Showing 24001 words to 27000 words out of 108527 words

Chapter 9 - MIN QALB complete Hausa novel

MAMUGEE   

08 Apr 2025

8454

infection biki ko suna dyadya ko sari ina kano gaida layin massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka 07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo.

ANNUR PERFUMES

TURAREN WUTA
KHUMRAH.
KULACCAM
MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)
DECORATIONS ..
KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING)

TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!



Koda zarah tayi parking bakin flat dinsu motat MD na gurin tabbacin Yana ciki,
Fitowa tayi tareda zagayowa ta budewa amatu qofa tana murmushi tace"

Muje ko amatu.

Kallon flat din takeyi tana zaro Ido sbd tsarinsa da kyansa tun daga wajen,
Fitowa tayi motar tana zare idanuwanta Kan kusan motaci biyar dake gurin a jere kowacce sai daukar Ido takeyi ta nufesu zata shafa zarah ta riqota tana cewa'"

Muje ciki ki huta kina buqatan hutawa sbd hayaniyar da akayi gashi kinta kuka zai iya taba lafiyan babyn kinji Dan haka please ki kula.

Kallon zarah din tayi tareda shafa cikinta tana cewa''

Wannan cikin zaki kula Dani ne har qarshen rayuwarki idan kina Kiran na haifesa Dan Babu uban komai aciki sai wainar iyami ta safiyar yau danaci.

Magana kike?"zarah ta tambaya tana juyowa daga tura qofar babban palonsu.

Qaqalo murmushi tayi taba cewa"

Cewa nayi harna Fara kewar babata.

Riqo hannunta zarah tayi suka shigo cikin palon tana cewa"

Karki damu Inshallah zakiga jimawa sosai zakiga kin haihu lfy saiki koma gurin babah kafin daga baya saimu sake daukoki kidawo Nan shikenan kinzama ta Dr khalil dinmu.

Dan sunkuyar dakai tayi tana qaqalo kunyar Dole tana Dan murmusawa saidai suna shigowa cikin palon ta fiddo idanuwanta gaba daya tareda Fara jujjuyawa tana sakin baki tace"

Wayyo USI Zo kaga aljannar duniya a gidan Nan.

Kallonta zarah tayi tareda sakin murmushi tana qarasawa ta ajiye gyalenta da keys din motarta tana nufar kicin da kanta ta dauko ruwa Mara sanyi tadawo ta dube robar ruwan ta zuba a cup ta jawo amatun data zage tana taba duk Abinda ya burgeta tana fiddo idanuwa tana Kiran sunan usi.

Zaunar da ita zarah tayi tana miqa Mata ruwan tace"

Sha ruwa amatu Kuma ki zauna kada ki Fadi da wannan zagayen da kikeyi idan kin huta zakiga komai ahankali tunda anan zaki zauna kibari ki huta tukuna.

Kwankwade ruwan tayi ta miqawa Zara cup din idanuwanta nakan dining dataga me aikin zarah din na jere wasu irin manyan kulolin abinci masu daukar Ido da fresh fruits daga fridge sai hayaqin sanyi suke ta hadiye yawu tana satar kallon zarah dake sake zubo Mata ruwan fuskarta na bayyanarda annashuwar datake ciki ta Basu amatun da akayi.

Ganin yanda take kallon gefen dining yasa zarah juyawa ta kalli dining din saita fahimci kamar yunwa amatun keji ta juyo tasaki murmushi tana cewa'

Muje nakaiki kifara watsa ruwa zakifi Jin dadin cin abinci.

Bedroom 'din dake kusa da nata takaita da kanta tasake gyara Mata shi ta sauya Mata zanin gado tareda kunna AC ta sauyo Mata room fresheners tana cewa'
Duk Wanda kikaji bakyason qamshinsa kifadamin sai a cire Miki shi kada ya sameki.

Toilet ta 'dan wanke Mata sama sama Dan baida dattin komai sbd babuma Wanda yataba amfani dashi dandai ita dana bedroom dinta take amfani batama shigowa Nan dakin gaba daya bare MD dako nata bedroom din baitaba shigaba bare yashigo wannan.

Towel tabata sabo fil tareda kawo Mata shower gel din jaggins da sabbin undies da wata doguwar jallabiya Mara nauyi me dogon hannu ta fice tana cewa' idan kingama zankawo Miki abincinki har daki kibi ahankali a toilet karki Fadi Dan Allah.

Gaba daya hankalinta nakan dakin da ake nufin ciki zata zauna batamaji me zarah din ke fada ba ta fada Kan gadon da qarfi Yana jujjuyawa tace"

Wayyo amatu ko daga Nan aka tsaya  qaramin burinki yacika kinshiga cikin Masa kudi.

