Showing 69001 words to 72000 words out of 107151 words

Chapter 24 - KANA NAKA completed hausa novel

01 Oct 2025

35

tayi shukeshuke har da su Zogale yanzu na fahimci mutane sune Rahma ina shiga makota na bayan kwana Biyu mu gaisa nima Sa'adatu da Habiba sukan lekoni Lokaci bayan Lokaci sai hakan yake min Dad'i ko da ba na ganin wani nawa a kusa dani Su din da nake gani sai suka Debemin kaso mai yawa na kewar da nayi shekaru yana Damuna.
Sai da su Amir suka tafi naji gidan yayi min shuru Kuka sosai Ahmad ya yi da yaga yan'uwan zasu tafi sai da na Shige da shi daki sannan suka samu Tafiya,Dakyar na samu yayi barci ballatana daman Ahmad akwai rigima irin goyon da nayi Anum ne itama akwai Rigima kuma har yanzu bata Daina ba tana tabawa wani Lokacin don ma ina had'a mata da Nasiha sai take rage rigiman wani Lokacin.
Sunan zai kama ranar jumma'a da Safe misalin karfe goma na Safe na gama wankin kayan yara kenan ina Daki ina shirya Ahmad da nayi mai wanka,kwata kwata ban ji sallama ba Saboda lalurata sai da naji Mganar ta kamar daga kofar Dakin da nake ciki,Ina juyowa muka hada ido Hudu da Yaya asiya Sabe da Jaririnta da karamar jakar matafiya a Hannunta.
Na saki baki fararan hakora na suka bayyana cikin yanayina da murnar da ta cikani nace"Yaya Asiya.."
Dariya tayi Lokaci daya tana karisa shigowa Dakin tana fadin"Na'am Yar Fa'i"Daman ta kan kirani da hakan in tana so ta zolaye ni..
Sai nayi Dariya,na bar Ahmad kan gado bayan na gama sakamai kaya na karbi jakar hannunta na sauke a gefe sannan na karbi Muhammad Auwal dake hannunta ita kuma ta Dauki Ahmad ta daga shi sama tana fadin"Kai Ahmadu naga ka kara girma ne daga ganinka Yaya Ishaq ka Dauko Tsawon kafa zaka yi"
Dukkanmu gefen gadon muka zauna na kamkame Muhammad Auwal da ya zama Lukuti da shi Dagani yana samun kulawa da kuma Nono mai kyau.
Cikin nuna farincikina na shiga gaisheta ta amsa itama cikin Fara'a kafin tace"Nace ni dai bari nazo na gani ko Fa'ina na lafiya ko bata san na Haihu ba ne? shuru baki ba wayarki sannan ina ta kiran ki a kashe kwata kwata bana samun ki kin gani Karofi zani nace bari na fara sauka naga Lafiyarki"
Tana fad'a tana karemin kallo Lokaci daya da nazarina sai na sunkuyar da kaina ina wasa da showel din dake jikin Muhammad Auwal,Naji kunya sosai shi yasa na kasa mgana na kuma san ko zan mutu Ya Ishaq bazai barni naje kano ba ko da ma nasan Haihuwarta ballatana ban sani ba sai zuwan da su Goggo suka yi,bayan sun baro kano alokacin.
Ganin na ki mgana yasa ta kyaleni ta Fahimci abun sai bata matsa min ba,Cikin Nazarin Dakin tace"Naji gidan shuru su Amir suna makaranta kenan..?
Kai tsaye nace mata"Suna chan wajen Babansu jiya mama ta aiko Badariya ta tafi da su baban su yace a taho da su"
Yaya Asiya tace"An yi haka jiya naje gida na iske su Hajiya nata shiri ni ban ma sani ba sai ajiyan ake cemin Amaryan Yaya Ishaq ne ta haihu aiki akayi mata gobe taron suna..har ma ake fadin Ishaq din ya yi ma mahaifin ita zainab din kara sunan babanta ya saka Lawal ammh zasu rika kiransa Farhan"
Kai tsaye nace"Allah ya raya sa"
Ta amsa da Ameen tana fadin"Ke ba'a je da ke ba kenan..?
Sai da na dago na kalleta sannan nace"eh bai ce a zo da ni ba"
Ta gyada kai tana fadin"Bakomai bayan an kwana biyu sai kije ki yi mata barka in kuma tazo shikenan"
Ban amsa mata ba na daga Auwal a Hannuna ina Fadin"Kai Yaya Asiya naga ya girma ne kun yi wata uku ne..?
