Showing 48001 words to 51000 words out of 70847 words

Chapter 17 - NIDA DALIBATA Complete Hausa novel

24 Aug 2024

12243

guduma,gabansa inbancin dukan Tara Tara babu abinda yake,ga wani jiri da yaji atake hade da bushewar makoshi sbd tsabar firgita da rudani,Dan besan daliliba ,anayimasa maganar yatuna Hafsat dinsa.

Daddy yace kobaka amince bane naji kayi shiru?

Murya a sarke yace na amince ,yafad'a cike da dauriya hade da mik'ewa tsaye yabar part din.

Part din sa yawuce ,ya kwanta sakamakon yadda kansa ke sarawa kamar zairabe ga xuciyarsa na bugawa da karfi,gefe guda kuma tunanin Hafsat ne fal aransa.

Gajiya yyi da juyawa a kan bed ,da sauri yatashi jiri na dibarsa yafita parking spaces yaja motarsa yyi gidansu Hafsat.

_________________
Hafsat kuwa bayan ta tashi tayi sallar la'asar ,mike rai adagule ta fito dan taje gun Fatima ta sanar da ita ko akwai shawarar dazata bata.

Shikuma sir Aliyu allane kawai yakawosa anguwarsu Hafsat lfy ,dan gudun da yakeyi ya wuce tunanin me karatu.

Yanayin parking ya fito ko rufe motar be yiba yashiga gidansu Hafsat ,idanun nan nasa sunyi jajir sai huci yake.

Asoro yahadu da Hafsat zata fita,aitana ganinsa da gudu ta fada jikin sa tasaki kuka me cin rai....NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿85&86

"Yah salam kawai yake maimaitawa azuciyarsa" ganin yadda Hafsat ke kuka,hannunsa yasa yadago kanta yasa yatsansa yatsare mata hawayen,tared a kok'arin rabata da jikin sa amma tasak e manne masa tana kukan shagwaba. "

dama tarasa wazatayi mawa ,sai gashi yazo",cikin kasalallar murya yace yi shiru kinji Hafsat d'ina kidawo nan gun,yanuna mata gefensa.
Tare da cewa kinga in baba yasamemu ahaka bazaiji dadiba mutuncina zai xube agunsa.ai da sauri tabar jikin sa tadawo gefensa tana cigaba da kuka
"cikin damuwa yace me kikewa kuka waye yasaminke kuka yanzun yakarbi mummunan hukunci aguna??"

"cikin kuka tace babane."

da sauri ya maimata Kalmar babane!!

""" d'aga kanta tayi tareda cewa yaya dan Allah katemakeni baba zaimun aure yarinya dani!
Wani irin bugawa yaji xuciyarsa tayi hade da jin jiri da wani mugun ciwon kai,murya asarke yace aure kuma Hafsat wa baba zai auramiki?,yafada had'e da kafeta da jajayen idanunsa."""

Cikin kuka tace wlh bansanshiba nima pls kaje ka rokesa yyi hkuri wlh banason auren da kuma Wanda zai auramun ta fada hade da sakin sabon kukan.

"Cikin wani yanayi yace ke wa kikeso?"

K'uri yyi mata yana jiran tace k'ila koshi takeso, sai yaji tace bbu koma nidai kawai banson auren.

Tsakin dabesan yyiba yaja ,hade da tamke fuska yace k'ila dakin gayamun Wanda kikeso to danayiwa baba magana ,sai a auramiki shi"amma innace abarki kada ayi auren ,yace waKikeso ?nace masa me?
da sauri tace amma yaya kag......da sauri yace ki koma ciki anjima zamuyi waya bance kije ko inaba kina jina?kallonsa tayi hawaye na zuba tace gidansu Fatima zanje",cikin isa yace nace bazakiba yafad'a had'e da dafa bango sbd jirin dayakeji had'e da kunar zuci dan ji yake damuwarsa ta nunku akan wadda yake ciki,saidai wani gefen na zucoyarsa na tahumarsa dalilin damuwarsa dan ance Hafsat zatayi aure."";;

"Kallonsa tayi ganin yyshiru,tace natafi."

