Showing 15001 words to 18000 words out of 108527 words
basa yadawo muku dasu ko?? Tafada tana dauke kudin tana sakawa jaka ta zura takalmanta tana cewa''
Acikin minti biyar kudi yayi aikin dana fi sati inayi Amma sun kasa fahimtata.
Adaidaita 'daya suka shiga suna Isa station din atake ya janye qarar tabiya kudin beli da tarar me shago dubu talatin kafin aka Basu usi din sukayo gida.
Tun a hanya tafe suke cikin adaidaita Amma batace qalaba tayi nisa sosai cikin tunani,
Ta gaji da wannan masifar ta kullum suna police ko gidan yari,
Duk yanda taso Hana USI rigima takasa sbd da rigimar sukeci suke Sha suke rayuwa,
Baya tunanin kansa sai nata danasu kawu,
Dukkanin aikin datakeyi tana ajewa shine yake samo matasu shi ya gammaci rigimar Amma dai ita yafison tayi aiki,
A iya saninta usi ya fison shi yayi satar a rufesa akan tayi shiyasa yaketa shiga rigingimu Yana kawowa gidan kafin lokacin albashinta
Ga kawu maganarma ace yayi sanaa Bata tasoba sbd tsufa daya taso Masa bama zai iyaba musamman tun zamansa gidan yari wahala ta cinye Rabin qarfin qafafunsa shiyasa yanzu yake Dan fama dasu,
Babban mafitar datake gano musu ayanzu itace usi dayake namiji yasamu yayi karatu yasamu damar daukar dawainiyarsu Nan gaba itadai karatu baya gabanta shiyasa duk burinsu itada kawu ya qare akan Usin yayi karatu Amma Abu ya gagara komai sai qara lalace musu yakeyi.
Koda suka Isa gida jiki a sanyaye kowannensu yashigo ita dakinta ma ta wuce Kai tsaye
Kawu ma haka
Usin ne dai iyami ta zaunar tareda dauko ruwan zafin data Dora na jiran tsammanin Abinda zaa dafa suci ta gaggasa Masa fuskarsa da wuyansa da bayansa dasuka kukkunbura sbd duka da tsamin dasukayi.
Haka suka kwana dukkaninsu Babu Wanda yaci abinci bayan usi da maman junior takawowa taiba yaci sbd lurada basuda abincin ci
Dama Kuma dabi'ar jama'ar gidance taimakon juna duk da irin zaman fitinar dasuke yi idan sunga juna a matsi suna taimakawa junansu sai dai idan masifar ta tashi akwana a yini anayi.
Washe gari sauran canjin hannunta dasuka rage dubu biyar da dari uku su ta bawa iyami dubu biyo aka siyo musu waina sukaci sauran Kuma ayi dubarar abinyi tayi Shirin fita aiki tasa Usin ya shirya tafadawa iyami idan kawu ya tashi asibiti zata Kai usi sbd dukkanin raunikansa sun kumbura sosai ga yankan kwalba a gefen cikinsa gwara suje asibiti tun wuri.
Ganin kudin hannunta nada dama Dama yasa suka nufi wani babban private asibiti dake hanyar gurin aikinta ta baya cikin sa'a kuwa suna zuwa ba layi aka Basu izinin shiga.
Usin ne a gaba tana bayansa fuskarta fayau ba wata walwala ayau sbd tunanin raunikan na Usin kada wata matsala ta biyo baya.
Doguwar rigace a jikinta irin ta gwanjon indiyawa din Nan sbd tana doguwa sai sukai Mata kyau gashi Dan hijabinta na iya wuya ne na uniform din aikinta.
Sanyin AC da qamshin office din yasa ta lumshe ido tareda sakin murmushi tana kallon Usi dashima dadin sanyin AC din yasashi sakin murmushi Yana kallonta qasa qasa tace"
Usi karkayi saurin bashi amsa idan ya tambayeka Dan mu samu mu more sanyin AC dinnan na kwana biyu bansamesa ba sbd banje aikiba
Kodan AC bazanyi saurin aje aikin blue fox ba.
Gyaran murya doctor din yayi sukai saurin kallon inda yake zaune cikin fararen kaftans dasukayiwa kyakkyawar fatarsa kyau fuskarsa daukeda wani sahirtaccen murmushin dayasa amatu bude baki akaro na biyu dataga kyakkyawan namiji Mai wata irin Kamala da kwarjini saidai wancan din nasu insfector Garba ba murmushi a fuskarsa saima wani irin izza Mai bada tsoro sabanin wannan da kyakkyawan murmushinsa yaqara kyakkyawar fuskarsa kyau,
Tasaba da ganin irinsu insfector Garba dasu Sargent salisu da manager dinsu dasukeda fuskoki kamar tuwon daya tashi shiyasa yanzu take ganin wannan amatsayin kyakkyawan dayafi kowa.
