Showing 36001 words to 39000 words out of 107151 words

Chapter 13 - KANA NAKA completed hausa novel

01 Oct 2025

16

ni nayi maraici ya'yana bazan bari su yi wannan maraicin ba, zan zame musu komai a wannan rayuwar zan zauna na basu tarbiya sannan na zama Tsani wajen inganta rayuwarsu domin sune Duniyata a yanzu bani da kowa daga Allah sai su sai yan'uwana.
Kamar kiftawan ido naji kukana ya Dauke na kurama Bangon Dakina ido ina Lissafin yadda zan fara gudanar da Sabuwar rayuwar da kaddara ta kara Budemin.
Abaya komai lalacewar aure na da Ya Ishaq bai furta zai jingine ni ba ammh ayau ya furta kuma alama ce ta angaji dakai ana neman maraba dakai,ni ba jahila bace ta bangaran addini nasan menene ma'anar Jingina amusulunci,Nasan zai kula da ya'yansa Saboda Dolensa ammh a yanzu ni ban zama Dolensa ba ya zama Dole na sama ma kaina mafita mafitar rike kaina tsayawa ga kafafuwa na ba saboda kaina ba sai Saboda in inganta rayuwar ya'yana anan gaba.
Ji nayi wani irin karsashin gwarin gwiwa  na kara shiga har cikin Tsokar jikina,Hawayena na share kafin na yunkura na mike,Fuskata nake ta faman gogewa araina ina nanata sunan Allah,Afili na furta"Tunda ka bukaci hakan ya ishaq zan yi maka hakan kamar yadda ka fad'a domin rama alheri da Baba yayi min..Sannan kamar yadda nayi maka alkawari babu wanda zai ji wannan mganar indai daga bakina ne sai dai daga bakin ka da ikon Allah zan zama Jajirtattaciya uwa ba domin na karfafa kaina ba sai domin na inganta Rayuwar ya'yana anan gaba"
Daga haka na fara laluban wayata dake saman madubin Dakin,Na dannata naga 1pm na dare ta wuce biyu saura,sauke wayar nayi nan saman madubin dakin nawa na Tura kofar Tiolet na shiga na dauro alwala nafito nazo na shimfida Darduma na Fara Nafilar da tazame min jiki duk daare na saka yakinin araina Bayan kowani Tsanani Allah na samar ma da bayin sa masu hakuri Sauka'kawa
Abaya in nayi sallolina na cikin Dare ina addu'ar Allah ya shiryamin yarana,ya saka musu tausayin junansu aransu,ya inganta goben su ya saka musu albarka acikin karatun su,Sannan na kan roki Allah ya sausauta zuciyar Ya Ishaq a kaina Ya sa ka Mama tasoni ta kaunaceni,ammh daga daran yau sai na sauya alakar addu'ata na roki Allah ya bani karfin gwiwa ya ciremin rauni da karaya yasa na tsaya nayi tsawon rai da zan zama Bango abun jigina wajen ya'yana na roki Allah da kyawawan sunayensa Chasa'in da tara akan ya tayani Tarbiyan y'ayana ya kular min da su ya zama gatansu ya tausaya musu ya shiryamin su duniya da Lahira yasa su zama abun alfaharin al'umma da musulaimai gabadaya.
Ban kwamta ba sai wajajen karfe uku na Dare,shima Ahmad ne ya farka da kuka na isa garesa na Daukesa na Fara Lallashinsa ganin yaki daina kuka sai na bashi Nono yana kamawa sai shuru ashe yunwa ce yana koshi sai barci,Garin nima na shimfid'ar da shi sai barci ya kwasheni sai jin Mganar Hafsatu nayi a kaina tana ta kiran sunana Lokaci d'aya tana Buga kafafuwana..
Firgigit din da nayi na farka sai da Ahmad dake rumgume dani ya farka shima a tsorace sai ya fashe da kuka mikewa nayi ina mika Sosai Hafsatu kuma na Tsaye a kaina ita ta D'auki Ahmad tana fadin"Kai sarkin kuka ai garin ka ya waye"
Sama sama na jita mikewa nayi a kasalance,na sauko daga kan gadon cikin yanayin mganata nace"Lokacin sallah ya yi ne..?
