Showing 75001 words to 78000 words out of 189977 words
dai ɗan Adam zai rama halacci ire-irena da yaran da ki ka riƙe, za su yi miki addu'a. Kar ki manta ba ke kaɗai ba ce uwar mumunai Allah ya ƙara mata yarda, ba ta samu haihuwa ba amma uwa ce ga dukkanin muminai, a rashin samun haihuwar nan, ke ba ki san me Allah ya tanadar miki ba, wanda bai bawa waɗanda suka haihu ba" kai tsaye kalaman Nana suka din ga shiga zuciyar Hajiya Amina, da sai da hawaye ya cika mata ido. Ta ji daɗin kalaman Nana, na ƙwarin gwiwa, ta yi mamakin yadda Nana ta iya tsara maganganu cikin hikima.
"Na gode sosai Nana, kin ƙara sawa na ji nutsuwa, Allah ya ba ki zuriya ta gari. Ka da Allah ya jarrabe ki da ƙaddarar rashin haihuwa. Duk ta tawakallinka, akwai gaɓar da mutane mussaman 'yan uwanka mata sun saka ka ji tamkar ba ka da amfani."
"Amin na gode sosai Hajiya. Amma ta ki jarrabawar ki ka sani, da wata jarrabawar gara rashin haihuwa sau dubun dubu" haka su ka din ga hira da Hajiya Amina, har lokacin tafiyar ta ya yi.
Tana shirin tafiya, Shukura ta dawo, Haidar yana kallonta, amma bai damu ya je gurinta ba, ya rirriƙe Nana yana cewa zai bi ta ta tafi da shi ba. Da ƙyar ta lallaɓa shi, ta fita.
Habu na ganinta ya taso zai buɗe mata gate, ya ce "Malama har kin taso?"
Nana ta ce "Eh malam Habu, shekaranjiya na zo zan fita, duk ba kwa nan"
"Eh wallahi mai gidan nan ne ya aike mu"
Ta ce "Allah sarki, yauwwa dan Allah ina wannan ɗan uwan naku?"
Habu ya ce "Wanne daga ciki?"
"Wannan ɗin nan"
"Ya sunan shi?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ban san sunansa ba, ɗaya ɗan uwan naku dai Sule ya ce mini ba shi da cikakkiyar lafiya, kurman nan" Habu ya kwashe da dariya ya ce "Kayya ba kurma ba ne ba yana magana"
Ta ce"To ai shi kullum baya magana, fuska a rufe kamar amarya. Shi ya buɗe mini ƙofar ranar na fita"
"Allah sarki, yana gane komai, kawai da larura ce a ƙwaƙwalwarsa, ba kuma wai hauka yake yi tuburan ba, wasu lokutan ma sai ya shafe sati bai ce uffan ba, yana kwance ma ba lafiya"
Cikin tausayawa Nana ta ce "Allah ya sauwwaƙe, na tafi sai da safe"
"To sauka lafiya, Allah ya tsare" ta amsa da Amin ta tafi.
Ɓoye wayarta ta yi, saboda ta san tsaf Baba zai ƙwace wayar nan, mussaman yanzu da yake neman kuɗi ido rufe.
Bayan Nana ta koma gida, Jamila take tambayarta ashe sun haɗu da Hajiya Sa'a a gidan rasuwa, amma ta ce ba ta santa ba.
Nana ta ce "Ina cikin jimami da alhinin mutuwar yaron ne, shiyasa na kasa gane ta"
Jamila ta ce "Allah sarki, ashe yaron ma sunanki ya yi ta kira kafin ya rasu"
Nana ta kalli Jamila daga sama zuwa ƙasa ta ce "Wannan karon ma ni na kashe shi ko?" Ta yi magana tana tsare Jamila da ido.
Jamila ta ce "A'a ni ban ce ba, kawai labari fa take bayarwa"
Nana ta gyaɗa kai cikin gargaɗi ta ce "Jamila ina son hawainiyar matar nan ta kiyayi rama ta, idan ta ci gaba da ƙoƙarin cin iyaka ta, za ta faɗo cikin wutar da za ta ƙona ta da ita da amfanin gonarta, wannan saƙona ne a gare ta." Saroro Jamila ta yi cikin tsoro, jin yadda Nana take magana kamar an shaƙe ta.
