Showing 33001 words to 36000 words out of 70847 words
break amma shi yakasa cin komai tunanin Hafsat yake,can yamik'e ,mommy tace babana ina zakaje?
Da sauri yace xanje gun telan danaba yyi mun d'inkin d'aurin auren Ahmed begamaba bari naje.
Bejira amsarta tafita yaja motarsa ,bai tsaya ko inaba sai gidansu Fatima.
Ya na fitowa Fatima na dawowa da mutanen dazasu je gidansu.
Da sauki ya tsaidata ,mutanan suka wuce ciki,yakalleta bayan sun gaisa yace Fatima kifada mun gsky kada kimun k'arya ina Hafsat tayi kuka jiya kobatayiba kifada mun dan Allah.......
Share plsNIDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
๐
ฟ59&60
"Ajiyar zuciya Fatim a tayi tace", gsky sir tayi kuka dan haka nature d'inta yake,b atason yiwa mutum laifi koda yarone ga ba daya saita damu. Nibanma son kai ta yiwa lafiba naga dai tana kuka nabata b aki amma taki haku ra har na k'yaketa y anzun haka tana ci kin gidan .
" ahankali yace jeki kiramun ita kinji dan Allah ki lallab'ata."
Nan Fatima ta ce to ta nufi cikin gdan.
Shikuwa sir Aliyu du k tausayin Hafsat yajeji axuciyarsa,yak'agu taxo ya rarrasheta .
Fatima nazuwa ta sameta zaune tayi tagumi ,tace sis ki zo sir Aliyu nakiran ki awaje.da sauri ha fsat tace sis dgaske kike?
Fatima ta ce eh am ma ni shawarar da zanbaki kada kije.
Da sauri Hafsat tace me yasa ?
Fatima ta ce haba mana kema kija masa aji kuma in ki n masa laifi kidena saurin kuka.
"Yanxun bara naje n ace masa na lallab' aki kink'i zuwa,alam un kema kina fushi dashi sosai.
Nan Hafsat tace to shikenan sis ,fatim ata fita tasami sir Aliyu, tasanar dashi yadda suka tsara .
Cikin damuwa yace wai da gaske bazat ata zoba tayi fushi s osai?
Fatima tace eh gsky sir,girgiza kansa yyi yace to shikenan a mma dan Allah kiku lamun da ita ,natafi yafad'a had'e da shiga mota yabar gun.
" Fatima taje tasanar da Hafsat yadda sukayi da sir Aliyu, tace sis yafa damu kinga yadda yawani marairaice wai dan Allah nakulamishi dke.murmushin jin Dadi Hafsat ta yi, nan suka tashi Hafsat ta cigaba da walwalalta cikin jin dad'in sir yadena fushi da ita.
Sir Aliyu kuwa duk yinin ranar beci komaiba sai tunanin Hafsat da halin datake yakeyi.
Ana yin azahar yyi shirin zuwa d'aurin aure ,cikin shadda light blue tasha dinkin hannu yar ci ki da babbar Riga sai kamshi yake. Yanufi gun daurin auren ya k'udurta aransa ko cikin gidan ne sai yashiga yaga Hafsat dinsa ya rar rasheta ta dena fus hi dashi.bayan anga ma d'aurin aure duk abokan ango suka bisa zuwa cikin gida nsu,shima Al-ameen yaci marun d'in sha dda yanaso yaga sa hibarsa wato fatima .
Har ciki suka shiga adede compound din gidan duk mutanene kuma ha fsat da fatima nagu nsun saka anko d'insu sunyi kyau so sai .sir Aliyune yahango Hafsat take away ahannunta tarike ta nama fatima gwalo, murmushi yyi afili yace sarkin tsokana.
Karasawa yyi gun ,saidai kawai Hafsat ta ji k'amshinsa da sauri ta juyo sukayi 4eyes.
Wani killer smile yasakarma,saita turo baki tajason tagudu ,da sauri yatare gabanta,fuska kalar tausayi yace haba mana tawan nifa bakonkine ,kuma anason ka girmama bak'onka shine ni kike guduna zakiyi tafiyarki kin kyauta?
