Showing 84001 words to 87000 words out of 108527 words
MD din banbanci nata na Mata nashi na maza hakama budewar wuyan rigar Amatun yasa taji tana kamo nata tana rufewa sbd Abinda taji Yana danne maqoshinta Kai tsaye ta kashe Kiran da kanta tana barin hawayenta saukowa ta kife Kan gadon datake zaune tareda fashewa da wani irin kuka Mai ciwo.
Su kuwa can Amatun ce tafara sakinsa ta sauka daga Kan jikinsa tana qin kallonsa sbd yanda taji hankalinta ya tashi da yanda anty zarah ta gansu wani bangaren na zuciyarta Kuma wani irin nauyi takeji saitaji gurin ya gundureta ma gaba daya ta wuce batareda tacewa kowa komaiba.
Washe gari Koda qarfe dayan Rana tayi sundawo harsunyi Shirin zuwa asibiti sbd ranar ne ranar sallamar Muhammad shiyasa duk damuwarta ta kau cikin tsananin farin ciki take su umme ma sunyi waya zasu hade a asibitin gurin daukosa sbd zumudi tarigasa fitowa Yana saukowa suka fada mota suka nufi asibitin.
Koda suka Isa sun tarardasu umme
Kallo daya umme tai Mata tasan komai yafara daidaituwa sbd yanayin 'yar walwalarta daya Fara dawowa.
Bayan dogon formalities aka sallamesa aka Basu dansu murna agurin kowannensu ba'a mgn saidai anbasu kakkauran sharadin kada aringa barinsa sanyi na shigarsa sosai sukace sunji.
A gida sasai aka ringa kiransu ana murnar samun nasara saidai anhana ashigo jirgi dashi saiyayi qwari sosai yasamu lafiya shiyasa ana sake kwana biyu umme ta tahowarta shima MAHMOUD din wata tafiya takamashi aka bar Mata anty salamatu.
Ahankali suka Saba da zaman qasar da Jin Dadinta tareda Fara sanin gurare Dan suke Kai kansu siyayya da sauran wasu abubuwan musamman dasu meenat Suma sundawo garin saita haihu zasu koma,
Ga Muhammad tuni ya warware yayi girma abinsa yanzu Yana samun nono koyaushe take ya canza yafara girma gashi hadda jiki sosai yayi gwanin sha'awa,
MD na kiranta lokuta da dama Amma iyakacinsu gaisuwa sai ya tambayi Muhammad wani lokacin ma anty salamatu yafi Kira.
Abu daya ne matsalarsu a garin shine rashin turancin arziki tayiwa kawu mgn saigashi kawu yaje har zabeera da kansa yayiwa su Andi tunin alqawarinsu na barinta karatu Allah yasa MAHMOUD din na Nan sai sukai Masa maganar yasanyata makaranta acan da zaman banzar.
Tunda anty zarah taji tafiya zaiyi zuwa Greece taji hankalinta nason tashi Amma ta danne sbd ba laifi ya Dade sosai a gida wannan karon saita danne harda saqon gaisuwarta ga Amatu sbd har yanxu tunda akai auren basuyi mgn ba sbd kowa bai Gama daidaituwa da al'amarin ba.
Zaune suke a Palo itada Muhammad dake koyan zama anty salamatu Bata Nan taje gidan meenat dake Dan zazzabi sosai ta tayata hidima.
Riga da guntun skirt ne ajikinta Wanda bai kamata ba ko kadan sai hular babies dake kanta Bata Gama rufe Mata gashin Kai ba Wasa takewa Muhammad sosai Yana dariya taji bude qofa batareda anyi knocking ba ta juyo da sauri cikin mamaki sai idonta ya gane Mata shi batasan lokacinda ta saki baki ba tana kallonsa da dukkanin zuciyarta.
Shima ita din yake kallo yanda Takoma kamar wata yarinya qarama Babu me cewa itace uwar yaron gabanta tafi Kama da yayarsa ta kusa bama ta nesa ba.
Muhammad dake bangala dariya ya kalla har baisan lokacinda ya sakar Masa kyakkyawan murmushi ba yana nufosu.
daukarsa yayi Yana kallonsa cikin tsananin qaunar yaron yace"
Muhammad you're looking great and handsome.
Kallonta yayi ta sauke kanta tana cewa''
Sannu da zuwa.
Bai amsaba bai Kuma dauke idonsa akantaba saima kissing Muhammad da yayi a fuska Yana cewa''
Thank you.
Bedroom dinsa ya nufa daukeda Muhammad Yana cewa''
Ko Zaki gyaramin dakin bazai rasa quraba.