Tana zama gefen gadon da Ahmad a Hannunta tace"Eh har su Ya Ishaq sun tafi masallaci da su Amir yau kin makara"
Da karfi tayi mganar shiyasa na jita idanuwana na mutsike bina da kallo tayi lokaci d'aya tana nazarina kofar Tiolet na Tura na shige na rufo alwala nayi a gurguje na fito na iske tana cire ma Ahmad Pampers naji tana fadin bai ma yi komai aciki ba.
Ina kokarin Tada sallah domin har na sanya Hijabi na juya ina kallonta Lokaci daya ina fadin"Ha..Hafsatu..Kin yi sallar ne..?
Kai tsaye tace"ina Hutu dame zan taimaka miki kafin ki idar da sallar..?
Shuru nayi ina nazarin abunda zasu tafi da shi makaranta babu cefane komai ya kare hatta lemun yaran da Biskit sai kawai cikin yanayina nace mata"Babu indomie ta kare dafa musu farar shinkafa ki yi musu amfani da miyar nan"
Da toh ta amsa min ta fice Dauke da Ahmad ni kuma na tada sallah sai da nayi raka'atul fijir sannan nayi sallar asuba ina cikin azkar sai ga Anum ta shigo da karamin hijabinta alamun itama tayi sallan ne bayana ta D'ane tana fadin"Umma ina kwana"
Yaran sun san raunin jina in zasu yi min mgana sai sun daga murya musamman Anun da Amir.
Mirmishi na saki na saka hannu na Jawota gabana, na zaunar da ita ina Fadin"Ina kwana Anum d'ita"
Lokaci d'aya ina jan kumatun ta Anum irin yaran nan ne masu yawon tsiya in suna mgana sai ka zata ana gaya musu ne.
Kuri tayi min da ido ni kuma hankalina na kan littafin azkar din dake Hannuna ina karantawa sai ji nayi kamar daga sama tace"Umma kuka kika yi ko..?
Waya dake ki..?
Ban ji mamakinta ba sanin Halinta da Sauri nace"A'a wani kwaro ne ya fadamin a ido Anum."
Da Sauri ta bata rai kafin tace"ko Daada ne ya yi miki Fad'a?
Shuru nayi ina bin ta da kallo yarinya ce yar shekara biyar da wannan mganar ina laluban amsan da zan bata sai ga su Amir sun shigo yana rike da Hannun Musty dukkan su jikina suka fada Amir dai gefe yayi agabana kusa da Anum yazauna Musty daman akwai son jiki shi ya lafeni sai na rike sa ina jin wani Farinciki in na Tuna nima uwace ina da iyalaina da zasu iya zama abun alfaharina watarana.
Amir ne ya daga murya yana fadin"Ina kwana Umma"
Na amsa masa ina shafa kansa Musty ma da gwarancinsa ya gaisheni na amsa ina Dariya zama na gyara ina Fadin"Kun yi azkar din Safe..?
Amir yace"Umma Daada bai barmu mun yi a masallaci ba ana ta kiran sa a waya sai muka dawo gida"
Amir da kasafai ya cika mgana ba, sai in yaga dama,ban ce komai ba sai na kauce mganar nace su karanta azkar din su na Safe kafin Lokacin wanka yayi.
Nan suka zauna gabana suna karantawa in da suka yi kuskure sai na gyyara musu har Musty da bai gama iya mgana ba yana ta garancinsa.
Muna cikin Hakane Hafsatu ta shigo tace ruwan wankan su yayi zafi sai nace ta bari zan yi musu wankan ita taji da abun karyawan su.
Ko kafin bakwai na Safe gabadayan su sun shirya cikin Uniform din Tahfeeez din su,Babansu ban gan shi ba Domin tun jiyan nan bamu sake had'uwa ba.
Farar taliyar Hafsatu ta dafa musu sukaci da Sauran miyan jajjagen da nakedashi,Sauran kuma nace ta saka musu a basket din su babu lemo ko Biskit sai kawai nace ta dura musu aruwa a gororin su.
Suna zaune afalon suna cin abincin ni kuma ina gyara ma Anum littafanta da ta wargazasu,Ahmad na bayan Hafsatu yayi barci tun da yaji Ruwan zafi ni ban yi wanka ba Hijabin da nayi sallah ne dogo ajikina.
Hafsah na Durkushe gaban Musty ta na bashi abinci abaki Anum sai ta rika Sako hannu tana d'ibar masa abincin sa da karamin Fork din su farare na cin abinci shi kuma sai ya fashe da kuka daman duk ya fisu Rigima.