Dariya tayi kafin tace"Watan sa biyu ne fa da kwanaki yana da girman jiki ne irin Goyon Husain ne zan yi"
Na mike ina Sab'asa a baya na kafin nace"Eh ai suna ma kama da Husain din"
Tace"haka kowa ke cewa"
Tsab na goyesa a bayana na Saka zani ya lafe Ahmad kuma daman da yaji Ruwan zafi sai barci kan gado Yaya Asiya ta kwantar da shi muka fito Falo muna Hira ni dai ina ta Fargaba kada ta sako mganar abunda ya faru Tsakanin Ya Ishaq da Yaya mariya sai naji batamin ba.
Ita tayi mana girki Shinkafa da wake da mai da yaji,Ita tazo min da yaji da kori a robobin su tunda Sana'arta kenan na Dauka ina shinshina kamshin Korin cikin jin dad'i nace"Yaya Asiya korin nan nada kamshi nima ina so na iya had'awa ko shi na fara saidawa in za'a siya"
Yaya Asiya tace"Indai za'a siya koyan sa ba shi da walaha Fa'iza..Sai na koya miki ke da ma na sanki da Sauri Dauke abu cikin Lokaci zaki gane komai sai ki rika zuwa kasuwa kina Siyo kayan  had'in kina hadawa da kanki kuma wlh akwai samu in dai kika Samu masu siya sosai"
Tun da naji ta ambaci kasuwa jikina yayi sanyi sanin ko sama da kasa zata Hade Ya ishaq bazai bar ni na rika fita kasuwa ba sai na share zencen ban kara mata mganar ba.
Sai bayan mun yi sallar azahar mun zauna muna cin abinci ta dago tana kallona kafin tace"in na kwana anan Gobe da Safe zan yi sammako na biya ta Dutsemah na gaida Tamadina na kwanan mata Daya daganan na karisa Karofi na sauke gajiya achan sati yace nayi kafin na koma"
Kai na jinjina kafin nace"Tamadina ta na lafiya..?
Kai tsaye tace min"Lafiya ke shuru Fa'iza muna saka ran haka kwanki da ina jego mun yi waya da Megidanta da Abokiyar zamanta sun tabbatar min tana lafiya,ban ce a bata ba ne kinsan ko tayi mgana awaya bazan gane komai shiyasa na bari sai nazo naje na ganta"
Na kasa mgana kunya nake ji ni da nake kusa ammh mahaifiyata na Raye sai ta shekara bata ganni ba Idanuwana suka ciko da kwallah Yaya Asiya ta gani ta kalleni sannan ta Girgizamin kai kafin tace"Kada ki dami Fa'iza nasan yanayin da kike ciki..Ki zauna ki yi ma aure Biyayya In sha Allahu zaki Rabauta ranar gobe kiyama a wajen Ubangiji..Sai dai duk Lokacin da kika samu dama ki rika zuwa kina Dubata bayan mu bata da kowa Fa'iza ita kadaice ta rage mana sauran gatan mu anan duniyan"
Jinjina mai kai nayi ban ce komai ba ina Tunanin to yaushe nake samun Daman. ?Ko karofi sai na jima ban je ba,in kuma naje sai mutuwa ko Biki suna ma ba na kowa ba sai wanda Mama ta amince min naje nake zuwa.
Zuwan Yaya Asiya ya D'ebemin kewa sosai,Sannan na Fahimci ko Rashin Lafiya na bata sani ba sannan ban ji  tamin mganar ba sai nima nayi mata shuru ban gayamata ba.
