Showing 30001 words to 33000 words out of 189977 words

Chapter 11 - BUZU BOOK1 COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Jan 2026

957

ko sunansa ba ta ƙaunar ji.
A can makaranta da take koyarwa, mahaifin ɗalibinta Muhsin, ya fara damunta, kullum ya zo ɗaukar Muhsin, sai ya ce zai rage mata hanya. Ga shi ba ta da damar tafiya, sai an gama zuwa ɗaukar yaran gaba ɗaya, kuma kullum Muhsin ne ƙarshen zuwa ɗauka.

Yau bayan ta dawo daga islamiyya, Yamma liƙis, Baba ya shigo fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce "Ke Nana, ki je ga Saleh can a waje yana jiranki" gaban Nana ya faɗi.

Imran ya tashi ya nufi hanyar fita, Baba ya ce "Kai malam ba kai fa kai na ce ba"

Ya waiwayo ya kalli Baba ya ce "Ni akwai gurin da zan je" ya fice.

"Ke kuma Nana ba magana nake yi miki ba?"

Jiki a sanyaye ta ce "Ina zuwa, kaya zan canza"

Imran kuwa yana fita ya tsaya ya ƙarewa Saleh kallo, ya ce "Kai ai kamar na sanka a gidan Ummi"

Saleh yayi murmushi ya ce "Ba kama ba ce ba ni ne ai"

Imran ya ce "Bala'i ashe idan na je neman aure nima za a bani, duk da ana ganin ba ni da saiti. Kai yanzu saboda ka raina wa kanka hankali gurin ƙanwata za ka zo neman aure a haka? Kalli wani shegen wando a jikinka ba ka san saukakkiyar Alqur'ani ba ce, kuma mahaddaciya ba?"
Saleh yayi saroro yana kallon Imran.

"Eh kalle ni da kyau, wallahi sai na je har gida na kasa wa Ummi warning, mai ku ka mayar da Nanan, wallahi ta fi ƙarfinka me za ta yi da ɗan jagaliya kamar ka?"

"Saboda na zo ƙofar gidanku neman aure, ka ke gaya mini abin da ka ga dama?"

Imaran ya ce "Malam gaskiya nake gaya maka, ba ka cikin irin mutanen da Nana za ta so da aure, a tsarinta tana son mutum mai kamala da sanya manyan kaya kuma...

Shiru ya yi, ganin Nana ta fito fuskar nan babu walwala.

Maimakon ya tafi sai ya ja ya tsaya, takaici ya hana Saleh magana, a girme ya girmi Imran amma ya tsaya yana gaya masa magana dan ya zo wurin ƙanwarsa.

Ya maze ya kalli Nana ya ce "Gimbiyata barka da fitowa"

Imran ya kwaɓe baki yana jiran me Nana za ta ce. Ta ɗago suka haɗa ido.

"Amma ko za ka bamu wuri mu yi magana" Saleh yayi maganar yana kallon Imran.

"In ba ku guri na je ina? Ka zo wurin ƙanwata zance da crazy jeans, meye banbanci na da kai, da ake cewa ba ni da hankali?. Kai wallahi ba za ayi zancen nan ba, ke koma gida ranar da ya shirya neman aure, yayi shigar mutunci ya zo"

Babu musu Nana ta shige gida, dama haka take so. Baba na ganin ta dawo ya tambayi ko lafiya?.

"Imaran ne ya ce na dawo gida"

"Ki dawo ki yi masa uban me? Idan ba ki yi aure ba zai aure ki ne?"

Ya nufi waje yana faɗa, ya tarar da Imran ya tare ƙofar gida yana cewa Saleh idan gidan ubansa ne, ya ture shi ya shiga da wannan shigar tsiyar.

"Imrana wai ba ka da hankali ne? Meye haka?"

"Baba, wai ya za a ɗauki aure a ba wa mutumin da zai zo neman aure, yayi ido huɗu da sirikinsa da yagaggen wando, da tarin suma kamar shekararren zakara. Kuma a gaya masa gaskiya Nanan nan fa ba son sa take yi ba"

Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imrana yaushe ka yi hankalin da ka fi ni sanin dai-dai? Shigar mutum ake dubawa ko halin iya riƙe auren? Ita Nanan ba taimaka mata zai yi ba, tun da ba lafiya ce da ita ba"

Imran ya ce "Baba neman kan da ka ke yi da Nana ba daidai ba ne ba, Allah ya ɗora mata larura alhakinka ne nema mata magani, ba neman kai da ita ba, amma shikenan 'yar ka ce, duk matakin da ka ɗauka a kanta daidai ne" yayi maganar yana barin gurin.