Bayansa tabi da kallo tana mamakin kyawun daya qaro da wani irin haske
Kodan ta Dade Bata gansabane.
Akwatinsa ta tura zuwa dakin nasa ta kallo sbd shine shigarta na farko
Dakin komai na cikinsa farine Wanda ta fahimci shi din yanason farin Abu ta dauko mop da bucket da sweeper ta a ajiye tafara gyaran dakin bayan ta sauya Masa zanin gadon ta goge komai Yana palo tafito Bayan tagama komai ta karbi Muhammad ya wuce bedroom.
Da daddare Koda anty salamatu tadawo ta tararda zuwansa tunda tashige daki Bata sake fitowaba Saida safe shima tana Gama shirya musu komai ta wuce gidan meenat sbd zasu sake komawa asibiti da ita yau.
Dakansa ya dauketa yaje ya Samar Mata admission da komai na makaranta ya damqa Mata daga can gidansu meenat sukaje dubata.
Dagacan gurin cin abinci suka biya sukaci kafin suka dawo gida.
Kwanansa takwas a qasar kafin yatafi da kewar Muhammad daya shaqu dashi cikin kwanaki qalilan Dan kullum a hannunsa yake Rabin kwana sai dare sosai yake maidasa hannun mamansa.
Itama bayan tafiyarsa yabarsu da kewarsa sbd kwanakin kullum Muhammad na taredashi.
Sosai ta nitsa cikin karatunta gadan gadan musamman dayake me wuyane karatun sbd medical ne tana karantar gynecology sai yazamto hankalinta nakan karatu yanzu fiyeda komai,
USI yazo Mata tareda Dr Salman har so biyu Wanda yasata Jin Dadi fiyeda tunani musamman usi daya dauki Muhammad a hannunsa ji yayi kamar zai hadiyesa sbd so da qauna,
Kawu da iyami ma kullum cikin waya suke Gama umme Anty zarah ce dai har yanzu ba wani sauyi sbd takirata har so kusan uku Bata taba daukar wayarta ba shiyasa ta Dan dakata tukuna.
Ta bangaren MAHMOUD ZABEERA kuwa Babu wani sauyi a rayuwarsu saina qaunarsu data zama kamar daya akan 'dansu sbd tunda Muhammad yayi wayon sanin babansa yake zuwar musu akai akai sbd yaron dako yaushe dadynsa yakeson gani Dan tuni yayi wayo sosai Dan kusan shekararsa biyu kenan harda watanni.
Duk Wanda yasanta abaya yanzu bazai iya ganetaba idanba farin sani kayi mataba,
Ta sauya sosai daga Amatun blue fox Takoma AMATULLAH zabeera,
Sam halayyarta da yanayinta sun sauya,
Yanzu ita mace ce me nutsuwa da Kamala,
Mace ce me aji da ilimin Boko ya shigeta yake Kuma bayyane atareda ita sbd ko zaman awa daya kayi da ita zaka fahimci da likita kake zaune musamman gashi suna shekarar qarshe ta kammala karatunta,
Amatse take data samu hutun wannan shekarar taje gida sbd tayi masifar kewar iyayenta Dan tunda tazo bataje gida ba
Har gwara anty salamatu taje gida harta Dade sosai kafin tadawo gashi ko yanzu tana Shirin zuwa ganin gida Kuma tareda Muhammad zataje wannan karon,
Ga USI ma yagama karatunsa yanzu yadan Fara aiki a asibitin zabeera.
Yau su Anty salamatu da Muhammad suka wuce tana dawowa daga rakiyarsu airport ta shige daki ta tube tayi wanka tana fitowa ta sanya three-quarter pink da farar riga Mara nauyi ta daure gashinta da band ta saka qaramar hula ta nufi kicin ta hado flakes da sabuwar madarar ruwa me sanyi ta fito Palo tanasha taji ana qoqarin bude qofa Kai tsaye tasan MD ZABEERA ne ya shigo qasar sbd tasaba da duk zuwansa saidai suji bude qofarsa kawai baya knocking kamar sauran baqi.
Juyowa tayi gaba dayanta daukeda mug din hannunta ta kallesa da fararen idanuwanta kafin ta qyafta idonta saiga anty zarah ta fito daga bayansa tana shigowa tareda rufe qofar take kofin hannunta yaso kubucewa tayi saurin taresa hannunta na rawa.
