Showing 6001 words to 9000 words out of 70940 words
akazo dashi zanmika ma wani friend Dina duni zanyi tafiya, Kuma yau Friday.
Ok barrister (haka Aliyu ke Kira idriss da barrister), Ina zakaje? Aliyu ya tambeyeshi.
Ya rage murya ya zo daidai kusa da shi yace" big bro guri princess Dina zanje a kano, biki yayarta za'ayi gobe.
La kace guri inlaw na zakaje" Aliyu ya fada.
Eh Yaya.
Toh ka gasheita, Kuma u should take care of yourself Aliyu yafada"
Okay bro I will, kila ma said Monday na dawo"
Okay safe journey.
Idriss Yana fita yadawo da saurishi yace" Yaya Aliyu da Allah in Ammi ko Mami suka tambeyaka ni, kace musu kawai akirani wani case ne a kano.
La see dis boy oo, so kake nayi karya daga dawuwa na?
a'a big bro mami ne Bata so na da yariya, basan maiyasa ba idriss yafada a murya tausayi"
Aliyu yace Kar kadamu zan shawo maka kansu"
Ohh that's my lovely bro idriss ya fada" ya rugume Aliyu , ya fice da sauri, Aliyu ya jijiga Kai kawai Yana murmushi.
Ya haura dakishi, ya wuce toilet, ya watsa ruwa, yayi alwala, bai jimaba saboda yasa baiyi sallah zuhr ba.
Yana fitowa yasamu Dan liti a baki kofa(dan liti amintace Mai aikishi ne, tundaga kan gyara wuri, sako, sometimes har girki Yana mishi sbd ya aminta dashi, Kuma ya na saka shi nishadin, dun Dan liti iri mutanina ne masu son barkwaci dasa mutum dariya, shiyasa Aliyu ke ji dashi).
Dan liti yace" yalabai sannu da zuwa, ya zuguna har kasa.
Aliyu ya amsa da musa maiku lafiya?
Lafiya rankashi dade, ai yallabai nayi matukar kewa ka, dun tun tafiya ka bani sukuni a gida nan , a guri waeina yara su biyu na , walahi yalabai su adabi rayuwana, nasa suna tsoraka, ka ga Sofia har sani wani rawa da waka takeyi , rahma na kwasheni a waya su, wassh wlh yalabai har nayi ciwo baya😅, nasa suna tsoraka, yanzu sa sayaya min.
Wai Dan liti kana ta zuba, Bari inyi sallah tukun Wana Kara na ka babba ne Aliyu ya fada"
Dan liti yace "yihakuri yalabai Kuma fa hajiya tace" Kar na damaika , Ina jera maka abinci in fito, ya dungusar da Kai Alama amishi afuwa.
Aliyu yace tashi katafi saina fitoh" toh yallabai.
Ya nufi wardrobe nashi Kaya ne, a ninike dayawa kamar wani boutique, tun daga kan English wears zuwa su shadodi. Ya cire wani armless t_shirt, baki da jeans trouser shima baki, yasa bakarami kyau yayi ba.
Ya shimfida dadurma yayi Sallah, yana idarwa, ya nufi wani jaka dayazo dashi, ya fitar da wayashi, da laptop. Yana kuna waya, Kira na shigowa, fawaz ne, ya dauka da sallama?
Fawaz yace"rike sallamarka tun 2:00 kana garina shine ko ka nimamu toh ka kyauta,
Haba likita boka tura kamin uzuri mana ya fada"
Fawaz ya katseshi da cewa" mudai gamuna zuwa, musa Kai ba zuwa zakayi ba, ya kashe waya.
Ya kishigede shiru a gefe gado,ya lumshe idon kamar Mai bacci. Ya rasa dalili dayasa tun da ya sauko Nigeria yake ji gabashi na faduwar gaba, ama yabar ma Allah komai,
Ya naji wayarshi na ringing ama ko yace zai tashi yaduba, dun yasa ba daddy shi bane, ko Ammi ko Mami, shiyasa ya share Kira, waya nata ringing har tsawo tw o minutes ama ko yadaga , har aka hakura abar Kira.
Waya na tsinkewa ana sallama a daki, bakowa bace ila Salma cousin sister shi, yariya uncle bello.
Salma yariyace Mai jida kanta. Tunda ta tashi da soyaya Aliyu yatashi.yanzu hk Tana 300l a KASU(kaduna state University)Tana karata computer science, ga kyau , turbakallah,tana bala' in son Aliyu , ama shi baima San tanayi ba.
