Showing 60001 words to 63000 words out of 189977 words

Chapter 21 - BUZU BOOK1 COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Jan 2026

954

ya farfaɗo cikin ikon Allah. Cikin harshen faransanci, Habu yake tambayarsa me ya same shi. Amma ya girgiza masa kai, ya sake tambayar sa ko akwai gurin da yake yi masa ciwo nan ma ya sake girgiza kansa. Ya tashi zaune ya jingina da jikin bango ya lumshe idanunsa.
Tunani yake yi wace ce wannan yarinyar a ina take? Ba damuwarsa yarinyar ba, mutumin da suke tare, yana da yaƙinin mutumin ya san ko waye shi.

*****
Wayewar garin Allah, tun bayan sallar asuba, Mama take bala'i wai a gaban Baba, Nana ta shaƙe Suwaiba, amma bai yi komai ba.

Babu wanda Nana ta saurara, ta shirya ta fice shi kansa Baban, ba ta tsaya ta kula shi ba. A ƙofar gida ta haɗu da Gaddafi, bai kula ta ba, bata kula shi ba, ta tafi. Dan tun da Allah ya sa ta dawo gidan, bai ƙara ko yinƙurin shiga harkar Nana ba.

Yau ma buzayen ta tarar a jikin bishiyar jiya, su na ta shan shayi, suna hira cikin nishaɗi, tana son ta ƙarasa gidan da ta zo, tana jin tsoro kar yau ma wani ya zare mata takobi, dan ita gaba ɗayansu tsoro suke ba ta, gani take kamar akwai wanda ba mutane ba ma a cikin su.
Tana cikin yin wasi-wasin, kawai ta ga an buɗe gate ɗin gidan, da sauri ta nufi gurin, sai ga Habu na ƙoƙarin fitowa. A ɗan tsorace Nana ta ce masa "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau sannu ko"

Ta amsa da "Yauwwa, dama shiga zan yi"

Ya ce "To bismillah" ta shiga tana ajiyar zuciya.
Ta nufi hanyar cikin gidan, ta ji haushin kare, gigicewa ta yi ta ƙwala ihu.
Sule ya fito da sauri, yana duba me ya saka Nana ihu.

"Mene ne?"

"Kare" ta yi maganar a diririce, tana jiran ta ga ta ina karen zai fito.

Ya ce "Ai yana ɗaure a baya, ba za ki ganshi ba"

Waige-waige take yi cikin tsoro, ba tare da ta yadda da abin da ya faɗa ba. Sai ma ƙoƙarin ja da baya ta koma da take yi.

Ya ce "Mu je na raka ki" ya yi gaba ta bi bayansa tana waiwaye kar karen ya fito.

A ƙofar shiga, suka yi kiciɓis da Yusuf. Ya kalle su ya ce "Lafiya?"

Sule ya ce "Kukan kare ta ji take jin tsoro, shi ne na rako ta"

Muryar Nana na rawa, ta ce masa "Ina kwana?"

Maimakon ya amsa sai ya yi dariya ya ce "Mu da muke saka ran nan gaba, ke za ki din ga ba shi abinci. Ki kwantar da hankalinki yana kulle ai" ta jinjina kai ta kalli Sule ta ce "Na gode sosai"

Ya jinjina mata kai ta shiga.

Yau ma Nana ta sha fama da Haidar, gaba ɗaya yaron sangartacce ne, ba a kwaɓarsa. Ba kuma ta son saba masa da zare ido, ya koma jin tsoronta gaba ɗaya, ace muzguna masa take yi.

Ga babarsa kamar dai babu yadda ta iya ne, ya sanya ta bar Nana take rainonsa, amma a zahiri take nuna mata ƙyama.

Aka ce Nana ta je kitchen, ta ɗauki abincin karyawa.

Bayan ta karɓo abincin, ta ɗauki Haidar, ta tafi da shi ɗakinsa.

Shayi ne da soyayyen dankalin turawa, da ƙwai.

Ta ajiye kwanon a tsakiya, ta kalli Haidar ta ce ya saka hannu ya ci.

Da wasa da rarrashi, da hikima yana ci yana zubar da wani, tana tattarewa tana yi masa wasa da haka ya ci abincin. A hankali Nana ta samu ya ɗan fara sakin jiki da ita, har ta yi masa wasa ya yi dariya.