Hafsah ta gaji da mgana ta kai ma Anum Rankwashi akai tana Fadin"Babbar banza wacce bata san kaninta ba"
Ni ban jin me suke fadi ina dai kallon su Lokaci bayan Lokaci ina Mirmishi sai kukan Anum naji kamar wacce ake yankata na saki littafin Hannuna na mike a firgice da yanayin mganata na fara tambayan Hafsah me ya faru Hararan Anum tayi kafin ta fara min bayani ta karishe da fadin"Anty Fa'iza rankwashinta fa kawai nayi shine ta wani yanka mana ihu kamar ana yankata in baki ma mutane shuru ba sai na bige ki yanzu nan"

"Karki kara dukar min yarinya kada ki Sake Hafsah.."

Kamar daga sama domin mu dai bamu san fitowarsa daga shashensa ba dagani har Hafsa mun ji mganarsa Saboda a kausashe yayi maganarsa,Da sauri dukkanmu muka juya muna kallonsa yana sanye da Jallabiya mai ruwan madara Kansa ba Hula fuskar nan nasa kamar ko yaushe a had'e,Anum na ganinsa ta tashi da gudu ta nufesa lokaci d'aya ta fad'a jikinsa cikin sangarta da shagwaban da ya bani mamaki tace"Daada kaga Anty Hafsah ta Dake ni ko..?
Riketa yayi Lokaci d'aya yasa ka hannu ya Dagota ya riketa a hannunsa ya Tako falon duka yaran suka mike suka bar abincin gabansu suka nufesa suna fadin"Daada.."
Zama yayi kan daya daga cikin kujurun falon yana Daga musty shima ya Daurashi kan cinyarsa Amir ne kawai ke tsaye a gabansa.
Kansu ya Shafa gabadayan su yana Fadin"Eyee..Ya'yan Daada yan makaranta..Mutsy me kaci haka bakin ka duk maiko.?
Da yanayin mganarsa yace"Chaliya"
Dariya yayi yana kwaikwayonsa Hafsah ce ta rankwafa ta gaisheshi ya amsa yana wani had'e rai nima na gaisheshi ya amsa a Dakile.
Kallonta yayi kafin yace"Hafsah ba na so ana dukan min ya'yana..Bana so..Har nawa Anum take da zaki dake ta.?
Hafsah mamaki ya kamata cikin mamakin tace"Rankwashin ta kad'an nayi akai kuma musty take sawa kuka"
Kai tsaye yace"Nace dai bana so kiyaye Ok"
Kai ta dagamai cikin wani yanayi kafin ta Dago ta kalleni sai naji wani iri araina ashe Ni ma kenan bazan iya Hukunta Anum ba tunda Hafsah ai kanwatace,Ahmad ya tambaya tace gashi a bayanta yayi barci daganan ta shige Daki jikinta duk ba Dad'i sai naji ban ji dadi ba sama sama nake ji yana Hira da ya'yansa ni kuma ina Had'a musu jakunkunansu waje daya na shiga kitchen na fito musu da Baskets din su guda uku nazo na ijiye ina Fadin"Anun Amir Musty kowa yazo ya Dauki jakarsa da abincinsa"
Amir da yazo ya Dauki nasa na taimaka masa ya rataya jakarsa,Anum kuma sai ta fara rigiman ba Biskit ba lemu.
Ya ishaq ya Dago yana kallona ni kuma kawai sai na Dauke kai na cikin Yanayin mganata na yi mata tsawa ina Fadin"Anum zan saba miki fa yaushe kika koyi rigiman ban..za.?
Kuka take neman ta sakamin sai na ware mata idanuwana na Daga Hannu kamar zan daketa sai ta yi shuru tana kallon Uban nata nima nasan ni yake kallo sai naki yarda na kallesa kada tsoron sa yayi tasiri a kaina.
Cikin Fadansa yace"Ammh kina ji na fada ma kanwarki bana son ana dukamin ya'ya shine zaki kwantata agabana ko Fa'iza...?
Kaina na kasa kawai sai nace"Ka..kayi hakuri"
Sai na koma na zauna,Kallona yayi kafin yace"Meyasa ba Biskit ba lemu a basket din nasu..?
Kai tsaye nace"Babu sun kare gabadaya"
Cikin Fad'a ya fara fadin"Gaskiya kina da matsala..Ke shikenan kamar ba mace ba..?komai na Dubaran mata baki iya ba..?to sun kare da kika yi shuru da bakin ki baki fadamin ba ke zaki siyo ki kawo..?
