Showing 60001 words to 63000 words out of 107151 words

Chapter 21 - KANA NAKA completed hausa novel

01 Oct 2025

18

Dagani sai ya'yana tun had'uwar mu da shi a kano sai da ya shafe wata biyu sannan yazo ya ganmu shima kwana d'aya yayi ya koma ko da daman ya Dawo komai na Cefanan mu ya kare daran ranar ma da yunwa yaran suka kwanta da Rana na samu nayi musu danwake da sauran garin Danwaken daya rage Shima jikinsa yayi sanyi daya ga ko kwaran abinci bamu dashi ya kira Mama yana mata mgana ga dukkan alamu komai na mu yanzu ya koma wuyar Mama ne.
Ya bani dubu biyar a hannu sannan ya Biya Haruna kudin watansa biyu ya tafi bayan ya fad'amin zai Dad'e bai zo ba zainab bata da lafiya Laulayi na Matsa mata shi ne ke kula da ita ban damu ba nayi mata fatan Allah yasa a rabu lafiya domin ni yanzu duniya baya gabana ballatana na Damu da abunda ke faruwa acikinsa ni dai kawai ya'yana sune nake ji sannan kuma zaman su nake yi,kuma Allah ne gata na garesa nake kai duka kukanaa..
Tun bayan da ya tafi ko gidan Mama da nake zuwa na Dauke kafata saboda sai in ina da kud'in zan je,kuma koma naje ba tarban arziki nake samu ba Shiyasa na kame kaina agefe Badariya ne ke d'an lekomu Lokaci bayan Lokaci sai Jamal in yazo gida Huta yakan zo Tunda suna yawan zuwa anguwan mu buga Kwallo.
Mama da Anty Binta kuwa Daman indai ka gansu to tabbas ba alheri ba ne ya kawo su.
Bangaran Karofi ma shuru ba wani Labari Hafsatun ma da kan lekoni kwana biyu ban jita ba tun rabuwar mu da ita a kano bana jin kowa nima bamai jina,Dani da yarana muka kulla kawance da juna in sun Dawo makaranta suna tare dani sai in barci yazo sun ma daina Damuwa da Zencem Daada Anum ce daman mai Rigima sai Mutsy to yanzu sun gaji sun Daina yawan damuna da Tambayansa sai nima hakan ya fiyemin saboda wani lokacin na kan rasa amsar da zan basu.
Ahmad na da shekara Biyu,na fara Tunanin ciresa a nono na yayesa ammh bani da komai da zan rika basa Tuni daman acikin Cefanan mu aka daina kawo mana kayan Tea,kuma ba ni da wani garin kuni ballatana na rika Damawa sai na kasa ciresa a nono Saboda kada ya wahala ni kaina bani da Lafiya duk na kara ramewa sannan ina Faman da yawan ciwon kai da jiri tsaye kawai nake ina tafe da Lalura ban sani ba.
Satin da muka shiga a Daddafe nayi sa saboda ciwon kan ya matsa min ga jiri  da zazzabi,sai dai ban kwanta ba Saboda yara,in suka fita makaranta sai na Dad'e ina kwance ina fama da kaina tun ina Daurewa har sai da ciwon ya kwantar dani Daran jumma'a,Cikin Dare na tashi na shiga Bayi na Dauro alwala kawai jiri ya kwasheni na koma na kwanta Tun daga Lokacin jikina ya rikice,sama sama nake jin komai kaina kamar zai Tsage gida biyu ga zazzabi na jin jikina,ina so na tashi ammh na kasa tashi ina jin su Amir suka shigo suna kirana "Umma.."Umma.."
Ammh na kasa amsawa Ahmad ma ya gama Budurina ajikina yana ta Dukana yana kiran sunana da gwarancinsa ammh na kasa tashi,ganin Halin da nake ciki yaran suna Tare dani barin ma Amir dake da wayau ya fahimci bani da lafiya su Anum nata damuna da surutu yace su daina Umma bata da lafiya Anum yar rigima sai ta saka kuka ganin haka Musty ya kama Amir ya Lallashe su.
Ina jin Amir na taba kafata yana fadin"Umma..Umma ana buga get"
Dakyar na iya bude baki nace"je ka bu d'e Amirr.."
