Showing 123001 words to 126000 words out of 189977 words
kuka, aka din ga surutu, har labari ya iske mai gari.
Aka yi ta yekuwar wa ya aikata wannan abu, kar a je wata fitinar ce za ta taso.
Kakan Lanti da kansa ya je ya samu mai gari, bayan sun gaisa ya ce "Ranka ya daɗe, ni ne na ɗaura wannan farin ƙyalle, yau da yamma zan yi wa jikata Lanti, girkar aljanu"
Mai gari ya waro ido ya ce "Girkar aljanu kuma? Kar ka janyo mana bala'i bayan wanda muke ciki, kuma ya za mu yi idan sarkin aska ya ji, kar aljanu su fushi da mu fa?"
"Babu abun da zai faru sai alkhairi, ba zamu dauwwama Sarkin aska, yana juya mu yadda yake so ba, ina son ka yi haƙuri ka bani wannan damar"
Da ƙyar ya shawo kan mai gari ya amince, aka din ga shela ana gayyatar mutane, gurin yin bikin girka.
Mutane suka din ga al'ajabi, tare da jiran yammacin ranar lahadin, domin ba su taɓa sanin yadda ake gudanar da girkar ba. Nana da labari har maƙwabtan garin, aikuwa jama'a suka din ga ɓarkowa cikin garin.
Kakan Lanti tun safiyar ranar, ya sanya ta yi lalle dungulmi, hannu da ƙafa. Ya bata fararen kaya na saƙi, ta saka ya kawo warki, na fatar kura da aka jeme, aka saka ta a shuni, ta ɗaura a ƙugunta, sannan ya kawo wuri ya bata shi ma ta sanya a ƙugun nata.
Daga bisani ya kawo wasu irin guraye, ta ɗaura a damatsenta.
Ya kawo sandar dargaza ya bata, sanda ce da aka yi da itacen tsamiya, aka naɗe ta da fatocin dabbobi daban-daban, suka yi beza a jikinta.
Tun daga gidan kakan Lanti, ta samu rakiyar mutane, ɗuuuu tamkar ƙudaje zuwa filin girka.
Fili ya cika ya tumbatsa, aka shimfiɗa saƙi kala-kala a gurin.
Ya bata wani kwalli ta sanya a gurin, ya ba ta goro da fure, ta saka a bakinta ta tauna, laɓɓanta suka yi jawur. Idanunta su ka yi rabajau da kwalli.
Tuni makaɗan borin, da kakan ya gayyato daga wasu garuruwan suka jeru, suka fara kaɗa garaya da goge.
Ya bawa Lanti, wannan tsumin na cikin kwatanniya ta sha, ya saka ta zauna a kan shimfiɗar nan. Ya din ga ɗebo ruwan cikin randar nan yana zuba mata, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, har zabura take yi saboda sanyi.
Ya kawo turare ɗan goma ya shashshafa mata, ya kawo wani gwado, ya rufa mata. Sannan aka koma gefe aka kunna hayaƙi.
Ya koma gefe shi ma ya hau kaɗa kacakaurar da ya haɗa.
An ɗauki dogon lokaci a haka, kafin ta fara murƙususu a cikin gwadon da aka rufe ta da shi, tana wani irin kakari. Shewa masu kiɗan borin suka hau yi, ana murnar aljanun sun fara hawa kanta, dan haka suka ƙara ƙaimi gurin ci gaba da kiɗan borin.
A hankali ta tashi tsaye, tana wata irin girgiza, bakinta na fitar da kumfa, ta ɗaga wannan sandar ta dargaza, ta fara tangaɗi a gurin.
Mutane suka ɗauki sowa, gwargwadon tashin kiɗan, gwargwadon tangaɗin da take yi, tana girgiza dogon gashin kanta.
Babu tsammani, gari ya yi duhu, wani irin hadari ya haɗu, sai dai hadarin na guguwa ne. A take jama'ar gurin, suka tsatstsaya, su na kallon yadda garin ya canza, su na jiran ganin abun da zai faru.
Tukunyar tsumin da aka zo da ita ta tarwatse, wata irin gigitacciyar guguwa ta turnuƙe gurin, har wani ba ya iya ganin wani.
Sarkin aska ne ya bayyana tamkar an jefo shi, a hankali kuma ƙurar ta fara lafawa.
