Showing 6001 words to 9000 words out of 70847 words
nan yafita,sai sannu Fatima ke mata.
Bayan 20 minit suna nan ,hafast na kwance Fatima na zaune,sir Aliyu yashigo tare da doctor.
Da ledoji a hannunsa, nan doctor ya buda ledar yahada allurai
Hafsat naganin haka ,ido ya raina fata,dan tana tsoron allura.
Kallon Sir Aliyu tayi taga yakafeta da idanunsa, cikin muryar shagwaba , tabatason tana da itaba ,
Tace sir pls banason allura , kada kabari ayimun !
Tausayi tabasa amma sai yace hmm yanzun kuwa za,a miki danki sami saukin jikinki.
Nan doctor yace ta gyara ayi mata,
Sir Aliyu tsintar kansa yyi da beson doctor din yyimata allurar a kugu.
Dan haka yace ayi mata ga hannu.
Nan ta runtse idanunta ,ta mik'a hannu tana hawaye.
Wata kara tasaki jin ansoka mata allurar.
Sir Aliyu har cikin kansa yaji karar.
Nan dai akagama ,sannan yace inta tashi dg bacci ,taci abinci tasha mgani ,doctor din yafita.
Sir Aliyu yakalli Fatima ,yace ,bara naje nayi sallah,inta tashi ga abinci nan kuci kinji.
To tace sannan yafita, takalli Hafsat taga tayi bacci,nan tashige toilet din dake dakin tayi alwalla.
Bayan ta idar da sallah ta zauna,tanajin tausayin kawar tata.
Bayan2 hours har Hafsat ta farka taci abinci da magani ,Kuma taji karfin jikinta sosai.
Suna nan zaune itada Fatima sir Aliyu yashigo gab da magrib.
Yyi sallama ,yace yajikin ,kallon sa tyi tace da sauki sosai .
Ok bari nakira doctor ,aiko saiga shi ma yashigo, nan yaba sir Aliyu takardar sallama yace tarik'a shan mgani alokaci.
To sir Aliyu yace sannan yakallesu yace muje ko.
Nan suka bisa ,Fatima tayi saurin shiga baya Hafsat ta zauna agaba.
Bame mgana sai kirara ar. katun alk'ur ani ketashi .
Parking yyi gun wani guri inda akesaida nama gasasshe, yasiyomusu had'e da ice cream.
Yadawo ,suka cigaba da tafiya,bayan sun iso skul yyi parking Fatima tayi saurin fitowa.
Mik'amata ledar yyi yace rik'emuku wannan,godiya tayi tarufe k'ofar.
Hafsat ma ahankali ta bud'e kofar tace sir nagode sosai da taimakonka gareni.
Kataimaki rayuwata ,kabimun hakkina, kanuna cewa inada daraja Bacin ni bakowa bace.
Bason da bakin da zangode makaba,tana ida fada ta fito a motar.
Tabi Fatima suka wuce hostel,
Shikuwa sir Aliyu ,shiru yyi yana. Mamakin mahanganun Hafsat ,jiki ba kwari yaje ya mayar da motar anakin get yyi masaukinsa.
Washe gari ,alhmdllh Hafsat tasami sauki, bayan ta shirya ,tayi kalaci tasha magani.
Saita tsinci kanta da son xuwa office din sir Aliyu dan ta sake yimasa godiya.
Nan ta tashi ta nufi area class , cikin sa,a tasami office in abude.
Nan ta shiga tayi sallama ,Turus tayi ,tare da jin gabanta yafadi batason daliliba.
Sakamakon wata yarinya kyakkyawa ,zasuyi sa,o injuna da ita ,zaune kan cinyar sir Aliyu sai surutu take masa ,da yunifoam na yan day skul ajikinta.
Inbaccin da yarinyar tadago taganta databar office in .
Shima da kansa keduk'e yana latse latse a loptop yaji sallamar amma be dagoba.
,sa,ada ta kallesa tace yaya wacece wannan,tana nuna Hafsat?
D'agowa yyi, yaga Hafsat, saiyaji beji dadin dataga sa,ada acinyarsaba.
Amma sai bai nuna hakanba ,ahankali yace sunanta Hafsat.
Sannan yakalleta yace yajikin da sauki tace ,sannan ta Duka tagaidashi.
