Showing 24001 words to 27000 words out of 107151 words
Dakinta Sai leda ba kujeru ganin Mama tace akwai wacce zata bamawa ban yi mgana ba, Sanin Halinta.
Haihuwar Mustapah yazo da Budi sosai Ya Ishaq har motar hawa ya mllaka ya siya mama nata,Budi ta ko'ona sai hamdala da Godiya yana Dinkamin suturu daidai gwargwardo sai dai na yaransa Dabam suke,Ni wani Lokacin ko yayi niyar yimin Rantsatsun kaya sai kalaman Mama su Dishe niyyarsa tunda tasha fadin siyamin kaya na alfarma barnan kudi ne, Tunda ba kyau zasu yi min ba sannan bansan yadda ma ake gayun ba kuma gaskiya suka fada ba karya sukayi ba ban san komai na gayu ba.
Ni dai iyakata nayi wanka na shafa mai na saka kaya,Abaya telan su mama ke min dinki Mama ta koma ba wata mace saboda sai nace yana kamani ni kuma bana so kaya su kamani na fison a shatamin na rika yawo aciki,ya Mariya ko Ya Asiya ko da wani Lokaci suna kokarin gyarani ni ko bana jin su gani nake yi gyara da gayu na wajen mata masu kyau da gata ban da ni da bani da ko d'aya daga ciki Dalilin dayasa Ya Ishaq yake Biye ma Mama kenan in ta fadi mgana hakan take indai a kaina ne ballatana ba ran Baba ita ke tafiyar da komai.
Mama ta bada shawaran nayi Tsarin iyali sai dai bai karbeni ba wannan yar ashanan aka sakamin ya sakarmin jini Dole aka ciremin ana ko Ciremin ko wata Biyar ban yi ba na Samu Cikin Ahmad,na haife su kusa da kusa domin a shekara ta takwas da auran mu da Ya Ishaq duka na Haifesu haihuwan gwarne na rika yi don ma Allah yasa ina da jarumta daukan duka kwarmiyan yaran
Cikin ikon Allah cikin ya'yana ba wanda ya Dauko Lalurata sai na godema Allah Ammh wani ikon Allah susan Lalurata barin ma Anum da Amir susan bana ji sosai in zasu yi min mgana sai sun daga muryansu.
Allah ya bani yara masu kirniya,musty Da Amun basa jin mgana komai suka gani sai sun taba abunga ga wanda bai da karfin ji ina chan ina aiki su kuma suna Falo suna barna bana sani kuma Duk abunda suka Lalata sai Ya Ishaq ya dora komai akaina,Shiyasa ya dinga masifan na bari duk sun bata gidan sun bata kayan kallo sun bata in ji min wanki kuma Mama sai tace bazai kara siya ba, a kyaleni na wahala ai da gangan na bari suka bata komai.
Ni kuma bana cewa komai,Saboda bani da wani zabi,Har zuwa yanzu da girma ya kamani da ya'yana ban daina samun tozarcin Wajen Mama da Anty binta ba tun ba'a sani ba har kowa ya sani,Goggo karofi dai hakuri take bani,in ta kirani a waya sai dai fa ta wayan ammh Sai na shekara kafata bata taka Karofi ba Tunda nayi aure Sau Daya naje naga Tamadina Shima Haihuwan Mustapah ne da naje karofi da Ya Ishaq yaji Labari masifa ya farayi wai baya son ya'yansa suna zuwa gidan wasu suna Rabe rabe.
Haka nan nake daga ni sai ya'yana sai Danginsa alhalin yasan bana jin Dadin su ammh ni nawa yan'uwan sai dai zumunci ta waya ya rabani da kowa nawa.Hafsatu ce kawai tana ta da Kulafucin yan'uwana bai da yarda zai yi da ita in sun samu Hutu tana zuwa ta zauna dani hakan sai yasa na Shaku da ita fiye da su Yaya Asiya.
