Showing 93001 words to 96000 words out of 108527 words
taje har dakin Amatu takirata Amma tayi bugun duniya ko cewa waye Amatun taqiyi bare tasa ran zata bude Mata ganin haka MAHMOUD yace tadawowarta tazo taci abinci Tasha maganin taje ta kwanta tana buqatar hutu,
Yasan masifa da rigimar dake cin Amatun shiyasa shima bazai shige mataba duk da yayi matuqar kewarta Amma rigimarta har fargaba take sakashi Sam bayason tashin hankali musamman yanxu da zarah Allah yabata Abinda takeso bayan shekarun jira masu tsayi,
Harga Allah shi baisaka damuwar rashin haihuwa aransa ba kodan yataso cikin kadaicinda har yake sha'awa da son rayuwa shikadai ne?
Sai lokacinda aka haifi Muhammad yaji son 'yaya yashigesa Amma dai still bai saka abin a Rai ba zarah ce ta qwallafa Rai ason haihuwa yanxu gashi Allah zai Bata sanin yanda ta dauki alamarin cikinta yasa yake tayata tattalawa da kulawa sbd taji farin ciki Amma wainnan kwanakin a Santorini shikadai yasan yanda yayi su day tunanin yanda Amatu take anan.
Abincin sukaci sama sama kafin ya miqe yashige Yana sake trying numbern Amatu daya Gama tabbatarda blacklist tasanya shi.
Washe gari dukkanin wasu kayanta masu daukuwa ta hadasu a akwatina ta rufe na Shan iskar dazata Sanya yau da gobe kafin jibi ranar tafiyar kawai tabari a waje ta shige toilet tayo brush da wanka tazo tayi sallah Dan tayi lattin tashi ta sanya jeans da baqar cardigan sbd sanyi sanyi datake ji Wanda tasan hadda na zazzabin dayaqi sakinta Wanda a nazarinta kozata daina qananun zazzabi zazzabin saita fita early months dinta na pregnancy.
Fitowa tayi taje cikin ta soya kwai da uban tomato sauce da bread ta dama oat tazauna a qaramin table din kicin din nacin abinci tana breakfast dinta cikin nutsuwa.
Ta windon kicin taji motsinsa yana balcony tasan geamin yakeyi a balcony kullum safe,
Batason ganinsa Dan haka taqarasa cinyewa Dan tabar kicin din Takoma daki sbd Yana gamawa kicin yake yowa direct Dan amfani da ruwan sanyi.
Bata shanye sauran oat dinba ta dauka zata Sanya fridge cikin tsautsayi kofin ya subuce daga hannunta ya fashe oat din ya zube gurin tareda glasses na cup din.
Juyawa tayi zuwa store dauko mop da Abinda zata kwashe glasses din kafin tayi mopping tana cikin tsore din saiga anty zarah tashigo kicin din idanuwanta plates din Kan table da akaci abinci dasu take kallo Bata ankara da abindake qasaba ta taka lokaci daya akai sama sosai da ita tafado da qarfi Kuma ta saki wani razanannen ihun dayasa Amatun fitowa batareda ta dauko Abinda taje daukowa ba.
Cikin sauri tace"
Sorry sorry nice na zubar wlh Bari nakoma na dauko mop sorry...
Juyawa tayi da sauri Takoma daidai shigowarsa ya qaraso gun zarah din da sauri ganin tana juye juye cikin azaba cikin sauri ya riqota Yana kallon fuskarta da tuni ta hada uban zufa yace"
Me wannan abin yakeyi a qasa Kika Fadi?cant you watch where you are going...
Fitowar Amatu da mopa a hannu yasashi dagowa ya kalleta ta dauke Kai tana qoqarin tattara gurin Kai tsaye cikin fada fada yace"
Ta Yaya wannan abun yake zube qasan kicin din?Kai tsaye tace"
Nice na zubar Kuma banzubar ba Dan wani ya Fadi duk Wanda yafadi qaddararsa ce ahaka,
Idan zaka dauketane na tattara gurin to....