Cikin damuwa sir Aliyu yace dan Allah Hafsat dina kidena kukannan haka,nima wlh ina cikin damuwa yau ,zanyimana addu a kinji kema kiyimana.

" daga masa kai tayi hade da shigewa gida ",dan intayi magana kukane zaixomata.

Shikuwa sir Aliyu da sauri yafito dg gidan,kallo daya zaka masa kasan yanacikin tashin hankali da damuwa.idanunsa sunyi jajir ,jijiyoyin kansa duk sun tashi ga jiri na d'ibarsa,da sauri yabud'e mota yashiga ya axa kansa kan sitiyarin motar."
yaya Ahmed dake tafe a mota yahangi sir Aliyu cikin wannan yanayi atake yasan bbu lfy.
"da sauri yyi parking ya fito yana kiransa be jiba yashige motarsa" da sauri yy Ahmed yabisa.yabud'e gaban motar yashiga yasamesa kansa duk'e.da sauri Ahmed yace friend lfy meke faruwa ne??
"cikin damuwa sir Aliyu yadago,saida yy Ahmed yatsorata da yanda yaganshi." Cinkin damuwa ya sanarda shi halin da yake ciki.
Ahmad yyi ajiyar zuciya yace wannan ne abin damuwa! Aini nan banga abun damuwaba,tunda kak'i kayi aure ai gara suyima.tsaki sir Aliyu yaja hade da cewa ,aibansone shiyasa ,itama Hafsat dina ,za 'amata auren dole yafada kamar zai yi kuka.
Yy Ahmed yace banganeba?nan yabashi labarin itama Hafsat auren dole za'a mata.murmushi Ahmed yy yace tokai meye damuwarka? Wata harara sir Aliyu ya bankawa Ahmed yace ,my Hafsat ta na cikin damuwa ya za ai hankalina yakwanta.

"Girgiza kai Ahmed yy yace wlh ko kaso ko ,kada kaso kanason Hafsat so mai tsanani Wanda ko a idonka gashina kwance had'e da tsantsar kishinta".

Wlh kama farka in bacci kake tun kan sonta yyimaka illah ko lahani kasani ka bayyana mata.amma wannan ai kishinta kake,wlh duk wanda yasan so,indai yyi zaman minti biyar daku zai gane kana ma Hafsat wani irin zazzafan so hade da kishinta me tsanani ,nagane hakan tun a hidimar biki na,kuma nayiwa Fatima tambayoyi ta bani amsa anan na kara tabbatar wa kaina kanasonta,inhar baka zameta ba ko mai zai iya faruwa. Nan dai Ahmed yyita masa bayani hade da ankarar dashi cewa yyi zurfi ason Hafsat dakuma tamvayarsa kanajin kaza inka ganta ko kaganta da wani?me kakeji intana cikin damuwa ko Bacin rai?nan yacigaba da cewa zakaji kaza da kaza inkiuna tare kobakwa tare ko in kun gamu ko kaganta da wani nmji.


doguwar ajiyar zuciya sir Aliyu yyi hade da cewa na yadda abokina da maganarka dan duk abubuwan daka lissafamin irinsu nakeji game da ita.

Nayarda indai hakan shine so to lallai son Hafsat yamun illah ,muddin bansametaba komai zai iya faruwa dani yafad'a cikin damuwa.

" ahankali Ahmed yace friend kayi hkuri kaji kayi biyayya ga daddy sannan kayita adduar ai nmj mijin mace4 ne daga baya saika auri Hafsat din inrabonkace.

Batare da sir Aliyu yyi magana ba yatada motar.

Da sauri Ahmed yace wait,nan yakira driver na gidansu yace yazo yamayar masa da motarsa gida.kallon sir Aliyu yyi yace nizan kaika gida bazan bari katafi kai dayaba komai zai iya faruwa.


Bbu musu sir Aliyu yafita Ahmed yazauna amazaunin driver yajasu suka dauki hanyar gidansu sir Aliyu.