Da yammah na rakata makota na ta gaida su Sa'adatu da Habiba ina jin Dad'i Lokacin da na nuna ta nace yayata ce itace Babba ad'akin mu Sa'adatu ta kalleta tace"Ba kwa kama Maman Amir"
Dariya nayi ban yi mgana ba Yaya Asiya ce tace"Ai mu mun fi kama da Babanmu..Ita yanzu da ace kin taba ganin Mahaifiyarmu sai ki iya cewa yaya da kanwa ce saboda Tsabar kamar da suke da juna"
Haka ma Habiba tace itama kamar yadda ta fad'ama Sa'adatu haka ta fadamata,Da muka Dawo gida Yaya Asiya tace"Ko kefa Fa'i ki rika shiga Mutane don.Allah..Yafi ki yi ta zama agida ke kad'ai kamar mayya..Mutane Rahma ne sannan Makoci yafi dan'uwaka tunda sai wani abu ya sameka kafin wani naka yazo ya kawo maka Dauki makocinka yazo ya taimake ka"
Cike da gansuwa da mganarta nace"Hakane"
Domin ya faru akaran kaina kuma nagani,Tare muka kwana agado daya yaran mu na tsakiyar mu mun dad'e bamu yi barci ba Duk Mganar Yaya Asiya na Hakuri ne da kuma hakuri da yadda zamantakewar aure tazo min kafin mu kwanta sai da tace min"Fa'iza gaskiya ya kamata ki fara wata sana'ar ai zama haka bazai haifar miki da komai ba sai takaici Daman mun yi mgana da Mariya zamu tarfa miki jari tunda kina sha'awar Korin ko shi zaki jaraba ki gani ko za'a dace..?
Nayi shuru ban ce mata komai ba sai ta kyaleni sai da Safe bayan mun karya tayi shirin tafiya ta karamin mganar cikin yanayin mganata nace"Yaya Asiya bazai bar ni na rika zuwa kasuwa ba"
Tayi shuru kafin chan tace"Kuma da wannan don wannan..To shikenan  dai zamu tattauna muga wata sana'ar zaki fara wacce bazata kawo miki matsala da mijin ki ba"
Da haka muka rabu da ita har waje na rakata,ina ta mata godiya tazo min da caryfish da yawa,tace na rika miya da shi sannan da Bushasshan kifin da tazo da shi zata kaima Tamadina da su Goggo ta D'ibarmin na karba ina jin hawaye suna kawomin cikin Idanuwana kalli yadda yan'uwana suka zame min garkuwa ammh ahaka su Mama ke min kallo kaskastttaciya mara gata.
Na bata sakon gaisuwa wajen Tamadina tace min insha Allahu zata sanar da ita Sannan nace agaida su Goggo da kowa da kowa ammh na kasa cewa ta gaida min Yaya mariya ina Tsanaanin jin kunyarta sannan ina Tunanin ta Rufamin asiri bata bayyana ma kowa abunda ya faru ba.
Sai naji ta burgeni ta zama yar'uwa mai Rufa ma yar'uwata asiri.

****

Sai Ranar Litini da yammah Jamal ya Dawo min da su Amir,sun zo da kaya niki niki da jakunkuna mai Dauke da Hoton Zainab da Ya ishaq da kyakyawan D'an su kamar balarabe sannan kaladan ma ta Hoton yaron Dauke da sunan Lawal Ishaq kabir karofi(FARHAN)
yaci kayan alfarma kamar asace sa a gudu in ka gansa kamar d'an larabawa,Dole yayi kyau daga uwarsa har ubansa masu kyau ne masha Allah.
Sun taho da kayan fulawa da yawa da Soyayyan Naman kaza,Samosa,Meatpie,Sprilroll,Cake,Da sauran sai lemukan gwangwani jaka shake da kaya Sannan sun taho da Sabbin kaya yan kanti a bakin Amir naji yace Antyn su ta basu sabbin kaya.
Su Anum yan Abuja sai tsallen murna take tana ta bani Labarin abunda ya gudana achan Jamal na zaune kan kujera mai zaman mutum d'aya yana Latsa wayarsa shi haka yake bai cika Hayaniya ba cikin Daga murya ya Dago yana fadin"Anun shut up.."
Da Sauri tayi tsit har tana saka Hannunta a baki ta kama tasan Halinsa baya musu da wasa Musty ya kwace motar wasan da ke Hannun Anum,Domin har da tarkacen kayan wasa suka shigo da su.
Ta mika hannu itama ta kwace sai ya kwabe fuska zai saki kuka da Sauri ta dora Hannu saman bakinta tana fadin"Shiii up.."
Dagani Har Jamal sai da muka yi Dariya Amir kuma mai hankali kayan su da suka watsar a Tsakar Dakin yake tattara zuwa Dakinsu ina kaunar yaron har acikin raina Saboda akwai Boyayyen Dabi'un da ya Dauko nawa.