Sai data gama juye juyenta akan gadon AC na shigarta tareda qamshi masu sanyin Dadi kafin ta miqe ta cire kayanta ta shiga toilet din Wanda tuni Shima ta rude da haduwarsa Wanda badan tayi aiki agureren masu girma ba kamar irinsu blue fox da bazata San ya ake amfani da irin wannan toilet din ba.

A toilet din tsayawa tayi gaban tangamemen madubin tana duba kanta tana shafa cikinta sai alokacin ta dawo hayyacinta gameda abinda yake faruwa ta lumshe ido tana tunano Khalil da halin dayake ciki,

Ita Sam Abinda Bata ganeba shine
Haj Mama data aikosu wannan aikin kukan datakeyi na qarya ne kokuwa?
Idan har kamar yanda tace MAHMOUD da KHALIL yayantane to meye banbanci Dan ance Khalil ne ba MAHMOUD ba?
Shin wannan abindaya faru yau din menene ainihin Abinda yake nufi sbd saitake ganin kamar yanda aka tsaro abin kamar ya sauya taku me matuqar hadarin gaske,

Ta Yaya zata haihu bayan batada ciki,
Ta Yaya zata auri Khalil bayan ba ranar haihuwa tunda ba ciki,
Shogowarta fa anan kamar tashigo wani mugun keji ne ta rufe kanta sbd tunda Babu ciki Babu ranar haihuwa,
Babu ranar haihuwa Babu ranar tafiyarta..

Shiru tayi tana jinjina Kai tace"

Ina buqatan ganin Haj Mama naji ni meye matsayina a yanxu.

Wankan tayi tana shaqar gel din me qamshin Dadi tafito ba wani shiririta ta shirya cikin kayanda zarah din takawo Mata tana cikin saka hula akanta zarah din tashigo daukeda tray din kayan fruits hafsatu me aikinta na bayansa daukeda tray din abinci.

Washe baki tayi tana zama qasa Kan qaramar carpet din dake gefen gado tana cewa"

Anty sannu da aiki kinata fama tunda nazo.

Aje tray din zarah tayi tana murmushi tace"

Amatu tunda aka banike nasan hidimarkice yanzu nafara harsai kin haifarmana me kama da Dr dinmu kokuma gwara dai ki haifar Mana me kama da MD dinmu dagani har Dr din saimunfi sonsa sbd MD shine 'dan uwanda Dr yafiso acikin familynsa gaba daya,
As for me nikuma MD shine rayuwata.

Apple amatu tayiwa babbar gutsura tana ci tace"

Anty Dr Yana ina yanzu?

Yar dariya zarah tayi tana zuba Mata Salad Kan dafaffen dankalin da aka dafa matashi da zallar Naman kaza da cabbage tace"

Dr Yana bangarensa Amma nasan tunda matarsa da babynsa na Nan bazamu Kai dare batareda yazoba Dan haka ki kwantarda hankalinki Dr nanan zuwa idanma baizoba zankirasa yazo.

To kawai tace tana cika bakinta da dankali da nama sbd 'dadin da abincin take Mata tace"

Anty idan nagama cin abinci mezanyi Kuma??

Bacci zakiyi ki huta amatu kafin zuwa gobe zanfadawa MD saimu kirawo Dr dina yazo afara dubaki da lafiyar baby.

Sarqewa tayi da qarfi tasaki tari Jin Abinda zaran tace.

Da sauri Zara ta dauki ruwa tana miqa Mata tana Mata sannu tace"

Amatu kodai abincin be Miki bane??

Girgiza Kai tayi da sauri har lokacin tana tari tace"

Ba Dr ne zai ringa dubani ba tunda shine Mijina??

Aje cup zarah tayi tana cewa''

Aa Dr bashi zai ringa dubaki ba munada Dr dinda zai ringa dubaki wato gynecologist Dr likitan Mata Wanda Nima shi nake gani sbd matsalar rashin haihuwarta.

Shiru amatu tayi tana tura abincin kawai sbd tasan ba jimawa asirinta zai tonu duk aka kawo wani likita yadubata zaisan batada ciki
Andi sakawa zaiyi a harbeta da kibiya sbd da gaskia ta fito.

Tana gamawa zarah tasata kwanciya bayan tayi sallah ta rage Mata sanyin AC ta fice bayan tasa hafsatu ta gyara gurin suka ja Mata qofa.