Alhaji Zailani na zaune a cikin motarsa, a harabar gidansa zai fita, sai ga ɗaya daga cikin yarn da suke yi masa hidima a gidan ya ƙaraso, ya durƙusa suka gaisa. Alhaji Zailani ya ce ya buɗe motar ya shiga.

Ya shiga motar, suka ƙara gaisawa, Alhaji ya ce "Ya ake ciki?"

"Eh ranka ya daɗe na je, na kuma yi bincike a kanta da gidansu sosai, gaskiya ba su da komai, ba ka ga gidansu ba ma kamar turken dabbobi. Rabi ginin ƙasa rabi na bulo, a iya binciken da na yi ko sana'ar kirki babanta ba shi da ita. Kusan kowa a gidan shi yake kula da kansa, kuma an saki babarta ba ta gidan, babu wani gata dai balle kulawa"

Alhaji zailani ya jinjina kai tare da ajiyar zuciya, ya ciro kuɗi ya bawa yaron nasa ya ce "Ga shi nan na gode sosai" ya karɓa yana godiya ya fita daga motar.

Da yamma liƙis ta fito za ta tafi, yau ma hannunta riƙe da ledar abincinta na rana.

Ta fito ta kullo ƙofar shiga cikin falon, tana ɗaga kai ta hango buzayen nan, zaune a cikin harabar gidan, suna ta dafa shayi su na sha, su na hira cike da nishaɗi.

Tunani ta shiga yi, yadda za ta ratsa ta gabansu ta wuce, da safe idan ta zo su na gefe, amma yanzu su na cikin gidan, dole ta gabansu za ta bi ta wuce.

Idanunta ne suka sauka a kansa, yana gefe shikaɗai, fuskarsa sanye da shuɗin rawani.
Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faɗuwa, da sai da ta ja ta tsaya.
Ta ɗan jima a tsaye, sannan ta fara tafiya a hankali ta nufi hanyar fita.

Kallo ɗaya ya yi mata ya gane ta, sai dai ya yi mamakin yadda aka yi yau, bai ganta tare da wannan mutumin ba.
Ganin tana tunkarar gate ɗin, tana haɗa hanya ya sanya Habu tashi, ya nufi gate ɗin shi ma.

A kusan tare suka ƙarasa, ya kalle ta ya ce "Kin taso kenan"

Ta jinjina masa kai kawai. Ya ce "To ki gaida gida"

"Tom na gode" ta fita daga gidan da sauri, sai bayan fitar ta sannan ta ɗan samu nutsuwa.

Ko da ta je gida, Yaya Atine ta tarar da Mama ga kuma Baba a gefe.

Tana ganin haka ta san akwai wani abu, da ƙyar ta dake ta ce wa Yaya Atine "Ina wuni"

Ta amsa da "Lafiya ƙalau, ashe kin samu aiki a wani guri"

"Eh" Nana ta yi magana tana tashi tsaye tana ƙoƙarin barin gurin.

Yaya Atine ta ce "Dawo nan, ai a kanki ake magana" Nana ta dawo ta samu guri ta tsuguna.

Ta ɗora da cewa "Wai ya jikin naki, bayan mun baro ki a gidan mai magani ya aka yi?"

Kan Nana a ƙasa ta ce "Da sauƙi"

"Kamar yaya da sauƙi, sauƙi sosai ko kuwa, kuma ya ki ke jin jikin naki yanzu?"

Nana ta amsa da "Lafiya ƙalau" kanta a ƙasa.

A ɗan hasale Yaya Atine ta ce "Ina magana, ki na sunkuyar da kai, to matar ubanki ta kafe, a kan sai kin bar gida ba za ta zauna da ke ba, tun da har kin fara shaƙe mata 'ya. Kin san dai ko kin bar gidan nan baki da gurin zuwa. Ana ta lallaɓata ta yi haƙuri, ta saka wa ƙofar ɗakin ki kwaɗo ta ce ba za ki shiga ba, sai kin bar gidan nan, ko ita ta bari. Mu na ta bata baki a kan ta yi haƙuri zuwa lokacin aurenki, na ce shi mijin naki haryanzu ba wata magana a ƙasa? Lokacin da suka tsayar ɗin har yanzu maganar na nan ko kuwa?"

Wani ƙululun takaici ya turnuƙe Nana, idanunta suka cika da hawaye ta ce "Ni bani da waya"

"Ni ki ke gaya wa baki da waya? Ba ya zuwa ne?" Nana ta jinjina kai alamar eh.

