, um...um..dama sa'ada batanan?naga gidan yyi tsit ba kowane?
"Murmushi mommy ta yi tace ah ah sa'ada nanan!su kabeer ne basu nan ," bara naturo maka ita."takawo maka ko drinks ne wani dad'i yaji sosai aransa,saidai abinda bai saniba mommy ta harbo jir
ginsa.kuma taji dadin hakan tunda Zakiyya bata auri Aliyu ba ,aigara ayi da Mubarak da sa'adar ko zumunci yasake kulluwa.
"Ahankali ta je tasami sa'ada a dakinta", tace taxo ga Mubarak can ta kai masa drinks.cikin tura baki ta nufi kitchen dan cika aikin mommy. Amma tunani take to meyakawo yaya Mubarak gidan har za'a wani ce taje ta kai masa drinks Bacin ga masu aiki nan agidan .
Itafa ko can da ,gaisuwa kawai kehad'ata dashi ,bayan ita ko fira basu tsayawa suyi.
da wannan tunanin ta isa parlourn tayi sallama suna had'a ido taji fad'uwar gaba, ga wani murmushi dayaketa yima ta.bayan sun gaisa harta zuba masa drinks din yasha ," sukayi shiru."babu Wanda yace wani abu cikinsu.
*can Mubarak yace baby sa'ada inbadamuwa ?"muje kirakani anguwa.
Turo baki tayi tace um um nidai bazaniba,hakan datayi yabasa dariya dan yanason mace shagwab'abb'iya.
Nan dai yyita janta da fira hartasaki jiki suna fira da fara,a dazai tafi yace wai dole sai ta rakasa.
Bbu musu tabisa,Saida zai shiga mota ya kalleta yace ILOVE You so much my angel.
Zaro ido sa'ada tayi hade da xurawa cikin gida aguje tana dariya,shikuwa murmushi yyi yashige motarsa Yana tunanin k'ila bazai sha wahalar shawo kantaba.
Itakuwa sa'ada mamakin kanta take ,dan tasan eh beda wata makusa amma sai ta ja ajinta sbd tanaso taga nmj ya rude akanta yana mata wani so nadaban.
"Tunawa tayi dasu Hafsat", afili tace soyayyarku na birgeni.
***** ****** ******
Bayan kwana biyu har ankawao lefen Hafsat,masha Allah komai yaji anyi kaya na kece raini, abin sai sanbarka.
Ayanxun haka ,Ahmed Nasir wato aminin ango kuma yayan babbar k'awar amarya ,yasaka Fatima suje suyi list din event din dasazuyi,dan abun yagabato.
Bangaren su Laure kuwa,bayan sunje asibiti duk taimakon daya dace su bata,sun bata bata farkaba sai washe gari, ta tsorata iya tsorata data ganta da k'afa daya sai kuka take hade da fara nadaman abinda tayi arayuwa.
Nan ta bada address din mlm aminu ,dan asanar dashi.
" haka kuwa akaje akasanar da shi halin datake ciki".
Wanda dama yana gab da fara bincikar ina taje kwana2?bata gida har yaranta na tambayarsa tana ina?
Da har yak'i xuwa Saida mairo ta nuna masa bacin ranta ,tukum sannan ya yarda zaije nan yadauke amashin sukaje asibitin.
Bayan sunje sunga halin datake ciki ,tabasu tausayi har kuka Saida mairo tayi dan tsabar tausayin Laure.
Nandai abinda yaka mata mlm aminu yyi ,yyi suka dawo gida sukabar danginta na kula da ita.
Hakafa al,amurra suka kasance inda yanzun haka, Zakiyya, Fatima, Hafsat, fa sa'ada sunxama k'awaye sosai bbu mejin tsakanunsu,dukda dai gsky Zakiyya ta girme musu sosai dan ita 200label take ,sukuwa yanzun zasu 100label.
Tsakanin Mubarak da sa'ada kuwa ,ta wahalar dashi,bawan Allah har yar rama yyi saiyaje gidansu sau ukku arana amma sa'ada bazata bari su had'uba,ta taboye jota rufe part din ta."tun sir Aliyu be saniba haryagane Mubarak yakamu da son sa'ada .amma yalura tana mugun ja masa aji.
Ayanxun haka shine zaune a parlourn gidan shidasu kabeer suna fira, yace wa kabeer yakirata ,bbu irin lallab'war da kabeer beyiba taki xuwa,hakan yasa ransa baci yaje yasanar da sir Aliyu kasancewar yana gidan.
Cikin bacin rai hade da tsawa sir Aliyu yyi mata dayaje dakin hade da cewa tagaya masa inbatason Mubarak shi akwai wacce XE hadasu da'ita.
