Showing 93001 words to 96000 words out of 107151 words

Chapter 32 - KANA NAKA completed hausa novel

01 Oct 2025

31

shirin na koma na cigaba da aikin gabana yace"ki sama min abunda zan ci"
Kamar nace zainab bata aiko maka dashi ba ne..?
Sai na fasa rashin kunya ba Halina ba ne sai na Tashi na shiga kitchen dafamai mai Dankalin Turawa nayi,sai nayi mai miyar kabeji da taji albasa sai na Dafa mai ruwan tea na Dafa mai kwai guda biyu kuma duka na Tattaramai ko abakina domin na koshi Faten jiya na dumama nasha abuna yaran, kuma Farar shinkafa na Dafamusu da Mai da yaji sukaci kafin su tafi makaranta.
Yana zaune afalon na kawo mai ya kalli Filet da jug din da na sanya mai Ruwan zafin kai tsaye yace"Gabad'aya komai naki ya tsufa Fa'iza..Ji kwanukan cin abinci sun fita Hayyacin su mtswww.."
Ya saki tsaki daga karshe ina jinsa ban ce masa komai ba na koma na cigaba da aikin gabana,sai da na gama na kashe komai na kwashe zan koma Daki naji ya daga murya yana fadin"Ki shirya in yara suka dawo makaranta zamu je gidan Mama a gabanta sai ki fad'amata in ni nayi miki iyaka da zuwa gaisheta"
Sai abun ya bani mamaki.matar nan Kwata kwata bata kaunar ganin kwanciyar Hankalina, burinta ta samo hanyar da za'a tozartani, to da ikon Allah kanta zai koma ni dai ina Daraja ta ko ban auri Yaya Ishaq ba. kamar uwa take gareni, tunda ta rikeni bata barni na yi rayuwa a titi ba sannan duk tsananin wuya da Dadi ta killaceni acikin gida rayuwata bata shiga tsaka mai wuya kamar na sauran matan da rashin gata da mafita yasa suka fada harkan banza ba,ballatana ina auran Abunda ta Haifa har abada bazan ki Darajata ba.
D'aya saura na rana yaran suka Dawo shi yaje ya Dauko su da kansa masallaci jumma'a ya tafi da mazan har da Ahmad ni da Anum mukayi tamu a gida,Shinkafa da miya Da salat nayi mana ni da Anum muka fara cin namu kafin su dawo suna Dawowa na zubo mai yaci tare da yaran,Suna ta Murnan tunda na saka musu sabbin kaya nace gidan mama zamu je.
Wajen uku saura na rana muka isa gidan Mama,Mun iske gidan cike Anty Binta,da su Halisa da Anty mahma da ya'yanta kamar ana biki yaran muna zuwa suka had'u da abokan wasa suka tafi suna ta wasan su.
Afalon kowacce tayi shigar alfarma har ta da Mama ko da taga jiya taga yau da na gaishesu dakyar suka amsa min gwara ma Anty mahma Halisa daman ita ta gaisheni har tana min gaisuwa,Ni da Badariya ne muke mgana kasa kasa kan gobe Badariya tace"Kin fad'a ma Yaya ishaq dai ko..?
Na girgizamata kai kafin nace"Ban fada masa ba ammh zan shaida masa yau in mun koma gida"
Badariya ta zaro ido kafin tace"in ya hana ki fa ?nasan Halin Yaya Ishaq barin ma in ya fad'ama Mama wlh bazaata bari ba"
Kai tsaye nace"Wannan karon bazai iya hana ni din ba"
Cikin mamaki take kallona bata samu zarafin mgana mukaji muryan Mama asama tana Sababi sai da na Saurara naji dani take tana cema Yaya Ishaq gatanan ka tambayeta yaushe rabon da kafarta tako gidan nan da sunan gaisheni.?
Anty Binta ta karbe da cewa"Ballatana ni banza abanza mama"