Murgud'a dan bakinta tayi tace to yaya bakaine jiya kayi tafiyanka ba kabarni,ni ina ruwana dakai tunda banda wani mahimmanci agunka kanaso nayita kuka dan namaka laifi.
"Ahankali yace I'm really very sorry kinji tawan ,banso kina fushi dani, dakuma yawan kukanki ,Amma kema kin fad'ane kawai aikin San nadamu dke sosai.
Shiru tayi ,yace meye a take away din?
" anhankali tace snacks ne."
Murmushi yyi yace to nike nan baza 'a baniba saina roka?
Kinga ga fatima can tanaba Al-ameen ha rma murmushi take yimasa ,Amma ni k'inki mun ko?
Cikin shagwaba ta ce, aiyanxun zanmaka bamun shirya ba .
Wasu kujeru dake gefen flows suka koma suka zauna, sir Aliyu yace hafsatttttttttttt dina!
Murmushi tayi tace yayanah,shima murmushi nyyi yace ai yanxun munshirya kindena fushi dani ko?
Ahankali Hafsat tace eh yayanah munshirya dariya yyi ,yafito da wayarsa yace kinyi kyau sosai bari nayi miki pics ko?
Ba musu tace to dan batason su cika fada dashi.
Nan yyita mata masu kyauhar yagama,yakalleta murya k'asa k'asa yace pls Hafsat d'ina kada na koma ganinki da kowa ne namiji kinjiko.
Ahankali Hafsat tace to yaya koda d'an uwanane?
Tunawa yyi da fatima tace masa Hafsat ce first born agidansu batada yaya,Amma axuciyarsa yace bari nagwadata shin tad'aukeni d'an uwanta bazata boyemun komaiba.
Kallon ta yyi yace Hafsat ,inaso kifada mun labarinki kuma ke wacece?
Da sauri ta kallesa da mamaki afuskarta,yad'aga mata kai alamar yana sauraronta.
Axuciyarta taji bazata iya boye masa komaiba,nan taduk'ar dakai tafara sanar dashi tarihin rayuwarta da labarin yanxun batason ina mahaifiyarta takeba.takuma sanar dashi labarin deeni gidoga.
Sir Aliyu yatausaya mata,har idanunsa sunyi jajir sbd koda can baya akwai abunda fatima tab'oye masa a labarin Hafsat.
Abu biyu yatsare masa arai,shine ba'ason ina mahaifiyarta takeba sai labarin deeni gidoga.yaji zafi aransa sosai da Hafsat ta ce wai har my wife deeni gidoga yake cemata,ya k'udurta aransa duk ran da yagamu da deeni saiya koyamasa hankali.
Kallon Hafsat yyi yaga tana hawaye,ahankali yamik'a mata hand chief yace ki goge hawayenki insha Allah za'a ga mama kinjiko.
Kuma shi baba ai lfy kuke dashi ko?
Ahankali Hafsat ta ce eh.
Mik'a masa hand chief din tayi murmushi yyi yace nabarmiki,duk sadda kika tuna dani toki kalli hand chief din kiyi murmushi xanji hakan ajikina.
Murmushin jin Dadin kalamansa tayi tace to Yayana nagode sosae Allah yabar zumunci.
Murmushi yyi yace ameen bbu godiya atsakanunmu.
Amma dai shi wannan deeni bedai yunkurin tab'aki ko?
Hafsat ta ce eh ai babana bazai bariba yanxun haka ma yahanasa shiga gidanmu.
Wani sanyi yaji axuciyarsa jin be yunkurin tabata kuma anhanasa shiga gidan.
Kallon ta yyi zomuje kirakani tawan kinji,murmushi tayi tace to yaya muje.
Har get suka fita ,yabud'e mata mota yace kishiga ranki yadade.
Murmushi tayi tace yaya kacika zolaya Allah kuwa,shiga yyi yaba motar wuta yace ai gsky na fad'a.
Kallon ta yyi yace wlh Hafsat banson muna batawa dake ko inga kina kuka pls kedena kinji tawan.
Murmushi tayi tace to yaya nah bazan koma yin kukanba ainima banason Bacin ranka wlh duk inkana fushi dani banajin Dadi arayuwata.
