Showing 168001 words to 171000 words out of 189977 words

Chapter 57 - BUZU BOOK1 COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Jan 2026

969

yanayin da suke.
Siyama na ta corridor ɗin  falon saman bene, tana hango su. Mutumin da ba ya magana, balle ya baka wata dama a tattare shi, shi ne yake wannan abubuwan haka.
Ya ajiye tiyon, ya ƙarasa gurin Nana, ya rungumo ƙugunta, da jiƙaƙƙun kayan jikinta, ya fara kissing din ta. A tsorace ta ce "Sayyid, kar a ganmu fa, kuma ka ɓata alwalarka".
"Bai kamata a ce kullum a ɗaki muke yi ba, yin abubuwa a wasu guararen, yana sanya wa zuckata nishaɗi"
A tsorace ta ce "To ai banda irin wannan"
Ya riƙo hannunta, suka nufi ɗakinsu. Sallar magariba sai da Isha'i suka haɗa su ka yi, a ɗaki wajen ma ya ƙi fita, sai dai idan an yi horn,ya je ya buɗe, ya dawo ya liƙe mata.
Siyama kuwa zaman dirshen ta yi a kan ɗaya daga kujerun Falon, zuciyarta na raya mata abubuwa daban-daban, a kan Sayyid.
Babu babban abin da ya tsaye mata, irin sumbatar da ta ga yana yi wa Nana. Wani irin takaici mara misaltuwa ya mamaye mata zuciya. Sam Nana ba ta dace da samun irin wannan damar ba  Tana ji a jikinta, za ta iya kashe ko nawa ne, ta raba shi da gadi, muddin za ta samu abin da take so a tattare da shi.

****
Alhaji Fatuhu kuwa, al'amura sun rincaɓe, duk iya ƙoƙarin likitoci suka yi, amma suka kasa gano abin da yake damunsa. Lokaci lokaci, ya kan yi jijjiga da kururwar jikinsa na wani irin matsanancin ciwo, mara misaltuwa. Wasu na zuwa duba shi tsakani da Allah su tausayawa masa, wasu kuwa gani suke yi, zafin abin da ya faru ne. Ya gaza yin tawakalli.
Ga kadarorin sa, ana ta ɗagawa ana sayarwa, da an ɗaga kadararsa, an karyar da ita, abokansa na kusa da shi, suke yin wuf su saye da arha.
Sai dai duk lalacewa, ba a rasa na Allah. A hakan an samu waɗanda suka tausaya masa, suka yafe masa kuɗaɗensu, aka kafa gidauniyar neman tallafi, domin taya shi biyan basussukan da suka narke masa a ka.
Gaba ɗaya Fadila ta fita daga hayyacinta, duk ba ta cikin nutsuwarta. Ba ita ba, ita kanta uwargidansa da yaransa duk hankulansu a tashe yake, duk da wani ɓangaren na Hajiya Suwaiba, ta zuba ido, dan ta san babu lallai Fadila ta ci gaba da zama da shi, tun da dama tun farko tana kyautata zaton saboda kuɗinsa ta aure shi, yanzu kuma ga jarrabawa ta zo.

Hajiya Sa'a cikin damuwa ta kalli Jamila ta ce "Jamsy, ko za ki raka ni Asibiti, gurin dubiyar nan"

Jamila ta girgiza kai ta ce "A'a a dawo lafiya, ba na son zuwa na ga abin tausayin nan, ranar da muka je da ke, sai da na yi kuka, gaba ɗaya iyalansa sun bani tausayi"

Hajiya Sa'a ta ce "Ke yarinya, ki ko yi dakiya, ba komai zai din ga razana ki ba, ko kuma ba ki tsoro ba
Ai ba a samun nasara da tsoro ko tausayi, kamar yadda nake yawan gaya miki. Na ga Abba bai tashi daga bacci ba, idan ya shigo ki ce masa na koma gurin duba kawunsa"

Jamila ta ce "To a dawo lafiya"

Bayan fitar Hajiya Sa'a, mata sun zo sayen kaya, kasancewar a bayan business take fakewa ta ci karenta, babu babbaka, ya sanya da yawan jama'a ba su san ainihin abin da take aikatawa ba".

Wayarta ce ta yi ƙara, ta ɗaukko ta ɗaga.

Cikin muryar bacci ya ce "Ƙanwata, kin shigo ne?"

Jamila ta ce "Eh"

"Akwai abin da zan karya ne? Ko kun cinye?"

