Showing 96001 words to 99000 words out of 107151 words

Chapter 33 - KANA NAKA completed hausa novel

01 Oct 2025

32

gefensa na wuce abuna,Kafin na fita sai da nayi addu'an fita gida,sannan na karisa gidan Sa'adatu muka gaisa na kwanto mata Ahmad Allah yasa yayi barci ta karbe sa tare da kuninsa tamin Fatan Alheri daganan na fita na samu Adaidaita sai cikin gari.
Makarantar ta yan mata ne zallah suna barayin su sannan mu kuma inda zamu zauna wani babban aji ne, ko da nazo mata sun fara taruwa sai dai ma'aikatan basu riga sun kariso ba,na gaisa da matan dake kusa dani muka zauna jiran su tara da wani abu suka iso,,Rukuni rukuni suka jeramu a layi mun nuna katin shaidarmu sannan suka sanyamu a rukunin da zamu fara koyan abunda ya kawomu.
Ni rukunin girke girken aka sanya ni shi zasu fara koyar damu sai sun gama sai ayi barayin Had'a lemuka da rana ne Rukunin Koyar da Turaren wuta da Had'a Dilka..
Sai na Fahimci da Safe duk abun ci ne zasu koyar damu shiyasa sai suka raba abun,Ni dai ban tsaya kalle kalle ba na saka ido sosai,ina Fahimtar komai masu koya mana Rukunin Farko,Su biyu ne dukkan su mata ne, Daga ganinsu sun san kan aikin su Sanye da Fararen riga da Hula na masu kirkin da muke gani a Kwatin Talabijin.
Ranar farko wainar kwai suka koya mana da miyar gyada mai allayahu,sosai na karu na kuma rubuta sunayen abubuwan da suke fad'amana bamu gane ba,Suna yi suna yi mana bayani yadda zamu fahimta sannan in baka gane ba sai kayi Tambaya komai da komai na girken girken su, sun zo da shi suka kafa karamin Dakin girki a babban D'akin da muke ciki, nayi tambaya in da naga ban gane ba.kuma sun kara yi min bayani suna da Sauki kai matuka da iya mu'amala.
Daman kuma Koyar damu ne aikin su, har kuma mh iya sun kuma tabbatar mana da cewa zamu iya girke girke masu kyau da inganci.bayan an gama dukkanmu muka D'andana mu biyar ne a rukunin Girke girken,muna ta santi saboda yayi dadi sannan da alkawarin in muka koma gida zamu gwada mu gani.
Sai rukuni na biyu Had'a lemuka,Zobo suka fara koya mana Had'ashi,Duk da na iya zobo sai naga nawa shirme ne ashe ga inda ake zobo nan,Ranar anan Rukunin ya kare shima sun bamu mun sha dad'i,Daga karshe sukace in da bamu gane ba mu yi mgana ni dai akwai karambani daman duk abunda ban ji ba sai da na tambaya suka kara gayamin,Ranar farko kawai da fara zuwana naji araina zan iya komai insha Allahu na dawo gida da Farinciki na iske Ishaq baya gidan ban Damu ba daman na fita da key da na ga ya Kulle gidan sai na bude bayan na Biya na Dauko Ahmad.
Ko girki ban yi ba Dakunan kawai na gyara na share, Lokaci yayi na makara ma a rukunin Rana sai d'aya da Rabi na isa har an fara an raba mutane kowa da Rukuninsa sai da na nuna Katina sannan aka kaini Rukuni na,Abu na farko da suka fara koya mana yadda zamu had'a Turaran kamshi na Icce ne ranar shi mukayi har aka tashi,shima in da bamu gane ba suna bamu ikon Tambaya in da kuma zaka manta sai ka Rubuta na dawo gida karfe hudu da Rabi na yammah na biya gidan Sa'adatu na kara dauko Ahmad sallah kawai nayi na shiga kitchen Saboda yan makaranta suna hanyar Dawowa.
