Showing 96001 words to 99000 words out of 108527 words
dinsa ta zauna bakin gado tana zare doguwar rigarta tareda warware Daurin gashinta Dan taji sauki ta miqe ta Shiga toilet sbd fitsarin daya Fara matsarta ta fito ta kwanta sbd hutun gske take buqata take bacci ya dauketa bayan Tasha magungunan ta.
Sai kusan azahar ta tashi bacci shima sbd qarar loudspeaker da ake Kiran sallah Wanda ta manta rabonta dajin hakan ta tashi tayi wanka ta sanya riga da skirt na atampar cikin kayanta data Bari tun na legend auren Dr khalil Kuma cikin ikon Allah sun Mata saidai sun Dan kamata kadan ba sosai ba sbd ita acan din Bata qara jikiba saidai kyau da gogewar da fatarta tayi sai cikowar albarkatun jiki.
Fitowa tayi Palo ta tarardasu anty salamatu da iyami saisu maman junior dasuka shigo ganinta aikuwa Nan aka hau ihu da hayaniya ba itaba ba mutuniyarta maman junior ba hadda junior daya girma yafara zama Dan saurayi Nan suka hau fira tana cin lafiyayyar sakwara da miyar Ganda da maman junior din takawo Mata da zafinta iyami dai Dole Takoma palon kawu tabar musu Nan sbd shegiyar firar iya shegen da maman junior tafara kawo musu suna dariya tana sake fesowa Amatu kalolin iya shegen da akeyiwa miji.
Firar nawa anty salamatu da maman basiru Dadi hakama Amatun datake sauraronta tanajin qaruwa aciki Amma sai tanajin abin wani irin banbarakwai sbd ba sa'aninta bane duk da duk kwamacalar duniya sunsaba yinta tare tun Ada can Amma wannan sbd ta rayuwar aurece sai kamar tanajin nauyi Amma dayake maman junior din ba ruwanta Dole wani abin saikayi dariya ba qaqqautawa.
Sai magriba majalisar palon tasu ta watse suka tashi yin sallah tukuna iyami tasamu kanta duk da wata firar tasu tanaji sama sama wani abin saidai ta girgiza kanta sbd rashin kunyar tayi yawa.
**_Athens GREECE_
Kiran wayar USI yake sakeyi kusan akaro na goma sha wani Abu Amma Bata shiga yakoma Kiran anty salamatu itakuma tanata ringing Amma sbd suna Palo fira tayi Dadi Bata jiba yasaki tsoki ahankali ya Nemo numbern kawu yakira shikuma ya fita waje tsohuwar majalisarsa tasu alhaji mande yabar wayar gida.
Ki yayi kamar ya fasa wayar hannunsa ya rintse idanuwansa dasukai jajir ya budesu ya miqe daga zaunen dayake a palon zai bar gidan Dan Yana buqatar ticket din Nigeria koman dare idan dai akwai flight zai tafi.
Da sauri anty zarah takira sunansa zatai magana ya juyo yayi Mata kallo daya da idanuwansa dasuka Sanya gabanta faduwa yace"
Please zarah karki Bari nayi Miki fada kizo kema ki qaramin wani ciwon Kan sbd idan maganata tana daidai you are completely at fault anan,
How can you be so selfish kina kallo ta fita Amma baki daga wayana kin kiraba you're telling me ma har bankwana tayi Miki Wai zata tafi
A woman who had a miscarriage kice Wai kin dauka na sani zata tafi kona sani ke baki fahimci batada cikakkiyar lafiyaba bai kamata tayi tafiya ahaka ba Kona barta tunda kinada hankali bazaki nada shawaran abar tafiyarba hartaji sauqi Amma Zaki ce Wai you thought nasani to hell with your thoughts...
Please I need some air kije daki kema ki kwanta ki huta kada wata damuwa ta baki matsala kema idan munsamu tickets zamu tafi gida I don't feel like staying Kuma sbd inada aikin da ake nemana a gaggauce.
Ahankali ta iya bude baki tace"
Sorry. Kafin ta juya ta nufi daki tashige tana Hana kanta Jin damuwa ko haunshin zancensa sbd ta yarda kaman yanda yafada tanada laifi sosai anan,
Ko tambayanta ya jiknta bataiba,
Rintse Ido tayi tana cewa''
Zarah meyasa Kika kasa tunani anan.