Fadada murmushinsa yayi har haqoransa suka bayyana Yana kallon fuskarta sbd yaji Abinda suke fada yace"
Bismillah to Nima bazan tambayeka da wuri dinba.
Sosa Kai usi gayi Yana cewa''
Kyaleta Wasa takeyi likita.
Kallonta yasakeyi akaro na hudu yana qara fadada murmushinsa yace"
To kema Bismillah zoki zauna.
Qarasowa tayi ta zauna tana kallon sunansa da aka maqala a table dinsa DR KHALIL ZABEERA.
murmushi tasaki tana fadan sunan a hankali sbd hada kalmomin Dan karatun nata sai ahankali.
#mamuh#
_________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.
______________________
#MIN QALB❤️
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[01/06, 8:52 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MIN QALB 9_*
_mamuhgee_
Gabaki 'daya hankalinsa nakan fuskar amatu da ita Kuma hankalinta nakan usi da akewa dressing raunikansa bayan an wanke Masa hadda 'dinki Saida akai Masa a inda kwalba ta fasashi.
Sakin murmushi ganin yanda takeyi kamar ciwon ne ajikinta tanata yamutsa fuska tana cewa"
Usi daga yanxu ko sunan Luna nasake ji abakinka nice zanmaka dukanda ko kawu bazai iya ganekaba bare iyami,
Yanxu duba kaga yanda kakejin azaba
Shima wancan kabirun nasa Amin maganinsu Dan na aika buge katangar bayinsu ta bayan gidansu ta yanda duk kudin dasuka karba zai qare a gyara kaikuma....
Cikin 'yar qaramar dariya ya katseta Yana kallonta cikin burgewa yace"
AMATULLAH antyn Usman ki kwantarda hankalinki Usman is perfectly fine,ba gashinan angama dressing ba shikenan kawai magani zai ringa Sha yanzu daganan raunikan zasu warke Suma.
Kallonsa tayi tareda kallon Usi dake cewa'"
Likita bafa antyna bace qanwatace.
Duka takai Masa da Jakarta tana cewa"
Kaine zakaita zama qani ako yaushe Dan haka kayi Mana shiru agurin
Ina sake ganinka da kabiru nice zan dawo maka da duka raunikan nan sababbi.
Dafe dinkinsa yayi da sauri Yana cewa'"
Wayyo amah jini na fita dinkin ya warwa.....
Da sauri ta durqusa cikin firgici tana qoqarin Kai hannu tana cewa"
Dagaske?
Mun shiga uku,
Likita Zo ka duba Mana...
Dariya Dr Khalil zabeera yayi Yana kallon firgicinta dayasa takasa tsayawa ta lura usi din tsokanarta yakeyi ya kalli usi Yana cewa'"
Usman ka daina 'dagawa AMATULLAH hankali ko na saka a warware dinkin Nan ayi maka sabo yanzu.
Dariya usi din kewa amatun Yana qoqarin miqewa sbd dukan datake Masa da Jakarta sbd sosai ya fifgitata Dan sanin Babu Abinda take tsananin tsoro kamar wani abu ya samu Usin.
Takardar maganin daya rubuta musu ya miqawa amatun Yana cewa'"
Ga maganin dazai ringa Sha Nan bayan sati daya saiku dawo mu warware dinkin ko?¿
Karba tayi tareda kallon fuskarsa dake yalwace da murmushin dake qayatar da ita tace"
Mungode likita.
Girgiza Mata Kai yayi Yana cewa'"
Ki kula da kanki ba USI kawai ba AMATULLAH.
Qoqarin fitowa sukeyi nurse dinda yayiwa usi dinki na shigowa ya miqa musu takarda yana cewa"
Yawwa ga wannan zakuje ku biya kafin ku wuce.
Karba amatu tayi suna kallon juna da USI ta duba ita batama gane Abinda ke rubuce ba ta miqawa Usin tana cewa"
Duba kaga Abinda sukace aje abiya din.
