Showing 45001 words to 48000 words out of 108527 words

Chapter 16 - MIN QALB complete Hausa novel

MAMUGEE   

08 Apr 2025

8487

tabawa hafsatu tace ta zubo Mata a plate
Ita Kuma dakinta ta nufa Dan yin wanka ta gyara jikinta Amma cewa anty zaran tayi zatayi sallah ne.

Wankanta tayo tareda shiryowa cikin riga da wandon bacci masu Dan kauri ta sanyo qatuwar rigar sanyi akai sbd ana Dan sanyi gashi gidan Sam komai sanyi sunsaba da rayuwar AC ta sanyo hula tareda slippers ta fito tana waya da Dr khalil Wanda yanzu take tsananin Jin kunya da tausayinsa.

Cikin annashuwarta ta fito suna wayar harda 'yar dariyarta sosai sbd labarin abincin dasuka ce na 'yan Chinese yake Bata kamar zaiyi kuka da amai
Ganin yanda labarin ke sakata nishadi yasa yaketa Jan labarin Yana sake fada Mata yanda kalar abincin yake da yanda ake cinsa sbd walwalarta na basa farin ciki da nutsuwa.


Dining ta nufa tana sake qyaqyata dariyarta datasashi tsayawa cak daga cin abincin dayakeyi akan dining din tareda zarah wadda yau duk farin cikinta a bayyane yake sbd gata ga Rabin ranta suna cin abinci tare.

Qoqarin zamata takeyi a dining din idanuwanta suka sauka cikin nasa daidai dagowarsa ya kalleta da idanuwansa dasuka narketa gaba dayanta saita samu kanta da kasa dauke idonta daga kansa zuciyarta na harbawa ahankali.

Sarqewa yayi sbd wani dalili daya kasa sani yafara tari ahankali Yana Kare bakinsa da tissue
Anty zarah dake Shirin Magana tayi saurin daukar ruwan sanyi zata miqa Masa daidain Amatun ita Kuma ta miqa Masa juice cikin cup.

Kallon juna sukayi itada anty zarah din tayi saurin dire cup din tana barin gurin da sauri ya 'dan bi bayanta da kallo qasa qasa ahankali kafin ya karbi ruwan hannun zarah din yakai bakinsa ya kurba kadan ya ajiye yakai hannunsa ya dauki cup din juice din yakai bakinsa yasha kadan sai kawai ya miqe Yana cewa''

Alhmdlh I'm full.

Binsa anty zarah tayi da kallo harya haye stairs din zuwa samansa tana karantar yanayinsa
Idan nazarinta yabata daidai MD na wasu abubuwan dabata ganewa kwanakin Nan duk da dai dama can Bata ganewa MD Amma dai yanzu kamar tana nazartan wasu abubuwan nasa.

Bin bayan Amatu tayi tana kawar da tunanin komai tana zuwa dakinta ta sameta Dr khalil na qoqarin cigaba da sata nishadi itama tana qoqarin nuna Masa nishadantuwarta sbd kada ta sace Masa gwiwa.

Palo suka dawo da anty zarah tasata gaba akan saitaci abinci ga cake din datakeso koyaushe Wanda ake Mata duk Bayan kwana biyu Amma ta kasaci komai ko ruwa ta kasa Sha sbd kanta dake daure tamau har wani sarawa yake Mata takasa cire tunanin komai cikin ranta saima wani irin tunanin MD din dayake neman zauta kanta bangare daya ga tunanin Dr da koma me zaije yadawo shi tayiwa alqawarin kanta matuqar suna raye saidai tunanin MD dakuma yake sake rikitata.

Miqewa tayi ahankali tace"

Anty kaina Yana ciwo sosai zanje na kwanta kozai rage.

Kallonta anty zarah din tayi tace"

Dakin daure kinci abinci ko kadan ne Kinga pasta ce aka dafa Kuma me ruwa ruwa ce zuwa anjima kadan lalacewa zatayi kada yunwar dare ta tayar dake ki rasa abincin ci yau ko fruits Babu a gidan Nan baa siyoba gashi rabonki da abinci tun rana da Kika ciyo a can gidanku.