Bayan ya amsa yakalli, saada yace ke autar Momy kidagani haka nan,
Kije driver yakaiki skul kada kiyt latti.
Turo baki tyi tamike tace ai mommy ta matsa nakawo maka break.
Nan ta tafi,itama Hafsat ta yi hanyar waye ,ahankali yace ke zonan!!!!!
A next page zakuji shin wacece Hafsat?
Kuma wanene sir Aliyu?
share plsNIDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
๐
ฟ15&16
Wannan page nakine my bestie nah ameera marubuciyar ramin mugunta, kiyi yadda kkso dashi,ina mugun yinki irin sosai din nan๐น
Ahankali ta tsaya, cikin husky voice insa metada hankalin yan mata yace bazakizoba?
Saurin juyowa tayi tace ah ah sir ,yi hakuri , nan taxo ta duk'a gabansa.
Kallon ta Yy yace yanuna basket din dake gefensa ,yace yi serving d'in kanki.
Da sauri ta d'ago kanta ,yakafeta da mayun idanunsa ,saita sunkuyadda kanta.
Ahankali tace sir nakoshi saida na yi break a hostel.
Batare da yakalletaba ,Yace miyasa kikeson yimun musu ko gaddama,
Natsani ayimun musu ko gaddama ,dama jiya kinbatamun raiko shine zaki sake batan ko?
Da sauri ,tace sir bahaka bane, nasaba bana iya cin abincin ni daya sai cikin jama ,a muci atare.
Inni dayace bazan iyaciba,
Kallonta yyi Yace bari nayi serving dinmu muci atare ko?
Da har zatace ah ah ,ta tuna bayason musu ,sai tafasa.
Plate yadauka da kula yyi serving dinsu Chip's ne sa kaji soyayyu ,
Kafeta yyi da ido Yace taso muci nibantaba break a 7:30 ba sai yau.
Kan duguwar kujerar dke office in ,ya zauna yasa plate in agabansa da cokali me yatsu.
Ahankali tazo ta zauna ,duk da abincin yaburgeta Kuma bata saba cin irinsaba.
Amma badantaso suci tareba ,saidan kada tabata masa rai,gashi shikuma yana kyautata mata.
Ahankali tyi bissimilla tafaraci saidai taki yarda su had'a ido dashi.
Shikuwa cin abincin sa yake tsakani da allah yana latsa wayarsa.
Can yadago yasaci kallonta yaga bata kallosa ,aiko yyi mata k'uri da ido.
d'an karamin bakinta yake Kallo datake tauna abincin kamar bata son ci.
Azuciyarsa ca yake nifa ban taba ganin yarinyar nan tayi make up ,ko kwallima bata ahafawa, datana kwalliya aisaitafi haka kyau.
Lallai maza ba sa gabanta ,karatune agabanta, tsaki yyi Yace to ni meruwana da hakan.
Aje spoon d'in tayi ,da sauri yadago Yace banganeba .
Cikin shagwaba ta ce yaya na k'oshi cikina kamar zai fashe,tafad'a tare da mik'ewa tsaye jin anyi ringing shiga class dn yau bbu assembly.
Har ,aransa yaji d'adin yayan datakirashi dashi,amma azahiri sai ya yatsina fuska.
Yace waye yayan ,lallai kinzama yar kalan dangi.
Turo baki tayi tace ah ah, niba kalar dangi nayiba ,nasandai ka girmeni nesa ba kusaba ,shiyasa nacema ka hakan .
Kuma wadda ta fita yanzun itama haka aitacemaka , tafakaici idonsa ta gallamai harara.
Sarai yaganta ,cewa yyi nikeke hara ko? Ya matso gab da ita har sunajin numfashin juna.
Matsawa tyi bakin kofa tajuyo tayimasa gwalo ta ruga aguje tna dariya.
Shima dariyar mugunta yyi Yace haba yarinya zankamaki ,zakisan Wanda kka ma gwalo.
Zaunawa yyi ,yafara tunani ,shinmeyasa yake kulada da duk wani al,amari na Hafsat?
Miyasa bayason ganinta cikin damuwa, Kuma bayason yaga ana cutar da ita??
Duk yadda yaso yadena kulata ,da yaganta saiyaji kosan su rabu bayaso.
Wata zuciyar tace masa, shakuwace kawai, da haka ,yadauki taxt book ya tafi ss2A.