Shi kuma sai ya d'ago daga Danna wayarsa yana kallona Lokaci daya yana fadin"Shiyasa na kawo ta gata gani ta fad'a in ni nayi mata iyaka da gidan nan? Gata nan ni da kaina na yarje mata zuwa Gidajen ku duk sati ta gaisheku ita zaku Tuhuma me ke hanata zuwa"
Mama ta tabe baki tana fadin"Rashin mutumci ne ba wani abu ba.ko yaran nan bata kawo su, nace to in kai ne ma kake so ka raba su da nan gidan basu da inda yafi gidan nan a wajen su ta bangaran ta da take takama wa take dashi ?uwar tasu da ta rage itama Allah ya karbi a binsa sai naga karyan tsiya "
Idunuwana suka ciko da kwallah na kasa mgana zagi da cin mutumci ba wanda Mama batamin ba Anty Binta na tayata sai da Anty Mahma tace"Haba Mama ki barta hakanan mana ba ta baki hakuri ba"
Sai Mama tayi shuru tana Numfarfashi ni dai kaina na kasa ina bata Hakuri Saboda Yaya Ishaq yace na duka na basu hakuri in ba haka ba sai ya sabamin ban ki ba na Duka gwiwa Bibbiyu na basu hakuri dakyar suka Hakura.
Daganan suka yi kamar bana falon suka cigaba da Hiran su sai Badariya tajani Dakinta tana bani Hakuri na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Bakomai duk wanda yayi ma Aure bauta bazai taba tabewa ba..Sannan sakamakon sa na wajen Ubangiji"
Daga haka muka saki mganar mu kama wacce nake ganin zata Fisheni Badariya sai jinjina yadda zan rika zuwa sau biyu arana take yi.nace mata kada ta Damu zan iya ai nace Allah adakin ta nayi la'asar sannan Mama ta aiko wai nazo nayi musu abincin dare haka na kwabe Hijabi na shiga kitchen da Badariya ta shgo zata tayani Mama na ganin haka sai ta kirkiri aikenta sai bayan mangariba ta dawo Lokacin na gama Tuwon shinkafar har na kulle a leda Miya ce bata karisa ba.
Har ta Anty Binta sai da taci tayi guzuri Anty mahma dai da wuri ta koma gidanta mu kuma sai wajen goman Dare tuwon nan ko bakina ban ci ba,su Amir dai sun ci da Babansu duk na Takura na kosa na koma gida.
Kusan Lokaci d'aya muka fito da Anty Binta itama zasu wuce afalon Mama ta kalleni tana fadin"Wai ni kam fa'iza ina kayan ki da Ishaq yake miki ne..?bana ganin ki da su sai tsumma kike sawa"
Gabada'ya suka kalleni harda shi da Mama,Bai dai yi mgana ba sai Mama ce ta tabe baki kafin tace"Daman da Tsumman ta dace.aiko don yan'uwanta su zagesa zata rika mugun shigga alhalin daidai misali yana fita Hakkinta"
Har muka isa gida mganar Mama tamin Tsaye arai bayan wannan kayan Da Anty binta ta bani ko Hijabi Ya Ishaq bai kara dinkamin ba.ammh Mama ta iya bud'e baki ta fadi yana Fita Hakkina, Lalle gaakiyan masu iya mgana da sukace wata shari'ar sai Lahira.
Sai da duk nayi ma yaran shirin barcin daman ko da muka dawo su Anum duk sun fara barci,sannan na Dauki wannan Katin I.d card kenan na nufi bangaran Yaya Ishaq acikin raina ina jin cewa wannan karon bazan iya bin Umarninsa ko ya amince ko bai amince ba wannan karon ba gudu ba kuma ja da baya insha Allahu.
Na shiga na iske baya falo yana cikin Bedroom dinsa ba domin ni nake bukata ba,ba yadda zai sa na bisa ciki Tuni na kiyayewa kusantar inda yaya Ishaq yake saboda Dalilai masu karfi.
Bedroom din na shiga da sallama baya Dakin sai nayi mamakin to yana ina..?
