Showing 42001 words to 45000 words out of 70847 words

Chapter 15 - NIDA DALIBATA Complete Hausa novel

24 Aug 2024

12248

baba bani wayarka zanyi wani lissafi!bbu musu yabata tareda cewa Nina fita dan ukku tayi ankusa la'asar,inna dawo na karba.
"Ahankali tace to baba adawo lfy nan yafita .Hafsat cikin zumud'i ta shiga cikin contacts, cikin sa'a taga bbu number sir Aliyu. Shiru tayi,can kuma tashiga receive call ta duba rana da lokaci Atake tagane number dukda ba suna.";;

Atake tasaka kira,harta tsinke ba'a d'agaba,turo baki tayi cikin jin haushi kamar agabansa take,kawai taji wayar na ringing tana dubawa taga shine yakira,saida takusa tsinkewa ta d'aga batare da tayi magana ba.cikin girmama wa sir Aliyu yyi sallama had'e da cewa baba barka da rana,murmushi Hafsat ta yi me sauti atake yagane itace,cikin zumudi yace my Hafsat kece? Wani murmushin tasakeyi tace nice yayanah,kaga nadamu dakai ko amma kai baka damu dani ba gashi Nina fara kiranka.

" cikin marairai cewa had'e da rarrashi yace ayya my Hafsat bahaka bane, wlh inason muyi waya amma inajin nauyin cewa baba yabaki ne shiyasa,amma yanzun kin hakura?"

"Kamar yana ganinta ta d'aga kai had'e da cewa eh."

Murmushi yyi yace to nagode ai nasan kinada hakuri da sauri yafiya,amma kina yawan tunanina?

Yar dariya tayi tace ah ah.

Had'e rai yyi yace to shikenan tunda ma bakya tunani,nima zan dena tunaninki.

Cikin shagwaba ta ce, yaya dan Allah kada kadena tunani na nafison koda yaushe ina cikin ranka.

Lumshe idanunsa yyi yajin dadin sweet voice dinta hade da kalamanta.

"Ahankali yace um um kema ai bakya tuna ni ."

Dasauri tace ah ah wlh ina tunaka namaka dubarane dan inji kana tunani,shiyasa,ammafa ko yanxunfa tunanunka nikeyi ,nayiwa baba dubara na karbe wayarsa nakiraka.

Murmushi yyi yace Allah tawan.

Lumshe ido tayi tace eh mana,yanzun kana ina ?yace ina part dina, tace inasu mommy da sa'ada ?

Murmushi yyi yace sunyi kewarki sosai,dariya tayi tace nima haka.

Murya k'asa k'asa yace gobe sai skul ko?turo baki tayi tace eh yaya ni banso in koma gobe nafiso sai next week murmushi yyi yace gobe insha Allah zaki koma skul.mur gud'a baki tayi tace to sai anjima, dasauri yace kingaji da magana danine? Ahankali tace ah ah kawai dai banso baba yasameni ina waya Bacin ban fada masa ba.ajiyar zuciya yyi yace hmm wata ta koma mak'aryaciya ko?

Cikin shagwaba ta ce allah niba mak'aryaciya bace ni munbata dakai.

Dariya yyi yace dama rannan kinmun gwalo ko? To zamu hadu askul gobe saina saka mlm rabe yabani dorina na zabeki.cik in kukan shagwaba ta hau basa hkuri,shikuwa jin tana hakan yyi saurin k'ashe wayar sbd wani yanayi da bak'on al'amari da ya tsinci kansa aciki.ita kuwa Hafsat ta dauka da gaske yake tunda har yakashe kiran duk saita ji tsoron komawa skul gobe duk da wata zuciyar nacewa wasa yake miki.