"Ahankali yace nima haka."
Parking yyi gaban wani shopping male, suka fito yace muje nan sukayi ciki...
Share plsNIDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ story & written by mmn fareesa
๐
ฟ61&62
Suna shiga Sir Aliyu nagaba Hafsat na baya , fannin kayan sawa sukayi .
"Ahankali sir Aliyu yace kixabi duk abinda kikeso kinji,murmushi tayi tad'an fara zab'a ,ga nin bata wani dauka yasa da kansa yashi ga jidar mata kaya h artace ya,isa amma be saurateta.dayaga abu sai kiji yace wa nnan zaimiki kyau ko?itadai sai tayi m urmushi kawai.
"""" haka yyita jidar mata kayan sawa da na kwalliya. "
Sungama siyan kom ai har sun biya,yatu na dawani turare ,da sauri yace Hafsat nayi mantuwa muje ki rakani ,mak'ale kafada tayi alamar bazatajeba ,murmushi yyi yace nine fa yayanki,hararansa tayi tace eh d'in,murmushi yyi yace haba yarinya nikike harara ko?
"daga masa kai tayi alamar eh, da sauri ya biyota tasaki ledar kayan ta zura aguje yarufa mata baya."
Sai d'an zagaye gun suke suna dariya abinsu, wasu na kallonsu suna birgesu.
Hafsat nashan yar kwana ta shigo fannin kayan provision, cikin gajiyawa tace yaya pls natuba muje narakaka kadauki abinda ka manta.
Sir Aliyu dke bayant a yana shirin yin mgn, kawai yaga Zakiyya itada wani d'an iskan boy friend d'inta.tasha kananun kaya surar jikinta abayyane,kallon sir Aliyu tayi da mamaki ganinsa tare da wata tace yaya wannan wawiyar ,jakar ina kasameta daga gani ta had'a iri da mayu, wa'annan kwala kwalan idanu nata haka.sir shiru yyi bece komai yanajin zafin kalaman da Zakiyya ta alak'anta Hafsat dasu. Saima yajuya yacigaba da duba wasu kayayyaki dke gaba nsa.
"Hafsat kuwa sarki ntsoro tana ganin y adda Zakiyya ke zare ido gata babba sai tasha jinin jikinta,tadawo bayan sir Aliyu tatsaya."
Zakiyya cikin jin haushin kin tankata da sir Aliyu yyi tace wai yaya Aliyu baka gannibane ina magana ka share?
Sir Aliyu yajuyo yakalleta sama da k'asa yyi murmushin takaici yace naganka me zanmaka ne?
Cikin mamaki Zakiyya ta ce kamar ya naganka saikace ni namiji ce ne?
d'aga kafada yyi alamar ko ajikinsa yace eh aini nan duk nan gurin Bacin wannan yanuna Hafsat dke bayansa yace banga mace anan gunba,dakai da wannan sokwan muna mazan duk daya na daukeshi dke.sannan daga yau kika sake kiran hafsat da kalmominki na hassada agareta sai nayi k'asa k'asa dke kamar yadda nakoyawa Mubarak hankali akan nagaba dashi. dan wannan dkike rainawa daya ce tamkar da dubu ,tafiki daraja ,matsayi ,aguna ,danke baki isa tayi magana dkeba sbd bakida d'a'a ,da tarbiya,itakuma bata hudd'a da marar tarbiya ,yana kaiwanan ya finciki hannun Hafsat sukabar gun azafafe.
"Cikin matukar jin kunya hade da bakin cikin kalaman sir Aliyu, Zakiyya tabar gun ko sallama batayiwa boy friend dintaba .
Shikuwa sir Aliyu suna barin gun yasake mata hannu yaje yad'auki ledar kayan suka fita.
Acikin mota yana driving yanajin d'acin kalaman Zakiyya datajefi Hafsat dasu ,axuciyarsa yace kwata kwata basuda tarbiya yan gidansu ko kad'an inbacin yanagudun Bacin ran su daddy da yyi mata abunda zatayi nadama har gaba ,da abada dan duk Wanda yanemi yataka Hafsat sai inda karfinsa yaka'r e.kallon ta yyi yaga alamar taji zafin kalaman Zakiyya,ci kin rarrashi yace kiyi hakuri kinji my hafs at zanyi maganinta banason Kisa damuwa aranki kinjiko?