Baba ya kalli Saleh ya ce "Dan Allah malam Saleh ka yi haƙuri, yaron nan ba cikakken saiti ne da shi ba, ka san idan mutum yana shaye-shaye sai a hankali ka yi haƙuri. Nana 'ya ta ce kuma na isa da ita, ka je ka turo magabatanka kawai kar ka ɓata lokaci kamar yadda wancan yayi"

Saleh ya ce "In sha Allah Baba na gode sosai"

"Yauwwa yi tafiyarka, kar ya zo ya yi maka wani haukan a ka" Saleh ya so keɓewa da Nana, amma Imran ya wargaza komai.

An fara kiraye-kirayen sallar magariba, Jamila ta shigo Nana ta fara nema, Nana ta ce "Wannan kiran fa ta samu ne?"

"Wai dan Allah ina kayan da Hajiya ta bani na kawo miki, ko sau ɗaya ba ki saka ba, balle na yi miki hoto na tura mata, tun da na san ba za ki je ta gani ba"

Nana ta ce "Zan saka ne, kawai ni ban san dalilin da ya sanya ta bani kayan ba ne, amma zan saka in sha Allah"

Jamila ta ce 'Ai mace ce mai kyauta, babbar 'yar kasuwa ce fa, kwanan za ta fara bani kaya ina ɗora nawa nima, kin ga turare ta bani na kawo miki " ta yi maganar tana miƙa wa Nana wani turare.

Nana ta karɓa tana murmushi, kasancewar tana son ƙamshi sosai. Ta sunsuna turaren ta kalli Jamila cikin murmushi ta ce "Amma ƙamshin turaren nan yayi daɗi sosai, ki ce mata na gode sosai"

Nana ta fara ƙoƙarin fesa turaren a hannunta, amma idan ta fesa babu abin da yake fitowa, ga kuma turaren tana gani cikin kwalba. Tayi tayi amma abu ya gagara.

Suwaiba da ta fito daga banɗki ta ce "Wai ke Jamila ba ki gaya wa hajiyar, ki na da 'yar uwa da ku ke uwa ɗaya uba ɗaya ba, ni ba zata bayar da komai a kawo mini ba sai wata Nana da uba kawai ku ka haɗa?"

Suwaiba ta ƙaraso, ta karɓi turaren hannun Nana, ta fesa a hannunta ta sunsuna.
Wurin da ta fesa turaren Nana ta ga duk ya ɓuɓɓule, kamar an caccaka allura jini ya fara fitowa. Sai dai ta ga Suwaiba normal, ba ta nuna wata alama na ta ga abin da ya faru ba, hakan ya tabattar wa Nana, ita kaɗai take gani.

Suwaiba cike da mugunta, ta feshe rigar material ɗin jikinta milk. Nana ta ɗan ja da baya ganin jini, ya ɓata rigar maimakon ruwan turare.

Suwaiba kuma ta ce "Amma turaren yayi ƙamshi" tana sake feshe jikinta da shi. Sai dai duk in da turaren ya taɓa a fatarta ɓulewa yake jini ya fara zubowa.

Ta gama fesawa, ta bawa Nana turaren ta ci gaba da sabgoginta.
Mama ma masifa ta hau yi, wai tana uwar Jamila ba a bayar da komai a kawo mata ba sai wata Nana.

Jiki a sanyaye Nana ta shiga ɗakinsu, tana sake kallon kwalbar turaren. Ta buɗe ta ƙara fesawa a jikinta da hannunta, amma yaƙi fitowa.

Ta ajiye turaren tana tunanin ko sharrin ƙaisar ne.

Ta sake fitowa yin alwala, Baba ya zaunar da Gaddafi yana ta gaya masa abin da Imran yayi, tare da ƙorafin ya gaji da rashin mutuncin da yake aikatawa.

Nana hankalinta ba ya kan abin da suke faɗa, hankalinta yana kan Suwaiba, da jini yake ta gangarowa daga hudar jikinta, kuma rigar jikinta ta rine zuwa jini. Amma normal suwaiba na ta ayyukanta.