Dakinsa ya nufa bayan yayi booking tickets dinsu na tafiya saidai bazasu samu jirgin Nigeria ba direct yanzu saisunyi kwana biyu kafin su Isa sai an tsaya qasashe dasu Dole ya amince ya zauna Yana dafe kansa dake neman bugawa sbd tension,
A rayuwarsa baisan gwagwarmayar rayuwar aureba da fadan yau da gobe da ake cewa sai yanzu,
Gabaki daya sai yanzu yasan me ake nufi da hakuri a zaman aure Dan gashinan kansa na neman kamawa da wuta Yama rasa ta Ina zai faro da kowaccensu ka taba sai wannan tace taji haushi,
Babban burinsa dai yanzu kada Amatu tadauka zafi da yawa Dan baisan ya zaiyiba idan ta dauka zafi Dan saukowarta qila saiya hada da neman agajinsu Andi.
Wayarsace tayi qara baiyi niyar dubawa ba Amma sbd jiran kira daga gidansu Amatun saiya duba wayar cikin sa'a kawu ne Dan haka ba Bata lokaci ya dauka suka gaisa Yana tunanin ta inda zai Fara tamabayar ko Amatun ta iso sai kawun ya rigasa da cewa''
Saiga Amatu tazo baku sanar Mana ba MAHMOUD,
Ana zuwan bazata ne a irin wannan doguwar tafiya saika biye Mata kaima kaki fada Baku kyautaba gskia.
Ajiyar zuciya ya sauke yabawa kawun hkr kawai a taqaice kafin suka Dan qara gaisawa suka aje wayar yana Jin wani irin nauyi na raguwa daga zuciyarsa da kansa.
##Mamuh#
[06/06, 7:27 PM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MQ 46_*
_INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_ _NA ZINNEE SMART WANDA TSARUWAR RUBUTUNSA DA TSAFTARSA TAREDA DADINSA SAIZA KU KAMU DA QAUNAR RUBUTUNTA A KARATUN LAYIN FARKO DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU
TA WANNAN NUMBERN_
👇👇👇
08080840567
Yau kwananta uku da dawowa batareda ta sanarda kowa dalilin dawowarta ba tadai ce musu hutu tasamu me Dan tsayi shiyasa tazo Dan haka Babu Wanda yasa ko kawo tunanin komai cikin ransa gameda zuwan ko tsakaninta da mijinta sai suka hau shaanin gabansu aka bude majalisar me zaman kanta gidan kawu tasu maman junior Dan har wasu abubuwan gyare gyare suka Fara Shirin Fara harhadawa Amatun na gyaran jiki Dana cikin jiki musamman ma iyami da dama batai gyaran yarta ba lokacin da akai auren Dan haka yanzu zata gyara abarta.
MAHMOUD ZABEERA kuwa tunda yaji daga bakin kawu tana gida taredasu sai hankalinsa yadan kwanta Amma duk da hakan a matse yake daya dawo Nigeria din tun kafin kowa yasan halinda suke ciki Dan shi kunyama zaiji ace matarsa ta tafiyarta Yana yawon neman komawarta ko Modibbo saiyace ba MAHMOUD ZABEERA din dasuka sani bane gashi kamar zuwan nasa Kai tsaye bazai samu ba sbd wani urgent work Kuma daya taso Masa Wanda dole saiyaje Dan haka zarah kawai zata taho Nigeria shi zai wuce inda zaije daga Nan daga can zai wuto Nigeria din.
Yau kwananta bakwai da zuwa zaune suke suna fira itada anty salamatu da iyami Dan yau Yan firar tasu duk basanan sunfita anguwa Dan haka yau gidan tsit ba hayaniya sai su kadai USI ma yadawo asibiti da wuri yau Yana dakinsa baccin gajiya yakeyi sbd a asibitin ya kwana yau.
Sallamar umme sukaji Muhammad na bayanta tafe cikin gudu hannunsa riqeda Ben10 soldier dinsa dayafi so cikin kayan wasansa Yana Kiran sunan anty salamatu yana shigowa yaga mummynsa a zaune da gudu yayi kanta Yana cewa''
Mumma mumma.
Rungumesa tayi tana cewa''
My Muhammad has become a superman ji wannan gudu fuiiiiii.
Dariya yayi Yana Jin dadin Superman data kirasa Yana sake hayewa jikinta yace"
Mumma where is my Daddy?
Inason ganinsa i miss him""yafada Yana leqa bayanta da kallon koina Yana son ganin baban nasa.
Murmushi tayi tana zaunar dashi gefenta tace"
Muhammad look"tafada tana nuna Masa su iyami tace"
Baka gaida grandma ba da antyty dinka"cewar anty salamatu.
