Showing 27001 words to 30000 words out of 70847 words
ta tuna zatayi kewarsa.
Ahankali yace shikenan tunda fushi ake dani ,nayi tafiyata juna kuma munbata dake.
Bejira abinda za,taceba yyi tafiyarsa.
Da sauri ta taddo Fatima sukawuce daki bayan sunci abinci tasha mgani, takwanta.
Cikin bacci taji Fatima na ihun murna,tana tayar da ita tace sis kitashi kiga result dinmu.
Da sauri Hafsat ta bude idonta,tace Mugani,nan Fatima ta ce, kekikayi first position, nikuma nayi forth position.
Nan cikin farin ciki tace alhmdllh.
Kitashi kiyi sallah sis mu ida had'a kaya gobe sai gida.
Cikin farin ciki Hafsat ta tashi ,tafita danyin alwarlla.
**************
Sir Aliyu ne zaune a office insa yana tunanin hanyarda zaibi yatambayi anguwarsu Hafsat,yanajin nauyin yatambayesu,itada Fatima,tunani yake ko yakawo masu sa'ada ta tambayeta tace zataje gidansu,saikuma yatuna sa,ada akwai surutu, gashi yalura Hafsat ta na fushi dashi,murmushi yyi da yatuna tayi first position a class dinsu,afili yace hafsatfa akwai brain.tashi yyi yadauki duk abinda yake bukata yarufe office din ya hau motarsa yafita daga get din skul din ,dan yakudurta gobe da kansa zaizo yakai Hafsat har k'ofar gdansu .bayan ya isa gd har yyi wanka sanyi lunch ,daddy yakirasa,yyimasa bayani yanzun yaje airport ya yankammasa bixa zaije Germany gun wasu kayansa da aka kama,akalla zaiyi 5days ko 7,days,harcikin ransa besoba sbd kudirin dke cikin ransa dande bazai iya musu da mahaifinsaba,nan yaje yashirya yanufi iya Port..
Washe gari farin ciki fal aransu saidai Hafsat taso taga sir Aliyu kobankwana suyi.
Hakadai driver yajasu zuwa gd dan yaya Ahmed ango yanacan gun hidimomin bikinsa dan yau saura8 days.
Bayan sun iso gida Fatima ta ce wa Hafsat sis anjima zanzo inkawomiki dunkunanmu in angama,Hafsat tace to sis nagode bari naje nan sukayi sallama.
Tanufi gidansu tun dg zaure taga anshafesa da sumunti anyi fenti hakama tsakar gd,saidai kaca kaca gidan yake kasancewar matar gidan bbu tsabta,sallama tayi bbu Wanda ya amsa,su Laure da ya'ayanta natsakar gidan suka jefeta da mugun kallo hade da Jan tsaki, axuciyarta tayimusu
Adduar shiriya,ahankali tace inna inakwana,adakile Laure tace kirike gaisuwarki ,in ubanki yafito dg bayi ki gaidashi danni nayafe anyi Hutu ,za,azo agallabi jama,a, Dede nan baba yafito dg bayi,cikin farinciki yace ah ah hafsatuna kece kikadawo sannunki da zuwa kinyi ya hanya? Murmushi Hafsat ta yi tace alhmdllh babana ina kwana? Yace lfy lau muje dg ciki ko,doguwar tsuka Laure taja tashige dakinta,baba yyi murmushin takaici ya girgiza kansa ,yakalli Hafsat,yace mujeko,nan yabud'e mata dakinta da daya ake aje shirgi cikinsa,taga angyarashi ansa mata labulaye da katfa da ledar k'asa,sai murna take tana yaba dakin..
Nan baba yafita yaje dakinsa yashirya yadawo ,sukayi ta fira da Hafsat.
Sai gurin karfe daya yafita ,itakuma taje tayi wankanta,tayi sallah ,saiga babanta yakawo mata nama gasashshe da fura danono yace taci tasha dan yasan Laure bazata bata abinciba.
Bayan sallar LA,asar,Fatima taxo gidan da ledar dinkunansu ga hannunta.
Inna Laure tayimata mugun kallo,fatimako gaisheta batayiba tayi tafiyarta dakin hafsat.