Karba yayi yana duba takardar Yana qoqarin hada kalmomin turancin Amma sunqi jaduwa ya duba gurin da akasa kudin yaga anyi 9 da zero hudu ya zato Ido da sauri Yana rawar murya yace"
Dubu casa'innn....
Mene?????ta fada da qarfi tana fizge takardar da sauri ta duba gurin kudin taga 9000 ta hadiye mugun yawu tana cewa"
Basuda hankaline??
Kuskure dai sukayi muje yayi Mana bayani
Dubu casa'in saikace fatarka suka sauya maka gaba daya tsabar gyara raunika.
Dr Khalil dake jinsu tun ayanda ya lura basuda wani ilimin bokon yasan ansamu rashin fahimta gurin duba kudin yaji sun sake burgesa ya taso yabi bayansu zuwa gurin biyan kudin.
Suna Isa amatu ta ajiyewa cashier takardar tana cewa"
Oga wannan dubu casa'in din da aka rubuto ta waye??
An Mana musayar takarda duba kagani.
Yanda tayi maganar yasa saurayin dagowa ya kalleta a wulaqance yace"
Malama takarda indai Kai aka bawa to Babu maganar kuskure idan biya zakuyi ku biya,idan kuna mamakin Abinda aka rubutane to wayace kuzo Nan da saiku tafi asibitin gwamnati.
Yanda yayi Masu maganar yasasu quluwa dama amatun a qule take da kudin cikin takardar kallon walaqanci tamasa tana cewa'
Kai Karen asibiti karkace zaka gaya Mana magana anan gurin
Da kake maganar asibitin gwamnati idan har irinku zasuzo Nan suyi Karen asibiti mezaisa muma bazamu zoba???
Miqewa yayi tareda fitowa ya zagayo gabansu Yana nunata da yatsa Yana cewa'"
Kisan Abinda zaki fada Nan bama tolerating 'yan iska irink.....
Saukar mari yaji daga sama kafin yakai qarshen maganarsa
A gigice ya dago usi ya cakumosa Yana cewa"
Bayan wannan Marin har kamanni zan sauya maka duk bakinka yasake furtawa 'yar uwata wannan kalmar.
Da sauri mutane dasuka Ankara sukayo kansu ana qoqarin rabasu Koda Dr Khalil ya iso gurin harya 'dan cika abin ya girmama da sauri ya qaraso gurin Yana zuwa ya kalli usi cikin tausasa murya yace"
Usman sakeshi.
Dakinda USI yayi Yana cewa'"
Ka iya bakinka wannan tafi qarfin ko uwarka.
A harzuqe saurayin ya taso Dr Khalil yayi Masa wani mugun kallon dayasashi dakatawa Yana huci yace"
Dr wainnan 'yan iskan.....
Shut up""Dr khalil yace da Dan fada Yana cewa'"
Jafar koma gurin aikin and everyone should leave from here please.
Da sauri kowa ya watse Yana mamakin Dr Khalil daya marawa wainnan baya maimakon staff dinsa.
Bayan kowa ya watse ya kalle Usman da har lokacin ransa zafi yake da kalmar 'yar iskar da aka Kira amatu da ita yace"
Usman this is not how to behave with people musamman wainda kasama gurin aikinsu,
Meye abin fada anan infact meyema matsalar??
Kallon Usi amatu tayi tareda sakin murmushi danta saka ya sauko tace"
Kai usi meye na wani fada tun bamu biya wannan kudin da ake fada akai ba zakayi wani fadan kaji rauni kasa kawu ya cinyeni 'danyata.
Kallonta yayi a raunane zaiyi magana tasaki murmushi tana ce Masa"
Karka damu ka manta bama saka maganar kowa aranmu sbd bamuda abin damuwa,
Duk sunanda zai kirani dashi tunda dai banida Wanda hakan zai zubar Masa da mutunci to meyene aciki?
Kawu ne Kuma Shima zagi da maganar kowa Bata tabasa Dan haka barsu su kirani da kowane suna baya damuna,
Usi Kaine damuwata Dan Allah ka daina shiga rigimarda zata saka a hadari,
Ka manta munada burin cikawa na zama alhazai" ta qarasa fada tana dariya sbd Shima ya sake.
Sakin fuska yayi Yana cewa'
Muje nidai.
Tunda suka Fara magana yake kallonsu cikin wani irin yanayi yanason fahimtar zancensu dakeson nuni da su din marayune.
Gyaran murya yayi tareda gyara tsayuwarsa Yana miqa Mata hannu yace'"
Bani takardar kudin mugani.