" ahankali tace bakomai yaya yawuce nifa bandamuba."
Kallon sa tayi tace gidansu fatima zaka ajeni?
Batare da yakalletaba yace eh aizakije gun walimar gobe ko ? Tace insha Allah.
Koda suka iso yyi parking, dazata fito yasake cewa my Hafsat kiyi hkuri kan...da sauri ta katsesa da cewa kadaina bani hakuri yaya niban dauki abun wani laifiba.kaje gida kayi bacci kafin LA,asar dan Allah inkak'i jikina zai bani hakan murmushi yyi yace to namiki alk'awari my Hafsat zanyi yadda kkso. Yasake cewa kikulamun da kanki, nan yafito mata da kayan shopping din ta karba had'e da cewa nagode sosae Allah yak'ara budi yyima dukiyya albarka.
"Cikin jin dad'in kalamanta yace ameen,baibar gunba saida tashige ciki San nan yaja motar yanufi gd.
Hafsat nashi ga direct d'akin fatima ta wuce da kaya nik'i nik'i ahannunta.
Bayan ta zauna tasanar da fatima sir Aliyu ne yyimata shopping, murmushi fatima tayi tace mungode sosai gsky.
Hafsat ta ce mubarsu sai bayan biki muraba saiki kai mun gd kice abbankune yasiyamana tare.dan bansan yaya zanyiwa baba bayaniba gsky.
Fatima tace eh hakanma yyi ,nan suka chigaba da firarsu.
****************
Zakiyya kuwa rai bace tabar shopping male din ta nufi gida.
Tana shiga tasami mommy n ta da mubarak yayanta za une a parlour. da gudu ta fada jikin mommy ta saki kuka,nan mommy ta shiga tambayarta dalilin kukan dan dama itace ta bata yaranta ta kuma shagwabasu.
Cikin b'acin rai ta sanar da ita abinda sir Aliyu yyi mata akan wata.
Tsaki mommy ta yi tace wlh dakinbi nawa da kin hakura da yaronnan, yanun a baya k'aunarki ke. Kuma kinnace mas a yana wulak'antaki. Gashi yyimiki irin wannan tozarcin gaban bainar jama,a barito alh yadawo kaji d'an iskan yaro nanfa tahau tsinewa sir Aliyu had'e da aibatasa.
" Mubarak dke gefensu bece komai ba sbd be mance, suburbudarsa da sir Aliyu yyi ba dayaso yiwa daddy nsa rashin kunya. Tun daga lokacin yke masifar tsoransa.
Washe gari, sir Aliyu yana d'okin zuwa gun walima yaga Hafsat dan jiya saida yyi baccin datace yyi,yanaso yje gunta yatambayeta taji ajikinta yyi baccin ko be yiba.yana zaune daddy yakirasa yanxun yaje Lagos gun wasu kayansa,kamar yyi kuka yatafi ga bbu lokaci Balle yaje yyima ta bankwana.
6angaren Hafsat ma hakan take,tun 3:00pm take sauraron xuwan sir Aliyu amma shiru har 6:00pm yyi bbu shi ,hardai tacire rai tana tunanin k'ila yanada wani uxuri.
Haka takoma gida cike da tunaninsa,ta natuna tun dg sadda sir Aliyu yash igo rayuwarta tafara samun farin ciki. Tatuna bayan sun had'u a skul tadawo Hutu tasami babanta yashiryu asirin da Laure tamasa yakare. Murmushi tayi afili tace zan cigaba da yimaka addua Allah yasa kana lfy.