Tanashiga tafad'a kan katifar tace kai sis amma naji Dadin d'akinnan wlh kinhuta kema ki aje abinda kkeso,amma dai yanada key ko dan kada ki fita waccan azzalumar taxo ta bude tayimiki bincike?
Murmushi Hafsat ta yi tace eh yanada key.
Nan Fatima ta fito da kayan,dogayen rigunane gowns kala4 kowacce kala2 sai Riga da siket na atamfa,suna yinin bikine saikuma kayan Fulani,dan za@yi Fulani party,sai les Wanda zasu saka a walima,gown dinkuwa daya ta material ce zasu saka ranar kamu,daya Kuma yar kantice sai ranar deenar zasu saka.Hafsat taji Dadi sosae tayi murna,haka suka zauna sunata firan bikin yadda zai kasance.
Bayan 4days
Yakama. Yaune za,afara event din bikin Kuma ,kamune farko,Fatima taci gayunta cikin gawnt dinta tasha kwalliyar zamani tanufi gdnsu Hafsat dan tajita shiru.tana isa tasami Hafsat ta saka kayan amma ba makeup afuskarta ,nan tabude Jakarta tafito da kayan make up, cikin40 minit Hafsat ta fito kamar amarya,duk Wanda yagantada personal dole ya yabata sunyi kyau matuka dan Fatima ma akwai kyau. gidansu Fatima sukaje dan can za,aso adaukesu ayi kamun gidansu amaryar.bayan sunjima da jiran azo
Adaukesu amma shiru ga mutane agdan anata jira hakan yasa umman su Fatima ta kira yaya Ahmed dan tambayarsa,bayan sugama wayar takakli su Fatima ta ce wai cewa yyi gashinan za,azo daukarku,su angunama da kyar zasuxo sbd babban abokinsa baya kasar sunyi tunani yau zedawa ,amma yace musu sai gobe da safe ,zaidawo,kinga gobe Fulani party anyidashi da sauran event din..
Tsaki Fatima ta ja tace lallai ma yaya yanzun sbd wani aboki zaiki xuwa gun kamun bikinsa dole sai da shi zashi.
Nitunkafin naganshi naji natsanesa wlh ,sbd wani banxa ,zaa shanyamu....hararanta ta ummanta tayi tace kinga banason rashin kunya,ga driver can awaje kuje yamika Ku inbazakujeba saiku zauna dan in yayanki yaji kina wannan surutan bazaku shiryaba.
Cikin turo baki, Fatima ta ja hannun Hafsat sukafita,suka shige mota saigun kamu.
Ko acanma ,haka akayita surutai wai dan babban abokin ango baya k'asar aguna suka k'i zuwa fun kamu.
Yammata da yawa sun k'agara gobe tayi suga, wannan wanne dan jinkanne hardan sabida shi ango yak'i zuwa gun kamu da abokansa.
Hakadai akayi kamu akatashi anata yan surutai ,kowace takoma gidansu, kafingobe Fulani party.............
Share pls
NIDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
๐
ฟ51&52
Washe gari da misalin karfe 3:30am,yanmatane da kayan Fulani ajikinsu,suncika compound dingidansu salma wato amaryar yaya Ahmed, dan gidansu anguna zasuxo daukar yanmatan amarya.juyawa Nayi nakurawa wasu y'ammata ido,Ashe wai Hafsat ce da Fatima, fad'in irin kyawun dasukayi 6ata lokaci, Masha allah kawai nace ganin yadda kayansukayi musu musammun Hafsat dan inba farinsani kayi mataba bazaka ganetaba,Riga da zanine suka saka da safar hannu y'anyatsunsu kawai ake gani ga himar sunsa,sai kwarya da faifanta ahannunsu ga takalmi irin na Fulani sunsaka.Fatima ce takalli Hafsat ta ce muje kinga sai fita ake kada atafi abarmu,nan suka nufi get suka fita, k'ofar gidan cike yake da motoci har anfara daukar wasu sun faratafiya gun daza'ayi partyn.yanmata gasunan ansha kwalliya fatimace kalli Hafsat ta ce sis bari naje gun amarya nadawo,ok kawai Hafsat tace tacigaba da tsayuwarta agun.
