Showing 72001 words to 75000 words out of 189977 words

Chapter 25 - BUZU BOOK1 COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Jan 2026

964

murmushi ya ce "Kin damu da ba ɗan da ke ki ka haife shi ba a kan kuɗi ƙalilan, ni a kan kuɗi masu yawa nake buƙatar ki ara mini dama, amma kin ƙi. Kuɗi zan baki ba ƙanana wanda ke da talauci har abada".

"Ka ce "Har abada? Kai wa ya baka wannan tabbacin? Dan Allah kar ka sake tunkarata da wannan maganar, ka rabu da ni ba na so".

"Daɗina da ɗan talaka girman kai, ke ga talauci ga girman kai"

"Na ji, dan Allah ka bani yaron nan na ba shi abinci"

Ya yi dariya ya ce "A tunaninki, zan zuba miki ido ne, na rasa damata wallahi ko za ki mutu sai na yi amfani da ke na cimma muradina, ba zan sake lallaɓa ki ba, ta ƙarfin tsiya sai na samu abin da nake so"

Jikin Nana ya hau rawa, sai ta marairaice "Dan zatin Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri bayan Allah da manzonsa mutuncina ne kawai ya rage mini dan Allah ka yi haƙuri"

Shima ya kwantar da murya ya ce "A'a Asma'u, mutuncinka kuɗinka, idan kina da kuɗi miji sai wanda ki ka zaɓa. Auren ma bai zama dole ki yi ba, na ishe ki komai. Kin ga yau ne ranar sa'ar aikin nan, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ba dogon lokaci za a ɗauka ba"

Dif! Dif! Dif haka zuciyarta ta ƙara ƙaimin bugawa, maimakon tsoro ya shigeta sai wata irin rawa da jikinta yake yi.

"Ka bani hanya na wuce, idan ba haka ba wallahi sai na kashe ka, ka je a duba maka taurarin Shukura, wataƙila na ta sun fi nawa haske. Ka bani hanya kafin na yi ajalinka"

Ganin ya ƙame kamar gunki yana kallonta, ya sanya ta hankaɗe shi, ta buɗe ƙofa ta fita. Tana fita daga ɗakin ta ƙara jin ta burkice, kamar hankalinta zai gushe.

Biyo bayanta ya yi, tana gaba yana bin ta a baya yana kiran sunanta.

Tun kafin ta ƙarasa gate, ta gan shi zaune a kan benci shikaɗai, addu'a ta din ga yi Allah ya sa a buɗe gate ɗin yake ta fice, domin in dai wannan ne ba kulata zai yi ba ya buɗe ƙofar. Kullum fuskarsa cikin rawani.

Sai da Alhaji Zailani ya yi mamaki, domin hatta masu gadi ya aike su, duk da ga babban yaronsa mai zuwa aike a gidan.

Ga mamakin Nana, kafin ta ƙaraso gurin gate ɗin, ya miƙe tsaye ya nufo su, taku biyar ya yi ya tsaya ya kafe Alhaji Zailani da ido. Ji ya yi tamkar an yi masa wani irin mugun dabaibayi ya kasa ɗaga ƙafarsa.

A hankali ya juya ya nufi Nana da take ta jijjiga gate ɗin, tana neman hanyar fita.

Bai ce mata uffan ba, ya buɗe mata gate ɗin ta fita ko takalmi babu a ƙafarta.

Ayshercool 08081012143
P22

A hankali Alhaji Zailani ya buɗe idanunsa, ya gan shi a kan gadonsa a kwance. Shiru ya yi yana ƙoƙarin tariyo abin da ya faru.
Fes komai ya dawo kansa, amma daga iya lokacin da ya biyo Nana, suka yi ido huɗu da wannan Buzun, ya kasa tuna komai.

Ya tashi zaune yana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, sai ga Hajiya Amina ta shigo ɗakin, hannunta ɗauke da kofin tea.

"Sannu Alhaji ka tashi?"

"Yaushe ki ka dawo?"

"Tun la'asar, nan muka tarar da kai a sume, Haidar na ta kuka na ce Nanan ba ta zo ba ne? Amma doctor Sharif ya zo ya ce ba sai an kai ka asibiti ba, ya yi maka abin da zai yi maka, ya ce jininka ne ya ɗan hau"

Ya yi shiru yana tunanin to meya same shi haka? Amma ya kasa tuna komai.