Lokaci da aka sanar mata da cewa zaiyi aure , taci kuka har ciwo sanda tayi, tan binciki yariya da zai aura wato suhaima, tagama Bata fita da komai ba, Kuma abun da yayi mata dadi ta taji cewa ai aure dole za'amishi shiyasa ta saki ranta. Mummy ta ta Sha fadamata tabar zance aure Aliyu ama taki, shiyasa tu Ranar da siyama tagaya mata Aliyu zai dawo ta tatara ta dawo Abuja da zama, dun Tasha aniyar cewa zata gayama Aliyu abunda ke ciki ranta, tasa ko ba komai zai so ta,
Shiyasa yau Tasha gayun ta nufo part dinshi, ta duba parlor Bata ganshi ba shiyasa ta haura har daki shi.
Tana ta sallama ba amsaba, Kuma Yana kwance Yana jita , baiso a damaishi.
Ta shigo a hankali, sanye take da riga da wando na Pakistan. Ta nufoshi a hankali, ta zauna ta zuba mishi Ido, akansa zuciya ta tace Kai ya Aliyu ya hadu, ya Allah kasa ya zama mijina, ta cigaba da kalloshi tun daga kan eyelashes har zuwa dan madaici light pink lips kamar ta taba. Shi Kuma kallo ya Soma bashi haushi,
Ya ce" yayya da kallo? Har ta firgita dun yayi kamar bashine yayi maganarba.
Tace" Yaya magana nazo muyi, ya Mike zaune, ya dauki wayashi Yana latsawa, can yatuna anata kirashi bai amsa ba, ya duba missed call yaga Ashe ma suhaima ne, ta mishi har 12missed call, wani dogo tsaki yaja, ya cigaba da Danna wayarshi,
Salma na zaune bai ko kalleta ba, saitaji jiki ta yayi sanyi
Can yadago yace" Ina ji jiki Mai ke tafe dake.
Murya na rawa ta Soma magana" da da -dam dama
Yace " keki natsu kimin magana basan bata lokaci.
Ta sukunyar da Kai tace" Yaya Ina sonka!
Ya dago Kai da sauri yace"What!! Salma yakira sunata da karfi ya Mike tsaye.
Ta cigaba da mgn tana kuka tace" walahi Yaya Ina sonka, banaji son kowa a zuciya inba Kai ba, da Allah yaya ka taimaka ka soni,
Mamaki ma ya Hana Aliyu magana, Wai yau shi Salma tazo tace ta na so.wai Wana wani iri duniya ne,
Salma ta sauko ta rike kafarshi tace" da Allah yaya please please, ka tausayi min, ya wani iri ball da ita, yada ka mata tsawa.
Yace" Wai ni saran wasaki ne, da Rashi kunya da fitsara shine har Zaki iya bin namiji ki ce kinasonshi, ya rike Kai Wai Mai yasa yanmata yanzu Basu da kamu Kai me, ya Dade Yana ji haushi suhaima da saura yanmata da sukecewa suna sonshi, Yana gani wanan kamar subar da aji ne da Kuma karaci tarbiya.
Salma tace" Yaya walahi Yaya inbaka soni walahi zan iya mutuwa, ya wani Kai mata Mari a baki
Yace" bara kinji nagayamiki bana sonki, Wai kwata kwata guda nawa kike Dan har kisan wani so😳, dube kifa da ko Isa ban za ce ya sonki ba, shine Zaki kwaso wani stupid jiki ki, kixo kice kina sona Koh
Toh bara nagayamiki this should be the first and last da zanji iri magana abaki, rubbish , tashi kibar min daki, kafi nabalaki a guri.
Da gudu ta fice da ta matukar tsorata da Yaya nata, dun bai taba ko canza ma ta fuska, shine yau kawai dun tace tana sonshi, har da Marita.
Wayyo ni Salma na shiga uku, Tana fita taji karo da Ammi a baki kofa, ta fado jikita takara fashe da sabo kuka.
Ammi Ashe taji komai, dun tu dazu take Shashi tazo taduba ko Aliyu yaci abinci dun tasashi da ranshi so ci abinci (uwa kenan♥️).
Tace" keki room Dina Ina zuwa, Salma ta fice da sauri da Kar ya Aliyu yaxo ya samaita.
Ammi na shiga daki tasamaishi rike da Kai, sai kwafa yake tayi, tanufi fridge ta dauka bottle water Mai sanyi ta Mika mishi, batayi magana ba shima haka, ya amsa,ya kafa Kai ya shanye duka yayi wurgi da gora.