___________________
Bayan kwana10
"""" Hafsat ce zaune ita daya ad'akinta kasancewar baba yatafi sarin kaya yau kuma sai jibi sai dawo.fargabanta sh ine tasan Laure zata matsamata da masifarta,ga kuma. Tunanin sir Aliyu dan tafara tunanin anya yana lfy wannan shiru haka ,rabonta dashi kwana10kenan tun lokacin da yyi mata shopping .muryar Laure ce taji tadaki dodon kunnanta,tan a cewa to y'ar so tunda uban naki bayanan shida yadaure miki gindi kiyi yadda kkso ko? To saikitashi ki d'ebomun ruwa dan yau bazan sayi ruwaba ke zaki jidomana su!zaki tashi ko kuwa kintsareni da idanu irin na uwarki.cikin zafin kalaman Laure Hafsat ta tashi tad'a uki bucket tafara jid o ruwa a monon anguwar.)""";;
Sir Aliyu ne zaune a part d'insa jiya da dare yadawo dg Lagos ,gaba daya hankalinsa na gun Hafsat,yanxun haka tunani yake so yake yaje gunta yanxun.
Amma yana ganin kamar bazai gantaba duk da yasan gidansu to in ya aika yace kiranta yace injiwa? Kuma meke tsakanunsu?
"Wata zuciyar tace mutunci."
Tashi yyi be bari kowa yaganshiba yadauki motarsa yanufi anguwarsu Hafsat.
6angaren Hafsat kuwa haka tayita jido ruwa tana cika komai da'ake xuba ruwa agidan.
Komawa tayi ganinn saura d'auka d'aya tagama,ta sake d'ebo na karshe yana a hannunta sai ga deeni gidoga yatafo zaishiga gidansu,dan yakira Laure ko baba nanan tace ah ah bayama gari shine yatafo gidan yanxun.
Da sauri Hafsat ta matsa dan ya wuce amma sai yak'i shiga gidan yyyi tsaye yana kallonta.
Ganin haka yasa Hafsat ajiye bucket din ruwan kasancewar ahannunta yake.
Matsowa yyi gab da ita kamar zai rungumeta my wife nayi missing dinki!
da sauri Hafsat ta ja baya tace mlm meye haka bakada hankali?
Dariyar rainin hankali yyi yace yaude tsoho bayanan Balle ya kwaceki ga hannuna.
Wani mugun kallon tsana Hafsat ta aikamasa dashi tace kai wawa Wanda besan darajar iyayansaba,inbakasan darajarsuba ninasan darajar nawa.
Afusace deeni ya cafki hannun yariketa gam tasaka dayan hannun dan kwatar kanta agunsa.
Adedenan sir Aliyu yashigo anguwar,yana parking yafito,yana d'aga kansa yahango Hafsat tsaye ga wani gardi rik'e da hannunta tanason kwatar kanta amma takasa.
Be auneba yaga yadauke Hafsat damari,wani irin abu sir Aliyu yaji axuciyarsa yace ko wannan ne deeni? azafafe yanufi gun ko motar be rufeba...
Share plsNIDA D'ALIBATA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
๐
ฟ63&64
Inamik'a godiya ta ga dukkan masoyan wannan novel nagode sosae naga comments dinku bbu adadi agrps da PC ,inamugun yinku irin totally din nan๐ค๐ค๐ค๐๐
Hafsat dke kok'arin kwatar kanta takasa addua ta ke Allah yakawomata d'auki. Kamar dg sama taji muryar sir Aliyu tad aki dodon kunnanta yanacewa mlm saketa!
Deeni da sarai yaji a mma yak'i juyawa b alle yasaketa,cikin karaji had'e da tsaw a sir Aliyu yace bazaka saketaba? d asauri deeni yajuyo sukayi 4eyes da sir Aliyu take yaji wani mugun kwar jininsa azuciyarsa yace ko ina tasami wannan dan gayun dg ganin sa ba dan Nigeria bane gsky.
Wata wawar cafka hade da wani mugun punch sir Aliyu yakaimasa Atake yasaki hannun Hafsat ta koma gefe tana kallonsu.
"binsayyi yacigaba da bashi kyawawan maruka,"
Deeni yaso yafara ramawa,Amma sai yaga abin bahaka ba,cikin yan mintina har jama'a sun fara taruwa suna gani.
Hafsat kuwa duk ta rud'e ganin irin yadda sir Aliyu ke suburbudar deeni,tsoron ta kada yakasheshi.
"Deeni kuwa dayafara jin kamshin lahira tuni yafara cewa ,me gida natuba narabu da ita har abada kakyaleni."