Washe gari da misalin karfe 4:00harsu Hafsat sungama shirinsu ,baba yyi mata nasiha akan takulada kanta tayi kuma karatu tunda Wannan ce shekararsu ta karshe dazasuyi askul.har yan hawaye saida ta yi,Laure na kallabta tana tab'e baki had'e da hararanta,sarai Hafsat ta lura da ita tadai nuna kamar bata gani ba, kallon su hanifa da shamsu kannanta tayi tace suxo sutayata d'aukar kaya,kallonsu Laure kawai tayi suka gane meta ke nufi. Atake sukak'i zuwa ,baba da agabansa akayi ya kallesu yace kuje kutayata dauka ko ranku yab'aci,ganin ba wasa afuskarsa yasa sum sum suka bita, suna tayata.awaje taga Fatima da driver,nan akasaka komai aboot suka dauki hanyar skul dinsu.


****************
6angaren sir Aliyu kuwa, mommy ta yi masa miyar kaji da danbun naman rago had'e da provision tace yakaiwa Hafsat a skul.

Sir Aliyu yyi Dadi sosai yyi farin ciki da yadda mahaifiyarsa ke nuna k'auna da tausayawa ga Hafsat.

Haka yaci wankan sa,cikin kananun kaya, sai k'amshi yake,abin sai Wanda yagani yaja motarsa sai skul.

Koda ya isa, office dinsa ya bude yashiga ya zauna aciki,yabar windows abud'e dan yana hangen get dg office dinsa.

"Yafison da Hafsat ta dawo yaganta."

Befi15minit ba yahango Hafsat cikin pink checks na doguwar Riga idanunta sunyi d'an ja alamar tayi kuka kenan.

"Azuciyarsa yace yah salam me tayiwa kuka ne?"

Hangowa yyi sun gama shigowa da kayansu Fatima ta saka ana dauka ana kaimusu daki,su kuma sun biyo bayan su.

"""""Hafsat ta saci kallon office din sir Aliyu taganshi abude, kallon Fatima ta yi tace sis xomuje gun sir naga office insa abud'e yake!da sauri Fatima ta ce ah ah sis kedai kije bari ni naje najere mana kayanmu a laka.Hafsat tace ba damuwa,nan tanufi office din Sir Aliyu. Shikuwa yana hangota yafito dan bayason yawan ke b'ewa da ita dan gudun ajimasu wani zato.

Tana ganinsa ta tsaya,shikuwa kafeta yyi da mayun idanunsa yana kallonta, murya k'asa k'asa yace waya samun ke kuka gayamun kinji tawan?

Sunku yadda kanta k'asa tayi tace ba kowa kawaidai banson in rabu da babana.

Murmushi sir Aliyu yyi yace kada kidamu zan rik'a kira miki shi kuna gaisawa.

Murmushi tayi had'e da kallon sa tace yauwa yaya nagode sosae, harnaji Dadi wlh.

Murmushi yyi yace nima har naji Dadi da kika kasance cikin jin Dadi.

" ahankali yace ga kayanki can a office da mommy ta bani nakawomiki."

d'an zaro ido tayi tace oh wai yaya mommy bata gajiya da yimun hidima ai d'awainiyar tayi yawa dan Allah.

"Ahankali yace kada kidamu mommy haka take."

Nan yaje yad'auko mata kayan tayita masa godiya sukayi sallama, ta nufi hostel shikuma ya nufi step quarters.


________________
WAIWAYE.....
Mahaifiyar Hafsat tunda mlm aminu yasaketa yakwace y'arsa tarasa ina zata gashi batada ko sisi Balle ta tafi gombe garinsu,kuma rabontada garin tun sadda mlm amunu yadauko ta dg can yakawota Kaduna ko labarinsu bataji.haka tarik'a tafiya cikin bak'in ciki da b'acin rai. Bata auneba taji mota ta bangajeta ta fadi daga nan bata sake sanin inda kanta yakeba.

Shikuwa Alh suleman rabo wato mahaifin sir Aliyu da yabanketa,hankali tashe yyi hospital da ita.

Babu bata lokaci akayi emergency da ita.

Bayan awa3 wani doctor yafito yakalli alh suleman yace muje office dina inason magana dakai.

Bayan sun zauna doctor yyi ajiyar zuciya yace a gsky akwai matsala

"Da Sauri alh suleman yace tame?"

