Showing 183001 words to 186000 words out of 189977 words
wani abu da ta yi miki na laifi. Kuma ita kanta Hajiyar, tana da gaskiya mijina ba shi da lafiya ba ta yi ba dai-dai ba".
"Ai shikenan, yanzu haka za ki tafi na daina jin ƙamshin girkinki mai daɗi"
"Haula, dan Allah ko ke kin san waye Sayyid, daga ina kuma yake?"
Haula ta waro ido ta ce "Taɓ, so ki ke dattijo ya kashe ni? Ko kuma ya azabtar da rayuwata. Yo bai bar ɗansa ba balle ni. Babu ruwana"
Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah ki gaya mini, babu abin da zai yi miki "
"A'a ba ruwana. Ai Ƙaisar ya gaya miki, shigen Asirin da aka yi wa Alhaji Fatuhu, aka yi wa mijinki, amma ke ni babu ruwana a wannan lamarin naku"
Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Da gaske, abin da Ƙaisar ya nuna mini a mafarki ya faru? Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu Asiri da ɗan Shukura?"
"Sosai da gaske ne, ba ƙarya ya yi miki ba. Da zai ci gaba da buɗe miki ido, ki cigaba da ganin ɓarnar da bil'adama ku ke yi wa junanku, sai kin haukace.
Alhaji Zailani yana gadon Asibitin, da aka ɗauke wa kishiyar Yusra ɗa"
"Wace Yusran?"
"Ƙawar ki mana, ita ce matar Sagir ta farko. Kin ga tafiyata kar na yi laifi, garin ɓare-ɓare na faɗi abin da za a hukunta ni" Nana ta zabura ta damƙi hannun Yusra da sauri, domin sake tambayar ta. Amma ta ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, ta buɗe idonta, ta kalli Sayyid, da ta riƙe masa hannu gam.
Ta yinƙura ta tashi zaune, yanayin yadda ta ji jikinta, ta gane abin da ya faru.
Ummi ta ce "Nana kin tashi? Ki wanke fuskar ki, masu ƙurƙurar sun kusa ƙarasowa.Ta tashi ta wanko fuskarta.
Tana fitowa kuwa, masu motar suka ƙaraso.
Aka kwashe kayan su Nana tsaf, sosai Nana take jin kewar barin ɗakin nasu. Ummi ta raka ta, suka shiga gurin Hajiy Halima, suka yi mata sallama.
Tar Nana take jin hirar da suka yi da Haula a bacci, tana dawo mata kanta, ba tare da ta manta komai daga hirar ta su ba.
Sai dai ta ƙi yarda zuciyarta ta gazagata komai a cikin maganganun Haula, ta dage wa zuciyarta da cewa shirmen mafarki ne, saboda tana yawan tunanin Yusra da take yi.
Duk da tana jin kamar wani abu makamancin haka ya faru, wani abu mai kama da Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu asiri, da kuma maganar jariri, amma ta kasa tuna komai.
Ummi ta fita waje, domin tabattar da an shirya komai, a kan motar.
Nana ta tarar da Sayyid a cikin ɗakin, yana ƙare wa ɗakin kallo.
"Shugabana" ya waiwayo a hankali yana kallon ta.
"An tafi samo abin hawa, za mu tafi, na ga ka zo ka tsaya a nan"
"Nana"
"Na'am Sayyid"
"Ina kewar rayuwar da muka yi a ɗakin nan tare da ni da ke, ban san ya zan misalta miki ba. Ga ki dai a tare da ni, amma ina kewar ɗakin sosai. Sai na ji kamar ba zamu sake Rayuwa mai daɗin da muka yi a cikin sa ba"
Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah, sai mun yi wadda ta fita komai da komai, da yardar Ubangijin talikai. Taho mu tafi" Da ƙyar ta riƙo hannunsa, suka fito idanunsa jawur.
A adaidaita sahu suka tafi, da shi da ita da Ummi, sai dai ya ƙura wa gidan ido, tamkar ya ce a tsaya ya koma. Nana ta riƙo hannunsa cikin nata ta ce "Mu kyautatawa Allah zato, ina da yaƙinin rayuwar da zamu ci gaba, ta fi wadda ka ke kewa daɗi"
"Ina fatan haka Rayuwata"
Ummi ji ta yi tamkar ta yi tsuntsuwa, ta fita, ba ta san lokacin da Nana ta fitsare haka ba. Ta yi ta biye masa su na abu a gaban mutane, idan shi ba bahaushe ba ne, ai ita bahaushiya ce.