Nasan Tabbas Ya Ishaq zai kara aure watarana ban daukesa alokacin da najisa ba Nima abakin Anty Binta na farajin mganar auran sannan Mama ta Fadamin nasan bani da wata Daraja a wajen ya Ishaq ammh na Dauka zan ci albarkacin ya'ya ashe bani da wannan alfarman na Kunshi Bakinciki Tundaga ranar farko da na wayi gari agidan Ya Ishaq a matsayin matarsa,Na kunshi takaici a matsayina na Uwar ya'yansa na fuskanci Tozarci a matsayina na kanwarsa tun a baya to wani tozarci ne ni Fa'iza da ya rage ban gani ba..?
Nayi Rayuwar aure shekaru Takwas da wani abu ammh Daidai da Rana d'aya ban Taba Danda'na yadda Dadin aure yake ba na dai yi shekaru Takwas ina Sanin yaya matsayin Tozarci da Gori yake sannan na kara zama Guilt akan kushen Hallita da kuma aibata Nakasa ta nayi rayuwa cikin Guilt din jin ban da sa'a na rayu cikin Guilt din Sannin ni bani da gata na zauna cikin Tunanin Mata ire ire na basu dace da suyi Farinciki ba.
Basu chanchanci miji mai kirki ba, basu chanchanci samun soyayyar ko wani Namiji ba,Sannan basu chanchanci Rayuwar Farimciki ba.
Mata ire irena Rayuwar kaskanci da Torzarci da Bauta ya dace damu,Ba kokarin mu goga kafad'a da kafad'a da mata masu kyau da gata ba shi yasa na Rayu cikin Tunanin kayan alfarma da shigar alfaarma da Kwalliya basu dace da ni ba, sun fi dacewa da mata masu kyau da Nagarta kamar yadda Ya Ishaq da mama ko Anty Binta ke yawan fadi akaina.
Tabbas na aminta da duka zencen su da Tunaninsu"
*Littafin KANA NAKA book 1 free ne book 2,3 paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*
*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*
*Janafty*[6/12, 12:11 PM] +234 808 711 8630: *KANA NAKA..!*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*Book 1*
_*Barka da Zagayowar Ranar Haihuwa HAFSAT MUSTAPHA HAFNAN(SAHIBATU),Madallake da ke,Allah ya karo shekaru masu albarka Happy birthday*_
*Assalamualaikum! Phydoors* *collection (home of all you need)tazo muku da kayan gyaran girki masu inganci da Gina jiki da faranta Ran Mai gida harda Ma yaranmu domin inganta girkin uwargida Kai harma da amarya tazo muku da egusi,* *crayfish ,manja ogbono dadai sauransu Zaku iya tuntubar ta wannan nomber 08062181151 ko Kuma shafinmu na yanar gizo https://instagram.com/phydoors_collection?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==Muna aikawa ko Wani gari da iKon Allah,ko gwada kayanmu da iKon Allah sai Kun dawo* 🥰🤗
*🅿️04*
Sai kuma girken girken zamani da na gargajiya da na koya a iya zamana agidan mama shima ba wai ita ta koyamin ba,Ni na koya da kaina Saboda ina da karambani Mama bata taba Damuwa dani ba tsakani na da ita sai Harara da hantara,tana ganina a matsayin wata aba mara gata da galishu wuya ce da wahala yasa tun ban iya komai ba har na koya.
Na yarda ina da nakasun rashin ji ammh bani da nakasun wani abun Hallita ajikina ina da rai na da lafiyata to zan yin komai,Na iya wasu girken girken a tashar arewa24 na shirin su Akushi da Rufi wani Lokacin Tibin ita kad'ai afalo tayi ta babatu in nagama aikina sai na Lallabo nazo na zauna Duk da bana jin yadda suke koyar da girken girken ina bin yanayin yadda suke Hada komai ina ganewa.
Sannan da kuma Anty Mamah babbar Diyar mijin Anty Binta ce mahaifiyarta ta rasu ne dalilin da yasa ma ya auri Anty Binta kenan.
