Showing 57001 words to 60000 words out of 189977 words
fara lumshe idanunsa, alamar ya gaji da kuka, bacci zai yi. Ta ƙarewa ɗakin kallo, babu wani abu da ya shafi addini a ɗakin, sai uban tarkacen ABCD da teddies.
Da ƙyar ya yi bacci, da azahar Jummai ta zo ta samu Nana, ta ce ta zo ta haɗa wa Haidar shayi, yana tashi ta bashi.
Nana ta ce "Wai ba ya cin abinci ne?"
"Ba ya cin komai, sai wannan shayin, idan kuma an yi sa'a yana cin biscuit ko chocolate"
"Amma wannan ba abincin yaro bane"
"To su haka tsarinsu yake, abin da yaro yake so kawai ake yi masa, ba bari ba hantara" Nana ta yi ajiyar zuciya, ta bi Jummai zuwa kitchen.
Kitchen ɗin makeke ne na gaske, ɗauke da kayan alatu na sarrafa abinci, manmanyan kayan wuta na girki na zamani duk akwai su a kitchen ɗin.
Aka haɗo shayi, da uban kauri, ta koma ɗakin da ta baro haidar, ta ajiye ta yo alwala ta fito ta yi sallar azahar.
Tana cikin lazumin bayan salla ne, ya tashi daga bacci, yana tozali da Nana ya sake fashewa da kuka.
Ta tashi ta nufe shi, cikin sanyin murya tana rarrashin sa, amma ya tubure, ta ba shi feeder amma ya yi jifa da ita a ƙasa.
Ta ƙarewa yaron nan kallo, wani takaici ya zo mata wuya, ga gida har gida na masu kuɗi, amma yaron a tsumbure tamkar ƙadangare sai rungumemen kai da uwar ƙeya kamar ƙwarya. Dama ya za ayi yaro ya yi kumari? Da shayi da chocolate kayan basir.
Wata uwar tsawa ta yi masa, ya gigice gaba ɗaya, ta ɗukko feeder, ta ce "Sha ko na murɗe maka kai" jikinsa na tsuma, ya karɓa ya kafa kai ya shanye.
Har ta yi masa wanka, ta canza masa kaya bai sake ko ƙwaƙwƙwaran tari ba.
*****
Alhaji zailani ne, yake zaune shirim a gaban mutumin, ya tattara hankalinsa a kan mutumin.
"Ka tabattar sunanta Asma'u dai ko?"
Ya jinjina kai ya ce "Sai da na sake tambayarta ma".
"To ka samo sunan mahaifiyar ta ta?"
Zailani ya ce "A'a Allah ya sa dai wannan ta yi, ina son ayi mini aikin nan wallahi. kamar yadda na gaya maka, sunan babanta kawai ta gaya mini."
"To ka zo da ƙasar sawun nata?"
"Eh gata a leda, ai tun da mu ka yi waya da kai jiya, na saka aka ɗebo mini" yayi maganar yana fito da farar leda, ɗauke da ƙasa a ciki.
Ya karɓi ledar, ya ɗaukko ɗan wani katako mai ɗauke da ƙasa a ciki, ya zuba ƙasar sawun Nana a kai, ya fara zane-zane.
Ya ɗan yi shiru, yana kallon ƙasar, ya ɗago ya kalli Alahaji Zailani ya ce "Buƙata za ta biye, wannan ta yi daidai sosai, fiye ma da abin da ake nema, za a samu a gurinta."
Washe baki Alhaji zailani ya yi ya ce "Ɗan da ƙyar, har na ji sanyi, yanzu dai ta yi kenan?"
Ya jinjina kai ya ce "Ɗari bisa ɗari ma kuwa. Ni nake baka tabbacin samun fiye da abin da ka ke tsammani, taurarinta masu haske ne, duk wanda ya yi tarayya da ita, bisa sharaɗin da zan gindaya masa, zai samu abin da yake so. Ana daɗewa matuƙa ba a samu masu irin tauraronta ba. Sai dai akwai wata matsala"
Alhaji zailani ya ɗan ɓata fuska ya ce "Ta me kuma?"
"Ban kai ga ganota ba tukuna...
"Dan Allah ba sai ka gano ta ba, ni dai kawai buƙata ta ta biya"
"Shikenan, an bari jeka Allah ya sa a dace"
"Amin, saura kuma batun wancan ɗan iskan fatuhu, ya za ka yi mini da shi ne?"