"""" sir Aliyu bedena dukansaba saidayaga baya motsi ,Hafsat hartagaji dabasa hakuri,anacikin hakan wani yaje yasanar da Laure,saigata zani ahannu,ta fito cikin masifa da bala 'I tana cewa ,oh Kaine kwarton nata data turo kayi kisan kai ko? To wlh hukuma zata rabamu bazaka dakesaba kaci bilis Allah kuwa.wani mugun kallon tsana sir Aliyu yawatsawa Laure koba a'fad'ab a yasan wannan ce Laure matar baban Hafsat.cikin isa da gadara yace kafin kikaiga hukumar ni zankirasu su rufemunke da wannan wawan!
Aituni Laure tayi tsit dan saitaji wani mugun kwar jininsa ga kuma akwaita da tsoron hukuma,tafad'ane dan tayi musu burga Amma bawani karar dazatakai.Hafsat ta jefa da wani lallon zamu had'u tace ke kuma karyar maza zamu had'u dke ba gida daya muke kwanaba,ai ubanki zai dawo zansanar dashi maza kika ko ma bi.
"doguwar tsuka sir Aliyu yaja yakalli Hafsat yace muje."
da alamar tambaya ta kallesa, saitaga ya tamke fuska hakan yasa ta bisa.
Laure kuwa mai adaidaita ta tsayar Yakama mata deeni suka saka shi ciki ,suka nufi asibiti dashi danko motsin kirki bayayi.
"Sir Aliyu kuwa mota yabud'e ma Hafsat ,bayan sun shiga yakalleta yace inane inda baban yake zama muje Nayi masa bayani?
" ahankali tace ai bayanan yyi tafiya sai jibi zai dawo."
Shiru yyi can kuma yadauko wayarsa yasaka kira,bayan and'aga yace friend kana ina?
"Ok ganinan anguwarku kafito zamuyi wata magana.
Befi minti,5ba dayin wayar aka kwankwasa glass din motar,sir Aliyu yakalli Hafsat yace jirani zamuyi mgn yanzun zandawo.
"Hafsat tace to shikuma yafita."
Can baya suka tsaya da yaya Ahmed bayan sun gaisa ,sir Aliyu yalabarta masa abinda yafaru yanzun. Ciki tausayi yaya Ahmed yace hmm ai yarinyarnan na ganin abubuwa wlh gwanin tausayi allah dai yasaka mata,sir Aliyu yace ameen.yaya Ahmed yace Amma kai meke tsakanunku da ita? Yatsina fuska yyi yace mefa?inbaccin mutunci,inakuma tausayawa rayuwarta ,kuma d'alibata ce!
"Yy Ahmed yace dalibarka banganeba?" Nan sir Aliyu yabashi labrin xuwanshi skul da governor yyi,sannan yace naga Ku makwabtane shin babanta yanada waya dan tacemun baya gari?
"Yy Ahmed yace eh bari nakirasa ,tunda dai bazamu bari ta koma gd ba ,tunda Laure tayi wannan kalami."
"Sir Aliyu yace hakane."
Nan yy Ahmed yakira baba yasanar dashi komai da kuma taimakon da sir Aliyu yyima Hafsat.
Nan baba yyita sama sir Aliyu albarka,da fatan gamawa da duniya lfy.
Duk sir Aliyu yanaji kasancewar a hansfree yasaka wayar,har cikin xuciyarsa yaji dadin adduar baba yaji kuma kaunar dattijon.
Nan yaya Ahmed ya ce to baba ,Aliyu zai tafi da Hafsat gidansu ta zauna sai jibi inkadawo zai maidota,da gidanmu zata zauna to su umma da Fatima basanan suna abuja,ka,amince dan na yadda da abokina ?
Baba yyi gyaran murya yace to shikenan nima har raina nji na yarda dashi kuma ai malaminsune ,inde bazai sami matsalaba da iyayansa to yaje da ita inkuma da matsala zan iya komowa yau dukda zanyi dare a hanya.
Sir Aliyu ne ya karbi wayar yyi sallama yace baba kada kadamu ,mahaifiyata Nada fahimta