Girgiza Kai tayi tana Dan dafesa tace"

Wlh banajin cin abinci saidai zuwa da safe idan ya warware zanci harda biyan bashin na yanzun din.

Miqewa anty Zaran tayi itama tareda wucewa gaba tana cewa''
Shikenan Allah ya tashemu lafiya Kisha magani kafin ki kwanta Dan Allah.

Hanyar dakin MD ta nufa tana gyara zaman rigarta a jikinta Wanda yasa Amatun binta da kallo idanuwanta na qoqarin cikowa da hawayenda suka sata saurin dawowa hayyacinta tayi dakinta da sauri tareda fadawa Kan gadonta tana rintse ido.


Tunda ta kwanta takasa bacci tana kwance ta qurawa Dan qaramin hoton Dr khalil dinta Ido dake cikin qaramin frame gefen gadonta Wanda anty zarah ce ta kawo Mata.

Dr Dan Allah kayi gaggawar dawowa sbd Ina buqatar kayi saurin aureni na zamo mallakinka
Bazan iya jira cikin Nan yakai wata taraba kadawo kasan yanda zakayi dashi nidai aurenka kawai nakeso yanzu fiyeda komai tun kafin zuciyata tafi qarfina.

Har qarfe goma sha biyu da arbain batayi bacci ba gashi zuwa lokacin yunwa tafara hanata sukuni sbd jikinta harya Fara 'yar makarkata
Ta tashi zaune tana kallon agogo.

Saukowa Kan gadon tayi tareda mayarda qatuwar rigar sanyinta me kaiwa har gwiwa ta zura hula tareda sanyo slippers ta fito tana adduar Allah yasa abincin bai buga ba Dan wlh bazata iya kwana haka ba.

Tana fitowa ta nufi dining Kai tsaye daidai shima yafito daga dining din sbd abincin daya sauko ci Dan duk yinin ranar baici abinci ba sai Daren Kuma spoon biyu kawai yaci yatashi sbd Abinda yafaru gashi yanzu yasauko abincin ya buga.

Kallonsa tayi bayan itama ta bude abincin batasan lokacin datace wlh yunwa nakeji ni bazan iya kwana ahaka ba.

Palo yadawo Yana tunanin zancenta koba komai tunda tanada juna biyu ayanda sukace Dole tana buqatan abinci akai akai.

Shima Dole Yana buqatan abinci bazai iya kwana a hakan ba ya juya zuwa dakinsa ita Kuma tayi kicin ta hau dube dube Babu Abincin ci ta dauko ruwa Tasha taji cikinta na neman qullewa ta fito tana riqe cikin daidai ya sauko sanyeda riga da wando masu Dan kauri kamar na sanyi hannuwansa daukeda mukullan mota da wayarsa batareda ya kalli fuskartaba kamar bada ita yake maganarba yace"

Muje.

Tsayawa tayi binsa da kallo harya fice kafin tabi bayansa da sauri.
##mamuh#


ZAFAFA BIYAR👇👇👇

SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma

MIN QALB
mamuhgee

SARAN BOYE
billyn Abdul

KIBIYAR AJALI
Miss xoxo

ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano

Pay @09033181070
Or 09032345899
[01/06, 8:40 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: *_MQ 24_*



Tafiya sukeyi ahankali cikin motarsa Babu me Magana sai sanyin AC da qamshin turarensa daya Gama Kama motar dama can yake ratsata Yana Bata wani sabon yanayi cikin zuciyarta Wanda yasata fadawa tunani.,

Tuqinsa yakeyi cikin nutsuwa shima Yana jiyo siririn sahirtaccen qamshin jkinta na Shiga hancinsa ahankali Wanda kusan shima yasashi Shiga tunanin banbanta yanayin qamshinta Dana zarah.,
Istigfari yayi saurin Yi cikin ransa Yana Dan tsuke fuska tareda 'dan qarawa motar gudu.