****

Nana kuwa tana shiga gidansu, gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu kanta, saboda a yadda ta shigo gidan, idonta a rufe, ƙafafuwanta babu ko takalmi.

Suwaiba ta ce "Jaraba"

Kukan tsuntsaye ne ya gauraye ilahirin dajin, sai kuma ƙaton tafki mai ɗauke da ruwa shuɗi, sai rugugi yake yi, yana tambal-tambal.

Tana tsaye tana kallon ruwan, ƙaisar ya bayyana a kan ruwan, yana shawagi yana kaɗa ruwan.

"Wallahi ba ka da wani amfani a rayuwata, kana kallon za a ci mini mutunci, amma ba ka yi komai ba, ba ka da aiki sai ƙoƙarin haukata ni." Ta yi maganar a hasale.

Bai yi magana ba, sai ƙara girgiza ruwan da yake yi, ruwan ya watso har sai da ya jiƙa ta, sannan ya ce "Allah ne zai tsare ki ba ni ba"

Cikin kuka ta ce "Ai dama ban ce kai zaka tsare ni ba, idan ma gatse ka ke yi mini ba zan taɓa neman taimakon ka ba, amma na meye za ka din ga razana ni a gaban mutane, sai na fita hayyacina na aikata abin da zai saka a ce ba hayyacina nake ba?"

"Abin da ki ka gani haka yake ko a zahiri, ba yi na yi dan na tsorata ki ba kawai" ya yi maganar yana fitowa daga cikin ruwan, da wani baƙin mayafi a jikinsa, yana jan ƙasa tare da ɗigar da ruwa.

"Biyo ni" ya yi maganr yana yin gaba. Bin bayansa ta yi, suka ƙarasa gaban wani dutse, ba ta san ya aka yi ba, ta gan su a cikin libraryn sa.

Ya ce "Wannan mutumin da ki ka gani yana kuka da hawayen jini, yana daf da faɗawa mawuyacin hali, a saboda abin da abokinsa zai yi masa. Abu ɗaya yake damunsa da yasa za a iya galaba a kansa, ba shi da riƙo da ibada sosai, sai baƙar aƙida da ra'ayin riƙau. Kuma ni ba na zama a guri mai ƙazanta, ko gurin da ake ta'amalli da jini, mussaman na bil'dama, ta yaya zan zo inda ki ke, alhalin inda ki ke zuwa ana ta'amalli da jinin bil'adama?
Jininku ya fi jinin kowace halitta ƙarni mara daɗi, amma ya fi kowanne zaƙi da daɗi idan aka sha. Shi yasa masu aiki da jininsin aljnun da suke ta'amalli da jini, da an ba su jinin bil'adama, suke aiki cikin gaggawa, domin babu jinin da ya kai na su zaƙi da daɗi in ji masu sha".

Mudubin da yake gurin ya nuna mata, ya ce "Kalli" cikin tsoro da razani, ta kalli mudubin.

Alhaji Zailani ta gani tsirara, ana kwarara masa jini a jikinsa, yana buɗe baki tare da ziro harshensa waje, jikinsa yana karkarwa.

Wata irin razana ta yi ta buɗe idonta, karaf ya sauka a cikin na Baba.

"Uban me ya dawo da ke gida yanzu? Ko suma kin yi musu wani abun sun kore ki?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"To me ya dawo da ke gida yanzu?"

"Kaina ne yake ciwo"

"Ki sha magani ki koma, idan ma korar ki suka yi, ki san abin yi, dan wallahi ban san ina zan nemo kuɗin nan na biya ba"

Ya gama faɗansa, ya bar ƙofar ɗakin, tana nan zaune ta ji sallamar Inna a tsakar gida.

Ta amsa daga ɗaki, tare da bata damar ta shiga.

"Nana ya na ganki a haka? Ba ki da lafiya ne?"

"A'a me ki ka gani?"

"Idonki ya yi jawur sosai fa"

Nana ta yi murmushi ta ce "Lafiya ƙalau bacci na yi "

Inna ta ce "Bacci kuma? Ina gurin aikin?"

"Daga can nake" ta bata amsa

"Wallahi da can gidan aikin zan je, kawai na fara zuwa nan".

Nana ta karanto damuwa a fuskar Inna, ta ce "Meyafaru?"

