Showing 30001 words to 33000 words out of 70940 words
dialing number Yana ringing ama ba'adaukaba..
Tace" Kara trying na daddy karami ko na hajiya" duka layi in yakira Yana ringing ama ba'adauka..
Anty zainab tace" hmm Allah yasa dai lafiya suke... Bata Gama rufe baki ba sukaji horn din motar, atare duksukayi ajiya zuciya... Daddy yace" gasunna ma su karaso"
Gate man na bude gate, daddy karami ya shigo da motar ko Gama parking baiyiba ya sauko a firgice Yana haweye ya nufi Daddy.. suka binshi da kallo mamaki gabasu na faduwa...
Daddy yace" lafiya ya na gaka a haka Ina saurane? Jini Maine Kuma a jikika?
Daddy karami duk ya firgice sai sharce haweye yakeyi yace" Essha, Essha .... Mummy da Daddy dam sukaji gabasu ya fadi..
Daddy yace" Ina Essha din, maiye samaita? Accident kukayi komai ya jera mishi tamboyoyi a take har jikishi na rawa..
Daddy k. Yace" tana asibiti, ku zomuje, ku yafeni nakasa rike amana, kunyafe nakasa Kare Essha""
Mummy taji kanta na juyawa tace" Wai Mai kake nufi ne? Wani asibiti ? Maiyesameta? Ta fada Tana haweye...
Yace" ku zomuje ku zomuje" mummy ko hijab Bata dauka ba, dogo rigane a jikita sai mayafishi ciki tashi hankali suka dunguma sai asibiti... Hajiya suka samu a baki kofa ba'abunda takeyi sai kuka, har da shesheka da sauri mummy ta nufeta tana hawaye ta dafata murya na rawa tace" Essha na ta mutu ko? Hajiya ta girgiza Kai.. mummy tasa kuwa kamar ta zare tace" ki gayamin gaskiya Kar ki boyemin da Allah hajiya, ta mutu ko? Kamar zautaciya takeyi...
Daddy ya janyeta yace" ya'isa "
" No ka kalleni Ina Essha , Ina take?
Hajiya bataiya cewa komai ba tayi daki da aka kwantar da Essha da hanzari suka bi bayata, suna shiga suka tarda Essha kwance hannu da drip, da mugu sauri mummy ta karasa wajenta tana girgiza ta da dukkani karfita, ama Essha ko gezau, Kara tasaki Mai karfi Wanda amonsa yacika daki da suke.. "ESSHA" ta fada Tana Kara girgiza ta, ciki tashi hankali idon ta ya sauka aka kafata , taga layi jini nabin kafata, ta Kara kallo da kyau, na kafa damata har yasoma bushewa, tasa Kara a karo na biyu, ta Mike ta nufi saiti kafa ta daga dogo riga ta leka,Nan take ta runtse ido, kirjita ne ya shiga bugawa da Karfi gaske, saitin zuciyarta na fat-fat Kamar zata yi tsalle ta fito , ta Soma furta " inalilahi waina ilaihi raju'un, inalilahi waina ilaihi raju'un" a hankali ta sulale a wajen ta zauna ta rike kai.. tana kallo Essha tana hawaye...
Daki yayi tsit bakiji komai sai sautin kuka mummy da hajiya.. Daddy yagamy rudewa yakasan fahimtar komai dake faruwa,.
Ya kalli daddy karami bakishi na rawa yace" Wai mai ke faruwa ne? Ku gayamin ku barni a duhu. Maiyesameta?
Mummy Dakar ta ' iya bude baki tace" Abba Essha, Essha was raped, fyade aka mata " ta sake fashewa da kuka...
Daddy kansa ya dafa, ji yake kamar zai balle daga madaukarsa, bugun zuciyarsa ya tsanata wajan bugawa.. ya nufi hajiya da kanta na kasa sai shesheka takeyi yace" hajiya ki gayamin zance na Dana keji karya ne, ki gayamin gaskiya "
Hajiya na kuka ta kwashe duk abunda ya faru tundaga farko haduwarsu da kungiya har zuwa su asibiti ...
Daddy da mummy su matukar firgita daji wanan labari ... Haweye ke sauka a idon daddy kamar an balle famfo yace" inalilahi waina ilaihi raju'un Allahum arjini fi musibati*2....