"Ai ni daga gida na karya, ka sayo buredi, na soya maka ƙwai, na san ba za a rasa shayi a flask ba"

Ya ce "Ok to na gode"

Kusan mintuna talatin sai ga shi ya shigo da sallama.

Jamila ta kai masa kayan breakfast ɗin ɗaya falon,  kasancewar na farkon a cike yake da mutane.

"Ina kwana" ta gaishe shi.
"Lafiya ƙalau. Ina Mummyn ne?"

"Ta tafi duba kawunka wai"

Ya ce "Bari na yi, sauri nima zan je na kuma duba shi, yana jin jiki sosai "

Cikin damuwa Jamila ta ce "Dan Allah ka saka baki, Mummy ta taimaka da wani abun, a biya masa bashin nan. Ko ba duka ba, na yi mata magana ta ce babu ruwana"

Yayi murmushi yana ajiye cokalin hannunsa ya ce "Tun da ta ce babu ruwanki kawai babu. Nima babu abin zan iya yi a kai. Kuma kema ki iya takun ki ƙanwata, Mummy mahaifiyata ce, amma wasu abubuwan da take yi ba na gane musu" Jamila ta ɗan yi shiru, sannan ta jinjina kai ta ce "In sha Allah na gode sosai "

Ya yi murmushi ya ce "Kayan nan sun yi miki kyau sosai "

"Kai ma ka yi kyau, bari n sallami masu sayen kaya" ta fice daga falon. Duk da ba wani sakar masa fuska take yi ba, saboda ta fuskanci take-takensa, zai cewa yana sonta, ita kuma sam bai wani yi mata ba.
Ba shi tsawo sosai, kuma ba shi da kauri, baƙi ne mai matsakaicin tsayi, sai ƙasumba da ya tara. Sai dai kuma sanyin halinsa ya sanya take ɗan kula shi.

Hajiya Sa'a ta je ta tarar da ɗan uwanta a gadon Asibiti, cikin yanayi mai ban tausayi.
Bayan ta gama duba shi, ta kalli Hajiya Suwaiba, ta ce "Wai ni ban ga abokiyar zaman ki ba fa"
Hajiya Suwaiba, ta kwaɓe baki ta ce "Ba ta daɗe tafiya ba"

"Ohh wancan zuwan da na yi, na tarar da ita hajaran majaran ai kamar gaske. Amma mu na nan mu na zuba ido, za ta zauna ne, ko kuma za ta yi gaba tun da babu abin hannu yanzu."

"Oho mata, ita ta sani dai"

Gaba ɗaya Hajiya Suwaiba, ta gaji da surutun da Hajiya Sa'a take yi mata, ita ba Fadila ce a gabanta ba yanzu lafiyar uban 'ya'yanta ce ta dame ta.

Su na nan zaune, sai ga Fadila ta yi sallama ita da mahaifiyarta. Hajiya Sa'a ta amsa da ƙyar, Rauda babbar 'yar Alhaji Fatuhu ce ta amsa musu sosai, ta ce "Anty sannunku da zuwa"

"Yauwwa Raudah, ya jikin Daddy?"

"Da sauƙi, ai na zata hutawa za ki zauna ki yi? Na ga kuma kin sake dawowa"

Fadila ta ce "Hankalina ya ƙi kwanciya ne, na je gidanmu na yi wanka muka taho tare da Mama" suka gaisa da su Hajiya Sa'a, sai kallon ƙasƙanci take yi wa mahaifiyar Fadila. Sai dai ba su tanka mata ba.
Mutane daga gurare daban daban, su na zuwa duba shi, sai dai wasu lokutan, ba ma ya gane wanda suka zo kansa baki ɗaya.

BAYAN WATANNI UKU.

Nana ce a zaune, ta ja uban tagumi, tana kallon Sayyid, da fuskarsa ke ɗauke da matsananciyar damuwa.