Tana aure acikin asibitin Kashi wato Othorpedic na katsina mijinta Likita ne tana da Yan biyu wato Twins,Mama na yawan Tura ni gidanta Saboda reno Yaran nata duka mazane Hassan da Husaini masu Rigima ne Anty Mahma ba kamar Anty Binta take ba,bata da mugunta sai dai akwai saka aiki,Kuma tana da kyauta sannan bata kyamatata ko tayi min fada, in naje gidanta kamar jaka har gwara ma gidan mama ina Hutawa sai dai ita bambamcin su bana girki da kaina ita da kanta take shiga kitchen tayi abunta ammh nakan shiga na taimaka mata da yanke yanke da miko miko to da haka nake zura ido ina Fahimtar wasu abubuwan nasan bani da gatan da zan yi karatu ko ina dashi ina jin tsoro zuwa makaranta saboda kada akusheni ko ayi ma Nakasuna Dariya shiyasa na kan kasa ido da raunannun kunnuwana ina duba wasu abubuwan da jin wasu abubuwan iya abunda zan iya ji na kuma d'auka.
Sannan agidan Anty Binta ma na koya su Snaks saboda Diyar Anty Binta ta farko mai suna Halisa zamu iya zama tsaran juna tunda Anty binta tayi aure tana da kananun shekaru alokacin to ita ke sana'ar yin Snaks in naje gidan nakan kasa idanuwana ina lura da abubuwan da take yi a hakan na nake daukan wasu abubuwan.
Da yake ita Halisa tana da bambamci da su ba kasafai take nuna kyama gareni ba sai dai bata shigemin sau tari nakan taya ta aikin Snaks din ta in an kawo mata dayake sana'arta ne tayi suna tunda tana amfani da Social media alokacin.
Tun ina da shekaru goma sha Hudu a duniya jikina ya gogu da aiki babu aikin da zai gagareni komai yawansa agidan Mama tun karfe Hudu nake tashi Daga barci naje kitchen na kintsa Sannan na Dora abun kari sai naje na tada Badariya bayan na saka mata Heater na wanka Saboda zuwa makaranta Domin dokar da Mama ta kwafanin kafin bakwai na Safe na gama komai kada ta fito bata iske abinci a saman dining ba,ko kuma taji kafafunta na taka Datti acikin Falonta Shiyasa ina yin abun kari wani Lokacin ina Share sharen dakuna hatta Dakin Jamal ni nake gyaramai in suka tafi makaramta Saukin ta ma shi bai cika mgana ba barshi da waya a Hannunsa irin su ba kasafai ake gane inda suka dosa ba.
Ya ishaq kuma baya gida sai an yi Hutu yake zuwa yana ABU Zaria inda yake Masters di'nsa nima abakin Anty Binta naji sunan karatun nasa har na iya rikewa,Hatta da kayan Jamal da na Badariya da na Mama ni nake wankewa ammh Baba bai sani ba Saboda yasan duk wata baya fashin bada kudin mai wanki da guga Tunda Mama ta sameni take soke yan kud'ade'nta,in wankin ya taru tun safe in naje baya na fara sai yammah watarana ma bana ko samin zuwa islamiya,Washegari kuma Baba na fita zan dasa guga har sai bayana ya kage ba ci ba sha sai na gama in kuma nace zan tashi ko sallah in yi sai Mama ta kai min duka tana Fadin"Me kika sani a karatun sallar..?Ni fa jin baban su kawai nake in yana Fadin kina da ilimin addini ke da kike Bebiya gaki ba kyau ba fasalin y'a mace ai bautar da ta dace da irin ku kenan.."
In ta fadi haka bana damuwa sai naga gaskiya ta fada domin na fahimci in baka da kyau ko Asali da gata ko kana da wani nakasun Hallita baka da wani amfani Domin wad'anda suka fi kusanci dakai sune suka fi kowa kyamatarka to inaga na waje wad'anda basu san ka ba, mu'alama ce zata hadaku..?
Ina tuna Lokacin muna Malumfashi Iyayena sun san ina da Lalura ammh ko sau daya basu taba nuna gazawar su ba sun min dukkan gata a malumfashi makarantan da aka kaini ina gane karatu tunda ana yimin yadda zan gane sannan bamai kyamatata Saboda ina da gata alokacin ammh daga Lokacin da gata na ya kare sai nima nake fama da guilt din shiga cikin Mutane ina ganin ban kai ko wani matsayi ba sannan na aminta da mganar Mama iri iren mata irina Bautace ta Dace damu..
