Showing 36001 words to 39000 words out of 70940 words

Chapter 13 - DOCTOR EESHA complete by J Hajara

J Hajara   

14 Jul 2024

7228

gatse tace" Mai nayi kuma?

Hajiya binta tace" baby na dawo, driver na ta horn babu Wanda yazo ya bude gate, sai jamilu driver yazo ya bude, Mai ki ma baba maigadi?

Tace" mummy na koreshi , Kuma basan kikara cewa komai akai, kawai ni munkarasa ki gayamin abunda yakamata naji" ta fda cike da Rashi kunya...

Hajiya binta ko ya yadamaita tayi murmushi tace" toh baby na, naji Allah ya huce zuciyarki, muje"

Suna isowa dki feenat da suhaima suka zauna a baki gado, hajiya binta ta nufi mirror tasa hannu ta cire sarka gold din dake wuyata.

Suhaima tace" mummy ke fa mukeji ra"

Tace" Kai baby matsala dakai Rashi hakuri" ta dauki baki handbag nata baki ta zazage musu agbsu da wani gora cike yake da madara shanu, suhaima sai bin kaya take da kallo tana yamutsa fuska..

Feenat tace" mummy what is dis ? Ta nuna Kaya

Hajiya binta tayi dariya , ta dauki kuli dayayi kamar tozali tana juyashi a hannuta tayi wani shu'ummi murmushi tace" wanan sunashi MANTA MASOYI"

Suhaima da feenat suka hada baki " MANTA MASOYI Kuma?

Hajiya binta ta sake saki wani shu'ummi murmushi tace" tabbas ku fada dai dai, sunashi kenan, ba karami kunne nakshe akn wanan magani na ba, nakashe sama da 2.5million akan wanan"

Suhaima ta karbi tozali tana kara kalloshi da kyau tace " mummy toh maiye amfani shi?

" Hhhhh, baby Wana dakike gani shi zai sa Aliyu ya Manta da masoyiyarsa, ya Kuma tsuduma ciki kogi sonki


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“š πŸ–ŠοΈ

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980946102? referrer= whatsa
_________________________


3️⃣9️⃣&4️⃣0️⃣

Hajiya binta ta sake dariya shakiyi ci tace" baby inhar kikasa wana,toh Aliyu zai Miki son da ke ma bara kima kanki ba,ita Kuma masoyiyar tashi, ko da suyi nisa a son, su Kai Layla da majnu ne, toh ya manta ta kenan na har abada, ama fa yace duk Rana da sukayi Ido biyu da masoyiyar, asiri zai washe, zai dawo hayacishi"

Suhaima ta tsume fuska zatayi magana, hajiya binta ta katse tana murmushi tace" baby nasan Mai za ki fada, ki kwantar da hankali ki, nasa boko ya kadata tayi nisa, bara su Kara haduwa ba"

Suhaima tayi ihu murna ta rugume hajiya binta tace" gaskiya mummy na ki na so na, ki ceci rayuwa na, masoyi da na ke so zai so ni, mummy ko yanzu ma zan sa na koma asibiti ya gani, wow zaga soyaya" tayi fari da Ido.

Hajiya binta tace" Kai babyna, sauri Mai kike, ai yanzu Aliyu a hannumu yake, sai yanda muka juyashi, boko yace ba yanzu Zaki Sa ba, sai Rana da aka ranar aureku zakisa, zakiga aiki da cikawa, dun na trusting boko"

Feenat tace" ama mummy ki ce sai Rana dauri aure, what if tasa wani daban yayi tozali da ita fa?

" Haba yanmata, ya Ina baku Kuna roko, wanan tozali Mai suna MANTA MASOYI saboda Aliyu kadai akayi shi, da sunashi da nata aka hada magani, ku ga kenan akan Aliyu ne kadai zaiyi aiki, ku chill mana " hajiya binta ta fada Tana kade musu Ido daya.

Suhaima tasa dariya tace" Bani mu kashe mummy na" hajiya binta ta daga hannu suka tafa taff..

" Wanan kuma" ta nuna gora tace" baby na Wana Madara da kike gani, magani ne shima, Madara ne da surki magani Zaki tatse shi da pant dinki"

Suhaima cike da mamaki tace" what!!! Mummy da pant fa kikace?

