Showing 78001 words to 81000 words out of 107151 words

Chapter 27 - KANA NAKA completed hausa novel

01 Oct 2025

33

yau din dai basu samu zuwa ba ne"
Shuru tayi kafin ta kalli su Anum lokaci d'aya tana fadin"Anum ko ba lafiya ne yau ban ji Surutun ki ba..?
Kawai sai yarinyar nan ta saka kuka cikin kukan take fadin"Yunwa muke ji tun jiya bamu ci abinci ba"
Musty ma sai ya fara kuka wai shima Yunwa Ahmad na jin su shima ya saka Rigima na saki baki kawai ina kallonsu na kasa mgana ta Dago tana kallo na kafin tace"Haba Maman Amir sai ki bar yara da yunwa in suka samu wata matsalar Dalilin haka fa..?
Sai na kasa mgana Hawaye suka cika kwarmin idona cikin wani yanayi nace"To ya zan yi Sa'adatu..?
Bani da wata mafita sai wacce ubangiji ya kawo min kawai"
Cikin mamaki tace"In shi babansu baya gari ba ga gidan iyayansa ba,bai kamata suna garin nan kuna zama cikin wannan halin ba ai yunwa bala'i ce musamman ma ga yaran nan"
Mirmishin takaici nayi mata ban kara mgana ba da Sauri ta mike ta fita ba jimawa sai ga shi ta Dawo da kuni da yawa abotiki da Soyayyan Dankalin Hausa ta Diremin tana fadin"In ke kin Daure ai su baza su iya daurewa ba saboda yara ne..Zaman taren kenan da ko Amir kika aikomin da nasan abunda zan yi"
Ni dai ban ce komai ba sai godiya nake yi mata nan da nan na tashi na shiga Kitchen na Dauko Kofuna na zo na Zuzzuba musu na saka ma kowa Dankalin,ita tafiya tayi ta barmu bayan ta kawo mana,Sai gashi mun ta  da shi duka Lalle gaskiyan almajiri da yace yunwa bata da Hankali na yarda sai da muka koshi na samu karfin jiki,Amir shi ya taimaka min ya gyara Dakin su ya kwashe kayan da suka zubar a kasa ni kuma na gyara Sauran d'akunan nayi ma Anum da Musty da Ahmad wanka Amir ma na cudamai baya sai bayan sun shirya naje nayi wanke wanke tun jiya ban samu yi ba nima kaina ba ni da karfin jiki.
Zuwa chan sai ga Sa'adatu da Shinkafa yar Hausa takai tiya Hud'u da Garin tuwo da Tsaki,Da kayan miya har da su maggi da mangyada,Na rasa da bakin da zan yi mata godiya na share kwallar data zubomin Lokaci daya ina fadin" Nagode..Nagode yadda kika ji kaina da ni da ya'yana ke ma Allah ya jikan ki"
Ta amsa min da Ameen Ameen ta jima muna hira sama sama da ita kafin ta tafi wannan kayan abinci su suka taimakemu suka fitar damu daga cikim Halin da muka so fadawa na rashin abinci Maman da ya bar ma sallahun komai namu bata Damu ba ko zamu mutu mun dad'e bamu mutu ba.
Abun da ke bani mamaki in ni bata kaunata ya'yan da har da D'anta aka bada gudummuwar fitowarsu duniya bazata tuna da su ba..?ammh bata Damu ina da yakinin ko rasa su sukayi sai nafi kowa asara ita d'anta yana da matar so sannan da yaron so bazata damu domin yunwa ta illatamu ba.
Ni kuma tundaga Lokacin nayi alkwarin ko zamu mutu bazan kara tambayanta wani abu daya Danganceni ni da ya'yana ba in suka Sauke Nauyin dake kansu ruwan su in basu sauke ba bazan matsa musu ba, duk wanda yayi nagari don kansa sannan Hakki ne ranar gobe kiyama sai Allah ya tambayesu domin ai ya'ya abun kiyo ne ga wanda aka bamawa,kuma za'a tambayi kowa yadda ya kiwata nashi.
Haka na dinga ririta kayan abincin nan Saboda in suka kare mu ne a ruwa bamu  kuma da wata mafita sai dai su kofofin ubangiji ba su da iyaka in ya kulle maka wata kofar kafin wani Lokaci sai ya sake bude maka wata Sabuwar kofar.