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid dan Allah ka cire damuwar nan daga zuciyarka, ka ga nima haƙuri na yi"

Ya ɗago ya kalle ta yana ajiyar zuciya ya ce "Shikenan burina na son gina zuriya tare da ke, ba zai cika ba kenan? Ba zan samu mallakar Ahali ba kamar yadda nake fata. Na uku fa kenan yana zubewa"

Duk da abin a dame ta ita ma, amma ta daure ta ce "Sayyid mu yi haƙuri, mu bar wa Allah, yana sane da mu, kuma zamu samu wanda zai tsaya in sha Allah, amma ka daina saka damuwar abin a ranka ya dame ka haka"

"Ba ni nake saka damuwar ba, zuwa take yi, ta yi mini nauyi ta hana ni sukuni, na rasa yadda zan yi amma abin yana taɓa ni sosai da sosai"

Ta rungumo shi jikinta, tana shafa bayansa a hankali ta ce "Na sani, duk mu yi haƙuri, babu yadda muka iya da ikon Allah. Kuma ka sani ma ko yanzu akwai wani ba mu sani ba"

Ya ɗan ja numfashi ya ce "Ni har fargaba nake yi, ki ce mini akwai cikin, saboda daga baya sai ki ce mini ya zube".

Nana ta ci gaba da rarrashin sa, "Ka yi haƙuri Shugaba, Allah zai bar mana, in sha Allah sai na haifo maka santalele ko santaleliyar jaririya"

Ya yi murmushi ya ce "Allah ya sa ma vie"

"In sha Allah " ta yi maganar fuskarta, ɗauke da murmushin hali, domin kwantar masa da hankali da sama masa nutsuwa.

Ya gyara kwanciyar sa ya ce "So nake mu bar gidan nan, ba na son zaman a cikin sa. Yarinyar nan tana takura mini, kuma hakan barazana ne ga zaman lafiyar da yake tsakanina da ke"

"Ai na riga na fahimce ka Sayyid, ka ga haryanzu su Sule suna nema maka wani gurin ne, idan muka bar gidan nan, bamu da wani gurin da za mu tafi. Ka yi haƙuri Allah ya fi ƙarfinta ka manta da ita kawai".

Ya ɗan girgiza kai ya ce "Shikenan, bari na je masallaci"

Ya tashi ya yi alwala, ya fita Nana ma ta tashi ta yi salla. Ko a yanzu ma tana kyautata zaton wani cikin ne da ita, sai dai ita kanta a cikin fargaba da damuwa take. Dan da cikin ya samu ba a zuwa ko ina, yake zubewa.
Abin ya dame ta sosai da sosai, kuma ta fi danganta hakan da Ƙaisar ne. Ga shi ƙawarta Siyama, da take hira da ita ta ji daɗi, ta bar gidan wai an kai ta Abuja, gidan Yayar Babanta a can za ta ci gaba da ganin likitan ƙwaƙwalwa. Tun da ta yi ɓari na farko, ta ga yadda yake, ko ta yi ma shiru take yi, ba ta sake gaya wa ko Ummi ba. Sai dai ta yi abin ta a ɗaki daga ita sai shi.

Yana tafe a hanya ya nufo gida, Siyama ta yi burki da motarta a gabansa. A dole ya ja ya tsaye ya kalle ta.
"Abin ƙauna, ka hau mu ƙarasa gidan, tun da can ka nufa?"

Ya zagaya ya fara ƙoƙarin kaucewa motar ya wuce, amma ta sake shan gabansa da motar.

"Ka hau mu tafi na ce. Duk wannan sunkuyar da kan da ka ke yi, da ƙoƙarin kaucewa buƙata ta da ka ke yi, ba zai hana na ci gaba da bibiyarka ba, da neman cikar burina ba. Ina sake gaya maka, idan ka amince da abin da nake so, zan baka kuɗi masu tarin yawa. Zaka bar aikin gadi, za mu yi rayuwa ma cike da farinciki da nishaɗi. Ita ma matar taka zan bata kuɗin da za su wadace ta, da ba za ta ji zafin rabuwar da za ku yi ba. Ka yi tunani ka duba mafitar ka"

Ya ƙara takawa ya matsa daf da jikin motar, ya sauke rawaninsa ya zuba mata ido. "Na saki matata, za ki bani kuɗi ko?"

Ta jinjina masa kai tana murmushi. Ya ɗan ja da baya, ya kalli layin babu kowa, kawai ya saka hannu  ya shaƙe mata wuya. Ƙoƙarin ihu take yi, amma ta kasa idanunta suka firfito waje, ta fara kokowa da numfashinta. Ta ga kamaninsa sun canza, ƙwayar idanunsa ta sauya, ya canza kamanni zuwa tsoho tukuf, tun tana ƙoƙarin ƙwatar kanta daga hannunsa, har ta gaza jikinta ya saki ya yi sanyi ƙalau.

