Showing 63001 words to 66000 words out of 70940 words

Chapter 22 - DOCTOR EESHA complete by J Hajara

J Hajara   

14 Jul 2024

7230

zai biku, toh tare zamuriga fita yawo, ba Wanda zai bi a acikiku, nagaya muku kenan"

Amir gani kallo da mummy ke bin Sadik dashi ne yabashi dariya yayi dariya yace" yadai mummy,karfa gari kallo miji wuyaki yayi ciwo" ya fada cike da barkwaci duk suka fashe da dariya..

Mufeedat tace" mummy ta ga miji cute boy ta rude, ta kasan daina kalloshi, please mummy ki juya Kai ki kalli gaba Kar wuya ya Miki tsami" duk suka sa dariya harda kyakatawa..

Mummy batace uffan ba, ama yanayi fuskar ta ya canza alamu ba lafiya, ta juya ga driver Tace" muje Driver Kar mubata masu Usman lokaci"

Driver kamar jira yake ambashi umarni ya tada motar, Usman ma ya tada nashi tundama su yake jira, suka dauki hanya uke.

Suna tafiya ciki kowane motar hirar kawai ke tashi, Essha duk ta ishe su hunaisat da surutu suna biye mata, ciki motar su Mummy kuwa hira sosai ke tashi, su khairat sai selfie kawai suke ta kashewa, har Sadik ya Saba dasu.

Ita kam mummy duk jikita yayi sanyi dagani fuskar Sadik, sai zance zuci kawai take ita daya tana tambaya kanta" Aya Essha ba canza mata yaro akayi ba ko, dun wanna tabbas ko makaho ya shafa sai yaji kamani yaro tycoon Dina a tare dashi, toh Wai mashi ina Yan kungiya da tare Dan Tycoon da kullum da masu tsarosu? Aya Essha ba yaro su ta dauka ba ko? Eya yallabai dayasa a kawo Video game dina eya bashi bane mahaifi Wana yaro? Da ga alama nagani Wanda ya kawo daya daga ciki securities su ne, wanan yaro baza dai ace kamanine ba, jinine ke aiki cus Blood is thicker than water, wayyo Essha yaushe kika canza ne? Maiye abun naki Dan daki ka canza ki ka dauko Wanda su ka fi karfi mu? Maiye daliliki nayi haka? Toh shi asali Danaki ina kika kaishi? Ko dai mutuwa yayi ne?ki ka dauko musu reino Dan ? Ta rike haiba " No wonder biri yayi Kama da mutum shiyasa tun baya arbain ko sau daya ba ta taba bashi muji muryasa ba, ohh Essha why why, maiyasa kika yi haka, in daddy ki yasani munshiga uku, Essha na Allah yasa dai baki canzaba" Nan taji hawaye Mai dumi su sauko mata tayi sauri ta goge..

Taji driver na horn ya katse mata tunani data ke ciki, taga har su karaso gida, tayi sauri Kara gyara fuskar ta, maigadi ya bude musu , suka kusa ciki.

Manya manya flat ne guda biyu a jere, tsari gini yayi, daya bagare Daddy Karami, na gefe haggu Kuma na Daddy, gida Babba gida ne ya tsaru sosai ba amagana.

Sugama parking duk suka fito, Walid da Amir suka kwashe Kaya zuwa ciki, Daddy karami, Anty zainab da hajiya duk suka fito tarbasu da fara'a a fuskokisu. Essha na gani hajiya da gudu ta je ta rugumeta harda guntu hawaye ta.

Hajiya tace" toh likita karasa ni kikeso kiyi Wana Shaka haka"

Essha tayi dariya ta sake ta rugume Anty zainab, ta tsuguna har kasa ta gaida Daddy karami, ya amsa sai samata albarka yake tayi yace" ina aboki nawane Yana ina?

Ta juya ta duba dube" Sadik, Sadik"

Usman yace" su khairat ana sauka suka fita dashi, Nima ko ganishi banyiba"

Anty zainab tayi dariya tace" kila rowa Dan zasu mana"

Mummy kam kala batace ba tayi gaba abinta.