Wata arniyar jib ce baka mai taya abaya,aka faka gaba daya ta dauke hankalin yanmatan sosuke suga waye mallakinta.
Ta kai 10 minit dayin parking amma ,ba,afito ba,gashi ba,aganin Wanda keciki,sbd glass din bakine,saidai naciki yaga na waje.
Can saiga akabud'e ,dogayen k'afafunsane yafara fitowa dasu sannan, yafito .gaba daya yatafi da hankalin sauran yanmata dake gun sai kallonsa suke sunajin inama inama, sir Aliyu kenan cikin kasaita da aji yarufe motar fararan suit ne ajikinsa,sai wani fitinan nan kamshi ketashi ajikinsa. yafara tafiya irinta k'asaita.Hafsat dake tsaye kamar amafarki taji kamshin turaren sa da sauri ta juyo sukayi 4eyes yasakarmata killer smile, turo baki tayi takauda kanta alamar haryanxun bata dena fushi dashiba,koda yaga hakan sai yyi yar dariya murya k'asa k'asa yace, muje mota sai inbada hakurin ko? Juyowa tayi danyin magana taga y'anmata gun suntsaresu da idanu ana kus kus. sai batace komaiba tabisa suka jera suna tafiya duk Wanda yagansu yasan su matukar dacewa da juna,marfin mota yabud'e ma ta ta shiga yarufe yana juyowa yaga wasu yanmata zasu bude gidan baya ,wani mugun kallo yyimu yace yayadai ?daya tace bagun partyn zakuba? ,adakile sir Aliyu yace bacan mukayiba yajuya yanufi side din driver.
Hafsat nashi ga motar taga kayan Fulani na maza Riga da hula ,tajanyesu tazauna, tamardasu gefenta.
Tunani take sir Aliyu waya sani agun bikin angon ko amaryar.
Shima sir Aliyu tunani yake Hafsat wata sani gun bikin,da tunanin yabud'e gidan gaba yashiga.
Hafsat ta kallesa batace komaiba, ganin yatada motar yasa ta kallesa da sauri.
Murmushi yyi yace matsoraciya niba guduwa zanyi dakeba gun partyn zamuje naga kinwani tsorata.
Shiru tayi batace komaiba, kallonta yasata caraf suka had'a ido, Hafsat tace hmm sir Aliyu hmm damefa?
Kinyi wani kwalliya amma aibakiyi wani kyauba ,murmushi tayi tace eh najidai,kallonta yyi yace ina Fatima naga bakwa tare?
Bata kallesaba,tace dazu muna tare da ita sai tacemun bari taje gun amaryar yaya Ahmed.
Da mamaki yakalleta yace, Ahmed Nasir yayankune?
Hafsat ta ce yayan fatimane uwa daya uba daya.
Kallonta yyi yace, oh nibansan kanwarsa bace,da sauri tace yaya kasandama yaya Ahmed, murmushi yyi yace banida wani amini ko abokin dayawuce Ahmed,kumashima haka,kallonsa tayi tace oh ko Kaine sbd kai yak'i zuwa kamun bikinsa wai ai babban abokin ango bayanan,sir Aliyu yace kwarai kuwa,yanxunma Muka gama fada adole sai na saka kayan Fulani nikuwa basa birgeni,kingansu nan gefenki..
"""" turo baki tayi tace haba yaya kasaka mana ,Allah inbakasaka zamu bata.
Kallonta yyi yace sarkin rigima na lura har yanzun bakidena fushi dani ba.
Cikin turo baki tace eh din ,yace to kiyi hkuri kinji tawan Niko yar dariyama bakimunba tunda naganki.
Hafsat ta ce, nibazan hakuraba,yace to mezanyi kihakura kinji?
Nidai saika saka rigarnan da hulai,tamik'o masa ,kafeta yyi da sexy eyes dinsa yace innasaka zaki hakura zamu shirya?
Dariya tayi har yar wushiryarta ta fito,Dan yabata dariya sosai shikuwa yashagala da kallonta.
Ahankali yace aimun isoma bari Nayi parking sainasaka.
Juyawa tayi tahangi gun cike da yammata da samari wasu Kuma matasane.
Juyowa tayi taga har sir Aliyu yasaka,kayan ,masha allah tace axuciyarta ganin yadda yyi kyau dukda suit din kawai yacire ,ya,aza tafulanin Asama yasa hular .