Duk da na gaji ammh ban damu in dai aikin wahala ne na saba shi kuma ya zame min jiki,sai da nayi wanka sannan naji dadin jikina Yara suka dawo makaranta da yammah suna ta Tambayan Daadan su nace ya fita bansani ba,ko saboda abun da ya faru ne sai da yaran suka gaji da jiran sa, suka kwanta sannan ya Dawo ina Falo ina Tattara kayan da suka zubar daya shigo nayi mai sannu da zuwa bai amsani ba sannan bai kalleni ba. ya shige bangaransa a raina nace ko nace a banza.
Washegari ma ya rigani fita,Nima ko Lokaci nayi na yi tafiyata kamar jiya,Sai dai na Fahimce zan rika shan wahala in dai ina jeka ka dawo sai na yanke shawaran in mukayi sati uku, zan fara zama achan sai mun gama Rukunin rana sannan zan dawo gida gabadaya kud'ina kada su kare wajen adaidaita na rasa mafita.
Yaya Ishaq kuma tun daga wannan sa'insan tsakanin mu mgana bata kara Hadamu ba, ni dai ina fita Hakkinsa in mun had'u ina gaishesa shine baya amsani duka duka kwana Hud'u yayi ya koma ko sallama bai yi min ba. ganewar ma da nayi bai kwana agidan ba nasan duk tsanaani in dai yana gari to zai kwana agidansa.nima ko na tattarasa na watsar domin da gaske nake yi na zabi Rayuwata da Rayuwar ya'yana sama da tashi Rayuwar.
Na cigaba da zuwa wajen koyon sana'o'i na hankalina kwance kusan indai akace wannan abun shi kad'ai ne Hope din ka da Fatan ka to gabad'aya Tunanin ka da Rayuwarka zaka Dorasa akansa ne,ya kuke gani in hakan ta faru da mace irina da daman jiran mafita take yi..?to kamar misalin nice Domin na maida gabad'aya Hankalina da natsuwata kan abunda nake koya,Shiyasa duk nafi kowa ganewa a Duka Rukunina tun bamu Rufe wata ba Ma'aikatan suke yaba hazakata da Kokarina,Gashi abubuwa Hudu nake koya ammh kwakwalwata tana Daukan abubuwa dadama. sannan ina gane duk abunda aka koya mana.
Muna rufe wata d'aya da Farawa na koma ina zuwa sau d'aya in na tafi sai Hudu nake dawawo saboda in aka tashi Rukunin Safe sai na zauna sai Rukunin yammah Tunda ma'aikatan suna nan suma ka'ida sai Hudu na yammah suma suke tashi, duk abunda muke yi suna daukan komai sannan suna Rubutawa saboda suna turama kungiyar Bayanan komai.
Yau da gobe zara bata bar komai ba kudin hannuna suka kare sai na koma takawa da kafata yara na fita makaranta nake fita da nisa sosai kafin na kai na jigata ammh hakan nake Daurewa na sama kaina yakinin ba wanda ya isa ko ya samu yana kwance, sai da ya fita ya wahala,Muna Hutu Ranar jumma'a duk sati sau Shidda kenan to ranar ne nake samun na gyara gida, har yi ma yara wanki da Sauran aikace aikace ni kaina nasan na Rame saboda wahala.
Badariya sai da muka raba rabin watanninmu sannan tazo gida ranar wata jumma'a muka hadu a bakinta nake jin Anty Binta tazo sau biyu bana gida ta je ta fad'ama Mama sai Fada take,Tana fadamin Maman ta kira Yaya Ishaq din tamai mgana ba'a san me ya fada mata ba,basu kara mganar ba,Badariya tace ita dai tayi gum da bakinta bata tofa ba, tana ji Mama na fad'an na fara gantalin bin gidajen makota.nayi dariya nace gwara da kika yi shuru baki ce musu komai ba.
Araina naji mamaki ban Dauka Yaya Ishaq zai yi Laushi ba ni dai abunda na sani bazan zauna Damar da na Dade ina jiranta ta Kubcemin ba,Bandamu domin ba ta su nake ba ta kaina nake da ni da ya'yana. Badariya taji dadin yadda na fadamata muna koyan abubuwa da Dadama,sannan wahalata ta ragu saboda Sa'adatu ta Daukemin Laluran Ahmad sai abun yazomin da Sauki,Ban gayama kowa ba So nake ko yan Karofi na basu mamaki Fata na da Dakiyata azabeni cikin mutanen goman da za'a basu tallafi saboda zai yi min matukar amfani.
