Showing 54001 words to 57000 words out of 108527 words
gskia da bakinta ko Dan zallar qaunarta gareta.
Wasu hawayen ne suka Kuma tsayayo Mata ta rintse ido zuciyarta na radadin Abinda zata fada ahankali tace"
Anty zarah ki gafarceni na zamo babbar butulu me mayarda alkhairi da cin Amana,
Na cutatar dake ta hanyar wahala akan Abinda Kika saka Rai da burika akansa,
Na hanaki bacci da sukuni gurin dawainiya Dani akan qarya yaudara...
Anty zarah banida ciki ajikina,
Bantaba daukar cikiba,
Bantaba sanin namijiba bare nayi Abinda zaisa nasamu ciki,
Dr khalil ba Mijina bane.........
Sakinta anty zarah din tayi cikin tsananin firgici da mamaki tayi baya tana zaman 'yan bori idanuwanta na silalo hawayen tsoro da karyewar zuciya ta Fara girgiza Kai tana son yin Magana takasa sai hawaye....
Anty zarah bantaba sanin a duniya akwai masu irin tsarkakakkiyar zuciya irin tasu kawu ba sai Dana hadu da Dr khalil dake da salman kuka kawo wani irin farin ciki da sanin mutuncin Kai arayuwata Amma Babu Abinda nakawo Muku sai yaudara da damuwa.....
Cikin rawar murya anty zarah dake rawar jiki gaba daya cikin firgici tace"
Idan duk Abinda Kika fada hakan ne to meya kawoki cikin rayuwarmu????
KUDI"""""tafada Kai tsaye tana sauke Kai hawayenta na qaruwa..
Son kudi da burin samunsu kota halin Yaya yasani shigowa rayuwarku
Saidai bayan haduwata daku na fahimci samun mutanen dake sonka da son farin cikinka tareda zama acikinsu shine asalin farin ciki da walwala Wanda kudi baya siya maka suba,
Anty zarah girmanki da qaunarki alqawarine da bazai taba gogewa azuciya da rayuwataba,
Anty zarah idan lokaci yayi Zan fada Miki gaskiyar duka Amma ayanzu iya Abinda Zan fada Miki kenan.
Miqewa tayi da sauri ganin irin hawayenda anty zarah din keyi tana bin cikinta da kallo burirrikanta akan cikin suna tarwatsewa daya Bayan daya,
Cikinda akai alqawarin Bata Abinda za'a Haifa Wanda tuni tafara kallon kanta amatsayin uwa Nanda lokacin qanqani.
Buga kofar da akayi da qarfine yasasu kallon kofar tun kafin su motsa aka sanarda saqone Andi nayiwa Amatu Kiran gaggawa.
Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro ta juya ta nufi qofa.
A tsaitsaye suke Babu Wanda yasamu damar motsawa daga Inda yake sbd tashin hankali kusan mintuna suka share ahakan sbd shock dinda su Andi suka Shiga Bayan Gama sanin wacece Amatu dakuma irin qazamtacciyar rayuwar karuwancin datayi qarshe ta qare acikin zuria mafi tsafta da mutunci,
Umme da sauran manyan yaran Andi da Modibbo da tuni aka kirasu suka qaraso Babu wanda ya zauna duk tsaye suke cikin tashin hankali da jimanin abinda zai biyo Andi kawai ake jira yayi Magana.
Dagowa yayi cikin wani irin yanayi na tsanani yayiwa Khalil kallon dayasa kowa sake Shiga firgici cikin amo me firgitarwa yace"
Kowace tambay amsa daya nakeso,
Ka auri wannan yarinyar??
Aa,
Acikin takardan Nan anrubuta cewa
Ita din Mara asali ce,
Yar bola ce,
Karuwa ce,
Barauniya ce,
Gidajen abinci,hotels da gidan rawa take aiki,
Babu police station dinda batayi zamaba har gidan yari
Gaskia ne ko qaryane???????
Cikin tsananin firgici da tashin hankali muryarsa na rawa yace"
Gskia ne Amma Banda.......