Sun ɗan yi doguwar tafiya, daga Tudun yola, zuwa Kurna.
Babban abin da ya soki zuciyar Sayyid, bai wuce ganin gidan akwai maza ba, duk da masu aure ne, amma har cikin zuciyarsa hakan bai yi masa tsari ba. Amma babu yadda ya iya, tun da ba shi da wata mafitar. Ɗakin nasu bai kai wanda suka baro girma ba. Cif ya ɗauke kayan su, sai dai babu sauran space ɗin kirki a ɗakin. Ga zafi saboda wata 'yar ƙaramar taga ce a ɗakin, kamar ɗakin tattabara.
Abin takaicin bai wuce yadda yaran layin suka cika gidan ba, saboda ganin ana sauke kaya ana shiga da su cikin gidan.
Sai da Ummi ta din ga korar yara, suka saka Sayyid a gaba da kallo, saboda ya yi shigar buzaye da rawani. Abin takaici har matan layin, wasu suka din ga leƙowa, masu son ganin ƙwal uwar daka kuwa, gidan suka din ga shigowa, da sunan sun zo gurin sauran matan da suke gidan, amma a zahiri, zuwa suka yi su ga suwaye kuma suka tare a gidan.
Ummi tana tare da su Nana, har aka gama shirya ɗakin tsaf, duk da Nana su na da sauran kayan Abinci, amma ta yi waya aka kawo mata kayan abinci daga gidanta, ta girka wa Nana. Kasancewar Nana ba ita ta dafa ba, sai ta samu ta ci sosai.
Sai da Ummi ta aiko musu da maganin sauro, saboda akwai sauro sosai da sosai a gidan, ga zafi, shi kuma ga yanayin ciwonsa ba ya son zafi yana buƙatar wadatacciyar iska. Haka Nana ta yi ta aikin fifita.
Da safe Ummi ta sake aiko musu da Abin karyawa. Sai dai daga shi har ita, ba wani ci suka yi ba. Nana ta shirya ta ce "Sayyid, bari na je na yi musu sallama, mu gaisa da mutanen gidan"
"To"
"Yauwwa, kai ma zaka gaisa da mazajen su dan Allah, haka ake yi idan an je gurin, da ba a san mutum ba" kallon ta ya yi, ya maze kamar bai ji me ta ce ba, amma ta san ya ji ta sarai.
Ta fita tsakar gidan, ta yi sa'a matan na tsagar gida, su na aikace-aikace. Nana ta ce "Sannu ina kwanan ku"
Suka amsa mata cikin sakin fuska.
Nana ta ce "Sunana Nana, ni ce muka tare a wannan ɗakin"
"Allah sarki, sannu, ni sunana Barira, ga kuma Sajida, mai wancan ɗakin"
Nana ta ce "Allah sarki, to ma sha Allah, Allah ya iya mana" sun so jan Nana da hira, amma ta tashi tsam ta koma ɗaki, gurin mijinta.
****
"Alhajin Allah, aka ce ka tafi umara?"
Alhaji Zailani ya ce "Ɗagawa na yi Alhaji Magaji, Madam ta tafi, saboda tafiyar ta yi karo da wani taro da za mu yi na shekara, shi yasa na ɗaga. Ashe kai ma na garin Abujan?"
"Wallahi kuwa, na ma kwana biyu, ina neman wata kwangila ne. Ya jikin amininka kuwa, Fatuhu?"
Alhaji Zailani ya yi wani irin makirin murmushi ya ce "Yana can ya kwanta dama"
"Subhanallah, rasuwa ya yi?"
"A'a na fa, yana nan a raye, amma rai ne kawai a jikinsa"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wallahi na yi mamakin yadda rayuwa ta yi wa mutumin nan tsutsun jaki lokaci guda, ga asarar dukiya, komai nasa an ƙwace an biya masa bashi. Kai Allah dai ya kyauta. Da tuni yanzu ya ja tawagar tafiyar umarar maulidin nan, da shi da 'yan uwa da abokan arziki"
Alhaji Zailani ya ce "Sosai kam, faɗuwar wani ai tashin wani, yanzu waɗanda ya tare wa ƙofar arziki tun da ya gusa su ma za su ɗago" suka tafa su na wata irin ƙyaƙyacewa da dariya.