Hajiya tace" kuzo munshiga ciki, matar Yayaki na na zuwa su gaida ki"

"Allah sarki hajiya da so kuwa nagasu kisan ayi biki ba na Nan" cewar Essha

Aina'u tace" Kar kidamu Zaki gansu har ki gaji"

Suka shiga ciki sashe Daddy, Hajiya sai matsifa take" Sadik yazo bai huta ba shaidanu yara harsu shiga dashi gari"

Essha tayi kewa sosai yau ganta ciki family ana hira sai taji sanyi a ranta, Delicious food kala kala aka tanadar mata kowa a guri nasan ta ci nashi tazama Yar lele, Big mum ta Kira sukasha hira sosai, suna Gama waya da big mum ta Kira Pooja, abun tausayi Arundh haryanzu kuka take, karshe ma Pooja kashe waya tayi hira da ba'ayi kenan ba.

Wurare la'asar duk kowa ya watse, masu aure kowa yayi hanya gida mijishi, aka barta dasu mummy dasu amir, sai a lokaci ma ta lura da canzawa mummy, gashi ta damu na Rashi dawowarsu khairat, tunda suka fita Basu dawo ba har ana neman magrib, hajiya dakata ta kirasu su dawo, sai da Isha suka shigo, su Sha fada sosai kuwa aguri Hajiya.

Amir dakashi ya bashi abinci, yamishi wanka ya shiryashi suka wuce masalaci. Har lokaci mummy Bata saki fuskar ba.

Essha na idar da sallah Isha ta shigo daki mummy da sallamata, ta samaita a daddurma tana ja carbi mummy ta amsa sallama, Essha ta karaso shigowar ta zauna a gefe mummy, mummy ta shafa Addu'a ta kalli Essha fuska, Essha ta gaida ta, ta amsa ba yadda ta saba amsa gaisuwarta ba, Essha Bata ji dadi haka ba murya a hankali tace" mummy ko dai laifi na Miki ne Naga tunda munka shigo ki ka canza?

Mummy ta kalleta shiru Bata Bata amsa tambaya ta ba can Tace" ina da magana dake ama ba yau ba sai gobe inda ki ka huta"

Essha taji gabanta ya fadi tace" mummy dafata dai lafiya ko?

Mummy zatai magana, sukaji an bude kofa an shigo da sallama duk suka amsa, Sadik ne Yana sanye da jalabiya fari fat, yamishi kyau, ya shigo da murmushi shi as usual hannu shi rike da iPad da packet din Laddu( alewa ne na kasa India)

ya nufi mummy yace" Granny I bought this for you, open your mouth, it's sweet it won't hurt your tooth"

Mummy batayi niyya murmushi ba sanda tayi taji tana matsifa son yaro.

Sadik ya bude baki yace" Granny Haaa?

Ya dauki laddu daya yakai saiti bakita, Mummy ta bude baki a hankali yasa mata, tana taunawa Tace

" Wai waga abun zaki shi yayi yawa ama akwai dadi" tanayi ta na lumshe Ido..

Sadik bai daiji abunda ta fada ba gani yadda takeyi da fuskar ne yabashi dariya.. Essha ta Mike jiki a sanyaye zata fita mummy ta dakatar da'ita

"Ki kaishi guri Daddy ku karami tun safe yake yake tambaya shi, yanaso ganishi"

Murya a sanyaye tace" toh mummy, Sadik let's go"

Sadik ya make kafada wai shi da mummy zai kwana, sanda tayi dagaske sanan ya binta, ya na daga ma mummy hannu, suna fita Mummy ta zuba tagumi ta rasa gane kan almari..

Essha na fita sukaci karo dasu Amir, Sadik ya musu murmushi ya Mika musu packet din Laddu sanan yace" good night uncle Amir, good night uncle Walid"

Duk suka shafai Mai kai, Amir yace" sis tare fa zamu kwanta ina Kuma za ki kaishi?

Tace" Mummy ne tace na kaishi guri Daddy k yanason ganishi"

Walid dayacika baki da laddu yace" sis yanaga yanayi ki yan canza lafiya daiko?

Ta gyada Kai ta Kama hannu Sadik sukayi sashe Daddy k, suna zuwa da Sallama suka shiga, Daddy k baiyi bacci ba idoshi biyu ya Kuna NTA news @10 Sadik da gudu yaje ya haye cinyarshi, Daddy k yayi murmushi yace" wash aboki zaka karyani, sai yanzu iyaye naka suka dama mun gaisa ko?