Har na juya zan fita naji karan Bude kofa kii..Sai na juyo muka hada ido shima kallon da yayi min nasan na mamakin ganina ne.
Yana sanye da kayan barci riga da wando, masu taushi Farare na barci,Ya kariso tsakiyar dakin yana fadin"Lafiya..?
Har yana wani gimtse ransa kila yayi tunanin wani abu nazo nema sai yaga na mikamai abun hannuna ya karb'a yana zama gefen gado lokaci daya yana fadin"Wannan kuma na menene.?
Sai dai yayi mamakin ganin Hotona da sunana da dukkan bayanan abubuwana ajikin katin sai ya kara Dagowa yana kallona cikin mamaki ya kara fadin"Fa'iza duk wannan abun na menene..?
Sai na duka a gabansa na gyara zama na Dakyau kafin nace"Kune yan boko ka karanta Dakyau zaka fahimta"
Ya sake karantawa ya Dago cikin mamaki yana fadin"Naga Katin shaida ne na Training din da za'ayi na koyon sana'o'i daga karkashin kungiyar Women charity Foundation."
Shine nace ban gane ba naga hoton ki da sunanki shaidar katin naki ne"
Mirmishi nayi Cikin karfin gwiwa na fara mai bayani da yadda kawar  Badariya da ita kanta suka samo min form din na cike,da kiran mu da akayi wanchan satin mukaje da bayanin komai na karishe mganata da fadin"Gobe zamu fara koyan abubuwa kuma na tsawon sati goma sha Biyu ne,Sannan sau biyu za'a je a rana ni kuma abubuwan da nake so na koya da Safe ake koyar da biyu da yammah biyu kenan kaga a rana sau biyu zan rika zuwa kenan safe da rana"
Har na gama bayanina yana kallona cikin mamakina daya nuna har a saman fuskarsa,Cikin kaushinsa yace"Duk a yaushe kika fara yanke ma kanki hukunci yin wani abu batare da sanina ba Fa'iza?
Nima kai tsaye nace masa"A ranar da ka zabi wata matar sama dani.Nima aranar na zab'i yanke ma kaina da Rayuwata komai batare da na saka ka aciki ba"
Maganata ta girgiza sa ya tsaya kawai yana kallona,ban damu ba sai ma naji kamar gwarin gwiwan. da na shigo da ita ta ninka wacce na samu yanzu tsoro ko fargaba sun fice daga raina kwata kwata.
Hanuna na saka na karbi katina daidai Lokacin da yace"Ni ki ke gayama wannan mganar Fa"iza..?Rashin kunya zaki yi min.?
Kai na girgiza kafin nace"Ko d'aya kada ma ka dauka ahakan Yaya Ishaq ai ko ba aure tsakaninmu kai yaya na ne,kuma babu rashin kunya har Abada tsakani na  dakai.kawai akwai lokacin da in mgana tazo a muhallinta gwara a fad'eta kawai da a barta tayi ta zama a inda ba Muhallinta ba"
Sai ya kasa mgana sai kallona yake yi cikin mamaki nasan aransa mamakin ya akayi na samun bakin yi masa mgana yake yi ni ko araina nace daga yau bakunan fa'iza sun bud'e kenan Har Abada.
Cikin Ajiyar numfashi yace"Naji yanzu meyasa kika fad'amin..?
Na gyara zama na nace"Saboda ya dace ka sani ko ba komai ina gadin gidan ka.
da kuma kula da ya'yanka in fita ta kamani naa jera sati ba ma wata ba, yana da kyau ka sani d'in shiyasa nake shaida maka"
Kai tsayae yace"In kuma nace baza ki fita ko'ina ba na isa ko ban isa ba..?
Ya fada yana kallona cikin ido nima sai na Dago ina kallonsa bansan Lokacin da bakina ya furta"a wannar gabar Isar ka bata isa ba Yaya Ishaq.."
Sai ya zabura yana kallona cikin bacin rai ya nuna da hannu yana fadi"Ni kike cema isa ta bata isa ba Fa'iza"?
