Showing 171001 words to 174000 words out of 189977 words

Chapter 58 - BUZU BOOK1 COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Jan 2026

982

me yasa sai dare, ka fi sakar mini fuska, ka yi ta magana ka na raha"
Ya gyara kwanciyar sa, ya ɗago daga kwanciyar da ya yi ya ce "Na gaya miki?"
Da sauri ta ce "A'a bar shi, ba sai ka faɗa ba"
Kawai ya tuntsure da dariya, ta ce "Hmm za ka yi dariya ne, Allah ya dauwwamar da wannan kyakyawan murmushi a fuskar gangar jikin da ke ɗauke da ruhina"

"Ashe ke ma kin iya, abin cikin film ɗin"
Suka yi dariya tare, ya fara kashe Nana da salon soyayyarsa mai tsayawa a rai, tare da haɗa yaren Hausa da fransanci, gurin gaya mata kalamai masu motsa zuciya.

Cikin rawar murya ta ce "Sayyid"ya ɗaga kai ya kalle ta.

"Kana ganin abin da nake gani?"

"je l'ai vu(Na gani) amma kar ki tsorata. Yi kamar ba ki gani ba"

"A'a ina ne nan Sayyid? Ina yawan ganin gurin nan, ina yawan ganinmu tare a nan."

Y girgiza mata kai ya ce "Nima ban san ina ne ba"

"Kuma ba mafarki ba ne?"

"Zahiri ne" ya amsa mata a taƙaice.

"Amm..." Bai bari ta sake magana ba, ya rufe bakinta da nasa, saboda tambayoyinta ba sa ƙarewa.

Bayan wani lokaci, ya rungumota daga banɗaki, sai rawar sanyi take yi.

"Ba ki da lafiya ne?"

Ta kalle shi ta ce "Me ka gani?"

"Kamar ki na jin sanyi, kuma na da ruwan ɗumi muka yi amfani"

Ta jinjina kai ta ce "Ina jin sanyi kam, mu je ka bani ɗumi"

Da sauri ya ce "To mu je"

"A'a ba fa abin da ka ke tunani ba ne"

Ya yi murmushi ya ce "To ma na ce miki ina tunanin? Zo na baki ɗumin jikina"

"Ba na so, ƙona ni ka ke yi"

Kawai ya yi dariya, ya ce "Daga ni har ke, Allah ya yaye mana abin da yake damunmu"

"Amin Sayyid, dama ka na ganin ɗakin nan kai ma?".

"Eh amma a mafarki galibi"

"To akwai ranar da ka ce azumina zai karye, na ganmu a ɗakin kuma na tashi, na ga ya karye ɗin"

Kawai ya shafi jiƙaƙiyyar kalbar da take kansa, yana dariya ƙasa-ƙasa.

"Ya ka ke dariya? ka bani amsa mana"

"Na saka ki bacci ne, sai na taɓa ki kaɗan"

"Ka yi mini me?"

"Abin da muka yi yanzu" sai kuma ta yi saroro cikin jin kunya, ta kwanta za ta juya masa baya, amma ya juyo da ita, ya kwanta shi ma. Gaba ɗaya yau ya fi kullum ba ta mamaki, hirarsa ta fi ta kullum yawa, zolaya da nishaɗinsa ya fi na kullum. Duk a 'yan kwanakin nan, sun ƙara samun nutsuwa da kusanci da juna sosai da sosai.

"Shugaba"

"Rayuwata"

"Ya ake ka ke saka ni bacci mai nauyi"

Ya yi shiru bai ba ta amsa ba, ta ɗan jijjiga shi, kawai ta ga ya yi bacci.

Sai dai tana sakankancewa bacci mai nauyi ya ɗauke ta, ya ƙara farkawa ya tashe ta.

"Sayyid gaskiya ƙasa zan koma, na bar maka katifar nan, halak malak haba, kwata-kwata ban yi bacci ba. Kaina har ya fara ciwo. Ga zuba ruwa ga rashin bacci haba Shugaba"

Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta, ta baya, ƙirjinsa a bayanta. Ji ta yi zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. Har za ta yi magana sai kuma ta fasa, jin jikinsa ya saki alamar ya yi bacci.

Siyama kuwa bayan ta farka ta ganta a gida, sai ta kasa tuna komai. Tayi-tayi amma ta kasa tuna komai. Ta tambayi Maminsu, me ya same ta, ta gaya mata a mota aka tsinto ta a sume
Abin ya ɗaure mata kai ya ba ta mamaki, a iya saninta, ta haɗu da mai gadi, sun yi magana daga haka ba ta sake tuna komai ba. Abu kamar wasa sai ta din ga zabura tana tsorata haka kawai.
Ta kasa zama a ɗakinta itakaɗai, ta tashi ta koma ɗakin mahaifiyarta.

