Showing 36001 words to 39000 words out of 70847 words
kuma zanriketa amana kafin kadawo .baba yace to aliyu nagode sosae Allah yyimaka albarka.nan sukayi sallama sir Aliyu yasaka number baba awayarsa ,yakalli Ahmed sukayi musabiha yakoma mota,Ahmed yabar gun cikeda zargin sir Aliyu son Hafsat yake.
Yanashiga yatada motar yakalli Hafsat yace ,gidan mu zanje nakaiki kizauna sai xuwa jibin in baba yadawo dan munyi waya dashi yanzun kuma ya amince muje,bayan mun isa zankirashi sai kuyi magana ko?
Mak'e kafada tayi tace nidai yaya inajin kunya,bazanjeba kabari naje gun Fatima mana.
Murmushi yyi yace aisu fatima basa gari shiyasa,kuma momin tawa kikejima kunya?
Sunkuyadda kanta tayi tana murmushi,tace wai yaya ina kaje har kwana10 bangankaba?
Ahankali yace Nayi tafiya Lagos ne dadinah yaturani,kuma jiya nadawo da dare yaukuma naji inason inganki shine nazo natarar da abinda yafaru.
Ahankali tace yaya nagode s..... da sauri yace bbu godiya tsakanunmu kidena mun godiya.
Murmushi tayi tace kacancanci hakanne yaya.
Amma ,Sa'ada na gida ?
Murmushi yyi yace eh tana gida nasan zatayi murna da ganinki,Amma zancewa mommy kunyarta ma kikeji.
Turo baki tayi gaba,ahankali yace saina murde wannan bakin da kike turowa gaba.
Dariya Hafsat ta yi tace Taf baka iyawa,kwafa yyi yace haba yarinya zankamakine kin rainani ko,?
Dede nan suka iso gidansu ,yyi horn get man yabud'e masa get yyi parking, Hafsat jitayi gabanta yafadi,haka ta daure ta fito sai tsokanarta yake Amma tak'i kulasa yana gaba tana bite dashi suka shige parlourn gidan...
Share plsNIDA D'ALIBATA
πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
Story &written by mmn fareesa
Dedicate to all my fan's ana mugun tare,yan nida dalibata grp fan's 3 comments dinku na yau yafi nakowa ina mugun jidaku irin sosai dinnan.ππ
π
Ώ65&66
Suna shiga sir Aliyu yyi sallama suka sami mommy da sa ada zaune ,sai Mubarak yyan zakiy ya abbansa ya aiko sa gun daddy nsu sir Aliyu,yasami daddy baya k'asarm a. Cikin fara'a mom my ta amsa sallam mar,kafin ta sake mgna taga wata kyakkyawar yarinya na bayan sir Aliyu.
" murmushi mommy ta yi tace bakuwa mukayi."
Aida gudu sa'ada tazo tayi hugging din Hafsat tana dariya had'e da cewa oyoyo my friend.
Shikuwa Mubarak mutuwar zaune yyi ganin wannan sura ta Hafsat me d'aukar hankali.
Sa'ada ta kalli mommy ta ce mommy wannan ce Hafsat.
Da sauri Hafsat ta xube k'asa tana gaida mommy, ta amsa cikin sakin fuska had'e da k'ura ma Hafsat ido tana tuna kamar tasanta ko wani me kama da ita.
"""" shikuma sir Aliyu zama yyi gefen kujera yana me jin Dad'in yadda Hafsat ta girma ma mahaiyarsa,kuma itama mommy ta karbeta da hannu biyu.gefen da Mubarak yake ya kallah dan sai yanzun yalura da shima.kawai yaga yak'ure Hafsat da ido yana mata kallon k'urullah.wani mugun tsaki sir Aliyu yaja Wanda besan lokacin dayayisa ba,hakan yadawo da Mubarak haiyacinsa yadena kallon Hafsat cikin in ina yace yaya barka dah dah ....dare ina wuni? Wani kallo sir Aliyu yyi masa atak'aice yace lfy,na n Mubarak ya kalli mommy yace natafi mommy ,zan sanar da abban daddyn bayanan,nan mommy ta ce ok kagaida yan gidan,nan yafita sum sum.""";;
"Mommy takalli sa'ada tace bazaki kawowa bakuwar komai ba?"
da sauri tace ah ah mommy yanzun zankawomata drinks.