Essha tayi murmushi tace" ai daddy aguri ka ma zai kwana, ni na wuce sai da safeku"

"Toh Likita Allah yatashemu yamiki Albarka"

Ta amsa"Amin daddy"

ta wuce side nasu ta Tara dasu Amir zaune su Kuna Tasha sport suna kallo tace" bros sai da safe ku"

Walid yace" sis wait da Allah?

Ta tsaya tace"yadai ?

Yace" Gobe in Allah yakaimu zamu fita da boy"

Amir ya Mike yace" yes sis mantawa nayi, bagayamiki ba, gobe zamu fita yawo dashi kinsa Sunday free time ne Monday zamu koma school, please grant us that permission mufita da boy kinji?

Tayi dariya tace"Amir Sadik fa Dankune, ai basai ku tambayi izini naba, Allah yakaimu gobe, ina da ina zakuje?

Walid yace" thanks sis, ShopRite kawai zamuje, movie munkeso kallo a cinema din guri da za'a fara 2pm, toh zamuje 9am Boy yasamu fun kafi time din yacika"

Yana Kira ShopRite Essha taji gabanta ya fadi, sai taji batason tafiya, bayanda taiya tace" okay Allah yakaimu sai da safe ku"

Suka amsa da bye sis mungode..

Walid yayi ihu murna yace" ye bro we will rock with your new car"

Amir yayi murmushi yace" bakada matsala yaro in aka wanane"


Essha na koma daki ta kwanta Sam Bata iya runtswa ba sai juye juye kawai take, Bata ki ace gari ya waye ba taji mak mummy zata gayamata, magana aiki da zata fara zuwa gobe ma bai damaita ba cus she knows her work tafi damuwa taji abunda Mummy zata fada mata.

Karshe toilet ta fada ta Dora alwala ta fito ta Soma nafila tana roko Allah ubangiji ta ya kawo mata sauki a alamurata, har Asuba tana idar da sallah subhi ta Kara gyara kwanciya bacci barawo ya saceta.

Tana ciki bacci ne taji ana tashita"mum wake up its nine"

Ta bude Ido a hankali, Sadik tagani a gefeta ya Sha wanka ya hade, jikishi sanye yake da white t-shirt da red jeans trouser,kana yasha gyara, kafarshi sanye yake da wata hadadiyar sneakers red mai, gefe takalmi a zangaya shi da white line, hannushi rike da p-cap red, gaba aljihu rigashi kuwa puzzle game ne.

Essha tayi murmushi tace" you guys are ready ko?

Ya daga mata Kai, ta Mike ta jawoshi gefeta tace" now say Mum's rules let me hear"

Yayi murmushi yace" rule number 1: Start everything with Bismillah, rule number 2, Don't talk to strangers, rule number 3, always be obedient, don't be sturborn"

Tayi murmushi tace"excellent my boy , hi five? Ya Mika mata hannu suka tafa..

Amir yashigo shima ya hade a ciki manya kanya yayi kyau yace" good morning sis?

Ta amsa da kai, yace" mu zamuwuce sai mun dawo, boy common let's go, sis mummy na kiraki"

Sadik ya sauko ya rike Mai hannu, Essha na kallosu gabanata tsanata faduwa yakeyi tace" Amir da Allah kuladashi kansa Sadik da kirniya"

Yace" sis Kar kidamu he's safe inshallah"

Itama ta sauko tasa teddy slippers nata ta biyosu, ta cima su khairat na hada table na breakfast, suka gaisheta ta amsa, ta gaida mummy har kasa ta zauna a gefeta, Sadik zasu fita ya dawo da gudu ya Bata peck a goshi yace" bye Granny, bye mum"

Ta daga Mai hannu tana murmushi..


Su Amir suna tada motar suka dauki hanya Abj, Sadik na gefe window sai bin kasamu namu yake da kallo, suyi tafiya awa daya suka isa ShopRite
Suna shiga ciki, Walid ya gyara ma Sadik zama p cap nashi, suka samu table suka zauna, Amir ya musu order su ice creams, drinks da su snacks, suna Sha suna hira hankali kwance..


Gidan Tycoon
*************************
Ammi ne zaune, cinyar ta Sofia ne kwance wow su Sofia angirma, sai zuba ma Ammi shagwabe take son ranta, Isa na zaune a kan carpet, Mami na kan dinning ita da Idrees da Rahma suna having breakfast, gefe Rahma Kato teddy ne dayayita hudu Mai kyau.

