Showing 42001 words to 45000 words out of 189977 words
wannan account ɗin
0069685771
Aisha Adam
Stanbic ibtc
Sai shaidar biya ta
Ayshercool
08081012143
BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA/002
P14
Cikin hanzari Nana ta ce "Na yarda na amince, na bar maka shi"
"Ai ba da baki kawai za ki faɗa ba, akwai buƙatar yin wani aiki, idan kin amince za ki sadaukar mini da shi, za ku rabu har abada"
"Eh na amince"
Sarkin baka ya ce "Za mu ƙarasa maganar da safe"
Kawai ta gansu a ƙofar ɗakinta, suka yi sallama ta shiga ta kwanta. Sai dai jikinta na ta tsuma da tunanin wace matar aka kashe, kuma ake ƙoƙarin cin zarafin gawarta haka.
"Hmmm za ki sadaukar wa wani ni ko? Har kin yi sabo da shi haka kin yarda shi?" Ta ji maganar ƙaisar a tsakanin zuciyarta da ƙwaƙwalwarta.
"Eh zan sadaukar da kai, muddin hakan zai sama mini lafiya da nutsuwa" ta yi maganar a fili. Dariyarsa kawai ta din ga ji, gidan baki ɗaya yana amsa kuwwa.
Bayan ta yi sallar asuba, ta zauna tana azkar bayan ta idar, ta yi shiru tana tunani, addu'a ta din ga yi Allah ya rabata da ƙaisar, muddin abin da sarkin baka zai sakata bai saɓa wa Allah ba, za ta yi domin ta rabu da ƙaisar.
Da kanta take zuwa gurin Sarkin baka yanzu, duk ta san hanyoyi a gidan.
Kuma ganin ta samu sassauci daga takurar ƙaisar, da sanya mata cututtuka da sauran damuwowi ga abinci tana samu babu mai takura mata da damuwa, ga kuma sukulle da kyautatawar da sarkin baka yake yi mata, sai ta fara sakin jiki da mantawa da damuwar da take ciki.
Abin mamaki, yau da Alqur'ani ta tarar da sarkin baka, bugun warshi yana karantawa, sai da ya idar sannan suka gaisa suka fita.
Sai da suka fara zuwa gurin da ake harhaɗa masa magunguna, har da injin niƙa a gurin, shi ma ma'aikatan gurin daban, ga tarin saiwoyi da tsirrai.
Gaggaisawa ya yi da masu aikin gurin, ya ce "An kawo saiwoyin nan kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Salamatu.
Salamatu ta ce "A'a sarki, ta rafi ake jira, ba ta kawo ba"
"Aljanar nan akwai sheɗainiya, idan ta bari na nemo wani ya ɗebo mini, wallahi sai ta ɗanɗan kuɗarta" Nana ta kalle shi ta ce "Aljana kuma?"
"Eh, wasu saiwoyin ai sai dai aljani ya ɗebo, ba dai mutum ba. Akwai abubuwan da a cikin ruwa muke ɗebo su, kuma akwai dai-dai lokacin da muke ɗibar su, idan ba aljani ba sai dai ka nemi masunta, su kuma idan ba su ga dama ba, ba za su baka ainihin abin mai kyau ba" Yana gama yi wa Nana bayani, ya ci gaba da maganar sa.
