Showing 45001 words to 48000 words out of 70847 words

Chapter 16 - NIDA DALIBATA Complete Hausa novel

24 Aug 2024

12240

to yaya jagaidamun dasu mommy.

Kallonta yyi yace nak'i bake kikace zaku gaisaba amafarki ,murmushi tayi tace eh ai namantane,batajira amsarsaba tayi cikin area hostel.

Shikuwa yar dariya yyi yawuce get yadauki motarsa yanufi gida.

_________________
Haka rayuwa taci gaba da kasan cewa ,inda shakuwa mai karfi ta sake shiga tsakani Sir Aliyu da Hafsat dakuma tsanani son junansu inda har yanzun bbu Wanda yasan yana son dan uwansa dan duk atunaninsu shakuwa ce sukayi da juna.
Kwanci tashi bbu wuya gun uban giji harsu hafsat sun kammala exams dinsu ta first term anbasu Hutu yau sun nifo gida cike da murna dukda wani gefen na zuciyar hafsat batason rabuwa da yayanta wato sir Aliyu dukda yace zai dinga xuwa yana kawo mata Sa,ada.

Washe garin dasuka koma gida Hutu Yakama satday ne ,tun safe hafsat ta keta aikatuwa kasancewar baba yana kasuwa gun aikinsa dan in gabansane bazai bariba yanzun haka uban wanki ne tasha na Laure da yaranta,ta zauna tana hutawa baba yashigo da ledar fura guda biyu hafsat daya Laure da yaranta daya .

Bayan hafsat ta yi masa sannu da zuwa yabata ya nufi dakinsa,bbu jima aka Aiko wai wasu mutane nayin sallama da Mlm aminu.

A k'ofar gida kuwa alh Suleiman rabone wato senator da body guards d'insa, governor yaturasa a anguwanni yasami me anguwa yaji matsalolin anguwarsa,shine suka shigo nan anguwar kasancewar gidan mlm aminu ne bakin hanya kuma farkon layin hakan yasa senator yace sutsaya nan akira me gidan yyimusu magana da mai anguwar ,anguwai.

Cikin gida kuwa mlm aminu yyi mamakin kiransa ,hakadai yafita dan ganin masu nemansa.

Yana zuwa da mamaki yakalli senator mutumin da sai a tb yake ganinsa ko ajarida amma shine k'ofar gidan sa allah yasa lfy .

Senator da yalura mlm aminu yadan tsorata daganinsu k'ofar gidan sa,nan yasaka akayima mlm aminu bayanin dalilin zuwansu.

Nan mlm.aminu yakawo gaisuwa gun senator tare da cewa bari akawo ta barma sai yaje yataho damai anguwa.

Nan yashiga ciki yadauko tabarmi,Laure na tambayarsa lfy?

Yace yyi bak'i ne k'ofar gida,bejira amsartaba yafita.

Shewa tayi dan dama sotake yafita ta kwace furar da hafsat ke damawa suhad'a da tasu itada y'ayanta su sha.

Yana fita tahau tsinewa hafsat ta karbe furar tace kuma in ta sanar da baba sai tajama ta Sharrin dahar ta mutu bata mantawa,sannan ta jefeta da bucket tace taje ta d'ebo mata ruwa.

Bbu musu hafsat ta dauka tana kuka tasaka hijab har kasa ta fito da bucket a hannunta.

Ak'ofar gida kuwa baba bayan ya shinfida musu tabarma sun zauna bbu wulakanci ko k'yama ,mutum daya yabisa dan kiran me anguwa,yabarsu senator zaune nan gun.


Hafsat na fitowa ta tsaya asoro tana goge hawayanta dan ta lura da mutane awaje.

Senator dake zaune yana fessin k'ofar gidan yana kallon Wanda ke zaure,a idonsa yaga hafsat tana hawaye yaga kuma ta goge su ka kakaro murmushi kamar batayiba ta na niyar fitowa da bucket a hannunta.

Tana fitowa ya gansu da sauri ta xube k'asa ta gaidasu ta tafiyarta.

Shikuwa senator se yaji yarinyar taba sa tausayi dan yalura tanada damuwa amma ta boye aranta sannan kuma uwa uba tanada kamun kai da tarbiyya,atake wani abu yad'arsu aransa.