*****
Alhaji Zailani ne a zaune a kan kujera, yana kallon Alhaji Fatuhu, da yake zaune, ya jingina da pillow, Fadila na ta ƙoƙarin ba shi Abinci.

"Sannu Fatuhu"

Alhaji Fatuhu ya ce "Yauwwa Alhaji Zailani, na gode" ya furta cikin ƙarfin hali.

Ya kalli Fadila, zaune ciki ya tsufa sosai da sosai. Ya ce "Babu wanda yake kula da shi, ke ga larura ga kuma ɗawainiyar jinya".

"He deserves it, Daddy shi mai kulawa ne a gare mu" ta yi maganar hawaye ns zirarowa daga idanunta.

"Allah sarki, sai haƙuri, ki yi haƙuri. Allah ya ba shi lafiya" kasa ci gaba da ba shi Abincin ta yi, ta ƙara fashewa da kuka.

A hankali Alhaji Fatuhu ya ce "Za mu yi faɗa idan kina kuka, ai na samu sauƙi"

Alhaji Zailani ya ce "Look, kukan nan ba abin da zai amfana muku. Ki yi haƙuri ki yi masa addu'a, kin ga juna biyu ne da ke. Ba zai so wani abun ya faru da ku ba, daga ke har abin da yake cikinki ba. Kin ga Shukura irin haka aka yi, ta saka damuwa mara dalili a zuciyarta. Ta zo ta haifi yaronta babu rai. Kuma ta zo ta sake shiga damuwa. Ki yi haƙuri dan Allah" Cikin rauni ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, na gode sosai da sosai"

"Yauwwa babu komai, idan Hajiya Suwaiba ta zo, ta kira ni a waya, ku koma Asibitin Doctor Sharif,a din ga yi masa komai a can. Ba zai gagara ba in sha Allah"

Fadila ta ce "Kar mu ɗora maka ɗawainiya, nan ma su na ƙoƙari Alhamdillah"

Alhaji Zailani ya ce "kai, Fadila. Kin san waye mijin ki kuwa a gurina? Da Suwaiba ce ma ba za ta yi jayayya ba na sani.
Dan Allah ku haɗa kayan ku, zan turo direba ya mayar da ku can zuwa dare in sha Allah. Abokina Ubangiji Allah ya ƙara afuwa"

Ya miƙa wa Alhaji Fatuhu hannu suka gaisa, Alhaji Fatuhu ya ce "Na gode sosai da sosai, da ɗawainiyar da ka ke ta yi, na gode sosai da sosai"

"Ai ka san babu godiya tsakaninmu, Allah ya sauwwaƙe". Bayan ya fito harabar Asibitin, ya din ga wata irin dariya. Ya hau motarsa yana faɗin da sauranka, tun da har yanzu ka na magna. Wannan matan ma duk sai sun gudu sun bar ka, abin da za ka ci ma sai an taimaka maka da shi. Ya ja motar ya bar harabar Asibitin.

*****
Gidan su Nana kuws, duk wanda ya yi surutun, gyaran da aka yi wa gidan, da yawon da Jamila take yi. Sai Mama ta ce Maman Khairat ce ta haɗa Jamilan, da wata Hajiya 'yar kasuwa, Jamila take taya ta aiki a kasuwancinta, tana biyanta.
Suwaiba kuma, abu kamar wasa jiki ya ƙi daɗi sam. Kullum cikin ciwo take, yau ciwon kai, anjima ciwon ƙafa da ciwon baya. Ga shi ta auri zaman ɗaki ba ta son fita. Idan ciwon kan nan ya tayar mata, tamkar za ta haukace, ta din ga burgima kenan tana ihu da kururuwa. Mama ba ta wani mayar da hankali ba a kan ciwon na Suwaiba, saboda hankalinta na kan abin duniyar da Jamila take kawowa, shi yasa ba ta damu sosai da sosai ba. Duk inda ta kai Suwaiba neman magani, wasu su ce Aljanu ne da ita, wasu su ce Asiri aka yi mata. Wasu su ce kambun baka ne da baki. Gaba ɗaya Suwaiba, ta rame ta yi baƙi. Idan abin ya motsa ko abincin kirki ba ta iya ci, sai aikin kuka sai bacci.

*****

Can gurin su Nana kuwa, fito daga gaba ɗaya Sayyid jikinsa yake yi tamkar an zare masa laka, wata irin mutuwar jiki da ta ƙaru a kan ta jiya da yake ji.

