Showing 105001 words to 107151 words out of 107151 words
manta da ita ba ina yawan mata Sadaka da fatan Allah ya jikanta da Rahma.
Matar da ta fara zame min uwa ita da ya'yanta a garin katsina itace Hajiyar su Raliya da ya'yanta ita ta zamemin makwafin Mama a garin nan ta Daukeni kamar yarta duk wani Cigaba ta bangaranta na fara samu ya'yanta da yan'uwanta a Dangi suka D'aukeni nima sai na Daukesu a Dangina ballatana da ta Fahimci halin zamantakewar da nike ciki sai ta zama tsanin dukkan wani Cigabana.
A yanzu haka kaf danginta da zuru'arta ni nake had'a ma ya'yansu turare da gyaran jiki in za su yi aure,Sannan ni nake yi musu kwangilar girken girken sha'aninsu suna zuwa wajena kai Tsaye nima ina zuwa wajen su kaina Tsaye sun daukeni dagani har ya'yana ahalinsu susan yan'uwana da Goggo suna zumumci da su Hajiyar su Raliya mace ce mai mutumci da Sanin Darajan Dan adam, kuma ko da nake da abun hannuna a yanzu ni da ya'yana alherinta bai taba yankewa a gareni ba.
Haka ma Badariya itama bazan manta da ita ba, Ita ta fitar da Zobo na da kunin aya na a jami'ar su ta Umaru musa yar'aduwa aka sanni na zama Dila ana sara, ni yanzu kusan in ba na gida gida da suka saba siya makota ba, na daina saida zobo da kunun aya rabe rabe sai dai a sara kamar D'ari ko sama da haka.
ballatana yanzu da Hafsa itama take aji daya a jami'ar itama tana zuwa dashi kuma ya kare,Har ta Yaya mariya duk sati tana zuwa ta karb'a Saboda ta fara yi da kanta sukace sun fi son dan'danon nawa sai kawai ta koma tana sara a wajena.
Ta ko'ina budi ya budemin na Roki Allah mafita kuma ya bani sannan na rokesa albarka acikin lamarin shima ya sakamin,Yanzu har ma'aikata na Dauka su uku suna taimakamin wajen hada zobon da kunin aya sai Sa'adatu da ita nake biyanta duk wata Saboda tana taimakamin kuma bazan manta da alherinta ba.
Sannan kuma Dawowar Hafsatu wajena sai itama na jawo mata Mutane Saboda Ina gyaran amare ita kuma tana kunshi sai gidanmu ya zama wajen shige da Ficen mata manyan masu abun hannuwan su,
Ni da ya'yana mun daina jiran wani ya yi mana ko ya bamu,na daina jiran kowa,ko Kudin makarantar su na biya musu ya kai su biyu,mganan kayan abinci da Cefane mantawa nake ma ina da Miji,na riga na saka ma raina ni kad'ai ce sannan ni ce uwa da uban ya'yana.Iyakata duk abunda naga zai yanke min na shiga kasuwa na siyo.
Ishaq ya dad'e da sanin Fa'iza yanzu bata jiran wani ko wata ballatana ta wulakanta.
Snnan ni na saka Ahmad a makaranta, naga ya wuce misali a gida ban jira kowa ba na kaisa da kaina,nayi masa registration,sannan Sauran bukatun yarana ma ba na jiran sa,ko Maman da ya saba wakiltawa ta kawo musu in taga dama.
Ya'ya na suma suna kece raini cikin Sutura mai kyau,da Tsada ashe rashin samun jin dad'i ne yasa fatar su ta Dishe da suka samu sauyin rayuwa da mayuka da sabulai masu kyau da Tsada sai ga shi sun yi tas da su, hatta ni bakin nan nawa ya rage nayi shar dani na kara kiba kamar ba ni ba.
Don ma ban maida hankali wajen gyara ba,da kila da yanzu fa'iza ta sauya sauyawa ta sosai.