Dama bana ganin kowa kuma hakan bai dameni ba jamal ma ya jima bai leko ba ashe sun janye yajin aiki an koma makarantu,Nima ban sani ba ni ba Tibi ba Radio ba, ina nan dai Dim d'in sai abunda akazo aka fad'amin yaran ma tun suna damuwa da kallon har ya fita ransu na rika na cusa musu karatu acikin ransu shiyasa lokacin wasan su kad'an ne lokutan karatun su yafi yawa.
Badariya ce da tazo ita da abokiyar karatunta Raliya sun taba zuwa sau biyu da ita,ita take fadamin sun koma makaranta cikin Satin nan sannan  Jamal kuma Yamai sukaje shi da Mama sai shekaranjiya suka dawo jiya kuma ya koma makaranta,Sun iske na yi Tuwom masara miyar kubewa Bushasshiya Da yaji caryfish,sai tayi Dad'i sosai Badariya tace na zubo musu na kawo musu suka zauna akasan Cafet ita da kawarta ta suna ci suna Fira ni kuma ina gefen su Ahmad na jikina ya lafe.
Kawar Badariyan ne ta Dago tana kallo na kafin tace"Gaskiya Anty Fa'iza kin iya girki sosai kiji kamar ka tsinke Hannu"
Mirmishi nayi kawai ban yi mgana ba Badariya tace"ai in dai bangaran girki ne in kika zo wajen Anty Fa'iza ki yi Salute kawai Raly."
Raliya tace"Naga alama irin su ne watarana sai ki gansu da Babban Wajen cin abinci"
Badariya tace"Allah ya amsa bakin ki ai zata iya ta iya girke girken kala kala na zamani da na gargajiya"
Raliya tace"Nasani ai wanchan zuwan Danwake mukaci da salad haka na koma gida ina ma su Hajiyarmu Zencen suka yi tamin Dariya suna fadin Duk Santi ne"
Badariya ta kwashe da dariya kafin tace"basu karya ba santin ne"
Atare suka yi dariya kafin su cigaba da cin abincin su sai chan Raliyan tace"Badar wai ina matar bro din ki da Lokacin ina Kaduna kikace an yi bikin?ko ba anan gidan take zaune ba..?
Badariya tace"Tana Abuja tare da Yaya Ishaq ai yar chan ce ya aura har ta Haihu ma namiji Lawal suna kiransa Farhan"
Kai ta jinjina kafin tace Allah ya raya sai da suka gama cin abincin Badariya ta kwaahe komai ta kai kichen,tazo ta sharemin Falon ina ta barshi bata ji ni ba,Wayoyin su suka dauka suna ta Latsawa suna Hira jefi jefi ni kuma ganin Ahmad yayi barci na mike da niyyar naje na shimfidar da shi sai naji Raliya na fadin"Ke Badar na  manta ban fada miki ba, kinsan Hajiyar mu tana shiga kungiyoyin tallafa ma mata da marayu ko..?
Badariya ta daga mata kai batare da tayi mgana ba ita kuma sai ta cigaba da fadin"To akwai wata kungiyar Womens Charity Faundation kungiyace ta manyan mata da suke tallafama mata da marayu domin su Dogara da kansu suna koyar da Training din sana'o'i da Dadama sannan in sun gama,suna ware kamar Mutane ashirin Hazikan ciki su tallafa musu da jari kyauta"
Kasa kunnina nayi tun da naji mganar tallafama mata sai na koma na zauna inaji Badariya na fadin"Ni kuma meyasa duk kike fadamin wannan..?
Raliya tace"Banza baki cin Ribam zencen..duk shekara suna zaban State din mu na arewa su zo su koyar da sana'o'in da kuma bada tallafin wannan shekarar katsinan mu ne har anbuga Form din Hajiyarmu guda Goma aka kawo mata shine nace bari nayi miki mgana ko zaki yi sai mu cike mu yi tare Allah Foudation di'n suna koyar da abubuwa masu kyau matuka komai da kika sani ko banza muma zamu karu"
Badariya tace"Da karatun zamu ji ko da Koyan sana'a?