Ya karishe fad'a cikin hayaniyar mganar dayace saboda yanayina ya koya kaina na kasa na kasa mgana suma yaran sai suka yi shuru duk sun yi tsuru tsuru.
Fad'a ya cigaba da yayi yana fadar duk mganar da tazo bakinsa ya karishe da Fadin"Ya'yanki ma baki san yadda zaki kula da su ba Fa'iza to meye amfaninki..?
Komai naki zero ne baki da wani amfani wlh aikin banza kawai"
Dagowa nayi ina kallonsa Hawaye sun cikamin ido bana so su zubo saboda yaran duk sun kuramana ido Kama hannun Anum da Musty yayi yana Fadin"Muje zan siya muku a hanya ku jira anan bari na dauko key din mota dina"
Kai suka gyada mai ya juya ya koma Shashensa yana ta tsaki yana shigewa hawayena suka kawo sai na kauda kaina ina kokarin sharewa sai jin Hannun nayi a kan fuskata ina dagowa naga Amir cikin Wani yanayi da Sauri na kakaro mirmishi ina Fadin"Amir..kwaro ne ya fada min a ido"
Bai ce komai ba yasa Hannu ya Sharemin hawayena Lokaci daya yana fadin"Kiyi hakuri Umma"
Kawai sai naji wani Dum acikin kaina jikina yayi sanyi nabi Yaron da kallon Duka duka shekarun Amir bakwai ne ammh yasan ya ganni ina kuka ya sharemin hawaye ya bani Hakuri kawai sai naji wani abu ya tasomin daga kasan raina bansan Lokacin da na kamasa na Rumgumesa ba da dubara ina Dauke Hawayen idanuwana.
Mganar Ya ishaq kawai naji a tsakar kaina yana fadin"In bazaki barsa yaje makarantar ba ne sai ki gayamin na tafi na kai masu zuwa"
Da Sauri na sake sa ina shafa kansa a sannu nace"Kada ku manta ku yi addu'a"
Suka gyadamin kai,Gabadayan su suka dagamin hannu kafin ya tasasu su fice,bayan fitan su na Dade zaune ina Tunanin rayuwa kafin na mike Dakin Hafsah na shiga na isketa ta shimfidar da Ahmad nata barci ita kuma tana Hada kayanta a karamar Jakar gabanta na tsaya ina Fadin"Yau zaki tafi.?
Mganata yasa tasan na shigo ta Dago tana fadin"Eh Yau goggo tace na dawo gobe muna da makaranta"
Gefenta na zauna na Dafa kafadarta ina fadin"Kiyi hakuri kin ji Hafsatu.."
Mirmishin da yafi kuka ciwo tamin kafin ta kalleni Lokaci d'aya tace"Ni mai sauki ne Anty Fa'iza kece za'a bama Hakuri..Allah ya kara miki Hakuri"
Ban ce komai ba sai mirmishi da nayi shuru mukayi na wani Lokaci kafin tace"Zan biya ta Dutsenmah na Duba Tamadina na riga na fadama Goggo zan biya tachan"
Kai na gyada mata kafin nace"Kice ina gaisheta nima in sha..Allahu zan..zan zo na Dubata"
Da kai ta amsa min kafin tace"Allah yasa"
Bamu cigaba da Hira ba na mike na koma kitchen na dora ma Ya Ishaq ruwan tea bayan ya tafasa na juye mai a falas ba komai na cefane har kwai ya kare wani sauran dankali ne bashi da yawa na fere na soyamai sai namai miyar albasa,na tattara komai na kai Shashensa na shiryamai afalonsa na fice Ganin Hafsa ta karbi gyaran gidan ni kuma sai na kwashi wankin yaran da suka taru naje bayan  inda tankin ruwa da famfo yake yi na Fara wanki Uniform na fara wanke musu da Hafsah ta gama sai tazo ta sameni tana tayani sama sama muna Hira,Saboda yanayina Allah yasa bani kuma da yawan mgana sosai

Muna cikin wankin Ya Ishaq ya Leko dauke da Ahmad a Hannunsa yana fadin"Sai ku bar Cikin gida ba kowa sannan ku bar yaro shi kadai adaki..?
Wannan wani irin rashin Hankali ne..?