Mommy ta ce oh Hafsat kisaki jikinki kinji nan gidankune naga sai kunya kkeji,sir Aliyu yace hmm mommy haka takefa,yanxunma wai kunya takeji bazatazoba.murmushi mommy ta yi har cikin zuciyarta taji kaunar Hafsat dan ta lura yarinyar Nada tarbiyya da kunya had'e da kawaici,kallon sa'ada tayi tace Auta kuje da Hafsat d'akinki ta huta saikuzo muyi lunch ,nan sa'ada ta ce to takama hannun Hafsat suka mik'e koda zasu wuce saida Hafsat ta saci kallon sir Aliyu aiko shima yasaci kallonta suka had'a ido yakashe mata ido daya had'e da wani killer smile. Abinda basu saniba duk mommy na lura dasu,kuma tagane sir Aliyu da Hafsat suna son junansu, dalilin dayasa tace su Hafsat sukoma dakin sa'ada dan ta tambayesa meke tsakaninsa da Hafsat dan tana kwad'aita masa au ren ta,co's yarinyar Nada kamun kai.
"Bayan su sa'ada sunbar gun mommy ta kalli sir Aliyu tace babana meke tsakaninka da wannan yarinyar kuma wacece ita??"
"Ahankali sir Aliyu yy gyaran murya yafara bawa mommy labarin Hafsat tun daga farko har yanzun da dalilin dayasa yakawota gidan ."
Be auneba yaga mommy na hawaye sbd tsabar tausayin Hafsat.
""""" ahankali tace insha Allah za'aga mahaifiyarta,kuma Laure aniyarta zata bita gara da kakawota nan sai ta zauna har babanta yadawo.sir Aliyu yace eh mommy Ai ankusa ma komawa Hutu dan yau saura8days sukoma,mommy tace allah yakaimu lfy,Amma babana kuna soyayya da Hafsat ko? da sauri yad'an zaro ido yace haba dai mommy d'alibata ce fa! Allah yakiyaye,nibanma San yaso yakeba.
Murmushi kawai mommy ta yi batace komaiba dan ta lura sir Aliyu besan yafad'a tarkon so bane shiyasa yake haka ,Amma zata saka masa ido taga iya gudunsa.kallonta sir Aliyu yyi yace mommy bari naje Nayi wanka!ok kawai tace,amamakinta saitaga yanufi part din sa'ada."""
"da sauri tace baban a kaida zakayi wanka ina kuma zaka?
Waigowa yyi yana d'an Sosa k'eya yace am am dama..dama zansanar da Hafsat zanshiga ciki kada tajini shiru tayita nemana,ko tayi kuk...saurin yin shiru yyi dan yana Neman yin subutar baki.mommy data guntse dariyar datazo mata tace ai baza nemekaba tunda sunsaba da sa'ada.bece komaiba sum sum yy part dinsa.
************
Bangane sa'ada da Hafsat kuwa ,sun baje kan gadon sa'ada suna fira abinsu can sa'a taje ta had'a ma Hafsat ruwan wanka tace sis jekiyi wanka.
Bayan ta fito sa'ada ta fito mata da black arebian gown tasaka,wow sai Hafsat ta yi kamar balarabiya,sa'ada sai wasata take hade da kod'a kyawun datayi take.can sa'ada tace naso ace daddy na yana gari kikazo wlh dan inabashi labarin inada k'awa Hafsat.murmushi Hafsat ta yi tace Allah sarki, Dede nan mommy ta shigo tace yarana kuxo muje muyi lunch, ta kalli Hafsat hade da kama hannun ta tace y'ata kidena jin kunya ta kinji ki daukeni tamkar mamanki kinjiko?
" ahankali Hafsat ta ce to."
Nan suka fito suka nufi dining area, a can suka sami sir Aliyu yasha kananun kaya ,kyawunsa da kamalarsa sunsake bayyana atare dashi.
Murmushi yyi ya kalli mommy yace oh mommy naga baki wani damu dani ba yasu Hafsat da sa'ada kawai kike.