Raliya tayi dariya kafin tace"Haka Hajiya tace da nace ta bani Form guda Biyu ni dake sai tace mu ji da karatun ma tukunnah yadda muke da son jikin nan ba abunda zamu iya koya"
Badariya tace"Allah ya saka ma Hajiya da Alheri"
Suka yi dariya a tare ban shirya ba kawai naji bakina ya furta"Zan yi..Badariya zan yi dom Allah"
Gabadaya suka Dago suna kallona Badariya ta kalli Raliya itama ta kalleta suka kuma dawo da kallon su kaina cikin Sauri nace"In ba damuwa ni ina so zan yi"
Raliya tace"Da gaske Anty Fa'iza..?
Ciki  jin dadi kamar an ce ma an Daukeni nace"In sha Allahu.
Badariya tace"To ke kin ji Raly maza ki samo ma Matar bro di'na Form dim ta cike kuma ki fad'ama Hajiya"
Raliya tace"In sha Allahu kuwa ai tashi zaki yi muje gidan tare ki mata bayani mu karb'o tare kada tace shiririta na ne"
Da Sauri ko Badariya ta mike tana Fadin"Yauwa muje..Anty Fa"iza bari muje gidan su Raly din na yi mgana da Hajiya insha Allahu zaki samu"
Kai na gyada musu ina ma Raliya godiya tace"Bakomai Anty Fa"iza ni dai don Allah ki dauki bangaran girke girke yadda zaki kara zama top a harkan sai mu bud'e gidan abinci watarana"
Sai ta bani dariya ammh a raina na amsa da Ameen haka suka fita suia barni kamar an sakani a aljannah haka kurum nake jin farinciki acikin raina na fara Hango mafitar da na Dade ina rokon Allah akanta,sai dai jikina yayi sanyi ganin har kwana biyu Badariya bata dawo ba ballatana naji yadda suka yi,Sai da Satin ya shige wani ya shigo sannan tazo da Form din tana fadin ba kowa a gida ne shiyasa najita shuru cikin mamaki nace"Ina mama taje..?
Badariya tace"Abuja suka je ita da Anty Binta"
Na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Me ya faru..?
Badariya ta tabe baki kafin tace"Farhan ne ba lafiya mura yake ta fama dashi har ta na hanashi Numfashi sai da aka kwantar dashi a asibiti Ya Ishaq duk ya Rud'e ya Rudar da su Mama sai da sukaje suka gansa Hankalinsu ya kwanta"
Cikin jimami nace"Wayyo ya jikin nasa..?
Cikin basar da zencen tace"Yaji sauki sun koma gida ammh naji su mama na fadin baban zainab din yace zasu fita da shi kasar waje a kara Duba Lafiyarsa Nimonia ce ke damunsa"
Na nuna jimami na sosai ina ta addu'an Allah ya basa lafiya Badariya ta fito da Jakarta ta Dauko Farar Takarda Doguwa tana fadin"Kin ji Anty Fa'iza matso mu cike wannan Form"
Cikin Farinciki nace"ashe kin karbo min?
Badariya tace"Eh ai tun ranar mukaje nayi ma Hajiya bayani bata da matsala tana jin ma matar Yayana ce tace bakomai basai mun biya kudin Form d'in  ba tace ki cike a maida mata in sha Allahu zata sanar in Lokacin Traning din yayi ammh akwai pasport guda uku kina da shi..?
Na kalleta saboda ban gane me take nufi ba da Sauri tace"Hoto karami nake mgana wanda za'a lika acikin Form din sauran kuma za'a kai musu"
Ta fada tana nuna min inda za'a saka Hoton sai na gane nace mata bani da shi sai tace"Bakomai in mun gama zan Dauke ki Hoto a wayata in na fita sai na Biya shagon Hoto a Wanke min a maida shi karami yau nake so naje na kai ma Hajiyar, Mama ma karya nayi mata da zan yi subbmitting wani aiki a makaranta"
Kusa da ita na matsa ta sauka kasa saboda yadda zataji dadin Rubutu ta dago tana fadin"da Farko a jikin Form d'in sunanki ake tambaya"
Kai tsaye nace"Fa'iza Sidi karofi"
Ina kallo ta Rubuta sannan tace shekaru na gayamata sai kuma ina da aure..?ta saka eh ya'yana na wa..?