" Eh" ta Bata amsa ta cigaba" in kika tatse da pant naki, baby na da sharadi fa, pant din daki ke amfani dashi ba sabo ba, Wanda kikesawa, if possible ma ki tatse shi da Wanda ke jiki ki"

Suhaima ta Bata fuska tana bin hajiya binta da kallo tana kara yatsine fuska..
Hajiya binta Bata kulataba tacigaba" ki na tatsewa za'a sa a fridge, a preserving nashi har sai ranar aureku, baya yayi tozali da ke, toh Zaki bashi Wana madara yasha, Yana Sha, shikena ki kulle mishi zuciya da soyayarki ba wata baya ke"

Suhaima tace" mummy ba wani hanya ne daban dole ne, sai na yi amfani da pant dina? Ni dai gaskiya bazan iya ba" ta fada ta yatsine fuska kamr taga kashi..

Feenat tace" haba nawa, Wana ai karami aikinne, so ki ke ki rasa Aliyu, inhar kina sonshi dole nefa kiyi yanda boka na fa kibi Sharadi boka"


" Yawwa fada ma ta dai yariya kirki" hajiya binta ta fada Tana kada Kai.

Suhaima tayi shiru for a moment, can tace" mummy duk abunda zai sa Aliyu ya soni, zanyishi"

Hajiya binta Tace" yawa Yar gari"

Suhaima ta Soma haweye.feenat ta dafata tace maiyefaru kuma?

Ta rage murya tace" mummy jiya Jace ya kira ni, haryanzu dai akan magana zubar mishi da ciki danayi"

Hajiya binta ta fashe da wani dariya mugunta tace" Jace , Jace hhhhh Wana karami kwaro, shima tun jiya nasa boka ya mantar da shi komai inhar aka ki ne, kai yanzu haka in aka tambeyeshi waye suhaima zaice baisantaba, balle ma wani magana ciki mtchewew a zubar din"

Suhaima ta rugume hajiya binta Tace" shiyasa nake kara sonki mummy"

Hajiya binta tayi murmushi tace" Kar ki damu wanan angama dashi, Jace din banza"

(Wanene Jace, Jace Steve dan kasar amurka ne, course mate din suhaima, school ya hadasu , har suka kula soyaya Mai karfi a tsakani su, ba tsiya da ba sa aikatawa, tare ma suke kwana. Har sau uku suhaima na ciki tana zubarwa , bada sani Jace ba, ana hudu ne asiri ta ya tonu, lokaci Kuma daddy ta ya dawo da'ita kasar Russian ta karasa karatu ta, baya ta koma Russian ta ga Aliyu , ta Soma sonshi, ta Manta batun Jace, kuma lokaci da Jace yaji cewa ta taba zubar mishi ciki har four times, shine yasa ta a gaba, yace mata kotu ne zai rabasu, tsora haka ne yasa ta dawo Nigeria , dun tasa hali Jace bai da mutunci tabbas zai iya. Babba dalili da ya ta na dawowa Nigeria kenan ta buya, sai aura na da zantayi, uwar take daure mata gindi duk wani shuumaci, gashi yanzu su shafar da Jace.)

" Toh mummy ya ake tatsa? Suhaima ta tambaya.

Hajiya binta ta Mike ta dauko fari kyalle da ruwa da cup, ta nuna mata yanda zatayi..

" Yawwa mummy zan' iya" ta fada Tana murmushi , ta dauki goro Madara hajiya binta ta Mika mata wani Dan karami bowl tace" kije daki ki kiyi baby na Kar wani ya ganki, sai ki kawo min nasa a fridge, Kar kiba wata tayi Miki fa da nasaki"

Tace" okay mummy" ta fice daga daki zuwa nata, ta zuwa ta dire gora akan gado ta na yatsine yatsine fuska tace" Allah ya kiyaye na tatse Madara na da pant din dake jiki na, sabo zan duba, ko ni Ina kyakyamin jikina balle abunda hubby ne zai Sha inaa" ta nufi wardrobe ta bude, tana duba sayaya da tayi jiya, im Bata mantaba ta sayi inner wears na Gucci masu shege tsada, ta fito da sabo pant na Gucci Mai tambari din Gucci, fari Kal, dal yake, ta aje akan Dan karami table dake daki, ta dauko gora Madara da bowl ta aje ta fara tatsa tana ya mutsa fuska, ba abunda yaiya sai shirme, Tana Gama ta cilla da pant din,ta kaima hajiya binta Madara ta bude fridge tasa, harda samata albarka.