Mutumin ya yi murmushi ya ce "Na ce a kawar da shi ka ce a'a"
Alhaji zailani ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar a kashe shi, so nake a naɗe shi da ciwo, komai nasa ya ƙare ya tagayyara ya wulakanta"
"Ba matsala, a kawo jariri sabuwar haihuwa, a haɗo shi da zaren mahaifar da mabiyiyyar, zan yi wani aiki da shi, a binne shi da ransa, gwargwadon wahalar da zai sha kan ya mutu, zuwa lalacewar da jikinsa zai yi, haka dukiyarsa za ta lalace. Bayan kwana arba'in za a ciro ƙwarangwal ɗin, a sake aiki a kansa, a binne a maƙera, gwargwadon yadda suke hura wutar a maƙera gwargwadon karfin ciwon da zai yi"
Wata irin ƙyaƙyatawa Alhaji zailani ya yi ya ce "Na gode mutumina, idan babu kai babu ni malam. Dole fatuhu ya ɗanɗana kuɗarsa. Godiya nake" suka rabu ya tafi cikin annashuwa.
****
A jikinsa yake jin daɗin jikinsa, da ɗan sauƙi, duk da cikin jikinsa yana jin raɗaɗi.
A jikin tagar yake tsaye, yana jin yadda sassanyar iskar la'asar ke ratsowa, tana dukan fuskarsa.
Ƙoƙarin takura ƙwaƙwalwarsa yake yi, ko zai iya tuna wani abu game da rayuwar sa, ko yaya yake. Amma ya ji tamkar an ƙara duhu a cikin ƙwaƙwalwarsa. Da ya ƙara ƙoƙari ma sai ya ji zuciyarsa na neman tsayawa da bugu, kansa kuma ya fara ciwo.
Hannunta riƙe da leda, ta fito daga cikin gidan, yanayinta ya nuna a gajiye take, sai ɗan yamutsa fuska take yi.
Kamar ya so ya taɓa ganinta, amma shi ma dai a wannan karon, ya manta a ina ne.
Nana ji ta yi tamkar ana hankaɗa ta, wani irin nannauyan jiri yana neman ya kayar da ita a ƙasa. Kawai ta tsinci kanta a cikin sahara, wata irin azababbiyar ƙura ta turnuƙe gurin baki ɗaya. Wani irin tari ya taso mata, numfashinta ya fara barazanar barin ƙirjinta.
Dafe goshinta ta yi da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma tana laluben, abin da za ta samu ta dafa, ko ta kuɓuta daga wannan iskar sahara mai ƙarfin gaske, da take neman sabauta ta.
Yana daga inda yake, yana kallonta, sai dai tsananin mamaki ya cika shi, ganin dogon mutumin da yake tare da ita, duk da yana da tsawo sosai, bai hana shi ganin fuskarsa ba. Babu yadda za ayi ya manta da wannan fuskar, domin ita kaɗai ce abin da yake iya tunawa, ko dai ita ce abu na ƙarshe da ya ganu kafin barowar sa, ainihin duniyarsa. Ko kuma shi ne na farko bayan ya shigo cikin wannan rayuwar mai kama da mafarki, a sabuwar duniyar da ya shigo!.
Ayshercool
08081012143
18
"La'ila ha illa anta, subhanaka inni kuntu, mina zalimin" Shi Nana take ta ƙoƙarin maimaitawa, duk da harshenta yana sarƙewa.
"Lafiya kuwa? Me ya faru?" Ta ji murya a gabanta.
Ta buɗe idonta, sai ta ga babu guguwar, babu kuma saharar. Wannan matashin saurayin nan ne na ɗazu da ta zo ta tarar a gidan.
"Lafiya na ga ki na dafe kai?"
"Amm.. kawai ji na yi kaina yana ciwo"
Cikin tausayawa ya ce "Sannu, Allah ya sa ba rigimar Haidar ce ta saka miki ciwon kan ba, idan kin ga aikin da takura ba za ki iya ba, ki ajiye kawai"
Da sauri ta ce "A'a ai babu wahala zan iya, kawai babu tsammani na ji ciwon ne, amma zan iya"
Ya jinjina kai ya ce "To shikkenan, har kin tashi kenan?"
Ta jinjina masa kai.
"To sai Allah ya kaimu"
Ta amsa da "To na gode" cikin sauri ta nufi hanyar waje, kuma duk wannan balahirar, ledar abincinta na hannunta.