Hannu Andi din ya daga Masa fuskarsa na nuna dukkanin fushinsa da bacin ransa.
Take yace kowa ya watse ya sallamesu ya juya yayi ciki 'yayansa na binsa abaya.
Kasa motsi kowa yayi sbd sanin abin bazaiyi kyauba.
Daga ciki kuwa kallon alhaji qarami yayi Kai tsaye yace"
Yarinyar da mariqanta a daukesu a rufe a central station dinda Khalil zaifi shekaru goma Yana nemansu baigansu ba a sanarda commissioner laifin datayi ta yanda zasusan girman laifin Bata sunan zabeera.
##Mamuh#
*_MQ 28_*
Cikin nutsuwa da girmamawa Modibbo ya kalli Andi a natse yace"
Kama yarinyar da mariqanta kamar su ba'a musu adalci ba sbd da yiyuwar qila bada masaniyarsu ta aikata hakanba kamar yanda shima Khalil Babu saninmu yaje ya kwaso Mana ita..
Tsit Sukayi kowa na kallon Andi da yanayinsa sbd maganar da Modibbon yayi ana jiran jin me andin zaice.
Zama batareda ya dagoba ya kallesu yace"
Alhaji qarami na damqa case din a hannunka a shigar da qara me qarfi akan yarinyar da mariqanta idan ka Gama binciko zancen gaskia ne ko aa akan laifin qage da shirin batawa zabeera suna ta hanyar qage akan cikin qarya,
Hakama asaka likitoci masu kyau suyi bincikenta aduba idan da akwai ciki a jikinta ko Babu,
Kada abari Khalil yasan inda aka Kai case din duk tsanani hakama MAHMOUD ZABEERA kada abari ko kadan yasan Abinda yake faruwa tunda baya Nan sbd acikin minti biyu zai iya saka agano wa Dan uwansa inda yarinyar take.
Cikin biyayya alhaji qaramin yace"
Angama Inshallah Andi.
Sahirtaccen numfashi Modibbo ya sauke zuciyarsa na daci da alamarin sbd baiso komai ya lalaceba.
Amatu na isowa sashen motar civil defense din na fakawa bakin qaton gate din ZABEERA
Alhaji qarami ne yafito daga palon ya kalli khalil yace"
Ka shiga ciki Andi na zaiyi magana da Kai.
Kasa motsawa yayi ya juya ya kalli Inda Amatu ke tsaye yanajin kunyar kansa daya Bari har suka tsintsi kansu a irin wannan Matsin dabai samo mafita ba tuna farko sukai aure tun kafin zuwan wannan ranar.
Kallonsa itama takeyi zuciyarta na sake karyewa da wannan masifar
Itadai komai tsananin hukunci da zafinsa zata dauka matuqar ba rabata za'ayi da Khalil din ba.
Sake maimata Masa alhaji qarami yayi Yana kallonsa cikin fushi Wanda yasashi dauke idanuwansa daga Kan Amatun yafara takawa ahankali ya nufi qofar palon yashige.
Yana shigewa alhaji qarami ya kalli Amatu dake tsayayo hawaye masu ciwo tanajin zuciyarta na sake karyewa ya nuna Mata hanya alamar suje.
Da sauri umme tayi gurinta tana qoqarin riqeta anty zarah data biyota tayi saurin rungumeta ta baya tana sake sabon kuka sbd su duka sun San matuqar aka tafi da Amatu ba lallai su Kuma ganinta arayuwarsu ba.
Daga umme har anty zarah din da Amatu kuka sukeyi sosai musamman umme datasan idan Amatu ta tafi rayuwar Khalil dinta na cikin hadarin rasata.
Haj maryam ma a katse take har lokacin sbd Basu Gama sanin inda Rana zata Fadi ba gashi dai Nuratun ma kuka takeyi sosai sbd wannan fitinar tasan shikenan Khalil bazai taba sonta ba yanda take fata komai yagama lalace Mata.