***********
WANENE SIR Aliyu
Aliyu Suleiman rabo ,shine cikakken sunansa,
d'ane ga alh Suleiman rabo senator na Kaduna, su 4 agun iyayansu.
Shine babba sai k'annansa ,kabir da sadik ,sai autarsu sa,ada.
Yayi digree dinsa na1 dana2 A ingila ,yakaranci fannin capinter ,yanada company dasuke kera furniture na gida DNA waje.
Dakuma abinda yashafi parlour, da kayan decoration na gida.
Suna zaune a unguwar gwamnati dake Kaduna,
Hjy Aisha itace mahaifiyarsu mace ce mai son jama,a bbu ruwanta da cewa sai mai wadata zatayi hudda dashi.
Akwaita dason taimakon talakawa,hakama mijinta asalinsu yan yolane ,aiki yamaido su Kaduna ,har sukadad'e alh Suleiman yazama senator.
Dalilin dayasa sir Aliyu yazo makarantar su Hafsat koyarwa ,shine governor yanasamun korafe k'orafe akan yan boarding skul ana xalintarsu.
Akan abubuwan da gwabnati kebasu ,ba a basu ,Kuma babu tsaro skul din da malaimai da suke koyarwa.
Kuma ba abincin kirki,hakan yasa governor, yatura amintattun yaransa amatsayin teachers dan su dauko masa da ruhoto.
Abinda yadace agyara agyarashi.
Kowace skul boarding dke Kaduna antura malami2 Kuma ba Wanda yasan wani amalaman.
To shine ,senator yaxo da maganar cikin familynsa nan sir Aliyu Yace zai iya.
Ba6ata lokaci, senator yagabatardashi gun governor,
Kuma governor yyi murna ,da akasamu nagida ,nan Sir Aliyu yasa hannu a skul dinda zaiyi teaching.
Dama shekara 2 akabasa, nan akakaisa skul din dake cikin k'auyen Kaduna, akabashi gd a step quarters
Dakuma hadadden office, din da zai zauna ,sannan ,yazabi subject din dazai rik'a koyawa.
Lokacin daya shiga skul din yalura da ss3 basuda kunya da tarbiya sai wani kallon sa suke ,atake yaji yatsanesu.
Dasu zai dunga koyamawa ,sai ,ya yafasa yacigaba da koyarda ss2 dukda suma saida yyi musu Jan ido.
Duk week end yake xuwa gd yadawo ranar Monday.
Hjy Aisha wato mahaifiyarsa da bataso yyi nisa da asu taso hana teaching din amma daddynsa Yace ah ah said yyi.
Sir Aliyu mutumin kirkine sosai cikinsa da wajansa Kuma miskiline na k' arshe .
Bayason shishshigi bayashiga abinda beshafesaba.
Sannan kwata kawata mata basa gabonsa dan har yanzun babu macen daya taba cewa yanaso.
Iyayensa sun so yyi aure amma yak'iyi da ammasa mgna sai Yace besamu wadda tayi masaba.
Har akafara tunanin ko beda lpia harde akagane qalau yake.
Dadinsa kuwa so yake duk wadda yasamu me tarbiya kawai yahadasu aure tunda yakiyi,
Kafin yazama tuzuru.
Sir Aliyu yanason familynsa sosai yashak'u da iyayensa musammun mahaifiyarsa tana k'aunarsa.
Kuma tanaji dashi, acikin k'annansa yafi shak'uwa da sa,ada.
Bata jin kunya ta hau cinyarsa tana masa shagwaba yana biyema ta,yasiyo mata Wannan yasiyo mata wannan
Dukda shekarunta basufi 15years ba sunshaku sosai,amma duk da haka tana mugun tsoransa,
Dan sir Aliyu ba wasa,inna yan miskilanci suka motsa ko sa,adar baya kulawa, Wannan shine labarin sir Aliyu.
WACECE HAFSAT.....
share plsNIDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
๐
ฟ17 &18
Wacece Hafsat?
Hafsat yarinyace yar kimanin15 year, farace ita kyakkyawa ajin farko,
Itaba gajeraba,bakuma doguwaba,tana da hanci da d'an karamin baki,sai girarta me gashi sosai harta kusa had'e wa.
Tana da dara daran idanu inta lumshesu tana kara kyau ,akwaita da sanyi Hali ga kirki.