Da Sauri na tsame Hannuna a ruwan Sabulu na karisa wajensa na karbi Ahmad ya juya batare da yayi min mgana ba sai nabi bayansa muna zuwa Falo ya tssya ya juyo yana kallona Lokaci daya yana fadin"Ga cefane nan..Ki lallaba kinsan ina da Hidima yanzu haka wajen Milyan daya zan yi ma Anty Binta ciko na Hidiman bikin nan sannan ba Lalle na kara miki wani cefane ba sai karshen wata"
Da kai na amsa mai kafin a Sannu nace"Angode Allah ya saka da alheri"
Ko amsa ni bai yi ba yayi gaba daidai Lokacin da wayarsa tayi kara kafin ya shiga ya Daga wayar kasa kasa yayi mganarsa ban ji ba.
Zama nayi na bama Ahmad Nono na maidasa baya na kwantar Domin bazai yarda na ijiyesa ba.
Na dauki Ledojin na shiga da su Kitchen Katan din Bobo ne sai na maltina sai Biskit kwali biyu sai Na ruwa faro sai kwai da doya sai Dankalin Turawa sai kayan miya,na Zazzage komai na jera a muhallinsa
Sannan na koma muka cigaba da wanki ni da Hafsah duka sai da muka wanke har da nawa muna bayan Ya Ishaq ya fice daga gidan bamu sani ba fitowa kawai nayi naga bayanan sannan ba Motarsa nasan bazai wuce gidan Mama ba..ga Hafsah zata tafi bani ko da naira Biyar balle na bata na Mota.
Ina so na bata wani abu ta kaima Tamadina bani da komai sai na Dibar mata Sabulin wanka da na wanki muna da Sauran su bai kare ba, nace ta kai mata,mganar kudin mota kuma tace min kada na Damu goggo ta bata 3k da zata taho zasu isheta ta koma Gida ina ji ina gani Hafsah ta tafi ni na rakata har kofar gida muna Daga ma juna Hannu.
Na dawo cikin gida Nepa sun kawo wuta na zauna na fara gugan kayan Su Amir saboda sai yammah zasu dawo,haka ma Ya ishaq sai da yammah sai nayi Tunanin sai da yamah nayi girkin ni kuma Daman cikina ya cushe hafsah kad'ai taci taliyan nan na Safe ni kuma sai na barta sai an juma.
Ban tashi Daga wajen nan ba sai da na goge rabi da kwatan kayan nan tas sai wad'anda basu bushe ba kawai Sallah kawai ke tadani sai bayan Sallar la'asar na tashi daga wajen shima Saboda girki ne.
Sai alokacin nayi wanka na saka wata bubar doguwar rigar wata atamfa da Yaya Asiya ta dinka mana mu hudu har da ita.
Na shiga kitchen na fara Tunanin me zan sarrafa sai kawai nace bari nayi jallop din shinkafa tunda ina da Sauran kayan lambu sai na Hada da su,Naso na hada ko lemu ne to bani da kankana ba aya ba abarba ba Sinadrin hadawa kayan zobo kuma Daman Badariya ke siyon irin wad'anan abubuwan duk Ya Ishaq baya siyan su sai abunda ya zama Dole.
Sai da na gama komai naje nayi sallar mangariba Allah ya taimake ni Ahmad yau barci ya yini yi bai yi rigima ba Tunda naji su Anum shuru nayi Tunanin Babansu ya Dauko su suna gidan Mama.
Shiyasa na idar da sallah sai na fara jera ma kowanne kayan sa a dirowansa ina Dakin wayata na kara ammh ban ji ba sai chan sama sama naji karan a cikin kaina.
Na daukota na Duba Goggon Karofi ce Ina hada Hausa Ina karantawa wanda bai da wahala sosai in dai kamar na sune ko mgana wacce ba'a rubuta tayi tsawo ba.
Ina Daukan kiran na sakata a speaker Hafsah ce muka gaisa tace ta Sauka lafiya taje wajen Tamadina taji sauki tana ta godiya Daganan ta bama Goggo muka gaisa ta yi tamin nasiha daman ita nata kenan Fadi take yi "Fa'iza ki yi hakuri kin ji ko..?Allah bai manta dake ba..In sha Allahu zaki ci Ribar wannan biyayyar taki"
Shuru nayi ban ce komai ba ta yi ta bani Misalai da matan da suka yi Biyayya agidan aure sannan suka Rabuta ranar Lahira hawaye suka kawo Cikin idanuwana ina tuna Baba a mganarta shima duka kalamansa ne..daga karshe tace min"Naji Isahaq zai kara aure ko..?to sai kin kara Hakuri Fa'iza daman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login