Doctor yace gsky brain d'inta tasami matsala dan kota farka bazata dawo hayya cintaba sbd brain dinta ta bugu sosai,saidai bazata dauwama ahaka ba ah ah zamu azata kan magani har Allah yasa ta warke brain dinta ta dawo normal.

Innalillahi wa inna ilaihir raju un kawai alh Suleiman yake maimai tawa.

Cikin tashin hankali yace wlh doctor bansantaba kuma da alama cikin damuwa take na kad'eta.

Amma bara naje nasanarwa da mata ta sainadawo.

Doctor yace babu damuwa."


Babu jimawa alh Suleiman yadawo da hjy Aisha ,kasancewarta mace mai fahimta ,ta fahimci komai takuma tausayawa marar lafiyar.

Saida tayi kusan wata daya a hospital sannan aka sallah meta,suka koma gida gashi ko magana batayi,mai aiki hjy Aisha ta dauka tana kula da ita.

Akuma lokacin sir Aliyu baya kasar yana karatu dashida kabeer.

sa'ada ce sai sadeek ita sa'ada alokacin tana yar8years shikuwa sadeek yana 13years duk da bawani lura suke da abinda ke faruwaba kasancewar part daban ake jinyarta.

Da alh Suleiman yaga har tayi shekara gashi bbu sauk'i kuma ba asamu danginta ba sai yaturata kasar waje yadauki wadda za ta je jinyarta.

Har akayi shekara 4tana can bbu sauki dai ga kuma lokacin har sir Aliyu yadawo yagama degree dinsa na biyu,kuma su mommy sun labarta masa abinda yafaru saidai betaba zuwa dubata ba saidai daddy ke xuwa duk karshen month.

Ko lokacin da Hafsat ta zo gidan baya kasar yanacan dubata.

Cigaban labarin...

Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿75&76

cigaban labarin
Bayan Hafsat ta koma d'aki tasami har Fatima ta je re musu komai a laka.

Nan ta nuna mata kayan da mommyn sir Aliyu ta bata.
"Fatima tayi murna sosai da godiya, sannan suka sake shirya kayan ."

Washe gari byan sun dawo dg class Hafsat suna daki wata mate dinsu tazo tace mata sir Aliyu yana kiranta,bbu bata lokaci ta saka hijab ta fita.

"" tana fita dg get din area hostel ta gansa atsaye yyiwa hanyar kuri da ido alamar ita yake ji ra."ahankali ta isa gunsa,bayan sun gaisa ta kallesa taga kamar yana cikin damuwa.murya asark'e tace yaya naaaaaaaa! kallonta yyi da idanunsa dasuka fara ja ,murya k'asa k'asa yace I'm sorry to say Hafsat yanxun daddy nah yakirani kan naje Lagos zanyi 7or8days nakula da kayansa dake can shi aiki yyi masa yawa.nadamu sosai wlh nafison ina acikin skul din nan akoda yaushe ina kula dake ,amma kiyi hakuri kinji,yafad'a cikin damuwa.

"Ahankali Hafsat tace pls yaya kamayar dani gd inkadawo nadawo."

Girgiza kansa yyi yace hakan ba zai yuyuba my Hafsat karatunfa?

Turo baki tayi hade da fashewa da kuka!ai gaba d'aya saita rikitasa co's yatsani yaga tana kuka.

"cikin rarrashi yace haba mana pls kiyi shiru da me kikeso naji ne da kukanki ko da zafin rabuwarmu?"

Yi shiru kinji Hafsat dina goge hawayanki kimun mgn ko zanji dad'i.

Da sauri ta goge hawayenta ,tana kallonsa,tace nadena amma yaya wlh baxanji dadin skul din nan ba inbakanan.

Cikin rarrashi yace ai bazan dad'eba yafad'a had'e da mik'a mata keys yace gashi na office dinane nasa anmiki daya ni daya,duk sadda kika tunani kije kibud'e ki gyaramun kinji tawan?

Karba tayi ta lumshe idanunta had'e da waresu a fuskarsa ,tace to shikenan nagode.