Matane su biyu da uniform dinsu na civil defense manya manya dasu kowacce tanaji qarfi da rashin Imani sbd Babu kalar bahaushiya acikinsu bare ace musulmai suna qarasowa alhaji qarami ya nuna musu Amatu sukayi kanta suka kana hannuwanta biyu suka Fara janta umme da anty zarah suka bisu abaya suna roqonsu cikin tsananin kuka Amma tuni suka wuce da ita,
Salman kuwa cikin palon yayi da sauri ko sallama baiyiba ya tsaya gabansu Andi ya kalli khalil dake sunkuye da Kai yace"
Dan Allah Andi a sassauta Amatu a tsaya a fahimci zancen ta hanyar nutsuwa mace ce ita wlh rayuwarta zasu lalata idan aka Bari suka tafi da ita aka kulleta Dan Allah....
Da sauri Khalil ya juyo ya kalli Salman din cikin tsananin firgici bai tsaya gama sauraren Abinda yake fadaba ya turesa ya fice da gudu ko gabansa baya gani.....
Ba Andi kadaiba hatta Modibbo Saida ya kidima da wannan alamarin,
Yaransu da Basu taba dago Kai sun kallesuba idan suna musu Magana,
Yaransu da Babu Abinda suka sani arayuwa bayan yimusu biyayya da bin umarninsu Koda baiyi musu daidaiba Amma ayau akan mace kamar abinda sukai shekaru suna Dora 'yayansu akai na neman rushewa,
Yau Andi da kansa Yana zaune ake tafiya abarsa yana magana hakama shima wannan yau shi Andi da kansa yake kalla Yana cewa ba'ayi Abinda yakamata ba....da matsala,da matsala babba ma kuwa.
Juyawa Salman yayi yabi bayan Khalil Yana fasa maganar da yayi niya cikin 'dacin Rai idanuwansa na sake sauyawa.
Koda suka Isa bakin qofar zabeera tuni aka wuce da Amatun motar alhaji qarami nabin bayansu.
Cikin tsananin tashin hankali Khalil ke qoqarin bin motar da gudu da qafafunsa Salman yayi saurin riqesa Amma ya fizge yabi motar da gudu Salman da umme na kiransa cikin tashin hankali umme ke cewa''
Salman dauko mota da sauri kabisa idan yayi gudu ciwonsa zai tashi Dan Allah kabisa kada kabari komai yasamu Khalil shikadai nakedashi.
Ciki yakoma cikin sauri jikinsa har rawa yakeyi yafada mota yajawo da gudu yabi Bayan Khalil din.
Koda ya cimmasa harya Fara galabaita numfashinsa yafara sarqewa.
Da sauri ya tsayar da motar ya fito yakamasa yasaka motar ya zagayo ya shiga Yana qara Masa sanyin AC din motar Yana janyo tissue da yawa ya miqa Masa yana qoqarin daidaita muryarsa yace"
Dr kada kayi Abinda zai kaika kwance sbd kana buqatar tsayuwa da qafafunka gurin fitarda Amatu cikin wannan matsalar.
Kasa Magana Dr khalil din yayi Yana fitarda numfashi cikin yanayi na azaba ya lumshe idanuwansa dasukayi jajir ahankali yace"
Muje gidansu kawu Ina buqatan daukesu daga gidan yanzu.
Hanyar gidan suka kama Yana tuqi Yana kallon Khalil din daketa fama da numfashinsa Dan daidaitawa kada yabari yaci qarfinsa.
Koda suka Isa Salman ne ya bude Masa motar yafito Yana sake qoqarin daidaita numfashinsa ya share zufansa suka nufi cikin gidan.
Zaune kawu yake Yana sauraron radio iyami na zaune gefensa tana shafawa qafarta daya Jan lalle sai gasu sunshigo da qaramar sallama suka qaraso iyami na ganinsu ta ajiye lallen datake qoqarin sawa dayar qafar tana musu maraba da zuwa duk da dai yanayinsu yasata fargaba musamman sbd zufan da kowannensu yaketa sharewa bama kamar Dr daketa fama da numfashinsa Yana dannewa sbd kada agane halinda yake ciki.