Ammi ta zauna a gefeshi, tana tapping nashi a hankali.
Tace" Allah ya huci zuciya gadagaa, gadagaa gutsa yaki, takawa ka lafiya da gaban goshi tycoon da mamishi. Sai yaji hankali shi ya kwanta da Wana kirari.
Ya kife Kai a kafada Ammi .tace" Aliyu da Allah ka rage zuciya na kaji ko?
Yace" Ammi kidubi yariyana Dan tsaba Rashi kunya...... Ammi ta tareshi da ssshh bansaji komai, naji abunda ya hadaku, ama Aliyu bai kamata ka mareta ba, kaga ita mace ne.
Comment & share😍😍🙏
Doctor Essha
👩⚕️
Written by J hajara.
1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣
Ammi tace"Amma Aliyu bai kamata ka mareta ba kaga ita mace ne,dakata tazo tace ta na sonka ai batayi laifi ko Rashi kunya ba,kamata tarihi Ma'aiki (S.A.W) lokaci da Nana khadijah (A.S) tazo tasamaishi tace tana sonshi ai hannu bibibbiyu ya karbeta"
Yace"Ammi a gsky bana son Salmah"
Ammi tace"ok naji, ai sai ka mata magana na fahimta Wanda baizai daga mata hankali ba,har ya Kai da Mari, kasan zuciya ba Kashi ko?
Yace" Ammi are you supporting her"
Tayi murmushi tace" Aliyu har yanzu bakasan so bane shiyasa kake Wana maganar"
Yace" toh Ammi naji u r just supporting ur daughter shiyasa"
Ta jijiga Kai tace"a'a Aliyu bahakabane"
Yace" naji Ammi yanzu ya kikeso ayi"
Tace" inaso kasame ta ka Bata hakuri"
Yadaga kanshi daga kafadata yace"Ammi hakuri fa!
Tace" eh hakuri mana, kace mata ka dauke ta ne a matsayi su siyama tayi hakuri baza kaiya aureta ba, ka lalasheta nasan cewa batasa da maganar aure ka ba,ka fahimtar da ita har tagane ama ba duka ko zagi bane zakayi, abun yadace kayi kenan"
Yayi shiru Yana tunani sai a lokaci da Ammi tace aureshi yarage wata uku sanan ya tuna da wani zance aure yayi ajiya zuciya.
Ammi tace"Aliyu are you with me? Ya daga Kai Alama eh.
Tace" yawa Dan mamishi tashi muje kaci abinci ga la'asar ya gabato tundama abunda yakawoni kenan"
Suna sauka sukaji sallamar su fawaz dukasu hudu sukazo fawaz, haydar, Suleiman da Hafiz suka gaida Ammi tace" Hafiz tundama Kuna gari shine ko ku laikamu sai yau duku ga aboki ku yazo ko?
Dukasu kowa sai soshe soshe Rashi gaskiya sukayi.
Ammi tace" ku kyauta"
Suleiman yace"Ammi aiki ne ke taremu shiyasa da Allah kiyi hakuri"
Haydar yace" wlh hakane Ammi ba time"
Tace" ai gashi kuzo duba abokiku ko?Wai ma na tambeyeku tun yaushe ku ka dawo?
Aliyu na gefe Yana musu dariya, suna ta mishi signal yacecesu, ya daga musu hannu Alama Babu ruwashi,
Aliyu yace"Ammi ai yau Friday satisu daya kenan da da dawowa,
Tayi murmushi tace" ohh Allah ya taimakeku,toh ku taso kuci abinci saura naji wani yace min ya koshi"
Ai da sauri suka hau kujera dining.
Fawaz yace" Ammi tundama yunwa mukeji"
Ammi tace"gwaraye kawai"
Dukasu sukayi tsit, dun suna amsa wani jamb question ne zai biyo baya 😅
Tayi serving nasu fried rice da farfesu kaza, sai fruit juice da salad, tace kawo ya cinye yabani empty plates"
Ta fice daga part din, Tana fita suka sauke ajiya zuciya .
Fawaz yace" Kai buddy yau kayi amfani ka cecemu daga jamb question din Ammi😅duka suka fashe da dariya.