Akuma lokacin mlm aminu yadawo da mai anguwa,bbu bata lokaci sukayi magana da senator akan abinda yakawosu.

Bayan sun gama magana senator, yacewa yaransa suje sujirasa ,yakira mlm aminu kasancewar dazasuyi magana da mai anguwa yabasu wuri.

Bayan mlm.aminu yazo senator yakallesa yace ...

Share pls[12/30, 9:37 AM] Ikhty Hafsat: NIDA D'ALIBATA
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

Story & written by mmn fareesa

๐Ÿ…ฟ79&80


"Bayan mlm aminu yazo senator yakallesa yace dalilin dayasa na kiraka shine inason inyimaka tambaya2 dan Allah inkabani dama?" Cikin mamakinsa mlm aminu yace to y'allab'ai ina sauraronka, senator yace na farko !wata yarinya nagani ta fito da bucket y'arkace?mlm aminu yace eh y'ata ce,senator yacigaba da cewa anyimata miji?mlm aminu yace ah ah gsky.
Senator yace inbazaka damuba inaso kabani dama na nemawa d'ana aurenta.zaro ido mlm aminu yyi yace gsky y'allabai kafi karfinmu ,mu talakawa ne ,murmushi senator yy yace kada kadamu Dame kud'i da talaka duk Allah yyi su inde zakaba d'ana aurenta bbu matsala. Ajiyar zuciya mlm aminu yyi yace gsky bata gama karatuba yanzun aji6 take a makaranta. Senator yace inna fahimceka befi saura wata 6tagama secondary skul din ta,mlm aminu yace eh hakane.senator yace bbu damuwa intagama sai ya aureta inma zataci gaba sai tayi agidansa.mlm aminu yace to y'allab'ai nagode sosae amma zan tuntubi yarin yar tukum.

"Wani kat senator yamik'a masa yace gashi address dina ne dakuma personal number ta,nabaka dama kaje kayi bincike akanmu dan shi aure yanason bincike sannan duk shawarar daka yanke ka kirani."


Baba yakarb'a yyi masa godiya ,senator yabada rafar yan1000guda2 yace akaiwa baba,amma baba yak'i karba yace suyi hkuri wataran ya karba,bbu yadda basuyiba yak'i karba har sai da senator yace ya karba had'e da cewa ba amaida kyau baya maida kyauta se shaidan sannan ya karba had'e da shigewa gida.

Shikuma senator ya yarda cewa inde sir Aliyu ya auri yarinyar nan to zaiyi suruka ta kirki dan yalura basuda kwad'ayin abin duniya dan inda wanine uban be wani shawara Atake zai yarda.

****************
Bangaren su kamal kuwa har ansakesu sati biyu da suka wuce.har yyi yar kiba haskensa yadawo,kuma iyayansa sunyafemasa yadawo da aiki a camfanin mahaifinsa.

Ayanxun haka tafe yake a motarsa zashi office d'in sir Aliyu dan yaje yyi bincike kansa yaga no office dinsa.

Bayan ya isa yyi magana akasanar da sir Aliyu yanada bako,nan akace yashiga.

Yana shiga yyi sallama sir Aliyu da kansa dake duke ya amsa yad'ago dan ganin wanene?

Atake ya hade rai sakamakon kamal dayagani,atsawace yace get out of my office .

Da sauri kamal yaduka harda yan kwallansa ya hauba sir Aliyu hakuri dan gani yake kamar zai sake suburbud'arsa.

Kallonsa sir Aliyu yyi bbu yabo bbu fallasa,yace meke tafe dakai?

Da sauri kamal yace pls katai makeni kayafemun da abinda na muku kaida kanwarka dan girman Allah badanniba.

Kallonsa sir Aliyu yyi yaga eh da alama yashiryu.

Nan yace bbu komai zaka iya tafiya Allah ya yafemana baki daya,nan kamal yyi masa godiya ya fita.
______________
Zakiyya ce tsaye bakin titi tun dazu ta ke jiran driver yaxo yamayar da ita gida ,tunda yakawota gun saloon tace bayan 50 minit yadawo amma shiru,kasancewar bbu waya gunta Balle ta kira dan tunda abbansu yasa sir Aliyu yadaketa,yakarb'e mata waya da mota itada Mubarak, yahana ta zuwa ko ina saidai inta kama driver yakaita.