Lanti kuwa cak ta tsaya, hannunta riƙe da dargazarta, ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sarkin aska ya nufo inda Lanti take, cikin azama kakanta ya shiga tsakaninsu, ya tari Sarin Aska, wani irin jifa ya yi da tsohon a gefe. Lanti ta ɗago da kanta, suka yi ido huɗu da Sarkin Aska. Cak ya tsaya yana kallonta cike da mamaki ya ce "Uban duƙusa"
"Ka durƙusa akan gwiyoyinka, ka nemi afuwar uwar gijiyata, kafin raina ya ɓaci" ta yi maganar cikin wani irin sautin muryar da ba tata ba.
Sarkin aska ya ce "Kai yanzu da kai aka yi wa maƙiyanmu girka? Ka manta zaluncin da bil adama suka yi mana? Ka manta gargaɗin da kakaninmu suka yi mana a kansu?".
"Ban manta ba, kuma ina bayan gaskiya har abada, ku kuka fara karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi, dan haka ba zan bi bayan ɓarna ba, dan haka ka yi abin da na ce"
"Har abada. Har abada ba zamu yi maka biyaya ba, duk da kasancewarka abu mafi soyuwa a zuriyarmu."
Nana ji ta yi an yarfa mata ruwa a fuska, ta buɗe idonta da sauri. Ido huɗu suka yi, ya sakar mata tattausan murmushi. Ya ajiye matajin da yake taje kansa da shi ya nufo ta, cikin hanzari ta shige cikin bargo da kanta.
Ya zauna a kusa da ita, ya saka hannu ya janye bargon, ta ƙi buɗe idonta, sai ma miƙa da ta yi, saboda duk jikinta ciwo yake yi, kuma sam baccin bai ishe ta ba. Ya zuba mata ido, murmushi ya gaza barin fuskarsa.
"Ina kwana" ya faɗa yana kallon ta. Kasa kallon sa ta yi, ta sunkuyar da kanta tana basarwa.
"A tashi a karya" ya yi maganar murmushi ya kasa barin fuskarsa. Ta ja jikinta ta tashi zaune da ƙyar.
"Bari na yi brush" ta tashi ta nufi toilet.
A banɗaki ta tsaya ta yi shiru tana tunanin littafin da take karantawa na Ƙaisar, ta san yanzu kafin ta sake samun littafin sai an daɗe. Kenan da gaske dai shi ne uban duƙusa? Ya aka yi sunansa ya canza zuwa Ƙaisar?
Ta wanke fuskarta ta yi brush ta fito. Har ya karkaɗe mata shimfiɗa.
Ta zauna, ya ɗaukko kofi da murfi ya miƙo mata. Ta saka hannu ta karɓa, ta buɗe ta ga abu a kofin kamar madara, da ɗan wani gari gari a kai.
Ta kalle shi ya ce "Sha" ta kai bakinta, ta ji babu ƙarni, ta yi bismillah ta fara sha.
Babu zaƙi, sai dai akwai garɗi da maiƙo a baki, ga ɗumi kuma babu ƙarni mai damu. Sai da ya saka ta shanye tas, ta kalle shi ta ce "Wai mene ne wannan?"
Ya yi murmushi ya ce "Nonon raƙumi ne"
"Raƙumi kuma? A ina ka samu Nonon Raƙumi?"
Ya ce "Habu na saka ya kawo miki, jikinki zai yi ƙwari, ga abinci ma sun haɗo da shi, na ce ba ki da lafiya"
"Gaya musu ka yi?"
Ya ce "Me?"
"Abin da ya faru jiya?"
"A'a ban ce musu, kin kore ni waje ruwa ya jiƙa ni saboda ki na tsoro na ba"
Ta ce "Ba wannan ba"
"To me?"
"Ba komai" tayi maganar cikin basarwa.
Ya yi dariya ya ce "Ban faɗa ba, daga ni sai ke kawai wannan" ta yi shiru wata irin kunya tana mamaye ta.
Babu babban abin da yake ƙara sanya Nana farin ciki, sama da samun abinci sau uku a rana da take yi a wadace, babu geji kuma babu hantara.
Ƙaton buredi ne lafiyayye, aka soya ƙwai fal, shayin ma shi ya zuba mata. Tana ci yana ƙare mata kallo.
"Ka daina kallona, ko na tashi"
"A'a"
Ta ce "A'a me?"