Shiyasa duk wahalan da nike sha bana Damuwa ina ganin ahakan ma ni kila nafi wasu ma ire irena,Baba duk baya sanin wasu abubuwan tun da in ya fita tun Safe sai Dare,in kuma ya Dawo yayi sallah yaci abinci zai kirani falo yayi ta kokarin na bayyana mai abunda nake bukata ko nake so ammh bana iya mgana Saboda Mama ina bala'in jin tsoronta kamar wata mala'ikar Mutuwa.
Baban katsina irin mazan nan ne marasa Bibiyan al'umuran gidansu shiyasa Mama ta samu dama tana Damawarta,Komai na Cefane Mama yake bamawa,Duk watan Duniya ita kuma sai ta samu nata aciki Mama tasan kan kasuwanci,Tana saida dikkakun kayan mata da maza anan ake dinka mata tana aika ma yan'uwanta dake yamai suna Siyar mata kuma har anan tana samun ciniki sosai tana harka da manyan mata bayan dikakku har Tamfofi da Lesuna tana saidawa da takalma Shiyasa take da tarin kawaye da Mutanen arziki da ke shiga suna Fita agidan,Shiyasa ko Sutura ita Baba ke bama kudin ko na Mutanen karofi ne kuma baya Bibiya,Shiyasa sai wanda taga dama ta bawa,ba kuma wanda ya isa yayi mgana duk sallah har da su Yaya Asiya Baban katsina ke yi ma Dinki adadin yadda yayi ma Badariya dani ammh ni ko Sabo daya Mama bata bani na saka sai tace Mace irina da kwance ta dace ni kuma sai mganarta ta zaunamin kayan alfarma masu kyau sai ajikin kyawawan mata wad'anda basu da wani nakasu Mata kuma irina da kwance muka Dace yawancin kayan yaran kawayen Mama nake sakawa Domin na badariya bazai min ba Na girmeta sosai alokacin,Su Yaya Asiya kuwa Kala dai'dai take jifan su dashi Yaya mariya bata da matsala ita da Hafsatu Goggo macece mai Tsayawa akanta ita da iyalanta Yaya Asiya kuma tace duk mugunta Hajiyar Dala tana barinta da Suturu Saboda ita yar gayu ce sannan mijinta Soja ne ya'yanta fes suke itama haka saboda haka Itama Yaya Asiya badai a ganta da kama mara kyau ba.
Ni dai ko da yaushe cikin Tsumma da Ragga In Baba ya gani yayi mgana Mama ta lawayance zance ni kuma bana iya karyatata agabansa,bazan taba mantawa da wata sallah ba,Sallah da na fara yinta a gidan Baban katsina Lokacin na kwashe wajen wata Tara a katsina,kuma tunda nazo ko Karofi kafata bata kara takawa ba Ga Hajiya na raina in Baba zai tafi gaisheta sai naji kamar na bisa,tunda duk karshen wata yake zuwa wani Lokacin shi da Mama suke zuwa wani lokacin shi kadai da Direba ko shi da Jamal.
Hajiya na rai na ita da su Yaya Asiya musamman Hasfatu kewar Tamadina kuwa har na cire sa araina tunda ba samun ganinta zan yi ba Tun bayan dawowata Ko mutum daya Daga karofi bai leko mu ba na dai ga Hajiyar Dala da suka taba zuwa Bikin Dangin mijinta ta sauka anan kawaye ne ita da Mama sai muguntar su tazo daya sai dai ita tafi mama ji da kai da nuna ita din watace.