Murmushi mommy ta yi tace eh ta y'ayana nike mana,kai ai kazama tsohon yyi,sa'ada da Hafsat suka yi dariya atare,murtuke fuska sir Aliyu yyi yace kai ina wasa dakune wlh innarike yarinya hmm zata gaya masu,Hafsat ta faki idonsu mommy ta yi wa sir Aliyu gwalo,kallonta yyi yanuna kansa wai dashi take ?d'aga kanta tayi alamar eh, kwafa yyi yamata alamar zai kamatane.
Duk abinda suke mommy na lura dasu tadai sharene.
Nan suka zauna sa'ada tayi serving dinsu,suka fara cin abinci ,Hafsat naci akunyace .
Sir Aliyu ne yak'ara turakafarsa k'ark'ashin table din ,kasancewar suna pessing juna da Hafsat yatake mata k'afa da k'afarsa mai takalmi sawu ciki.
Wani mugun zafi taji,har zata fasa ihu ta tuna inda take sai tayi shiru tad'an rintse ido alamar tanajin zafi.shikuwa sir Aliyu murmushin mugunta kawai yake ,yana satar kallon Hafsat,ita kuwa ta d'auka wani abu ne yadatse mata k'afa ganin sir Aliyu yana murmushi kuma ita yake kallo yasa tagane shine.fakar idonsu mommy ta yi ta galla masa harara,kara take k'afar yyi,da ido take basa hakuri,sai can dayaga dama ya janye kafarsa,itakuwa ta murgud'a masa baki had'e da harararsa, ta had'e k'afafunta yadda bazai sake take mata suna .nan Hafsat ta ce ta koshi sir Aliyu yace aidama mommy haka take batason cin abincin sosai, murmushi mommy ta yi tace kiladai bakunta take mana. nan sa'ada ta ce ita ta koshi ,taja Hafsat sukabar gun.
"Shima sir Aliyu yatashi yatafi masjid."
___________________ Zakiyya ce zaune kan bed adakinta tanajin wak'ar music awayarta.
Mubarak yashigo yazauna kan bed side,yakalleta yace sis yasu nan yarinyar da kikaga yaya ALiyu da ita a shopping males?
"da mamaki Zakiyya ta kallesa tace lfy yaya?'
Murmushi yyi yace ki amsamun tambaya ta.
Zakiyya tace sunanta Hafsat!
Mubarak yace to naganta da yaya aliyu yau agidansu yaje da ita!, kutumar uba zakiyya ta fad'a cikin karaji,murmushi Mubarak yyi yace minene abun tada jijiyar wuya ,ni yarinyar tamun wlh danko bansame taba inason inhuta da ita dan kalar skin d'inta yamun,saidai inatsoron yaya Aliyu wlh dan naga kamar sonta yake.
Wata muguwar dariya irinta basawa Zakiyya tayi tace naji Dadi data maka dan nadau ki alk'awrin kota halin kak'a saina auri yya Aliyu.
" kabarmin komai zanbincike akanta ."
Mubarak yace to shikenan dan ni inzan aureta inaso inkuma bazan auretaba inason in lashi zumarta.
Wani mugun murmushi Zakiyya tayi tace kada kadamu ko satota sai muyi ko mu nunawa iyayanta kudi su aura maka ita.
"Dan ina tunanin yar talakawa ce."
Nan Mubarak yace to shikenan yafita.
Da misalin 8:00pm sir Aliyu yashigo parlourn gidansu yasami sa'ada zaune a parlour ,yace ina mommy da Hafsat?
Sa'ada ta ce mommy na d'aki sallah take ,itakuma Hafsat ta na d'akina tana game.
Da sauri sir Aliyu yanufi dakin,yana shiga yasami Hafsat ta na game tana dariya ,kawai tagansa kamar daga sama.
Kusa da ita ya zauna ya kalleta yace wana kama?
Shiru tayi tana zare ido,can tace to bakaine kayita takemun k'afaba.
Murmushi yyi yace hmm saina gyaramiki wannan bakin da kike turowa.
"Ahankali tace yauwa yaya kiramun baban mu gaisa saika bani inyi game da wayarka.