Kokarin bude motar take Ashe yasa lock,adan tsawace yace ina zaki kike rawar jikin fita.
Dan koda tahangi mazajen dakegun gakuma Hafsat yadda yahadu din nan saiyaji wani mugun haushi yaji bayason tafita duk sai yawani hade rai.
Itakuwa Hafsat mamakinsa take ,axuciyarta tace anya mutumin nan koyanada aljannune?
Lfy muke dashi amma jiyadda yawani hade rai.
Satar kallonsa tayi ahankali tace, yayaaaaaaaaa!
Kallonta yyi yace Hafsat dina menene,?cikin shagwabar dabatasan tayiba tace nidai mufita kada Fatima ta yita nemana mana,kallonta yyi cikin wani yanayi yace aiko munfita babu inda zaki fira zamuyi kibani labarin abinda kikayi da kika dawo gd.
Kallonsa tayi tace to yaya zan baka mujeto,nan yabud'e lock din suka fito.
Wow wasu ke cewa gani yadda kayan suka karbi sir Aliyu.
Wasu daga cikin abokansu ,sun dauka Hafsat ce budurwarsa ,wasukuma sun dauka kanwarsace.
Koda suka fito sai kallonsu ake ahankali sir Aliyu yanufi gun abokansa.
Hafsat kuwa gun Fatima ta nufa tana mata masifa tabarta hakuri Fatima ta bata tace sis wlh yayane yace inbisu naga keba bakuwabace shiyasa .
Amma kinsanko asheda sir Aliyu shine abokin yaya da akecewa baya kasar.
Hafsat ta ce eh aitare mukazo,dariya Fatima ta yi tace ainaji wasu nacewa gayan yyimusu .
Wani haushi Hafsat ta ji jin kalaman Fatima ,amma saita canjamusu fira.
Wasu yanmata ne zaune suna fira daya tace wai Ashe wancan gayenne ake jiran yazo baya kasar.
Daya ta ce aiyakai ajirasa dan duk cikin nazan gunnan inkika cire ango banga Wanda yakaisa haduwaba.
Kinga waccen babyn da ita yazo k'ila budurwarsace dan sun dace dajuna.
Sir Aliyu yana cikin abokansu ga ango da amaryarsa agefe anata raba yogurt da su fura da madarar shanu tafulani,wani sameer yakalli sir Aliyu ye mr man waccan yarinyar babynkace?
Cikin kosawa sir Aliyu yace ah ah kanwatace,da sauri samir yace ,yayanmu wlh tamun dg yau kazama yaya wlh ta tafi da imanina irinsu na wahalar samu.
Tsaki sir Aliyu yaja dan surutun samir yafara isarsa,gawani haushin kansa dayaji kan yace kanwarsace,sai yaji dama yace eh babynsace da yanzun samir bazai matsamasaba ,tashi yyi yabar gun ,shikuwa samir yasan halin sir Aliyu da miskilanci kuma yasan kaifi dayane,dan haka yadauki niyar zaishigar da kansa gunta.
Koda yatashi cikin yanmatan yakutsa yana Neman Hafsat sukuwa sai wani iyayi suke kozai kulasu.
Can yahangota ,da rake ahannunta da yoghurt.
Yana isa gunta bece komaiba ,itakuwa kamshinsa taji taduba aiko tagansa murmushi suka sakarma juna dan sun manta da mutanan dake gun ,ahankali Hafsat ta ce shine kayi tafiyarka kabarni ni kadai ko? Marairaicewa yyi yace sorry Tawan aigashi nadawo muje kiji wata maga me Dadi, kallonsa tayi tadan zaro ido tace da gaske yayanah? Murmushi yyi yace Allah kuwa,to muje inji tace tareda jerawa dashi dansu tafi.
Ai baki daya mutanan dake gun maida Hafsat da sir Aliyu dukayi kamar tb saida suka fara tafiya wasu sukabar kallonsu.
Itakuwa Fatima tagama yarda, soyayya Hafsat fa sir Aliyu suke saidai yadda tafahimta basu son sunason junansuba.