"Muhsin fa ya rasu yau ne uku"

Wata irin zabura Nana ta yi, ta ja da baya tana bin ƙwayar idon Inna da kallo, domin ta gazagata abin da yake fitowa daga bakin Innan.
"Ba Muhsin Fatuhu ba amma ko?" Nana ta yi maganar cikin tashin hankali, da ya gaza ɓoyuwa a kan fuskarta.

Cikin damuwa Inna ta ce "Shi mana, idan ba kya komai ki tashi mu je ki yi musu gaisuwa, an gano gidansu mun je ma daga makaranta".

Tamkar an tsinkewa Nana laka, haka jikinta ya mutu laƙwas, fatan ta a ce bacci take yi kawai mafarki ne. Can kuma sai mafarkin da ta yi da Muhsin ɗin ya dawo mata fes.
Zabura ta yi tai waje, Inna ta bi bayanta, tana kiran sunan ta.
Baba da yake tsakar gida ya ce "Lafiya ina za ki haka?"

Inna ta ce "Ɗaya daga cikin ɗalibanta ne ya rasu za mu je gaisuwa" gaban Baba ya faɗi cikin tsoro, ya fara fargabar kar dai ta tabbata iskokan Nana ke kashe wanda take mu'amala da su?.

"To Allah ya jiƙan sa"

Inna ce ta amsa ta bi bayan Nana.

Inna ta tare musu abin hawa, suka hau suka tafi. Sam Nana ba ta gane abubuwan da Inna take faɗa, fatanta kawai ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba. Saboda akwai kyakkyawar shaƙuwa a tsakaninta da Muhsin, saboda lokacin da aka kawo shi ma, bai kai a ɗauke shi ba, saboda ƙanƙantarsa, har goya shi Nana take yi, Allah ya sa mata ƙaunar yaron a zuciyarta.

Sosai ake zaman makoki a gidan Alhaji Fatuhu, ɗan sa bai taɓa mutuwa ba, sai a kan Muhsin, shi ne ƙarami amma ya shiga ransa.
Rumfuna aka kafa a cikin gidan, inda yake karbar gaisuwa, cikin gidan kuma mata ne suke karɓa gaisuwa. Gida ne katafaren gaske, ga girma ya sha kayan alatu.

Alhaji Fatuhu yana tsaye yana gaisawa da wasu, ya ga wucewar Nana da Inna.
Jikinsa ne ya yi sanyi, ganin yanayin tashin hankalin da yake kwance a kan fuskar Nana.

Inna har falon ta raka Nana, don yi wa babar Muhsin gaisuwa.

A gigice Nana ta shiga falon, kamar mai neman wani abu, ta tsaya tana rarraba ido ba tare da ta cewa kowa komai ba.

Inna ta taɓa ta ta ce "Ga mahaifiyarsa ki yi mata gaisuwa"

Nana ta kalli matashiyar matar da ba ta wuce shekara ashirin da huɗu ba, idanunta jawur.

Nana ta ƙarasa gabanta ta risuna ta ce "Baiwar Allah wai dan Allah Muhsin ya rasu?"

Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falon, suka amsa Nana ta waiwaya tana kallonsa ya ce "Nana kin samu labarin mutuwar ɗan ki ko?" Sai mahaifiyar Muhsin ta zabura ta ce "Ke ce Nanan dama? Muhsin har ya rasu kafin ya daina magana sunan ki yake kira, yana cewa a kai shi gurinki" sai a lokacin Nana ta ji kuka ya ƙwace mata, Inna take ba su labarin Nana ta je makaranta ganin Muhsin lokacin ba shi da lafiya ba ya zuwa makaranta.

Cikin kuka maman ta ce "Na gode sosai da sosai, ƙaunar da ki ka nuna masa ce ta sanya, duk wanda ya san shi, zai san sunan ki a bakinsa"

A wannan karon ta yarda da zancen mutane, ta fara lura da duk wanda ya shiga ranta take son shi, sai ya rasa rayuwar sa.

"Wai ke ba za ki daina kukan nan ba, kamar a kan ki aka fara rashin ɗa? Wannan ai rashin tawakalli ne?"

Nana ta waiwaya ta kalli mai maganar suka yi ido huɗu. Matar ta ce "Ahh wannan ba Nana ba ce, yayar Jamila"

Alhaji Fatuhu ya ce "Kin santa ne? Antyn su Muhsin ce a Young talented academy"

Hajiya sa'a ta ce "Na santa, ba ki gane ni ba ne?" Nana ta girgiza mata kai alamar a'a.