Yadda Yaya Ishaq ya tattarani da ni da ya'yana gefe d'aya.haka nima na tatrarasa na watsar Sai dai ya'yansa ban isa na cire musu tunaninsu akan sa ba,ko bakomai mahaifin su ne,ya zama Dolen su ni kuma ko da yake mijina ai ba Dole na ba ne,Na riga na jigata da tafiyar kasan da nake yi ammh ban ji ko sau d'aya na gaza ba nayi fashi sau Biyu shima Ahmad ne yayi ta zazzabi ba Halin na fita na bar shi kuma zuwa da yara an hana, shiyasa na zauna na Kula da shi har yaji sauki muna gabda cinye wattani ukun mu,Badariya ta dawo wajena da kwana ashe Mama da Anty Binta Abuja sukaje sulhu Zainab ta samu ciki sai suka yi sa'insa da Ishaq akan Farhan bai yi kwari ba, zata zubar da cikin shi kuma ya hana ita kuma sai ta Ture mganarsa ta yi mgana da mahaifinta yace ta zubar, tako je aka markadesa shine rigima ta kai su ga Har Ishaq din ya mari zainab din ai ko Badariya tace Mahaifinta ya Kira Mama yana fadin Ishaq ya gama marin auransa kuma sai yayi mganinsa sai ya yi kararsa a kotu,Ai ba jaka ya aura masa ba.shine Mama ta rud'e ta yi ma Anty Binta mgana ta rakata suka tafi Abuja su sulhunta mganar.
A raina sai nace tun yanzu..? Auran barikin fa kenan,ai na Dauka ko me zainab tayi Yaya Ishaq zai yi hakuri da ita,tunda ita yar so ne kuma ita ya zaba ban dai nuna komai ba nayi fatan Allah ya Daidaita su Saboda ni bazan yi Dariya don haka ta faru ba Namiji ai duk inda yake yana amsa sunan sa na Namiji ne.
Wajen kwananta hud'u a gida na sannan su Mama suka dawo, sai ta koma gida Saboda harkan gabana nake yi yasa ban damu da na Bibiya ya suka kare ba,Nidai bana fatan tun yanzu auran su ya samu matsala ina Fatan su tara kyakyawan zuru'an da Yaya Ishaq yake mafarki da fata ko zai daina kallona a matsayin wacce ta zama Sillar shiga tsakaninsa da mafarkinsa da Burinsa.
Mun cigaba da zuwa muna koyan abubuwan da ake koya mana har ga shi yau da gobe bata bar komai ba zamu kammalah,Watanni uku kamar kwana uku ne a wajen Ubangijinmu,Ranar jumma'a muna Hutu asabar zamu gama gabad'aya ranar Lahadi kuma za'a sallame mu da Takardan shaidar abunda muka koya, a kuma wajen za'a bama wad'anda suka chanchanta tallafi.
Ranar jumma'an ina gida tunda bama zuwa ranar Sai ga Badariya da Raliya sun zo min da labari mai dadi bayan mun gaisa na kawo musu ruwa su Amir suna haraban gida suna waasa.
Raliya ta kalleni tana fadin"Anty Fa'iza ina tayaki Murna kin yi abu mai kyau, Hajiyar mu tana ta fad'amin a duk report din da ake kawo musu a duka Rukunin da kike Dauka kin zama zakara sosai ma'aikatan suke yabawa da kokarin ki"
Sai naji dadi na godema Allah acikin Raina Badariya na gefenta tace"Ai Anty Fa'iza ba daga nan ba Raly ni daman nasan zata iya"
Raliya tace"Haka na fad'a ma Hajiya..Nidai mun zo cin sauyin Sabon girki ne Anty Fa'iza me zamu samu..?
Na mike ina Dariya nace"Daman jiya alalan mai kifi da kwai aka koya mana yau daman ina da niyar gwadawa"
Ihu suka saka gabadayan su Badariya tace"a hada mana har da lemu mai Dadi don Allah"
Sai nace to a raina ammh ina Tunanin ina zan samu kudin kifi da kwai, tunda ina da wake kamar Badariya ta sani taja Raliya suka fita ba jimawa sai ga shi sun dawo da cefane har da kankana da kankara sukace Lemun kankana suke so nan da nan ko na shiga Kirchen na fara aiki suka shigo suna Tayani da hira da d'an taimakon da bazai gagara ba.