"Akwai masu shanyewar ɓarin jiki, mutum biyu Salamatu a je a duba, idan na aljanu ne, a jira ni ki ba su taimakon gaggawa. Idan kuma na larura ne maza a haɗa musu magani, a ɗauki ɓawon kwakwa, da sassaƙen zogale, da zoɓo da ɓawon abarba, a dafa su sosai, a ƙara ruwa, a din ga basu kofi ɗaya sau uku rana. Ba cin man gyaɗa, ba cin gishiri ba cin kanwa, uzairu ya yi musu ƙaho zan zo na ga jikin nasu" cikin girmamawa ta ce "To sarki"
Tun Nana tana mamakin al'amuran sarkin baka, har ta zuba wa sarautar Allah ido kawai
Amma duk da haka, Nana ta kan kasa jurewa sai ta tambayi wasu abubuwan, yanzun ma ɗan gyaran murya ta yi ta ce "Sarki, su wannan magungunan da ka ke bayarwa haka da ka, ba ka tunanin ya yi wa mara lafiya illa, a asibiti akwai maganin da idan mutum yana da wani ciwon fa ba a ba shi, ku kuma nan ba tantancewa ku ke yi ba, kuma ba auna maganin ku ke yi ba"
Ya gyara zaman sanhonsa ya ce "Ban da sharri irin naki, da kuma abu irin naku na 'yan boko aƙida, da ku ke cewa maganin hausa ba shi da awo, ba yanzu a kunnen ki na faɗi gwargwadon abin da za a ba su ba? Wanda ya sani fa ya sani Asma'u, wanda bai sani ba bai sani ba, galibi gurin masu neman na Abinci kawai ake zuwa, wani koya ya yi amma ba a koya masa maganin yadda yake ba, dan ba kowa ne yake yarda ya bayar da sirrin sa ba. Ni na gada kuma na koya. Bature ya yi nasa ban raina masa ba, kuma nima na yi nawa ba wanda ya isa ya raina mini. Ke shaida ce duk abin da ba ni da maganinsa ina gaya wa mutane. Kuma ni ba dan neman kuɗi nake bayar da magani ba. Ki din ga tambayata abin da ba ki gane ba zan yi miki bayani, amma muddin na ji kushen abin da nake yi, ba zan ba ki amsa ba, kuma kin yi wa kanki, dan ba ki san a ina abubuwan da ki ka koya a gurina, za su iya amfanar ki ba, ko su amfani wani ba" jin sa kawai Nana take yi, tana ganin me za ta amfani wani da wannan abubuwan da babu scientific proof ko research a kan su.
Bayan sun gama da nan suka tafi ɓangaren da ba ta taɓa zuwa ba a gidan.
Shi kuma garke garke ne na dabbobin dawa da na gida, wani abin ma ba ta taɓa ganinsa ba.
Ya din ga nuna mata dabbobin, da magungunan da ake yi da wasu sassa na jikinsu.
Yana cikin yi mata bayani, ta ga ya yi shiru ya daina magana, ta leƙa fuskarsa za ta yi magana kawai ta ga ƙwayar idonsa ta koma baƙa gaba ɗaya, jikinsa ya hau tsuma.
Cikin sanhonsa ya zira hannu, sai ga shi ya fito da wani shirgegen zaka, ya gaji da riƙa cerarsa jawur da ita.
Jiki na tsuma Sarkin baka ya saka hannu ya raba kan zakaran da gangar jikinsa.
Ya ɗaga gangar jikin, ya tsiyaye jinin a bakinsa, ya gama ya hau cin gangar jikin zakaran a ɗanyensa da gashinsa da komai yana zazzaro ido.
Ihu Nana ta saka tana karkarwa, ta juya za ta kasa da gudu, kawai ta ganta a jikin Salamatu tana shafa mata wani abu.
Nana ta juya ta ga ba ta ga Sarkin baka ba, sai ita da Salamatu a ɗakin.
Salamatu ta ce "Nana zamanki a gidan nan, ya ci ace kin daina tsorata a mafarki, ki koyi dakiya garin tsoron nan wataran za ki iya zaucewa fa. Shi ya sa Sarki yake nuna miki wasu abubuwan domin ki saba ki rage tsoro"
Ajiyar zuciya kawai Nana take yi, cike da tsoron abin da ta gani da ta kasa tuna mafarki ne ko kuma gaske.
***
Gaddafi na zaune a rumfar mai shayi, yana jiran a dafa masa noodles da ƙwai ya ci.
Babu tsammani sai ga jami'an tsaro sun dira a gurin, tare da Imran.
Imran ya nuna Gaddafi aka kama shi, cikin mamaki Gaddafi yake tambayar ba'asin abin da ya faru, amma ba su gaya masa ba suka tafi da shi.
Sai da su ka je charge office, sannan aka ce Imran ya faɗi abin da ya kawo ƙarar Gaddafi a kai.