*****
Jamila bakinta ya ƙi rufuwa, kasancewar a wannan karon a jirgi za su tafi babban birnin tarayya tare da Hajiya Sa'a.
Hajiya Sa'a ta ce "Ai sai ranar da za mu je Dubai, ko Qatar ma, wannan ai ba wani abu bane ba sam. Sai kin gaji da hawa jirgi, muddin za ki ci gaba da bayar da haɗin kai"
Jamila ta ce "Kai, wa ya ganni a Qatar"
"Amm Jamila ina Nana kuwa?"
"Tana gidanta, kwanaki ma na ji an ce ta yi ɓari"
Hajiya Sa'a ta jinjina kai kawai. Daga airport aka zo da mota, aka ɗauke su aka tafi da su. Wani irin katafaren gida ne, da ko a irin finafinan Hausa da Jamila take gani, ba a taɓa hasko mai girma da kyansa ba.
"Hajiya amma nan Hotel ne ko?"
"A'a gida ne, a nan za mu yi taron shekara"
"Ikon Allah, ai ganin gidan na yi ƙato guri-guri. To gidan waye?"
"Gidan wani ne" Hajiya Sa'a ta bata amsa tana dariyar, ganin yadda gidan ya ƙayatar da Jamila.
****
Kwanakin su Nana uku a gidan da suka koma, amma ita kanta, ba ta jin daɗin zaman gidan, duk da a gehtto area ta tashi ita ma, amma zaman gidan nan sam babu daɗi. Inda suka baro, sai ka wuni ba ka ji ƙwaƙwƙwaran sauti ba, sai na giftawar motoci. Amma gidan nan, musamman idan yamma ta yi, mata ne suke cika shi dam. A yi ta hayaniya, ana gulmace-gulmace, ga zantuttukan batsa da suke bajekolinsu a cikin gidan. A kafa dashi, a ci bashi, a yi gulmar wannan a yi ta mijin waccan. Hatta shimfiɗar aurensu ba su bar ta ba, bajekolin ta suke yi a wannan gidan.
Yanzu ma yana kwance ya lumshe idanunsa, su na ta hayaniya su na musu, a kan kuɗin cefane.
"Shugaba" ya ɗago idonsa ya kalle ta.
"Sannu ya jikin?" Ya sake lumshe idanunsa ya ce "Na warke"
Ta yi murmushi ta ce "Sayyid, na san ba ka jin daɗin zaman gidan nan, amma ka yi haƙuri in sha Allah, idan muka samu hali sai mu bar gidan nan"
Ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar sauran jin daɗi, in dai ki na kusa da ni" ya yi maganar yana shafa fuskarta.
"Sayyid"
"Husnah" sai kuma ta yi shiru. "Faɗi mana"
"Ba komai fa"
"Shikenan zan shigo mafarkin ki, na ji"
Ta ɗan yi dariya ta ce "Allah ne ya san dalilin da ya sanya ya haɗa mu, gaba ɗaya rayuwarmu wata iri, daban da ta sauran mutane, mu dai gamu nan"
Ya yi murmushi ya ce "Shi yasa ba zan daina yi wa Allah godiya ba, da ya haɗa ni da ke. Rayuwa da ke wata afuwa ce a gare ni Rayuwata" ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi. A hankali murmushin fuskarsa ya gushe, ya ce "Ba ni wayar nan, mu sake dubawa, ko wayar Habu za ta shiga"
Nana ta ɗaukko wayar daga gefen ta, ta miƙa masa, ya karɓa ya danna lambar Habu, amma ta ƙara maimaita masa, wayar a kashe take. Ya sauke hannunsa cike da damuwa da fargaba.
"Sayyid ka daina damuwa, in sha Allah su na cikin ƙoshin lafiya"
"Asmy, rayuwa ba za ta tafi a haka ba. Akwai ɗawainiya da yawa. Ki yi haƙuri na san juriya da rashin son damuwata ya sanya, ki ke danne wa. Da nuna mini ba komai, amma na san ɗawainiyar nan ta yi miki yawa. Wallahi zuciyata na yi mini zafi, idan na ga ki na wahala"
"Ni ba wahala nake yi ba" ta yi maganar tana tsuke baki.
"Shikenan, na daina maganar"
Jin wayar na vibrating, ya sanya suka kai hankalinsu kan wayar a tare. Amma sunan Adda Saude ne yake yawo, a kan screen ɗin wayar.
Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Adda Saude ta amsa Nana ta ce "Adda ina wuni?"
"Lafiya ƙalau Nana, ya ki ke ya mijin naki?"
"Lafiya ƙalau, ina Adda Fati?"
"Tana gidanta, ga Maijidda take son yin magana da ke" wata irin zabura Nana ta yi cikin murna ta ƙara nutsuwa.
"Assalamu alaikum"
"Mama"
"Na'am Nana ya ki ke?"
"Lafiya ƙalau, ya gida ya su Walida?"
"Su na nan lafiya ƙalau Alhamdillah, ya mai gidan na ki?"
"Lafiya kalau Mama"
Sayyid ya ƙura wa Nana ido, yana ayyana abin da take ji a zuciyarta. Saboda fara'ar da ta mamaye fuskarta.
"Ki na ji Nana, ina nan ina ƙoƙari, duk yadda zan yi zan zo Kano, na ganku in sha Allah, ki ƙara haƙuri, na san kin yi ki ƙara, ina nan tafe in sha Allah"
"Kar ki damu Mama, ni jin muryar nan ta ki ma da na yi, na ji daɗi sosai. Kuma in sha Allah kafin ki zo, za mu riga ki zuwa da yardar Allah"
"A'a ni ɗin dai zan zo na gan ku in sha Allah, ina fatan dai babu wata matsala?"
"Babu matsalar komai Mama"
"Yauwwa Nana, zan ci gaba da jaddada miki, ki riƙe Allah ki riƙe addu'a. Ki bi mijinki ku zauna lafiya. Ina fatan kin fafa sana'a Nana?"
"A'a Mama, amma zan fara in sha Allah"
"A'a Nana, kullum ki ce mini za ki fara, amma ba ki fara ba. Ina da buhun barkono, zan sayar na turo miki kuɗin, ki fara sayar da wani abin. Idan kuma barkonon ki ke so, na aiko miki Nana. Ni dai ban taɓa ganin mijin nan naki ba, amma yadda su Fati suka bani labari, da yadda nake jin muryarki, a duk lokacin da na kira waya, ina samun nutsuwa. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Amma ki yi sana'a, tun da mai ƙaramin ƙarfi ne, ki taimaka masa, kar ki sakar masa nauyi gaba ɗaya"
"To in sha Allah Mama, amma dan Allah ki bar barkonon ki, zan yi sana'ar nan da yardar Allah, na rasa abin da zan fara sayarwa ne. Amma zan fara"
"A'a zan sako miki buhu ɗaya a mota, ki gwada, kar ki zauna haka ba kya juya taro da sisi"
"To Mama in sha Allah, na gode sosai da sosai "
"Yauwwa, haryanzu ba ki da lambar Imrana ki turo mini"
Nana ta ce "Ba ni da ita Mama"
"To shikenan, ki gaida mijin naki" suka yi sallama, ta sauke wayar a hankali, ta yi shiru tana zancen zuci. Ta san da Mamanta su na tare da Baba, da ko ba za ta ɗauke mata ɗawainiyar da take ciki ba, za ta tausaya mata ta taya ta jajanta lamarin. Amma tun da ta je gida ta sanar da Baba halin da take ciki, ko ta waya bai kira ya tambayi ya suka ƙare ba, ya kuma mai jikin ba. Dama Mama ba a magana, mutanen da tun da ta yi aure, ba su taɓa taka gidan da take ba, yaushe za ta sanya ran su damu da halin da take ciki.
Tana iya ƙoƙarinta, gurin rintse idanunta, daga aibun iyayenta, saboda kar zuciya ta ɗebe ta, ta afka cikin fushin Ubangiji, amma daga yadda Baba ya yi mata gurin aurenta, zuwa yanzu zuciyarta na ƙoƙarin bijirewa.
"Ya ne?" Ta ji muryarsa. Firgigit, ta kalle shi ta ce "Babu komai. Mama na gaishe ka"
"Ina amsawa, ina son na yi magan da ita, amma ina tsoron na karɓi wayar, maganar ta ɗauke"
Nana ta ce "Haka ne, bari na fita da gas ɗina waje, na dafa mana taliya, ga kayan miya na aika yaran Ummi, sun sayo mini, ai za ka ci ko?"
"Ke ma za ki ci ko?"