Yaya Asiya da tazo kwanakin baya ta taga yadda rayuwata ta dawomim fad'i ta ke yi "Allah mai girma.Shi yasa akace kowa yayi hakuri zai dafa dutse har ya sha romonsa,ga shi Fa'i ta dafa tana shan Romon sa"
Sai dai nayi dariya domin suma daidai misali ina taimakon su tunda ina da shi,Bangaran Yaya ishaq kuma zan iya shaidar sa ta banganran, bai taba nuna bakinciki ko hassada kan samuna ba,Kamar yadda bai tabamin mganar ta yaya komai ya fara Fa'iza..?nima ban taba gayamai ba kuma bai Damu da ya sanin ba.
Nima ba ni da wannan lokacin,sai dai shi kanshi yasan Fa'izar da ya sani a baya yanzu ba ita bace wannan Fa'izar ta samu ingantattacen Rayuwa,da sauyin da na tabbata ko a mafarki bai taba tunanin ni Fa'iza zan samu ba,sai dai shi Allah ba ruwan shi da wannan in ya tashi,Daukakarsa ba nasaba ko chanchanta yake dubawa ba,Bayi duka D'aya muke a wajensa.
Da gaske dukkanmu mun zab'i Rayuwar da muka ga zata Dace damu shi ya zabi zainab da iyalanta, nima na zabi ya'yana da sana'ata sai yayi wata uku bai zo katsina ba,ko yazo kwana d'aya biyu ya koma,ni ko baya gabana da zuwansa da rashinsa duk d'ayane a wajena,yadda baya shiga Sabgata haka nima ba na shiga tasa kowa tasa tafissheshi.
Suma yaran suna girma suna kara Fahimtar Babansu yafi son zama wajen Antyn su fiye da zama a inda Umman su take sun rage zumud'in zuwansa.
Zainab ta kara haihuwa an samu Fadil ita ta matsamin ta kuma matsa ma Mijinta naje har Abuja karo na Farko sunan fadil kuma nayi mata abun arziki kamar yadda take yi ma ya'yana Anty Binta kamar ta kasheni haka takeji sai dai ba dama Saboda Dan zaki ya riga ya girma, duk da basu daina cin zarafina ita da Mama ba,ammh sun rage suna shakkar min wani abun ganin yarana sun girma sannan nima na wuce Tunaninsu yanzu Fa'izar yanzu ba Fa'izar da suka saba tozartawa a baya ba ne.
A sunan Fadil di'n zainab da mahaifiyarta sun sakarmim komai ni nayi gabacin girke girken da akayi kuma ba'a ji kunya ba, abokan aikin Zainab suka zo suna ta santi,Dani da yara dukkanmu mukaje mun fi Sati a Abuja,kuma Uban gayyar na Abujan lokacin, ammh yadda ban gabansa nima haka na nuna masa tuni na daina masa ma karan,Sai mu had'u in ban ga dama ba, sannu bana ce masa,shi kuma mamaki da girman kai yasa ya ke nuna kamar bai ganni ba.
kwana Goma muka kwashe a garin Abuja Sannan muka Dawo katsina, har kums gobe Zainab bata tab'a min wani abu na Tozarci ba,sai kanwarta ita kuma ance bata kasar ta tafi kasar waje karatu.
Mama ta samu labarin Daukakata Daga sama ne, bata yarda ba sai da tazo ta ganin ma idonta komai ta koma gida tana fada,ta kira Yaya ishaq ta tirkesa kan ya barni ina tara mata agida sannan ina yawon zuwa gidaje da sunan yin girki, tunda aikin abinci sana'a ce da zai bar ni ina gantali da sunan girki.