##Mamuh#
[01/06, 8:45 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MQ 41_*
*_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku da Allah idan kunada rabo Allah ya shiryeku_*
Wani irin bugu zuciyarta keyi me qarfi da sauri hannuwanta na Yar rawa take kallon anty zarah din da akwatinta datake janye dashi batasan lokacinda wani qarfin hali da juriya suka shigeta ba ta qaqalo wani talwataccen murmushi tana ajiye cup din hannunta ta nufi anty zarah din da itama tafi Amatun dauke wuta tana cewa''
Anty zarah sannu da zuwan bazata.
Duk yanda anty zarah din taso Nemo qaqalo murmushi ta nema ta rasa sai kawai ta 'dan washe baki Wanda kowa yagani yasan yaqene Tace"
Amatu sannu da gida mun sameku lfy?
Akwatinta Amatun ta karba tana qarasa shigo Mata dashi ciki tana cewa''
Alhamdulillah anty.
Rasa abinyi tayi sbd ruden datake duk da ba'a iya ganewa sai kawai ta nufi kicin ta hado drinks da snacks a tray ta fito dasu tana 'dan satar kallon inda ya zauna Yana sauya layinsa zuwa na qasar ahankali ta ajiye tray din gabansu tace"
Dady sannu da zuwa.
Qwarewa anty zarah tayi da ruwan data zuba bakinta duk suka juyo suka kalleta bandashi daya dauke Kai baima Gama juyowarba tace sannu anty ko ruwan yayi sanyi ne da yawa.
Batareda ya kalletaba yace"
Ki gyaramin dakin and kiban keys din motarki zan fita urgent.
Miqewa tayi tana Dan Jin wani iri ta nufi dakinta ta dauko Masa keys din ta miqa Masa ya fice ta juyo ta kalli anty zarah datai saurin dauke Ido daga kallon datake Binsu dashi tace"
Anty zarah Bari nakai Miki kayan dayan dakin tunda anty salamatun ma Bata Nan kafin agyara nasa dakin saiki koma can ki shigo kiyi sallah ki huta idan nagama saina Dora dinner.
Batareda tace komaiba ta miqe tabi Amatun har cikin dakin ta ajiye Mata akwatinta tareda ficewa tana cewa''
Ina zuwa anty idan akwai Abinda za'a yi Miki ki kirani.
Tana fitowa dakin ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya tareda dafe qirjinta tana Kiran sunan Allah.
Itama anty zarah Amatun ta fita ta sauke numfashi me qarfi tana cewa''
Ya Salam.
Daukar akwatinsa tayi ta nufi dakinsa ta ita ta ajiye kafin tafara aikin gyaran dakin tanayi tana sauke ajiyar zuciya akai akai.
Tana gamawa Ta nufi kicin ta Dora girkin pasta da cabbage source me kidney aciki.
Har lokacin sallar magriba tayi Bata kammala ba sai guraren 7 ta Gama ta jere a dining ta nufi bedroom dinta ta fada wanka sbd ta 'dan gaji.
Sallah tafarayi bayan tafito wanka kafin ta sanya doguwar English gown Mara nauyi kwata kwata black ta sanya hula ta fito cin abinci.
Tana fitowa Yana dawowa amatuqar gajiye yake Dan haka Kai tsaye ya nufi dakinsa Yana cewa takai Masa abinci can Yana Jin yunwa.
Nata tafara zubawa taci ta qoshi tsaf abinta kafin ta hada nasa a tray tareda komai ta nufi hanyar bedroom din nasa tanayin knocking yabude Mata sbd tunanin da Kaya a hannunta sai gashi kuwa hannunta dauke yakeda tray
Daure yakeda towel zaishiga wanka kenan yaji buga qofarta shiyasa ya bude matan.
Kallo daya tai Masa ta dauke Kai ta nufi table ta ajiye abincin tana cewa''
Ko amaida ne saika fito wankan Dan kada ya huce?
No Bari naci kafin nashiga wankan Ina buqatan abincin zansha magani.
Zaunawa yayi yafara cin abincin a natse ga ciwon Kai dake matuqar damunsa sbd stress ta juya zata fice yace"
Zansha magani Ina buqatan ruwa.
Fitowa tayi Dan dauko Masa sai kawai taga anty zarah zaune a Kan dining turuss ta tsaya wata irin kunya da nauyi yasa takasa daga qafa saidata ga kamar anty zarah adin hankalinta nakan abinci kafin taja qafafunta daqyar ta nufi kicin ta dauko Masa ruwan saikuma taji takasa fitowa ta tsaya karba ruwa ahankali tana tunanin yanda zatazo ta keta anty zarah ta shige dakinsa.