Kamar kuma wadda ta razana a cikin bacci, jikin Nana ya ɗan yi girgiza sannan ta ce "Jamila yau wainar fulawa nake sha'awa, zan sai fulawa ki sai mana manja, mu soya mana" da yake sun saba yin haka.
Jamila kawai ta jinjina mata cikin tsoro.
Da daddare Jamila ta samu Nana tana shirin kwanciya bacci ta ce
"Nana wai Hajiya Sa'an wani abun ta yi miki ne, ki ke cewa na yi mata kashedi?"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce Hajiya Sa'a?"
"Wadda ku ka haɗu a gidan rasuwa"
Nana ta ce "A'a wani abin ta ce na yi mata?"
"A'a to ai ke ce ki ke cewa na ce ta kiyaye ki, kuma babbar mace kamar wannan shi yasa na tambaye ki"
Nana ta waro ido ta ce "Ni babu abin da ta yi mini, ni fa ko magana ban yi mata ba, me ta yi mini zan ce ta kiyaye ni?" Sai a lokacin Jamila ta fahimci kamar Nana ba ta san ta yi maganar ba sai ta ƙyale ta.
Ranar da aka bawa Nana albashi, kamar ta taka rawa, ganin ta mallaki dubu ashirin ta ta, ta kanta. Ga dubu ashirin da Alhaji Zailani ya ce a bata, baban Haidar kuma ya ce a bata dubu goma, sai da ta tashi da dubu hamsin. Iya salarynta ta yi murna da shi, wanda aka ce Alhaji Zailani ya bata kuwa, ji ta yi tana ƙyanƙyamin su.
Da murna ta nufo gida, tana tunanin wace bajintar yakamata ta yi a gida, yadda kowa zai amfana.
Amma tana zuwa Baba ya turke ta da bala'i "Wai Asma'u ba za ki ƙuƙuta a samu komai a hannunki ba? Ƙanin uban yaron nan ya kira ni a waya, yana idan ba zan dawo da kuɗin ba, hukuma ce za ta raba mu, ba ki da asara ko a jikin ki ko?"
Nana ta saka hannu a aljihun rigarta, kasancewar kuɗin dubu goma goma ne, ta ciro uku ta bawa Baba ta ce "Baba wannan ne kawai a hannuna, nima yau aka biya ni albashi".
"Yauwwa ko ke fa, ba zan taɓa su ba kiran su zan yi su zo su karɓi abin su, duk da koma me aka yi mini ke ce sila, da kin haƙura kin kwantar da hankalinki shikenan, amma mugun halinki ya sanya ki ke ta yi wa yaron nan wulaƙanci, yanzu kalli halin da ki ka jefa mu" Nana ta daina mamakin ƙarfin hali da son kai irin na Baba, sai dai ta yi shiru ya gama surutansa ta tashi ta tafi.
Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta juye zuwa ga babba, domin kuwa Saleh cewa ya yi ba zai karɓi dubu talatin ba, dan ko kwatan abin da ya kashe ba a ba shi ba. Dan haka ya kai Baba police station.
Haka aka turo jami'an tsaro, suka tisa ƙeyar Baba zuwa gurin 'yan sanda. Sai Gaddafi aka nemo, ya bi bayan su.
Gaddafi ya kalli Saleh, ya ce "Yanzu kai Saleh saboda rashin ta ido, ka rasa wanda za ka kawo gurin 'yan sanda sai mahaifina, saboda rashin kara, ko dan zaman amanar da muka yi a ikko, ga yayanka na auren ƙanwata."
Saleh ya ce "Ka ga malam, a batun kuɗi babu wata kara, yarinyar nan ba ƙaunata take yi ba, har tana neman hallaka ni, ban aure ta ba zan bar muku kuɗina ne?"
Duk yadda a ka yi da Saleh a yi sulhu, amma ya ƙi yarda, sai da aka yi yarjejeniya, cewar nan da kwanaki uku za su kawo kuɗinsa gaba ɗaya a ba shi".
Ranar yau na ɗaya daga cikin ranakun da Nana, ba za ta iya mantawa da su ba, domin bayan dawowarta gida, Baba ya din ga yi mata bala'i tamkar zai tsine mata, har da cewar ya yi dana sanin haihuwar su da ɗan uwanta, ya yi dana sanin haɗuwa da mahaifiyar su har ya aureta ta haife su".
Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ka yi haƙuri ka yi shiru haka mana, sai ɗaga murya ka ke yi duk maƙwabta su na jin ka, kuma ka na ta cewa ta nemo kuɗi a biya, ka san dai ba wata sana'a take yi ba, idan kuma ba hanyar banza ka ke son ta shiga ba"
Cikin takaici Baba ya ce "Ka bar ni Gaddafi, ban taɓa haifar ɗan da yake neman ya yi ajalina ba kamar Nana, da me zan ji ne? Ba ta tausayina ko kaɗan duk wata hanya da zan bi na aurar da ita, ta nutsu nima na nutsu ta ƙi, a dalilinta a ka kai ni station a ke nema a rufe ni. Lokacin da aka haife ki babu farin cikin da ban yi ba, na so ki, amma kina neman ki kashe ni. To wallahi idan kuɗin nan ba su samu ba a ka rufe ni, sai kin bar gidan nan, kuma kwana ki bakwai na baki ki fito da wani mijin, ko ki koma gurin uwarki ki bar mini gida"
Ayshercool
08081012143
23
Cikin maɗaukakin sauti Nana take kuka "Baba ka kashe ni ka huta, idan ma ba ka kashe ni ba, ni zan kashe kaina wai ya ake so na yi ne?" Gane nufin Nana da Gaddafi ya yi, ya sanya cikin tsananin zafin nama ya rigata isa gaban rijiyar, ya rufe ta, tana ƙarsowa ta yi karo da Gaddafi ta faɗi ƙasa.
Ya kalli Baba ya ce "Yakamata ka din ga haƙuri, ka din ga tausasa lafuzanka, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya idan ta kashe kanta, kai fa abin zai dama fiye da kowa. Kuma maganar kuɗin nan, ka bar komai a hannuna ko ba duka ba za a samo wasu, ka daina cewa ta fita ta nemo kuɗi a biya. Ka daina biye shawarar da ake baka ta banza, mai baka shawarar ba za ta bari ka yi wa yaranta haka ba"
Ya durƙusa ya ɗaga Nana, kawai ya ji tausayinta ya kama shi. Matsaloli sun yi wa rayuwar ta yawa.
Duk da uban nauyin da ta yi, tamkar ta haɗiyi dutse, haka ya ɗaga ta ya kai ta ɗakin su, ya kwantar da ita.
Har ya yinƙura zai tashi, Nana ta danƙo rigarsa, ya kalle ta, idanunta a rufe, sai ruwan hawaye da yake zuba ta gefen idonta.
"Nan gaba kan tsohon nan zan cilla a rijiya, ya iya bakinsa"
Gaddafi ya ce "Wane tsohon? Baban ki ke nufi?"
Kawai ta tashi zaune, ba tare da ta buɗe idonta ba ta riƙe hannayensa. Ji ya yi kamar an jona masa shocking, jikinsa tamkar za fizge naman jikinsa, ga shi ya kasa motsi, ya kuma kasa magana.
Ta yi murmushi ta ce "Ina fatan yanzu ka gane mai baka saƙon? Ina ƙyale ku ne saboda ku ne abu ma fi soyuwa ga uwar gijiyata."
A hankali ta saki Gaddafi ta silale a gurin. Tamkar korarrare Gaddafi ya fita cikin tashin hankali, babu wanda ya tsaya yi wa magana ya fice. Tun da Gaddafi yake bai taɓa shiga bala'i irin wannan ba. Har a lokacin da ya fita, da ƙyar yake iya sarrafa jikinsa tamkar zai fita hayyacinsa.
Washegari da safe tamkar babu abin da ya faru, Nana ta shirya ta gaida Baba za ta fita amma ya yi mata banza, jikinta babu ƙwari ta tafi gidan Alhaji Zailani.
Inda Allah ya taimake ta, tun da wannan abin ya faru, bai ƙara yinƙurin far mata ba.
A hankali take bubbuga gate ɗin, duk da ba ta da tabbacin ma, ana iya jin bugun nata. A yadda take jin duniyar ta yi mata zafi, ji take tamkar ta nemi guri ta kwanta a nan ƙofar gidan.
Aka buɗe gate ɗin, tana ɗaga kai suka yi ido huɗu. Dumm! Gabanta ya yi mummunar faɗuwa, babu shiri ta sunkuyar da kanta, ita ba ta shiga ba, ita kuma ba ta koma ba.