Kallonta yyi yace bazan kiraba.
Aisaita hau kukan shagwaba harda dire dire ita sai yakira mata babanta.
Sir Aliyu kuwa lumshe idanunsa yyi ,azuciyarsa yanace wa yah salam sakamakon wani abu dayakeji ganin yadda Hafsat ke Wannan shagwaba r dan yalura akwai kuruciya da ita.
Share plsNIDA DA'LIBATA
πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
Story & written by mmn fareesa
π
Ώ67&68
"""" Ahankali Hafsat ta ce bara naje nafad'awa mommy kak'i kiramun baban a."bud'e idonsa yyi yace hmm aibazaki iyaba ,abinda kunya r momin kike,marairaicewa tayi tana lallab'a sa sannan yakira baba n,Hafsat tayi mama kin yadda sir Aliyu ya saba da babanta ganin yadda suke fira dashi.
Sir Aliyu ya mik'a mata wayar yafita nan Hafsat suka sha fira da baba yyita mata nasiha tayi hakuri da rayuwa kuma ta rik'e mutuncinta.sannan sukayi sallama,tafit o dg dakin dan kaiwa sir Aliyu wayarsa."";;
A parlour tasamesu harda mommy, nan taje ta mik'ama sir Aliyu wayarsa sai kallonta yake da idanunsa dasuka canja kala.
Mommy ce tace suje ayi deener,Hafsat tace ta koshi,wani kallo sir Aliyu yabita dashi yace mekika ci da har kika k'oshi?
Sunkuyadda kanta tayi tace nasha fura gun sa'ada ai.
Girgiza kansa yyi yace banyarda fura zata k'osar dakeba oya muje kici abinci.
Murmushi mommy ta yi tana kallonsu cikin birgewada sha'awarsu ,tace kai babana kacika takura dole sai taci aboncinne?kallon Hafsat ta yi tace y'a ta zakici ko kin koshi?Hafsat ta saci kallon sir Aliyu taga yyimata alamar intace ta koshi in yakamata zata gayamusu ai da sauri tace eh mommy zanci!murmushi mommy ta yi danta lura da abinda sir Aliyu yanuna wa Hafsat. Dining area suka nufa,bayan sun zauna mommy ta yi serving in kowa,harsuka gama sannan ,sukayi sallama kowa yawuce makwancinsa.
Washe gari da misalin karfe 6:30am ,Hafsat ce ta fito da ga d'akin sa'ada,kasancewar bayan sun idar da sallah sa'ada ta koma bacci.itakuma ta kasa komawa Dan tasaba agidnsu da anyi sallar asuba Laure zatayi ta sakata aiki,zai zirga xirga take bata waiting parlour bata part din sa'ada,gash I tanason ganin sir Aliyu, kuma batasan inda yakeba,mommy dake part dinta taji motsin yyi yawa ta fito ta sami Hafsat zaune kan carpet ta yi shiru.
"Ahankali mommy ta ce y'ata yaya dai?"
Da sauri Hafsat ta gaida,ita ta amsa fuska cike da walwala,kan kujera mommy ta zauna ta ce zonan kinji,ba musu Hafsat ta je ,hannunta mommy ta kama ta zaunar da ita kusa da ita.tace kifad'amun mekkso?inde kin d'aukeni mamanki kinji?
"Ahankali Hafsat ta ce ina yaya yake banganshiba?"
Murmushi mommy ta yi tace, yana part dinsa ,k'ila bacci yake,amma ai lokacin motsa jikinsa yyi ,yanzun kingansa yazo,inkuma xakije ga kwana can inkikabi har part dinsa sai kije.
Da sauri Hafsat tace ah ah mommy basai najeba.
Murmushi mommy ta yi, dan tasan da k'yar taje,dan talura yarinyar akwai tarbiyya da kamun kai.
"Can kuma Hafsat ta mik'e tace mommy na tafi gun sa'ada!mommy tace to y'ata,nan ta nufi dakin,kafin ta ida isa taji kamshin turaren sa da sauri ta juya sukayi4eyes dashi yana sanye da kayan motsa jiki wani killer smile yasakar mata ,itama tayimasa.
