Showing 54001 words to 57000 words out of 70940 words

Chapter 19 - DOCTOR EESHA complete by J Hajara

J Hajara   

14 Jul 2024

7233

ma yakeyi.

Kuma kasan hali indiyawana Basu da yarda" ta Kara ja murfi motar ta rufe..

Driver yace" yallabai kayi hakuri, sha'ani hanyoyi kenan a Delhi na sai hakuri"

Suhaima taja tsaki tana tsuke fuskar don haushi tafiyar takeji , tafiyar yazomata a bazata bahakatasoba dun Bata shiryaba. ... Aliyu har suka bar layi bai bar kallo su Essha ba, yaso ace ya sauka kodan yagasu, baisan maiyasa ganisu yasashi ji faduwar gaba ba.

Bada jimawaba suka isa haraba asibiti , babba tarba aka musu zuwa office din babba Doctor, su samu tarba cike da girmamawa, Essha kadai ake jira , bakita su karaso, sukira layi kanta duka baya shiga, babba Doctor yaba su hakuri na Rashi zuwa Doctor da zuka zo wurinta, yace shi zai dubasu"
Aliyu ya amsa badamuwa " Babba doctor ya dubasu da kanshi, su Sha gwanje gwanje, suhaima hankalita duk a Tashe yake, tsora ya cika ranta fal, kamar zatayi kuka dun tasa asiri ta ya kusa tonuwa, tarasa sukuni kanta har wani zufa takeyi duk ssnyi Ac daya cika office din, baya likita yagama gwanje gwanje shi yace musu suyi hakuri su dawo gobe , dun karba results duk abunda yanuna zasuyi kokari sumusu aiki akai.

Suhaima taji haka taji wani sanyi aranta, ta shaida ma kanta cewa sai tayi abun da zai sa bara su dawo asibiti na ba gobe, dun dagani likita ya mata kwarjini bai da wasa gashi ya Soma tsufa , suka mike zasu fita kenan, Pooja tashigo rike da files a hannuta, tana gani Aliyu ta ware Ido mamaki da tsoro yasata zubar da files a kasa Hannu ta na Bari, dun mamaki ma kasam magana tayi.

Aliyu yatsaya Yana kallo ikon Allah yanda ta sare musu hanya ta Kuma kafeshi da Ido, baidamu ba don mata dayawa su Saba mishi haka, suhaima ta ja hannushi cike da kishi ta buge Pooja suka fice.

Pooja kuwa kamar ankafata kasan motsi tayi tana kallosu suka fice, suna fita da daddewa ta dawo hayacita tabin bayasu da sauri, Kash Bata ci musu ba, koina ta duba na asibiti Basu , ta tsaya shiru ta kasa gasgata abunda tagani, Mai Kama da Sadik sak, bambaci kawai daya ne shi Wana Babba ne, sadik Kuma yaro ne, ai da sauri ta juya ta koma office din babba Doctor da ya dubasu ta Tara shima bashi har ya fice, ta bugi table, ta kalli gefe daya tana tunani" Aya Wana danagani ba maihafi sadik bane, Kai ima ba papishi bane su hada dangi, Kai let me call doctor" ta ciro waya a pocket din labcoat ta , ta dialing number Essha Yana ta ringing ba'a dauka ba tace" oops na tuna yau birthday din sadik" ta fice da sauri har Tana tuntube ta isa guri motar tajashi zuwa gida, kafi taisa go slow ya tare, kamar ace ta daga Kai ta hango Aliyu ciki motar, Pooja ba hali taje gurisu, dun har suyi u_turn zuwa daya titi, Saba rudewa ta fitar da Kai Tana ta kwala mishi da Suna Sadik , sai binta ake da kallo, Aliyu kam ko harka gabashi yakeyi baimasan tana yi ba saboda akwai da tazara a tsakani su.

Tana kallo motarsu Aliyu ya tashi za subar wuri, da sauri ta bude murfi motar zata fito, watar motar ta Kara Parker a gefeta, ba hali fitar tana kallo motarsu Aliyu ya wuce..Pooja kamar tayi kuka tsabar takaici , hanya su na budewa da sauri tayi u_turn tabi baya su, haryanzu ba sa'a dun Bata cimasuba, jiki a sanyaye taja motar ta zuwa gida...........