Kallo daya kawu yayi musu yasan ba lafiya ba
Ya tashi zaune daga kishingiden dayake ya janyo radionsa kusa ya qure murya sbd kada aji zancen dazasuyi ya kalli khalil daya zauna gefensa yace"
Likita lafiya naganku kamar 'yan saqon mutuwa???
Salmanu lafiya kuwa??
Numfashi Dr ya sauke Yana lumshe ido sbd azabar dayake ji ya kalli kawun cikin taushin murya yace"
Kawu zanyi maka bayanin abindake faruwa Amma Dan Allah yanzu inason ku biyoni muje wani guri muyi maganar.
Kallon juna kawu da iyami sukayi suka sake maido da kallonsu kansa cikin rawar murya iyami tace"
Akwai Abinda yasamu Amatu ne?
Meya faru ne kafara fada Mana mu musulmaine zamu dauki qaddara koma menene.
Ajiyar zuciya salman ya sauke cikin sake bawa kansa nutsuwa yace"
Ba Abinda kike tunani bane iyami Amma dai yanzu muna buqatar barin Nan ne tukuna.
Kallon Dr khalil kawu yayi da kyau kafin ya miqe Yana cewa'
Iyami sanyo hijabinki muje na yarda da Khalil fiyeda kowa arayuwata Dan haka koma menene Yana mahimmanci barin Nan din tun sun fada.
Jiki mace iyami ta miqe ta wanke qafa dayar dakeda lalle ta fada daki ta sanyo hijabi hannuwanta na rawa sbd hakanan takejin tashin hankali tun kafin suji koma menene yake faruwa.
Babu Wanda suka fadawa suka rufe dakunansu suka fice.
A mota Dr khalil yakira babban yaronsa na asibiti Ibrahim ya sanar dashi Yana buqatar gidansa daya Gama be tare ba na kwana biyu,
Cikin sauri yace angama likita.
Anguwar can take nesa kusan hanyar wajen gari duk da akwai mutane da yawa a anguwar Amma kasancewar dukkaninsu sun Saba da anguwannin cikin gari sai sukaji anguwar wani iri.
Gidane qarami me daki biyu sai bayi da kicin a qaramin tsakar gidan sai daki 'daya a hanyar shigowa.
Zaune suke akan qatuwar tabarmar da Ibrahim din yakawo suka shimfida kowannensu shiru sunkasa qwaqqwaran motsi alokacinda Dr khalil yagama yimusu bayanin dukkanin Abinda yafaru.
Wasu irin hawayen baqin ciki iyami keyi tana sauke kanta sbd tsananin kunyarsu Khalil din ahankali Tace"
Bantaba tunanin son kudi da rashin hankalin Amatu yakai har haka ba,
Yanzu wace irin masiface wannan ta dauko wadda bamusan ta Yaya zamu fuskancetaba.
Shiru kawu yayi sbd nisa da yayi a tunani Yana Dora dukkanin laifin akansa sbd shine yafara daukar rayuwa da rashin mahimmanci har su Amatun suka dauka shiyasa tayi irin wannan alamarin me girman gaske Wanda ba mutuncin Zabeera ba kawai shi kansa idan zancen ya fita da wane Ido zai kalla mutane duk rashin kunyarsa kuwa.
Ganin yakasa magan yasa Salman yashiga basa Magana Dan rage Masa nauyin zuciya Amma sam ko kadan yau bayajin komai bayan qunci.
Da zasu tafi Dole yace sutafi dashi gurin neman ofishin da aka Kai Amatun.
Yawon ofishin Yan sanda da civil defense suka Fara tun abin na aikin hkr har suka sake Shiga tashin hankali sbd duk inda sukaje ba anan aka kawota ba tuni suka fahimci Alamarin Babu sauqi acikinsa Babu Wanda baishiga cikin mummunan tashin hankali acikinsuba musamman kawu dayake ganin kamar kasheta za'ayi.
Wasa Wasa har dare Babu labarin komai daganan suka nufi wata local government din dake kusa canma baa kaitaba.