Imran ya ce "Yallaɓai, ƙanwata ya ɗauka suka haɗa kai da yayar babanmu, aka kai ta wani guri wai neman magani. Kusan sati guda kenan na yi na yi, su gaya mini ina suka kai ta sun ƙi, kuma ita kaɗai aka baro a gurin babu ɗan jinya".
Cikin mamaki da takaici Gaddafi ya ce "Amma ka cika mara mutunci, me ya hana ka saka a kama da Baban, sai ni zaka saka a kama, bayan tare muka kai ta".
Imran ya ce "Eh wannan ai ubana ne, kuma Kai ka kawo shawarar a kai ta can ɗin. Ga Suwaiba nan a gidan tana aljanun ita ma, ita baku kaita ba, saboda ita ana son ta ƙanwata ce ba a so, kawai ka gaya mini ina aka kai mini ƙanwa"
D.P.O ya ce "Ya isa haka, wannan maganar ta cikin gida ce, kuma shi ma yana da gaskiya, babu yadda za ayi ace an kai mutum gurin mai magani, babu wani nasa a gurin, kuma ba asibiti ba. Ko Asibiti ne?" Ya yi maganar yana kallon Gaddafi.
Gaddafi ya girgiza kai.
"To ka gani, shi ba ubanta ba ba ɗan uwanta na jini ba, ba ma kwa tsoron ya lalata rayuwar yarinyar. Ga ku a cikin ƙwaryar birni kamar masu hankali, amma kun yi abu kamar mutanen farko. Duk yadda ake ciki wajibi ne gobe ka wuce gaba, zan bayar da mutum biyu a nan, aje a dawo da yarinyar nan, muddin ba ku dawo da ita ba, to wani abun ku ka aikata kuma sai na rufe ku daga kai har wanda ku ka kai ta" Gaddafi ya jinjina kai tare da yi wa Imran wani mugun kallo.
*****
Nana a ɗakin da sarkin baka yake bayar da magani ta tarar da shi, yana ganin wata mata da yaronta.
Ƙafafuwan yaron tamkar lagwani 'yan sirara marasa ƙwari, da hannayensa. Haka kansa ma ɗan mitsitsi da kaɗan ya fi lemon zaƙi fuskarsa tamkar tsoho abin tsoro yaron.
Uwar kuma sai rungume shi take yi cike da so da ƙauna.
Sarkin baka ya ce "Wata rana kin kashe gizo gizo cikin dare, a banɗakin ki, lokacin ki na da ƙaramin cikin yaron nan, ba tare da kin yi bismillah ko addu'a shiga banɗaki ba, an yi haka?"
Ta girgiza kai ta ce "Sarki ba zan iya tunawa ba"
"To an yi, shi ya faɗi abin da ki ka yi masa, kin bugawa jaririnsu takalmi, kin nakasa shi, shi suka ajiye a jikin gizo-gizo yana wasa, ki ka dake shi da takalmi, da kin yi addu'a da ya bar jikin gizo-gizon. Dan haka yanzu ɗan su suka ajiye a jikin yaron naki, jininsa da sauran sinadaran jikin yaron ki, da za su saka ya girma, su yake sha yana girma, dan haka ko an cire aljanin mutuwa zai yi ba shi da sauran mamora sun gama lalata jikin yaron da garkuwar jikinsa" matar ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah sarki ka taimake ni"
Ya girgiza kai ya ce "Magani kawai nake bayarwa, ba ni da ikon kashewa ko rayawa, zan baki magani ki koma gida, Allah ya baki wani"
Nana ta ce "Ya a ka yi ka san aljanin ne a jikinsa, kuma idan ya fita ba zai rayu ba?"
Buɗe ƙwaryar can, ki ɗaukko mini habbatussauda, akwai tazargade a ciki da tsakin kuka, da garin farin muski, duk ɗebo su da kan ki ki zo" babu musu Nana ta harhaɗo kayan da ya ce ta kawo masa.
Ya zira hannu a jakarsa ya ɗaukko garwashi, ya ɗora a kan wata tasa, ya ɗebi haɗin nan ya zuba a kai. Ko sakan goma ba a yi ba, yaron ya mimmiƙe ya din ga tsala uban ihu.