Kawai ya mayar da ƙofar zai rufe, babu shiri ta tura ta shiga, ta kalle shi tana son ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kwarjini da babu wani ɗan Adam da ya taɓa yi mata. Ƙoƙarin gane kamaninsa take yi, amma babu dama rawaninsa ya rufe ko ina na fuskarsa sai idanunsa kawai.
Ta kama hanya ta nufi cikin gidan, sai da ta je tsakiyar harabar gidan, sai ga wasu irin murguza-murguzan karnuka da ba 'yan Nigeria ba, idan ta zo haushin su kawai take ji, ba ta taɓa ganin su ba, da daddare ake sakin su, da safe kuma a mayar da su keji, da guda ɗaya ne a ka ƙaro biyu. Yau kuma Sule bai samu ya mayar da su ba.
A gigice ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta watsar da takalmanta ta zura da gudu, aikuwa suka rufa mata baya su na wani irin haushi mai ban tsoro. Yana tsaye yana kallonsu, kafin ta ƙaraso gurin da yake har ta fara fita daga hayyacinta.
Cukuikuye shi ta yi tana ihu, ta daina ganin komai, sai su biyu a cikin sahara, sai kuma jin sautin haushin karnukan.
Ƙaisar ne ya bayyana, ya yi wata irin girgiza, ya zama wani irin narkeken kare shi ma, haushi ɗaya ya yi sai da gurin ya yi amsa kuwwa a take karnukan suka gudu, kamar barewar da ta ji kukan zaki.
Ya girgiza jikinsa ya koma yadda yake, ya miƙa masa hannu ya ce "Ko da wasa, idan ka sake yinƙurin razana ta, ko wani abu na cutarwa a gare ta, zan shafe tarihinka a duniya".
Nana ta buɗe idanunta da kyar, ta kalli yadda buzun nan, ya rikiɗe ya koma tsohon nan mai kama da ƙaisar. Sai dai ko motsi ta kasa.
Wata irin dariya tsohon ya din ga ɓaɓɓakawa, gurin ya din ga amsa kuwwa.
"Kai ɗan samari, ka sake nazarin kalaman da ka faɗa, bayan tsawon shekaru mun sake haɗuwa, mun kuma haɗu a gaɓar da ta dace Ƙaisar" ya yi maganar yana ci gaba da dariya.
A hankali ya ɗago Nana daga jikinsa da ta riga ta suma, ya kalli harabar gidan duk wannan kururwar da ta yi, babu wanda ya fito.
Ya sanya yatsunsa biyu, manuniya da na kusa da shi ya daki goshin Nana sau uku.
A hankali ta motsa ta ɗaga kanta, a falon cikin gidan ta ganta. Hajiya Amina ta ce "Ohh sannu Nana, haka ki ke tsoron kare? Laifin masu gadi ne da ba su mayar da su sun rufe ba, sannu ba ki ji ciwo ba ko?"
Nana ta jinjina kai hawaye na zubowa daga idanunta. Alhaji Zailani ya fito falo, sai baza ƙamshi yake cikin dakkakiyar shadda.
Ya tsaya a falon ya kalli inda Nana take ya ce "Lafiya kuma take kuka?"
"Wallahi karnuka aka bari ba a kulle ba, suka biyo ta shi ne har da kakunta, yanzu suka shigo tare da Yusuf"
Ya girgiza kai ya ce "Laifin masu gadi ne ai, bari na fita sai na dawo"
Nana ta ƙura masa ido, tana son tuna wani abu a kansa, amma ta kasa, ta ci gaba da kallonsa har ya fice.
Da ƙyar ta iya jan ƙafafunta, ta tafi ɗakin Haidar. Ta shiga banɗaki domin wanke fuskarta, ta tsaya ta zuba wa fuskarta ido a jikin mudubi.
Ta yi shiru tana tuna tun daga tashinta, zuwa yadda ta zo gidan nan, daga lokacin da karnukan nan suka biyota, tunaninta ya hargitse gaba ɗaya, ta kasa bambance mene ne ya faru a zahiri, menene ya faru ba a zahiri ba, kuma Hajiya Amina ta ce mata, tare suka shigo da Yusuf to ta yaya?