ESSHA
*************************
Anty zainab ta zuba mata abinci ta zauna agaba ta, Essha ta kaudai Kai , dai*2 doctor da nurse din dake kula da ita sun ka shigo, da magaguna da allurai. Dr Abbas tun jiya daya ma Daddy mgn bai Kara lekasu ba, kuma Yana ciki asibiti.

Juyi duniya na Essha taci abinci Taki ci komai, sanda aka Sha daga sanan ta yarda mummy ta kada mata hot tea, tana Sha tana hawaye, rabi cup Tasha tace ta koshi, doctor ya mata allura , Tasha magani, tana gama sha, daddy ta ya shigo shi da daddy karami, Yana rike da wayata a hannu ya Mika mata, ta amsa, haryanzu batabar kuka ba, tayi fayau kamar ba' itaba, tana haweye ta bude waya, missed calls din Khalid da bestie ne ba'adadi , harda hunaisat, tana kan dubawa Kira Khalid nasake shigowa bata amsaba takara feshewa da sabon kuka, jikita har Yana karkawa, har Kira ya tsinke Bata daukaba, mummy ta matso ta rugume ta tana hawaye , daki tsit kuka Essha ne kawai ke tashi.

Daddy karami yayi gyara murya yace" Essha hakuy zakiyi kibar yawa kuka na, kuka na wani ciwo zai Kara Miki, karki sama kanki damuwa, Essha ke Kuma iri Taki kadaran kenan, haka Allah ya tsara mana, nasan Allah baya taba yi abun babu dalili, duk abunda kaga Allah yayi akwai dalili dayasa shi, haka Allah baya dorawa bawashi abunda bazai iya ba, ki rugumi kadaraki da hannu bibibbiyu watara na sai labari"

Ciki sanyi da tausayawa hajiya tace" toh maganar aure da ke kanta fa, tun da ba miji kusa, Kuma ba'asan asalishi ba, balle a Nemo shi"

Daddy yace" Kar kudamu zamu tambeyi malamai akai"



Baya Kwana biyu, an sallamorta daga asibiti, dun ta da warware, Essha duk ta chanza, Bata da wani aikiyi sai kuka, gaba daya ta chanza, gashi yanzu daddy ta ko na da can ya Hana ta fita, ya chanza mata layi wayata cewa yanzu ita matar aure ce, abun na bala'in Kona mata Rai , mummy ne kullum Mai lallashi..Sam yanzu Bata da wuya kuka, mummy mamaki take a kullum , Essha ce ta dawo haka, yariya da batasan Mai ye damuwa ba, ko yaushe murmushi shi ne shimfide akan fuskar ta, yanzu Sam Bata da wuya kuka.

Yau ma zaune take a parlor, ita da siblings na ta suna kallo , mufeedat ne a cinyata, ta zuba uban tagumi tayi zurfi a tunani. Sumaiya(bestie) ta shigo da sallama ta, su amir suka amsa, ta nemi guri a gefe Essha ta zauna, ta kalleta shiru, Essha ba ta masa ta shigo ba sbd tayi nisa, Bestie ta Mike ta zungure ta a kai, a zabure ta juyo tana kallo bestie idon ta har ya fara Tara ruwa, ta marairace fuska kamar zatayi kuka, zatayi magana bestie ta rufe mata baki tace" zo muje" ta sauke mufeedat, sukayi hanya daki Essha , suna karasowa..