Sarkin baka ya cewa matar "Yaushe rabonsa da kuka, ko ya motsa wata gaɓa ta jikin sa?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya tunawa ba, kullum a kwance kawai yake"
"To tun da ya yi kuka yanzu har da mimmiƙe wa, kin san ba ƙalau ba, baiwar Allah ki je gida, Allah ya baki wani"
Nana a ranta ta ce "Yaro ya ji wannan uban hayaƙin ba dole ya tsala ihun azaba ba".
Ya ce "Kamar har yanzu ba ki yarda da abin da ki ka gani ba ko?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a na yarda"
" 'yar wace ɗariƙa ce ke ne?"
Ta girgiza kai ta ce "Ɗariƙa ba ta cikin sharaɗin addini, dan haka ni ba ni da wata ɗariƙa"
Ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne, kin san kowace ɗariƙa akwai malamin da ta ke yarda da shi, da ki na da ɗariƙa da na ce ki saurari bayanin da wani babban malami ya yi a kan aljanu, amma manta kawai kin tashi lafiya?"
"Lafiya kalau Alhamdilillah" ta buɗe baki za ta sake magana ta ga bakin sarkin baka duk jini da sauran gashin zakaran da ya cinye jiya, wanda lokacin da ta shigo ba bu shi a bakinsa.
Zabura ta yi ta ja da ba, dan a zaton ta a mafarki ta ga ya ci zakaran ba a gaske ba, kuma da har ma ta manta ma.
Sarkin baka ya sanya hannu, ya zaro sauran gashin daga bakinsa, ya kalla ya yi murmushi ya ce "Kar ki tsorata Nana, tun a zuwan ki gidan nan da na so cutar da ke, sai na cutar da ke ta in da uban duƙusa ba zai iya ba ki kariya ba.
Har ga Allah bani da niyyar cutar da ke, kuma da gaske na san ba zan iya raba ki da shi ba, amma na rage masa tasiri ta wasu fuskokin daban-daban a tattare da ke.
Tabbas na cinye zakara da ransa, kuma uban duƙusa ne ya zungure ni, sai da na yi a gaban ki, dan ki cire yarda da ni kar ki yarda ki sadaukar mini da shi. Da na mallake shi zan ƙara ƙarfi da ƙarin tasirantuwar magunguna na, kuma zan kerewa sa'a tsakanin mutanenmu.
Ainihina ɗan wanzamai ne, na gaji wanzanci daga nan aka kai ni bara, na samu karatun Alqur'ani daidai gwargwado sai dai babu sauran litattafai na addini. Azabar yunwa ce ta sanya na fara bin matasa daji farauta, daga baya na watsar da allo na bar gurin malamin da aka kai ni gaba ɗaya, duk mahaifiyata 'yar maharba ce, amma na fi ƙarfi ga ɓangaren wanzanci.
Na yi rashin ji, na yi faɗi tashi, na yi wa harkar baka haye, har na so na fi 'yan gado ƙwarewa, hakan ya saka sauran maharba sako ni a gaba, da tsaface-tsaface da ƙoƙarin son kawar da ni. Sun sha haɗa kai domin su kashe ni.
Suka yi mini shiri, na zo ba na iya kama komai idan na fita harbi, ga rashin lafiya, dole na bazama neman magani a nan na haɗu da uban gidana, a masu magani ya bani maita, wadda ita ma wasu baƙaƙen aljanu ne suke tasrifinta, ya ƙara koya mini harkar magani, ga wanda na gada na wanzanci a gida. Ya yi mini girkar aljanu na zo na gawurta, na nemi na fi shi ma ko ma na ce miki na fishi ta kaowace fuska, kawai sai ya fara neman ya kashe ni, saboda hassada. Wataran mun fita farauta tare ya rikiɗe ya koma ƙaton maciji ya yi ƙoƙarin haɗiye ni, ni kuma garin ƙwatar kaina na kashe shi har lahira.