Tare suka fita da Anum da Musty yana kai wa daman wajen sakatar tsakiya ne ya bud'e ashe Haruna ne yana ganin su basu shirya ba yace"Au yau ba zuwa makaranta ne Kabiru..?
Amir ya karkace kai kafin ma ya samu mgana da Sauri Anum tace"To ba Umman mu bata da lafiya ba ne"
Haruna yace"Subhanallah..Allah ya bata lafiya"
Aransa daman yayi tunanin haka Tunda bakwai da rabi bai taba fashi basu shirya ba,har zai wuce Anum ta saka kuka tana kiran Umman su,Haruna ya kalli Amir yana fadin"Jikin nata yayi zafi ne..?
Amir ya gyada mai kai yana fadin"eh bata iya tashi ma"
Cikin alhini yace"Bari nayi ma mai dak'i na mgana sai ta shigo ta duba ta..Allah ya bata lafiya"
Cikin Hanzari ko ya shiga gidansa ya samu matarsa Sa'adatu na sharan Tsakar gida tana ganin mijinta cikin mamaki tace"Ah baka tafi ba ne Megida..?
Cikin wani yanayi yace"Wlh ke dai bari naji shuru ne yaran basu fito ba na buga gidan sai ga su sun bude gwanin ban tausayi suna ta kukan wai Umman su ba lafiya"
Sa'adatu tayi salati kafin tace"Wayyo..Allah ya bata lafiya"
Ya amsa da Ameen kafin yace"Sako mayafin ki ki shiga gidan ki ga Halin data ke ciki"
Bata yi musu ba ta ijiye tsintsiyan Hannunta ta shiga D'aki ta sako Hijabi tace bari taje ta gani,a kofar gidan ma taga su Amir taja su zuwa cikin gidan Halin data ganni a ciki yasa Hankalinta ya tashi da Sauri ta fita ta koma gida ta fadama mijinta ga Halin da ake ciki.
Cikin wani yanayi yace"Jikin nata yayi zafi kenan..?.
Sa'adatu tace"Gaskiya ya kamata a tafi asibiti"
Ya jinjina kai yana fadin yana da lambar Ishaq bari ya kirasa sai dai yayi ta kira har sau uku bai daga ba sai kawai yace Sa'adatu ta shiga makotansu gidan wata Habiba ta mata mgana sai a kai yaran gidanta su kuma su tafi dani asibiti tunda ba'a samu Ishaq a waya ba.
Haka ko akayi ta shiga tayi mata mgana Habiba duk da bana Huld'a da ita bata ki ba tace zasu zauna a wajenta har mu dawo tare da Fatan sauki a gareni.
Sa'adatu ta sakamin Hijabi dakyar ta iya fito dani na shiga adaidaita sai general Hospital muna zuwa ganin Halin da nake ciki yasa suka karb'eni suka shiga dani bayan Dube Dube da gwaje gwaje suka bani gado bayan sun Dauramin Drip ana bukatar kudi mganguna,sannan Likitan ya fad'ama wad'anda suka kawo jini na ne ya yi sama sannan ga Zazzabi a jikina sosai.
Na galabaita da sai sun rikeni anan na kwana Biyu,Allah sarki ni ban san inda kaina yake ba ammh ina kwance ne Hankalina na wajen ya'yana sai da yammah na farka da su na Bude bakina Sa'adatu ce a wajena tun Safe girki kawai ta koma gida tayi,ita ke fadamin su Amir na gidan makociyarta Habiba cikin koshin Lafiya ta tambayeni ko ina da Lambar wanda za'a kira a sanar da su nace babu Saboda Lambar goggo kad'ai na Haddace kuma bana so a kirata a tada mata hankali.
Sai Dare Haruna ya biyo bayan ya Taso daga aikinsa ya Dubani ina ta musu godiya,ya kalleni kafin yace"Na yi ta kiran megidan ki bai Daga ba..Ko kina da lambar yan"uwan ki na nan sai ki bada na kira su na shaida musu"?
Kafin ma nayi mgana Sa'adatu ta bashi da amsa da nace babu.
Sai ya kara fadin"To ko gidan kakanin yaran nan zan je na shaida musu..?.
Sai na kasaa mai gaddama na D'aga mai kai kawai nan na kwana Sa'adatu ta kwana dani nayi nayi ta tafi gida tace bakomai su Amir kuma ta kira Habiban ta mata bayani tace bakomai zasu kwana a wajenta.