"Ba zan daina ba"
Ta juya gefen sa, yadda sai dai ya kalli side ɗin fuskarta, ta gama ci ta koma gefe.
Shi ya yi mata komai, da ta motsa sai ya ce ta zauna. Sai dai ya lura gaba ɗaya ta zama so silent yau, ba karaɗi da surutu. Duk sai ya ji hakan babu daɗi. Ita kuwa ta yi matuƙar mamaki, ganin yau bai fice ya bar ta ita kaɗai ba.
Ya dawo kusa da ita ya zauna, har gashin sa yana taɓa wuyanta, kasancewar bai tufke shi ba, sakin sa ya yi.
"Me ya faru?" Yayi maganar yana ɗora hannunsa a nata.
Ta girgiza masa kai, alamar babu komai.
"Ko ana fushi ne?" Ta ɗaga kai alamar eh.
"Me yasa?" Ya tambaye ta, yana shafa jikinta.
A ranta ta ce "Ikon Allah, ji mutumin nan da samun guri"
"Ba ki ce mini ya jiki ba, kin kore ni ruwa ya jiƙa ni, ba ni da lafiya"
Nana ta tura baki ta ce "Ba ga shi ka warke ba, kuma ba ina sane bane ba"
"To ke kin warke?" Yayi maganar ƙasa-ƙasa. Cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa, hakan ya ba shi damar haɗe bakinsa da nata. Gaba ɗaya Nana sai ta rasa bakin magana, sai rarraba ido.
Yana sane yake wannan shirun, yana sunkuyar da kai, ko kuwa ya abin yake? Ta tambayi kanta.
Tana jin yadda ya ƙanƙame ta a jikinsa, sai yawo yake da hannunsa a jikinta, yana neman ya sanya lissafi ya ƙwace mata. Domin har mamakin kanta take yi, yanayin da take shiga, idan su na tare ko da kuwa a cikin bacci ne.
"Ammm ya aka yi yau ka ke magana sosai? Maganar ba ta ɗauke ba?"
Ya ce "Mmmm, tun jiya ma na ji ina iya yi, haryanzu ban ji kaman an shaƙe ni ba ta daina fitowa. Wataran ina son na yi nake kasawa"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To yanzu baka san sunan ka ba, wane sunan zan din ga gaya maka kenan?"
"Ko wanne"
"In ce Buzu nima?"
"Nima in ce buzuwa?" Ya tambaye ta.
Ta ɗago ta kalle shi ta ce "Buzuwa kuma?"
"Eh, macen buzu shi ne buzuwa ba? Idan ki na kallona zan kuma sumbutar ki ne a baki"
Ta yi sauri ta sunkuyar da kanta, ya sake gyara riƙon da ya yi mata da hannayen sa.
"To yanzu me zan din ga ce maka ne?"
"Ki saka mini ko mene, nima zan ji daɗi, kowa yana da suna ni ba ni da shi"
"To da yaya aka ɗaura mana aure ba ka da suna?"
Ya ce "Habu za ki tambaya"
"To ni yanzu ina na ga Habun?"
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ce "Ka ga kai mijina ne, to in ce maka Sayyid ka na so?" Ta yi maganar tana ɗagowa ta kalle shi.
Sake haɗe bakinsa da na ta ya yi, na wani ɗan lokaci, sannan ya cire bakinsa ya kalli idanunta ya ce "Sayyid, j'aime ça (I like it) ma vie"
"Ni ka daina yi mini wannan yaren ba na ganewa" ta yi maganar da sigar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba.
Murmushi ya cigaba da yi, yana lumshe idanunsa.
"Yau ba za ka fita ba ne? Kar su zo su na neman ka, kana nan a zaune"
"Ba na son fita"
Ta ce "Saboda me?"
"Saboda ke"
"Ni har yanzu mamaki ka ke bani, kamar an canza ka, ka yi magana ta fi guda goma sha biyar"
Wannan karon sosai ya buɗe haƙoransa ya yi dariya, ya ce "Kin ƙirga ne?" Ta ɗaga masa gira ɗaya tana murmushi.
"Me yasa nake ba ki tsoro? Me na yi yake ba ki tsoro?" Shiru ta yi ta rasa abin da za ta ce masa, kenan shi ma bai san abin da take gani ba.
Horn aka yi da mota, Nana ta fara ƙoƙarin zame jikinta ta ce "Ana horn, shi yasa na ce maka ka shirya ka fita, kar a zo ana buƙatar ka".