Sallar azumi ne Dama da azumi duk na Rame na kara lalacewa,Ni bansan gayu ba, bansan komai mai kyau ba ni na dauka abu mai kyau a wajen mata masu kyau ake samun sa,Wani Riga da Sikat na saka cikin kwancen kayan ya'yan kawayen Da mama ke bani ne wuyan zamemin yake haka ma Sikat din yayi min yawa sai da na saka Tsumma na Taresa ajikina Hijabi ne kadai Sabo Shima Anty Mahma ce ta dinkamin domin jiya gidanta na wuni na tayata soyan Nama da aikin cinci Sai Dare ita da mijinta suka maidoni gida ita ta na da kyauta in nayi mata wahala tana min alheri takalmin kafata na Roba ne shima din Na jamal ne da ya daina amfani da shi na Dauka
Da farko Mama bata so aje dani Sallar idi ba,Sai Baba yace dani za'a tafi Ya Ishaq ya dawo agida yayi azuminsa Shi na lura kamar baya ma san kallo na shiyasa ban cika giftawa ta gabansa ba.
Lokacin da na fito Kofar gida Baba ya ganni sai da yaji kwallah ta cikamai ido,Ya kalli Badariya ta kure adaka ita da Mama,Jamal da Ya ishaq sun ci Fararan Shaddodi sai Faman sheke suke ni kuma bazar bazar kamar mahaukaciya wata yar aikin ma tafini kyan gani ni kuwa bakina kamar zai Tsage Saboda murna zan fita masallaci naga jama'a Tun kafin Baba yayi mgana Mama ta rigasa da fadin"Ke Fa'iza meyasa kika saka wadanan kayan..? Ina naki irin na Badariya..?
Sai na kasa mgana Saboda ni dai bansan da wani kaya ba,ba'a bani ba ganin Baba ya saussauto yana kallonta yasa ta kara karya murya tana Fadim"Bansan meke damun Yarinyar nan ba Abban Ishaq ko da yaushe bata da aiki sai saka Tsumman kaya nama ce ta hada su in zaka Karofi ka tafi da su arabama mabukata"
Ban yi mamakin kalaman Mama ba Domin tun zuwana gidan ba Dadewa,Ta daina Fada da Baba akaina sai ta koma aiki da Kissa shima shawaran wata kanwartace daga Yamai hure ita tace mata in tana so taci Ribar Rayuwa to ta daina tada Hankali ta yi amfani da kiss,kuma Tabbas kissanta tana Tasiri wajen Baba don nan take ya kalleni kafin yace"Haba Fa'iza ya zaki saka wadanan kaya..? Baki ga sauran yan'uwanki ba ne.?maza je ki sauya kaya mu tafi kada mu makara'"
Da Sauri Mama tace"Zamu bata Lokaci Alhaji muje in mun dawo sai ta sauya"
Sanin Halinsa na rashin bincike kan al'umura yasa tace haka,Haka muka tafi su kamar zara cikin wata ni kuma kamar yar aikin su Shikenan ko da muka Dawo Baba yayi baki yana falon waje har Dare bai kara bi ta kaina ba,Sai da Washegarin Sallah da kwana Biyu mukaje Karofi ranar dai Mama ta bani Sabon kaya na saka ta kuma ja kunnena in taji wata mgana sai na Raina kaina ni ko araina nace wazan gayamawa.?bata san ina da zurfin ciki ba ba tun yau ba,bakomai ake jinsa bakina ba.
Duk da Sabon kayane ammh da na sanya kamar wata Dussa komai ba Tsari ni kaina nasan ba kyakyawa bace ban mallaki komai na mata masu sa'a da gata ba,Kusan daman Hausawa kan ce in kana da kyau ka kara da wanka to ni bani da kyau din sannan ban iya wankan ba ballatana na kara dashi,Wani Lokacin sai Dare nake samun Damar yin wankan Tunda Dakin da nake ciki akwai karamin Tiolet to iya wankan ne ko shi ba don kyau nake yi ba Komai bazar bazar ne bansan iyakarsa ba.
Da mukaje karofi na hadu da su Ya Asiya har sai da sukace har baki na kara na rame sun yi tambayan Duniyan nan kan wani irin rayuwa nake yi agidan Baban katsina naki ce musu komai sai dai in kallesu ina mirmishi naji dadin ganinsu haka barin ma Hafsatu da ta zama kamar ba ita ba ta kara wayau da girma.
Ina jin su a tsakaninsu suna tattauna yadda Rayuwa ta jefa su a inda suke ni dai bana ce musu komai