Ai tuni sa'ada ta aje Jan aji ,tace wlh yaya inasonsa.
Tsaki yaja yace kuma kike wahalar dashi haka ko ?hmm kekika sani.
Nan dai sa'ada taje gunsa suka ida daidaita Kansu.
________________
Akwana atashi bbu wuya gun uban giji yau dai aka fara event din bikin sir Aliyu da Hafsat.
Wa'azine farko kuma gidansu Fatima za'ayishi,kasancewar Hafsat canta koma umman su Fatima na kula da ita ,kuma can ake mata dilka .
Hafsat ta sha gyara tayi kyau naban mamaki,dama abinka damai kyau ga wani k'amshi daya kama jikinta na musammun.
Tun kafin afara wa'azin sir Aliyu ya aiko kabeer yakawoata had'add'iyar waya mai tsada wadda zasu rika jin murya juna kafin aimasa ita.
Shikuwa dama kabeer haka yaso ,kodan yaga fatimarsa,kodaje haka ya lik'e ma Fatima sai gab da la'asar ta lallabasa yatafi gida da zumar zai dawo da dare,Dan kabeer abin nasa bbu kunya har cikin gidan su Fatima yake shiga kasancewar abban su Fatima abokin daddyne.
Bayan la'asar ,malama tazo tasha wa'azi akan xaman aure da hakk'ok'insa ,duk jikin Hafsat yyi sanyi takuma kara tsorata.
Da haka akatshi dg gun wa'azi da xumar gobe kamu.
Sir Aliyu kuwa ango yyi kewar babyn sa Hafsat,yanzun haka kiranta yyi awaya tana d'agawa tasaka masa kukan shagwaba rta me rikitasa,ita adole sai yazo yaganta kuma yasiya mata ice cream.
Kashe wayar yyi dan bazai jure jin wannan abubuwan datake ba dan zai iya shiga wani yanayi,tashi yyi yanufi parking space yadau motarsa yaje yasiya mata ice cream in sannan yanufi gidansu Fatima dan yasan tana can......
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿101&102
Koda ya isa gidan,yyi parking yafito,dan yashiga ciki...turus yyi ganin yan matan acampound din gidan kowace da boy friend dinta suna xance.
"Yasha mamakin ganin kamal da Zakiyya."
Tunani yake aransa Ina suka had'u harta sansa suka fara soyayya?
Gefensu yabi dan wucewa ciki ,nan shima kamal yalura da shi ,cikin ladabi yaje yaba shi hannu suka gaisa,yawuce .cikin mamaki kamal yake kamal tambayar Zakiyya ina tasan sir Aliyu? nan ta sanar dashi ai yayantane,jikin sa yyi sanyi dan yacire rai da samun Zakiyya amatsayin matar da zai aura.
"nanta sake sanar dashi cewa aishine angon", dan ta sanar dashi inda yazo yasameta sunxo gun wa'azi na biki.kasancewar besan ko bikinwa akeba yadai zo yasameta,kuma besan Hafsat ce amaryarba.
Koda sir Aliyu yashiga ciki awaiting parlour yahadu da umman su Fatima bayan sun gaisa ta tashi tashiga ciki ta turo masa Hafsat.
" cikin shagwaba "ta yi sallama ,murmushi yyi ya amsa ta zauna a gefensa had'e da cewa yaya ina icecream dina yake?
cikin xolaya yace ban siyoba!mik'ewa tayi dan tafiya da sauri yace indai kika tafi munbata dake. Turo baki tayi tace to kabani abuna.
Miko mata ledar dke gefensa yyi yace hmm haba yarinya ALLAH kirage shan kayan sanyin nan kinga ke amaryace.
" yafad'a Yana dariya",cikin rashin fahimtar kalamansa tace to dan ina amarya saina bar shan abu maisanyi ,aiyanxun nafarama.batare da yakalleta yace hmmm kicigaba inkinxo hannu kinyi bayani,kuma ma in aka kawomunke bazan bari kina yawan shan abu mai sanyiba.
Shiru itadai Hafsat ta yi tana tunanin kalamansa harta shanye kayanta.
nan ta kallesa cikin tsokana tace sir katashi katafi gida.
da mamaki yakalleta ya maimaita kalmar SIR dan ya mance wai antaba kiransa da ita.mik'e wa yyi yabita ganin tana masa dariya hade da gwalo,Yana cewa ALLAH idan narike ki zaki gayamusu,wato nikike kora ko?
"Eh din"
Ta fada hade da xurawa aguje,tabarsa murmushi yyi