Gurin iyami ya nufa Yana miqa Mata biscuits din daya Ciro aljihunsa wanda yakawo Mata yace"
Kaka iyami ga biscuits da umme ta siyomin ki ajewa kawu.
Dariya dmtayi tana jawosa jikinta suna sake gaisawa da umme data zauna tana amsa gaisuwar Amatu data salamatu tana cewa''
Amatu wato muda muka matsu dason ganinki gamu munzo Muhammad ya isheni Wai babansa yakeson akaisa gurinsa shine nace Bari muzo dai idan yaganki qila ya rage fitinar neman uban.
Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba saita kamo wani zancen suka fada wani zancen Bayan anty salamatu takawowa ummen ruwa da brabiskon dasukai Wanda ummen na sonsa sosai musamman yanda iyami keyinsa yayi wani irin laushi.
Sai dare umme ta tafi tabar Muhammad dayace gurin mamansa zai zauna.
Washe gari kwananta Tara kenan da zuwa suka shirya itada anty salamatu suka fita da motar USI daya bar musu Wanda duk yanda taso taja motar kasawa tayi sbd yanda ta koya tuqi a Greece daban da tuqin nan din Dan haka Dole tabar anty salamatu da USI ya koyawa tuqi sbd fita da iyami ko lalurar gida idan antashi Dan yakan bar musu mota ya tafi asibiti musamman idan acan zai kwana.
Family house dinsu maman basiru sukaje barkar haihuwar da qanwar maman basirun tayi shiyasama kwana biyu basa zaman fira sun Dan jima acan kafin suka baro suka nufi kasuwa siyayyar takalman iyami data Basu saqon anaso sun qare daga Nan gurin bada dinki suka Amatu tabada dinkuna sai yamma sosai suka dawo gida Dan haka suna komawa sallah kawai sukai sukaci abinci Amatu ta kwanta Dan matuqar gajiye take.
Washe gari tana buqatan gyara kanta daya Fara damunta suka shirya zuwa blue fox itada anty salamatu Dan haka guraren 12 suke fice bayan sunfara biyawa sun ajiye Muhammad a zabeera taje ta gaidasu Andi dasukai mamakin Jin zato hutu Ashe Amma sanin ba ayi maganar tarewarta ba yasa suka barta takomawarta gidansu inda ta sauka saidai Kam tunda har tazo Dole ayi maganar tarewarta ta tare sbd daga yanzu idan tazo ta sauka a gidan mijinta dama tuntuni anyi gyaran sashen marigayi Dr khalil an rushe komai ansauya tsarin gurin gababaki daya Kuma sai akai qatuwar katanga aka zagayayesu cikin qaramin gate me kyau tareda sashen zarah sai harabarsu ta zama daya me girman sosai.
Daga zabeera blue fox din suka wuce suna Isa Allah ya hadata da manager kuwa ai Nan ya tsaya kallonta cikin girmamawa da sauri ya qaraso Yana cewa''
Ran Amaryar zabeera ya dade yau an tuna baya kenan.
Dariya taso Yi ta gimtse tana kallon gurin da aka sauyawa tsari me kyau fiyeda da ga girma da fadada gurin da akayi ya sauya matuqar Dan yanzu ma tun a gate Saida tickets ake shigowa ga uban securities tana jinjina kai tace"
Manager komai na blue Fox yasamu sauyi Banda Kai kana Nan yanda kake har halayen.
Dariya yayi Yana cewa''
Allah ya taimaki Amatun zabeera ai mu Babu wani sauyi daya fiyemin blue fox musamman yanzu datake zaman mijinki Dan kuwa ya jima ya siyeta gabaki dayanta Kuma nasan idan Allah ya yadda sbd ke ne tunda kowa yasan har yanzu kina qaunar blue fox dinnan shine yayi Mana dukkanin wannan gyare gyaren Takoma kamar turai yanzu hadda sashen geaming da sports munada aciki haka Kuma komai namu anqara fadadashi daga restaurant din har spa din dasauransu.
Girgiza Kai tayi tana kallonsa tace"
Ga antyna dai ku gaisa sbd Naga ko ganinta bakayiba sbd dadin labari.
Da sauri ya kalli anty salamatu dake sanye cikin riga da skirt na red embellished atampa da gyalenta red shima sai tsawonta me tsari ya fito cikin dinkin riga da skirt din ya washe dukkanin haqoransa da fara'a yace"
Sannu da zuwa blue fox Ina Miki barka da zuwa sirikar me gidanmu.