"Har gyale da saka k'ananun kaya,duk yahanata saima yasakata islamiya,cikin ikon Allah tafara shiryuwa dan yanzun haka ma hijab ce ajikinta.

Kamal dake driving hankali kwance dan yaji Dadi da sir Aliyu ya yafemasa.har ya wuce yadawo sbd wata yarinya dayagani atake yaji tamasa."

"Ahankali yyi parking yafito yanufeta."

Zakiyya dake tsaye taji anyi mata sallama, juyowa tayi dan ganin waye?har cikin ranta kamal yamata amma afili sai ta wani d'aure fuska ta ce mlm lfy ?

Kallonta yyi yace dan Allah inbazaki damuba muje narage miki hanya.

Kauda kanta tayi tace nagode ,yanzun driver zaizo ya mayar dani gd ,murmushi yyi yace muje ki zauna baya sai in zauna gaba kinga nazama driver dinki ko? Yafad'a had'e da wani langabe kai.

Atake kamal yabata dariya nan ta bisa ,yabud'e mata gaba ta shiga yaja motar,nandai suka daidaita Kansu.

Bayan kwana2

Mlm aminu ne zaune da Hafsat suna fira ad'akinsa.kallonta yyi yace Hafsat!tace na'am .

"" ahankali baba yace ina Neman wa ta alfarma agunki !da sauri Hafsat ta zaro ido tace nikuma baba tana nuna kanta?yace kwarai kuwa.da sauri tace bbu alfarma atsakanunmu saidai kabani umarni kawai nikuma Nayi biyayya. murmushi baba yyi hade da saka mata albarka yace komene nabaki umarni zakiyimun?da sauri tace eh ko menene.baba yace Alhmdllh, abinda zanbaki umarni saikin gama makaranta ne ,kin amince ko nafad'amiki yanzun ko sai lokacin?kallonsa Hafsat ta yi tace komenene babana ashirye nake da Nayi maka biyayya.

"Cikin jin Dadi baba yace to shikenan."

Bayan kwana3
Duk binciken da baba zaiyi gameda alh Suleiman da zuri'arshi yyi kuma yadace,wato alh sulaiman da d'ansa sunkai yadda kowanne mutum nagari zaiso had'a xuri 'adasu.

Bbu bata lokaci baba yakirashi yace ya amince .

Nan senator yaji Dadi sosai, tareda cewa zasu zo gobe nemawa sir Aliyu auren Hafsat.

Haka kuwa akayi senator yaturo magabatan sir Aliyu, kuma baba yabada aurenta ga reshi,sannan ansaka auren dasunyi SSCE da sati4 za'ayi bikin.

Baba yyi shiru be fadawa laureba itada Hafsat yabari sai lokacin yyi.

6angaren senator ma hakan take besanar da sir Aliyu ba yabari sai Hafsat ta yi SSCE tukum sai ya sanardashi tukum.

Yau Yakama Friday duk yau sir Aliyu yatashi da kewar Hafsat,ana tashi dg masjid yawuce yyi mata shopping sannan ya nufo anguwarsu.

Bayan yyi parking agaban gdn su yafito,akuma lokacin baba zai fita dg gidan,sir Aliyu da sauri yarusuna yana gaidashi cikin sakin fuska.

Baba yace Muje ciki aliyu,murmushi yyi yabi bayan baba...

Share pls
[12/30, 6:25 PM] Ikhty Hafsat: NIDA D'ALIBATA
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

Story & written by mmn fareesa

Ina godiya ga dukkan masoyana aduk inda kuke kuyi hakuri masu yimun magana ta PC ko ta grps bana reply muna hidimane wlh ina gani kuma inajin dadi,wannan page din nayisane sbd farin cikin Ku.love u all anamugun tare๐Ÿค๐Ÿค.

๐Ÿ…ฟ81&82

Suna shiga suka had'u da Hafsat asoro da bucket a hannunta zata debowa Laure ruwa.kasancewar Laure taga lokacin da baba yafita,tadau ka bazai dawoba yanzun shine tasaka Hafsat adole ta debomata ruwa.