Nana ta fito daga wanka, ta ɗauro zani ta fito tana ɗigar da ruwan wanka. Ta yi fari da idonta, ta ce "Shugabana"

Yayi murmushin da ya saba, tare da sunkuyar da kansa, yana kallon wayarta da ke hannunsa.

Ta buɗe drowern mudubi, ta ɗaukko kibiya da comb, ta nufo shi, ya kalle ta ya tsuke fuska.

Ta kwashe da dariya, ta ce "Mutumina akwai shagwaɓa, kalbar kanka ta tsufa sosai, ka bari a tsefe dan Allah. Idan ya so ma yi kitson gobe"

Ya girgiza kai ya ce "A'a"

"Gaskiya sai na tsefe ta, na yanke maka farce, ka yi wankan juma'a ko Rayuwata"

Yana hararta, ta kwantar da kansa a kan cinyarta, tana yi masa dariya.

"Rigimammen Shugabana"

Tana tsifar tana yi masa hira. Yana ta shiga yana fita a cikin wayarta, ya kunn waƙr kewa, ta wani mawaƙi ɗan nijar ta kewa.
Cikin nishaɗi,take bin waƙar, ta riƙo tafin hannunsa cikin nata, tana bin, baitukan waƙar.
Kowa tsaneka, ni na tsane shi sanya a ranka...
Zuciyata na baka, duk masu ƙin ka su daina shakka...
Rayuwata na baka...
Ni ta ya zan guje ka...
Ka dawo gare ni dan Allah, zuciya ta bar kewa...

Murmushi ya gaza barin fuskarsa, fararen haƙoransa a waje, ya juyo gaba ɗaya ya ƙanƙance idanunsa, yana yi mata wani irin kallo cikin nishaɗi.

Ta ci gaba da bin waƙar, tana ɗan jan kunatunsa "Mallakina ne, kai zan kira da sheriena...
Ko iyayena sun ce na bi ka mai so na...
Kai jinina ne...
Mahɗina ne...
Ƙaddarata ne
Mai yabona ne...
Ashe kai ne, ashe kai ne, ashe kai ne abin so ne, abin so ne, abin so ne.
Dan Allah ka dawo gare ni mai so na ina kewa...

Ya ɗago hannunsa ya kalli azurfofin hannunsa, ya ciro ɗaya ya kamo hannunta ya damƙa mata. Tana dariya ta ce "Iyee gaskiya na iya waƙa, har da kyauta? Amma ya yi mini yawa ai"

"Ki samo zare ki zura a ciki ki yi sarƙa da shi" Nana ta din ga tuntsura dariya. Ta ce "Riba biyu, ga tsifa na yi ga kuma kyauta an ba ni.

Ya din ga kallon dariyar da take yi yana murmushi.

Can zuwa la'asar Nana ta fuskanci jikinsa gaba ɗaya a sanyaye yake, kamar babu kuzari haka yake gudanar da komai.

Sai dai ba ta tambaye shi ba, saboda tana tsoron ya zamana wani abu ne yake damunsa, ba ta son ganinsa a cikin damuwa sam.

Su na cin abincin dare, tana yi masa hira yana amsawa muryarsa a sanyaye.

Wayarta da ke caji a ɗakin, ta cika ɗakin da ƙara. Nana ta duba ta ga Hajiya Amina.

Cikin rawar jiki ta ɗaga tana murmushi ta saka a hansfree ta ce "Hajiya tuba nake yi, kwana biyu ma ban kira ki na gaishe ki ba".

"Alhajin ne, ba Hajiyar ba"

Wata irin mummunar faɗuwar gaba, ta riski Nana, ta kalli Sayyid. Ta ga bai ko kalle ta ba, yana cin abincin sa a nutse.

"Wa..wa..wane Alhajin ya aka yi? Ina mai wayar?"

Zailani ya ce "Mai waya tana nan ƙalau, na ji kin saka wayar a blacklist ne, shi ne na ce bari na biyo ta inda dole ki ɗauka. Me ki ka yanke game da maganarmu? Idan kin amince zan turo miki inda zamu haɗu, mu gama na baki kuɗin ki na sallame ki, babu wanda ya ji babu wanda ya sani. Idan kuma ba haka ba zan ɗauki mataki na gaba"

"Na shiga uku, zaka kashe mini aure, wannan wace irin masifa ce, ban yadda ina budurwa ba sai da na yi aure" Sayyid ya miƙa hannu ya katse kiran, ya kashe wayar gaba ɗaya.