Ɓangaren kanta ɗaya ya sara, da sai da ta dafe kan nata. "Wai ko ni ma dai ba mutum ba ce ba? Ko kuma dai ƙaisar ya fara nasarar raba ni da hankalina ne?" Ta furta a hankali cikin tsoro da sheshsheƙar kuka.
Jin ana bubbuga ƙofar banɗakin, ya sanya ta sauri ta wanke fuskarta ta fito. Haidar ta gani a tsaye yana mutsutsuka idanunsa. Ta kama shi ta wanke masa baki, ta yi masa wanka.
*****
Alhaji Zailani ne a zaune a cikin motarsa, gefensa kuma doctor Sharif ne a ciki a zaune.
"Sharif"
"Na'am Alhaji" ya yi maganar cikin girmamawa.
"A wannan karon ma, taimakon da ka saba nake so ka yi mini"
Doctor Sharif ya ce "Babu abin da zaka nema, na kasa yi maka shi, ka faɗi ko mene ne"
"Yaushe ne EDD ɗin Shukura?"
Ya ɗan yi shiru ya ce, scanic biyu dai ta yi a yanzu, amma duk a cikin watan jibi ne, suka nuna za ta haihu"
"To ka saurare ni da kyau, na san dole a asibitinku za ta haihu, idan ta sauka ina buƙatar jaririn"
Doctor Sharif ya kalle shi da sauri, ya ce "Ban fahimta ba"
"Sharif da hausa nake magana, idan Shukura ta haihu, ina buƙatar jaririn duk yadda za a yi, a yi kawai ina buƙatar jaririn. Ka tuna idan ka kuskura kalma ɗaya ta fita daga maganar da muka yi da kai, to zan iya zame kaina na barka, kuma ba ka da shaida, idan kuma ka yi shiru komai ya tafi dai-dai, zan baka abin da zatonka da tunaninka bai taɓa zata ba" Jiki na tsuma Sharif ya ce "In Allah ya yarda babu wanda zai ji, ba zan taɓa buɗe sirrinka ba"
Alhaji Zailani ya ciro envelope ya bawa Doctor Sharif ya sallame shi.
*****
Nana kuwa tana tunkarar gida, gabanta na tsananta faɗuwa, tabbas da tana da wani gurin zuwan, babu abin da zai sanya ta je gidan ta kwana, saboda fargabar abin da za ta tarar a gidan.
A can ƙasan maƙoshinta take sallama, Mama ta kalleta ta yi mata banza, haka ma Suwaiba.
Ba ta sake magana ba, ta shiga ɗaki ta jima a ɗaki sosai, sannan ta fito tsakar gida ta fara ɗan kaye-kaye, saboda yadda zama ɗakin ya ishe ta, tunani da damuwa, duk suka addabi Zuciyarta.
Tana jin sallamar Baba, gabanta ya faɗi, ta miƙe tsaye hannunta riƙe da tsintsiya, dan ta san dole sai ya yi mata wani abin da ranta zai ɓaci. Sai dai ga mamakinta sai ya washe mata baki.
"Yarinyar kirki irin albarka, kamar dai yadda na yi tsammani, ke ɗin ce dai maganin hawayena. A dalilinki Allah zai fitar da mu daga wannan baƙin talaucin da wahalar da muke ciki. Idan zan iya tunawa shekarar da aka haife ki an yi ruwan sama marka-marka, an samu amfanin gona mai kyau da yawa"
Nana ta yi fakare da kai tana kallon Baba, duk wannan hawa da saukar da yake yi ba ta gane ina ya dosa ba.
"Zo ki zauna mu yi magana Asma'u ma'ulle, maganin kukana dama na daɗe ina mafarki gani a harami, ashe ke ce za ki yi silar komai" da kansa ya jawo tabarma ya shimfiɗa, ya karɓe tsintsiyar hannunta ya jefar, ya yi mata umarnin ta zauna.
Ta nemi guri ta zauna, ya kalle ta fuskarsa cike da farin ciki ya ce "An gama biyan wancan matsiyacin kuɗinsa"
Kai kawai Nana ta jinjina, zuciyarta ɗauke da tambayar a ina Baba ya samu kuɗin.
"Ɗazu wajen azahar, ina zaune ina ta hamma, na yi wani baƙon alkhairi. Wallahi Nana komai na duniya rabo