"To ke kuma ba zaki bibiya ki neme shi a wayar ba? Wato zaman gidan nan ne bai ishe ki ba ko Asma'u? Da ki ka samu wanda zai kwashe ki, da ke da larurar ki, amma ba za ki nutsu ki kwantar da hankalinki ba. Idan matar ubanki ta zube masa yaran nan, ta tafi, ke za ki maye masa gurbinta ne? Ki yi wa kan ki faɗa, duk gidan nan ke ki ka fara kai wa shekaru kamar naki ba ki yi aure ba" Yaya Atine ta gama yi wa Nana ta tas.

Ba ta ce uffan ba, ta tashi ta nufi ɗakinsu, ta ga kwaɗo a jiki. Ta dubi Mama ta ce "Zo ki buɗe mini, zan shiga"

"Ni ki ke gaya wa haka?"

Ta sake cewa "Eh, ki zo ki buɗe mini ƙofa zan shiga ɗaki"

Baba da bai yi magana ba tun ɗazu, sai yanzu ya ce "Nana babar taku ki ke gaya wa haka?"

"Baba ya zan yi ne? Jakata zan ɗauka na fita na shiga duniya? Na karɓi zaɓin ka zan auri mutumin nan, amma ni ba na son sa, saboda na faranta muku, na yadda zan aure shi. Baba duk cikin yaranka nice kawai baka ƙauna saboda kana jin haushin mahaifiyata, kuma ba ni da cikakkiyar lafiya, Baba ya zan yi ne? Na daina zuwa Islamiyya saboda tsangwama, cewa fa ake ni na kashe malam Auwal. Gida ma babu daɗi, an ce mini mayya, an ce ina shan jini Baba ko dai tsinto ni ka yi, ba kai ne ka haife ni ba?" Da ƙyar sauran maganun nata suke fita, saboda kuka da ɓacin rai."

Yaya Atine ta din ga tafa hannaye ta ce "Ma'u malam Isa ne fa baban ki, shi ki ke gaya wa wannan maganganun?"

"Idan ki ka ci gaba da ƙyale matar nan, sai ta haɗa kai da matar babanku ta saka an kore ki daga gidan nan, ki je ki shaƙe ta kawai" Ƙaisar ya ci gaba da sanya mata wasi-wasi. Ta dake ta fara addu'a, amma jikinta ya hau rawa.

Ayshercool
08081012143


Page 19

Baba ya ce "Atine kin gani ko, Allah ya sa ba jangwalo ta ki ka yi ba"

Gaddafi da tun ɗazu yana soro, yana jin duk abinda ake yi. Duk da ya yi alkawarin fita daga shirgin Nana, ga haushinta da yake ji, amma abinka da jini ɗaya, kawai sai ya ji bai ji daɗin abin da aka yi mata ba.

Sallama ya yi ya shiga, suka amsa ya kalli yadda Nana ke ta tsuma idanunta na zubar da hawaye.

Ya kalli Mama ya ce "Ina mukullin ɗakin nan yake?"

"Kamar yaya?"

Ya ce "Mukullin ɗakin da ki ka rufe"

"Ni fa ba zai yiwu na ci gaba da zama da yarinyar nan ba...

Gaddafi ya katse ta da cewa "Baba zai iya canza ki, amma ba zai iya canza abin da ya haifa ba.
Kuma so ki ke kamar yadda ta yi iƙirari ta ɗauki jakarta ta shiga duniya? Yadda ake zaginta a yanzu da cewar mayya ce, ana gudun larurarta, kuma ba za ku tsira ba, idan ta shiga duniya ta yi abin kunya, dan zai iya hana sauran yaran auruwa. Ki yi haƙuri kawai tun da kwanaki ya rage ta bar gidan. Idan ba haka ba kuwa Baba sai dai ka tabattar da ka sama mata gurin da za ta je ta zauna. Idan kuma ka shirya abin da wancan makakken ɗan naka zai yi maka idan ya dawo ya tarar ka kori ƙanwarsa shikenan. Dan wallahi tsaf zai kai ka human rights ya rufe ka"

Jikin Baba ya yi sanyi, babu yadda ya iya, ya ce wa Mama ta bayar da mukullin ɗakin da ta rufe.