Kallonta yyi yace kimun alk'awari bazakiyi ta kukannanba,

"Ahankali tace baxanyiba insha Allah zan dunga yima ka addua Allah yasa kadawo lfy".

Murmushi yyi yace yauwa kokefa tawan har naji Dadi wlh, muje ma kirakani get.

" ba musu ta bisa sukajera suna tafiya cike da burgewa da sha'awa."

Ahanyane yace my Hafsat zan dunga kiran mlm rabe yana banike muna gaisawa kinji ,kuma nabada not kuyi innadawo zanyi explanation.

"Ahankali tace to yaya nah,amma zanyi missing dinka sosai,kallonta yyi yace nima haka my Hafsat nunawa ne kawai banayi,amma me kikeso nasiya miki pls kinji tawan kada kice ah ah kifad'amun ?

Da Saudi tace duk abinda kaga yadace dani kasiyamun zanyi murna dashi,tafad'a had'e da tsayawa kasancewar sunzo bakin get gun motarsa.

Bud'e motar yyi had'e da kafeta da lumsassun idanunsa yace zantafi zo kimun addua.

Ba musu tazo gab dashi tayimasa,ta kallesa hawaye na zuba murya na rawa tace yaya ka kulamun da kanka sannan kaji tsoron Allah aduk inda kake kaji?

Yah salam yafada azuciyarsa ganin batadena hawayeba,ahankali yace insha Allah tawan matso kiji ba musu ta Dan matso yarad'a mata wata magana wadda nikaina banji komai yace ba sbd yyi maganar k'asa k'asa. Da sauri Hafsat ta fashe da dariya tana kallonsa tanacewa allah yaya,shima dariyar yake yi yace eh mana,murmushi tayi tace to shikuma kaje kada kayi latti.ba musu yashiga hade da Jan motar ,Hafsat dake tsaye tarika daga masa hannu harya fita get ta nufo hostel cike da kewar sir Aliyu.

Bayan ta dawone take labartawa Fatima sir baya gari yayitafiya ,Fatima tace allah yadawo miki dashi lfy dan wlh sis ko kiso ko kada kiso keda sir Aliyu kunason juna sbd alamomi sun nuna hakan.

Harararta Hafsat ta yi tace gsky sis ba kanki dayaba,malaminane.

Fatima tace hmm allah yabamu rai da lfy ko Ku menene amma dai kuna son juna.

Hafsat bata sake cewa komaiba ,amma maganar ta tsayamata arai da tunanin maganar ta kwana.

Washe gari haka ta yini sukuku,jira kawai take taga mlm rabe yakirata yace ga sir Aliyu yakira su gaisa amma shiru har dare.
*****************

Bayan kwana4 yakama sir Aliyu lwamansa 5da tafiya Lagos,Hafsat ce zaune a bed dinta tanata tunanin sir Aliyu, kodai ba lfy har yanzun shiru be kirataba.tunawa tayi da keys d'in da yabata da sauri taje ta d'auko taja Fatima suka wuce office dinsa,bayan sun bud'e suka shiga,suna shiga Hafsat ta ji gaba d'aya office din k'amshin sa yakeyi,jitarik'ayi kamar zata gansa ,duk abin nan Fatima na lura da ita sbd itama tayi nisa asonAl-ameen dinta dan jitake in akarabasu zata iya rasa ranta,Hafsat ce ta katse mata tunani da cewa sis ki gyara office nikuma na gyara bed room,ok Fatima ta ce ta koma office Hafsat ta cigaba da gyara bed room din cike da tunanin sir Aliyu had'e da kewarsa.

"Bayan sun gamasuka fito,Hafsat ji take kamar karta fito."

Nan suka koma hostel abinsu.


Bangaren sir Aliyu kuwa da gangan yak'i kiran Hafsat dan acewarsa soyake yagwada zuciyarsa kozai iya yin wasu kwanaki beji muryarta ba ko be ganta,sbd yasan SSCE zatayi ba jimawa dole yabar ganinta kullum,dan aganinsa yyi mugun sabo dakuma shak'uwa da ita, amma me?adaddafe yyi5days yaji bazai iya jurewaba sannan ga yawan mafarkinta dayake yawan yi,dan jiya da kyar yyi bacci sbd tunaninta,bbu shiri yakira mlm rabe yace yaje yabata wayar zai kira ne yabata wani sak'o bbu musu mlm rabe yace to nan yanufi hostel dan kiran Hafsat.