Mlm Aminu shine mahaifinta ,suna zaune a unguwar kawo dke Kaduna
Mlm aminu talarkane lik'is ,yanzun matarsa 1 tana da yara2 . wato inna Laure.
Mlm aminu sun hadu da mahaifiyar ,Hafsat agarin gombe, suka fara soyayya, inda kawunanta suka bayar da,ita ga mlm aminu.
Kasancewarta marainiya ba uwa ba uba.
Bayan andaura auren mlm aminu da Maryam wadda akafi sani da mairo.
Yatafo da ita Kaduna, suka cigaba da zama cikin so da kauna.
Bayan shekara 2 mairo ta haifi yarta wato Hafsat,
Bayan Hafsat batasake haihuwa ba, hartayi shekara6 .
Nan fa mlm aminu yanuna yanason haihuwa.
Ba bata lokaci yace aure zaiyi, mairo batayi masa gaddamaba.
Nan yanemi inna Laure dake zawarci Kuma ,yar uwarsace ya aureta.
Bayan auren ,inna Laure ta lura da Mlm aminu yanason matarsa da yarsa sosai baya wulakantasu.
Dama ita tazo gidan da niyar fitar da mero,kota halin kaka.
Dan haka tayi makirci amma abun ba armashi , dan haka saita canja shawara, ganin tanada juna biyu.
Akwana atashi bbu wuya awurin uban giji,yau inna Laure ta tashi da nakuda.
Dan haka kafin takira mairo ta zo ta taimata mata ta tanaji wuk'a ta boye.
Bayan ta kira mairo,cikin ikon Allah ta haifi d'a nmj Kuma mlm aminu bayanan.
Nan aka aiki Hafsat takirasa ,Aiko suka taho tare ,Laure najin sallamarsu.
Tayi ihu da kara tafiddo wukar nan tayanki gefen hannunta.
Lokacin mero tagama shirya yaron yana hannunta.
Tayi saurin rike Laure ,Dede nan mlm aminu yashigo .
Nan Laure ta ture mairo tana kuka tace gara da Allah yakawoka sotake takashemu nida yaronka.
Gashi harta fara yankana,salati yy ,itakuwa mairo mamaki yahanata mgna.
Atake yyima mairo saki2 yakoreta yace tabar masa gidansa da yarsa.
Hafsat naji nagani akarabata da uwarta, alakacin tana yar8 years.
Nan rikonta yadawo gun Laure,inda duk aikin gdn yadawo kanta.
Ga tanasa mata talla,da farko mlm yahana ,dg baya data hadasa da boka yabari hardashima ake hantararta.
Akwai makwabcinsu alh Nasir me haline sosai yanada ya' Fatima, tare suka tashi da Hafsat sun shak'u da juna.
Duk yan gidansu Fatima suna tausayin halin da Hafsat take ciki .
Haka tacigaba da azabtuwa da shan wahala gun Laure sannan intake rainon danda Laure ta Haifa.
Ana haka tagama primary skul, alokacin Kuma Fatima ta gama itama amma boarding zata.
Tasoma Hafsat itama taje amma inna Laure ta hana.
Mahaifin Fatima shiyasama mata day skul tacigaba da zuwa intaje yau gobe bata xuwa sbd ukubar inna Laure.
Shikuwa mlm aminu yazama mjin tace.
Ana haka ,inna Laure ta sake haihuwa tasami mace ,hanifa ,
Akuma lokacin Hafsat tayi JSCE itada Fatima.
Nan Fatima taita had'a abbanta da Allah akan yaje yasami mlm aminu akan yanason yakai Hafsat boarding.
Nan abbanta ya yarda kasancewar anaji da Fatima,itada yayanta ,Ahmed sukadaine agun iyayansu.
Bayan abban Fatima yyi ma mlm aminu bayani haryaki yarda dan yason Laure bazata yardaba.
Se abban Fatima yyi masa dubara yace dg skul dinsu hafsat gwabnati tazabeta ,inkuma zaiyi musu adaureshi bbu ruwansa.
Atake ya yarda, nan yaje yyima Laure bayani da harta fara bala ,I taji ance gwabnati aisaitayi tsit.
Nan abban Fatima yyimusu komai tare da Hafsat aka kaisu ss1 ,class daya ,house daya.