Rintse Ido yayi ya bude akanta Yana cewa''
Meyasa kullum kinfison tashin hankali akan zaman lafiya?
Wannan kishin da kike is nothing but madness idan zaki ji haushin wani come to me not my wife sbd itane tafi cancantar wannan madness din not you sbd itace aka aurewa Miji....
Na aka aure mijin inaga ai bani nace a auramin ba sbd Nima inada nawa mijin qaddara ta rabani dashi harna qare anan and idan kanajin ka gaji da da madness dina bana tunanin akwai Wanda yasaka zama Dole Dani infact ma ni nagaji da auren na mijin wata sbd Nima bashine gabana ba Mijina da duk duniya yafimin kowa na Rashi na dangana to waye Zan rasa ban hakura......
Cikin wata irin tsawa data Sanya anty zarah bude idanuwanta ta kallesa cikin tsoro sbd Bata tabajin ya daga murya hakaba kaf zamansu ita ko sa'insa haka Bata taba Jin yayiba idanuwansa na sauya launi da bacin ran kalamanta yace"
Get out of my sight.
Not only your sight am going out of your life gaba daya...
Daqyar anty zarah ta bude baki ahankali tace"
Amatu Dan Allah kiyi shiru meye amfanin tashin hankali....
Hannu ta daga Mata idanuwanta na rufewa tace"
Dashi nake magana sbd shiya kawo zancen,
Kuma tashin hankalin waye yajawo tun farko ayishi?
Muna zaune gida daya muna kwana cikin guri daya gari baitaba wayeba ba banje har dakinki na gaidakiba,
Bantaba fita makaranta ba banzo nace Miki na tafi ba Amma da ciwo ya kamaki nida nake cikin gari baki kirani kin sanar daniba Dan nice akusa saikina Kirasa shida baya gari sbd shine zai baki lafiya nikuma ciwo Zan qara miki,
Daya Kira Yana kirana careless meya Hana ki sanar dashi baki kiraniba kokuma bansan bakida lafiyaba?
Anty zarah Ina ganin girmanki haryanxu so please stay out of this.
Wurgi tayi da mopar Tana ficewa zuciyarta na mugun tafarfasa idanuwanta dasukai jajir suna bushewa.
Su duka kallonta sukeyi shi cikin mamaki da takaicin kansa dayake kasa daukan mataki akanta itakuma anty zarah sai alokacin tasan eh lallai bata kyautaba Amma Kuma itama ba laifinta bane Babu Wanda ya cancanta ta sanarwa batada lafiya bayan mijinta.
Daukar zarah din yayi Wanda sai alokacin su dukan suka lurada jini yafara gangaro Mata batasan lokacinda tasaki wani razanannen kukaba tana qoqarin qwacewa daga jikinsa Dan ta miqe yayi saurin riqota Yana daukarta gabaki daya ya fito ya fice zuwa asibiti da ita lokacin mararta tafara mugun ciwo sosai tuni tafara ficewa hayyacinta ga wani irin hawayen tsoron karta rasa cikinta datakeyi Dan kuka Yama daina fita.
Suna Isa asibitin aka karbeta ya nufi reception ya cika duk wasu formalities ya zauna zaman jira.
For morethan 3hours Yana jira kafin likitocin suka fito suka sanar dashi tayi loosing jini sosai Amma sun samu sun tsayar cikin baiyi komaiba Yana nan saidai akwai yiyuwar zai iya barewa sbd mahaifarta batada qwari ko kadan Dan haka zasu daure Mata sbd kada cikin ya zube.