Ganin sun kamo hanyar blue fox yasata saurin kallonsa murmushi na sauka Kan fuskarta tace"

Rabin ran Anty Dan Allah muje blue fox akwai abinci me kyau da dadi acan.......

Wani irin kallo ya juyo ya aika Mata Jin sunan data kirasa dashi Wanda yasashi qurawa cikin Idanuwanta Ido Yana son sake tabbatarda Abinda takirasa dashi  _Rabin ran anty_  yanda tafada sunan batareda kulawar komaiba yasashi yimata wannan kallon itama Jin idanuwansa akanta yasata kasa juyowa ta qurawa waje Ido Yana damqe hannunwanta dake rawa zuciyarta na harbawa.

Jin shiru yasata Dan dagowa tareda juyowa ahankali ta kallesa hankalinsa na Kan hanya saita qurawa fuskarsa da fararen hannuwansa dake tuqin motar cikin nutsuwa da qwarewa,
Kan fuskarsa ta tsayarda kallonta tana yaba kyawu da tsarin fuskarda ubangiji yayi Masa me daukeda da tarin kwarjini da Kamala,
Dogon hancinsa ta kalla zuwa manyan idanuwansa batasan lokacinda ta lumshe ido ba hawaye na gangarowa daga cikinsu batareda ta gogesuba cikin ranta tace"

Meyasa zuciyata ta zabi wahalar da rayuwata data Dr ta hanyar son Dan uwa mafi soyuwa agaresa?
Dukkanin kyawu da Abinda MD yakedashi Dr khalil dinta nadasu harma yafi MD din kyawawan halaye masu sanyaya Rai hasalima kusan kamanninsu daya sbd duk mahaifinsu Modibbo suka dauko har Khalil dinta ma yagi MD din hasken fata saidai MD ya nuna Masa gogewa da hutu irin na Boko da yawan qasashe suka hudasa sai kalar fatar mahaifiyarsa daya dauko me sheqi.

A harabar blue fox din yayi parking tareda Dan juyowa ya kalli gefenta tayi saurin share hawayenta tana bude motar ta fito tana washe baki cikin tsananin farin ciki ta juyo daidai ya zagayo tace"

Yau duk abindake restaurant dinnan saina cire kwadayinsa na tsawon aikin danayi anan din.

Bai kalletaba yayi gaba ta biyosa tana sake bayyanar da murnarta ta zuwa gurin.

VIP direct suka nufa inda tuni aka hau sintirin attending dinsu ga mamakinta kusan Rabin ma'aikatan gurin an sauyasu Nan ta bada odar abinci kusan kala hudu da tarkacen su fruit salad harda ice cream da furar blue fox din me shegiyar Madara da Laban yoghurts.

Table dinsu kusan kasa daukan abubuwan yayi sai kawai yayi odar  noodles with veggies salad da power drink yafara ci cikin nutsuwa Yana kallonta tana cin abincin cikin tsananin Jin Dadi Dan harwani lumshe ido takeyi tana cika bakinta da Naman kazar chicken rings dataji carrot da spices.

Yana kallo ta Gama yagalgala kazar ta janye gefe ta jawo shawarma tafara ci itama ta ajiye ta janyo soyayyan dankalin dayaji egg source
Furarta ta janyo ta kurba ta lumshe ido tana cewa''

Wayyo Dadi" kafin ta aje tacigaba da cin noodles Kuma.

Jingina yayi da Bayan kujera Yana zuba Mata iduwansa masu karya kuzarinta tareda dukkanin nutsuwarsa Yana kallonta kamar ya baby a gabansa.

Saida tayiwa komai ci rabi aje rabi kafin ta qoshi ta dauki ice cream dinta ta bude ta diba tana hadiye yawun matsuwa taji sanyinsa ya sauka a bakinta taji anrike ice cream din
Da sauri ta dago idanuwansu suka shiga cikin na juna ahankali ya girgiza Mata cikin qaramin sauti yace"

This is not good for your health......