Tunda hajiya ke bada labari anty zainab ke haweye take haweye, Bata taba jin labari iri haka Mai firgirtawa da abun al'ajabi ya taba faruwa ba ko da a film ne ko littafi ....
Daddy ya rike saitin zuciyarshi Yana girgiza Kai yace " Essha Dina ne aka aurar da ita, ga yaro da ba'asanshiba , ba'asan asalinsa ba, Allah Mai iko ya share haweye " alhamdullila tun da har aka daura aure, ba fasikaci suka aikata ba, haka ma yazo da sauki, aure alkhari ne, toh maiyasa kuka bar shi a can baku daukoshi ba?
Daddy karami yace" mun rikece ne da gani hali da Essha take ciki, shiyasa na Manta da batun yaro" dai dai lokaci Doctor Abbas ya shigo daki ya tardasu fuskokisu cike yake da haweye...ya Mika ma daddy Essha hannu sukayi musabaha..
Doctor Abbas yace" kuyi hakuri zata farka, firgice da tsoro ne ya hadasa mata Suma,ya kalli daddy" inason gani ka a office na..
Daddy yakasa magana ya bin baya Doctor Abbas zuwa office nashi , baya su zauna .. Dr .Abbas ya kalli daddy ynda ya shiga damuwa, ya kadan kai" Yaya ku ka Bari haka ya faru da ita? Dr. Abbas ya Mike a fusace yanuna daddy da yatsa yace" ga abunda na ke fadama kenan akullum inmu hadu, kadaina sake ma yaraka da yawa, kullum Kai burika ka, ka farata musu ne baka tsawata musu ba, baya kuma kasa hali yaran zamani na, Wana ya'isa ya zama ishara a gareka, yawa bama yaraka freedom shi ya janyo aka ma Essha fyade . A matsayi na na makwabcika nake gayama gaskiya " Daddy ya bude baki sheke Yana kallosa har yagama magana , mamaki zance sa ya hanashi bashi amsa.. bai San asali magana shine har ya ke hukuci yake Daura minshi laifi.. toh Wai ma shin maiye aibu wanan duk ka sake ma yaraka, wanan ai sunnah ne na Ma'aiki (S.A.W.) ka riga farata ma iyalaka, ka Dora musu da tarbiya nagari, takura, matsi ko iyaye suriga hade ma yarasu gira shine zai sa yaro ya natsu no yawaici ma shine ke cefa yara ciki wani hali( kaluballe agaremu iyaye).
Daddy aranshi yace" wani amsa yaka mata ya ba bawa Allah na? Kai na ma fasa gayamishi abunda yafaru" baice uffan ba ya Mike yabar office din fuska cike da damuwa..
Yana fita Dr Abbas ya tabe baki yace" tundama iriku bakusan gaskiya, kullum Kuna tsakiyar yaraku Kuna washe musu hakora Wai shi soπ², Kaya sai Wanda suka sa, Tayays bara'aji sha'awa yi musu fyade ba, toh kawace da yanta ma na kusan rabasu very soon "ya kada hannu..
Daddy na fita magaganu Dr Abbas ne ke masa yawo akai, sai tambayar kansa yake" ayya Dr Abbas ne kuwa amintace makwabcishi, shine yake gayaminshi haka, bai tayashi jaje ba, bai Kuma San kan magana ba shine ya yake hukuci, hmmm yayi ajiya zuciya, Yana gode ma Allah a yanda kaddara nashi yariya yanzo a haka , da aure akanta komai ya faru.. yama kanshi alkawari baya family shi bawanda zai gayama ko da kuwa abokaina shi ne, dun yasa tabas bawanda zai yarda da zanceshi, ya bar ma Allah komai, ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi......
Ur comment is my strength ππ₯°
Comment &shareπ₯°πππ
π©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈ
DOCTOR ESSHA
π©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈπ©ββοΈ
WRITING BY
J Hajara
π MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION π ποΈ
Kungiya d'aya tamkar da dubu. masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.π€π»
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
____________________
3οΈβ£5οΈβ£&3οΈβ£6οΈβ£
Ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi, ya nufi daki da aka kwantar da Essha,Yana kaiwa baki kofar suka ci karo da daddy karami da haryanzu kuka yake, daddy ya kalleshi duk ya hargizai yajashi gefe suka zauna a kujeru da aka jera agefe dakuna. Baya su zauna. Daddy ya kalleshi yayi ajiya zuciya yace" yakamata ka daina kuka na haka duk abunda yasamu bawa mukadarine daga Allah, yanzu kawai munjira farkawata"
"Yaya kunya hada Id......