" murya k'asa k'asa yace my Hafsat kintashi lfy ?"
Turo baki tayi tace lfy had'e da duk'awa ta gaida shi murmushi yyi ya amsa tare da cewa sarkin rigima to menene kike wani tura baki gayamun kinji?
"Ahankali tace bakaibane bangankaba sai yanzun."
Kallon ta yyi yace to sorry ina part dina ai yanzun gani ,mujema kirakani gun exersic . mak'e kafada tayi alamar ah ah bazata jeba.murmushi yyi yace shikenan zamu bata kuwa.....muryar mommy yaji tana cewa Auta sai yanzun kika tashi har Hafsat ta rigaki tashi,wata irin kunya sir Aliyu yaji,itakuwa Hafsat bata juyaba da gudu ta shige dakin sa'ada, shima ko kallon mommy be iyaba sum sum ya wuce.
Ita kuwa mommy murmushi tayi ,axuciyarta tace allah yasa kunada rabon mallakar juna ,dan daga gani Hafsat saita canja maka ak'ida,gashi dama bakason raini ita kuma tana girmamaka ,ko dazata gaidashi saida ta duk'a fg ita harshi sun manta da ina gun ,amma zan cigaba da adduah allah yazaba abinda yafi alkhairi.
Bayan su Hafsat da sa'ada sunyi wanka ,sukayi break fast Wanda sir Aliyu be zoba dan yanajin nauyin mommy sai dai sadik , shikuwa kabeer yana skul. Nan sa'ada taja Fatima suka wuce islamiyarsu.
"Sir Aliyu da ke bed room dinsa yaga fitarsu ta window."
Basu jima da fitaba yaji k'arar anbude get ,da sauri yaduba yaga ko sadiq zai fita da mota dan anhanasa fita da mota yyi karanta aceawar sir Aliyu. Kawai saiyaga motar Mubarak yyi parking ,hakanan sir Aliyu yaji wani mugun fad'uwar gaba, yajikuma be yadda da zuwan Mubarak ba dan yasan dagashi har Zakiyya basa zuwa gidansu saida dalili,be auneba yaga sun fito mota tare da Zakiyya, nan yasake mamaki,amma sai yasake bude labulan windon dan yagansu sosai ,amamakinsa sai yaga sun nufo setin windon dayake da sauri yasaki labulen windon,har zai juya yakoma kan bed sai yaji muryarsu suna magana k'asa k'asa.
"da sauri yatsaya yafara sauraransu."
Ji yyi Mubarak yace kin gane sis inkinje ki nuna kinzo musu yini ne ,Nina kawoki zanzo na d'aukeki .
Kinsan sa'ada fa surutu sai kibigi ciki nta kiji inane anguwarsu da kuma iyayanta,kinga in talakawane ta kwana gidan sauki,sai muje muyi musu b'arin kudi ,kin gane? Wata yar dariya Zakiyya tayi tace babu damuwa Allah yasa zan iya dan mugun haushi suke bani daga Hafsat din har sa'adar.
"Ahankali Mubarak yace kinga inmun sami information akanta shikenan, sai mubita gidansu dg nan inta yarda zata aureni ba matsala."
Inkuma tak'i kawai sai insaka asatomun ita nabiya buk'atata da ita.
Dariyar mugunta Zakiyya tayi tace kaga ko yaya aliyu ya aureta bazata yi daraja gunsaba tunda abud'e zai sameta,ballema bazan bari ya auretaba.
"""" mutuwar tsaye sir Aliyu yyi agun ,sai wata irin zufa ke keto masa,innalillahi wa inna ilaihir raju un kawai yake maimai tawa,had'e da jin wani fad'uwar gaba da b'acin rai,Atake idanunsa sukayi jajir suka k'ank'ance,da sauri yaja glass din windown.
Arazane Zakiyya da Mubarak suka juyo sukayi 4eyes da sir Aliyu.
Ai take yan hanjin cikin Mubarak suka kulle dan tsabar firgita yatsorata da yadda yaga idanun sir Aliyu.
Ita ma Zakiyya ta tsorata sosai musammun data lura da sir Aliyu yaji duk firarsu da sukayi.