Miqa Masa tayi tana shafawa idonta toka tace"
Dr mudai wannan kudin da aka rubuta mu biya bazamu iya biyansu ba sunyi yawa ni banma taba Kai qirqen casa'in ba a lissafin kudi
Ni ko inadasu bazan bayarba wlh ba kawuba koni bazan iya barciba duk ranarda nabayar dasu.
Murmushi yasaki sbd dama yasan za'a Rina ya kalleta yana cewa"
Basaikin kasa bacci ba AMATULLAH dubu Tara ne a rubuce ba dubu casa'in ba.
Kallonsa tayi da sauri tana karban takardan da sauri tana sake dubawa tana bin numbobin dakyau tace"
Eh hakane kuwa..
Dagowa tayi tana kallon Usi cikin masifa zata Fara magana yayi saurin cewa'"
Yi yi hakuri da masifar Inaga banduba daidai bane kokuma ban fahimta bane.
Hadiye masifar tayi tana cewa'"
Usi rashin karatun Nan saiyasa an dauremu wata Rana.
Dariya sukayi atare kafin ta kalli Dr khalil tace"
Dr ai maganar gskia ko dubu Taran Nan bazan iya biyaba zandai biya dubu biyu idan zaa karba.
Kallonta ya shagala da yi tana sake burgesa yace"
Usman kanada 'yar uwa anan,
Kawun Nan Shima yanada 'ya anan.
Murmushi tayi tana dauke ido daga wallet dinsa daya 'dan fito da aljihunsa daga gani Kuma tasan bazai rasa kudiba aciki Amma sbd kirkin Dr din tanata dauke ido akai sbd hakurinta yakusa qarewa takaiwa wallet din Hari.
Zaro wallet din yayi ya bude yaciro ATM dinsa ya miqawa cashier ta window tareda takardarsu yace acire.
Bayan ancire aka miqo Masa receipt ya miqawa amatu receipt din Yana cewa'"
Shikenan har dubu biyunki anbar Miki AMATULLAH.
Karba tayi ba wata kunya a idonta tace"
Aikuwa ka kyauta Mana Dan akan dubu Taran Nan nafison na kwana 'daya a station da safe na fito nayi gida da dubu Tara ta.
Girgiza Kai yayi Yana murmushi harsuka wuce Yana binta da kallo zuciyarsa na karban baqon yanayin dake shigarta akaro na farko da mace ta sauya bugun zuciyarsa a ganin farko.
Suna fita ya koma office dinsa yasa Akira Masa daya daga cikin nurses dinsu dayaji Yana fadin yasansu amatun lokacinda ake fadan dazu
Yana buqatar sanin inda suke.
##mamuh#
_________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.
______________________
#MIN QALB❤️
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[01/06, 8:52 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MIN QALB 10_*
_mamuhgee_
Suna fitowa daga asibitin gurin aikinta suka nufa ya ajiyeta da adaidaita kafin shi yawuce gida,
Babban Abinda yasa yau tazo aikin shine Jin ko hajiyar Nan tazo nemanta sbd yanzu dai Kam tana buqatar ganinta kodan Abinda yafaru yau na rashin ilimin dasukedashi sosai yasa taqarajin buqatar karatun nasu Amma dai yanzu na usi ne agaba.
Da manager tafara haduwa a reception din blue fox din tana ganin ya washe Mata baki ta tsuke fuska tana cewa"
Wannan Dan wahalar zai Fara damuna yanzu da surutansa wainda basuda amfani aguna,.
Yana qarasowa itama ta washe Masa baki da gayya tana cewa'"
Manager sannu da yawo.
Washe baki yasake yi Yana shaga dogon kansa yace"
Amah 'yan amata ya aikin?¿ Sai yanzu Kika shigo?
Eh sai yanzu nashigo na yagi robana daya wuceni kwana biyu.
Me Kika??
Aa cewa nayi nayi latti Bari naje kafin a nemeni.
Tana fadar haka ta wuce tana cewa''
Kuje kuga gayu da wayewa gurin Dr
Amma kunzo kaida insfector Garba bansan Waye haqoransa sukafi na wani dafewa ba.
Tana shiga saloon madam bell ta kalleta cikeda mamaki tana cewa"
Amah sai yau kikaga Daman zuwa aikin???
Ta gefen ido ta watsawa madam din mugun kallo kafin tace"
Madam lalurace ta hanani zuwa ba ganin dama ba.
Bude Ido madam tayi tana cewa"
Ni kike wa magana haka?