Nana ta ware a gefe, tana ta jan "wa hifzan min kulli shaiɗanin marid"

Sam jikin Nana ba ƙwari ta kwanta, duk addu'a da ta zo bakinta yi take yi, ta waiwaya ta kalli in da Suwaiba take, ta jiƙe jagab da jini ga ƙarnin jinin ya cika ɗakin babu daɗin ji.

Suwaiba na ta kallon kaɗe-kaɗenta a waya, har bacci ya kwashe ta. Nana ko kyakyawan ƙifta ido ta kasa yi, ganin yadda jinin ya jiƙa katifar da Jamila da Suwaiba su ke kai, ya gangaro ƙasa.

Ana haka Suwaiba ta kurma wani irin uban ihu, Nana ta razana, ganin wannan bararojin da ta ba ta magani ta lasa, jikinta baƙi ƙirin ta koma kamar gawayi, fuskarta ce kawai ba a ƙone ba sai gashinta, ta tsaya a kan Suwaiba ta kafa haƙoranta a wuyan Suwaiba tana zuƙar jini. Maimakon Nana ta yi addu'a kawai ita ma sai ta saka ihu ta suma a gurin.

Cikin ihu da kururuwa Suwaiba ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Mama Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, Nana tana shan jinina dan Allah ku yi mini rai Nana na shan jinina!!!


Ku tuntuɓe ni kai tsaye, domin fara biyan naku kuɗin littafin.
https://wa.me/2348081012143
Ayshercool
08081012143
Ko kuma ku kasance da ni a kan manhajar arewabooks @ayshercool7724
BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL
YOTA/002

P11

Ɗungurungum, page ɗin yau naku ne, YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION, Tare da 'yan Ayshercool media, ina godiya sosai da sosai.

A wannan karon Mama ce ta fito da gudu, jin muryar Suwaiba tana ihu.

Sai dai ta tarar da Nana a gefe, tana bacci.

Ta ɗago Suwaiba tana kiran sunanta, sai dai Suwaiba ta rirriƙe wuyanta, tana numfashi da ƙyar tana cewa "Nana ce, Mama ki taimake ni za ta kashe ni"

Cikin kuka maman ta fara ƙwalawa Baba kira "Malam Isa ka zo Nana za ta kashe mini 'ya, na daɗe ina faragbar kar ta cutar mini da yara, gashi za ta kashe Suwaiba"

Jamila ma tuni ta tashi, ta ja gefe, domin ita ma a tsorace ta tashi, saboda mummunan mafarkin da ta yi da Hajiya sa'a tana ƙoƙarin shaƙe ta, ta caka mata wata wuƙa.

Baba ya ce "Wani irin Nana za ta kashe ta kuma? Ba ga Nanan a gefe tana bacci ba?"

Cikin fushi da tsawa ta ce "To ka ƙaraso mana ka ga abin da take yi"

Ya ƙarasa ya ga Suwaiba, ta rirriƙe wuyanta, idanunta duk sun fito waje sai kakari take, da ƙyar take furta Nana za ta kasheta.

Baba ya ce "Suwaiban Baba, buɗe ido ki ganni, Nana bacci take yi me ki ke gani?"

Cikin kuka da kakari Ta ce "Baba wallahi Nana ce, jinina take sha, ka hana ta zan mutu"

Baba ya koma gurin da Nana take, ya kai hannunsa ya juyota, idanunta a buɗe, amma babu baƙar ƙwayar idonta, sai farar kawai. Jikinta kuma sanyi ƙalau kamar gawa.

"Ni wannan wane irin abu ne haka?"

"Ke Jamila, je ki ki taso mini Gaddafi" Jamila ta tashi jiki a sanyaye ta fita ƙofar gida, ta ƙwanƙwasa wa Gaddafi ɗaki.

Tare suka dawo, yana tsaki yana bala'in shi tattarawa zai yi ya koma in da ya fito, ya gaji da wannan bala'in na gidan.

Ɗan tsayawa yayi yana kallon in da Nana take, ga gefe Mama riƙe da Suwaiba tana kuka.

Ya ce "Mutuwa Nanan tayi ne na ganta a haka?"

Cikin kuka Suwaiba take miƙa wa Gaddafi hannu ta ce "Yaya ka taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take sha" tayi maganar tana kuka.

"Wane irin shan jini kuma?"

Nana kuwa tuni ta lula wata duniyar a yanayin da take ciki.