Cikin kuka ta ce "Dan Allah Sayyid ka fahimce ni, zan yi maka bayani"

Ya girgiza kai ya ce "Babu buƙata, ci abinci"

Sosai Nana take kuka ta ce "Wallahi Sayyid"

"Don't talk.(Kar ki yi magana)"

Gaba ɗaya hankalinta ya yi mummunan tashi, duk jikinta ya mutu. Amma bisa ga mamakinta, ta ga ya ci gaba sabgoginsa ko ta kanta bai bi ba.

A tsorace ta raɓa shi ta kwanta, tana tsoron kar ya shaƙe ta.

Ya kamo hannunta, ya ɗora kan tsefaffen gashinsa ya ce "Ki yi mana addu'ar bacci"

Ta yi ajiyar zuciya, ta fara karantowa a hankali. Suratul falaƙi, Nasi, ayatul kursiyyu da ayoyin farko na Suratul Baƙara. Sai dai tana karantawa muryarta na rawa. Ta idar ta busa masa a fuskarsa. Kamar yadda ta kan yi musu, ranar da take cikin ƙoshin lafiya.

Gani duk ta takure ta ƙi sakin jikinta, ya sanya ya yi ƙoƙarin kawar da damuwar da take ciki. Amma ya ji jikinsa ya ƙara nauyi, yana jan numfashi da ƙyar. Duk ƙoƙarin da ya yi, ya kasa komai, sai kokowa da yake yi da numfashi.Nana kuwa jin ya ƙyale ta, ya sanya ta yi bacci.

Hatta sallar Asuba, a gida ya yi, a ɗaki. Ta sab wasu lokutan idan ba ta tashi da wuri ba, sai dai ta tashi ta ga ya sayo ƙosai ko buredi, amma yau har ta makara, ta tashi ta yi abin karyawa yana kan katifa bai tashi ba.
Ta tsaya a gaban mudubi ta shirya, ta yi kwalliya.
Vibrating wayarta take yi, sai da gabanta ya faɗi, saboda tana tsoron kar ta je ko Alhaji Zailani ne. Jiki a sanyaye ta ɗaukko wayar, ta kalli Sayyi, ta ga bacci yake yi.
Ta ɗaga kiran gabanta na faɗuwa, ta saka a kunnenta.

"Nana ba faɗa me ya kawo gaba?"

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Jamila, yau ke ce da kira na?"

"Eh, tun da ba kya neman mutane ba. Rannan na wuce ta wajen gidanku, kamar na biyo na ce kar na je, na takura muku"

Nana ta ce "Kashh, amma ba ki ji daɗin halinki ba, dan wulaƙanci?"

"Ba wani wulaƙanci, lokacin ma Ummi ce ta ce kin yi ɓari, ai an kwana biyu da na wuce ɗin ai"

"Kai Ummi sai da ta faɗa? Ina su Mama, ba ta taɓa zuwa gidana ba, Yaya Atine ma haka"

"Aikuwa na ji Yaya Atine tana ta masifar, ba ki je mata ba."

"Wallahi ba ya bari na fita ne, sai na yi ta fama. Ina suby ne?"

"Tana gida babu lafiya, tana ta fama da matsanancin ciwon kai"

Cikin damuwa Nana ta ce "Subhanallah, in sha Allah zan samu dai na zo gidan, ba ni ita dan Allah na yi mata sannu"

"A'a ni ba na gida ma, na fita tun safe"

"Zuwa ina?"

"Gurin neman halal mana. Kin san Hajiya Sa'a nake yi tayawa saye da sayarwar kaya tana biyana".

Nana ta yi murmushi ta ce "Jamila kenan, ni dai wallahi matar nan ba ta yi mini ba, ba zan ɓoye miki ba, ina iya jin alamun rashin gaskiya a tattare da ita. Na san yanayin gidanmu, dole ka nema idan kana so ka rayu. Amma Jamila ki san abin da za a saka ki ki yi, duk wani abu da zaka tara a duniya koma bayan imaninka da mutuncinka ne. Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari, masu tsoron Allah masu wadata."

Jamila ta ce "Hajiya Nana sarkin manyance, dama kuma ga shi an yi aure, sai abin da ya yi gaba. To na gode sosai na ji ana sallama"

"To ki gaida su Mama da Suwaiba kafin na zo"

"To shikenan, sai anjima" ta kashe wayar, ta ajiye ta shashshafa turare.

Ta juyo ta kalli Sayyid ta ga idanunsa kar a kan ta.

"Shugaba ya dai? A tashi a zo a ci Abinci"

Murmushi ya yi da ƙyar, amma bai yi magana ba, kuma bai motsa ba.