Rai a ɓace ta ɗaukko ta bawa Gaddafi, ya karɓa ya buɗe ƙofar ɗakin, ya dubu Nana ya ce "Shiga, gashi nan an buɗe ɗakin"

Sai dai ya ga ta ƙi gaba ta ƙi baya, tana tsaye a guri ɗaya tana ci gaba da tsuma, hawaye na zuba daga idanunta.

Har zai ƙyaleta, sai kuma ya kama hannunta, ta din ga takawa a hankali ya shigar da ita ɗakin, ya kwantar da ita ya fito.

Ya kalli Baba ya ce "Dan zatin Allah ko ta farfaɗo, ka da wanda ya shiga sabgarta, kar ku ja ta ƙara birkicewa, ta hana mutane bacci yau. Shi kuma batun Saleh ina da lambarsa, zan tuntuɓe shi na ji ya ake ciki"

Yaya Atine ta miƙe ta ce "A'a ni bari na tashi na tafi, kar ta zo ta shaƙe ni a banza"

Mama ta kwaɓe baki ta ce "Ke ma kenan da ki ke zuwa ki tafi, mu kullum a haka muke."

Da haka Yaya Atine ta tafi ta bar gidan.

Nana ba ta farka ba sai can dare, ta fito ta yi alwala ta yi sallar magariba da isha'i, ta ga ledar abincinta a cikin ɗakin, ta zauna ta ci ta sha ruwa, sannan ta nemi guri ta kwanta. Ta yi addu'oin kwanciya bacci. Sai dai tana rufe idonta, ta ga hoton Buzun nan kamar yadda ta ganshi ɗazu da yamma kafin ta taho gida. Dumm wannan karon ma ƙirjinta ya buga, ta buɗe idonta tare da dafe ƙirjinta. Tun daga lokacin bacci ya ƙauracewa idonta har aka yi assalatu...

****
Kaiwa yake yi yana komowa a cikin falonsa, a tsakiyar dare, yana ta lissafin yadda zai ɓullowa lamarin. Yana matuƙar son buƙatar sa ta biya cikin gaggawa. Ya ma fi ƙaguwa ya cimma wannan nasarar kafin ya koma kan Alhaji Fatuhu.
Saboda ya sha fama sosai, kafin kwatsam a samu wadda aikin zai yiwu da ita.
Sai dai bai san yaya take ba, 'yar hannu ce za ta ɗauki haske kai tsaye, ko kuwa sai ya yi 'yan dabaru?. Haka ya yi ta wasi-wasi shikaɗai.

Wayewar garin Allah, Nana ta tashi normal, sai dai bacci da take ji sosai, saboda baccin da ba ta samu yi jiya ba.
Babu wanda ya tashi a gidan, ta shirya ta fita.
Makarantar da ta bari ta fara zuwa, Inna tana ganinta ta din ga murna. Ta ce "Mutuniyar, daɗina da ke akwai amana, ai na zata har kin manta da ni ne"

Ta yi murmushi ta ce "Haba da kuwa na kama ni an zane ni"

Inna ta ce "A'a babu wanda ya isa zane ki, to yaya aikin? Ba wata matsala?"

Ta jinjina kai ta ce "Babu matsala, da farko dai yaron ne rigimamme, amma daga bayan nan mun fara sabawa da shi"

Inna ta washe baki ta ce "Ai dama na san za ki iya, ki na da haƙuri sosai"

Nana ta sake murmusawa ta ce "Ya jikin director kuwa?"

"Oho masa, an ce dai haryanzu ba ya magana, yana nan a wheelchair ake ɗora shi. Ga shi tun da ya kore ki, an rasa wanda zai iya da rigimar yaran nan"

Nana ta ce "Wallahi Inna kewar yaran nan nake yi, mussaman Muhsin, shi ne na zo da kaina na gansu, mu gaisa"

"Eyya Muhsin babu lafiya, ya daɗe ba a kawo shi ba"

Nana ta kalli Inna ta ce "Ba shi da lafiya, me ya same shi?"

"a'a ban sani ba, amma haka dai aka ce"

Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ta san abin nan, kamar ya taɓa faruwa a wani guri an ce mata yaron ba shi da lafiya, amma ta rasa a ina ne.

"To Inna ba ki san gidansu ba, na je na duba shi?"