You'll never change manager" Amatu tafada tana yin gaba Yana biye dasu Yana musu bayanin yanda tsare tsaren gurin yake ayanzu da kansa yaje jiki na mazari ya karbo musu tickets na komai da zasuyi yakawo musu a kebantaccen gurin da sai oga zabeera din yazo da kansa shikadai ke zama acan suka Fara cin snacks kafin suka nufi spa Dan komaima yimata zaayi.
Da gyaran Kai aka Fara musu kafin da aka gama aka koma gyaran qafafuwa daganan aka koma gyaran jiki.
Basu baro blue fox ba sai magrib suna isowa gida itace tafara fitowa tana juyowa sai Jin Muhammad tayi a jikinta ya Fado Yana mata "oyoyo mummah"
Da mamaki take kallonsa suka nufo cikin gida tana cewa''
Waye ya dawo da Kai?bakace Kuma gurin umme kakeso ba sbd ka ringa wahalarda mutane zaka ringa saka masu kaika da dawo dakai yawo.
Daddy yazo Dani...
Kallonsa tayi da sauri tana kallon bakinsa daya furta dadyn tace"
Dadynka Kuma?
Eh dady ne yadawo yau yazo Dani yace muzo mutafi da mummah.
Kallon inda yake kalla tayi numfashinta nason sauya fita ta hanyar qara sauri tana dannewa ta kalli gurin tagansa zaune Kan kujerun harabar gidan tareda kawu
Kawu sai zuba yake Masa Amma shi idanuwansa na kanta ya zuba Mata su cikin yanayi da kasalar da ganinta ya sakar Masa idanuwansa na bayyanarwa sbd wani lumshewa dasukeson Yi Amma Basu lumshe din ba.
Bugawa ZUCIYARTA ke Naman Yi sbd wani irin kyau da sheqi tareda qwarjinin da Allah ya horewa wannan bawa nasa MAHMOUD DAHEER ZABEERA ta dauke idonta ahankali tareda juyawa ta shige ciki batareda tabari kawu ya gansu ba Dan yanzu zai Fara kawo Mata zantukan tazo ga mijinta.
Suna shiga daki tashige ta tube saidatai wanka kafin tayi sallar magrib da yanzu aka gama ta sanya doguwar riga mara nauyi me kamar boubou ta fito tana tambayar abinci ta nufi kicin ta dauko zobon da iyami keyi tana sawa a fridge sbd baqi dakuma kawu dakeson ruwa me kala ta fito tana Shan zobon saiga USI yashigo yace taje palon kawu yana namanta.
Can ya wuce Kai tsaye sbd ta daina Jin hayaniyar Muhammad tasan sun tafi ne tunda dare yafara Yi takumasan babansa bai Bari ana fitar dare dashi.
Tana shiga da Muhammad din tafara cin karo kwance yayi bacci jikin kawu tana ganin hakan saita daure fuskarta taqi kallon dayan gefen Dan taji ajikinta MD ne agurin.
Kallon kawu tayi muryarta na daidaituwa cikin nutsuwa tace"
Kawu likita yace kana kirana.
Eh mijinki ne gashinan zaune yazo tun dazu bakwanan yanata zaman jira.
Miqewa kawun yayi daukeda Muhammad ya fice yakaiwa iyami dakinta ya fita zuwa gurin abokanan hirarsu ta dare a qofar masallaci.
Kawun na fita ta nufi qofar fita itama batareda ta kalli inda yake ba ko qofar Bata qarasa isaba taji yariqo hannunta tareda dawo da ita baya har bayanta na gugar qirjinsa ya bude baki da muryarsa me taushi yace"
Why?
Meyasa Zaki taho a irin yanayin da kike ciki Kuma ki dauki fushi Bayan nine yakamata na dauki fushin tunda kin baro batareda sanina ba.
Juyowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta zame hannuwansa cikin nata daya riqe ta wuce tabarshi tsaye Yana kallonta.
Qofar data fice yabi da kallo Yana Dan rintse idonsa ya sauke numfashi Yana komawa zaune dama yasan Amatu bazata sauko acikin sauqi ba.
Hakanan ya fito ya wuce batareda kowama yasaniba Yana Isa gida ko abincin dare daqyar yaci sbd kada Zarah daya lura kamar itama tafara iya Magana akan Abu tayi Magana bazai iya daukar wani stress Bayan Wanda yake daukaba yanzu aikin dayayi a Sudan duk tsawon kwanakin baiwani bada hankali yayi Abinda yakaisa ba sbd har lokacin komai Kiran dazaiyiwa Amatu baya samunta,
Wanka yayi ya kwanta kawai dama akwai gajiya a taredashi sbd yau din ya dawo.