Jin shiru Bata dawoba gashi yagama ci ruwan yake buqata yasa ya miqe yafito hannunsa daukeda magani
Bai lurada zarah dake zaune tsit ba a dining ya nufi kicin inda yake hango Amatu tsaye tayi nisa a tunani
Tana ganinsa cikin kicin din ayanda tabarosa daki dagashi sai towel ta zaro idanuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta janyosa da qarfi sukai gefen fridge ta bayan qofa Ido waje da firgici tace"
Bakaga anty zarah ba a apalo zaka biyoni Nan Kuma ahaka ba kaya ajikinka me kake tunanin anty zarah zata dauka..
Zuba Mata fararen idanuwansa dasukai laushi yayi Yana kallon tsoron dake bayyane fili akan fuskarta da bakinta dake Magana kafin ahankali ya sauke idanuwansa zuwa kallon hannuwanta dake riqe da qugunsa har hannunta dayama nakan daidai mararsa yaji ahankali gajiyarsa da ciwon kansa na warwarewa ya maido da kallonsa Kan fuskarta ta ankare da inda hannunta yake ta zabura zata janye ya riqeta Yana matseta da bango ga idanuwansa dasuka qarasa hargitsata ta bude baki ahankali murya na rawa tace"
Anty zarah na Palo kartayi tunanin wani Abu dabam.......
Zancenta yasashi sake matseta jikin bangon tayi saurin rintse iso zuciyarta na harbawa tasake bude baki maganarta na fita a rarrabe tace"
Dan Allah anty zarah nake gudun ta.....
Bakinsa kawai taji akan nata sbd firgita batasan lokacinda ta qanqamesa da hannuwanta ba tana rintse Ido da qarfi.
Qarar faduwar plates yasashi saurarawa daga kissing bakinta dayakeyi cikin nutsuwa ya saketa batareda ya kalli kowaccensuba yabar kicin din Dan yasan zarah tariga taga komai yasamu kansa dajin wani iri kamar nauyintama.
Amatu kuwa rawa jikinta ya dauka tahau rawar murya tana zazzare Ido sbd tsananin kunya ko kallon inda zarah din take bata iya yiba ta durqusa tahau kwashe plates din tana cewa''
Anty zarah Yi hkr wallahi.....
Katseta zarah din tayi cikin wata irin muguwar dauriya da danne kukan dake zuwar Mata tace"
Saida safe zanje na kwanta.
Juyawa tayi tabar gurin tana rufe bakinta sbd kukan dayake Shirin kufce Mata.
Ajiyar zuciya Amatu ta sauke tana miqewa daga durqushen datake tattara kayan ta ajiye tareda barin kicin din itama tana sake tunano Abinda ya wakana tsakaninta da MD ZABEERA.
Tana Shiga daki kwantawa itama tayi tana rufe idanuwanta tana Hana kanta tuno Abinda yafaru Amma kamar bazata hanuba zuciyar.
Washe gari tun 6 tafito tafara aikin breakfast sbd tanada karatun dazasuyi da annah wata qawarta a school.
Potatoe ball da toasted bread me kwai tayi musu sai lemon tea Takoma daki tayi wanka ta shirya cikin blue straight skirt da light blue chiffon top Me Fadi tayi rolling ta fito riqeda handbag dinta tana duba agogo batason tayi latti gashi key din motarta Yana hannunsa gashi da alama be tashiba tunda bataji motsinsa ba.
Zaman jira ta dasa tanayi tana kallon agogo har kusan awa daya sai kawai ta hkr ta miqe ta fice zata hau taxi.
Anty zarah ce tafara fitowa Bayan ta Dade da tafiyarta ma anty zarah din na zama a palon sai gashi yafito a shirye shima da kayan zaman gida ta tashi ta nufesa tana qoqarin Hana shedan Sanya Mata tunanin ko tare yakwana da Amatu ta Dan rungumesa tana qaqalo murmushi tace"
Good morning.
Dafa kanta yayi Yana amsawa kafin suka nufi dining Yana cewa ta dubo Amatu.
Tayita knocking shiru saita bude kawai ta shiga taga Bata Nan taje har qofar toilet din dakin takira sunanta shiru saita tura qofar bayin nanma Bata Nan ganin sanyin toilet din yasa ta fahimci tayi wanka may b ta fita to
Tazo ta fada Masa sai alokacin yayi tunanin may b tawuce makaranta.
Breakfast dinsu sukayi anty zarah ta tattare gurin Bayan sun Gama tadawo gefesa ta zauna tana kallon news taredashi yanayi Yana amsa wayoyi ahankali.
Da Rana ganin sun buqaci abinci yasa anty zarah dafa Masa noodles da kwai itakuma tasake cin sauran breakfast din dasuka rage sbd yafi Mata dadi.