Ammi sai hararata take cike da matsifa tace" wlh Isa bakaisa ba, Kuma baka kyauta ba, Rahma ne zaka kawo mata tsaraba Teddy, Sofia Kuma hannu rabbana, toh bazai sabu ba, duk yanda zakayi dai ka kakawo mata nata, asamu zama lafiya"

Isa yace"Ammi kiyi hakuri, Sofia fa ta girma, Kuma ta girme ma Rahma kiga kenan dole a nunamata ta girma"

Sofia ta fashe da kuka tace" kiji fa Ammi, Yaya Aliyu tare yake tsaya mana abun, shine zakacemu na girma, kaje har Dubai kazo ma Rahma da Teddy nikuma Empty wlh Ammi da sake"

Mami tace" common shut that ur stupid mouth, ki girma bakisan ki girma ba"

Rahma tasa dariya tana ma Sofia gwalo..

"Ammi ki ganta ta na min gwalo ko?

Ammi ta Mike a fusace taje dinning ta dauko Teddy tace" tunda haka ne kema ki rasashi kenan har ki iya mata gwalo"

Idrees yace" yihakuri Ammi ki bar mata, itanefa autar, Sofia Kar ki damu za'a siyo mata nata"

Ta baka Mai harara tace" when?

Isa yace"Ammi duk ranar Dana koma"

"Baku isaba, yau Dina nakeson kasiya mata nata inhar Kuna neman zaman lafiya, toh yau nakeson Naga autar na da Teddy"

Mami tayi dariya taji tanakara son Ammi, har taiya fifita Yar kishiya akan nata, Allah sarki Ammi Mami ta fadi haka a zuciya ta, tace" Ammi ki shagwaba ta dayawa, Teddy na fa tana dasu bawai ta rasa bane, toh ima irishi takeson , ai'na za'a samu kalla Teddy Mai girma haka?

Sofia ta shagwabe fuska tace" Ammi akwai a ShopRite Wanda ma yafi wanan girma"

"Yawwa tashi kuje ya sanya Miki"

Jin Ammi ta fadi haka ta Mike da murnata ta dauko gyale ta yafa ta kalli Rahma ta mata gwalo tace"Kuma zanyi waya da Yaya Aliyu yazomin da Sari, zance Kar ya kawomiki"

Mami tace"oho dai"

Isa ya Mika ya na hararata Yana kwafa, Ammi tagani tace" lah Sofia maza dauko min mayafi na rakaku danaga Alama zai ita karya Mike a hanya"

Ya marairace fuska yace" haba Ammi ba abunda zan matafa"

Tace" yi min shiru nasan halika Sarai tashi muje"

Sofia ta Mika mata mayafi ta yafa, zasu fita Mami ta Mike Tace" da Allah kuda jirani na dauko handbag Dina, akwai small Shipp danakeso yi"

Sofia tana tafiya tace" Mami Meet us in the car, mun muyi gaba"

Bada jimawa ba, Mami ta fito suka shiga motar, motoci uku na guards na baya dasu masu rakiya, duk aka tada motoci zuwa ShopRite, suna isa , aka bude musu,Sofia tayi sauri ta shiga tayi hanya guri Saida Teddies da aka kilace su a glass manya manya dasu, Su Ammi na biye da ita, Mami kam guri shopping ta nufa, guri Saida Teddies badai nisa daga guri zamasa Sadik, Mami hartagama shopping, Sofia na na guri zaba teddy ruwa ido yahanata zaba da wuri, Isa na gefe yanaji kamar ya bugeta ba hali ga Ammi ta kasa ta sare tana kareta...


Sadik vannila ice cream ne a gabashi baiwani Sha sosai ba puzzle game na Mickey mouse yake ta hadawa...

Walid dake zaune ya Mike yace" bros zanje na sanyo tickets na movie di na kafi ya kare, zanbiya Kuma. Na sanya coins dun zamuyi game da boy"

Amir yayi murmushi yace"yawwa Walid Kama kana Raina, abunda nakeson fada kenan, sai ka dawo"

Walid ya wuce.