A matuƙar kasalance, ya tashi ya je gaban mudubin ya tsaya.
Nana ta tashi ta ɗaukko masa yin rawaninsa. Sai dai mai horn ɗin ya ci gaba da yi babu ƙaƙƙautawa.
"Sayyid ko za ka buɗe musu, sai ka dawo ka saka rawanin?"
Hankalinsa a kwance ya ce "Za ki iya fita ba riga?" Sororo ta yi tana kallon sa.
"Idan ba za ki iya fita ba riga ba, ba zan iya fita babu rawani ba, gashina a buɗe. Yadda ki ke jin abin da ki ke ɓoyewa haka buzu yake ji, idan ya fita bai suturta gashin sa ba".
"To ni dai ka bar wannan falsafar, ka yi sauri" a nutse ya naɗa rawanins, Nana na ta azalzalarsa, saboda horn ɗin ya wuce hankali.
Ya gama naɗawa ya fita, ya buɗe gate ɗin.
Ko ƙarasa shigo da motar ba a yi ba, ta fito daga cikin motar a matuƙar hasale cikin matsananciyar fusata ta ce "Malam bagidajen ina ne kai? Kurma ne kai ko ba ka ji ne? Wannan ai tsagwaron wulaƙanci ne?"
Bagidajen da ta faɗa ya sauka a ƙirjin Nana. Kallo ɗaya ya yi wa matashiyar budurwar, ya sake gyara zaman takunkumin fuskar sa, ya nemi guri ya zauna a kan bencin da yake zama.
"Ba magana nake yi maka ba? Ba za ka iya ba ni haƙuri ba?"
Cikin azama Nana ta sako hijjabinta ta fito, ta nufi inda Siyama take ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yana uzuri ne shi yasa bai fito da wuri ba"
"Ni kun san meye nawa uzurin da zan ta horn over 10 minutes, amma bai buɗe ba, kuma ina magana ya yi mini shiru dan wulaƙanci?"
Nana ta sake kwantar da murya ta ce "Ai ni na baki haƙuri a madadinsa, dan Allah ki yi haƙuri, ba zai sake ba"
"Wawa kawai" ta furta tana juyawa t nufi gurin da motarta take.
Nana ta haɗiye wani abu mai matuƙar ɗaci, ta ji zafin maganganun da aka gaya wa mijin nata. Duk da ta san ya yi laifi amma kalmomin sun yi tsauri. Ta kalli idonsa ta ga ya yi jawur, hannayen sa na rawa, launin fatarsa ya canza zuwa ja.
Ta zauna a kusa da shi a kan bencin, ta ɗora hannunta a bayansa ta ce "Sayyid. Ka yi haƙuri na fika jin zafin abin da ta gaya maka, amma ka yi haƙuri ka ji?" Kawai ya jinjina mata kai.
Ta sake kallon idanunsa, yadda suke ƙara rinewa zuwa launin ja, hakan ya ƙara bayyanar da matsanancin ɓacin ran da yake ciki.
"Taso mu koma ciki to, tun da ka buɗe mata" ya girgiza mata kai alamar a'a.
Jiki a sanyaye Nana ta tashi ta ƙyale shi, dan ya fara ba ta tsoro.
Duk da yanayin da take ciki, ta ji daɗin hirar da suka ɗan yi da shi.
Ta kama aikace-aikacen ta a cikin ɗakin.
*****
Jamila ce take gaya wa Mama batun unguwar da Hajiya Sa'a ta ce za ta raka ta.
Mama ta ce "To mene ne a ciki? Ai babu komai yadda take nuna miki ƙauna, ni ko bangon duniya ta ce za ku je, ai ba zan hana ba"
"To Mama Baba fa? Ni ba na son masifar nan tasa"
"Dalla rabu da shi, uwar me yake bamu a gidan, Ubangiji Allah ya haɗa ki da iyayen ɗaki masu ƙaunar ki, mu na samun alkhairi ta hannunsu, za ki din ga kawo zancen sa, ki yi tafiyar ki, ni na san abin da zan gaya masa"
Jamila ta yi murmushi ta ce "To shikenan, ni dama ba na jin ki, na san za ki bar ni"
Can Asibiti kuwa, likitoci sun yi deciding, tiyata za a yi wa Shukura a cire jaririn cikinta, saboda a tseratar da rayuwarta da ta abin da yake cikinta.