Hafiz yace" gobe fa Alhaji na zai tura manya gidasu my queen"
Haydar yace" shege Kaya kace kashirya kenan"
Yace" eh mana"
Suna hira sunaci abinci, Aliyu kam ba wani ci yake ba, kwata kwata hankalishi ma bashi aguri, sai juya cokali yake tayi, Suleiman ne ya lura dashi, ya dafashi yace" buddy are you okay? Mai ke damuka? Duka sukayi shiru hankalisu ya dawo kansu. Bai amsa ba ya Mike daga dining ya wuce parlour, ya kwanta shiru, Suma kowa jiki a sanyaye suka bi bayashi, fawaz ne ya katse shiru dacewa" Wai buddy Mai ke damuka ne? Aliyu yamike ya zauna, ya Soma Basu lbr abunda Salma tamishi, sai jimami kawai suke, haydar ma abun yafi damushi, don tunda yaga Salma yake ji Sonta a ranshi, Ashe ita ga inda ta dosa, yace" Aliyu bai kamata ka hk ba, abunda Ammi ta fada tayi gaskiya ka sameta kuyi magana ta fahimta, zataji dadi a ranta" duk suka goyi baya magana da haydar ya fada, yaja wani dogo tsaki, sbd ya tuna da batu suhaima.
Hafiz yace" kazo kenan zaka samu agaba, Kai bazaka tsaya ayi magana ta fahimta ba, sai dai kata hada fuska,ni wlh abinci na zanje nakarasa ci" ya Mike yaje ya cigaba da ci abinci, ba Wanda ya tanka mishi don su sanshi baya wasa da cikishi.
Aliyu yace" kunsa Nanda 3months ne fa aurena" ai nandana Hafiz dake ci abinci ya shake, dukasu suka hada baki guri cewa" what!!! Dagaske kakeyi? Ya daga musu Kai Alama eh"
Fawaz yace" kwal ubancan, tabdi jam, Wai yaushe aka sa Rana ne baka gayamana ba"
Aliyu yace" Nima basani ba, Ranar Thursday ne dad yaki rani yake gayamin, Nima na Manta sai yau da Ammi take mgn na tuna" ai sai duka suka fashe da dariya shakiyaci, Aliyu ya tsaya yana kallosu yarasa dalili dayasa suke mishi dariya.
Suleiman yace"ango ango kasha kamshi, ango na suhaima"
Aliyu yace" da Allah u guys should stop"
Fawaz yace" toh ango ya magana Salma?
Yace" ni gaskiya bani da niyyar yi mata biyu daya ya isa, Kuma Salma na dauke ta a matsayi kanwa na ne, baza iyaba"
Haydar yace" hmm toh nikamin hanya wlh ni Ina sonta"
Suleiman yace" wayo ku kaisan kumana kenan ko, toh baku isaba"
Haydar ya kalleshi yace" buddy stop Allah am serious wlh ni inasonta , zan aureta"
Aliyu yace" karkadamu zan mata magana"
Aka Kira sallah la'asar duk suka Mike zuwa masalaci dake ciki gida gida.
A daki Kuma Salma be keta rusa kuka kamar nufashita zai dauke, Ammi da siyama suyi lallashi har su gaji, takikiyi shiru.
Ammi tace" Wai Salma yaki keso ayi ne, ki cika gida da kuka, har ki ja makaki ciwo a banza, kema kisan Aliyu inyace bayayi to ya zaunu, sbd hk kiyi hakuri kijiko, Allah zai zaba maki Wanda yafi alkhari, Kuma kisan Koda a fada ma daddy su ra'ayi shi yakebin, kiga bahali a jegunda kenan, kiyi shiru kibar wanan kuka". Ta share hawayeta, sai ajiya zuciya take tayi da shesheka kuka.
Ammi tace" siyama kaita side naku, ta huta, siyama ta mikar da ita suka fice daga daki. Ammi ta jijiga Kai Tana mamaki yara yanzu.
Su Aliyu na idarwa suka fice a gida gabadaya don ko daddy shi baikara lekashi ba.
*************************
Suhaima sai haushi takeji, Aliyu ya dawo kasa na, shine bai naimaita ba, abun takaici ma ta kirashi yaki daga waya, wanna wani iri Abu ne, sai wurgi da Kaya dakita ta keyi, sbd haushi da matsifa.