Kasa motsi tayi ta harya zare ice cream din daga hannunta ya ajiye idanuwansu na cikin na juna Saida waiter din dake tsaye yayi gyaran murya da qarfi Yana sake miqawa MD din bill dinsu.

Fuskewa yayi Yana Dan tamke fuskarsa ya juyo ya Ciro ATM card dinsa ya miqawa waiter din batareda ya karba bill dinba.

Bayan andawo Masa da atm din anyi clearing bill dinsu suka fito suka Shiga mota sukabar gurin.

A mota shiru tayi tana sauraron karatun Qur'an din dayasa a motar Yana fita ahankali saitaji tana sake samun nutsuwa da yanayin da suke ciki na kasancewa da juna ahaka.

Koda suka dawo zabeera har bacci yafara daukarta cikin motar shiyasa da yayi parking sai bai tayarda itaba hakama bai kashe motarba sbd AC ya zauna ya fiddo wayarsa Yana duba saqon dayaji shigowarsa sunacin abinci.

Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda bacci ta zuba akansa tana lumshe ido ahankali ta furta"

Tabbas Ina cikin tsananin son MAHMOUD ZABEERA Kuma so me qarfi Wanda nakejin kamar ruhina zai rabu da gangar jikina idan nayi nesa dashi,
Lumshe ido takuma Yi tareda budesu akansa cikin sauti me taushi dazai iya jinta tace"

Nagode.

A natse ya juyo ya kalleta da nasa idanuwan dasuka nuna sunfara Jin bacci taji zuciyarta na qara narkewa da sonshi tayi saurin dawowa hayyacinta tareda tashi zaune tabude motar da sauri ta fice hartana hadawa da Dan gudu tayi ciki.

Kai tsaye bedroom dinta ta nufa ta fada Kan gadon tana sakin hawayen dataketa riqewa tace"

Amatu kidawo hankalinki Mana,
Kidawo Amatunki da kowa yasani,
Amatun Dr khalil matar Dr khalil,
Babu kowa a zuciyarki sai Dr khalil sbd shine Wanda zuciya da ruhinki keson aure.

Ta jima ahaka kafin ta miqe tafada toilet ta wanko fuskarta tayi fitsari tazo ta kwanta tareda lullubewa tana qudurtawa ranta gobe zata amayarwa Salman abindake zuciyarta kafin ta rufe zuciyar gaba daya ta mallakawa Dr khalil dinta Wanda idan har tana Raye Inshallah batada miji sai Dr khalil.

Washe gari tunda wuri ta tashi yau da kanta ita tafara Kiran Dr
Meeting zasu shiga Amma ganin kiranta Saida ya tsaya ya dauka yaji lafiyarta kafin yace idan yafito zaikirata.

Wankanta tayi ta shirya cikin riga da skirt na atampa kalar blue tayi Mata kyau sosai ta yafo gyalen akanta sbd Bata dauro dankwalin kayanba.

Palo ta fito ta nufi kicin da kanta yau ta dafawa kanta indomie da dafaffen kwai guda biyu sai custard data hado Wanda yaji uwar Madara takoma dakinta acan tayi breakfast dinta tana gamawa ta fitoda kayan ta maida kicin Takoma daki ta sake kwantawa tana tunanin Dr da irin dibbin soyayya da qaunar daya Bata,
Ya juyawa iyayensa baya akanta alokacinda aka koresa ya amince zaibar komai da komai ciki hadda iyayensa da 'yan uwansa da rayuwar daya taso ciki duk sbd ita
To menene Dan itama ta danne zuciyarta ta tauyeta daga Abinda takeso ta bashi koba komai Al'amarin da zuciyarta ta dauko me girma ne sbd mijin anty zarah ta haramtawa kantashi Koda sonsa zai kasheta har abada su biyun Nan anty zarah da Dr bazata taba barin susan halinda zuciyarta ta Shiga akan mutuminda sukafi qauna da komai arayuwarsu.....

Kiran Salman ne yashigo wayarta cikin nutsuwa ta daga tana qoqarin kawar da damuwarta tace"

Likitan qashi na duk Nigeria""ta qarasa tana Yar dariya.