Amir ya Mike ya kalli Sadik yace"Boy let me use the toilet, don't go anywhere" ya kada Mai hannu

Sadik ya kada Kai Yana murmushi, Amir yasha fa Mai Mai yace" sai na dawo, good boy"

Amir ya wuce suka barshi shi kadai zaune, afi mintina acikisu babu Wanda ya dawo, Walid ya sanyo tickets, gurin Sanya coins ne a cika shiyasa baidawo da wuri ba, Amir Kuma Yana fita daga toilet ya hadu da wani course mate nashi sunata zuba hira, a tunanishi Walid ya riga yadawo shiyasa ya kwantar da hankali shi suka cigaba da hira..

Sadik yahada puzzle har yagaji, shiru shiru aciki su babu Wanda ya dawo, har ya fara gyagadi, yajigana da chair dayake, har yayi bacci..



***********************

"Wai haryanzu bakusamu teddy da ya muku bane? Ammi ke Kuma ki tsaya biye ma shirmata" cewar Mami..

Isa ya harari Sofia yace" wlh kuwa Mami, ni da friends Dina zamu fita fa, ama Wana stupid girl din tana Bata min lokaci"

Sofia ta tura baki zatayi magana, Ammi ta tareta tace" yi shiru kallesu, natsu ki zabin Wanda ya ranki keso"

Sofia tayi murmushi tace"yawwa Ammi na"

Mami tace" uhmm kafi kugama dai bara na nemin guri na huta kafi ku Gama shirmeku"

Ammi tayi dariya tace"dayafi Miki"

Mami ta juya tabin gurin da kallo, bawasu mutani sosai a downstairs din anfi yawa a sama, tables da suka jera, two table's ne daya ma an cikashi, ta kalli damata guri table dinsu Sadik, daka chair din Sadik ya Bata baya, Bata ga fuska yaro dake zaune a Kai ba tace" yawa nasamu guri zama, bazaiya juri tsayuwa ma shirmena na"

Ta karasa table din hankali ta na kansu Ammi, Mami tana murmushi, tana Alfahari da ita, a matsayi Yar uwa ta dauke ta ba kishiya ba,ta ja chair ta zauna tana kallo Sofia nata zuba shirme Ammi na biye mata, Nan taji Kara faduwa Abu kusa da'ita, ta Kai duba ta kasa taga Mai yafadi taga p-cap ne da puzzle game na robar , su fado lokaci daya ta tsuguna ta kwaso tace" Allah sarki Dan samari ba........magana makale mata yayi , gabata yayi muguwar faduwa sakamako tozali datayi da fuskar Sadik daketa shara baccisa Hankali kwance, Ido Mami ta ware sosai Dan ta tabbatawa kanta abinda ta gani, da sauri cike da razana ta goge idota" Wai son ne kemin gizo Yana karami ko dai maikamadashi ne?

Jiki Mami na rawa ta Mike taje kusa da Sadik ta shafi fuskarshi abun mamaki ma Dan digo baki karami dake fuskar son nata duk yanadashi, abun da yakara razana ta Yana bacci murmushi dimples nashi suka Kara lotsewa gabadaya, jiki ta na rawa takai hannu ta tabo dimples din murya kuka tace" inalilahi waina ilaihi raju'un, hasbiyalahuu waniimal wakil, walahi son ne, Wana sonane, ko dai gizo yakemin ne Yana karamin?

Takara murza Ido da kyau ta bude taga tabbas ba gizo idonta kemanta ta fashe da kuka......





.. More comment more typing ❤️❤️❤️❤️❤️




Love you guys 💛💛💛



👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
*DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️



*WRITING BY*
*J Hajara*




🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️


*M.W.A*


_Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
____________________________




6️⃣8️⃣


Tycoon jiki na Bari cike da tashi hankali ya ciro wayarshi a aljihu shi ya bude ya dialing number Aliyu, buga daya Aliyu yayi picking, ya Soma gaidashi cike da girmamawa.

Tycoon bai amsa ciki baci rai yace" Aliyu kana ina ne?

Aliyu yaji tambaya a bazata yace" Daddy ina India mana na fadama ko ka Manta ne? Lafiya dai ko naji murya ka haka?


Tycoon tambaya ba murya na rawa yace" inasa gani ka, na baka na da three hours Aliyu ka dawo gida"

Aliyu ciki rudewa yanayi da daddy nashi yake sounding

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login