Hafsat kuwa dawowarsu kenan daga gyarama sir Aliyu office mlm rabe ya Aiko tazo,da sauri ta fita dan ranta yabata sir Aliyu ne keson magana da ita away a.


Tana isa taga mlm rabe tsaye bayan sun gaisa yace mata dama gashi yanzun mlm Aliyu zai kira suyi magana .

Nanta karb'a tadan matsa bayan staffroom, nanko wayar tayi ringing saida ta k'osa tsinkewa ta d'aga shikuwa bawan Allah jin ta d'aga wayar yyi wata ajiyar zuciya dabesan yyiba.

Hafsat najin haka tasaki kukan shagwaba kamar tana agabansa.

Shikuwa gaba daya ta susutashi da shagwaba rta,lumshe idanunsa yyi murya k'asa k'asa yace I'm sorry kinji yi shiru kifada mun me kikewa rigima ne?

Cikin turo baki tace bakaineba tunda ka tafi baka kiraba sai yanzun meyasa kayi hakan?

Cikin wata kasalallar murya yace my Hafsat bahaka bane wayana ta fadi saida na canxa layi Nayi welcome back shiyasa .

Murmushi tayi tace to nayarda bakada laifi to ina wuni?

Murmushi yyi dan yalura akwai k'uruciya da yarinta atare da ita,lfy ykk ya karatu?

Ahankali tace alhmdllh.

Nandai sukayi ta fira daga karshe sukayi sallama,taje taba mlm rabe wayarsa ta koma daki cike da farinciki.

____________________
Bari mu lekasu kamal muji awane babin suke........

Share plsNIDA D'ALIBATA

Story & written by mmn fareesa

🅿77&78

Bari mu lek'asu kamal muji awanne babi suke..

"" zazzaune suke bayan sun gama shan aiki sun gaji",kamal dake tsakiyarsu kallo daya zaka masa kasan yaji jiki duk yarame yyi bak'i sbd wahalar dasuke sha shi ne yyi gyaran murya yace wlh wlh naga rayuwa kuma na yarda duniya makaranta ce ,lallai xuwana gidan jarin nakoyi darasi.insha Allah aka sakemu zanje har gun mlm Aliyu na rok'i yafiyarsa dakuma yarinyarnan hafsat.
d'ayan dake gefensa yace nima haka na shiryu dama Kaine oganmu kuma ka shiryu,dayan dke gefe yace nima haka amma kai kamar basunsaka anbata maka ta karduba? Kamal yace eh Wannan ba matsala bane sbd abbana kamfaninsa yaso na zama manager amma naki na nuna ni sai teaching zanyi ,amma inmunfito zanje narok'esa gafara yamayardani a camfaninsa.baki dayansu sukace ameen Allah yashiryu masu Hali irin namu.

Bangaren su hafsat kuwa sundage da karatu ,kuma tunanin sir Aliyu yana nan dank'are axuciyarta,yanzun haka tunaninsa take tana tunanin yau ko gobe zai dawo.shiru tayi can kuma sai takama kuka sakamakon mahaifiyarta data rasa ina take tana Raye kota mutu? Fatima ce taji kukanta ta taso tana tambayarta lfy?nan cikin kuka tace mamana sis bansan inatakeba banson kowa nata ba yazanyi da rayuwata? Ahankali Fatima ta ce kada kidamu Allah yana tare da mai hakuri kuma duk tsanani yana tare da sauk'i ki dage kiciga ba dak'ara addu a insha allah za'a ganta dan inajin hakan ajikina kinji da haka dai Fatima ta rarrasheta da irin Wannan nasihar har tayi shiru.