Shima 'yar dariyar yayi Yana gyara zama cikin motarsa yace"

Zakije mukai usi airport kokuwa na tafiyata?

Wuntsilowa tayi bakin gado tana janyo dankwalinta da gyalenta ta fito tana cewa''

Ai karma kamin haka idan ban takasa a matsayin 'yar uwarsa da bamu taba rabuwaba arayuwa sai yanzu to zan takasa amatsayin matar Dr khalil tunda bayanan Dan shine yafi kowa cancantar ganin wucewar usi Dan shine yakawo wannan murmushin akan fuskarsu na samun cikar buri su samu ilimi kamar sauran 'yaya.


Ganinta kawai yayi tana bude gaban motar ta shigo ta zauna tana kashe wayar tace"

Muje ko¿

Dariya tabasa ya girgiza Kai Yana cewa'

Amatun likita bokan turai.

Kallonsa tayi tana cewa''

Nidai muje tun kafin na huce da zafi zafina nafito Dan yiwa USI huduba.

Jan motar yayi suka fice suna Dan taba fira ahankali har suka Isa gida inda su kadai ake jira suzo dauki usin.,
Tunda tashigo gidan idanuwanta suka sauka Kan 'yan gidan kaf a tsaye cirko cirko tsakar gidan kowanne fuskarsa cikeda yanayin damuwar rabuwa da USI din ta juya ta kalli kawu dake zaune radionsa a kunne Amma yanayin fuskarsa yasa taji idanuwanta suna qoqarin cikowa da hawaye tana kallon iyami sai kawai ta qaraso da sauri Yana sake hawayenta ganin yanda Usin yake tsaye riqeda hannun iyami Yana Bata qwarin gwiwa.

Usman din ta kalla tana share hawayenta tasaki murmushi Dan cirewa kowa damuwa takai Masa duka a baya tana cewa"

Ki yanda kasa kowa cikin damuwar tafiyarka bayan duk hutawa zamuyi da rashin Jin ka musamman maman junior da anty salamatu ko???""tafada tana kallon maman junior da anty salamatun dake qarasowa da jakarsa data fito Masa da ita.

Murmushi maman junior tayi tana cewa''

Usi Allah yabaka sa'a kamaida hankali kayi karatu ko zaka tallafa Mana wata Rana idan lokacin cin amfanin karatun yazo sbd Kaine kasan wahala da gwagwarmayar rayuwa damukeyi anan gwamnati batamasan da ire irenmuba.

Maman junior kada ki damu daya bayan daya dukkaninmu sai usi yakaimu Hajj da umrah da albarkar wannan karatun dazaije Amma idan kuka tsaya Kuna Masa wannan fuskar ta marayu ta Yaya zaije da gwarin gwiwarsa ai kawai ki Masa tashin hankali da hayaniyar da kuka Saba shizaisa yaje Yana tuno kowa ayanda halayyarsa take....

Dariya dukkaninsu suka dauka Nan aka hau hayaniya ana Masa Allah ya kiyayaye shima sai hakan yasashi Jin Dadi ya saki fuska Yana amsa musu kowa ana Masa alqawarin Abinda za'ayi Masa idan akai kudi.

Kawu da iyami dasu akeje har airport inda suka taru su duka da hayaniyarsu suka cikawa Salman motar da hayaniya sai suke qara burgesa musamman Amatun dake qoqarin Hana kowa shiga damuwar tafiyar Usin bayan ita Yana iya hango tsananin damuwa da fargabar rabuwa da Usin a idanuwanta tana daurewa ne kawai.

Suna Isa ko zama basuyiba aka Kira jirginsu Salman ya kallesa Yana basa sauran dukkanin bayanan da Dr yace yayi Masa tareda basa takardun komai Dana atm card na account din da aka bude Masa tareda wadataccin kudi aciki ya miqa Masa tareda Dan rungumesa Yana cewa''

Zaka ringa ganina akai akai inshallah har sai kagama sanin komai da komai just take care brother,
Kuma Ina fatar zaka saka mijin 'yar uwarka alfahari dakai wata Rana.