Bestie ta kalleta tace" Wai Essha what's wrong with you? Ki canza gabadaya, tun Ranar da daddy na yagayamin kina asibiti na shiga tashi hankali na tambeyeshi ko accident kukayi bai bani amsaba, Kuma ya Hana ni fita, Kuma Ina trying number ki a kashe"

Essha ta share hawaye da ya zuba mata ta zauna a baki gado , Tana share hawaye wani na sake zubowa, tanason tayi magana ama kuka yaci karfita da Kuma yada kirji kemata yasa baza tai iya ba, kawai ta rugume bestie ta fashe da kuka.. Mai tsuma Rai.

"Subhanallahi, Essha Wai maike damuki ne" bestie ta fada Tana share mata hawaye,

" Bestie ki fada min mana daga wuri Khalid fa nake Yana ciki tashi hankali, Yana Kira ki, number ki a kashe, Kuma yace min first day da ku ka dawo ya Kira ba ki dauka ba maiyasa?

Essha ta kalleta shiru tana hawaye, itama bestie kuka takeyi.

Tace" please bestie kimin magana ko zaji sanyi, Khalid na Bliss park Yana jiramu , na mishi alkawari zan mu zo tare, tashi muje kibar kuka na, nasan bai wuce menstrual pain, shi ne yake bata min bestie, don't worry zai wuce tashi muje, Kar kice a'a please, khalid na ciki tashi hankali"

Essha zuciya ta zafi yake mata, na ji hali da masoyita ke ciki, gashi ba hali zuwa gareshi ta rike bestie murya kuka tace" bestie kiyi hakuri, ki je kawai, ki bashi hakuri, ki ce mishi ya cire ni a zuciyarsa, ya yafe min in da rabon zamu sake haduwa......

"What!! Kisa Mai kike fada kuwa, Anya ma kina ciki hayaciki, Khalid ne fa " bestie ta katse ta fada a fusace... Ta sausauta murya tace" wlh bazai iya wa ba, Essha ki tausaya minshi, yace fa bazai taba iya wata ya mace ba , Im bakeba, Kar kimishi haka bestie, ki tausaya ma rayuwa bawa Allah na, Wai Maiyasa ma ki ka canza haka? Wani abun ne ya hadaku? Tunda ki ka dawo ki ka canza why?

Essha bataiya Bata amsa ba ta girgiza Kai Tana kuka sosai..
Bestie tace" toh gayamin reason dayasa bake dauka kirashi, har kina cewa ya cireki a zuciya sa ki gayamin" tasa kuka

Essha tasa hannu a baki ta na girgiza Kai, haweye ne kawai ke ambaliya a fuskata, sumaiya ma kuka take.. dai lokaci waya bestie ya Soma Kara, kira ne , ta duba taga Khalid ne da sauri ta pick ta sa a loudspeaker tace" Essha fa Wai bazata zo ba" ta fada har muryata na rawa....



More comment, more typing ❀️❀️❀️❀️❀️



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“š πŸ–ŠοΈ

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
_________________________


4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣



Khalid yace" love mainamiki? Wani laifi na aikata Miki da kikeso ki hukutani haka? Baby love please talk to me, please forgive me Ina azabtuwa"

Essha naji muryashi ta rutse Idon ta na fitar da hawaye masu zafi, ita kadai tasan yadn takeji a zuciya ta, ta kalli bestie murya a hankali tace" ki ce mishi ya manta dani
Bestie ni....... Ta kasa karasawa kamar an rufe mata baki ta fashe da kuka tace" kawai ki ce mishi ya fita daga rayuwa na, ya daina sona"

Khalid daji haka ya sarke da wani mugu tari, Basu Kara ji komai ba, sai hayaniya mutani, duk hankali su ya tashi, bestie na kuka tace" ki gani ko, kigani Zaki kashe yaro mutani a banza, ki manta alkawari daku ka ma juna ne, Essha Bata ba zato zakiyi haka na, ni zanje na sameshi" ta fice rai a bace.

Essha ta kife a gado tana kuka, bestie na fita mummy ta shigo, duk ta ji hirasu, ta dagata ta rugume Tana lalashita, sanda taga ta bar kuka tace" Essha ki cika Yar halak, ki na bi duk sharadi da daddy ki ya daura Miki, baki bi so zuciya ba,am proud of you, a kullum ki kasace Mai tawakali, in khalid mijiki ne, in Allah yaso Zaki aureshi, komai mai wucewa ne, watarana sai lbr, nasiha sosai ta mata Wanda ya rasata, yasa ta Kara saduda ta mayar ma Allah lamarita..