Ma'aikata gida sai hakuri suke Bata ama kota kullasu, daya daga cikisu taje takira mommy ta tagayamata hali da suhaima ke ciki, da sauri mummy ta nufi dakita ta sameta rike da kwalba turare ta farfasa mirror hannuta nata jini,
Hajiya binta(suna mummy ta kenan) tace" baby na maiyasameki haka? Wayata ba min ke? Mummy ta Kira suna ta da Karfi" hajiya binta ta matso kusa da ita tayi sauri ta karbe kwalba fasashe dake hannuta tace" Wai suhaima so like ki illata kanki a banza, nace kigayamin waya tabaki ne a garinan? Bata amsaba tasake durgusa a guri da ta fasa kwalba da sauri hajiya binta ta riketa. Tace" zo muje dakina kigayamin kiga Ina barki ana zakiji makaki ciwo" tana magana Tana gyara mata kitso attachment nata da ya barbazo yayi kamar wata aljana 😅.ta jata suka fita daga daki, takira daya daga ciki maid nata, da tazo ta share mess din da suhaima tayi, ai da sauri ta karaso, dun suna bala'in tsoro hajiya binta Bata da kirki ko kadan daga ita har suhaima din, sam Basu San mutunci dan Adam ba.
Suna Isa daki ta kaita toilets,ta watsa ruwa ta da towel, Kaya da ta cire aguri tabarsu , don a rayuwa ta batasan wani aiki ba, hata pants da bra Yan aikisu ne ke wanke mata.
Tana fitowa hajiya binta ta tareta tace" zo ingyara maki guri da kikaji ciwo da first aid kafi daddy ki ya dawo, yaga wanan ciwo"
Wace ce suhaima?
Suhaima yariya ce sagartaciya na buga a jarida, Wanda tun tasowata iyayeta suka Bata ta da kudi, sbd ita kadai Allah ya azurtasu da ita. Mahaifita Ambassador ne na Nigeria dake kasar Russian🇷🇺 .
Suna mahaifita Alhaji rabi'u Hussain Dan asali jahar kano, matashi daya hajiya binta, family nasu daya da Ambs rabi' u Hussain aure zumuci ne aka musu, tun da sukayi aure har tsawo shekara biyu Basu samu haihuwa ba, sai a shekara na uku ne, Allah yabasu suhaima , Kuma tsanadiyar haihuwata ne, mahaifar hajiya binta ya lalace, aka cire mata gabadaya, shiyasa ita da Ambassador suka daura mata son duniya, duk abunda takeso Bata taba rasawaba, rayuwa ta rabi a kasa waje tayi shi, tarbiya da al'adu mu na hausa suhaima Bata sanshiba, duk shiga da taka dama tanayi tafita, kaweyenta kalla kalla, Yan club goggu mata masu ji da kansu, Ama Tana da best friend maisuna nafisat ama suna kirata da feenat, itama yariya babba Dan siyasa ne a kasa namu.
Suhaima tun lokaci da ta hadu da Aliyu a Russian, yakawo ma daddy ta ziyara, taji dun duniya ba Wanda takeso kamar shi, shiyasa ta nace ma daddy ta har ya ma tycoon magana, har aka kai ga muzali aure.
Suhaima manager ne a daya daga ciki company tycoon, ita tasa daddy ta ya naima mata aiki a company sbd ta saba da Aliyu da Kuma ahalishi.
Cigaba lbr
Hajiya binta tace"yawwa baby zona kigayamin maiye samaiki har da taba lafiya jiki?
Suhaima tace" Mommy ba Aliyu bane, yadawo ko ya naimeni, ko ma yagayamin yau zaidawo"
Hajiya binta tace" toh ke baby waya gayaminki yadawo?
Tace" daddy shi mana, yau yazo office da safe ya sanar cewa Aliyu na zuwa yau, Kuma na Kira number shi na Nan har 12 missed calls bai dauka ba"
Hajiya binta tace" ho babyna Kisha kuruminki, ai yakusan zuwa hannumu, mujuyashi son ranmu, bandai aure saura wata uku ba , toh ki kwatar da hankali kawai babyna"
Suhaima tace" Allah ko mummy na?
Tace" eh mana Kar damu"
Suhaima tayi murmushi tace " yawwa dats my best mum" ta rugumeta ,ta gyara kwanciya a gado mommy nata, taja bargo ta rufe jiki .
Hajiya binta tace" babyna badai bacci bako? Yanzu fa 4:00 ne dots, Kuma nasa bakiyi sallah azahar ba balle la'asar"
Tace" uhm uhm ni mummy ki kyalleni inatashi zanyi, ni na gaji"
Hajiya binta tace" toh baby na, na kyaleki sleep well" ta gyara mata bargo(waiyazubillahi🤦).
Su Aliyu suta zagaya gari har misali 6:30pm ,sanan suka tsaya a central mosque, sukayi sallah magarib, suka jira Isha , sanan sukama hanya gida, dun daddy shi nata kira, ya dawo gida hakama Wai yafita bada security ba, ya sallemi su haydar yace musu sai suyi waya.
Yana shiga , ya wuce parking lots direct, ya ije mota a