"Wallahi Nana ban sani ba, ai ke ya kamata na tambaya ma, yadda babansa yake mutunta ki"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ban san gidansu ba, amma haka kurum na ji na damu, yaron nan yana matuƙar ƙauna ta. Allah ya ba shi lafiya dan Allah Inna ki ɗan bincika mini, ko Allah zai sanya a samu gidan nasu"

"In sha Allah, ya na ga kin tashi har za ki tafi? Ba za ki jira yaran su zo ba, ku gaisa?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a gara na tafi kawai, kar na makara a can gidan"

Inna ta raka Nana har ƙofar makarantar, suka yi sallama.

Sosai batun rashin lafiyar Muhsin ta tsaye mata, duk da normally yara su na rashin lafiya, amma sai ta ji wannan kamar akwai wani abu da ba dai-dai ba.

Da tuna-tunanen ta ƙarasa gidan da take aiki, sai dai yau ba ta ga buzayen a waje ba.

Ta fara bubbuga gate ɗin da ɗan ƙarfi, a zuciyarta tana ta karanto Addu'oi tare da fatan Allah ya sa kar ta yi wani abu da zai saka su san ba ta da cikakkiyar lafiya.

Habu ne ya buɗe mata ƙofar, ta shiga tare da gaishe shi, ya amsa mata cikin sakin fuska. Sai dai tana jin haushin kare ta ja ta tsaya.

Ya kalle ta ya ce "Ya dai?"

"Dan Allah ka raka ni bakin ƙofa, tsoro nake ji"

Yayi dariya ya ce "Karen fa a ɗaure yake, amma muje"

Yana kwance a cikin ɗaki, idanunsa a lumshe yana bacci, kamar a mafarki ya jiyo sautin muryarta.
Cikin azama ya tashi zaune, ya kalli gefensa Sule ne yana ta bacci. Ya tashi ya ƙarasa gaban tagar ɗakin da suke, ya leƙa.
Tare da Habu ya hange ta, sai dai a wannan karon ma, babu mutumin da ya gansu tare wancan karon.

Har ta samu ta shige cikin gidan. Ya sauke ajiyar zuciya, ya dawo ya nemi guri ya zauna ya yi shiru.

Shigarta falon ke da wuya, ta tarar da Alhaji Zailani kirim a kan kujera, shikaɗai a falo. Dan sai da ta ɗan tsorata.
Da ƙyar ta iya gaishe shi, amma maimakon ya amsa mata, sai ya yi zuru da ido yana ƙare mata kallo.

Ba ta sake yi masa magana ba, ta wuce ɗakin Haidar.

Yana ta bacci, ta tashe shi, tayi masa wanka ta wanke masa baki, ta haɗa masa tea ta samo plate ta gutsutsura masa ƙosan da ta zo da shi, ta ajiye masa.

Ta saka shi ya yi bismillah, sannan ya fara ci. Yana wasa, yana jagwalgwalawa, tana gyara masa a haka ya ci ya ƙoshi.

Ta gyara ɗakin, ta ɗaukko shi suka dawo falo, yana ta wasanninsa, tana kallonsa tana murmushi, sai dai lokaci lokaci, idan ta tuna da Muhsin sai gabanta ya faɗi.

A haka Hajiya Amina, mahaifiyar shukura ta zo ta tarar da Nana da Haidar, ta shiryo za ta fita tare da Alhaji Zailani.

Ta ce "Ga Haidar ga kuma Nana, lallai ke 'yar baiwa ce, zuwan ki gidan nan, mun samu sassauci da ga rikicinsa na tsiya, me ƙaton kai kawai" Nana ta yi murmushi ta gaishe ta ta amsa.

Alhaji Zailani bai ce komai ba, sai kallon Nana kamar tsohon maye. Har suka bar falon.

****

Muhsin na kwance a kan gadon Asibiti, an saka masa oxygen ga ruwa ana saka masa, Alhaji Fatuhu ya yi shiru cikin damuwa, ya riƙe hannunsa cikin matsananciyar damuwa. Gefe mahaifiyarsa ce a zaune sai share hawaye take yi.

Wata babbar mace ce a gefen su, ta kalli Alhaji Fatuhu ta ce "Wai Alhaji kai ma kukan za ka yi ne? Kai ka na yi ita tana yi, maimakon ayi masa addu'a." Babu wanda ya kula ta a cikin su.

Ɗaya matar wadda take kama sosai da mahaifiyar Muhsin, ta ce "Kin san ƙaramin yaro da shiga rai, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login