"A taso mana ranka ya daɗe" ya yi shiru dai yana kallonta.

Nana ta yi murmushi ta ce "Yau mulki ake ji kenan, bari na zo na ɗaukko ka, tun da tashi ya gagara" ta ƙarasa ta ɗaukko kayan abincin, ta jera a inda suke ci. Ta kunna turaren wuta, ɗakin ya gauraye da ƙamshi. Ta ga dai da gaske ya ƙi tasowa, ta nufe shi tana rangwaɗa.
Ta sunkuya a gabansa, ta yi masa kiss a goshi ta miƙa masa hannu, ta ce "Bismillah taso Shugaba"

Bai kama hannun ba, ya ci gaba da kallonta, sai kuma jikinta ya yi sanyi, da kallon da yake yi mata.
Jiki a sanyaye ta ce "Wai Sayyid lafiya kuwa? Ko maganar ce ta ɗauke?"

Ya miƙa hannunsa, ya kamo nata, ya ɗora a saitin zuciyarsa.

Ta yi shiru, ta ji zuciyarsa ta buga sau ɗaya, sai kuma ta yi shiru ba ta sake bugawa ba, sai bayan wasu sakanni, sannan ta sake bugawa.

A razane Nana ta kalle shi jikinta na rawa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid meyafaru? Me ya same ka haka?"


Ayshercool
08081012143
48


Bai ce uffan ba ya ci gaba da sauke numfashi. Tashi ta yi a matuƙar rikice, ta zari hijjabinta ta yi waje, cikin matsanancin tashin hankali da kuma damuwa.
Ta kai a ƙalla mintuna ashirin, sannan ta dawo a rikice, ta tarar da shi a zaune ya jingina bayansa da jikin bango, ya lumshe idanunsa.
"Sayyid na samo abin hawa, Asibiti za mu tafi"
Ya buɗe ido da ƙyar ya kalle ta. Ta nufi wardrobe ta duba ta ɗaukko irin kuɗin da Imran ya bata. Ta buɗe wardrobe ɗin sa, ta ɗaukko masa riga jallabiya. ya tashi da ƙyar, su ka shiga banɗaki, ya wanke bakinsa. Ya fito ta naɗa masa rawaninsa, ba ta damu da ko rufe ɗakin ba, suka yi waje.
Ƙarfin hali kawai Nana take yi, amma zuciyarta ta gama tsinkewa, ta karaya a mugun tsorace take.
A cikin adaidaita sahun ma, a jikinta ya kwanta ya yi lamo, ya yi shiru ba ya cewa komai.
Addu'a kawai Nana take yi, da fatan Allah ya kawo musu ɗauki. Amma a yanayin yadda zuciyarsa take bugawa ta yi mugun tsorata.
Asibitin da suka je aka saka mata ruwa, suka je, amma aka ce musu ai weekend ne, kuma ƙaramin Asibiti ne ba sa aiki weekend.
Hankalin Nana ya yi mugun tashi, yana son ya yi mata magana, amma ya kasa.
Sai suka bawa ɗan sahun tausayi ya ce "Ko na kai ku Asibitin cikin gari emergency, ko wani taimakon a yi masa"
Muryar Nana na rawa ta ce "Yauwwa malam, na gode kai mu dan Allah" ya ja babur suka tafi.
Ya kamo hannun Nana, ya danne saitin zuciyarsa da shi, ji yake numfashinsa ma na neman ya ƙwace masa.
"Sannu Sayyi, Allah ya baka lafiya, Ubangiji Allah ka dube mu, babu mai kawo mana ɗauki bayan kai, Allah ka yi mana ba dan halinmu ba" muryar Nana na rawa, take wannan addu'oin, har suka ƙarasa Asibitin.
Mai adaidaita sahun ya yi mata mutunci, har zai ja babur ɗin, ya ga yadda Sayyid ya kasa tsayuwa,yana neman faɗuwa Nana kuma ba zata iya riƙe shi ba. Ya kashe babur ɗin ya fito ya ce "Ƙanwata, bari na riƙe miki shi, ba za ki iya ba"

Ya saƙala hannun Sayyid a kafaɗarsa, suka taka a hankali zuwa ɓangaren emergency.

Matashin ya kalli Nana ya ce "Karɓo kati, ki dawo" ta tafi da sauri gurin karɓo kati.

Shi kuwa Sayyid, ƙarnin da gurin yake yi, da warin gyambo kala-kala da yake gurin, ya sanya jin numfashinsa zai ɗauke.
Ya zaunar da shi a hankali a kan wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login