Wanka takuma yowa ta sanyo riga da skirt na atampa tafito tana waya da ummanta dake sake jaddada Mata tayi hkr da dauke Ido akan duk Abinda zai Bata ranta Dan Abinda bakada maganinsa gwara ka rungumi hkr da dauke Ido Dan ita umman batamaso zarah din tabiyosaba da nufin Wai zata Zo duba Muhammad ne sbd tunda aka taho dashi Bata taba ganinsa ba saigashi suna zuwa sukuma suna tafiya.
Zama tayi daidai fitowarsa a shirye kamar fita zaiyi ta miqe tsaye tana Yana kyawu da cikar haibar mijinta Wanda kullum sonsa ke qara Shiga Yana Kama kowane lungu da saqo na zuciyarta..
Gabansa tazo ta tsaya tana kallonsa shima ita din yake kalla ganin irin kallon qurullar datake Masa yasan ba komaine ke dawainiya da itaba sai sonsa sai yaji tausayinta da qaunarta na sake shigarsa ya janyota ahankali ya rungume cikin jikinsa Yana shafa Bayanta ahankali Jin yanda take sauke ajiyar zuciya ta dago kanta ta kalli fuskarsa cikin sanyin murya tace"
I love you so very much MAHMOUD ZABEERA..
Dora bakinsa akan nata yayi ahankali Dan nuna godia ga Abinda tafada din.
Qarar rufe qofa da qarfi dasukaji yasashi dagowa yana kallon qofar shigowar sukai Ido biyu da Amatu dake Masa wani irin kallon tsana zuciyarta na harbawa da qarfi saikuma ta maida kallonta Kan anty zarah da itama takejin wani iri akaro na farko dataji kaman taji kunyar Amatun ta qaqalo murmushi tana basarwa ta qaraso ciki tana saka wayarta cikin handbag tace"
Anty zarah sannu da zaman gida nafita Baki tashiba shiyasa na fice bansanarba gashi ma wallahi lattin danai gudu saidanayi.
Ayya bakomai Nima ai nayi tunanin kinjira banfito da wuri ba.
Hanyar bedroom dinta ta nufa batareda ko inda yake ta kalla ba batama nuna alamar tasan da mutum ba tana cewa''
Bari nashiga ko sallah banyiba wlh.
Kamar bazai kalletaba saikuma ya Dan juya yabi bayanta da kallo kafin ya juyo ya kalli zarah yace suje.
Daki taje ta dauko mayafi da wayarta ko jaka Bata daukaba suka fice.
Tunda tagama sallah tayi wanka ta fito taci abinci take zaune Palo tayi waya dasu iyami,tayi da kawu,tayi da umme,tayi da Dr salman zabeera tayi da USI Wanda sukafi awa suna Magana duk Dan tasamu sauqin Abinda takeji aranta Amma takasa samun salama sai kawai ta kunna TV tafara kallo tana dariyar qarfin hali kamar wata wawuya.
Kallon agogo tayi taga qarfe goma harda minti arba'in ta miqe taje kicin ta hado tea tadawo ta zauna tana durawa cikinta idanuwanta akan kallo.
Goma da Sha daya da minti Tara taji bude qofarsu ta Dan kalli agogo taga lokaci taci gaba da kallonta tana Shan tea suka shigo ta Dan dago ta kalli anty zarah ta saki murmushi tace"
Lah anty Ashe fita kukayi banma Ankara ba wlh na dauka kina ciki kina bacci.
Kallonta yayi da mamaki saidai ko inda yake batada niyyar kalla ta tashi tana cewa''
Anty kawo kayan na riqe Miki.
Ta karbi kayan hannun anty zarah din yakai Mata har dakinta ta fito tana cewa''
Bari naje na kwanta gobema inada zuwa makaranta da safe.
Shigewa tayi ta rufo qofa ta Isa bakin gado ta zauna tareda sauke ajiyar da numfashi me qarfi idanuwanta na cikowa da hawaye batasan lokacinda ta kifeba Tana sakin kukan kewar Dr khalil dinta.
Washe gari ko abincin breakfast qin Yi tayi ta wucewarta makaranta taga keys dinta na mota ya ajiye Mata a palon taqi dauka ta tafiyarta.
Bata dawoba sai yamma tayi shigewarta bayan tashiga har dakin anty zarah sungaisa.
Washe gari ma haka takuma ficewarta ba Wanda yaganta sai abin yazama kamar tana wasan buya dasune Dan tasawa kanta zama very busy kullum Babu me ganinta take fita har gwara idan tadawo sukan gaisa da antyn tata ogan gidan kuwa Sam taqi Bari suga juna tuni kewar su Anty salamatu da Muhammad suka sanyota gaba