**************
Sir Aliyu ne tsaye gaban mirror yana taje sumar kansa yyi wani kyau na musammun ,sai sauri yake sbd dawowarsa kenan dg Lagos yanaso yaje yaga hafsat dan bazai iya kwana be gantaba.

Yana gama kimtsawa yafito awaiting parlour yasami mommy zaune tana ganinsa tace baba ga abincinka can dining yana jiranka.

"Ahankali yace mommy na k'oshi".

Da sauri yyi waje ,murmushi mommy ta yi afili tace hmm tunda kana zumudin kaje kaga hafsat ai bazaka tsaya cin abincin.

" Sir Aliyu be tsaya ko inaba sai skul dinsu hafsat ko office be budeba straight area hostel yanufa."
Cikin sa'a Fatima zata skul shop ta hangosa ya nufo nan ,danshi bema lura da ita ba ,ai dagudu ta koma ta kaiwa hafsat labari.

Da gudu hafsat ta fito dan murna tanufi get ,tana fita get sir Aliyu yana kawowa zai shiga saura kad'an hafsat ta fad'a ajikinsa.
Cikin murna had'e da farincikin ganin juna suka tsurawa juna ido suna kallo ko k'iftawa bbu.

"Ahankali sir Aliyu yace my Hafsat nasameki lfy?"

Lumshe idanunta tayi tace lfy lau Yayana Nayi kewarka da yawa .

Murmushi yyi yace nima haka, amma ai gashi nadawo kinga mahakurci mawadaci ko?

Ahankali tace eh,inasu mommy da sa,ada ?

Murmushi yyi yace wato ni ba'a wani tambayata yanike ko wani abu saidai ki tambayi su mommy da sa'ada ko?

Marairaicewa tayi tace lah yaya ba haka bane ,ba yanzun nace Nayi kewarka ba kuma kasan ai nadamu dakai, amma tunda ma kishi kake dasu mommy da sa'ada shikenan ,zandunga yin mafarkinsu sai murika gaisawa cikin mafarki ko?

Yatsina fuska yyi yace eh naji ,ni kingama tafiyata ,murgud'a masa baki tayi had'e da masa gwalo .

Murmushi yyi nidaiko ?yanzun nazo shine kkemun haka ,kinsan dama inatara laifukanki ko gashi yanzun kin sake ,gobe zankarbi bulala gun mlm rabe na zaneki da ita.

Cikin shagwaba hade da marairacewa tahau basa hkuri,shikuwa kamar gaske sai yawani sake d'aure fuska, shi adole da gaske yake.

Ai tuni hafsat ta rud'e tafara zare ido dan ta dauka da gaske yake.

Shikuwa dama haka yake so sbd hafsat tafi masa kyau a haka in tana atsorace,shagala yyi da kallonta harta lura ga murmushi kwance a fuskarsa.

Turo baki tayi ta kafesa da ido tana kallo,cikin shagwaba tace shine ka tsoratani ko?

Murmushi yyi yace hafsat dina kenan aikinfi kyau ahakan ne shiyasa na tsorataki.

Yar dariya tayi tace yaya kaje kayi aski duk wannan kasumbar ta ragemaka kyau kaje agyara maka .

Murmushi yyi dayaji tace tarage masa kyau wato hafsat ta na ganin kyawunsa kenan,kallonta yyi yace to my Hafsat duk abinda kikeso shi za'ayi kinaso insaka a askemun ita duka?

Da sauri tace ah ah anbar sajenka kafumun kyau ahakan kawai dai agyaramaka naga duk fuskar ta cika.

Murmushi yyi yace hmm garin ne banyarda damasu gyaran fuskansu ,nabari sai nazo nan nagyara da kaina,kuma dawowata kenan nace sainazo naganki.

Murmushi tayi mai sauti tace hakane yaya nah wlh kana ji dani sosai nagode .

Ahankali yace kada kidamu kinfi haka aguna ,abinda nikeso dake ki maida hankali kiyi karatu kinga final year kuke kinjiko?

Ahankali tace insha Allah ,kallonta yyi yace ni zan wuce maraice yyi ,kije kiyi alwalla kiyi zikiri kafin magarib.

Ba musu ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login