Jamal na je na kawo ma ruwa ya Dago yana fadin"matar yaya anya ruwan nan zai shiga kuwa..?
Ba waku ne..?
Nayi dariya daman nasan Halinsa kafin nace"Tuwon Masara nake yi miyar Kubewa D'anya zaka ci..?
Da Sauri ya mike yana fadin"Tuwo fa..Am ok."
Na wuce sai da Safe..My childreen Good Night'
Anum da Musty suka bisa da Bye bye uncle ni kuma ina yar Dariya nace ya gaida su mama yace zasu ji,nayi mamakin yadda nake yawan ganinsa a gida lokaci bayan Lokaci,sai washegari da ya shigo anguwan ya kara shigowa na tambayesa ashe yana garin.?sai yace min ya koma makaranta wlh yajin aiki aka shiga shiyasa ya Dawo shekaran jiya.

Nasha Labarai wajen yara musamman ma Anum Amir bai da surutu Musty kuma mganar ba wani kwari tayi ba rabi gwaranci ne,Anum sai fadamin take Umma jaririn Anty mai kyau ne muma yaushe zaki haifo mana Jariri mai kyau..?
Sai na kalleta nayi dariya naja kumatunta kafin nace"In sha Allahu zan haifo muku jariri mai kyau Anum"
Ta Dameni sai faman tambayana takr yaushe da nagaji nace mata watarana sai ta fara murna na kalleta ina jinjina yarinta yara dai basu da matsalan komai a duniya.
Nasan ko kayan da Anum suka Dawo dashi Darajan su Anum naci ba Domin haka ba nasan ko abunda ba'a so ba wanda zai kawomin
Naci kayan fulawan da suka zo da shi kazan dai su na saka ma fridge da safe ina saka musu cikin kwandon abimcinsu in zasu tafi makaranta da Lemuka daman kwanakin baya ruwa nake saka musu pure water da ya kare sai dai na d'ura musu na Famfo a Gorinan na su tunda bana da shi ban kuma da hanyar samu.
Ashe gayya ne guda akayi aka tafi Abuja Badariya taje ita da Halisa Anty Mahma da Anty Binta sai Hajiyar Dala da manyan ya'yanta guda Biyu,duk sai da Badariyan tazo ta ke fadamin.
Ranar da tazo gidana ta kwana Tunda basa zuwa makaranta suna yajin aiki kwananta ta uku mama ta matsa mata sai da ta koma gida ita kuma tana som zama saboda tana koyon girke girke a wajena Ammh Mama bata kaunar wani nata ya rabeni ballatana in tasan nata d'in yana so na ko Fad'an da take yi da Goggo saboda ni ne da ace Goggo bata kaunar mu kamar Yadda Hajiyar Dala ba ruwan ta damu da zaman Lafiya za su yi ammh Saboda ni ta yanke alaqa da Goggo sai wanda ya zama Dolen Dolen an had'a Dangi bata da yadda zatayi.
Ana haka ba Dad'ewa Yara suka yi Hutun makaranta suna gida sai na koma koyar da su na addnini a gida na Bokon kuma ban yi musu wasa ba nakan matsa musu su Dauko Littafansu Amir dake gaba dasu ya Rika Duba musu,nasan zafin rashin Ilimin boko tunda har da shi yasa na zama Bora agidan mijina tunda ko nasan zafin kaskasci bazan so wani daga cikin ya'yana ya Dan'dana abunda nayi shekaru ina Fuskarta ba.
Hutun yaran a gida ya taimakamin sosai na rage damuwa sannan walwalata ta Dawo har na fara maida jikina,sun gama cinye Hutun su suka koma makaranta a satin aka fara musu mganar kudin makaranta da Sabbin Littafai Anun kuma jakar makarantar ta mutu tana bukatar Chanji,sannan sabon Registration ne zata shiga primary 1 da suka fad'amin nace su bari in Uncle Jamal yazo su fad'amai Saboda ni bani da mafita.
Shi kuma kamar yasan ana jiransa sai ya Dauke kafa agidan ni dai fatana da addu'a ta kada su koresu daga makarantar karatun su ya tsaya,Ranar jumma'a sukace duk wanda bai biya ba kada ya zo ina jin haka sai na sakama kaina gwarin gwiwa na Fahimci an kawo gabar da ni ce uwar ya'yana kuma nice Ubansu Ranar Monday nace su shirya tare zamu je makarantar suna ta Murna,na yi wanka na saka kaya na mai kyau da Hijabi na shirya Ahmad na kulle gida nabi Haruna muka je makarantar ban taba zuwa ba Ya Ishaq ke zuwa ko Jamal in wani abu ya taso.