❤️Love you guys ❤️


More comment more typing ❤️❤️🙏🙏


👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

WRITING BY
J Hajara


🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M.W.A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta. 🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________


5️⃣6️⃣&5️⃣7️⃣



Pooja na parking ta fito, ta shiga ciki jiki a sanyaye, ciki gida ta tarar da yara da manya. a decorating gida da ballons gabadaya, ta nufi parlor, takara gani wani decorations da ya rudata
Ya yi kyau batasan sanda ta furta wow ba, gaskiya decoration din birthday din ya mata kyau, har wani babba balloon aka sa a sama tsakiyar parlor, Center kuwa table da ke dauke da babba cake na favorite cartoon show na Sadik wato PJ Masks, wow cake din PJ masks ya hadu, Ash color ne jiki cake din, left side din kuwa owlette ne, middle Kuma cat boy , right Kuma gekko,( Don't mind me ooo😆 duka sunayana actors din PJ masks ne, Kar kurikece😁).

Tsakiyar cake din kuwa 7 ne Mai dauke da candle a ciki( Kai gaskiya Mai cake din ta kware) .
Pooja ta share hawaye tana ta shafa cake din a hankali tace" Sadik mummyka na matukar sonka, tana tsoro abunda zai rabaku ne kawai, but very soon nasa komai zai zo mata da sauki" ta Kara bin parlor da kallo decoration din ya gama haduwa, harda number ballon Mai dauke da seven da aka kafashi a tsakiyar aluminum balloons dake gefe parlor, gefe guda Kuma Happy Birthday Sadik akasa da flowers na zangaye da rubutu, ga white bulbs da akasa a gida gabadaya sai ya bada wani yanayi Mai annashiwa, Kai guri birthday yagama haduwa, Pooja ta nemi guri ta zauna tana bin yara da ke ta wasa su da kallo, can Arundh ta shigo da guduta ta Sha wanka tayi kyau gashi kana yasha gyara, Pooja ta kirata tana tambayarta Ina su sadik? Ta Bata amsa da cewa taje Airport dauka brother nata"

Da Hindi tace" mummy surprise birthday ne fa aka hada ma sadik, mummy guri ya mi kyau"

Pooja tayi murmushi tace" nasani saura kifada Mai da baki ki na surutu na"

Arudh ta rufe baki tana dariya...



👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

Essha ne ke tuki a hankali harta iso Airports din, tana fitowa sai waige waige take tana neman Amir, can ta hangoshi zaune ya makala earpience a kunne, sai danne waya yake hankalishi a kwance, Batama ganeshi ba, sanda ta Kara murza Ido da kyau, Amir yazama wani handsome guy, da sauri ta karasa wajashi ta bashi bugu Wasa a kafada tana murmushi. Amir naji a tabashi ya Mike a zabure, Yana ganita yafara zuba murmushi cike da tsokana yace" kaga manya ba, Doctor Essha, sis kiga yanda kikara kyau, wow sis bamaraki da indiyawa ma"

Taja mishi kunne tana murmushi tace" haryanzu baka canza bako, tsokanar na"

Yayi murmushi yace"sis Ina fa zan canza, gaskiya sis we really miss you, daddy yace nafada Miki gobe, gobe na ba sai jibi ba, ki koma gida, kiga zamu koma tare kenan"

Essha daji haka jikita yayi sanyi, ba haka tasoba, ama dole tabin umarni Daddy, tafison ako yaushe ta riga farata mishi..

Amir ya katse mata zance zuci ta da " where is my son? Yau ne birthday shi ko?

Tayi murmushi ta kada Kai ..

Yace" toh Ina yake?