Ta saka,sannan yaushe Mahaifina ya rasu na ce ta saka shekaru goma sha da Rasuwarsa ta saka,sai ina da Mahaifiya..?
Nace ta saka eh,Sai ina da Sana'a ?in akwai wata sana'a nake yi acikin gida? nace ta saka Babu,Sannan matakin karatuna nace itama ta sani ko Takardan gama primary ai ban da ita Saboda ban gama ba sai Badariya ta saka matakin karatu na addini Saukakkiya a Qur'ani da Sauran Littafai.
Na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Kada su k'i daukata Badariya kila sun fi son masu takardan ko Sakandiri ne ko Hafsatu zan bar mawa..?
Badariya tace"Zasu Dauke ki in sha Allahu ai ba da Takarda zasu amfani ba, da Kwarewa ce ke kuma ai bana jin ki ta wannan bangaran"
Ni dai duk sai naji jikina yayi sanyi ta cigaba da karantomin ko'ina tana Fassaramim yadda zan gane tace ance in da wata matsala ta fanni hallita ko wani ciwo..?
Nace ta saka ina da matsalan ji,ta saka Hearing problem,Sai adireshin gida nace ta saka na gidan yayanta
Daga karshe sai jerin abubuwan da zasu koyar akwai girken girken zamani da na gargajiya nace ta cike min shi saboda na kara kwarewa, sai Gyaran jiki dilka da Halawa nace shima ta Cikemin,sai kuma koyan yadda ake had'a lemuka kala kala nace shima ta cikemin akwai koyar da Kunshi Fulawa,koyar da manshafawa da su sabulan wanka da na kamahi sai koyar da su yaji kori da kayan kamshin Girki sai koyar da Turaran kamshi na Itace da kwallacha
suma nace ta cikemin duk zan koya Badariya na Dariya tace"Anty Fa"iza duk ke kad'ai an ya zaki iya..?.
Ina da yakini acikin raina nace"In sha Allahu ai basu da wahalan dauk'a zan iya da amincewar Allah"
Ta amsa min da in Allah ya yarda sannan daga karshe akace in mutum nason a bashi tallafi yace eh ta sakamin eh sannan da kuma abunda zakayi da tallafin in an baka
Na kalli Badariya ina fadin"Kice ina son a bani tallafi nan saboda na kama sana'a daga cikin sana'o'in da suka koyar damu..Sannan saboda na rike kaina na kuma tallafama rayuwar ya'yana saboda inganta goben su watarana"
Haka kuma ta rubuta sai lambar waya nace ta saka min nata tunda ni bani da waya sai ko ta saka lambar wayarta.
Daga karshen karshen sai saka hannuna ta bani na jagwalgwala hakanan,Kafin ta tafi sai da ta D'auki Hotona  a wayarta bayan na saka Hijabi tace zataje a fito mata dashi a gyara muka yi sallama zuciyata ta cika da murna ammh ban daina saka Allah cikin lamarina ba adaran nayi salla sannan nayi addu'an  Allah yasa mafitan nan ta zame min mafitan alheri a rayuwata gabad'aya.
Ni dai ina ta addu'a ko da naji shuru ban damu ba daman nace in mafitan ta alheri ne Allah ya tabbatar min in kuma ba alheri aciki Allah ya kawo min wata mafitar ta alheri Ameen.
Kafin kayan abincin da Sa'adatu ta kawo mana ya kare ta kawo min Dankali hausa da yawa tace itama daga gida aka aiko mata dashi,Babansu ne ya noma na karb'a na saka albarka shi nakan soya ma yara da Safe su tafi makaranta,Wata rana ma har da rana ina soya mana muci mu sha ruwa,kuma dayake na koyama yarana cin komai duk abunda suka samu zasu ci basa zabar abinci shiyasa sai rayuwar tazo min da Sauki.
An yi wata da cike Form din da mukayi ni da Badariya tazo sau d'aya mukayi mgana tace Raliya tace an Tura Tarkadun namu chan kaduna inda Babbar Jibiyar kungiyar take da su zabi wad'anda zasu dauka za'a turo ma kowa ta sakon waya da lambar da ya saka Badariya ta tabbatar min da Hajiyar su Raliya tace ba matsala sai na saka raina asalama araina nace bakin Da Allah ya tsaga bazai taba hanasa abinci ba.