Yaran suka rakani har Office din mai makarantar Mace ce ina ta Fargaban ance da Turanci ake mgana ni kuma ban iya ba,Muna shiga Matar ta Dago fara kyakyawan gaske,na samu karfin gwiwa jin ta min mgana da Hausa ganina da su Amir yasa tace"Umman su ce ko..?
Na gyada mata kai ina mirmishi sai tace na zauna su kuma ta kada su aji suka tafi suna lekena.
Bayan mun gaisa cikin yanayin mganata nayi mata bayanin komai nace su yi hakuri babansu baya nan ne ammh in ya Dawo zai biya.
Sai tace bakomai tasan ba su da matsala da yaranmu nan tace zasu yi ma Anum Rigistration su bata Uniform din Primary section sai su had'a cikin Bill din kudin makaranta nace ba Damuwa muka rabu cikin mutumci a raina nace ashe ba ko'ina ne ake mgana da Turanci ba in ko Hakane nima zan iya shiga ko'ina da yarena na Hausa kuma nayi mgana a Fahimceni.
Haruna ya tafi bakin sana'arsa abun hawa na hau zuwa gida,Daman shi kudin da goggo ta bani da na wajen Yaya Isa na had'a na bashi na wata daya yanzu yana bin na wajen wata uku zuwa Hudu shuru Ya Ishaq bai basa kuma ko zuwansa na karshe bai tsaya ba ya tafi ma ban sani ba ballatana ma ya bani yace na basa ni fa na fara Tunanin tashi Tsaye kawai na nema ma kaina mafita na gama Fahimtar Sabon Iyalin da Ya Ishaq ya Had'a ya zabe su sama da ni da ya'yana ko da yake ai ni ya Dade da Zabar Zainab a kaina ya'yansa ne na Fara Gane ya fara mantawa da matsayin su a wajensu.
Sai a satin da naje makarantar ta su Jamal yazo gidan Anum sarkin karad'i ita ta fadamai an ce su biya kudin makaranta,To kwana biyu tsakani suka zo Da shedar an biya komai Anun an bata sabbin kayan makaranta da Text books,ranar kuma da Daddare shi Jamal din ya kawo musu littafan Rubutu da Sabbin Safuna da takalma ganin ba Jaka sai nake gayamai ta Anum ta lalace yace duka kudin da Ya Ishaq ya Turomai sun kare ammh zai yi ma mama mgana kamar nace ya bar shi ba sai yayi mata ba sai na kasa mai mgana.
Ni nasan za'a rina aiko da yaje yayi mata mgana fad'a ta kama yi tana fadin ina fakewa da ya'ya ina mai da D'anta bawa,ba domin Mama tasan ba'a sauya ma Tuwo suna ba da Tuni ta Hana Yaya Ishaq Dawainiyar ya'yansa to tasan dai ya'ya nasa ne sannan yana son su bazai iya kyalesu ba duk da Yaya Ishaq bashi da Kirki a wajena bazan yi mai karyan baya kula da Laluran ya'yansa ba wani Lokacin har da Muguntan Mama aciki gani take ina Fakewa da Guzuma ina Harbin karkasa.
Jakar da kuma taki bada kud'i a siyan ma Anum kenan Jamal yazo yana fadin da ya ke shi Santsi daya ne baya munafunci kaf abunda Mama ta fad'a ya fadamin sannan ya kara da cewa bai da kudi da ya siya ma Anum din Sabuwar jaka nace kada ya Damu ai na Gode da kokarinsa.
Dakyar na Lallashi Anum ta rika tafiya da Tsohuwar jakarta ni kaina naga duk ta mutu ta yayyage ammh ya na iya..?Tunda ba ni da wata mafitan sai dai ina jiran mafitan da na Roki Allah ya samar min kuma ina ji ajikina ya amsa duka addu'o'i na.

   Yau ta kama alhamis ne tun bayan tafiyar yara makaranta da suka maido wuta na fara guga sallar azahar kadai ya tadani sai rigiman Ahmad na shiga Kitchen na Damamai kuni na basa yasha sai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login