Ta yi dariya ta ce "In sha Allah" Ta ɗauki kayan girkinta, ta fita kusa da ɗakinta, ta ɗora.
Gaisawa kawai suka yi da matan gidan, ta nutsu a kan aikinta. Tana zaune mata na ta shiga suna fita, kowacce da abun da yake kawo ta. Da tana da isasshen guri, a ɗakinta, da babu abin da zai fito da ita waje yin girki, balle ta din ga kallon tumasancin da matan suke yi. Har da wadda daga ita sai hijjabi, da zani, babu riga babu brezia. Idan masu gidan suka dawo, haka suke tsallake mata su shiga ɗakunan su. Tun da Nana ta kammala girki, ta tattara komai nata ta shige ɗaki.
Ta ji daɗin ganin yadda yau yake iya cin abinci, dan haka ita ma ta zage, duk da ba wani daɗi yake yi mata ba.
Saboda rashin kamun kai na matan layin nan, sukan kai har goma da rabi, su na shiga su na fita a gidan tamkar bariki.
Nana har ta fara murnar abincin da ta ci ya zauna, lokaci ɗaya ya taso sai da ta amayar da shi baki ɗaya.
Tana fitowa daga banɗakin, ya ƙura mata ido, har ta ƙaraso ta kwanta a jikinsa, tana ɓata fuska.
Ya ƙanƙame ta yana faɗin sannu.
"Ɗan ka ya hana ni cin abinci, kuma yunwa nake ji" ta yi maganar hawaye na cika mata ido.
"Yi haƙuri, sannu, to mu je Asibiti"ya yi maganar a jere.
"A'a Sayyid, dole mu din ga tattala kuɗi yanzu. Yunwa nake ji sosai" ta yi maganar cikin shagwaɓa.
"Me zan sayo miki?"
"Ba komai" ji ta yi numfashinsa yana fita da sauri da sauri, a tsorace ta kalle shi ta ce "Sayyid jikin ne?"
"A'a" ya furta a hankali.
"Dan Allah ka yi haƙuri, da wasa nake yi maka, ai na san mata masu ciki, su na fuskantar irin haka, dan Allah ka kwantar da hankalinka. Ba na so mu zauna shiru, shi yasa na tsokane ka"
"Tom" ya amsa a hankali.
Kasancewar jikinta babu ƙwari, ya sanya ta kwanta da wuri, ganin shi ma ya samu bacci.
A cikin bacci ta din ga jin wani irin rugugi, tamkar na hadari, ga shi ba lokacin damina ba ne. Ta buɗe idonta, ta ji wani irin huci, na fitowa daga gurin da yake kwance, ga wani irin nishi da kakari da yake yi, tamkar an yanka rago.
Ayshercool
08081012143
51
Fitila ta laluba, ta ɗaukko ta haska shi, wata irin jijjiga yake yi, tamkar zai zauce, yana wata irin miƙa, yana nishi.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya faru? Me ya same ka?" Ta kai hannunta jikinsa, wani irin zafi ta ji yana fitowa daga jikinsa.
Cikin zafin nama, ta cire rigar jikinta ta fara ƙoƙarin rungume shi. Amma ya hankaɗe ta, yana ci gaba da kakari.
Ta sanya ƙarfi, da ƙyar ta shiga jikinsa ta ƙanƙame shi .
"Zafi, ƙonewa nake yi, wuta Nana jikina ana ƙona ni" ya yi maganar haƙoransa na karo da juna, muryarsa na sarƙewa.
"Sannu Sayyid, ka yi haƙuri ka daure, na san ka na shan wahala, kar mutanen gidan nan, su fuskanci halin da muke ciki ka yi haƙuri" Ta yi maganar cikin dauriya da dakiya, saboda yadda ita kanta zafin jikin nasa, ya sanya take jin, tamkar ta yi ihun, saboda tamkar ta rungume ƙarfen da aka ciro daga cikin wuta haka take ji.
"Ahhh zafi!" Ya sake furtawa cikin mawuyacin hali.
Ta kwantar da kansa a kafaɗarta, tana karanta masa abin da ya sauwwaƙa a kunnensa.
"Ki cika ni, kar cikin nan ya kuma zubewa"
"Babu abin da zai same shi"
Ta saka bakin ta a kunnensa na dama, ta fara kiran salla. Ya yi wata irin miƙa, jikinsa ya sandare a haka.
Ta koma kunnensa