Ko tsinke mlm aminu betaba siyama hafsatba .
Abban Fatima tunda yyi mata siyayyar farko besake mataba dan yadauka mlm aminu yana mata.
Itakuma Hafsat ta hana Fatima ta fad'i dan haka ,duk abinda aka kawoma Fatima dashi suke amfani.
Suna haka harsuka shiga ss2 sannan sir Aliyu yazo skul din.
Duk sadda sukazo Hutu sai Hafsat taci ukuba kafin takoma.
Sannan akwai wani tantirin dan iska waishi deeni gidoga.
Dan yayar inna Laure ne tunda yaga Hafsat ta girma yanuna yanasonta.
Itakuma batasonsa sbd ba mutumin kirkibane.
Itakuwa inna Laure catake ta bashi ,dan dama burinta Hafsat tasha wahala ta tozarta arayuwa.
Wannan ne labarin Hafsat.
_______________
Cigaban labarin "
Bayan kwana2, Hafsat ce zaune akwanarsu tanata tunani,
Yau kwana2 kenan rabonta da sir Aliyu , anya yana lfy, gaba daya saitaji skul in duk bbu Dadi
Dan tun ranar da tabar office insa da gudu tayimasa gwalo rabanta dashi kenan.
Dama ranar basudashi a class dinsu,jiya da yau Kuma sunadashi amma be zoba.
Tashi tayi tasa ka hijab dinta ,ta fito ta nufi area class.
Alokacin karfe2:30 pm.
Dede staff room ta tsaya ganin mlm rabe zai rufe, nan ta je ta gaidashi.
Amsawa yyi ,zai juya yatafi,da sauri tace mlm wai ina sir banganshiba kwana2.
Dukda tana tsoron kada yyi mata wata fahimta.
Kallon ta Yy yace wai baki saniba ,aibashi da lfy ,yana gidansa dake step quarters.
Yanzun haka ,kinga ga doctor can zan kai yadubasa.
Muje ma ,kin kuladashi matsayinki na yar uwarsa.
Dan shi mlm rave atunaninsa ,Hafsat kanwar sir Aliyu ce.
Kallon sa tayi tace mlm ai anhana zuwa step
NiDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
๐
ฟ19&20
Wannan page nakune yan NIDA D'ALIBATA fan's kuyi yadda kukeso dashi,inamugun yinku irin sosai din nan๐๐
Kallon sa tayi tace mlm ai an hana zuwa step quarters.
Girgiza kansa yyi yace ,aini ke dukan dukan duk Wanda yaje ,
Nabaki izni kije ki kula da yayanki,aike yakamata kije matsayinki na muharra marsa.
Itadai Hafsat shiru tayi tana,tunani wai itace muharramarsa.
Amma ta k' agara taje taga yajikin nasa yake.
Mlm rabene yace muje ko,da sauri tadawo tunaninta tabi bynsa.
Nan doctor din yabisu, suka dauhanyar step quarters.
Tun daga k'ofar shigowa sukejin kakarin amai,Aida sauri suka shige.
Duke' gaban tape din gidan suka samesa yana amai kamar ze amaye yan cikinsa.
Kuma aman yellow ne,da sauri Hafsat ta isa gunsa.
Cikin tausayawa tace sir sannu,d'agowa yyi yakalleta yamayar da kansa.
Buta ta dauka ta Tara jikin tape din tacika,ahankali ta tsugunna kusa dashi,
Tana xubamishi ruwan yana wanke fuskarsa da bakinsa.
Mlm rabe da doctor suka shiga parlour sunajiransa.
Kallon sa tayi taga ya dan rame fuskarnan tayi fiyau har dan yellow take.
Ahankali yace hafsattttttttt!!
Har cikin kanta taji sunan ,ahankali tace sir sannu!
Kallon ta Yy yaga tana hawaye, murya asark'e yace ,meyene nakuka ai nasami sauki ko.
Waye yasanar dke ne? share hawayenta tayi tace mlm rabe ne.
Kallon ta yyi yace to muje ,amma banaso kisake kuka nafa sami sauk'i kinji.
To tace tabi bayansa dan shiga parlour, kallon sa tayi taga shirt ce da 3quarter ajikinsa.
Jikinnan nasa amurde yake ga gashi kwance baki k'irin ajikinsa.