Yana kallon yadda mutumin nan, yake biye da Nana, tana zuwa giftawa gurin ɗakin da yake tsaye, mutumin da yake binta, ya zura wata sanda ta tagar ya hankaɗa shi da ita.
A take ya yanke jiki ya faɗi a sume.
*****
Likita ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Babu wani abu da yake damun Muhsin, malaria ce +1 sai ɗan infection a jininsa, common antibiotics ma sun isa da ɗan anti malaria"
Alhaji Fatuhu ya ce "Haba doctor Sharif, ka ce babu abin da yake damunsa, ga malaria ga kuma infection, ni ban san ya aka yi aka bari sauro ya cije shi ba, matan nan sakacin su ya yi yawa"
Doctor Sharif ya ce "A'a su na iyakar ƙoƙarin su fa, ɗan Nigeria ai ɗai ɗai ne, ba su da malaria. Zan rubuta magunguna in sha Allah ba wani abu".
Ya yi rubuce-rubuce a kan takarda ya bawa Alhaji Fatuhu, ya ɗauki Muhsin ya je pharmacy ya sayo masa. Su na tafe Muhsin yana cewa "Daddy ka kaini gurin Anty Nana"
"Muhsin Anty Nana, ta bar school ɗin ku, kuma na tambayeta lambarta, ba ta da waya, amma zan saka a nemo ta in sha Allah"
Ya jinjina kai, suna tafe a hanya yana shafa kan yaron nasa, cike da so da ƙaunarsa.
Wayar Alhaji Fatuhu ce ta fara ringing, ya ɗaga tare da yin sallama ya ce "Alhaji zailani kun ji ni shiru ko?"
Daga can ɓangaren ya ce "Wallahi kuwa, ya gida ya iyali?"
"Alhamdilillah, wallahi Muhsin ne babu lafiya, na kai shi asibiti bari na ƙaraso kawai mu yi abin da za mu yi"
Cikin kulawa Alhaji zailani ya ce "Allah sarki, ɗan auta babu lafiya? Subhanallah abu bai yi daɗi ba, ayi masa sannu Allah ya bashi lafiya"
"Amin Daddy mun gode, bari mu ƙaraso yanzun nan in sha Allah" suka yi sallama.
****
Yamma ta yi sosai, Nana ta na sauri ta ƙarasa kafin magariba.
Tana shiga layinsu, Baba ya hangota ya washe baki ganinta da baƙar leda yana faɗin "Ga Nanaz ga Nana"
Ta ƙaƙalo murmushi domin ta san tatsuniyar gizo; ba wuce ƙoƙi, wannan sannu da zuwan na baƙar ledar hannunta ne.
"Baba sannu da gida"
"Yauwwa yarinyar kirki, sannu ya gidan aikin naki? Ina fatan babu wata matsala dai ko?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, babu wata matsala Baba"
Ya jinjina kai ya ce "To ma sha Allah, haka ake so, me ki ka ƙullo a cikin ledar nan ne?"
"Baba Abinci ne, ko za ka zo mu koma gidan sai ka ci?"
Ya ce "Ahhh lallai kin fara aiki a sa'a, yanzu jeki gidan maza ki jira ni, bari na je na yi salla yanzu zan dawo."
"Tom" ta amsa ta nufi gida.
Ko da ta yi sallama, ta yi mamaki da Jamila ta amsa mata.
Ta shiga ɗakinsu, ta ajiye ledarta da hijjabinta, ta fito Suwaiba na kwance kanta babu ɗan kwali, tana ta jin kaɗe-kaɗe, kanta ko ɗan kwali babu, ga shi an daf da fara kiraye-kirayen sallar magariba.
Nana ta yi alawala, ta je ta zauna ta fara azkar a ɗakinsu da yanzu suka bar mata, su Jamila a ɗakin mama suke kwana, Baba kuma sai dai ya kwana a tsakar gida, ko ɗakin su Nasir da suke tsula fitsarin kwance.
Idonta ne ya sauka a kan jakar fatar gurin sarkin baka, har cikin zuciyarta ta ji tana son sanin halin da yake ciki yanzu, tana son sanin halin da yake ciki ko ya warke?.
Tun da ta zo ba ta taɓa buɗe jakar ba, haka kurum ta ji bata ra'ayin hakan.