Kallonsa yayi ya kalla Amatu Yana qirqiro murmushin qwarin gwiwa yace"

Inshallah Dr khalil saiyayi murmushi ga wannan aikin alkhairin nasa.

Gyada Masa Kai tayi tana qoqarin maida hawayen dake subuce Mata
Suka rungume suna tana sakin hawayenta gaba daya suna zubowa ba tsayawa.
Cikin kunnenta yace"

Amatu Ina Miki fatar samun Abinda kikeso arayuwa Wanda zaisaki farin ciki,
Inaso Kuma kimin alqawarin Babu wani Abu dazai sauya matsayin Dr acikin rayuwarki kimin alqawarin da ke da kanki zaki kirani Dan sanar Dani aurenki da Dr Khalil idan lokacin yayi.

Rintse ido tayi hawayenta na sake gudu ta janye jikinta tana kallon qasa tace"

Usi zuciyata takamu da son wani Wanda ba Dr khalil ba so me girma Amma wlh shima son Dr khalil bai sauyaba a zuciya da rayuwata,
Ba laifina bane sbd bansan yaushe hakan yafaru ba,
Bansan ta Yaya zan kankare wannan son daga zuciyata ba Amma nasan ta yanda zan dannesa dannewar da har abada bazai tasoba bare wani yasan dashi zanbarshi cikin Raina har mutuwata,
Jan kuka tayi ahankali tana cigaba da cewa''

Usman ayau ni Amatu nayi maka alqawarin bazan taba auren kowaba sai Dr khalil,
Nayi alqawarin Dr bazai taba fuskantar sauyawa daga gareniba sbd shi kadai na zaba amatsayin mijina Inshallah...."wani siririn kuka taqarasa maganar dashi zuciyarta na wani irin nauyi.

Baiyi mgn ba ya juya gurinsu kawu yayi musu bankwana ya wuce Yana danne zuciyarsa dake Jin tsananin damuwa da tsoron Abinda Amatu ta fada,
Shin yayi Mata adalci satayin alqawarin auren Dr Bayan tafada Masa akwai Wanda zuciyarta ke tsananin so???

Baya tunanin baimata adalciba sbd a nasa gani da sanin Babu Wanda zata aura ya sota ya qaunaceta yabata farin ciki da kulawa fiyeda Dr khalil zabeera Dan haka koma waye zuciyarta keso farin cikinta da kulawar dazata samu daga Dr yafi matasu ahankali zata manta sonta zuciyarta ta koya son KHALIL din.


Ahanyarsu ta komawa Babu me mgn acikinsu kowa yayi shiru Yana tunani kamar basune suketa hayaniya ba a hanyar zuwa.

Su kawu tunanin rahuwarsu dasu Usin sukeyi sbd dukansu basa gabansu yanzu sai sukejin kamar rabuwa sukayi dasu gaba daya musamman iyami datakejinsu kamar itace ta haifesu gashi yanxu ta tashi Babu ko daya a gabanta.

Shikuma Dr Salman yasan irin ciwo da radadin datake ciki na zabar danne sonta tabi Abinda rayuwarta da 'yan uwanta keso.

Ajiye su kawu sukayi suka nufi gida har lokacin Babu me Magana acikinsu Saida yayi parking qofar part dinsu anty zarah sai ga MD ZABEERA yafito Yana amsa waya fuskarsa sai sheqin kwarjini takeyi ya nufi motarsa ya bude ya shige drivernsa na ciki yaja sukabar gurin idanuwanta na binsa da kallo har motar ta bace Salman na lure da ita ya saki numfashi ahankali yace"

Duk zabin dazakiyi Amatu kisani ni Salman zabeera Ina bayanki dari bisa dari saidai bazanso ki zabi Abinda zai kawo damuwa da qunci cikin rayuwarkiba,
Soyayyar MD ZABEERA Babu Abinda zata baki sai damuwa sbd

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login