Daddy ya daga mishi hannu yace" ya'isa haka, Kar ka Manta fa duk abunda yasamu bawa haka Allah ya rubuta mishi, ni musulmi ne kaima haka, Kuma duk muyi Imani da kaddara, Ina Kara godema Allah ba keta mata haddi sukayi ba, aure suka hada rokona ana shine Allah yasa ya zamto alkhari, idan da rabo za su hadu tom, dun ace matar mutum kabarisa, fatana Allah yaba Essha lafiya da juriya"
Daddy k ya amsa da ameen yaji dadi kalamai daddy, sukara kwantar mishi da hankali, suna zaune suyi jungum sanda aka Kira sallah magarib suka Mike zuwa masalaci dake ciki asibiti.
Har akayi isha'i, Essha Bata farka ba, mummy na makale a gefeta , wata likita daban tazo takara dubata ta tabatar musu cewa suyi na bada jimawa ba zata farka.Dare ya tsala dukasu ba bu Wanda ya runtsa mummy da Daddy, hajiya da daddy k tun baya isha'i, Bala driver ya wuce dasu gida dun su huta.. Essha kuwa can tsarka dare ta farka batama gane kosu wa ye akanta sai kuka take tana fisge fisge tana magaganu" hajiya kuce mishi ya sakeni wlh basan aure, na tsaneshi, mugu ne, hajiya ki taimakeni"
Daddy da gudu yaje yakira likita dake da duty a daren yana zuwa ya mata allura bacci, mummy kam tayi kuka da Bata tabayishiba..
Washe gari sai misali 1:30pm na Rana Essha ta farka." Alhamdullila ta farka" maganar nurse din data zo dubanta ta ratsa dodo kunnuwansu haka yasasu juyowa a hautsune Dan gani zahiri abun da kunnuwasu suka jiye musu" Tabbas ta farka" mummy ta fada lokaci da idanuwansu suka hade waje daya, da sauri ta karasa wajenta tana " Essha daddy" ta fada Tana kokari ruko hannu ta, Essha ta Mike da ga kwance da sauri ta rugume mummy ta, ta fashe da wani kuka Mai kashe jiki Mai sauraro, mummy ma haweye takeyi tana shafa kwantace gashi ta da ya gaji da hargitsewa.
"Mummy tsoro nakeji inaji fargaba mummy, su aurar da ni, they have ruined my life" ta Kara sauti kukata, daddy ya matso kusa da su ya shafa kanta, a firgice ta juya tana gani shine ta rugumeshi " Daddy zuciya, daddy kasana, zan mutu daddy, ka raba aura na wlh banso, shikena an aura dani daddy na bazai kaini makarataba balle na cika burina har yakai ga kirana DOCTOR ESSHA, nasan daga Rana ita yau zan daina sa .... Ta dakata, jiki ta har rawa yake saboda tsumayi kuka" daddy why me? Why? Why?
Daddy haweye fuskata yashiga gogewa shima dauriya kawai yayi, Yana rike haweye bai barsu su sauka ba ya daure yayi murmushi Yana girgiza Kai yace" ya'isa haka Essha daddy, ki daina ai'bata aureki Kar ki mantafa aure sunnah ne na Ma'aiki (S.A.W), aure rahma ne Kuma alkharine, magana karatu inshallah ba abun da zai hanaki bearing suna DOCTOR ESSHA" yaja mata kumatu yayi murmushi " ba abunda zai saimeki inshallah, ni da mummy ki dasu hajiya muna tare da ke"
Daki ya dauki shiru, bakaji komai sai shesheka kuka Essha da hajiya, Essha na kuka zafi da ke damunta, hajiya Kuma tausayi hali da Essha ke ciki shiyasa ta kuka, Essha sai zabura take ita daya, haryanzu da alama tsoro a atare da ita, daddy nata aiki lallashi, can ya Mike yace" Essha zanje sallah ankira zuhur"
" Ni ma zanyi sallah daddy" ta fada Tana share hawaye , tun jiya banyi sallah ba"
" Toh mummy ki da antyki zasu tamaika miki" ya fice da sauri baison ya rasa jam'i.