Bayan sun zauna doctor ,yazo yafara treating d'insa.
Yarubuta masa mgni ,sannan yyi masa allura ga hannu,dg karshe yace yarage tunani.
Nan sir Aliyu yaba mlm rabe takardar magani dan yasiyo, sukayi sallama da doctor.
Dazasu fita mlm rabe yace ke Hafsat ki zauna kkula dashi , yakalli sir Aliyu yace ashe batason baka lpia ba,
Saida ta tambayeni kana ina nafada mata.
Murmushi sir Aliyu yyi yace ainasami sauki mlm, nan suka fita.
Hafsat bataso mlm rabe yace wai taje nemansa,tasan sir da disgi kadama yyi mata wata fahimta.
Shikuma Sir Aliyu ,samun kansa yyi da jin dad'in yadda Hafsat tadamu dashi ,gashi har kuka tayi masa na tausayinsa.
Hafsat tashi tayi , sir Aliyu yakalleta yace ina zaki, azuciyarsa ca yake Allah yasa kada ta tafi.
Tsintar muryarta yyi tana cewa, zan dan shiga kitchen ne sai in gyara gidan.
Yaji dad'in hakan har cikin ransa amma afili sai yace .
Nifa bana cin jagwalgwalenki, kinma iya girkine?
Bata ce komaiba tafita,azuciyarta tace oh mutumin nan ba,a iya masa, beda lafiyar amma jin kansa na nan.
Tsakar gidan ta share ta goge, tana bakin tape zata d'ibi ruwa, mlm rabe yashigo ,ledar magani yabata yace kibasa kice sai yaci abinci ,yasha.
To tace ta kar6a , shikuma yafita, parlour takai maganin tasami sir Aliyu baya parlour n.
Ajewa tayi ta fita tashiga kitchen, taga akwai komai na bukata.
Dubawa tayi taga electric da risho, nan ta kunna risho ,ta aza tukunya kafin ta tafasa tagyara wake.
Nan taxuba waken tayi dan jajjage a greater, tatsane waken bayan yazabku
Tasoya kayan miyan ta zuba kayan k'amshi da maggi.
Nan dai cikin 1 hour ta yi masa faten wake da dankalin turawa ,yaji kifi da alaiyahu.
Tuni gidan yadau kamshi,nan ta wanke kayan data bata.
Tun cikin bed room sir Aliyu kejin kamshin girkin nan,
Har parlour yafito amma kamshin karuwa ,yake .
Atake tsohuwar yunwarsa ta taso yaji yakagara yaci abincin ko zazzabi nsa yasauka.
Befi minti gomaba da zamaba, ,tashigo da kula da plate da serving spoon.
Zaunawa tayi gabansa tace sir mlm yakawo magungunan ,amma yace saikaci abinci.
Sannan kashasu, yatsina fuska yyi yace ok sai anjima innaje restaurant naci.
Turo baki tyi tace gara abinci na mararsa lfy kaci pls nyi serving dinka?
Ah ah,Yace ahankali tace meyasa sir,
Kallon ta Yy yawani langabe kai kamar wani yaro,yanunata.
Yace bakece kika dena cemun yayaba, aikinga bazanci abincin wadda bata daukeni yayantaba.
Dariya yabata sosai amma sai tadaure tace, bakaine kacemun yar kalan dangiba.
Murmushi yyi Yace tskanarki fa nake,
Kallon sa tayi tace to yaya zakaci abincin ko?
Kaga saikasha magani, haka doctor Yace,kafeta yyi da firgitattun idanunsa yana Kallo, yajin dadin yadda take lallabasa.
Kallon ta yasakeyi Yace,akwai sharad'i ,inkinyarda to zanci.
Azuciyarta tace ,towai dole saikaci abincin ne xakace saida sharad'i.
Amma a fili saitace meye sharadin Yace kinyarda muci atare.
Da Sauri tace ah ah banajin yunwa ai.
Had'e rai yyi Yace ok zaki iya tafiya, tunda bazakbi umarnina.
Murmushi tayi tace ,tsokanarka nake,fa nan tabude kular.
Tsaki yyi Yace tunda ga abokin wasanki ko,aidama ina hagwanki,amma zankamaki,zakison Wanda kikayima gwalo rannan.
Kamshin girkinne yadaki hancinsa yalumshe ido.
Bayan ta xuba musu a