"Babane ya kalleta yace ina zaki da bucket?"

"Cikin jin kunyar sir Aliyu tace inna zan dibar wa ruwa." Afusace baba yace wuce ki mayar Naha na,sum sum Hafsat ta wuce ciki.
"Baba ya kalli sir Aliyu yace Aliyu ya mutanan gidan?sir aliyu dke jin haushin anmayar masa da Hafsat dinsa baiwa,yace suna nan lfy."

Baba yace masha Allah Dede nan Hafsat ta dawo da tabarma ta shimfidawa sir Aliyu.
"Baba yakallesu yace Nina wuce", Aliyu kagaida gida sir Aliyu yace to baba,nan yafita."
Hafsat kuwa kanta na duk'e akasa batace komaiba.

"Ahankali sir Aliyu yace waini laifin menayi ne da baza'amun maganaba?"

Kuma kinki ki kalleni,agayamun sai inbada hakuri.

"""" d'agowa tayi bata kallesaba tace, ah ah babu komai ai baka laifi aguna.ajiy ar zuciya yyi yace to kalleni mana,dan tura baki tayi tace ni kunya nikeji,dan tunda yaganta da bucket sai taji ba dadi bataso hakan ba.tashi yyi tsaye yace to ni na tafi tunda bazaki kalleniba,da sauri ta d'ago dan cewa kada yatafi caraf suka had'a ido da shi,wani killer smile yasakarmata,da sauri tasa hannayenta ta rufe fuskarta tana dariya k'uri yyi mata yana kallonta ,dg bisani yace to ni dai yau kuma ake jima kunya ko?batare da ta kallesaba tace kayi hkuri bansan meyasa nake jin kunyarkaba.""";;

Kafin sir Aliyu yace wani abu har sunga wata k'atuwar mage ta shigo soron ,shamsu yabiyota dan yasan Hafsat na mugun tsoronta.ai tana ganinta tayi wani uban ihu da gudu tanemi hanyar guduwa duk ta rude shikuwa sir Aliyu mamaki yake wai sbd magen ko me Hafsat keyin wannan ihun?be auneba tafad'a jikin sa du mammiyya,cikin tashin hankali yad'agota yaga bata numfashi da sauri ya kwantar da ita kan tabarma ya nufi cikin gidan.

Shikuwa shamsu da yakoro mage ,ganin Hafsat ta suma yasa yyita dariya hade da Jan magen sukayi cikin gidan.

Sir Aliyu yana shiga ko sallama bbu yawuce gun da ake aje ruwa ya debo ze fito kenan Laure ta fito a toilet, tawani kurma uban ihu hade da cewa kwart....maganarce ta mak'alemata sabida mugun kallon tsanar da sir Aliyu yajefeta dashi hade da Jan doguwar tsuka yabar gidan.

Ai Laure saitayi tsit dan tun sadda sir Aliyu yadaki deeni Laure ke shayinsa.

Yana zuwa soron yadinga yarfa mata ruwan afuska ,can ta tasaki wata nauyayyar ajiyar zuciya, tareda cewa yaya Aliyu dan Allah kada ka bari mage ta kamani tsoronta ni...rike mata hannu yyi yana girgizawa ssita bude idon ta,atake tadawo hayyacinta ta janye hannunta.

Kallonta yyi fuska cike da damuwa yace Hafsat dina haka kike tsoron mage dama?wane yarone yashigo da magen,?

Cikin marairai cewa tace pls yaya k'anina ne ,kada kayi masa komai kaji dan Allah.

Kafeta yyi da idanunsa yace kina nufin sumar min dake da yyi zaitashi a iska bazai yuyuba....

Kafin tace wani abu deeni yashigo soron,aiji yayi kamar yakoma sakamakon arba da yyi da sir Aliyu, amma da sauri deeni yaduk'a jade da cewa mai gida barka da rana.

Wani mugun kallo sir ya aika masa had'e da jin kishinsa yataso masa Wanda besan kishi bane atunaninsa tsanar deeni yyi.

Cikin bada order sir Aliyu yace dg yau kada kasake shigowa nan gidan,kaji ko baka jiba ?ya fad'a atsawace .