Nurse din ta kalli mummy tace" hajiya bara na taimaka mata dun ba'ason tayi kwakara motsi saboda dinki dake jikita"
Essha ta makale kafada ta tura baki tace" uhm uhm mummy nane zata taimakamin"
Nurse tayi murmushi ta shafa kanta tace" okay beauty badamuwa Bari na baku waje" ta fice..
Mummy ta Mike ta dauki flask din da hajiya suka kawo da safe, tafasheshe ruwa ne dam , tashiga toilet ta juye a baho wanka, da taimako anty zainab ta kaita toilet, ta zuba gishiri kadan ta Kara surka ruwa, sanda suka Kai ruwa Rana Essha ta Amince ta shiga ruwa zafi, ihuta yagama cika asibiti, kuka tasaki da Karfi tana Kira hajiya da daddy ta su zo su taimaketa, Wai balle Essha iyaye raki.. sanda mummy ta tabbatar ta gasu sosai sanan ta cire ta tasata tayi wanka janaba ta Dora alwala tafito, tan Dan ji dama dama, Dakar take takawa mummy na rike da ita, har su ka Kai baki gado, haweye kawai take sharewa ta hura baki, ita kadai tasan yanda takeji a zuciya ta, sai tsine Aliyu takeyi, yasha Allah yaisa ba adadi.
Mummy ta shimfidar mata daddurma tabata riga da skirt na atamfa tasa da hijab , a zaune duk ta Rama sallolita tana hawaye..
ABUJA
************************
Gari na wayewa ummi tasa su a gaba sai fada take musu" tun jiya nagaya muku cewa su shafi Aliyu ama kuka ki yarda da batuna, gashi har su na nema sumishi illa, Allah sarki bawa , Yana ban tausayi , ke Kuma aljana Essha, Allah yama jikana kataga karfe dake" Mami ta amsa da ameen sanan tace" ummi maiye mafita?
Ummi ta rike haiba tace" mafita kenan ana sallamorshi atara malamai Yan ruqiya kawai suriga mishi tofi har tasakeshi"
Tycoon ya Mike yace" ummi ni zan wuce asibiti"
Tace" bamugama magana ba"
Yace" duk abunda kika ga yadace shi za a yi, sai na dawo"
Mami ta Mike tace" jirani na dauko mayafi na muje"
Yace" sai ki fitoh"
Suna isa asibiti Tycoon ko yaji ra a bude minshi kofa ya bude kofar da kanshi, guards na gani hk da sauri suka bi bayashi ya dakatar dasu.. I C U ya wuce Mami na biye dashi, suka Tara a canza ma Aliyu room an cireshi a I C U. Mami tayi ajiya zuciya tace" Alhamdullila son yasamu sauki tunda acireshi a ICU" tana magana saiga haydar yamusu iso zuwa harzuwa daki da Aliyu yake , Allah sarki, Hafiz suna na a zaune su zuba uba tagumi harsu dan fada kamar a jikisu ciwo yake, Tycoon ya binsu daya baya suka yi musabaha cike da girmamawa suka gaida mummy ta amsa .
Tace" Allah ya muku albarka" suka amsa da ameen Mami
Tycoon ya nufi gado Aliyu ya ke kwance kamar gawa, baya ko motsi, fuska na tayi fayau, lips nashi duk su bushe, ya shafa ganshi kan Aliyu yayi ajiya zuciya sanan yace" boy Allah yabaka lafiya suka amsa da ameen, ya nemi guri ya zauna a gefeshi ya kalli fawaz yace" Doctor yajiki nashi?
Fawaz ya su sa Kai yace" da sauki dad.gani sauki ne shiyasa aka canza mishi room.
" Ya farka dai ko ? Mami ta tambaya
Yace" eh mami ya farka around two na dare, sai sambatu yakeyi Yana Kira suna dai Essha, shine kawai mikamishi allura bacci, inshallah na bada jimawa ba zai farka"
" Inalilahi waina ilaihi raju'un, Essha Essha haba haba, wanan Essha mutum ce ko aljan da zata adabi rayuwa dana" Mami ta fada ta rike Kai ta fashe da kuka..