Bayan sunyi parking ko sallama sir Aliyu bebari sunyi ba yafito arikice yyi cikin gidan.

"Shikuwa Ahmed ya fito dg motar yyi waje,had'e da yiwa abokinsa adduar samun sassauci."


Yana shiga bbu ko sallama yanufi gun mommy dake zaune akushin kusada su sa'ada da kabeer,kamar wani yaro haka yafad'a kan cinyarta,yana Sabbatu cikin tashin hankali.

Mommy kuwa naganinsa tasan dama hakan zai faru tunda daddy yace zai sanar dashi maganar aurenshi.

Cikin tausayinsa tace baba na meke faruwa ne kke cikin wannan yanayi?

Arikice hade da rik'e mata hannuwa yace pls mommy kitaimakeni zanrasa Hafsat dina mommy itace bugun xuciyata mommy can iya rasa raina inbansametaba,mommy baban ta zai mata auren dole zai aura mata wani ba niba.

Wlhy matata ce duk Wanda yyi yunk'urin auranmun mata wlh zanyi ajalinsa domin dan ni akayita dani ta dace hafsat pls mommy kada kibari arabani da matata wlh zan iyayin komai akan hakan bazan sau....da sauri mommy ta rufe masa baki hade da cewa ya isa haka!

"Waya jamaka ?"

Kai kajawa kanka gudun hakan yasa na tambayi meke tsakanunku ?amma sai kacemun ai dalibarkace.

Sai yanzun dakaji za'amata aure zakace kanasonta.

Sukuwa su sa'ada da kabeer mamakin sir Aliyu suke dan tunda suke dashi yaune sukaji yace yanason wata mace.

Shikuwa kabeer azuciyarsa yace madallah anxo gurin ai dama duk masu cika bakin basayin soyayya duk ran da takamasu hmm basuji da daddy ji dai yaya ko ina ya aje miskilancin nasa duk yake wannan haukan akan mace?

Sir Aliyu ne yatashi dafe da xuciyarsa yana kiran Hafsat !Hafsat!! Hafsat!! Yana dafe bango dan gaba daya ya haukace musu,sai surutai yake musu,basu auneba sukaga ya fad'i kasa su mamme.

Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story written by mmn fareesa

🅿87&88

"" da sauri mommy ta yi gunsa tana salati,sa'ada kuwa kuka ta saka."
Kabeer ne yyi hanxarin dakko swan mai sanyi yadunga kwaraya masa ,cikin ikon Allah yasa ki ajiyar zuciya hade da bude idonsa.

"Sannu kawai su mommy ke masa da su sa'ada ."

Ahankali yatashi zaune ya karbi sauran swan din yashanye sannan yatashi batare da yayi magana ba yyi part dinsa.
Kabeer ne yyi saurin cewa momm yko maje hospital adubasa dan Allah. Wani mugun kallo sir Aliyu yajuyo ya aikowa kabeer hade da cewa kai yaushe nafara wasa dakai?
Sunkuyadda kai kabeer yyi yace yi hakuri yaya.
"Tsaki sir Aliyu yyi yabar gun", mommy kuwa hararan kabeer tayi hade da nufa part dinta"".

Tana zuwa ta bincikowa sir Aliyu magunguna harda na bacci sannan ta wuce kitchen ya had'a masa tea mai kauri ta nufi part dinsa.

" shikuwa sir Aliyu kwance yake kan bed yyi rigingine idanunsa alumshe yana tunanin Hafsat dinsa mommy ta sh igo d'akin."
Saida tayi sallama sau3 tukum ya amsa yana dan Sosa kansa."ahankali mommy ta ce tashi zaune babana! Bbu musu yatashi ta bashi tea din ,bayan yasha tabasa magani ,hade' da yimai nasiha yyi biyayya ga daddynsa kuma yyita addua."
Bajimaba da shan tea din bacci mai nauyi yyi gaba dashi.mommy ta kallesa cike da tasayi tabar dakin.