08081012143
CHAPTER 47

Wayar hannun Nana, ce ta fara ringing, ta yi shiru, tana kallon lambar, tamkar kar ta ɗaga sai kuma, ta ɗaga tare da yin sallama.

"'yan matan adon gari"

Gaban Nana ya faɗi, jin muryar Alhaji Zailani ta daki dodon kunnenta. Jikinta na tsuma ta ce "Waye?"

"Bai kamata ki tambaye ni ba, na san kin san waye. Kiranki na yi na ƙara yi miki tuni. Hankalina ya dawo kan ki baki ɗaya. Tun da kin bujirewa buƙatata ta laluma, to za ki biya mini ta ƙarfi da yaji.
Ba zan taɓa barin ki ba sai buƙata ta biya, dama ta biyu na kira ki na baki, ko dai ki amince, ko kuma sai na tagayyara rayuwar ki, daga ke har wannan sakaran mijin naki".

"Yanzu da auren nawa ka kira ni, ka ke gaya mini wannan maganganun? Da aurena me ka ke so na yi maka?"

Alhaji Zailani ya ce "Babu ruwana da aurenki, buƙatata ce a gabana"

Nana ta ja ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, ga fili ga mai doki, idan ka ga dama kar mu kwana a raye daga ni har mijin nawa"

Ba ta gama gane me yake faɗa ba, ganin Sayyid ya faɗo ɗakin, kamar ba ya gani ma sosai. Jefar da wayar ta yi ta nufe shi, "Sayyid Meyafaru?" Ya ture ta ya nufi kan katifar, ya faɗa ya kwanta.

Ta bi bayansa, ta taɓa jikinsa ta ji babu zafi, amma ya lumshe idanunsa. Ta kwance masa rawaninsa, ta ɗan gyara masa kwanciyar sa.

"Sayyid" ta yi maganar tana leƙa fuskarsa, amma bai amsa ba, kuma bai yi magana ba.

Ta ɗauki wayarta, za ta kunna masa karatun Alkur'ani, amma ta yi shiru tna kallon wayar, gabanta na faɗuwar, kar ta je Alhaji Zailani ya kuma kiran wayar ya ɗaga, ba ta san me za ta ce masa ba.
Tun da ya ma fi ta amfani da wayar,  ita wayar ba wani damunta ta yi ba. Daga jin litattafai, sai kallo shi ma sai lokaci lokaci.
Da sauri ta saka lambar Alhaji Zailani a blacklist, tare da fatan Ubangiji Allah ya tsare su daga sharrinsa da mugun nufinsa.

Ga shi kwana biyu ba ta je gida ba, tana son zuwa ta gaida Baba, amma ba ta son zuwa ta tarar da damuwoyin gidansu, da ba sa ƙarewa.

Ta saka Sayyid a gaba, kawai tana kallonsa, tare da tunanin abin da ya same shi, ya dawo a haka.

Sai wajen sallar Isha'i ya tashi, bai ce mata uffan ba, ya yi salla ya zauna ta zuba masa abinci ta ba shi.
Yana ƙoƙarin fara cin abincin, aka fara horna, ya tashi da sauri, ya fita waje. Ya buɗe gate sai ga Motar Hajiya Halima, Nuradeeni yana jan motar, Hajiya Halima na baya ita da Siyama.

Nura ya ce "Ba ka san abin da ya faru ba ko? Wallahi Siyama aka gano a bayan layi, a sume a cikin mota, na raka Mami unguwa, wani maƙwabcinmu ya gano ta, ya kira mu"

Ya girgiza kai cikin tausayawa, ya ce "Allah ya kiyaye"

Su ka shige da motar, ya rufe ƙofa, bayan ya koma ɗakinsu, ya gama cin abincin yake ba wa Nana labarin abin da ya faru.

Ta ce "A ina aka ganta?"

"Ya ce a bayan layi ne"

Nana ta ce "Allah sarki, abin mamaki"

Sai da ya gama cin abincin sa ya ƙoshi, ya sake kallonsa ta ce "Ka gaya mini tsakani da Allah me ka yi mata?"

"Wa?"

"Siyama" ta bashi amsa.