Suleiman dake gefe ta ya Mike ya dafata yace" Mami ba kuka zakiyiba, addu'a zakimishi, Allah yabashi lafiya, yanzu Yana farkawa yaji kina Kira suna Essha Dina Kara rikecewa zaiyi"
Mami ta hada hannu ta na addu'a Tana haweye tace" Allah ga Dana na, ka. Fitar da shi daga ciki wanan hali dayake ciki, Allah na rokeka" suka amsa da ameen, suna amasawa sukaji an bake kofa anshigo bako sallama, suna daga Kai sukaga suhaima ne, dogo riga ne a jikita na atamfa ta cugale dauri dankwali bako mayafi s jikita, car key ne da waya a hannu ta kirar iPhone 11 pro max, Suleiman na gani itace ya baka mata harara, ya Mike ya fice, saura ma suka bi bayashi, don bakarami haushi ta sukeji ba, toh su San hali, ita kam ko ajikita kallo sama da kasa ta binsu dashi taja tsaki.
Suleiman suna yaja tsaki yanemi guri ya zauna yace" wlh I hate this girl, gsky an cuce Buddy, yariya batasan daraja mutani ba, Mai karanci addini" ya Kara ja wani dogo tsaki..
Hafiz yace" Nima ko kallo ta basanyi Mai Kama da sisiya, wlh ko a office ko kallo Bata isheniba, Allah ancuceshi , dubeta ma Kama kara, Allah yasa ma aljanana Essha Dina , aljana ce dagaske, Allah zan iya biyata tayimin maganita yariya ba tarbiya kawai (lolz kuji Hafiz fa).
Haydar yace" Kuna ma da lokaci ta kenan bara kuga hoto da ta daura a page nata na Instagram guri misali karfe 3 na dare fa" ya ciro wayar shi daga aljihu Yana nunamusu hoto suhaima, suhaima ne zaune a club, su hudu itace kawai mace a ciki su, tasa dogo riga ne a cikita ya matse ta sosai ko rabi cinyar ta baiyi ba, fixing da tayi na attach duk ya barbaje tukunyar shisha ne a gabansu, tana tsakiyar maza, hayaki take fesowa cike da korewa a fuska yan samarin.
Fawaz ya ja tsaki yace" tir da hali iri nata, ni narasa dalili da yasa for the first place daddy ya Amince da aure na, wlh da abani irita guda goma goda aban Yar karkara wancan batasa komai ba" duk suka fashe mishi da dariya..
Hafiz yace" ahaf Kar kudamu nasan buddy zaiyi maganita, zanta gane kureta, Allah sarki buddy yaro kirki Allah yabaka lafiya" suka amsa da ameen..
Ciki daki kuwa, suhaima Chewgum take fasawa fas fas kas kas batama San da su Tycoon a daki ba, hankali ta na waya tana chatting, yantsu zaro zaro yasha pink artificial nails, Mami sai binta take da kallo mamaki, Bata cemata uffan ba, ita akullum tir takeyi da Wana Hadi aure batasan maiyasha kan maigida nata ba da ya nace sai ya aura ma Aliyu Wana gataleliyar, kwanaki baya har batawa sukayi akan magana aura Ammi ne tabata hakuri tace su zubamishi idon Allah yasa haka shine mafi alkhari..
Mami ta tabe baki ta bita da kallo.. Tycoon yace" a'a daughter welcome ga guri ki zauna"
Suhaima har ta Dan firgita da taji magana ta daga Kai suka hada Ido da tycoon ta saki murmushi tace" good morning Dad " a tsaye ko ta Dan ragwafa.
Yace" morning daughter ga Mami ki " ta juya ga kallota ga inda yanuna mata, Mami sai binta take da harara kamar idon zai fadi.. na take taji shakku Mami ta sukunyar da Kai tace" good morning ma"
Mami ta amsa fuska a hade ta kauda Kai..
Suhaima Sumi Sumi taja jiki zuwa gefe Aliyu tace" dad ya Mai jiki?
Ya amsa da sauki Yana shafa kafa Aliyu, yana shafa kafa kuwa, kamar ace ma Aliyu ya farka, ai da sauri Mami da Tycoon suka Mike , Tycoon ya rike hannu shi