"Ba da ke mu ka haɗu kwanaki a gidan maman khairat ba?" Nana ta sake ɗaga ido ta kalle ta, a take ta so ta nemi nutsuwarta ta rasa.
Wani abu mai muhimmancin gaske take son tunawa, amma abu ya gagara sai ma wani irin sarawa da kanta ya yi.

Hajiya Sa'a ta nemi ta rasa nutsuwar ta, ganin fuskar Nana tana canzawa kamar ba ta mutum ba, tana wani irin ja tamkar an shafa mata jar kala. Neman guri ta yi ta zauna da sauri, jin jiri zai ɗebe ta.

A hankali Nana ta ɗauke kanta, daga kallon hajiya Sa'a, ta yi musu gaisuwa, ta tashi jiki a sanyaye ta ce tafiya za ta yi.

Mahaifiyar Muhsin ta ce "Bari mu je ki yi wa kakarsa gaisuwa dan ita ma ta sanki a bakinsa.
Haka Nana ta din ga yi musu gaisuwa, tana jin tamkar su ma suna zargin ita ta kashe musu ɗa, mussaman da aka ce yana ta kiran sunanta.

Ta rako Nana har harabar gidan, tana ci gaba da yi mata godiya. Alhaji Fatuhu ya ƙaraso ya ce "To Nana Allah ya ƙara mana haƙurin rashin Muhsin"

Ta jinjina kai amma ta kasa magana. Ya kalli maman Muhsin ya ce "Yanzu Alhaji Zailani ya kira ni, yake bani haƙuri bai shigo ba yau, ba shi da lafiya ne wai"

"Ai ɗazu Hajiya Amina ta zo da safe tare da mai aikinta sun kuma yi mana gaisuwa ai ba komai sun yi ƙoƙari mun gode sosai"

Gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, ba dai Alhaji Zailanin dai da ta sani ba, tuno abin da ta gani a falonsa ɗazu ta yi. Sai dai ta rasa me ma za ta ce, wataƙila ma ƙaisar ne kawai yake wasa da hankalinta.

Haka suka kama hanyar komawa gida.

Nana na komawa gida la'asar, kasancewar ba ta salla, sai ta shiga ta yi wanka ta kintsa jikinta.
Wani abu mai ɗaci ya tsaye mata a wuyanta, har ya fara ƙoƙarin hana ta numfashi.
Ba ta ko iya gani saboda azabar jiri da ciwon kai, ta kwanta ta yi shiru ta rufe idanunta, ta din ga tuna mutanen duk da suka rasa rayukansu da yanzu ita ma take kyautata zaton saboda ita ne.
Ta fashe da kuka, tana "Wannan wace irin rayuwa ce, gaba ɗaya na kasa tantance ni mece ce ma gaba ɗaya. Allah ya tsinewa tsohuwar da ta gada mini wannan masifar wallahi ba zan yafe ba".

*****
Malam Gambo mai allon ƙasa ne zaune a kan buzunsa, ya nutsu yana sauraren Alhaji Zailani.

"Ni dai abin nan ya firgita ni malam, ni ban taɓa abu makamancin haka ba, yanayin kamar ɗimuwa ko gushewar hankali"

Malam Gambo ya numfasa ya ce "Me yasa ka yi gaggawa? Wutar ciki ce da kai Alhajin Allah, ai a sannu za ka bi ta, ba kowacce yarinya za ka yi wa irin wannan tayin kai tsaye ba, mussaman idan ba ta saba ba, duk lalacewar zamani akwai na Allah"

"Wallahi kuwa yarinyar ta bani mamaki, akwai taurin kai na tsiya"

"Yanzu ba wannan ba, matsalar da nake gaya maka akwai, ita na duƙufa bincike a kai, kwanaki ba akwai wani wuridi da na yi maka ba, na kira wani aljani ya yi mana aiki ba ya ƙi?"

Da sauri Alhaji Zailani ya ce "Eh an yi haka"

"To wannan aljanin shi ne a kanta, goɗiyarsa ce"

Alhaji Zailani ya waro ido ya ce "Haba, ni fa na ce, wallahi da ta buge ni ta wuce, kamar wani ingarman doki ne ya hankaɗe ni"

"To ya zame maka dole ka kula ka yi taka tsantsan, ka bi a sannu burinka ya cika idan ka ci gaba da far mata zai iya ajalinka!"