Badariya ke fad'amin a gaban Anty Binta yace bazai iya hanani abunda nake so ba,kamar yadda shima ban taba hanasa abunda yake so ba. daganan sai ya kashe bakin su,Nasan sun yi min abubuwa da Dadama ammh ban rike su a raina ba, Mama har gaban abada matsayin uwa take gareni ina yi mata alheri sai dai bata tab'a karba ba har Atamfofi na taba siyan musu dukkan su Har Hajiyar Dala Mama ta Dawo min dashi tace a Fad'amin ban yi arzikin da zan siya mata zani ta Daura ba.tun kafin Ubana Sidi yasan kudi ta sani bazan Rud'eta da abun duniya ba.
Bana damuwa da mganganunta,Anty Binta dai ta amshe tana fadin nima haka na rika tatsan kaninta abun nasu ma kamar sun haukace Koda yaushe Goggo ke nuna min Ribar Hakuri tabbas kuma nima naga Ribar wannan hakurin da nayi shiyasa nake nuna musu komai ba komai ba ne.
To ni ina naga lokacin biye musu ma..?
Ina da abun yi lokaci na sana'ata ne da ya'ya na,ko D'an nasu da suke takama da shi Fa'iza ta daina ara masa lokacinta yanzu ballatana su.
****
Kiran sunana da Amir yake yi ne ya Dawo dani Daga tunanin da na shiga Firgitgit na sauke Tagumina ina fadin"Uhm me kuke fad'i..?
Amir yace"Umma wannan dogon Tunanin fa..?
Gyara zama nayi ina fadin"Ina tunanin watarana zakayi aure ka kawomin suruka nima"
Sai ya bata rai su Anum suka saka Dariya ya daka musu tsawa Hafsah tace"A"a kyalesu su dara Mallam"
Sai ya yi fushi ya wurgar da Sandar Hannunsa ya wuce fuu ya shige Dakinsu,Na bisa da Dariya Saboda shi yasha fadi'n bazai yi aure ba sai yayi kudi ya kaini Saudiya.
Su Anum na bari suna rubutu kan karamin allon na koma kusa da Hafsah ina fadin"Hafsah inaga fa hostel zaki koma ki fara bincikawa tun yanzu"
Sai ta dakata da abunda take yi ta kalleni tana fadin"Meyasa..?
Mikewa nayi ina fadin"Ba yanzu zaki san dalili ba.Ki dafa ma yaran nan indomie ki hada da kwai,kuci ni cikina ya cika"
Da Toh ta amsamin tabi ni da kallo tana mamakin meyasa nake wasu abubuwan kwana Biyu haka fa Sa'adatu tace na gayamata zan bar mata sana'ar zobo da Kunin aya nan da Lokaci kad'an,kuma naki cewa komai, bayan haka Ni kaina nasan Hafsat ta fara zargin wani abu ni kuma bazan bari ta fahimci komai ba ko Goggo bata san abunda na Kudura a cikin Raina ba, har gobe ina jin bakinciki da Yayata mariya bata kara takowa inda nake ba sai dai mu had'u a karofi ko in naje gidanta tunda yanzu na samu sake Fita free,to ina ma jiran sa kenan..?
Shi da sai ya yi wata uku bai zo ba,nima ko nake gaban kaina.
ammh indai gidana ne Ya mariya ta daina zuwa tun sanda mai shi ya yi mata iyaka da shi.
Cikin Sati d'aya na gama Had'a kayana waje daya,Ranar ma cewa nayi basai anyi zobon yammah ba, na safe daga daya kare a barsa haka,Da Daddaran nace ma Hafsat gobe zan tafi karofi tare da ita su Anum kuma Gidan Mama zan kai su,mamaki ya sa ta kasa mgana nima ban kara ce mata komai ba Domin ta shiga D'akina taga kayana a had'e waje daya kamar wacce zata tashi,ko zata yi Hijira.
Ni ko da na koma D'aki sai na shiga Tunane tunane na tuna sanda na saka Ahmad a makaranta har barazana Ishaq ya yi min in ina nuna mai iko kan ya'yansa sai ya rabani da su ya kai ma Mama su,niko a lokacin sai nace mai kada yayi gaggawa ya bari Lokacin da zasu koma karkashin kulawan maman ai ya kusa,
sannan na fad'amai suma ya'ya na ne, sannan komai nayi musu ban fadi ba ni uwace garesu kuma in yana ganin don yace na kula dasu ai baya biyana, balle yace aikin kudi nake yi masa.daga Lokacin bai kara tada mganar ba.