" Kai amir sauri Mai kake, yana gida nannyshi tana shiryashi,muje na daukoshi "

Yayi murmushi yace" to muje sis ko Doctor zance"

Bata bashi amsa ba tayi gaba da jakashi Yana biye da'ita , suna isa baki motar ta kunna motar ta bude ta bude ma Amir ya shiga , itama ta shiga, suna Bari Airports sai gida ummulkulsum nanny sadik, suna zuwa suka tarar sai fitina yake mata, yayi kyau jiki shi sanye da black jeans trouser da jeans jacket itama baki, gashi kana yasha gyara, he looks cute. Yasa nannyshi a gaba Wai sai ta hada mishi Khirr( sweet ne da indiyawa ke hadishi da shinkafa da sugar) ya damaita lallai shi Khirr yakeson ci.

Tace" toh Sadik bara na hada ma"

Basu ma lura da shigowar su Essha ba, sanda takara doka wani sallama , nanny tayi sauri amsawa tana murmushi ta musu barka da zuwa tayi hanya kitchen.
Sadik na daga Kai yaga Uncle Amir tsaye Yana mishi murmushi da gudu yaje ya rugumeshi, Amir ya tsaya yana kalloshi girma yaro yabashi mamaki, Essha gani kallo da amir yake ma Sadik ne yasa ta zargu duk ta rikece a tunanita, yagane wani Abu ne , da sauri ta yi gyara murya kamar Mara gaskiya da turanci Tace

" Sadik yau ga uncle Amir"

Sadik ya Mike daga jiki uncle shi yakali fuskar shi ya na Mai murmushi yace" Namaste uncle"

Amir bai amsaba sai bin sadik yake da kallo, yaro ya burgeshi, Kuma yashiga ranshi sosai. Sadik gani bai amsaba bane sai yasa hannu ya waving a fuskar Amir.


Amir ya dagoshi Yana murmushi yace" my boy yakake?

Sadik bin baki Amir uncle nashi kawai yake da kallo yanda yaga ya furta yakake , shi dai yaji my boy ama yakake dine bai ganeba..


Amir ya Bata fuskar ya kalli Essha yace" badai haryanzu Sadik baiji hausa ba?

Ta gyada mishi Kai.

Yace" lallai sis ke da daddy ne, gobe akwai drama, sis ki duba fa , ko yakake din ma baisani ba, wlh muna da ja aiki.

Shifa fa yaro fa, da yare da yatashi dashi nefa yake rikewa har girma, yanzu inmukoma Nigeria, misali ya shiga mix din yara da basaji turanci balle asa wani yare Hindi, kiga Sam basai ji dadi har ya sakeba, gobe Allah yakaimu, Zaki hadu da Daddy, ni baruwana, Allah yasoki ma zaiyi tafiya yau, sai Sunday zai dawo. kila ma boy ko gaisuwa baiya da hausa ba"

Ya dubi Sadik yace" hey greet me with Your mum's language"

Sadik sai Ina Ina yake yanason ya tuna gaisuwa da mummyshi ta koyamai da hausa ama yakasa sai "En... En " yake tacewa har ya ba Amir dariya..

Amir ya rugumeshi Yana dariya yace" Don't worry boy, nasan ba laifika bane, is ur mum's fault, da Bata koya maba, Kar kadamu Autar mummy da grandpa zasu koyama, Dani zankoma school, mummy ka Kuma. Tasan ma ranta fada sai Tasha shi guri daddy , dun wanan rubutace"

Essha ta baka Mai harara ta nemi guri ta zauna..

Yayi murmushi yace" oho dai ni dai bazan dukuba"

Essha tayi dariya tace" Allah Amir ka rainani"

Yace" Allah sis acire maganar wasa fada zakishs aguri Daddy, balle yanzu da muka koma uke gabadaya ba kamar lafia bane, zai Dan Sha wuya kafi yasamu friends dun kisa baya ji yaresu Suma basa ji nashi, kiga ko shine da Sha wuya, Anya ma yasa wasu abubuwa aka kasashi kuwa?

Tace" gashi gaban ka tambeyeshi"

Yace" okay tom, boy bara nafara ma Dana India, what is the name of your prime minister ? Nasan Wana zaka sani"

Sadik yayi murmushi yace" *NARENDRA MODI*"

"Toh Who is the current president of Nigeria? Amir ya sake jefo Mai wani tambayar

Sadik ya sake saki wani murmushi Yana su sa Kai can yace" *President *MOhammadou Bu'aali* "


Daga Essha har Amir duk suka fashe Mai da dariya, sadik ya Tsaya shiru Yana ya tabe fuskar Kamar zaiyi kuka, gani haka Amir ya dakata ya rugumeshi yace" No boy don't cry, u tried, that's the correct answer"

Sadik yadago yace" really?