Nikan Waken Amir na aika ya kai mana makota muke da gidan nikan, kusa da gidan Habiba ne daman in dai aike ne ko nika kusa haka to Amir nakan aika Tunda ba nisa sosai,cikin awa uku muka gama alalan kwai da kifi na kuma had'a musu lemun kankana nan sukayi sallar mangariba suka zauna suka ci suna santi Raliya tace"Anty Fa'iza in da saura a samin a leda sai na kai ma Hajiyarmu alalan nan taci taji itama"
mirmishi kawai nayi daman na Mudu daya da rabi nayi na Dibar mata da yawa tace kowa sai yaci a gidansu ta karishe da Fadin"Zan miki tallah Anty Fa'iza dole mu bude Fa'iza Kitchen"
Badariya tace"Sosai ai Oder zamu fara yi wannan girki ai ko Hotel ko Restaurant albarka"
Haka suka yi ta zuzuta girkin da zasu tafi mukayi sallama suka tabbatar min da jibi zasu zo tunda taron a babban Hall din makarantar su ta Umaru musa yar'aduwa za'ayi.
Washegari da mukaje gwaji dukkanmu mukayi,Ma'aikatan duka gefe suka koma suka bar mana abunda zasu yi ranar, Kunun gyad'a muka yi bangaran abun sha kuma ni na zama zakaran rukunin mu sai bangaran girki kuma yam ball muka yi ma'ana Fanken doya,shima ni na zama zakara na Rana ma rukunin hada Kolaccha  ma ni na Jagoranci Rukunin mu,haka bangaran had'a Dilka da Halawa anan wajen muka mulkama kafafun mu da Hannuwan mu,wasu har da Fuska ni dai ban saka ba,Sannan mun had'a Turaren Humra na ruwa mai kamshi shima muka goga a jikin mu saboda muji yanayin kamshin,Ranar sai Yammah na dawo gida su Amir gidan Sa'adatu suka zauna sai da  na dawo.
Ranar Lahadi kuma na fada ma su Amir su yi min addu'a yau zan gama abun da nace musu ina yi suka yi ta cewa Umma Allah ya baki sa'a na amsa da Ameen.
Saboda taron gamawa ne Tare da Ahmad naje bansan makarantar ba, mai adaidaitan ya kaini hall din ba Boyayye ba ne ina zuwa na tambayi inda ake taro wasu yanmata suka nuna min, da wuri naje wasu duk basu zo ba ammh naga wasu daga cikin mu.
Karfe sha d'aya aka fara taron manyan mata masu alaqa da kungiyar duk sun zo ciki har da Hajiyar su Raliya na ganta ba su gayyato yan jarida ba Saboda basa son duniya ta sani su don Allah suka yi,Sai mu kawai da muka samu Horan sai kuma yan'uwan wasu daga ciki da ma'aikatan da aka Dauka suka koyar damu sai yan kallo.
Su Badariya sun zo su da gayyar kawayen su sai dai hannu suka Dagamin, tunda su suna baya mu kuma gaba akace mu jeri mu Talatin din da muka samu Horan.
Bayan jawaban godiya da kuma Fatan alheri ga wannan kungiyar aka gayyaci wata Hajiya Zubadai  itace kamar ma'ajin kungiyar reshen Jahar katsina ta fito tayi jawabi akan manufar kungiyar da kuma manufar taron da suka shirya garemu na mata talatin da suka koyar da su sana"o'i goma.
daganan aka bata sunayen mu ta rika kiran mu d'aya bayan d'aya muna karban Takardan shedar abunda muka koya ni ce ta goma acikin wad'anda ta kira Fa'iza sidi karofi. Dayake tana amfani da amsa kuwwa abun mgana, najita na fita Ahmad na goye a bayana ta bani Takardata sai da nayi Hawaye,Ina gani wata ta kusa da ita nayi mata rad'a a kunne ta kalle tace"Fa'iza sidi karofi ko..?