******************
Hafsat kuwa tun bayan Sir Aliyu yatafi takoma dakinta ta cigaba da aikinta wato kuka.
Domin itadai kowama zata aura wlh tana tsoron sex dan tanaji in mate dinsu na bada labari in sun karanta a littafi ,cewa da wahala sosai,saitaji duk ta tsorata da aure to Balle batasan wanne marar imanin zaa aura mata ba.tana kukan da tunane tunane had'e da fushi da sir Aliyu bacci yyi gaba da ita, bata farkaba sai gab da sallar la'asar bayan tayi sallah ,tajima tana adduar allah yazaba mata abinda yafi alkhairi yakuma baiyana mata mahaifiyarta.

Cikin ikon Allah saitaji damuwarta ta rage ,nan taje tayi wankanta ta wuce islamiya kasa.cewar yanzun hadda take,amma fa tayi fushi da sir Aliyu sosai.

Bangaren sir Aliyu kuwa shima sai bayan laa'asar yatashi ,yyi wanka hade da sallah.
Cikin ikon Allah yaji duk wani k'unci da damuwarsa sun rage .
"Neman guri yyi ya zauna yafara tunani n Hafsat dinsa." mur mushi yyi daya tuna duk abinda yakeso matar dazai aura takasance dasu Hafsat tanadasu du ka.nafarko ya. Yana son wacce zai aura takasance yarinya danya sharaf,yadda zai raineta da kansa zai koya mata sonsa da kula da yaransu su zauna lfy.sannan kuma mai kunya ilimin addini da tarbiyyamai son danginsa,sai yaduba yaga Hafsat duk ta had'a wa inna abubuwan. Wata zuciyar ta ce kanada tabbas din zaka mallaketa?

Tunawa yyi kilama har yanzun batadena kukaba da sauri yazaro wayarsa yakira baba.

bbu bata lokaci baba yadaga had'e da sallama,Hafsat dke gefensa cikin sanyin muryarta tace baba waye yakiraka?

Baba dke cewa lfy lau aliyu ya gida?

Atake Hafsat ta gane cewa da sir Aliyu baba keyin waya,aisaita kwanta ta rufe ido kamar me bacci.

Shikuwa sir Aliyu tun sadda Hafsat ke tambayar baba yaji muryarta,dama dan ita yakira yanaso suyi magana.

"can yace baba ko Hafsat na kusa mu gaisa?"

Kallonta baba yyi ,yace aiko kamar tayi bacci Bari natasheta.

Da sauri sir Aliyu yace ah ah baba rabu da ita tayi baccinta.nandai sukayi sallamada baba,sir Aliyu kuwa yasan sarai Hafsat ba bacci takeba kwaidai fushi take dashi.
Murmushi yyi yace oh Hafsat akwai rigima da shagwaba ,nasan haka zanta fama da rigimarta inmukayi aur......da sauri yyi shiru sakamakon tunawa da yyi Hafsat wani za'a aurama ita.
" cikin jin haushi hade da wani kishi da yataso masa yatashi yafita dan xuwa masjid.

Koda dare Hafsat da sir Aliyu bbu Wanda yyi baccin kirki duk da damuwa suka kwana ,kowa na tunanin dan uwansa.

Washe gari haka sir Aliyu yatashi duk yad'an fad'a saidai fuskarsa tayi fiyau da shi,ko break beyiba yanufi gidansu hafsat ,dan hankalinsa yak'i kwanciya Hafsat tana fushi dashi.

Yana isa yyi parking yafito kaitsaye yakutsa kai cikin gidan ,asoro yasami Hafsat tana sharewa kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa.

Ai tana ganinsa tasaki tsuntsiyar tayi cikin gidan aguje.

Murmushi sir Aliyu yyi dan yalura har yanzun fushi take dashi,dan haka shima yasaka kai cikin gidan...

Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿89&90

"Yana shiga yasami bbu kowa tsakar gidan", kallon wani d'aki yyi yaga yan takalmi bakin k'ofar dakin atake jikin sa yabasa nan Hafsat ta shiga.
Beyi wata watab a yashiga had'e da sallama, da sauri Hafsat ta d'ago dan batayi tunanin zai biyota ." nan ta ammasa sallamar".
Ta juya masa baya batace komaiba,aha nkali yace my Hafsat duk fushinne har haka ,bazaki tausayamunba ki barni najida abinke damuna,sai kin karamun wata damuwar!yakikeso nayi da raina?
"Ahankali tace nidai yaya katafi ni bazan hakuraba ", Allah kuwa.
Shiru yyi yana tunani,can yace my Hafsat gidanku fa nazo,shine zakimun haka.
Kallonsa ta d'ago tayi hade da murguda baki tace eh din tun....shiru tayi ganin Laure a k'ofar dakin.

""" ckin masifa tace keko?kinanan kuna aikata masha,arku har cikin gd ko to asirinku yatonu wlh oh da rana Kiri k'iri bbu tsoron Allah ai.. Wata rikitacciyar tsawa sir Aliyu yadaka mata had'e da cewa ya isa haka wlh kinci darajar baba da wlh yau kinyi nadamar kalamanki,amma ko yanzun zan had'a ki da k'ananun yan sanda,yafad'a tareda da Jan doguwar tsuka yabar gidan. """;;

Hafsat kuwa shiru tayi kamar andasata agun tanajin ciwon maganganun Laure da haushin tafiyarda sir Aliyu yyi.

" Laure kuwa jiki amace ta nufi d'akinta".dan ta tsorata da maganar sir Aliyu.

Shikuwa sir Aliyu gida yanufa yanajin haushin kintsayawa da yyi ya rarrashi Hafsat.

****** ***** ******
bayan kwana biyu
Sir Aliyu ne zaune kan bed duk yyi yar fuska ga sajen fuskarsa yyi yawa baya gyarawa kwana2 sbd hankalinsa ba kwance ba sai Karen hancinsa dayyi siriri ya k'ara fito da ramarsa,sai tunani yake can wata dubara ta fad'o mishi da sauri ykira mommy yace ta turo masa sa'ada yanzun .

Bbu jimawa sa'ada ta shigo dakin ,bayan ta zauna ,cikin sakin fuska sir Aliyu yace y'ar autarmu wani aiki zakimun kinji ko?

"Ahankali tace wanne aiki?"

Kallonta yyi yace matso kiji bbu musu. Tamatsa kusa dashi yarad'a mata wata magana Shewa sa'ada ta yi had'e da cewa to yaya bara najira kashirya danni ashirye nake.

Murmushi yyi yace ammafa inaso abun yazama sirri kada ki nuna mata cewa inasonta,kin fahimta?

"d'aga kai tayi alamar eh."

Bece komai ba yashige bathroom itakuma sa'ada ta fito dg dakin.

Bayan yagama shiryawa sai wani fitinannan k'amshi yakeyi ya kalli kansa a mirror, yaga duk k'simba ta cika masa fuska.

Murmushi yyi daya tuna Hafsat ta tab'a cemasa yafi mata kyau inya gyara sajensa na fuska ai da sauri ya jawo wata lokar yafito da kayan gyarawar ya gyara abinsa yy kyau sosai,nan yasami mommy da sa'ada a waiting parlour a zaune.
Kallon sa'ada yyi yace Auta muje,na musu ta mik'e hade da kallon mommy ta ce muntafi da yaya zaimun shopping.
Murmushi mommy ta yi dan tasan bbu wani shopping dazasu.
"Ahankali tace kudawo lfy", sa'ada ta ce ameen hade da fita ta bisa .

Sa'ada da sir Aliyu bazu tsaya ko inaba sai gidansu Hafsat.nan sa'ada ta kalli sir Aliyu dke nuna mata gidan da hannu yace ga gidansu can yi gaba zan biyoki intsaya a soro sai kifitomun da ita.

Bbu musu sa'ada ta fito dg motar tayi cikin gidan,tana shiga tayi sallama Hafsat dke daki tanasaka kaya dan fitowarta kenan dg wanka,tanajin muryar sa'ada ta fito da gudu suka rungume juna ,cikin farin ciki Hafsat tace yau inada babbar bakuwa nan tajata dakinta.