Washe gari ma taso fita Amma iyami ta hanata sbd cewar mijinta na gari ba Maganar yawo yanzu Dan haka Dole ta zauna gida tana kallo su Anty salamatu hadda iyamin suka tafi gurin sunan qanwar maman basiru suka barta.
Tana zaune Palo tana kallo sama sama bayan la'asar har bacci ya Dan Fara daukarta taji qamshin imperial majesty na shiga hancinta kobata juyoba tasan shine zai shigo palon ta tashi zata shige daki tun bai qarasa shigowaba tana kaiwa tsakiyar palon Yana shigowa da sallamar cikin sauti me taushi ya tsaya gabanta Yana kallon fuskarta dake daure tam sai yaji jikinsa yayi sanyi ya rasa kalmar furtawa ya riqo hannunta cikin nasa idanuwansa na kanta a gajiye da wannan fitinar yace"
Wannan shirun naki is killing me
Kiyi mgn Koda zakiyi fada ne I'm ready Zan dauka infact I won't say a word indai har Zaki sauko.
Bata kallesaba ta kwace hannunta a hankali kafin tace"
Zan kwanta Kuma bakowa a gidan nikadai ce.
Tunda yadawo gida zarah ta rasa gane kansa abun duniya ya isheta ga cikinta nada damuwa an hanata sakawa Rai damuwa Amma wlh bazata iya rashin damuwarba sbd Abinda take gani shi ake Kira da asalin damuwar,
Yau satinsa guda cif da dawowa Amma yarasa gane Kan Amatun tun abin na iya tsakaninsu har gidansu Amatun dai kowa yasan Abinda yake faruwa kawu dayaji hadda 6arin ciki tayi sai baiji dadin yanda MAHMOUD din yabari tadawo ba ita kadai cikin yanayi irin wannan Amma zamansa uba saiya ringa bin Amatun da rarrashi har gwara iyami na Dan Mata zafi wani lokacin Amma duk da hakan shidai MAHMOUD baiga sauqi ba saima yakoma ya hurawa su Andi wutar batun tarewar Amatun Wanda yabar Andi cikin mamakinsa dakuma tunanin shima wato lokacin gyaransa yayi a hannun Amatu sai suka aikawa kawu yace zai Basu ranar tarewa idan yayi mgn da Amatu.
Jin hakan sai tension dinsa yafara bayyana ga aikinsa Dan duk wasu ayyukansa da meetings dinsa na watan kusan duka yayi postponing dinsu sbd kwanakin Yana samun matasalar saurare a bangaren aikin shiyasa ya tsayar.
Batareda tsayawa neman bayanin kowaba yasa aka Zo aka zubawa sashen sabbin royal furnitures masu kyau da tsari saidai har lokacin Amatu takasa tsayawa dashi ko Magana suyi tun Yana daukar Muhammad Yana zuwa dashi harya Bari kada ya kwashi sanyi da yawa
Zaune yake Yana duba wayarsa hankalinsa gabaki daya baya Kan wayar Yana wani gurin..
Fitowa tayi daga dakinta cikin Dan adonta na riga da skirt na atampar data Dan fitar da qaramin cikinta daya Fara Dan turowa ta kallesa tana nazarinsa tsawon lokaci kafin ta sauke numfashi ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko Masa lemondrink da cup ta Dora Kan tray ta dawo takawo gabansa ta ajiye tareda zama gefensa ahankali tana budewa ta zuba Masa ta miqa Masa ahankali tareda Kiran sunansa cikin sanyin murya.
Waiwayo yayi ya kalleta tareda kallon kwalliyar jikinta datai Masa ya karbi drink din Yana qaqalo sahirtaccen murmushi ahankali yace"
Thank you and you look great.
Kurbawa yayi ya ajiye Yana kashe wayarsa gabaki daya ya ajiye ya qara daukar drink din yanasha harya shanye ya ajiye cup din yasake Dan juyowa ya kalleta Yakuma cewa''
Thank you"Yana maida kallonsa kan TV Yana kallon news.
Jinjina Masa Kai tayi tareda fuskantarsa gabaki tana jinjina qarfin Rai irin na MAHMOUD din dayake dannewa da boyewar abindake ransa kamar yanda ya Saba boye al'amura saidai yanxu wannan damuwar ta dabance Dan itadake taredashi tana iya hango damuwa ataredashi.
Numfashi takuma saukewa akaro na biyu