A asibitin suka yini sai dare sosai akai discharging dinta suka dawo gida duk da taji jiki Amma zuciyarta farin ciki ne fal sbd tunda ta auri MAHMOUD baitaba Bata lokacinsaba bare irin wannan kulawar datake samu a yanzu daga garesa wadda ta tabbatarda bawai Dan tanada ciki bane sbd tun kafin samuwar cikin ya sauya Mata tana samun kulawarsa Wanda tasan ba kowa bace tafara sauyasa qarfi da yaji sai Amatu Dan Nan gaba ma qila abin yafi haka Dan qila har kalmar so zata samu wata ran ya furta Mata.
Murmushi tasakar Masa tana riqo hannunsa ahankali tace"
Thank you.
Batareda ya kalletaba ya Dan jinjina Kai Yana lumshe idanuwansa zuciyarsa gabaki daya batada sukuni har lokacin kalmomin Amatu na dazun akan mijinta daya rasu dashi kansa suna yawo cikin kansa da kunnuwansa ko asibiti zaune kawai yake amma kalmomin suke ihu cikin kansa.
Meyasa zuciyarsa zata kasa sukuni akanta Bayan itace ciwon kansa gabaki daya ita Bata tsoron tashin hankali ko fitina,rigima cikinta take Bata ko gajiya ya tabbata yanzu tanacan tana zafin zuciya ko abinci qila bataci ba.
Suna shigowa har daki ya raka zarah data gama yanke shawarar komawa gida cikin satin data samu qarfin jiki kafin ya fito.
Ya jima tsaye a qofar dakinta hannuwansa zube cikin aljihu Yana tunanin halinda take ciki yasan koya buga bazata bude ba Dan haka ya sauke ajiyar zuciya tareda juyawa yabar gurin ya nufi dakinsa.
Washe gari daga zarah harshi Babu Wanda tabari yaganta a daki tayi komai nata amatse takeda gari yasake wayewa ta tafiyarta.
Ranar dazata tafi Kwana tayi kuka zuciyarta mugun zafi take Mata,
Ranar harda kukan mutuwar Dr khalil saidaya dawo Mata sabo.
Marartace tafara ciwo kadan kadan ta tashi zaune tana dafe cikin saigashi ciwon yafarayin gaba gaba ta rarrafo ta sauko gadon tana duba agogo taga qarfe ukun dare tana qoqarin komawa gado qafafunta suka riqe azabar tafara fin qarfin ta zube agurin tana Kiran sunayen Allah cikin tsananin azabar da Bata taba jiba tafara rarrafowa tana hawaye ta bude qofa ta fito tana Jan numfashi daqyar tanajan jiki ta Isa bakin qofar dakin anty zarah a taba qofar batada qarfin bugawa sbd qarfinta da ciwon yaci sosai sbd zuwa lokacin ciwon ya zaburo gabaki daya take ta zube gurin tana numfashi daqyar idanuwanta na gangaro da hawayen azaba.
Anty zarah dataji kamar antaba kofarta tana zaune ne farko Tasha ruwa ta kalli qofar cikeda mamaki ta taso ahankali ta bude kofar batasan lokacinda takira sunan Amatun da qarfi ba tana zare Ido akan jinin dake kwance qarqashin Amatun tace"
Innalillahi Amatu??
Hanyar dakinsa ta nufa ta Murda Kai tsaye tashiga tana Kiran sunansa a rude ga mamakinta shikuma zaune ta tarar dashi ya dafe kansa Sam ba alamar yayi bacci kozaiyi bacci ataredashi tana kallonsa da mamaki take cewa''
Amatu ce gatacan kwance ba lafiya.
Dagowa yayi ya kalleta saidata Kuma maimaita sunan Amatu ya dawo hayyacinsa ya miqe Yana ficewa dakin.
Yana ganin jinin jikinsa yabasa cikine da ita take wani irin mutuwar jiki takamashi bai damu da jininba ya rungumeta gabaki daya ya fice Yana mantawama da zarah dake tsaye.
Tun a hanya yake Kiran sunanta Yana shafa fuskarta cikin tsananin damuwa da kulawa yake cewa''
Please please please Amatu I can't bear to loose this pregnancy idan babyna ne ajikinki please ki daure karki Bari yafita.....