"Cikin ladabi deeni yace to bazan karya dokarkaba."

"Sum sum deeni yafice dg gidan."

Sir Aliyu ne yakalli Hafsat cikin tausayinta had'e da rarrashi yace muje kirakani mota ,ba musu ta tashi suka fito har bakin motarsa.
Gidan baya yabud'e yamiko mata tsarabarta, bbu musu ta karba had'e da godiya,bude gidan driver yayi zai shiga.

"Ahankali tace yaya!!!"

Kallonta yyi tasakarmasa murmushi ,shima yyi mata ,yace ki kulamun da kanki kinji tawan?

Murmushi tayi batace komaiba.

"Kallonta yyi yace koba tawan bace?"

Da sauri tace takace mana ,lumshe idanunsa yyi ya shige motar,itakuma tana masa addua.

***************
6angaren su Mubarak kuwa shima ba laifi ya shiryu dan saida abbansu yadage da tsayuwar dare Kansu.Allah majik'an bawansa yakarb'i addu ar sa.ita kuwa mommy n su kyaleta yyi yafita harkarta duk abun yadameta,ta yi masa mgana miyasayashareta?sai yace aure zai k'ara!aiduk saita rud'e,kasancewar yasan bata son kishiya.ai da kuka taje gun daddy wato senator takai k'ararsa nan senator yatarasu yyi musu nasiha,sannan duk tabada hkuri ta karbi laifinta tareda alk'arin zata gyara.shikuma abbansu Zakiyya ya janye maganar kara aure.

Ayaune mummunan kabari yazowa Fatima cewa 'al,ameen yarasu sakamakon accident, Fatima ta shiga tashin hankali tayi kuka kamar ranta zai fita.itama Hafsat kawa ba abarta abayaba dan itama ta damu da hakadai har Fatima ta dangana tacigaba da yimasa addu a.

Kwanci tashi bbu wuya gun uban giji su Hafsat har sun koma skul sun cigaba da karatunsu ,sir aliyu nacigaba da kula da ita.

BAYAN WATA6
Hafsat ce da sir Aliyu cikin mota guda sir Aliyu yana driving farinciki fal a fuskarsa.hakama Hafsat kasancewar yau suka kammala SSCE itada Fatima,ga kyaututtukan data samu abayan motar kasan cewarta gifted.shikuwa sir Aliyu yace shizai daukota, dukda taso tabi Fatima su shigo mota1,fatimarce tace taje ta bisa.

Shiru Hafsat ta yi axuciyarta kuwa kishine fal aranta sbd sunbar skul kuma zai cigaba da koyawa student tanajin haushin ayita kallensa ko ace ana sonsa. dan yanzun ta gane tana sonsa,kuma tayi alk'arin bazata tab'a nuna masa ba ko fad'a masa saidai inshi yanuna hakan.

Sir Aliyu ne yalura da yanayinta,murya k'asa k'asa yace ,Hafsat dina menene naga kamar kina cikin damuwa pls kigayamun kinsan bansan ganinki cikin damuwa?

Sunkuyadda da kanta tayi tace babu komai.

Hade rai yyi yace shikenan,tunda kinfison nima na zauna a damuwa,tunda kema kina cikinta.

Ganin yyi zuciya yasa ,tadan kauda kai ,murya na rawa kamar zatayi kuka tace,bakai bane ,zaka cigaba da koyawaba a skul din mu damuka bari,nikuma banason kana koyarwar.

Murmushi yyi jin shirmenta dan shi a shirme yadauki maganar,batare da yakalleta ba yace to naji tawan ai abinda kikeso shinike so ,kinfi so nadena koyarwar?

"Da sauri tace eh."

Yace to shikenan nida skul din Ku har abada da sunan koyarwa.

"Shikenan bbu wata damuwa yafad'a tareda yin parking kasancewar sunxo gida."

Wani farin ciki Hafsat ta ji jin kalaman sa.

"Ahankali tace bbu wata damuwa yayanah,amma nima meke bakaso kaga Nayi?"

Da sauri yace baniso ki kula ko wanne saurayi ,dan skul zaki cigaba kinajina?

Cikin murna tace to Yayana nagode sosae.