Shiru ta yi tana tuna abubuwa da dama, na rashin Auwal, sake guduwar Imran da haryanzu ba ta san a wane halin yake ciki ba, an kama shin ko ba a kama shi ba Allah masani. Ga uwa uba rashin mahaifiya da yake damunta. Babu maraba da ita da marainiya. Ga uwar a raye amma an nesan ta su da ita, kuma ita ma ba ta bibiya ta ji a yaya suke.
Ga tarin matsalolin gidan su, da babu daɗi, ga rashin lafiyarta da ƙaddarorin rayuwa da suke bin ta kashi-kashi, kuma babu wani wanda za ta raɓa ta ji sanyi. A take ta ga duhun magaribar da ya kawo kai ya ƙara tsananta a zuciyarta. Sai ta ji tamkar duniyar ita kaɗai aka tsana. Duk da ta san idan ta yi aure, akwai yiwuwar ta samu sassauci, amma a wane irin aure ake saka ran sassauci? Auren da babu bincike babu shiri babu komai, burin mutanen gidan kawai su rabu da ita, saboda ta zame musu tamkar wani kaya ne marasa amfani da suka rasa yadda za su yi da ita. Baƙin cikinta ya ninku bayan tuna yadda mama, ta dage a kan ba zata ci gaba da zama da ita ba, ga sharri da ƙage kala-kala da suke nema su zama barazana a gare ta.
Ta yinƙura da ƙyar ta tashi ta yi sallar magaribar, da ta idar ta yi tasbihi ta idar, sai ta rasa wace addu'a ma yakamata ta yi.
Muryar Baba ta jiyo yana ƙwala mata kira a tsakar gida. Ta tashi ta ɗauki ledar abincin nan da yake doya ce fal da miyar ƙwai, ta kai wa Baba ta ce dama shi ta kawowa. Ya so ya tsare ta da surutu, sai dai ganin yanayinta ya sanya ya fasa, kar ya je ta burkice masa.
Har aka yi sallar isha'i ma, Nana na zaune tana ta tubka da warwara. Ba ta san iya adadin lokacin da ta yi, tana zaune tana ta tunani ba. Ji ta yi mararta ta cika da fitsari, dan haka ta tashi ta fita.
Tsakar gidan shiru ba kowa, alama dare yayi sosai, ta shiga ta yi fitsarin, ta fito da niyyar ta ɗebi ruwa ta yi alwala, ta jiyo Suwaiba ta fara kururwar a taimake ta, Nana tana sha mata jini.
Cak Nana ta tsaya, aikuwa Suwaiba ta fito da gudu tana kurma ihu, cikin zafin nama Nana ta danƙe ta.
Mama ta fito da gudu, haka ma Baba ya kaso da gudu daga ɗakin su Nasiru.
Kafin su ƙaraso Nana ta shaƙe Suwaiba, cikin ɗaga murya ta ce "Kar ki ƙara kiran sunana ki ce ina sha miki jini, ko dai ki bayyana kanki, ko kuma ki ka kuma kiran sunana sai na murɗe miki wuya, ko na haɗa ki da Ƙaisar ya babbake ki"
Mama ce ta yo kan su, tana ihun Nana ta cika Suwaiba, amma Nana ta saka hannu ɗaya ta ƙara shaƙe Suwaiba, aikuwa ta din ga kakari idanunta suka yo waje.
"Ki gaya musu ba ni ki ke gani ba"
"Dan Allah ki cika ni, wallahi ba ke nake gani ba, ki yi mini rai"
"Da ba ki yi galaba a kaina kin cutar da ni ba, sai ki koma kan 'yar uwata ki saka a din ga zargina?"
Cikin dasashshiyar murya Suwaiba ta ce "Ba zan sake ba ki yi haƙuri"
"To bar nan gurin, ko kuma na saka a kai ki gurin sarkin baka, ya rufe ki a cikin randarsa"
"T..to..tom" Nana ta hankaɗeta ta faɗi ƙasa.
Baba da Mama suka yi kan Suwaiba da take ta wani irin tari, yawu mai kauri da yauƙi na wahala na fitowa daga bakinta.
Nana ta nuna su da yatsa ta ce "Kullum ba ta da aiki sai jin kiɗa da shigar banza, idan ba ku yi wasa ba, sai ta kashe ta tukuna"
Baba ya kalli Nana ya ce "Wace ce?"
"Wata bararoji ce take zuwa kanta, tana shan jininta, amma na manta meyafaru amma dai... Ba ta ƙarasa maganar ba, ta daina ganin su Baba, sai ƙaisar.