Koda suka isa gun motarsa saman motar yazauna yace ,kinde sani adole nasaka kayannan yafada tareda da fito da wayarsa yana latsawa.
Hafsat dake tsaye gabansa tace, yaya meye lbrin ,murmushi yyi yace sai kinbiya kudi saina baki.
Murguda masa baki tayi, ashagwabe tace nidai bawani biyan dazanyi nisaika fadamun.
Murmushi yyi yace haba yarinya darabon intafi gida inbari,kallonsa tayi tace hmm aibakasan gidanmuba kuma ai akwai waddanda zasu mayar damu gda.
Yatsina fuska yyi yace ainasan gidanku ,da sauri tace wanne anguwane?
Ahankali yace saikinbiya sannan na fada miki.
Aisaitafara dire dire ita saiyafada mata,abinda Hafsat batasani ba sir Aliyu yasa wayarsa yanata mata video din abinda take da pics itakuwa atunaninta latsa wayarsa yake.
Ganin da yyi tana dire dire dire gakuma maza yakalleta hade da haratanta yace kibari komubata bakigani ga maza gun kuma zasu iya kallonki....karamar wayarsa ce tayi ring in da sauri yaduba yaga dad dinsane faskekiyar wayarsa yamik'ama Hafsat yace rikemun nadawo anamun waya ,amma kada kije ko ina kinga dazu saida nayita nemanki ,karba tayi tace to,shikuma yazagaya bayan gun.
Yana tafiya ,da sauri Fatima ta zo suka kashe suna dariya Fatima tace kinajin dadinki wlh kinganki keda sir kamar masoya.
Tsaki Hafsat tayi tace zaki fara ko,tonidai mutumci ketsakanunmu ba wani abu ba kingane.
Kallon wayar hannunta Fatima ta yi tace ,sis wayarsa ce ?
Hafsat ta ce eh,nan Fatima ta ce yimana selfie,nan kuwa suka bude camera kasancewar wayar ba,a ki take ba ,nan suka rika pics kala kala dg karshe Fatima ta karbi wayar tahauyima Hafsat pics.
Can sukabari ,sukayi ta ganin pics din dan sunyi kyau gasunan baro baro kasancewarta babbar waya ,can Hafsat ta ce kinga sis bari Nayi deleting dinsu kafin yadawo dan wata kawai zai amsa yadawo.
Dede nan sir Aliyu yadawo Hafsat nakokarin deleting sukaji muryarsa yace abani wayata nadawo,ahankali Hafsat tace am... Am.eh d...zamu goge pic ne ,kallonda yyimata yasaka tabasa wayar batashiryaba,nan Fatima ta gaidashi ,tawuce su sum.
Itakuwa Hafsat turo baki tayi batace komaiba, kallonta yyi dan yaji dadin pics din dasukayi koyayi missing dinta ya kalla ai,yace kixo muje gida kinga marece yyi yanzun anyi magarib.
Bata kallesaba tace yaya tareda Fatima zamu tafi.
Fuska atamke yace da ai da ita kikazo ko,?
Kinsan banson musu ko gaddama ko inkuma kinfison raina yabaci to saiki zauna kutafi tare da Fatima.
Da sauri ta kallesa taga alamar ransa yabaci,da sauri tace yaya bafa hakanike nufiba.
Atsawace yace kije kawai ,aitunda naga bkyason zuwa gida yanzun kunyi appointment da wani zaku hadu anan dan haka nibazance kada kikulasa.
Azuciye yabud'e k'yauren motar zaishiga,yaji tafashe da kuka da guru taxo ta bude gidan gaba tashige bece komaiba ,yaja motar sai shashshekar kuka takeyi.
Ahankali yace Hafsat dan Allah kiyi shiru indannayimiki fada ko dannace dole kixo nakaiki gida kike kuka kidena bazan sake takurakiba.
Cikin shashshekar kuka tace ko daya dagacikinsu basubane.
Yace to menene?
Tace da batafiya zakayi kabarniba kuma nabatamaka rai shiyasani kuka.
Har cikin zuciyarsa yaji dadin kalamanta yasan Hafsat ta daukesa da mahimmanci arayuwarta.
Murya k'asa k'asa yace to aiyanxun nahakura kema kin hakura ko?