Amir yabashi amsa da "yes boy"


Sadik yace" then why are you laughing? Ya fada kamar zaiyi kuka. ....


Amir yace" am laughing at your pronouciation, it's Muhammadu Buhari, not Mohammadou Bu'aali, give me five "

Yayi murmushi ya Mika mishi hannu suka tafa...

Amir yasa hannu a dimple na Sadik yace" sis Allah boy Kama yake min da wani, kamarsu ma har ta baci "

Essha daji haka ta Mike da sauri a tsorace murya na rawa tace" Amir jiramu ake, abun na hada ma sadik baso yasani, tashi muje sauri nake" tayi haka ne da ta kawar da zance, kafi su Mike ma hartayi waje, jikita har Yana Bari, Amir zaiya tsareta da tamboyoyi tasashi Sarai.

Tanaji murya sadik na sallama nannyshi, Yana mata godiya Khirr da ta hadamai, tana kallosu suka fito Amir rike da hannushi, daya hannu kuwa food flask ne ya rike na Khirr da nannyshi ta zuba Mai.

Suna shiga ta tada motar sai gida, Tana Gama parking sadik ya bude ya sauka da saurishi Yana kwala ma Arudhati Kira tazo taga uncle Amir.

Essha da sauri itama ta sauka tabin bayashi tace" wait Kar kashiga Ina zuwa"

Taja Amir suka shiga ciki tabarshi a tsaye, suna shiga suka tarar da yara da manya acika sosai harda colleague nata naguri aiki, yara dukasu sanye suke da birthday cap na pj masks, Pooja ta karaso tace" Ina sadik Dr?

Essha tace" surprise party ne basan yasani"

Pooja tayi murmushi tasa aka kashe wuta guri gabadaya, guri sai yayi dulum Kamar bakowa, sai Kara Ac kawai kakeji.

Essha ta fito ta samaishi a zaune Khirr dishi yake ci hankali kwance Yana ganita yamike yace" mum Kai huwa?

Bata bashi amsaba tayi murmushi tace" shigo" ta koma ciki da sauri...

Sadik ya shigo a hankali gani yadda guri yayi duhu bagani komai yasoma Kira suna mummyshi bai ji ta amsaba ya Soma tafiya Yana Kai tsakiyar parlor aka Kuna haske, ballon dake tsakiyar parlor yabada Kara shining glitters✨✨🎉🎉suka fara Mai poping a jiki, Nan aka fara singing mishi happy birthday , Sadik yakasa motsi ya bude baki cike da mamaki da annushuwa, he was surprised, ya bin parlor da kallo Yana murmushi idoshi ya sauka aka cake, ihu murna yasa, ya daka tsale ganishi kawai nayi a gaba cake din, camares sai daukoshi hoto ake, saban mamaki ma kasa magana yayi, da gudu ya rugume Essha ya rakwafar da ita yabata peck a goshi Yana hawaye yace" *mujhe **tumse Pyaar hai mum* "(I love you mum) thanks mum, thank you thank you, Pj masks are my favorite" ya Kara rugemeta.

Yan guri video suke musu sbd subasu sha'awa, Pooja ta janyeshi tace" common boy come and cut your cake" ta dagashi ya rike hannu Essha Dana Amir suka karasa gaban cake din, sadik yakasa rufe baki saban murna.
Pooja ta dauki lighter ta kunna wuta candle na guri yasake canzawa sai glowing yake, kowa na murna yanayi guri, waensu na tafi wasu Kuma na hotuna, birthday boy nananda ya murtuke fuskar, Idona yayi rau rau kamar zaiyi kuka, narasa dalili canzawarshi, guri kuwa bawanda ya lura dashi.

Murya Pooja naji tanacewa" Boy say ur wish and blow your candle"

Kowa aka natsu kallo yakoma kan sadik daya shiru duk yanayishi ya canza.