Sai dai da Jininta ya sauka sai ya sake hawa, saboda gaba ɗaya a tsorace take, ta yanke tsammani da rayuwar duniya ba ki ɗaya. Duk da irin rarrashi da ƙoƙarin kwantar da hankalinkin da ake yi mata.
Bayan Nana ta ɗora girki, ta kira Hajiya Amina su gaisa, a nan take gaya mata halin da ake ciki, cewar su na Asibiti an kwantar da Shukura. Hankalin Nana ya tashi sosai da sosai, tana son zuwa duba Baba da Jamila ma, ga kuma wannan maganar ta rashin lafiyar Shukura. Sai dai yadda ransa yake a ɓace ta san ba ta da damar yi masa magana.
Tun da abin nan ya faru, bai sake shigowa ɗakin ba, ta je ta same shi a kan ta gama girki ya yi mata shiru. 'yar walwalar da ya fara yi ta gushe baki ɗaya.
Gaba ɗaya abin ya dame ta sosai da sosai, ko abincin kirki ta kasa ci.
Sai bayan sallar isha'i ya shigo ɗakin ya nemi guri ya zauna, ba tare da ya furta komai ba.
"Sayyid ba ka ci abinci ba fa tun na safe ba ka kuma cin komai ba, dan Allah ka yi haƙuri ka ci abinci".
Bai ko kalle ta ba, balle ta saka ran zai ci, ƙarshe sai haƙura ta yi ta zura masa ido.
Ta gama shirinta, ta nemi guri ta kwanta, amma yana zaune. Nana ta jinjinawa girman zuciyar sa. Ya jima a zaune sannan ya tashi ya canza kayan jikinsa.
Bacci har ya fara ɗaukar Nana, ta ji yana shigowa cikin bargonta, gabanta ya faɗi tuna abin da ya faru jiya, sai dai ba ta motsa ba, sai addu'a da take yi a karkashin zuciyarta.
Ya matsa sosai ya rungume ta, yana yi mata numfashi a wuya.
"Idan ina fushi, ki daina kula ni" ya faɗa kamar mai raɗa.
Ba ta iya tanka masa ba, bai kuma sake ce mata komai ba, sai da ta ga babu alamar zai yi mata wani abu, sannan nannauyan bacci ya ɗauke ta.
Tamkar wani zai ƙwace ta, ya ƙara ƙanƙame ta a jikinsa. Sai ƙamshin turaren sa take yi.
A cikin baccin ta ji muryar Ƙaisar "Ba kin shige cikin bargo ba, idan ki ka kuma ɗaukar littafin nan ki ka karanta, sai na baki mamaki, sai na yi miki abin da ba ki taɓa tsammani ba"
"To ina ruwanka da bargon da na shiga, ya naga kamar ka na kishi da mijin nan nawa ne?"
Tsaki ya ja ya ce "Da me zan yi kishin? Haryanzu ba ki san a hatsarin da ki ke ba, wauta da shirme ne kawai yake ɗawainiya da ke. Kin ƙi ki buɗe ido ki kalli gaskiya. Gaba ɗaya kin ma manta da batun tantance waye shi, duk da irin abubuwan da ki ke gani da ya saɓa da ɗabi'ar bil adama"
"A'a ba kyau zurfafa bincike, tun da Allah ya sa ina samun shinkafar da zan ci, ba ya saka ni kuka, babu tashin hankali ai gara na haƙura na lallaɓa haka. Duk wani abu da yake yi da ya saɓawa ɗabi'ar Adam wannan kuma na san kai ne, kai ka ke ƙulla komai. Na san so ka ke ka kashe mini aure, saboda kai duk yadda za ka yi hana ni jin daɗin rayuwata, shi ka ke yi"
Galala yake bin Nana da kallo baki buɗe cikin mamaki. Ya ce "Gaskiya ne, idan ya gama baki jin daɗin za kuma ki ɗanɗana kuɗar ki, banda ina duba wani abu da da kaina zan bayar da jininki ga matsafan nan ki mutu uban kowa ma ya huta!"
Ayshercool
08081012143
37
Nana ta saci kallon ƙaisar, jikinsa har fitar da hayaƙi yake yi saboda fusata.
Ko a jikinta ta ce "Amm dan Allah ka gaya mini ya aka yi da Lanti a gurin yin girka?