Sai ya mike yana Huci Lokaci d'aya yana fadin"Lalle kin fara rai na ni kin manta waye ni a wajen ki kenam? Gantalin da kika farayi na shiga makota yasa kika koyi rashin kunya da rashin Tarbiya ko..?
Sai nima na mike kai tsaye nace"Na fada maka kada kawo mganar rashin kunya a wannan muhallin saboda kai kanka kasan ba Halina ba ne yanzu ta kamane kasan wasu abubuwa.."
Cikin Hargagi ya katse ni bayan ya tasomin yana fad'in"To nace bazaki yi ba in kuma zaki nuna ban isan ba ne bismillah Fa'iza wlh sai na nuna miki Oder side of me da baki taba gani ba"
Ban bari ya sauke mganarsa ba nace"A matsayin ka na waye kake fad'in bazan yi ba..?
Yadda nayi mganar ta basa mamaki sai ya tsaya yana kallona Lokaci d'aya yana nuna kansa cikin mamaki yace"Ni ki ke fad'ama wannan mganar..?
Kai tsaye nace"Eh tambayar ka nayi a matsayinka na waye..?
Mirmishin gefen baki yayi kafin yace"Ina da matsayin yaya gareki sannan kada ki manta ni mijinki ne"
Nima mirmishin takaicin nayi kafin nace"Mijin jingina..?ko yayan da baisan Hakkin kanwarsa a kansa ba..?
Nace mijin Jingina Yaya Ishaq ka ke kira Miji..?
Mgana takara  girgizasa ban bari ya fita daga Girgizan ba na Dora da Fadin"a shari'an ce kai ba mijina ba ne yanzu.Saboda ka zabi wata matar sama dani,ka jingine aure na shekaru biyu kenan,ni matsayina kawai ina kula da ya'yan ka ne sannan in amtsayin Yaya kake mgana baka da wannan Hurumin saboda sai yaya ya zama nagarttace nagartansa zai yi yab'o har ta yab'anyan, da k'anwa bazata iya zarta da wani abu batare da yardan sa ba,Duka baka cike kowani Gurbi ba shiyasa nace isar taka bata isa wannan karon a wajena ba"
Baya ya juyamin ya kasa juyowa ya kalleni, ban damu ba sai nayi kokarin Dauke Hawayen da suka kawo idanuwana na cigaba da fadin"Tun Lokacin da ka zabi iyalan Zainab sama da ni da ya'yana.isar ka ta zama bata isa akaina ba, sannan tun alokacin na Zab'i ya'yana sama da kai,kuma tun lokacin da ka zabi Dangin zainab Sama da Dangina nima na zabi Dangina sama da naka dangin, ban ce Dole sai ka amince ba ina fad'a maka ne Dole zan fita na nema ma kaina mafita Kuma Dolenka, ka kare mganar hakan daga bakin kowa in kana gudun fallasar Jinginannen auran mu zuwa kunnuwan da bazaka so hakan ba"
Shuru yayi ya kasa juyowa ni kuma da nagama mgana sai kawai na kama Hanyar fita cikin Shakewar murya yace"ya'yana fa wazai kula da su.?
Na juyo muna kallon juna ido cikin ido kafin nace"Nima ai ya'yana ne..Ni nake kula da su Lokacin da ka zab'i zainab da ahalinta sama da su.ai a yanzu ba'a wulakance ka gansu ba, nayi alkawarin zan kula da su domin nan duniya nice gatan su nima sune karfin gwiwata da dalilan da yasa nake zaune cikin kaskantataciyar rayuwa"
Ina gama fadin haka na bude kofa na fice har nakai dakina hawaye ne ke kwaranyomin sai na zauna agefen gado na rumgume abun hannuna a saman kirjina,na fashe da kuka,a hankali a hankali kuma ina samun salama da Sauki acikin zuciya ta.
Sama na kallah nace a fili"Allah kana ji kuma ka na gani.
Ya Allah ka sama min Mafita, mafita mai amfani a rayuwata da ya'yana. ka hananin jin kunyar duniya ka bani dukkan karfi da juriyan daukan duka Jarabawowinka."