Pooja ta matso gefe Essha tace" Dr maiyasameshi?

Essha ta kalleshi shiru duk jikita yayi sanyi tace" Nima bansaniba"

Amir yace" sis ko ki mishi wani abune kafi kunshigo?

"Aa amir kana kallo fa ya shigo na da fara'a shi farat daya kawai yacanza ni ba'a abunda namai"

Amir yaiso gaba Sadik ya tsuguna yarike Mai kumatu yasoma Mai magana da turanci yace" common boy, yaufa Ranar ka ne , Yar Ranar murna ne a gareka , duk na a taru ne saboda Kai, Kar ka canza mana maza, ga mummy ma gan anty Pooja ga Arundh"ya pointing Arudhati dake rike da water gun...

"Kaji boy give me that ur smile"

Sadik ya da saki fuska kadan ama kwaya idonshi kwalla ne cike dam kiris suke jira su zuba..


Amir yamike ya kaishi gaban cake din yace" common boy say ur wish and blow ur candles"

Sadik yadaga Kai yakalli mummy shi Nan take hawaye suka zubo, da sauri ya share karta gani, idonshi a kanta yakai baki zai hura.


Arudhati takaraso ta tareshi tace"wait sadik, u didn't say ur wish, say it before blowing the candle"

Sadik yayi shiru na waesu minti na, ya sauke wani nanauya ajiya zuciya yasoma furta wish nashi, a hankali yake furtawa yace" *I wish to see my Dad*" Anashi zato a ranshi yake fada, baisan ya fito fili ba. Haryana sauke ajiya zuciya.......






.



Da Allah ku manage ba time muna busy shiyasa 🙇🙇🙇




More comment more typing ❤️❤️


♥️Love you guys ♥️



👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

WRITING BY
J Hajara


🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

M.W.A


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer= whatsa
_________________________


5️⃣8️⃣&5️⃣9️⃣



Sadik nagama fada haka Yan guri sai duk jikisu yayi sanyi, su tausaya Mai, anasu tunani mahaifi shi mutuwa yayi, Essha binshi kawai take da kallo har idonta ya Tara kwala tarasa baki magana.

Wata arniya daga ciki colleague na Essha ta karaso gefe Sadik ta dafashi fuskar tausayi tace" Don't worry son, you will meet your Dad in heaven, am very sure he is here with you, Jesus Christ has bring him down to celebrate your birthday with you, now blow ur candle"

Sadik bai tanka mata ba yajaye hannu ta yakarasa gaba Essha da harta fara hawaye, ya rike hannuta yace" mummy stop crying, let's go and blow the candle together"

Essha ta kalli Pooja , Ta kada Kai ta mata thumps up tace" You deserve it Doctor, Do it"

Essha ta murmusa a hankali ta sukunyar da kai, suka hura atare one blow ya mutu, Nan aka sa tafi. Sadik ya yaka cake yayi kamar zai sama ma Essha a baki har ta bude baki kawai gani nayi ya dangwala mata a goshi da kumatu ta, duk aka sa dariya, yakara yaka yasa ma Essha, Amir da pooja.

Essha takai hannu kamar zata yanka cake din, Bata yanka ba, tasa yatsa ta lakuta cream din cake din ta shafa Mai a fuska, duk suka fashe da dariya, Essha ta kada Mai hannu a fuskar tana murmushi Alama ta Rama, sai daukasu akeyi domin su burge. Amir har Kira su mummy yayi Video call Bata kusa khairat da mufeedat ne suka dauka,wow su zama yanmata, Suma suka wishing Sadik happy birthday, mufeedat harda guntu kukata na Rashi zuwa da Amir bai je daitaba, su jima sosai kamar karsu rabu, sanda Amir ya shaida musu cewa gobe zasu dawo sanan sukaji sanyi suka kashe.

Aci asha a watse a taro birthday lafiya, Gifts kala kala Sadik yashasu, gifts boxes su cika room nashi dam(hhhh yaro dun ba daddy ka kenan😉)




*************************

Aliyu tunda suka koma lodge nasu yakasa sukuni, yarasa Mai ke Mai dadi, yasan ba results din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login