Tanajinsa sama sama Amma Bata iya motsi sai hawaye dake gangaro mata har suka Isa asibiti
Suna Isa ana karbarta cikin na qarasa barewa.
MAHMOUD ZABEERA baitaba sanin yanason haihuwa hakaba saidaya rasa cikin jikin AMATULLAH Wanda yaji dukkanin burinsa da farin cikinsa kamar ya ruguje ne musamman yanda Amatun ke hawaye ko kallonsa batason Yi taqi bude idanuwanta ko kallonsa tayi.
Duk yanda yaso kusantota taqi Bari qarshema kuka ta fashe Masa dashi na tana buqatar kasancewa ita kadai.
Dole ya fice yabarta yadawo harabar asibitin ya zauna cikin mota tareda Kiran Gida Nigeria yacewa kawu Dan Allah anty salamatu ta shirya tadawo zaisa asiya musu tickets itada Muhammad dake hannun umme yanzu.
Gida yakoma yayi wanka ya sauyo Kaya sbd har qarfe goman safe tayi Masa tun asibiti,
Tea kawai yasha yakoma asibitin yabar anty zarah da kallon ikon Allah Koda yakoma har an taimaka Mata tayi wanka an sauya Mata Kaya da green patient cloth zuwa blue tana zaune anbata tea da magani Tasha tareda snacks.
Tunda yashigo ko dagowa batayiba sai sauraron nurse din dake qoqarin cheering dinta up take ga idanuwanta dasukai jajir bayan uban kumburin dasukai tabbas MAHMOUD ZABEERA baisan waye AMATULLAH ba,
Zaisan ita Bata cikin matan dabasusan darajar kansu ba,
A banza yasameta shiyasa baisan darajarta ba Amma yanzu sai San AMATULLAH SALEH daban ZARAH ZABEERA daban,
Sunansu ba dayaba,halinsu ba dayaba hakama yanayinsu ba dayaba.
Agogo ta kalla taga akwai sauran awanni biyar kafin jirginsu ya tashi Dan haka tana buqatar komawa gidan kafin ta dauki komai nata ta wuce airport kafin lokacin.
Qarfe biyar na yamma yabar asibitin ta karbi discharge papers dinta ta fito ta tari mota ta fada.
Koda suka Isa gida Bata sallamesaba tashiga gidan Kai tsaye dakinta ta nufa ta sauya Kaya ta janyo kayanta tafara fitowa dasu takai qasa tadawo tadauki handbag dinta ta jakar labtop dinta ta fito ta bugawa anty zarah qofa tana budewa batareda ta kalli fuskarta ba tace"
Anty Zan wuce Nigeria Kuma Ina baki hkrn maganganun Dana fada Miki idan na Bata miki Rai.
Juyawa tayi Bata jira Abinda antyn zatace ba ta fice.
Koda ta Isa airport lokacin tafiyarsu yayi Dan haka kawai ta wuce ta karbi ticket dinta ta bada ta wuce.
Ko mintuna arba'in basuyiba jirginsu ya tashi suka bar qasar.
##Mamuh#
_INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_ _NA ZINNEE SMART DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU
TA WANNAN NUMBERN_
👇👇👇
08080840567
[04/06, 11:47 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MQ 45_*
Sai Bayan sallar asuba jirginsu ya sauka Nigeria ta dayake ta Kira USI ta ta sanar dashi dawowarta Bata mayi tunanin ganinsaba harta fito zata dauki drop saigashi ya tsaya gabanta cikin wata EOD dark blue sabuwa shine yake tuqin tana ganinsa ta saki murmushin farin cikin ganinsa idanuwanta na cikowa da hawayen murnar ganin 'dan uwanta Rabin jikinta Kuma abokin shawara,
Dr Usman Saleh usi Wanda shine sunan da akafi saninsa dashi yanzu
Yayi wani irin hasken samun hutu da nutsuwar rayuwa ga wani irin sajen daya Tara da sumar Kai sai qyalli takeyi duk da baiyi wankaba sbd kayan jogging nema ajikinsa ga wani irin girman gabban jiki dayayi sbd geaming dayakeyi kullum shiyasa ya zama wani irin qaqqarfan namiji Wanda yanzu haka 'yan Mata masu aji da wayewa suke rububinsa musamman sbd kyawunsa dayafi rinjayarsu.