Shiru tayi tsawon mintuna tana tunanin goben idan likita yazo
Miqewa zaune tayi tana cewa''

Dole Naga Dr khalil yau nafada Masa kafin goben Amma dai yanzu inason Fara magana dasu usi.

Jakarta da aka saka cikin wardrobe ta bude ta dauko matacciyar wayarta ta lalulo numbrn USI ta Danna Masa Kira.
##mamuh##


______________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

#MIN QALB❤️
Mamuhgee

ZAFAFA BIAYAR

SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma

MIN QALB
mamuhgee

YANKAN BAYA
billyn Abdul

KIBIYAR AJALI
Miss xoxo

ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano

Pay @09033181070
Or 09032345899
[01/06, 8:53 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MIN QALB 14_*
_mamuhgee_

ANNUR PERFUMES ANNUR PERFUMES!!!!!!

JAMA'A MA'ABOTA SON QAMSHI DAN SANYAYA ZUCIYA Ina kuke kuzo ga sabuwar duniyar turare sabon tashe ANNUR PERFUMES sunkawo muku,
Turarensu qarshene,
Qamshinsu na daban,
Kayansu tabbataccine,
Aikinsu ingantacce ne
shin kataba/kintaba amfani da ANNUR PERFUMES kuwa?
To maza qarzayo karki Bari ayi badakeba dankuwa kayansu lamba dayane Kuma amintaccine masu guarantee domin kuwa mun tabbatar.

ANNUR PERFUMES donjindadin customers  munkawo muku dadadan turaruka na musamman  masu nishadan tarda Amarya da uwar gida harma da angonta kamar haka turaren wuta humra kala daban daban kwalaccha  Dana matsi na infection biki ko suna dyadya ko sari  ina kano gaida layin  massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka 07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo.

ANNUR PERFUMES

TURAREN WUTA
KHUMRAH.
KULACCAM
MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)
DECORATIONS ..
KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING)

TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!

**************
Ringin numbern usi din keyi harta katse bai daga ba tasake Danna Kiran tana cewa'

Usi idan muka hadu saina fasa maka baki da kai tunda har zaka iya bacci baka kirani kaji Yaya ta kasancemin ba a wannan zabeerar da kallo daya Andi da Modibbo sukewa mutum sai cikinsa ya mur'da,

Uwa uba arasa gurin ajeni sai anan cikin wannan me bada tsoron da matarsa.

Kira biyar tayi Masa Amma baa daukaba takira wayar iyami cikin sa'a kuwa ta dauka Nan suka jima suna mgn iyamin na maimaita Mata karta taba duk Abinda zata gani na kowa karkuma ta jawowa kanta fitina ko rigima ta jawo musu kafin aka miqawa kawu wayar Shima dai yayi Mata maganar karta taba abun kowa sbd kada 'yan kudin Nan dasuka samu su qare a gun kashe rigima Shima usi sunfada Masa kada ya kuskura ya janyo rigima sbd tanadin kudin Nan zasuyi sbd abinci dakuma qarasa hada takardun komawarsa karatu.

Fadawa lafiyayyan gadon tayi ta kwanta tana lumshe ido bayan tagama wayar
Tai wani juyi tana lulluba da bargon me shegen laushi sbd sanyin AC dake ratsata ta lumshe ido tana cewa'"

Masu kudi wato ko a gurin bacci sunfi talaka samun nutsuwa
Da agidanmu ne da yanxu radion kawu da qarar dakan turmin maman junior da qarar bude tukunyar maman basiru sun Hana mutum bacci,
Rufe idanu tayi tana sake gyara kwanciya take bacci me dadi yayi gaba da ita ga gajiya ga lafiyyan abinci dataci ga lafiyayyan gurin kwanciyar dakuma sanyin AC ga ba hayaniya ai Dole baccinta yau yayi dadi.

Saida garin ya hantse ta tashi tana wata irin miqa me Dadi fuskarta a sake da farin cikin irin baccin data samu tana qoqarin saukowa gadon ne zarah tashigo daukeda sababbin brushes da toothpaste masu kyau tana kallonta tace"

Amatu Yaya? kintashi lfy? Ya babyn dr?

Qarasa saukowa gadon tayi tana sake yin wata doguwar miqar datasa zarah saurin ajiye kayan hannunta tana riqeta tace"

Amatu zakiwa kanki illa idan kina irin wannan miqar
Idan kinajin gajiya ne za'asa ayi Miki tausa ahankali Amma Dan Allah ki daina kinji??