Nan ta fito ,yafito mata da kayanta Duka duk kyaututtukan data samu suka shige gidansu ,asoro suka had'u da baba,nan suka gaisa baba nata masa godiya da sakamasa albarka.

Nan Hafsat ta yi ciki da kayan,tadawo ta dau sauran ta koma ,baba kuwa yaraka sir Aliyu har mota,sannan yadawo gd.

Shikuwa sir Aliyu driving yake zuciyarsa cike da kewar Hafsat dinsa wani gefe kuma na xuciyarsa na fargabar maganar da daddy sa yace zaiyi dashi ,inyadawo daga Egypt dan yace mihimmiya ce,kuma k'ila gobe daddy nsa zai dawo.

Haka yyita tunani har ya isa gida yyi parking yafito ya nufi ciki....

Share plsNIDA D'ALIBATA

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

Story &written by mmn fareesa

๐Ÿ…ฟ83&84

Yana shiga, awaiting parlour yasami su sa'ada da mommy, nan ya zauna sukayita fira da bisani ya wuce part dinsa.

"Washe gari da misalin karfe 2:00pm daddy yadawo dg Egypt."

Bayan ya huta yaci abinci ,suna zaune shida mommy suna fira canyakalleta yace inaso muyi wata magana dke?mommy tace to alh inajinka.nan daddy yakoromata bayani akan auren da zaiyiwa sir Aliyu, dakuma cewa yau zai sanar dashi.ajiyar zuciya mommy ta yi cikin fad'uwar gaba tace amma shine alh har aka kai wannan lokacin baka fadaba.kumafa yaronnan yanada wadda yakeso.tsaki senator yaja yace kinsan bansan yawan Jan magana ko?nariga na yanke hukunci ,in yanada wadda yakeso meyasa be kawotaba?inma yanada ita to ya aureta dg baya amma nagama ,magana banason jin komai,kawai kiyi masa addua.shiru mommy ta yi ganin daddy zai dauki abin da zafi saitace Allah yazaba abinda yafi alkhairi. Amma a zuciyar ta tana tausayin sir Aliyu da Hafsat, dan talura suna son junansu.daddy ne yakatse mata tunani da cewa inyadawo kituromin shi nayimasa bayani.to mommy ta ce tafita.

****************

Babane zaune da Hafsat suna fira,adakinsa,can baba yakira sunanta har sau ukku tana amsawa ,sannan yyi gyaran murya, had'e da cewa kinsan abaya kinmun alk'awari kome nasakaki zakimun biyayya ko?jiki a sanyaye tace eh baba yace madallah.

"Nan baba yakora ma Hafsat bayanin nanda 4weeks za'ayi aurenta."

Cikin fad'uwar gaba tareda rawar jiki,had'e da tsoro Hafsat ta zaro idanu tace aure baba?

"Baba yace eh ,ko kinmanta kinmun alk'awari ko me na umarceki zakiyi biyayya."

Cikin dauriya hade da karanta inna lillahi wa inna lillahi raju un, tace to baba Allah yasa hakanne alkhairi.

"Ahankali yace ameen had'e da sakamata albarka."

Tashi yyi yace natafi masjid, bejira amsarta ba yafita,kamar jira take ta fad'a kan katifarta tasaki kuka me cin rai,afili tace yanzun yaya Aliyu wani zai rabani dakai bazan samekaba,dan Allah kazo kaceceni kabawa baba hkuri.

Haka tayita surutai da kuka har idanunta suka kumbura sbd kuka dg nan bacci yyi gaba da ita.

Bangaren sir Aliyu kuwa,bayan yadawo mommy ta ce yaje gun daddy yana son magana da shi.

Bayan yaci abinci, yanufi part dinya shiga.bayansun gaisa daddy yyi gyaran murya,yace da farko Allah yyimaka albarka ina alfahari dakai a y'ayaana sbd kanamun biyayya.

"Atake yaji fad'uwar gaba."

Daddy yacigaba da cewa, hakan yasa na yi bugun gaba dakai dan nasan bazaka watsamin kasa a idoba.

Nan daddy yazaiyane masa maganar aurensa nanda da4weeks.

Ai ji sir Aliyu yyi tamkar andasasa agun ga wani sarawa da kansa keyi kamar anbuga masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login