Fitowa yayi shima Yana kallonta cikin kulawa da tsananin qaunar 'yar uwarsa dabaida kamarta kaf rayuwarsa sbd kallon dasukewa juna na uwa daya uba daya.
Kai tsaye Yana hango damuwa da rashin nutsuwar zuciya tareda rauni atareda ita musamman yanda idanuwanta sukai laushi ya saki numfashi sbd yariga yasan dawowar Bata lafiya bace ya qaraso kusa da ita ta karbi kayanta ya zagaya ya bude Bayan motar ya sanyasu ya rufe ya zagayo ya bude Mata gaban motar Yana cewa''
Bismillah mummy Amatu"ya qarasa fada cikin sigar tsokana dason dawo da dariya da walwalar Amatunsa.
Murmushi tasaki tareda Shiga ta zauna ya rufe ya zagaya yashiga ya tayarda motar suka kama hanya.
Suna fitowa daga airport ya kalleta yana qara qarfin AC din motar ganin kamar sanyinsa bai ishetaba sbd 'dan warware rolling dinta dayaga tayi alamar zafi ya maida kallonsa Kan tuqi Yana cewa''
Gida ko zabeera?
Batareda ta kallesaba tace"
Uban me zanyi a zabeera tunda ko can farkon auren ba tarewa nayiba acan daga gidanmu na tafi Greece Dan haka daga Greece gidanmu zani.
Dariya tabasa ya murmusa Yana cewa''
Amah Wai meyasa bazaki canza ba bayan kinriga kinzama uwa fa.,
Wanda yake tareda miji for morethan 3 years now Amma kike cewa uban me zakiyi a gidansu.
Muguwar hararar data sakar Masa tasashi yin shiru Yana dariya ya kamo wani zancen har suka iso sabon gidansu da batasan dashiba duk da acikin dai anguwarsu din ne Amma tsarin ginin yafita dabam da kusan duk gidajen anguwar sbd kyawunsa duk da baida mugun girman Nan Amma ba qarami bane yanada nasa kalar girman.
Tsohon gidansu dake gefen sabon ta waiwaya ta kalla cikin yanayi na farin cikin dawowarta gida cikin Yan uwa da abokanan hurdar arziki dasuka taso taredasu aka buga gwagwarmayar rayuwa iri iri ta arziki data rashin arziki data rigingimu iri iri musamman fadace fadacen dasuka Saba Wanda duk anguwa an shaidi gidansu da zaman masifa da tashin hankali kafin shigowar Dr khalil zabeera cikin rayuwarsu Wanda ya fahimtar dasu mahimmancin zaman lafiya da qaunar abokin zama tareda mutunta juna Wanda yakaisu ga zama tamkar zuria daya yanzu.
Juyowa tayi ta kalli USI da shima wasu abubuwan yake tunowa sbd fahimtar itama baya take tunawa cikin shauqi da tausayi da baqin cikin wata rayuwar dasukai a baya.