Dauke Kai tayi tai qasa qasa da murya tace"
Ke din uwatace?
Me kike cewa amahhh?
'dan washe baki tayi cikin gatse tace"
Cewa nayi sorry madam.
Qwafa tayi sbd taji Abinda amatun tafada da farko tace"
To ki tafiyarki kawai Dan anyi replacing dinki da wata.
Kallon baibai tayi Mata tana cewa"
Madam korata kikayi ne?
Eh" madam din tafada Kai tsaye tana cigabada da aikin datakeyi.
To Ina tayaki murna madam bansan an maidake manager ba da bana nan.
Aje Abinda takeyi tayi tana yiwa amatun kallon mamaki sbd tasan baqar Magana ce ta jeho Mata wato tunda ba itace manager ba bazata iya korarta ba.
Amatu na ganin ta kunnata ta gyara tsayuwarta zata sake wata maganar aka bude qofar shigowa ana cewa" welcome ma.
Madam ce tayi saurin aje towel din hannunta tana nufar qofar bakinta a washe tana cewa'
Welcome ma.
Gyara tsayuwa amatu tayi batareda ta juyaba Kuma batada alamar juyawar
Taji ankira sunanta
Da sauri ta juyo sbd ta 'dau muryar
Aikuwa ita din ce ta qarasa gabanta tana kallon madam bell tasaki yaqen tura haushi tace"
Madam dama bankwana nazo Miki tareda tayaki murnar samun matsayin manager Dan haka Allah ya sanya alkairi.
Kallon hajiya aisha tayi tana qaqalo murmushi tace"
Haj Mama Ina kwana???
Murmushin mamakinta umme tasaki tareda kallon madam bell tace"
Dama ita nazo nema sai dai next time idan nadawo,amah muje ko???
Gaba amah tayi tana murmushin farin cikin daga yau rayuwarsu zata canja idan har hajiya mama tabata sabon aikin datake cewa.
Motar haj Aisha din suka shiga wani sanyin AC da qamshin ya ratsata ta lumshe ido tareda shafa kujerar motar datajita da wani irin laushi da santsi,
Yaune karo na farko a rayuwarta data taba shiga motar Dana taxi ba ko taxi din tafi shekara goma rabonta datashiga.
Kallon motar takeyi tako Ina tana tabawa ta kasa 6oye farin cikin datake ciki a fili tace"
Hajiya mama ko ahaka Kika barni kincikamin qaramin burina....
Dauke Kai haj Aisha tayi cikin gundura da amatun tun yanzu tace"
Motarma gaba daya zata iya zama mallakinki ko 'dan uwanki usi da Wanda ma ya tsinceku idan har zakiyi Abinda nakeso Wanda a wata biyar kingama aikinki Kuma kin mallaki Abinda zakiyi hannun riga da talauci.
Parking motar tayi daidai kwanar gidansu amatun Wanda yasata juyowa ta kalleta ta yanda tasan gidansu zatayi magana hajiya aishan ta katseta Kai tsaye da cewa"
Zan baki naira miliyan uku tareda makaranta me tsada wa 'dan uwanki harya gama sai gidan zama me kyau ga kawunki da jarin sana'a me kyau ga matar kawunki idan har zakimin Abinda nakeso.
Suman zaune amatu tayi tareda sakin baki gaba daya ta daga hannu tana lissafa abubuwan da hajiyar tace har lissafinta ya 6ata tayi saurin girgiza Kai tana 'dan dukan kanta tace"
Amatu amatu amatu dawo kanki... Dawo kanki.....
Hajiya mama duka abubuwan Nan dakika fada saidai naji kokuwa kunnuwanane????
Qaramin tsoki umme tasaki tareda bude wata 'yar jaka dake daukeda kudi dubu 'dari uku ta miqa Mata tana cewa"
Kije kibawa su kawunki wannan idan kingama aikin zanbaki dukannin Abinda nace
Qaninki kuwa zanbaki takardun makarantarsa ki riqe a hannunki.
Da sauri ta karba kudin ta shafa cikin zaquwa take cewa"
Wannan yanxu duk nawane halak malak??
Hajiya mama na amince zanmiki aikinki koma wane iri ne na shekara biyarma zanmiki bana wata biyar ba.
Kallon takaici umme tai Mata tana mamakinta saidai duba da 'yar tashace Kuma 'yar bola hakan ba wane abin mamaki bane Dan duka tarihinsu tasamu agurin binciken datasa