Bestie lkc dai Mai napep ya sauke ta a Bliss park, tun zurutu mutani tagani su taru a gefe daya, sai baza Ido take ko zata ga Khalid, banshi, wayashi take ta trying ama bai dauka ba, kawai ta yake taje inda aka taru ko Allah yasa tagashi, tana zuwa ta samu ta kusa ciki, Tana shiga khalid tagani kwance numfashi sama sama yake fita, tana ganishi tasa ihu tana a taimaka mata,ba Wanda ya kulata karashe ma watsewa akariga yi daya baya daya, tana kuka ta rasa yanda zatayi , ta fara neman wayashi, ama ba waya, batasaniba, tun lkc da suke waya ya sarke da tari, waya ya fadi,daga ciki masu zuwa kallo ne, wani ya dauke waya.

Khalid numfashi Dakar ya ke fita ga tari ga amai jini, da sauri ta dauki wayata ta Kira Bashir, ta gayamishi hali da Khalid ke ciki, da address din guri, bada jimawa ba sai gasu su karaso, suka Parker motar a gabasu, su uku suka zo, da Bashir sai wani saurayi Mai Kama da Khalid din, ama Khalid ya fishi girma, sai mahaifi Khalid.cike da matsifa baba Khalid ya fito Yana babbali matsifa ya nufo khalid yace" wlh ko zaka mutu, bara ka auri yariya na ba, yariya da aka gayamin tagama talla kanta a titi, shine kake neman kashe kashe ka ka akanta, toh wlh ba ka isaba, Kai ko Mai halaka da yariya bara na bar wani nawa ya aura ba, labari tas yazo kunne na, har hanata fita akayi, sbd abun kunya da ta aikata( ohh ni ya su🀦 mutani mutani, hmmm)..

Toh bakai bar Yar iska yariya na har abada nagayama kenan"

Bestie dake zungune ta kasa gasgata abunda kunnuwata suka jiyo mata, bestie ta ne ake mata Wana shairi , Wana abun da mamaki yake, abun daurai Kai ma Bashir(saurayita) tunda yazo guri yashareta Yana wani kauda fuska kamar bashi ba, bai ko kulataba, tun shekarajiya ta lura da chanzawashi, ga Kuma abunda baba khalid ke fada ya matukar girgiza ta, ta Soma tambaya kanta maiyasa yake aibanta bestie na haka? Yana kirata da Yar iska baya ba halita bane, toh maiyasa ma bestie ta canza? Tsikaro murya baba Khalid tayi Yana cewa" sa shi a motar , Kai Kuma Bashir na ji ance kana nema kawata ko? Toh ku rabu tun da wuri,kafi su shafa ma Kashi kaza"

Bashir ya dagaa hannu Alama baruwashi yace" ai daddy na dadane da cireta,sai dai ta nemi wani a gaba ba niba" ya baka ma sumaiya harara

Bestie ta sandare a guri daya ta kasa gasgata abunda takeji, Kuma take gani da idonta, tana hawaye tayi sauri goge idonta da Karfi ko za ta farka Killa mafarki takeyi , tana budewa dsame tagani , ta fashe da sabo kuka ta nufi guri motar ta rike Bashir tace" sweetheart ni ne fa, Wai maike faruwa ne? Kugayamin, wlh Essha na ba yar iska bace"

Bashir ya fisge rigashi da ta rike ya nuna ta da yatsa yace" kul Kar kisake kirana sweetheart, asiri ku ya tonu, a rayuwa na na tsani mace fasika, Kar ki sake nunawa ki sani , shima Khalid giyar so ne, ke dibarsa ba da daidawabs zai farfado, Allah ya hada kowa da rabonshi" ya shiga motar.
Sumy sandare wa tayi a guri ta saki baki da hanci ta na kallosu
Murya Khalid taji daker yake mgn taji yana cewa" sumaiya kiyi hakuri, ki ce ma Essha Kar ta Manta da alkawari da ke tsakanimu, baza taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login