Domin kuwa Ƙaisar take gani. Ya ce "Kin ga da kin sake kin fesa turaren nan a jikinki, da jininki za a sha ba nata ba. Aike ne na musamman domin ke, da na bari kin fesa turaren nan da sai dai wata ba ke ba"

Nana ta kalle shi ta ce "To ni me za ayi da jinina? Kuma meyasa ba ka hana wannan mummunar matar shan jinin Suwaiba ba?"

Ya tanƙwashe ƙafafuwansa ya kaɗa kai ya ce "Saboda ke ce uwar gijiyata, alhakin kula da ke ne kawai a kaina. Duk da ba jininta suke buƙata ba, amma idan 'yar aiken ta ji daɗin jinin na ta, to fa ta samu wurin zama. Ko da su can jinin bai yi musu amfani ba, to ita za ta ci gaba da amfani da jininta, domin ta warke daga ciwon jikinta, idan ba ayi wasa ba hakan zai yi ajalinta."

Cikin damuwa Nana ta ce "To ka yi wani abu a kai mana"

Yayi murmushi ya ce "Zan iya wani abu a kai tabbas, amma daga lokacin da ki ka fara bani umarni hakan yana nufin kin karɓi gadon gidanku. Kuma zamu yi aiki tare"

Da hanzari ta ce "A'a ni ba zan iya shirka ba na gaya maka. Amma ba zan zuba ido komai ya tafi a haka ba. Idan haka ne anya ba wannan matar Hajiya sa'a da ta kawo turaren babu masaniyarta a kan wannan abun?"

Murmushi ya yi ya shafi gefen fuskar Nana ya ce "Ban sani ba, amma ke ma zan shafe komai daga kanki yanzu wani binciken ba shi da amfani sam. Mussaman ke da ba za ki yi abin da ya dace ba, idan ki na tsananta bincike wataran za ki shiga gurin da ba zan iya ciro ki ba.
Kalli nan ki ga, ta waiwaya domin ganin abin da yake nuna mata.

Ɗakinsu ta gani, Suwaiba ta samu bacci, Jamila kuma ta ce Allah kar ta, ba zata kwana a ɗakin nan ba tsoro take ji.
Mama ta ce su tarkata su koma ɗakinta, su kwana tare da yaranta a bar Nana ta ci kanta.
Baba ya kalli Gaddafi ya ce "Gaddafi, gobe in Allah ya kaimu dole mu yi sammako, mu kai yarinyar nan gurin da ka faɗa ɗin nan. Ni kaina na fara jin tsoron abubuwan nan".

Gaddafi ya ce "Allah ya kaimu"

Nana ta dubi Ƙaisar ta ce "Ni dama gurin mamana ka nuno mini, na ganta ko na ji daɗi"

"Idan na fara karbar umarninki, haka yana nufin kin amince da sharaɗina, ni kuma zan yi miki mubaya'a na zama mai hidima a gare ki"

"A'a bari ba na so" tayi maganar tana girgiza kai.

Ya saka dogwayen yatsunsa yana ci gaba da shafa kumatunta ya ce "Alamu na nuna, sarƙar ƙaddara ta mayen ƙarfe na ƙoƙarin janmu wani wuri, ta yi wani ɗauri mai wahalar kwancewa. Ko na ce sarƙar na ƙoƙarin sarƙe ki. Gobe za a wuce da ke gurin mai magani, 'yar uwakki ta shafa miki mugun tabo, tun da ta ce kina sha mata jini, babarta ba za ta yi shiru ba, za ta yi ta gaya wa mutane ne. Ga yayanki can ya sha ƙwayoyi yana ta bacci, gobe har ku tafi ba zai farka ba, domin na ƙarawa abin da ya sha ƙarfi. A duniya zan ga wanda ya isa ya raba ni da ke. Zan ga mai karambanin mai maganin da zai jarraba hakan".

"Allah ne zai raba ni da kai" ta yi maganar a hasale.

"Da zai rabani da ke, da bamu haɗu ba" ya bata amsa.

Nana ta waro ido ta ce "Kaii zaka yi saɓo, ki ba musulmi ba ne? Ko da yake musulmi ba zai yi abin da ka ke yi ba"

Ƙaisar ya yi dariya ya ce "Kamar ba musulmin ne ke neman jininki su yi tsafi da shi ba"

Ya koma ta bayanta, ya zuro kansa gefen fuskarta, hakan ya ƙara adadin bugun zuciyarta, jikinta yayi sanyi ƙalau kamar wadda aka saka a cikin firinji.