Dawowa sukayi suka ajiye kawun anan gidan Ibrahim gurin iyami suka nufi zabeera cikin sabon tashin hankali.
Koda suka Isa Kai tsaye gurin Andi suka nufa inda suka tararda Modibbo acan anan suka zube qasa Khalil din na roqo da ban hakuri abisaga laifin Amma Sam Babu wani sauqi sbd atake Andi yabata umarnin ya rufe maganar case din daga ranar kada Wanda Yakuma tayarda zancen.
Kasa komawa ciki Khalil yayi yafice daga zabeera din yaje ya siyo abinci da kayan buqata ya nufi gurinsu kawu.
Zaune suke tsakar gidan zaune sunyi shiru Babu me Magana acikinsu kowanne da tunanin dayakeyi yashigo da sallama suka dago suka kallesa cikin sanyi da mutuwar jiki.
Qarasowa yayi ya zaune gefen kawu tareda ajiye musu abincin Yana qaqalo qwarin gwiwa yadan Basu Magana kafin ya miqe ya fita yadawo motarsa ya zauna tareda rintse ido sai kawai hawaye suka gangaro Masa Yana dafe kansa yace"
Allahumma ajirni fi musibati..
Zaune ya kwana cikin mota a qofar gidan kamar yanda Suma ciki su kawu Basu rintsiba iyami kwana tayi sallah.
Gari na wayewa ciki yashigo anan yayi sallah dakin farko yafito yaje yasiyo musu abinci yakawo haka suka takurasa shima yadan ci kadan yafice zuwa zabeera.
Duk yanda yaso ganin Andi ma abin ya gagara sbd hanyar sashensa anrufe ga Modibbo ma yaqi ganinsa sai alamarin yaqara daukar zafi Yana fitowa daga zabeera Salman yakirasa yake sanar dashi anshigarda qarar maganar sbd gashinan 'yan jaridu harsun buga zancen ya Basu koina alamarin yayi Muni sbd dukkanin inda amatu tayi aiki anbinciko kowa yabada shefar qwararriyar barauniya ce Dan haka yanaga suyi qoqarin sanin inda take ayi belinta kafin case din yashiga Court akwai matsala sbd itada umme ne zasu kwana ciki musamman idan sunan MD ZABEERA yafito amaganar Andi da Modibbo bazasu dauka da saukiba.
Cikin tsananin tashin hankalin dayafi na farko Dr khalil yasake bazama yawon neman inda aka rufeta ga bangare daya su kawu sun matsa Saida ya maidasu gida saidai tunda suka dawo ake nunasu da Abinda Amatun tayi inda aketa cewa Ashe shiyasa khalil zabeera ya tsaya musu yaketa kashe musu kudi tarewa tayi a gidansu Yana muamala da ita.
Duk masifa da fadan kawu yakoma ko zaman waje ya dainayi sbd maganganun hadda qari da cin zarafi sawa akeyi wainda suke cikin gida dayane kawai suke ganin mutuncinsu har lokacin suna Kuma tayasu baqin cikin wannan alamarin.
Kwanaki kusan shida kenan Yana bulayi yakasa samunta,
Duk iya inda alamarin yake ya girmama,
Ko abinci baya iyaci sai ruwa idan ummensa ta takura Masa yasha,
Ya rame cikin kwanki shidan yakoma kamar bashiba,
Ya daina zuwa asibiti gabaki daya sai sakin kudi yakeyi koina ana bincika Masa kowace station da office din civil defense Amma Babu haske.
Zaune yake gaban kujerar dake kallon insfector Garba acikin office dinsa Yana kallonsa da idanuwansa dasuka shige sbd damuwa ahankali yace"
Zanbaka dubu dari biyar kamar yanda ka buqata cikin awa biyar zaka bincikamin dukkanin ofishinku na cikin gari da qauyuka.
Murmushi insfector Garba yayi tareda kallon Dr khalil din yace"
Mutum me mutunci da girma dai kamar wace irin qaddarace zata kaika batarda kudade masu yawa irin haka akan Amatu da kowa yasan dabadan kudinkaba wlh ko kallo bazaka ishetaba sbd Ina fada maka yarinyar terror ce tasan siririn iya sata......