"Babu"

Ta yi murmushi ta ce "Haba Dattijo, a duk lokacin da ka kawo mana ziyara, ina sani fa. Ka gaya mini me ka yi mata?" Ya ɗago ya ƙura wa Nana ido.
Ta sunkuyar da kanta, ta ce "Ka daina kallona haka, ka san ba zan iya haɗa ido da kai ba, ka gaya mini me ka yi mata. Kar ka sanya a zo ana zargin mijina da aikata laifin da bai san hawa ba bai san sauka ba"

Ya yi gyaran murya ya ce "Duk abin da zan yi, na gama aikina a kansa, ba zan bari a cutar da shi ba, sai cutarwar da na san, za ta yi miki raɗaɗi a zuciyarki da gangar jikinki, duk da na san hakan ba zai sanya na huce, daga mugun abin da ku ka yi wa zuriyarmu ba?"

Magana Nana take son yi, amma tamkar an saka igiya an ɗaɗɗaure ta, ta ji bakinta ya toshe, ko magana ta kasa yi.

Ta ɗauki tsawon lokaci a haka, kafin ta ji an taɓa ta. Kamar wadda aka yaye wa wani nannauyan bargo, ta ɗago a razane ta kalle shi.

"Lafiya?"

Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya saka hannunsa ya shafo gumin goshinta ya girgiza kai ya ce "Meyafaru?"

"Bakomai fa. Amm Sayyid ka je masallaci ko?"

"A'a a daki na yi salla, na yi bacci, ba ki tashe ni ba"

"Ka haɗu da Siyama?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Eh"

"Meyafaru?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba zai yi miki daɗi ba, ki bari kawai"

Ta ce "A'a ina son ji, ai ni na tambaya"

"Ba zan faɗa ba. Ina gaya miki za ki faɗa"

Ta yi murmushi ta ce "To ya zan yi, idan ban yi kishin mijina ba, amma na bar maganar"

Ya ɗan yi miƙa ya ce "Ji nake kamar ba ni da lafiya, zo ki danna mini bayana"

Ta ce "To"

Ya hau kan katifar ya kwanta, ta din ga yi masa tausa a hankali, tana matsa masa jikinsa, ya lumshe idanunsa ya hau bacci.

Bayan ya yi bacci, ta tsallake shi, ta je ta yi wanka, ta canza kaya ta zo ta kwanta a kusa da shi.

Tana kwanciya ya matsa kusa da ita, ya rungume ta.

"Shugaba, baccin kenan?"

Ya cusa fuskarsa a wuyanta, yana sauke numfashi ya ce "Duk baccin da nake, ki na zuwa na tashi".

Ta yi murmushi ta ce "Abokin ruhina, to yaya ruhin nawa na jikinka?" Ya yi dariya ya ce "Yana nan ƙalau, cikin aminci da salama"

"Ba wata salama, bayan wata na sonka"

"To ai ni ba na sonta"

"To idan ka fara sonta fa? Tun da fara ce, kamar kai"

"Nana" ya kira sunanta.

"Nana kuma? Au har ma na tashi daga rayuwar taka na koma Nanata, gatsal?"

"Ai har abada ke rayuwata ce, nutsuwata, mai rayuwa da ruhina a jikinta. Idan zuciyarki ta sosu, a jikina nake ji. To ta yaya zan bar abin da zai din ga ɓata miki rai. Ita ma daga ranar da ta san ni mahaukaci ne, za ta daina son nawa"

Nana ta yi dariya ta ce "Da alama hausa indiyar nan da ka ke kallo, haddacewa ka ke yi, wannan kalaman masu ɗauke da falfasa ai ba wuya za ka saka mutum ya fara sonka".

"es-tu sûr(kin tabattar?"

Ta ce "Yes am very sure"(Eh na tabattar)

"Ma sha Allah, nice to hear that"(Ma sha Allah, na ji daɗin jin haka"

Ta waro ido a cikin duhu, tamkar yana ganinta ta ce "Turanci kuma? Wai yare nawa ka ke ji ne?"

"Biyar" ya bata amsa kai tsaye.

"Wanne da wanne?"

"Da Nana, da Asma'u, da Husna, da Asmy, da rayuwata, da Duniyata, da Ruhina. Kai ashe yarukan sun fi biyar ma"

Ta ja dogon hancinsa ta ce "Wai duk lokacin da nake so mu yi magana serious, sai ka mayar da maganar wasa. Idan kuma kai ne ka ne so mu yi magana kuma, sai ka haɗe rai"

Dariya ya din ga yi, da jin abin da ta faɗa ya ce "Sayyid, shugaba, ko kin manta sunan da ki ka saka mini ne?".
"Shugaban da babu masarauta"
"Ai a cikin Duniyata masaurata take"
Nana ta ce "Wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login