Kallon sakarai amatu ta Mata Jin hadda miqar ma yanxu wani tsurku zaa kawo sbd ciki...
Amma dai ko yayane bazata Bari banxa ta wucetaba tubda damace tasamu gwara ta dama kafin Takoma inda tafito Dan haka sai ta 'dan yamutsa fuska tana 'dan dafe bayanta tace"

Anty zarah ko Ina jikina ciwo yakeyi na gajiya shiyasa nake 'yar miqar ko zanji jikin ya sake Amma tunda kince za'amin tausa inaga idan anyi zanji jikin ya saki.

Murmushi zaran tasaki tana sakinta Takoma gaban mirror ta dauko toothpastes din different flavors kusan kala biyar tace"

Ga Macleans ki bude kowanne kiji Wanda qamshinsa ya Miki Wanda bazai tayar Miki da zuciyab saiki ringa amfani dashi.

Karba tayi tana washe baki tana duddubasu tace"

Duka ma sunmin abarminsu kowanne  ma qamshinsa zaimin sauran gida zanje dasu idan zantafi.

'yar dariya zarah tayi tana girgiza Kai rashin damuwar amatun na sake burgeta musamman data 'dan Fara lura tun jiya inda amatun tafito tana tareda yunwa gskia Dr be kyautaba barinsu su wahala haka tana matsayin matarsa bayan duk arzikin dayakedashi.

Fita tayi Takoma kicin ita Kuma amatu toilet tashiga tafara yin brush da kusan toothpaste kala hudu kowanne saidata fasa ta 'dan lakata tayi dashi take bakinta suka ringa bada wani qamshi masu Dadi dasuka sakata yin wanka cikin nutsuwa da annashuwa.

Tana fitowa saidatayi sallah kafin ta shirya cikin doguwar rigar jallabiya Mara nauyi Wanda duk zaran ce takawo Mata daga gani duk nata ne Amma suka sabbi ne Babu Wanda ta taba sakawa.

Tana cikin fesa turare tana lumshe ido cikin jin Dadi tace"
wainnan turaren dasu zankoma gida idan zankoma ma komai saina dauka naje dashi bazanga irin wannan Batinba nabariba.

Turarukan ta kwashe duka tabude wardrobe tazubasu cikin Jakarta daga can qasa ta rufe zip din tadawo gaban mudubin tana gyara zaman rigarta a jikinta saiga zarah tashigo tana kallonta Jin dakin yacika da qamshin turaruka yasata Dan 'yin tari tana cewa'"

Amatu wannan turarukan bazasu cutatar dakeba kuwa¿
Qamshin yayi yawa Zo muje dining muci breakfast idan Kuma akwai Abinda kike buqata ba Wanda akayi ba sai hafsatu ta Dora miki ga Dr khalil ma yazo Yana palon MD suna Magana.

Ba qaramin Jin Dadin zuwan Dr khalil tayi ba sbd sanar dashi Abinda su zarah din ke shirin Yi na Kiran wani Dr shiyasa ta farayin gaba tana cewa''

Ni komaima aka dafa yamin zanci Amma Dr nakeson Fara gani anty zarah Dan Allah kinji.

Biyota tayi tana cewa''
Wannan rashin hkr haka amatu bazaki jira yagama yazo yasameki har dakin ba.

A palon ganin Dr khalil baida lokacin fitowa daga gurin MD yasa ta marairaicewa zarah fuska tana taba cikinta
Take zarah ta tashi da kanta ta hado Mata nata abincin a tray sbd kada yinwa tai Mata illa sbd cikin dake jikinta bazata iya jiransu ba.

Dakinta Takoma acan tayi zaman Yan bori akan carpet tafara cin lafiyayyan breakfast din tana bude plate din farfesun kifin da akayi kawai sbd ita dayaji kayan qamshi da 'dan yaji batasan lokacinda tasaki dariyar farin cikiba tana diba takai bakinta saiga Dr khalil yayi knocking yashigo fuskarsa tayi wani iri na yanayin damuwar dake tattare da ita.

Tsayawa yayi daga bakin qofar ya qura Mata ido yanda take cin abincin sosai cikin Jin dadinsa dakuma bayyanarda baqone agareta sai yaji jikinsa yasake yin sanyi ya rintse ido Yana Jin zafin zuciyarsa na qaruwa sbd baisan ta Ina zaifara da wannan qaqqarfar rigimarba sbd Nan ana Magana ne akan ciki da aure Wanda baa Wasa dasu sbd komai dadewa gskia zata fito idan akwai idan Babu,
Ta Yaya zaifara neman mafita?
Ta Yaya zaifara neman inda mafitar cikin amatu zata fito?
Gasu usi yanxu da Dole nauyinsu zai dawo kansa sbd inganta rayuwarsu su duka din ta yanda har abada komai zai faru bazasu Yi shaawar sake komawa rayuwar dasuka fito ba,
Idan har amatu zata iya saka kanta acikin irin wannan masifar me hadari akan kudi to tabbas zaiyi amfani da kudi da qarfinsa ya wadatasu da dukkanin abin buqata har sai amatu ta cire kwadayin kudi a ranta,
For now Abindake gabansa shine mafitar cikin jikinta da ake zaton akwai Amma bazai Yi rushing abubuwan ba tunda tana Nan hannun MD yasan Babu abin dazai sameta she's morethan safe anan Dan haka zata cigaba da zama anan zaije gurinsu kawu zaifara aikin kulawa dasu daga yanzu.