Washegari da Safe ta koma gida ta yi wanka ta yi abinci da Haruna yazo da Safe yace daganan gidan Mama zai je ya fadamata saboda yasan gida yana kai su Amir watarana in ya Dauko su daga makaranta.
Abun mamaki har Dare ba wanda yazo kuma daya dawo yace yaje ya sanu Maman da kanta ya fadamata,ammh kuma ba wanda ya lekoni sai Habibar ne tazo da yammah ita da su Amir suna ganina suka Nufeni suna kiran sunana na Rumgumesu ina jin Tausayin kaina,basu jima ba ta tafi da su ina ta mata godiya ganin su Amir sun yi tsaf dasu,tace bakomai ai d'a na kowa ne sai Dare sa'adatu ta dawo min da abinci da kayan da zan sauya na rasa da kalmar da zan gode musu su yi min gatan da su mama suka kasa yimin.
Sai da na kwana uku a asibiti sannan Sai ga Mama da anty binta sunzo dubani Lokacin ma naji sauki sosai basu iske sa'adatu ba ta koma gida ina gadon asibiti ma ban tsira wajen Mama ba, sai fad'a take min wai da gangan na kirkiri ciwo saboda ishaq ya dawo gabana ya Lalace to ban isa ba kaina na kasa ina kokarin maida hawayen dake cikin idona Anty Binta ne ta kalleni tana fadin"To meke damun ki..?
Wata mata dake jinyar na kusa da gadona Saboda general ward ne na mata tace"Haba baiwar Allah kya yi mata hankali baki ga bata da lafiya ba ne..?kun sameta ma yau da Sauki Sauki da kun ganta sanda aka kawota sai kun Tausaya mata Hawan jini yanzu ya zama ruwan Dare baga yara ba, ba ga manya ba"
Anty Binta da Mama suka kalli juna kafin Mama tace"Hawan jini..?
Anty Binta tace"Ba dole ta samu hawan jini ba ta sakama ranta bala'i ..Ishaq dai kike ma wannan kwanciyar shima mara lafiyan garesa achan tunda muna nan basai yazo ba"
Mama ta karb'e da cewa"Ai na gayamasa yayi zamansa kawai ya kula da Zainab"
Ina jinsu kaina na kasa ban ce musu komai ba suka gama cimin mutumci suka tafi ko tsinke basu zo min dashi ba,ba tambaya waya kawoni asibiti ina yarana..?ba abunda ya Dame su bayan tafiyar su haka na koma na kwanta ina ta kuka Matar dake kusa tace"Ki daina kuka kada ki kara ma kanki Lalura..Wad'anan dai ko suwaye basu da kirki kina gadon asibitin ma baki tsira ba..?
Ni dai na kasa mgana Likita yazo yayi zagaye da yazo wajena na tashi zaune idanuwana sun kumbura ya duba Fayel d'ina yana kallona kafin yace"Fa'iza Ishaq kin san abunda ke Damun ki..?
Na girgiza kai na alamun a'a cikin Sanin aikinsa yaja farar kujeran dake gefen gadon da nike kwance ya zauna yana fadin"Hawan jini..Jinin ki ne ya d'aga Sosai sannan kina da maleria"
Na dago ina kallonsa duk da naJi matar d'azu ta fad'a sai da nayi mamaki cikin yanayina nace"Hawan jini Likita..?
Sai ya d'agamin kai ya cigaba da fadin"Ki daina yawan Tunani in kina so ki Tsira da lafiyarki..Damuwa ita ta Haifar miki da matsalan da kike ciki..Sannan daga yau ki rika kwana cikin gidan Sauro saboda rigakafin Cizon Sauri Maleria na tada Hawan jini..Shima Hawan jinin yana Tada maleria in suka Had'e ma Mutun kuma bama son haka kiyi kokarin cin abinci sosai ki kuma kiyaye dokokin mu"
Na jinjina kaina kafin nace"Nagode likita..ina so ka sallame ni na koma gida"
Ya kalleni kai Tsaye kafin yace"Mijin ki ne zai dawo..?Domin wanda ya kawoki ya ce shi makocin ku ne mijinki kuma yana wajen aikinsa"
Cikin yanayin mganata nace"Ya'ya na..Likita na bar yarana ba su da kowa sai ni don Allah ka Sallameni"
Mirmishi yayi kafin ya mike yana Fadin"kada ki damu zuwa gobe da Safe zaki koma gida"
Na gyada mai kai daga haka ya wuce gado na gaba ni kuma na koma na kwanta ina Tunanin yadda rayuwata ta kare ace ina kwance bani da lafiya ammh ba wanda ya damu dani nasan da Goggo taji bazata zauna ba ni kuma bana son Damuwarta,Yau in da ace mutuwa nayi babu wanda zai san na mutu shi kawai ke sakani kuka.