Bayan tasaka kaya,suka dan fara fira Hafsat nason ta tambayi sir Aliyu amma tanajin nauyi,fan kwana biyu nan dabata gansaba adaddafe tayisu.

" sa'ada ce takatse mata tunani gun cewa pls muje gidansu Fatima naga tanada kirki."

Hafsat tace ok muje nan tasaka hijab suka fito,suna isowa asoro taji kamshin sir Aliyu da sauri ta d'ago kanta caraf suka yi 4eyes dashi. Sa'ada naganin haka ta maixa tayi tafiyarta gidansu Fatima dan dama haka suka tsara da sir Aliyu.
"Kallonta yyi yace my Hafsat kin huce ne?" Shiru tayi sai tura baki gaba take. Murmushi yyi yace duk Dan sabida kiyi farin cikin nakawo miki sa'ada ,kuma inji kindena fushin dani.
Cikin shagwaba ta ce ai yanzun na hakura ,amma pls kayimun murmushi yaufa kusan 4days rabon da inga murmushinka.

"Ahankali yakalleta yace nima haka Nayi missing smile naki amma kalleni,tsurrawa juna ido sukayi kowa na mamakin ramar da d'an uwansa yyi."

Sir Aliyu ne yafara mata murmushi itama tamaida masa,ahankali yace kinyi kyau bana gajiya da kallon wannan kyakkyawar furkar taki.

Murmushi tasake cikin yar shagwaba rta hade da yarinta tace kaima yaya kayi kyau banason in rabu dakai pls ta fad'a kamar zatayi kuka.

Kallonta yyi yace dakinyi kuka zamu bata ,mudage da addua kinji ko?

"To tace."

Ahankali yace abinda nibaki tab'a cewa ma Nayi kyauba kuma wannan gyaran fuskar danayi danke nayisa.
Da sauri ta kallesa axuciyarta tace kodai yana sona shima?

"Afili saitace Allah yaya kanamun kyau sosai ayanxun nikayiwa wannan kwalliyr taka?"

Kafin yace wani abu sa'ada ta shigo tace yaya muje dan Allah marece yyi bata jira amsarsaba tayi gaba.

Kallon Hafsat yyi yace my Hafsat zamu tafi,turbune fuska tayi kamar zatayi kuka ,cikin shagwaba ta ce nibanyatdaba dg xuwa sai tafiya.

Cikin rarrashi yace to ai gobe zanzo muje na kaiki amiki steaming kinjik..shiru yyi gani yadda take ta dire dire da bubbuga kafa kasa ita bata yardaba.

Lumshe idanunsa yyi dan in Hafsat ta yin irin wannan rigimar tata yana shiga wani yanayi.

Matsawa yyi gab da ita ,murya na rawa yace gayamun me kikeso kike wannan rigimar ,?

Cikin kukan shagwaba ta ce nibanason katafi kabarni dan bangaji da ganinkaba.

Murmushi yyi dan jin dadin kalamanta ya yadda kobata sonsa to tadamu dashi.

Rarrashinta yyitayi abu ga masoya saigashi yashawo kanta,hartahakura tamasa rakkiya hade da cewa sa'ada ta gaidamata mommy.

Sannan yaja motar suka bar anguwar.

Washe gari da misalin karfe 9:am sir Aliyu zaune kan carpet gaban daddy yazo gaidashi.bayan sun gaisa daddy yace kaga lokacin bikin nan yadan matso tunda saura3weeks yau xanje Dubai da mommy nku muhad'a lefe daganan muje Egypt mutaho da marar lafiyar nan a maodota gidan nan akwai wani doctor da zaixo yasake bincika rta. Shine nikeso ko inmuntafi ko bayan mundawo kaje gidansu yarinyar nan kuga juna kakuma gaida mahaifinta.

Wani fad'uwar gaba sir Aliyu yaji da Bacin rai jin maganar auran nan na nandai.

Jin yyi shiru daddy yace ina sauraronka ,inmuntafi zakaje ko kuwa sai bayan mundawo dg Dubai?.......

Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

Wannan page din nakune amintattun mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login