A haƙiƙanin gaskiya, ba na yadda na bawa mutum duk wani abu da zai cuci mutane a kan zalunci. Ina da tarin aljanu kala-kala da nake aiki da su. Na nemi ki sadaukar mini da uban duƙusa ne domin na ƙara ƙarfin tasirina. Rabona da maita har na manta, tana nan a jikina amma bana amfani da ita, na daina ta'amalli da aljanun maita, shi ne jiya ya zunguri maitar ta motsa mini. Yanzu haka sai na je na yi jinya, kuma zan ja dogon lokaci ban yi aiki ba, sai dai yarana su yi. Hatta Salamatu da ki ke gani ba mutum ba ce ba. Ainihin matar ba ta da lafiya sihiri aka yi mata, ba ta iya komai aka kawota nan. Na saka Salamatu a jikinta take yi mini aiki, Salamatu na fita gangar jikin za ta faɗi ta ci gaba da jinya. Shirin a jikin gawa aka yi mata, aka binne gawar ni kuma ba zan iya sakawa a ciro gawa daga makwanci domin karya sihirin ba, hakan tamkar tozarta gawar ne."
Jikin Nana duk ya yi sanyi da jin labarin da sarkin baka ya bata.
"Yarinyata da tana raye da ta kai kamar ke, na tafi farauta abokan adawa ta, su ka kasheta da babarta, tun daga nan ban kuma aure ba,, shiyasa na yi iya ƙoƙarin da zan yi na gagare su. Zan saka a mayar da ke gida, ba sai kin yi makonni biyun ba, domin kuwa jiya an turo mini 'yan aike, ana so a haɗa kai da ni, in bayar da jininki, kuma ina da yadda zan yi na bayar, za ayi mini musaya da wani abu mai tsoka, wanda da na so, zan karɓa na bayar da jinin naki na yi maganin uban duƙusa, amma ina jin tausayin ki, ban san gaibu ba, amma akwai yiwuwar kina daf da buɗe sabon babi na ƙaddara, dan zuwanki gidan nan tuni kin yi wa ƙaddarar mukulli"
Cikin mamaki Nana ta ce "wace irin ƙaddara ce kuma haka?"
"A'a ba ni da damar cewa komai, amma ki tambayi ƙaisar mene ne tarihin kakaninki, za ki ga ta in da zuwanki gidan nan ya buɗe sabon babin ƙaddararki. Babu lallai ki fahimci labarin a take sai a gaba kaɗan za ki fahimta sosai da sosai. Abu ɗaya zan iya gaya miki, nima ina da alaƙa da labarin kakaninki ta wata fuskar"
"To kai ka gaya mini labarin mana"
Ya sauke numfashi ya ce "Ƙarfin hali kawai nake yi, maitar da take cikina ce take ta wahalar da ni, rabona da cin wani abu da sunan maita na fi shekara goma sha, saboda na sha maganin danne ta, kwatsam jiya na ci na san sai na yi jinya"
Nana har da gyara zama ta ce "To ita maitar mece ce? A addini babu maita sai dai kambun baka, to ita a ina ake samun maitar kuma ya ake yin ta"
Sai da ya yi dariya, Nana akwai tambaya ba kasafai take barin kanta ya kulle ba.
"Tabbas babu maita a addini, sai kambun baka. Maita tsafi ce sihiri ce, wani siddabaru ne da aljanu, da yake ƙara tasirin kambun baka. Ya danganta da wadda ka ke da ita. Akwai wadda ka ke iya ganin kurwoyin mutane, a siffofi na dabbobi, akwai wadda muke amfani da ita mu lalata abu. Idan muka kalli abu, ko ba mu tanka ba zai lalace. Mu kan zuba yawunmu idan ta taso mana a cikin abinci mu bawa mutum, sai ya yi ta rashin lafiya. Ina da jar maita ne, mai bala'in fiye da kowacce tare da wani aljani nake sarrafata, shi ne idan ya buƙaci jini yake zuwa kaina, sai na sha sai ya samu nutsuwa ya sake ni. Ina iya sarrafa maitar yadda nake so, ko shi ne Uban duƙusa ya zunguri maitar a cikina"
Nana ta jinjina kai ta ce "To amma ya aka yi ya iya zuwa gurin da ka ke, bayan ka na da magungunan su?"
"Ban gaya miki a cikin aljanu irin ƙaisar ba su da yawa ba? Yanzu ki je zan kwanta in