Da yammah Sa'adatu tazo na tambayeta su Amir tace yau sun je makaranta,har acikin raina naji Dadi idona ya cika da Hawaye na kalleta ina Fadin"Nagode sosai..Allah ya saka da Alheri"
Ta amsa min da Amin a raina na Guduri niyyar in naji sauki na koma gida zan gyara mu'amalata da duka mokota na Domin na Lura sune Dangina dake kusa dani,Washegari da Safe aka bani sallama sai dai bamu tafi ba ba'a biya kudin gado da Sauran kashe kashe ba,Sai da Haruna ya koma gidan Mama ya fad'amata tace zata zo sai da muka kusa yini a asibiti sannan Anty Binta tazo tana ta wani yamutsan fuska ita ta biya duka kud'in da ake bukata sannan ta siya mgangunar da aka rubuta bata tsaya ba ta kara gaba Sa'adatu ta kamani ta Daukan mana Sauran kaya  muka yi sallama da yan daki muka fice.
Har cikin Dakina Sa'adatu ta kaini ta zaunar dani ina ta mata godiya matar nan bata tafi ba,Sai da ta share Dakunan ta gyara ta Dora girki Saboda yara ita ta Dinga fad'ama makotanmu bani da Lafiya duk da bana shiga ammh suna ta Shigowa Dubani har da Habiba ina ta mata godiya tace bakomai wlh..
Har yammah tana tare dani sai da su Amir suka dawo makaranta sannan ta koma gida bayan har wanka sai da ta tsaya nayi na sauya kaya naci abinci dakyar na sakata ta D'iba abincin da ta Dafa tatafi da shi su Amir sun yi murna da ganina motsi kad'an sai Amir yace"Sannu Umma Allah ya baki lafiya'
Sai na amsa mai da Ameen Amir su Anum kuma ba wayau suna ta wasan su sai dai sun yi murnan ganina Ahmad kuma saboda kwana Biyu bai sha Nono ba,sai ya manta da shi,Sai dai Habiba tace ya sha Rigima kunu take Damawa tana bashi,ya lafe a jikina yayi shuru Tausayin sa ya kamani na Rumgumesa ina jin kamar na fashe da kuka kwana biyu ne bana nan ammh ya'yana ma sai makota ne suka kula da su inaga in ba na tare da su gabad'aya Allah kad'ai yasan wani Hali zasu shiga shiyasa zan Daure zan kuma Jajirce saboda goben su
Washegari da muka Dawo gida ma Tun Safe sa'adatu ta shigo ita ta shirya yaran tayi musu kari dayake ita bata taba Haihuwa ba,bayan sun tafi makaranta tazo ta gyaran gidan,ta koma gida chan anjuma kuma tadawo tayi ma yara girki nasan ko bata fada ba aranta tana so ta tambayeni bani da Dangi ne..?
Ai rashin gatan yayi yawa sai dai bata ce min ba nima ban ce mata ba.
Kwana na Hudu da dawowa asibiti na ji sauki Nace sa'adatu ta daina zuwa tana min wahala na samu lafiya,Ranar har gidan Habiba sai da na shiga na kara yimata godiya sai dai duk wanda yaganni yasan na rame duk na kara Lalacewa.
Sati daya da faruwar abun Badariya tazo Dubani tana bani Hakurin bata sani ba sai abakin Halisa taji har asibiti na kwanta,ta yinin mu sai yammah da Halisa tazo dubani suka tafi tare,Ita ce ma suna mgana da Hafsah ta wayar Goggo ta fad'amata nayi ciwo har asibiti na kwanta ashe su Hafsah suna kano Yaya Asiya ce ta Haihu,suna kano shekaranjiya akayi suna Hafsa ke fad'ama Goggo tana ta Fadan ba wanda ya fadamata ballatana sauran yan'uwana kuma suna ta kiran wayata a kashe basu san ta Lalace ba..