*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..



*Janafty**KANA NAKA..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Fatan alheri,ga mutane masu kirki da karamci.*

*Aisha muhammad alto(Sisinah)Sannu barka da arziki kin yi kokari da kika Haifa min D'a,Allah ya raya mana Baby boy.*
*Fatan alheri zuwa ga Khadija Salisu yusuf(Ummina)*
*Halima yusuf gwarzo(Besty) ina miki fatan alheri*
*Nana Halima(Masoyiya)ina gaishe ki Fa'iza tace na fada miki,tana kaunarki kamar yadda kike kaunarta.*
*Ina gaida Uwar biyu Mrbb,Allah ya raba lafiya*
*Sannu gwana uwar Dakin gwanaye,Feedhom nace Allah ya sa afi haka.*
*An gaida Uwar Muwaddata da Anum Ramlat Abdurrahaman Manga,Maidambu,ina godiya Allah ya saka da alheri*
*Ina miki Fatan alheri Uwar Farha Fatima miss flower(Rabin raina).*
*Sannu Amina minajo na,Fa'iza na gaida Masoyiyar asali.*
*Sannu Anty maryam,Fa'iza tace nayi miki godiya,da shawarwarki ta fara sanin cewa itama Yar Adam ce.*


*Madallah da mutane masu karamcin irin ku,Nagode sosai Allah ya bar zumunci,ya kuma had'amu a aljannah*



           *🅿️19*

Saboda Zumud'i ko fargaba zan ce, sai wajen uku saura na dare na iya samun, barci kuma cikin ikon Allah Kasala da nauyin jiki sun kasa barina na tashi na dauro alwala.
nayi salollin Nafila sai dai ina daga kwancen ban daina Hailala da ambaton Allah akan dukkan lamurana ba.
Washegari kamar yadda na saba tashi da wuri haka na tashi, na shirya yara na sama musu abun kari. sukaci sakamakon sun saba tafiya ba abinci,yau din ma haka suka tafi sai dai kamar yadda na sabar musu sai sunci sun koshi suke tafiya yadda kafin yunwa ta jigatasu, lokacin sun dawo gida sai na ba ma kowannen su Goran ruwan faro guda d'aya sun tafi da shi koda bukatar shan ruwan ya taso musu.
Suna tafiya nima ban zauna ba, na fara shiri falo kawai na gyara Dakin yara kuma nace sai na dawo nayi wankana na shirya kaina shima Ahmad na shiryasa bayan na Dama mai kokon sa. na duramai a wani karamin jug,Sauri sauri nake yin komai kada farkon fari kuma nayi latti na samu Tsoffin littafan su Amir da suka gama amfani da shi na Dauka da pencil saboda rubutu duk da ban iya Turanci ba, kuma ban iya Hausa ba, ai na iya rubutu da ajami kuma ina iya karantawa shiyasa ban damu ba.
na tabbatar ma kaina duk abunda na Rubuta zan iya ganesa.
Na hada da katin  shaidana na goya Ahmad a baya na daukan mai wasu kayan. ko da ya bata na jikinsa na fito Falo Tara saura,naci karo da Yaya Ishaq a falon yana waya kallo d'aya nayi mai ban kara ba,shi kuma ganin kamar tafiya zan yi yasa ya katse wayar Hannunsa,ta gabansa na gifta cikin yanayin mganata nace"Ina kwana.."
Ina fad'in haka na kama hanya zan fice sai ya mike jiya ya kwana yana mamakina sai da yaga abunda nayi yau sannan ya amince da gaske nake yi,sai ya saka baki ya kirani da karfi na Dakata na juyo ina kallonsa kai tsaye yace"Ina kike shirin zuwa..?
Ni kuma sai naga kamar yana batamin Lokaci sai na juya ina fadin"In da na fad'a maka jiya..Ina Sauri ne kada na makara"
Na fada ina jimke dubu d'ayan da na Dauko cikin kayana sun sha ajiya tun Kudin da Yaya Isa ya bani ne Lokacin da ya maidoni gida, Dubu buya kad'ai na Taba ukun suna na nan ina Boye da su, sai da hakan ta faru na Daga hannu nagodema Allah domin zasu yi min amfani.
Kawai sai naga ya sha gabana a matukar fusace cikin d'aga murya yace"Ni kike nuna ma ban isa dake ba Fa'iza..?
Baya naja ina fadin"Ban ce baka isa ba.Sai dai na nuna maka isar taka ce wannan karon, bazata isa a wajena ba ka bani hanya na wuce ina bata Lokacina"
Sai ya tare hanyar ni kuma sai na kasa wucewa cikin Daka tsawa yace"Ki koma nace ba inda zaki je"
Sai nayi wani kayattacen mirmishi takaici na Fahimci in na zauna haka Ishaq zai cigaba da Nakasa rayuwata kamar yadda ya saba to wannan karon ya makaro domin d'an zaki ya riga ya girma.
Sai kawai na kallesa ido cikin ido kafin nace"Sai dai kayi hakuri wannan karon bazan ji mganarka ba.Na fada maka tun Ranar da ka zabi Zainab da Ahalinta sama da ni..Nima Daga wannan ranar na zab'i Rayuwata da ya'yana sama da kai"
Mganganuna sun dake sa sai ya kasa motsi har na raba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login