Gyaran murya yayi Yana sake gyara tsayuwa tayi saurin dagowa tana ganinsa ta miqe tana qarasa kwankwade sauran kakkauran tea din dake hannunta cikin cup tace"

Dr tun jiya kaina ke neman bugawa da son ganinka na.....

Quite amatu""yafada cikin 'yar tsawa ransa a 'dan bace.

Cak ta tsaya tana kallonsa ganin yanda bacin Rai ya bayyana a fuskarsa sosai sai hakan yasa jikinta yin sanyi tayi qasa da Kai tana kallonsa fuska a marairaice.

Ya dauke Kai sbd ganin zata sa zuciyarsa saukowa yace"

Kinsan zaman da kikeyi acikin zabeera?

Saurin matsowa tayi tareda katsesa da cewa"

Wlh dr aiki Na....

Amatu just keep quiet please,
Wane qarya kike tunanin zakimin bayan duk abin daya faru jiya gaban kowa and yanxu Ina tambayanki kinason kawo min wani different story
Ki saurara kiji usi yafadamun komai Wanda yasa nake mamakinki har yanzu
Amatu har kudi yayi mahimmancin dazaki 6ata sunan wani akansu,
Rayuwarsa kike neman batawafa gaba daya
Shin kinsan shi Wanda kikaso batawa rayuwar shine Wanda nafiso a rayuwata fiyeda kowa bayan iyayen dasuka haifeni???

Tsit tayi tana sake yin qasa da kanta cikin rashin Jin dadin yanda yake maganar cikin tsananin 'daci da bacin Rai
akaro na farko a rayuwarta dataji nauyin wani mutum.

Juyowa yayi Yana kallonta yacigaba fa cewa"

Amatu wannan duk Abinda kike tunani ya wuce Nan
Wannan alamarin babbane bazaki ganeba sbd tunaninki kawai ya ta'allaqa ne kawai akan kudin dazaki samu
Meyasa kudine kawai Abinda kike gani amatu wannan alamarin babbane meyasa bazaki ganeba,
Umme mahaifiyatace duk Abinda tasaki kizo kiyi tayine sbd rashin mafitar datake gani tana ciki
Gashi yanzu kunsani a tsaka me wahala bansan yazanyi da kowannenku ba,
ku duka bazan iya barin wani Abu ya sameku ba kokuma wani mummunan hukunci ya hau kanku sbd kowaccenku nada matsayi me girma agurina gashi yanzu ta kowane bangaren nine zansan Yaya zanyi.

Kuna tunanin MD sakarai ne daza'a Zo Kai tsaye afadi wannan alamarin ace shine ya zauna ya dauka kawai sai sunansa ya baci?
Tabbas dakun aikata babban kuskure sbd ilimi da matsayin MD yawuce inda umme ke tunanin ke bakyama ciki sbd komai ma qaramin kanki bazai ganeba gameda waye MD Dan haka ki saurareni da kyau kiji,

Daga yanzu dakike cikin zabeera duk Abinda zakiyi da Wanda yake faruwa ki tabbatarda kina sanar Dani,

Karki kuskura Koda Wasa kiyi maganar Abinda yake ainihin gskiyar maganar Nan da kowa Koda kuwa zarah ce ko a waya karkiyi maganar da USI sbd kadama wani yaji,

Kince kinada ciki Dan haka zakici gaba da zama a me cikin harsai na samu mafitar fita cikin wannan shirmen da kuka faro,

And bayan zarah karkiyi muamala da kowa acikin zabeera batareda izininaba lastly Kuma karki yarda kiyi Abinda za'a zauna meeting akanki kokuma asan asalin waye ke acikin zabeerar Nan hakama karki yadda kiyi Abinda zaisa a fahimci bakida ciki idan nace karki kuskura I mean kada Koda Wasa ki kuskura

Duk Abinda kike so kifadamin zan kawo Miki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login