Ranar laraba da Safe sai ga su A gidana Daga kanon suke Yaya Isan goggo yaje ya Dauko su a motarsa,Goggo ce sai Anty Nasara da Yaya mariya sai Hafsatu sai matar Isa Amina,sun zo sun ganni suna ta tafad'a gani na duk na fad'a na rame Goggo ta kalleni tana fadin"In wayarki ta lalace baki aron wata wayar makota ki kiramu Fa'iza"?
Kaina na kasa nace"Goggo ban da lambar kowa a kaina kuma layin yana gida"
Anty Nasara tace"to wa ya zauna dake..?
Kaina na kasa tace"Matar makocin mu haruna mai kai su Amir makaranta"
Su Goggo suka saka salati suka Dire,Yaya mariya tace"Daman wa kuke tunanin zai zauna da ita..?
Mama ko Binta..?azzalumai bakomai a zuciyar su sai mugunta ayi dai mu gani"
Goggo ta juya tana kallonta Lokaci daya tana fadin"Mariya..mariya ana rabaki da kiwon awaki kina fadin kyalla ta Haihu daga Saudatun har Binta ai ba sa'anki ko.?
Yaya mariya ta tura baki kafin tace"Ai gaskiya na fada goggo wlh wani Hisabin sai a lahira kalli yadda Fa"iza ta koma kamar wata yar aiki kalli gidanta kalli kujerun ta duk sun Fita Hayyacin su kuma wai wannan mai kudi take aure Allah dai ya waddan kudin miji in dai na irin mijin Fa'iza ne bashi da amfani ko ni da mijina karamin ma'aikaci ne wlh d'akina yafi na Fa'iza kyau sau dubu Saba'in wlh"
Anty Nasara na gefe ta kad'a baki tace"Ai ba gidan ne ya fita Hayyacinsa ba..ita kanta Fa'izan ku dubeta ku gani yadda duk ta fita kammaninta"
Fadin haka yasa duk suka sakamin ido suna karemin kallo Goggo tace"Duk kubar mganar nan mganar kayan daki zamu sauya mata in sha Allahu ai mune yan'uwanta Dolenta na kanmu Ishaq ba wajibinsa ba ne yayi ma Fa'iza komai ba"
Yaya mariya ta kad'a baki tace"ammh ai yana da shi..kuma bai gagaresa ba in da mutumci a wahalan da Fa"iza tayi da shi da danginsa ta chanchanci komai a wajensa"
Goggo tayi saurin tare mganar da kallona tana fadin"Fa'iza wannan ramar tayi yawa me ke damun ki ne..?
Sai nayi shuru na kasa mgana nasan in nace Hawan jini gareni na bude Sabon Shafi sai nayi kamar ban ji ba Sai da goggo ta kara mgana Sannan na ce mata Zazzabin cizon Sauro ne.
Goggo nata fad'an ko bana kunna mganin Sauro ne ni dai nayi shuru ban ce komai ba.
Hafsatu tayi girki Yaya mariya kuma ta ragemin wankin su Amir,daman sun taru Aminan isa kuma ta gyara Falon da Dakunan.
Bayan sun ci abinci sun yi sallar azahar na saka Hafsatu ta shiga da su gidan Sa'adatu suka yi mata godiya daganan nace suce ta kai su gidan Habiba itama suka mata godiya sukace bakomai ai yiwa kai ne.
Muna tare da su har La'asar akace Dan'uwa mai dadi naji Dadi sosai Yaya mariya ta nuna min Yaya asiya da D'anta a waya hoton da suka Dauka Ranar suna tasha kyau abunta sunan yaron Muhammad Auwal.
Sai bayan La'asar suka yi shirin Tafiya,Yaya Isa daman ya shiga cikin gari ne sai ga shi ya Dawo Hafsatu ta sakamai abinci da yake tana fashin Sallah tana falo Aminan Isa da Anty Nasara na Dakina suna sallah ni kuma ina Dakin su Amir ina sallah da ni da Yaya mariya Ahmad na goye a bayan Goggo Tun da ya fara rigima ta karbesa ta goyasa.
Ni dai na idar da sallah ina zaune ina azkar Sai naji mgana sama sama afalo Yaya mariya ta tashi ta fita,ba jimawa sai ga Hafsatu ta leko tace Goggo na kira na,Ina fitowa nagan su Tsaye sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login