Na kwana sallah da neman zabin Allah duk da zuciyata naso ta karye Saboda in na kallesu bansan yaya zasu ji in yau suka wayi gari bana tare dasu ba sai dai ko bana so lokaci yayi da zan hakura da rayuwa tare da Ishaq kabir karofi.
Allah mai aiko da kaddara a lokacin da yaso washegari da safe su Anum na shirin tafiya makaranta ni kuma ina dakina ina faman jan casbaha ina hawaye,Kirjina yana ta zafi Saboda yanayin da nake ciki naji Hayaniya afalo da Mganganu sama sama,da Sauri na fito da Hijabina sai naga Jamal hankalinsa tashe yara duk sun yi cirko cirko a falo.
Hankali tashe na karisa ina fadin"Lafiya Jamal me ya faru ne..?
Cikin wani irin yanayi yace"Wlh Yaya Ishaq ne EFCC suka kama shi Daga Wajen aikin su na Abuja. tun jiya yana Hannunsu,Zainab ta kira Mama ta na kuka take fad'amata"
Sai naji na Rude yara ma suka fara tambayan me ya samu daada.
Cikin Tashin Hankali nace"Me yayi..?su waye EFCC..?
Cikin tashin hankali yace"Wata hukuma ce ta federal goverment da ke kula da sace sacen kudad'en gwammatin kasa,To abun dai kamar shiryawa akayi ance wasu miliyoyin kudi ne suka yi batan Dabo a ma'aikan su Yaya ishaq da aka tsannanta Bincike sai aka gano da saka Hannanunsa kudaden suka fita, shine hukumar tazo ta kamasa ance ko ganinsa basu bari an yi ba har yanzu.."
Sai na sulale na zauna kan kujera ina salati Amir ne yabi bayana da Salatin su Anum kuma kuka suka saka suna Kiran sunan Daada cikin kad'uwa nace"Hafsah cire mu su kayan makaranta mu..mu tafi gidan Mama"
Jamal Ahmad ya Dauka yana Lallashi ni kuma sai na koma D'akina na kalli kayana da suke had'e waje d'aya sannan na Maida su gefe a Fili na Furta"Ashe har yanzu Lokaci bai yi ba..?
Shin sai wani Lokaci ne ya Dace na Fara wata Sabuwar rayuwar..?
*Karshen littafi na D'aya*
*Nan na kawo karshen Littafi na D'aya na KANA NAKA,akwai sauran gwagwamarya,ga dai Ishaq a hannun EFCC,ko ya zata kaya..?*
*Ya matsayin aikin sa?Ina kudurin Fa'iza..?Zata tafi ne ko zata sauya ra'ayi..?ya makomar auran Zainab da Ishaq..?tunda da yuyuwar Abuja zata gagareshi shiga wannan karon?ya Mama zata yi..?Ishaq shine duka karfinta,Wani irin Daukaka ce take Bibiyan Fa'iza..?*
*Duka tarin amsoshin ku suna cikin Littafi na biyu da na uku,akan farashi mai sauki regular N500,sai kuma tsarin VIP1000,wannan karon bana son tsarin kati,a turo ta POS, akan wannan acct no din 0552179550 Jamila Umar gt bank,Zamu tafi Hutun sallah,sai bayan sallah in muna Raye zamu dora daga littafi na biyu,ammh in dan kun cika adadin ku na Mutane 250 da suka siya,ni nasan ina da masoya Fa'iza ma nada masoya ku yi Dafifi wajen rakata har border domin jin Abunda zai cigaba da gudana a rayuwarta da Ishaq,Janafty tace ta gode Allah ya hadamu a aljannah Ammen*
*Janafty*