Ana haka kwatsam sai ga Ya Ishaq ya Dawo ranar wata asabar da azahar Lokacin bana gida na shiga wajen sa'adatu  muna hira to yara in sun tafi makaranta sai ni kadai kamar mayya na da zauna tunani ya kasheni sai nake shiga muna hira tana Debemin kewa rashin dangina akusa dani.
Get din a bude na barsa saboda ban yi nisa ba yagaji da Hon ya fita ya Bude ma kansa ya shigar da Motarsa sai da ya shiga gidan ya tabbatar da ba na gidan mamaki ya kamasa ya D'aga waya ya Kira Mama ko nazo Mama tace tafi wata biyu ban zo inda take ba.
Ransa ya baci nan da nan ya fara Tunanin haka nake fita ina barin masa gida a bude ina tafiyata gantalin da baisan yaushe na iya ba,Ni kuma ban san ya dawo ba sai biyu da rabi na Dawo gida domin yi ma yara girki,sannan nazo da Guzurin Dambun Dankalin da Sa'adatu ta zubamin mafarin zamana ma yau saboda na koya ne ina so nima watarana nayi lokacin da na shigo Haraban gidan naga Motarsa ban ji tsoro ko fargaba ba Allah na Tuba in da sabo ai yaci na saba da Tozarcin sa a gareni.
Kaina Tsaye na shiga cikin gida kamar daman yana jira na ne sai yau ya gwada kiran wayata a kashe duk tsawon Lokacin da ta lalace bai sani ba.
Yana ta Safa da marwa a falon ya kasa zama na shigo bayana goye da Ahmad Hannuna Dauke da kwanon Silba da Sa'adatu ta zubomin dambun aciki.
1do hudu muka had'a dashi Sanda na shigo yana bi na da wani kallo na raini kamar yadda ya saba ni kuwa sai na Dauke kaina ina fadin"Sannu da zuwa.."
Nafada ina nufar Hanyar Kitchen nasan yayi mamakin yadda nayi mai shiyasa ko taku uku ban yi ba yasha gabana cikin bacin rai yana fadin"Ni kika gani kika dauke kai kamar kin ga Dan'iska Fa"iza?
A gajiye na kallesa cikin yanayina nace"Nayi maka sannu da zuwa..ina so na shiga kitchen na sauke abun hanuna ne"
Kallo hannuna nawa ya shiga yi Lokaci daya yana fadin"Miye wannan kuma..?
Sai na Bude masa ina fadin"Dambun Dankalin Hausa ne na shiga ta koyamin ne saboda ina so nima nayi ma yara"
Yamutsa fuska yake yi kamar yaga kashi kafin yace"Wannan bakin abun ne zaki yi ma yarana su ci..?Shiyasa kika bar min gida a bude kika fita yawonki me na sha fada miki..?
Ban ce ban amince ki rika fita ko na  nan da chan ba indai ba gidan Mama ba..?shine kike so ki nuna min kin isa har kina shigowa kina ganina kika Dauke kai kamar kin ga sa'an ki ko..?
Na kallesa da Idanuwana da suka yi ciki ciki ban iya rashin kunya ba Saboda ba Halina ba ne ammh dai naji Tsoro nan nasa da nake ji a baya ya gushe araina na kasa ce mai komai kawai sai na rabasa na wuce kitchen na sauke kayan hannuna a zafafe ya biyo ni yana fadin"Fa'iza ina miki mgana kina wucewa yaushe kika raina ni haka ban sani ba..?
Ko tankasa ban yi na sauke kwanon Hannuna ya shigo Kitchen din yana Fadin"Daga gidan uban wa kike..?rokon abinci kika fara na salon zubar min.."
  Bai karisa mganarsa ba yayi shuru ganin Dankalin hausa zube a kitchen din sannan na bude karamar kular dake saman wajen wanda na soya ma su da Safe ne na rage ma Ahmad in ya tashi daga barci yaci,na dauko na barsa akitchen din yana Dube dube cike da mamaki..
Afalo na zauna akasa na kwanto Ahmad daga bayana da naji motsin tashin sa kamar walkiya sai ga shi a gabana yana fadin"Fa'iza wannan dankalin fa..?sannan naga store ba komai wannan watan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login