"Ajalina fa ka ce?"

"Ƙwarai da gaske, hatsabibin matashin saurayin aljani ne, ba ya neman rigima da kowa amma idan aka taɓa shi faɗa da shi ba ya ƙarewa har abada"

Alhaji Zailani ya jinjina kai cike da gamsuwa, dan kuwa a rayuwarsa babu babban abin da yake tsoro sama da mutuwa, ko zancenta ba ya so gani yake, yana da cikakkiyar lafiya da ba za ta tunkaro shi a daidai wannan lokacin ba.

Sai da Nana ta shafe kwanaki uku, babu lafiya ga wani irin zazzafan zazzaɓi da take fama. A kwana na huɗu ta lallaɓa ta koma gidan Alhaji Zailani.
Hajiya Amina na ganinta cikin damuwa ta ce "Nana kwana biyu lafiya kuwa?"

"Wallahi Hajiya ba ni da lafiya ne"

"Allah sarki, ga shi ke ba waya balle a ji halin da ki ke ciki, Haidar duk ya damu yana ta tambayar ki."

Tana rufe bakinta sai ga Haidar ya fito da gudu, ya ɗane jikin Nana. Sai ta tuno da Muhsin, take wata fargaba ta shige ta, kar shi ma abin da ya samu Muhsin ya same shi, saboda sun shaƙu sosai. Jiki a sanyaye ta rungume Haidar.

"Nana anya kin warware kuwa, bari na kira Doctor Sharif ya zo ya duba ki, duk kin yi zuru-zuru".
Ita dai Nana ba ta ce komai ba, har mamakin kirkin Hajiya Amina take yi.

Har gida doctor Sharif ya zo, ya duba Nana, ya bata magunguna da allurai, ya saka mata ruwa a gidan. Ganin Nana a kwance duk sai Haidar ya damu, ya koma kusa da ita ya kwanta shima.
Nana cike da ƙaunar yaron take kallonsa, tana tuna Haidar, ta din ga addu'a Allah ya kare shi ya kiyaye shi, kar abin da ya samu Muhsin shi ma ya same shi.

Kafin yamma Nana ta ɗan ji ƙwarin jikinta, har ta din ga ɗaga Haidar tana yi masa wasa, saboda yadda duk ya damu, da ganinta a kwance.
Hajiya Amina ta fito falon ta miƙowa Nana waya, Nana ta saka hannu ta karɓa tana kallonta.

Ta ce "Tun da shi sirikin nawa, bai kawo miki waya ba, ni ga shi na baki, ki lallaɓa da ita, bai kamata a ce budurwa kamar ki ba ta da waya ba. Ga dubu uku, idan kin fita ki tsaya ki sai layi a yi miki rijista ki saka a ciki, in sha Allah nan da kwana uku za a biya duk ma'aikatan gidan nan albashin su. Ko wani abun ne ya faru kya din ga bugo waya ki sanar"

Nana ta juya wayar, da gani ba wani amfani aka yi da ita ba, sai ƙyalli take yi, har da charger.

"Yanzu Hajiya wannan tawa ce?"

"Eh mana Nana, ko ba ta yi miki ba?"

Nana ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce "Wallahi ban taɓa zaton zan riƙe waya mai kyau da tsada har haka ba. Allah ya faranta miki, ya kula miki da zuriyar ki, ya dauwwamar muku da farin ciki na gode sosai da sosai"

Hajiya Amina ta yi murmushi ta ce "Nima na gode sosai, ina jin daɗin yadda ki ke kula da Haidar da zuciya ɗaya, na ga kina da yawan ibada da azumi, dan Allah ki yi mini Addu'a idan ina da rabo Allah ya bani haihuwa" Turus Nana ta yi tana kallonta, a wannan shekarun nata me za ta yi da wata haihuwa?.

Ta yi murmushi ta ce "Kin yi mamaki ko? Ai ban taɓa haihuwa ba, ki roƙa mini, idan kuma ba ni da rabo, Allah ya ƙara mini dangana"

Nana a ƙasan zuciyarta murna ta taya Hajiya Amina, na rashin haɗa zuriya da wannan majanunin mijin nata mara addini. Amma a zahiri ta ce "Ki yi haƙuri Hajiya, kin san komai rabo ne, kuma Allah ya fi mu sanin abin da ya dace da mu. Ko kin bar duniya in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login