Muryar ƙaisar ta ji ya ce "A tunaninki bayanin da ki ke yi musu zai sanya su yarda da ke ne? Sai ma dai su yi miki wani sharrin. Uwar ɗakin Jamila ce suka bayar da turare a kawo miki, da kin shafa turaren nan, da shikenan jininki za a kai ƙungiyar matsafa."
Cikin damuwa Nana ta ce "Meyasa a zahiri idan na tashi ba na tunawa?"
Yayi murmushi ya ce "Saboda babu wanda zai yarda da ke, kuma ba ma wannan ba, muddin ki ka fara faɗar haka kin haifar da matsalar da dole sai kin samar da maganinta ne. Maganin kuma shi ne karɓar ƙaddararki."
Tsaki ta ja tare da haɗe rai.
Ya bayyana a gabanta a suffar wani ƙaton baƙin tsuntsu.
Ya ce "Da kin amince ki na zaune, ni zan din ga kawo miki maganin, aikinki bayarwa kawai. Marasa lafiya za su din ga magana da ni ta hanyar ki"
"Ban san tsawon shekaru nawa za a ɗauka ina nanata maka ba zan yi shirka ba"
Ya buɗe fuka-fukansa yana shawage a gurin ya ce "Ba zan nemi yanka, ko sadaukarwar jini ba, in nemi a yi mini yanka ko makamancin haka shi ne shirka.
Kuma maganin da zan bayar babu najasa a ciki, ba na cikin jerin aljanun da suke zama a cikin najasa. Ba zan ci gaba da musu da ke ba.
Na san dole akwai lokacin da zai zo ki buƙace ni.
Zan nuna miki wani abu, amma kafin nan ki tabattar zan hukunta ki a kan tsakin da ki ka yi mini.
Kalli can"
Ta kalli gurin da ya nuna mata, Muhsin ne ya bayyana a jikin mahaifinsa, yana karkarwa. Wata mata ta gani tana ta ɗaɗɗaura masa wani baƙin zare a jikinsa, amma da alama daga uban har uwar yaron babu wanda yake ganinta. Dan sai ɗura masa maganin bature suke yi, su na shafa masa ruwa a jikinsa.
A take Nana ta kiɗime, sai dai kafin ta yi magana ya tari numfashinta da cewar "Kuma ina mai sake gargaɗinki da lallai ki daina zuwa wannan gidan da ki ka fara zuwa, dan kuwa ba ni da tabbacin za mu tsira daga abubuwan da suke tunkarar mu daga ni har ke"
"Ni Allah ne yake kula da ni da ƙaddarata, kuma idan na bar gurin na daina zuwa, kai za ka din ga bani ci da sha? Ina duk a dalilinka na rasa aikina?"
"A'a ba dalilina ba ne ba, kuma dan dai abin da za ki ci ki sha ki yi buƙatun rayuwa ba zai gagara ba. Na san inda zan kai ki, ki bayar da maganin na samar miki da komai"
"Wallahi ba zan yi ba"
"Shikenan, sake kallon can"
Ta sake ɗaga kai ta kalli gurin, da sauri ta sanya tafukan hannayenta ta rufe idanunta. Alhaji Zailani ne, a tsaye tsirara ya gurfana yana lasar jini a wata tasa.
Ƙaisar ya ce "Jinin ɗan Adam ne ɗan uwanku yake lasa, wanda duk muguntarmu a jinsinmu ba za mu yi wa junanmu haka ba. Kuma yana cikin mutanen da ku ka gani, da ke da sarkin baka, da gawar mai ciki. Sannan ki sani a gidansa ki ke aiki, kuma kema babu tabbacin za ki tsira daga gare shi"
Nana ta sauke tafukan hannayenta da sauri, domin yi wa ƙaisar magana, amma ta ganta a kan shimfiɗarta a kwance, zuciyarta na wani irin matsanancin bugu, da take iya jin sa har cikin kunnuneta. Sai dai juyin duniya ta tuna me ta gani a bacci abu ya gagara, tayi-tayi, amma ta kasa tuna komai.
****
Sosai su sule su ka yi mamaki yadda suka zo ɗaki, suka tarar da shi a sume. Saboda ya samu sauƙi, har ya tashi ya yi wanka ya ɗan fita ya zagaya. Duk da baya magana amma akwai alamun sauƙi a tattare da shi.
Su na tunanin ko Asibiti za su kai shi, sai kuma