Na jinjina mata kai sai ta bani Hannu muka gaisa cikin kayattacen mirmishinta tace"Weldone Fa"iza"
Duk da ban ji me tace ba nasan yabo ne sai na jinjina mata kai sannan na koma na zauna,ina Duba Takardan Hannuna da Turanci ne sunana kad'ai na iya ganewa aciki,ammh nasan ko a hakan na tsaya na cinma wata gagarumar nasara a rayuwata ba Nakasashe sai Mai nakasar zuciya, sannan akace babu maraya sai Raggo. in ka tashi ka nema bayan ka bama Allah zabi to shi kuma Allah zai saka maka da kyakyawan sakamako.
An cigaba da kiran mu har zuwa ta karshe sannan wata Hajiya laila daga kaduna itace mai rike da mikamin P.R.O na kungiyar ta fito zata bada shedar girmamawa ga wad'anda suka zama zakaru a rukuninsu,Allahu Akbar ban taba zata ba, Ba zato ba Tsammani naji sunana Fa'iza sidi karofi na fita aka bani wani d'an kwalba mai ban sha'awa da sunana ajiki sannan matar ta tsaidani tayi jawabi da turanci sannan tayi da Hausa tana mgana akan cewa ina da Hearing problem, sannan ban yi boko ba.ammh na iya zama ta farko a fanni masu kokari a dukkan abunda na Koya, sannan ta sake bani wani abu nazare a wuya na ta makalamin na Girmamawar na koyi abu hudu masu wahala a acikin wattani Uku,Sai tafi raf raf ta bani Hannu muka gaisa har tana yi ma Ahmad dake bayana wasa ko da na koma na zauna sai na daga hannuwana sama ina fadin"Allah na gode maka..Alhamdullahi ya Allah dukkan wata ni'ima daga gareka ne"
Matan dake kusa dani suna ta min murna ina amsawa bakina har kunni na juya ina hangen su Badariya ta D'agomin hannu na Daga mata kyautan da takardan da aka bani, ita kuma sai ta Dagamin babban yatsanta alamun jinjina.
Bayan ni an kira mata uku suma an basu lambar girmamawa ta zama zakaru a rukuninsu,Daganan an wakilta uku daga cikin mu suka fita suyi jawabin godiya ni dai nace bazan iya ba Saboda ban taba fita gaban jama'a nayi mgana ba ko karban kyatuttukan ma Dakyar na iya fita kamar zan fadi haka na rika ji.
Ma'aikatan da suka koyar damu suna sun yi jawabin godiya ga wannan kungiyar sannan sun gode mana Bisa yadda muka basu had'in kai har muka koyi abunda ake so mu koya har kwalliya ta biya kudin sabulu.
Daganan sai suka koma gefe suna mganganu bayan minti goma aka sanar da kungiya ta ware zakaru guda goma da kungiya zata bama tallafi,Sauran kuma da ba'a basu ba,ba domin ba su kai ba ne a'a haka tsarin kungiya take suma nan gaba zasu iya samu.
Gabana sai ya fara fadi na riga nayi yakinin ko ba'a bani ba bazan bari abunda na koya ya tafi a banza ba sai ga shi nice ta Biyu Fa'iza sidi karofi Hawaye sharr suka zubomin na kasa sharesu bakina har kunne na fita. Kudin a Farar takarda ne an nade sannan ga sunan kungiyar ajiki Hajiyar su Raliya ta bani na Duka har kasa zan karba sai kawai na Daidaici gabas duk da goyon Ahmad dake bayana ban damu ba nayi Sudujul Shukur sai Hall din ya Dau Tafi da kabbara ina dagowa ina hawaye Shabe shabe na saka hannuwa bibbiyu na karb'a sai ta bani abun mgana tace nayi godiya,muryata ta shake ga kuka sannan ga yanayina cikin mganata nace"Alhandulillah ya Allah Godiyar ta sace.Domin abu mai kyau ko akasasin sa daga gare sa ne,Ina godiya ga wannan kungiyar na gode..Madallah da mutanen kirki, madallah da mutanen kwarai masu karamci.
Nagode Allah ya jibanci lamuran ku, kamar yadda kuka jibanci namu Allah ya suturtaku kamar yadda kuka suturtamu Allah ya albarkaci dukiyar ku da ya'yan ku da iyalan ku gabadaya, Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login