Kayanta yaja yafara shiga dasu cikin gida dayake katangarsu ta gate irin guntuwar Nan ce me qarafuna wadda ake ganin komai na waje Wanda kawune yace hakan yakeso sbd yaringa sanin komai dake wakana cikin anguwa tunda yasaba zaman qofar gida yanzu kuwa cikin harabar gidansa yake zama Kan kujerunsa na musamman da USI yasiyo Masa na zaman Shan iska Yana ganin komai na waje daga cikin harabar gidansa da surukinsa guda sukutum ya gida Masa da MAHMOUD ZABEERA tareda zuba musu furnitures na alfarma dajin dadin rayuwa Dr USI Kuma daya Fara cin qashin kansa yanzu shine daukeda nauyin komai na Jin dadin rayuwarsu yanzu Dan tuni ya ware kudi ya Kai iyami babbar kasuwa ta saro kayan siyarwa buhuhuwan takalman Yara Dana manya sosai Kuma kasuwancin nata yakeci shiyasa komai nasu yanzu sai hamdala Dan kuwa yanzu sune masu taimakawa wasu,
Anty salamatu dama marainiya ce gaba da baya Dan haka tuni tadawo cikinsu kodan irin dawainiya da wahalar datakewa Amatu da Muhammad.
Anty salamatu ce tafito daga kicin riqeda kofin Lipton data hado Yana hayaqi zata Sha sbd ciwon Mara data kwana dashi na period dinta dazaizo taga USI Yana shigowa palon janye da akwatina Niki niki ta tsaya tana kallonsa zatai magana saiga Amatu tashigo daga bayansa
Cikin tsananin mamaki dakuma farin ciki tasaki ihun ganinta tana Kiran sunanta da qarfi Wanda yasa Amatun washe baki cikin murna da farin ciki suka rungume juna saiga iyami da kawu sunfito daga palonsa harsuna rige rige Jin an ambaci sunan Amatun gakuma muryarta dasuke jiyowa.
Iyami na ganinta ta tsaya idanuwanta na cikowa da hawayen tsantsar farin cikin ganin 'yarta bayan shekaru gashi yanayin yanda take ganin 'yar tata tazama yaqara habbaka farin cikinta ga bayyanuwa saijin Amatun tayi ta fado jikinta da qarfi ta qanqamesa tana fashewa da kukan farin cikin ganinsu itama.
Kukanta yasa iyama maida hawayenta tana washe baki da farin ciki take cewa''
Meyene na kuka Kuma abun farin ciki da murna.
Dukkanin annashuwar kawu da haqoransa a bayyane suke Yana kallon Amatun cikin kewa da farin cikin ganin dukkaninsu sun Sami nutsuwa a rayuwa.
Zama sukayi dukkaninsu a palon Amatu na zaune tsakiyar kawu da iyami sai kallonsu take tana washe bakin farin cikin yanda suka sauya sosai tace"
Kawu nayi kewar gida sosai nakuma ji dadin ganinku.
Saikuma zuwa ba sanarwa Amatu" iyami tafada tana kallon Amatun da USI daya daukota.
Iyami bazata nakeson muku Danma anty salamatu ta Bata bazatan tawa so nayi saina saikun fito zuwa anjima ku ganni kawai zaune Ina cin abinci kokuma Ina muku Ina kwana saigashi ihunta yasa kunji kunfito musamman kawu so nayi Yana fitowa yaganni ya dauka inuwatace zuciyarsa ta kusa harbawa.
Dariya dukkaninsu sukayi kawu yace"
Wlh zuciyata na harbawa kun shiga uku Dan uwarku ma tata bindigewa zatayi kunga kunzama marayu kenan har gwara ke kina gidan mijinki shi wannan qaton banzan gantalewa zaiyi gurin siyan abinci ma kawai it's kuwa salamatu zaman tunanin kadaici kawai ya isheta Dan haka gwara ku taru kuyita yimin adduar tsawon kwana.
Kaikuma dason tsawon kwana kullum adduarka kenan"cewar iyami.
To karar kwana kikeson nayi fata?
Zaki Fara halin naki kenan muyi Abinda nace nadaina.
Dariya sosai Amatu tayi tana sake jinjina halinsu kawun da basa taba canzawa.
Daqyar dai aka tsagaita tasamu Shiga dakin iyami inda aka shigar Mata da kayanta tashiga tana kallon tsarin dakin dayayi Mata kyau sbd simple furnitures