Ahankali tace eh ni aibanyi fushiba ,kallonta yyi suna had'a ido suka saki sanyayyan murmushi.
Sir Aliyu yacigaba da driving dinsa yace yauwa kokefa banason muna yawan batawa pls kirika kiyaye Bacin raina kinji ko.......
Yawan comment yawan typing๐๐
Share pls
NIDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
Nasadaukarda wannan page din ga dukkan wacce tayi boarding skul.
๐
ฟ53&54
Ahankali tace to insha Allah, amma kaima yaya kacika ,saurin fushi karage, murmushi yyi yace to zandenama baki daya. Haka yacigaba da driving dinsa yana tunani azuciyarsa shin wacce anguwa zasu nufa gashi yace mata yason anguwarsu can dubara tafado masa dayatuna aiyasan gidansu Ahmed Nasir kuma Fatima tace s makwabtane dasu Hafsat, kawai sai yanufi can anguwar Hafsat kuwa murna tayi Ashe da gaske sir Aliyu yasan gidansu,muryansa taji yana cewa gobe zakije gun deener din? Bata kallesaba tace eh insha Allah ahankali yace goben zanxo da karfe 7:00na kaiki ko,to tace ganin zai wuce gidansu yasa tace yaya yyi nan katsaya da sauri yace Aina San nan ne zan saukeki parking zanyiko,ahankali yatsaya tabude zata fito ,hafsatttttttttttt! Yakira sunanta ahankali kallonsa tayi yace to saida safe kink'agara kije gd ne murmushi tayi tace ehmana yace to nacema sa,ada kina gaida ita da sauri tace eh wai yaya ni yaushe zatazo gidanmu ne ahankali yace saikin fara zuwa gidansu t uro baki tayi tace shikenan ,amma goben kasameni gidansu Fatima yac meyasa?tace hakanan OK yace tare da cewa ko murmushi n baza amunba sai narok'a murmushi tayi masa ,harda daga masa hannu ta rufe motar bebar gunba saida yaga ta shiga gida tukum sannan yyi tafiyarsa.
Agajiye takoma gida bayan tacire kayan tayi wanka tayi sallah.
Fura kawai tasha dan Laure tadena bata abinci kumafa tanasata aiki,taje tayima baba saida safe takwanta.
Amma me data rufe ido sir Aliyu take gani yana mata murmushi.
Itama murmushi ntayi afili tace oh yaya sarkin fushi sai kuma tayi yar dariya dahaka bacci Yy gaba da ita.
A6angaren sir Aliyu shima hakan take dan yana kwanciya tunanin Hafsat ya addabesa.
Tunawa yyi da wayarsa da sauri yadauka yashiga video, yaita kallon irin yadda take shagwaba da murguda baki sai murmushinsa yake shi daya.
Can kuma yabud'e pics yana ganin wani itada Fatima wani ita daya.
Can yaga wani ita daya tayi wani fitinan nan kyau Atake yamayardashi akan screem din wayar.
Sai kallo yake yana tuna gobe k'ila tafi haka kyau tunda betaba ganinta da parsonal ba.
Wayarce tayi ringing yaduba yaga Zakiyya ce tsaki yaja afili yace aikin banxa wasu matan ba class wlh .
Tunawa yyi da irin kamun kai had'e da tarbiyya irin na Hafsat yyi murmushi afili yace ke dabance acikin mata .
Kashe wayar yyi ganin xata matsa masa yyi kwanciyarsa cikin farinciki.
Washe gari takama Friday, Hafsat tun10:am tagama shara da wanke wanke ta gyara dakin ta dana babanta.
Tana zaune dakinta saiga baba yashigo da shirinsa zaije kauye sariin kayan miya dana masarufi dayake siyarwa.
Kallon Hafsat yyi yace, yar albarka ni tafiya zanyi kuma nasan sai gobe zan dawo sbd inason insami daurin auren yaronnan Ahmed, tunda kince zakuje parti yake ko mene?
Murmushi tayi tace party baba deenar ko ,yace to kidai kula da kanki kinji dannaga abun nagidane shiyasa nabarki,inkun dawo kinga dare yyi kikwana gidansu Fatima dan nasan Laure zata rufemiki kofa da wuri .ahankali tace to