Miqewa yayi Yana katsesa da cewa''
Mungama Magana Ina jiranka Nanda awa biyar din.
Ficewa yayi ransa abace yabar station din Yana sakejin kamar zuciyarsa zata fashe babu me bude baki yafadi alkhairi akan Amatu duk station 'dinda yaje.
##Mamuh#
[01/06, 8:40 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MQ 29_*
Zaune yake gefen kawu Yana Shan furarda iyami ta matsa Masa yasha Kiran Insfector Garba yashigo wayarsa cikin sauri ya daga Yana aje ludayin hannunsa
Su kawuma duk shi suka tsurawa ido suna jiran jin Abinda za'a fada Masa.
Ahankali ya lumshe ido tareda sakin boyayyan numfashi jin Abinda garban yafada Masa ya katse wayar tareda kallon kawu dayayi zuru zuru cikin farin cikinsa daya kasa boyuwa yace"
Tana central ta hanyar zaggen.
Ajiyar zuciya kawu yasaki tareda Dan rufe Ido batareda yace komaiba hakama iyami numfashi ta sauke sbd harta yanke hukuncin yau dai zata fadawa usi yasan halinda ake ciki.
Miqewa Dr khalil yayi Yana zura takalminsa yana cewa''
Kawu muje inshallah yau Amatu agida zata kwana.
Zabura kawun yayi dama jira yake ace yatashi din.
A mota Dr khalil kasa nutsuwa yayi wani irin yanayi yakeji na tsananin kewar Amatun
Inama ace Amatu mallakinsa ce da tabbas ayau rungumeta zaiyi ajikinsa saiyaji dukkanin kewarta ta sakesa,Amma ko yanzu wannan alamarin daya faru bai barsa da zabin komaiba face na aurenta cikin qanqanin lokaci sbd samun Bata kariya daga kowanne irin barazana.
Doguwar tafiya sukayi Mai Dan tsayi takaisu central din inda daqyar aka barsu suka Shiga sbd tsaro.
Yana yin parking suka fito kawu na qarewa gurin kallo cikin tsananin tashin hankali ace anan Amatu take zaune akan qanqanin laifi irin wannan Wanda ko zagi da bannar suna da gorin da mutane suke musu aka barsu dashi sun hukuntu,
Amma ace ankawota irin gurin Nan dasai masu laifin babbar kisar gilla ake kawowa sbd kawai tayi Abinda ba laifinta bane,
Wani irin kunci da bacin Raine ya cika zuciyarsa yanajin ba'a taba yimusu rashin adalci ba tun takaicinsu irin wannan,
Yarinya qarama mace budurwa za'a kawo irin gurin Nan?¿
Yanda yakejin tsananin bacin Rai wallahi daba mahaifiyar Khalil ce tasata a wannan halinba wlh dasai yayi shari'a da duk Wanda yake cikin zuriar zabeera sbd arziki ba hauka bane hakama talaka ba dabba bane.
Shi kansa Dr khalil Jin yayi dukkanin gwiwoyinsa na sanyi zuciyarsa na cika da baqin ciki da bacin ran ganin anan Amatu take,anan aka kawota cikin masu manyan laifuka sbd kawai tayi qaramin laifinsa baifi ayisa agama cikin gidaba...
Babu Wanda ya iya yiwa wani Magana acikinsu sbd halin tsananin baqin cikin dasuka Shiga na ganin irin cin zarafi da wulaqantawarda akayiwa Amatu.
Koda suka Isa bakin office din commissioner Saida aka Shiga aka isarda zuwansu shima sbd Khalil din 'dan Zabeera ne da Babu wanda zai Bari ko hanyar office din su Isa.
Daga cikin office din commissioner kuwa Bayan anzo ansanar Masa da zuwansu waya ya dauka ya dannawa alhaji qarami Kira Wanda akaci sa'a a lokacin Yana gurin Andi.
Shiru alhaji qarami yayi bayan yagama sauraran Abinda commissioner ke fada