Ya ce "Bari na sake nuna miki wani abu, amma akwai buƙatar na tsaya kusa da ke, idan ba haka ba, wannan 'yar ƙaramar ƙwaƙwalwar ta ki bugawa za ta yi. Kalli can" ya nuna mata wani mudubi. Ta ɗaga kai ta kalla.

Kawai ta ga Auwwal a kwance ana yi masa wankan gawa, gefen cikinsa na ta zubar da jini.

Razana tayi za ta miƙe, amma ya riƙe ta ya ce "Kar ki zarge ni, babu sanya hannuna a cikin wannan abin, ya gama shirinsa gobe zai tafi Abuja, ɗazun nan masu ƙwacen waya suka tare shi, suka karɓi wayar suka caka masa ɗan buda.
Yaran kuma da suka yi, abokan yayanki ne, nan da 'yan kwanaki idan bincike yayi nisa shi ma za a kamo shi".

Wani irin yinƙuri Nana ta yi, domin ta ƙwace daga jikinsa amma ta ji an riƙeta. Ta ɗaga kanta kawai ta ganta a ana kiciniyar shiga taxi da ita, ta waiwaya ta ganta a tare da Yaya Atine da Baba.

Ta ja ta tsaya ta ce "Wai ya na ga haka?"

Baba ya ce "Ba ki da lafiya, gidan mai magani za mu je"

"To Baba ai ban yi sallar asuba ba"

Yaya Atine ta ce "Mu je, idan an je gidan mai magani sai ki yi sallar"

Nana ta kalli sama yadda gari ya fara haske, ta ce "A'a ni a bari na yi salla"

Baba ya ce "Ta dawo hayyacinta, a ƙyale ta tayi sallar"

Nana ta shiga gida Yaya Atine ta bita, ta yi alwala.

Yaya Atine ta ce "Rabi ki bari a tafi da Suwaiba gidan mai maganin nan a duba ta ita ma"

Mam ta ce "Eh ko ba gidan mai magani ba, ta je ta ƙarasa lasheta a hanya ta kashe ta, babu in da za ta je, kuma wallahi kurwar Suwaiba ta fi ƙarfinki" ta yi maganar tana hararar Nana.

Nana dai ta yi alwala, ta gabatar da sallar asuba, aka saka ta a cikin taxi, aka ja aka tafi, ba tare da ta san ina suka dosa ba.

Suwaiba kuwa ba ta tashi daga bacci ba, sai bayan ƙarfe tara na safiya, kuma babu wanda ya tashe ta, domin ta yi salla. Sai a lokacin ta yi salla, ta nemi abin karyawa.

Jin Mama na ta jera mata sannu ya sanya ta ce "Wai mama sannun me ki ke yi mini ne?"

Mama ta ce "A'a abin da ya faru da ke jiya mana, wannan azzalumar tana neman kar ki"

Cikin rashin fahimta Suwaiba ta ce "Wace ce? Ni fa ban gane ba"

"Jiya kururwar da ki ka din ga yi ki na Nana za ta kashe ki, tana miki jini, ba mu yi bacci ba fa" Suwaiba ta zaro ido ta ce "Ni ɗin?"

Jamila ta ce "Eh mana, kasa numfashi ki ka yi fa, kina ta kuka wai Nana tana sha miki jini"

Jikin Suwaiba ya yi sanyi, ta ce "To ai ni tun da na kwanta, ko juyi ba na tunanin na yi, sai yanzu na tashi daga bacci"

Jamila ta ce "Ikon Allah, kin ga kururwar da ki ka din ga yi kuwa, wai Nana na sha miki jini?"

"Ni dan Allah ku daina wannan zancen tsoro ku ke bani wallahi kar na je, aljanun nata ne nima su ka shafe ni"

Muryar Imran ce ya dawo da su kan tsakar gidan, yana ta kwaɗa wa Nana kira.

Nasiru ya ce "Nana fa sun tafi gurin mai magani, bayan sallar asuba"

"Kamar yaya ita da wa?"

"Asubar farko, aka je aka taho da Yaya Atine daga gidanta, a taxi ɗin malam Shehu, gari yana fara haske suka tafi. Jiya ne Suwaiba ta din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login