Basu auneba sukaga sir Aliyu baya bakin window din,arazane Mubarak yace muje mukoma mota wlh zagayowa zaiyi ,kinsan kuwa mukayi arba dashi kashina ya bushe asukwane suka nufi gun da suka yi parking.
Adede nan kuma Hafsat da sa,ada suka turo get suka shigo ciki.
Sir Aliyu kuwa da sauri yafito dg part dinsa, zai nufi k'ofar fita parlour n, da sauri mommy ta tsaidashi ganin yanayinsa dan tasan ba lfy.
Da sauri tace ina zakaje ne haka ranka bace?
Cikin damuwa yace pls mommy kibarni naje kada su gudu .
Mommy ta ce su wanene? Da sauri yace Mubarak da Zakiyya,kara su cutarmun da Hafsat mommy ki barni naje dan Allah yafad'a kamar zai yi kuka.
Cikin mamaki mommy ta basa hanya ya futa afusace kamar zai tashi sama.
Ya fita ya hango har get man yabud'e masu get zasu fita, da gudu yakoma ciki ya dauko key din motarsa ya fito mommy na tambayarsa ina zaije be kulataba ya fito asukwane.
Parking spaces yawuce,nan yahango su Hafsat zasu shiga ciki,da sauri yashige motar yabata wuta.
Dan yyi alk'awarin ko gaban abbansune karshe kenan sai yakoya musu ahankali.
Da mugun gudu ya isa gidansu Zakiyya,a parking spaces yaga motar Mubarak da alama suna ciki shida Zakiyya.
Azuciye yafito dg motarsa yyi cikin gidan afusace....
Share plsNIDA D'ALIBATA
πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
Story & written by mmn fareesa
π
Ώ69&70
Ko sallama bbu ya afka cikin parlourn fuska ba annuri.yas amesu zaune a parlourn Mubarak yana shan lemo,ai yana ganin sir Aliyu yasaki cup d'in lemo n had'e da mik'ewa tsaye yana tari sbd k'warewar da yyi.
Shikuwa sir Aliyu gu n mubarak yyi gadan gadan,mommy na ganin haka afusace tace kai lfy zakashigo min gd bako sallama? Ko gun datake sir Aliyu be kallaba ,fisgo Mubarak kawai yyi yafara basa kyawawan maruka masu rai da lfy Atake Mubarak yasaki ihu had'e da cewa mommy ki ceceni dan Allah. Ita kuwa mominsu tsinewa sir Aliyu kawai take yi had'e da aibatasa.shikuwa ko ajikinsa,dukan Mubarak kawai yake yana cewa dakaji dukan dnayi maka a farko dabakayi yink'urin abinda kayi yanxunba ,bedena suburbudarsaba sai da yakumbura masa fuska tukum .sannan yanunasa da yatsa yace wlh wlh wlh duk abinda yasami Hafsat Kaine da Zakiyya dan wlh zan aje yan uwantaka gefe Nayi muku hukunci da abinda kuka aikata,ai inkacika tantiri basai kasaka asato maka ita ba kabiya bukatarka da itaba ah ah har gidansu zakaje da kanka gaban kowa saika d'aukota ammafa in zaka iya.
Ita kuwa Zakiyya part dinta ta gudu ta rufe.
Koda sir Aliyu yajuya yaga bbu ita yasan guduwa tayi.
Cikin masifa mommy ta ce wlh saina dau mataki akanka dan kafi k'arfinsa saika rik'a zalintarsa ,kuma akan wata banzar mace ma .
"Ahankali sir Aliyu yakalleta yace mommy ina ganin girmanki kidena zagina haka,yaradai k'annena ne kuma na isa dasu insunyi laifi na hukuntasu. "
Wani tsaki taja tace wlh z....muryar abbansu Zakiyya taji yana cewa kincuceni Hajara kin b'atamun tarbiyyar yara gaba d'aya kuma Nayi duk abinda Aliyu yafad'a kinaji yace zaisa asato masa yarinya ya aikata masha'a da ita amma bazakiga laifinsaba,saikirik'a zagin Aliyu.cikin b'acin rai Abba yakalli sir