Showing 1 words to 3000 words out of 58156 words
๏ปฟ๏ปฟ[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 1~October~2016
๐ถ๐ธNI DA K'AWATA๐น๐ท
NA BILLKISA IBRAHIM๐
๐ท๐น1โฃ๐ธ๐ถ
BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM
Da sunan ALLAH mai rahma mai jink'ai, ya ALLAH kabani ikon fad'in abinda zai amfani Al'ummarka, ka tsarkake harshena daga fad'ar abinda zai cutar da Al'ummarka. Amin ya "RABBI".
Assalamu alaikum, ina mai farin cikin sake had'uwa daku asabon littafina, akaro na 4, ina godiya ga d'umbin masoyana aduk inda suke, "UBANGIJI ALLAH" yabar k'auna. Nagode๐๐ป
Zanyi amfani da wannan dama, domin taya d'umbin Al'ummar MUSILMI shiga sabuwar shekarar musulinci, ALLAH ya albarkacemu da rahamarsa.
๐HAPPY NEW YEAR๐
..........'Yammata biyune ke tafiya, cikin nutsuwa, jikinsu sanye da kayan makaranta, (uniform) pink d'in wando da farar riga, sai farin hijjab daya tsaya musu iya k'ugu, dan baikai d'uwawunsuba, bayansu goye da jakar makarantarsu (school bag).
"Sukaja birki abakin titin da d'umbin d'alibai ke tsaiy tsaye suna jiran motar makaranta,wash ALLAH!!!, d'aya daga cikin 'yammatan ta fad'a.
D'ayar ta bita da kallon mamaki, kai fareeda badai gajiyaba???
"Wadda aka kira fareeda tad'anja tsaki wlhy kuwa sopy nagaji.
Sopy tai dariya nikam bansan randa zaki zama jarumaba fareeda, ke komai kin gaji sai kace mai yaron ciki??
"Fareeda ta harari sopy, "k" ki kaimin cikin ko??
Gaba d'aya suka tuntsure da dariya harda tafawa,, sopy tace"ina ni ina yimiki ciki rufani ki sayani,, suka kuma tuntsurewa da dariya.
Tsayuwar wata bak'ar motace ta tsayar musu da dariyar,suka k'urawa motar idanu, da alama sunsan mai ita, ko kuma suna son sani.
Wani farin saurayi mai d'an jiki yafito yana murmushi, idonsa akan 'yammatan, yak'araso da sallama, suka amsa cikin sakin fuska, suka gaisheshi, sopy ta d'ora da fad'in habibina daga ina?? Da wannan farar safiyar ga sanyi??
Ya shafa sumar kansa, yana fad'in gimbiyatace ta fito dani ko fareeda??
Fareeda tai 'yar dariya mai kama da yak'e,, tace''hakane.
Saurayin yayi d'an murmushi to kuzo mutafi karku makara, dan wannan motar makarantar taku saiku kai k'arfe takwas baku tafiba, yafad'a yana karb'ar school bag d'in sopy.
"Sopy ta tab'a fareeda K'AWATA tunanin mi kikeyi ne??
Fareeda taja ajiyar zuciya bakomai mikika gani???? Sopy tace''ban yardaba fad'a min gsky!!
Kunga kumuje sai ayi wannan magar a mota, saurayin yafad'a yana nufar motar.
Suka bishi abaya, bayan sun shiga motar, yaja suka tafi,, sopy tadage sai fareeda tafad'a mata damuwarta, ita kuma fareeda tadage akan babu abinda ke damunta.
Saurayin yay dariya nikam tunda nake arayuwata bantab'a ganin k'awance irin nakuba, mai cike da k'auna da yarda, dakuma aminci, wai idan kun tashi aure yaza ayine??
"Sopy ta kalli fareeda, my sister kinji wani zance,, aii mu insha ALLAH agari d'aya zamuyi aure ko?? Fareeda tace" insha ALLAH.
Tofa saurayin yafad'a, to ALLAH yacika muku burinku,, amma aii har yanzu bamusan gwanin K'AWAR tamuba??
Wlhy habibina nima kullum damuwata kenan,, bani da wani buri bayan naga mijin k'awata, tunda ni nakama nawa tafad'a tana kallon saurayin,, shima ya kalleta yay Murmushi, fareda yakamata ki tsaida gwani gashi har munkusa k'are makaranta.
Fareeda tad'an ja tsaki mara sauti, azuciyarta tace,, haba K'AWATA dama kin daina zumud'in ganin gwanina,, dan ganin mijin dazan aura bak'aramin tashin hankali bane agareki,, dan saurayin dakikeso da k'yauna shine wanda nake burin yazama mijina kota halin k'k'a๐ณ๐ณ tofa.
Amma afili saitace karku damu gwanina yakusa bayyana insha ALLAHU.
"To ALLAH ya yarda cewar sopy"
A bakin get d'in makarantar ya ajiyesu, suka tsaya shida sopy suna sallam, yayinda fareeda tai gaba zuciyarta na zafi saboda kishi.
Bayan yatafi sopy tak'araso inda fareeda ke tsaye fuska a d'aure,, sopy tabita da kallo dan son gano matsalar K'AWARTATA,, amma sai fareeda tai gaba, tabar sopy a tsaye tana kallonta.
"Sopy tabita abaya, tana mai mamakin duk sanda suke tareda ABDUL sai fareeda taita fushi ko me yasa hakan???
Zuciyarta tace k'ila itama tana sonsane, kobatason tarayyarku,, tai saurin cewa kai A'a fareeda bahaka takeba,, domin na yarda da fareeda d'ari bisa d'ari,, nayarda da ita kamar yanda na yarda da kaina,, shaid'an bazan yarda da hud'ubarkaba, balle har ka haddasa rashin yarda tsakanina da K'AWATA, abin sona da k'aunata,, dan bayan iyayena da 'yan uwana, babu wanda nake k'auna kamar fareeda da Abdul, mutanan nan biyu sunada matuk'ar muhimmanci arayuwata fiye da tunanin mai hankali.
Turk'ashi lallai akwai matsala,, shin yazata kasance ga fareeda da safiyya,, shin miyema dangar takar fareeda da safiyya ne?? mizai faru ga wad'annan k'awaye biyu?? ga fareeda taci burin auren saurayin k'awarta aminiyarta,, wanda kuma k'awartata tafi so da k'auna, gashi yakai kud'in aurenta,, shin burin fareeda zai cika?? Idan safiyya tagano fareeda nason ABDUL yaza ayine???
Nice kad'ai mai baku wannan amsar,, kubiyoni dominjin gundarin labarin ""NI DA K'AWATA"" yananan zuwa nan bada dad'ewaba, takuce dai mai sonku da k'aunarku BILLKISA IBRAHIM.. nagode๐๐ป..............โ๐ฝ
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐?
๐ I LOVE U MY FAN's ๐๐
๐
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 2~October ~2016
๐ท๐นNI DA K'AWATA๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ2โฃ๐ธ๐ถ
ASALIN LABARIN ............WACECE SAFIYYA???? SAFIYYA IBRAHIM KABEER shine cikakken sunanta , malam ibrahim shine mahaifinta, cikakken haifaffen kano ne, a unguwar rijiyal lemo,, kowa dai yasan rijiyar lemo unguwar talakawace irinmu.
"Dan haka malam ibrahim talakane tib'is irin wanda sai annemo na gobe aci, sai dai malam ibrahim yanada wadatar zuci, dan mutumne mai taka tsantsan da tsantseni, matarsa d'aya hajara wadda suke kira da inna, itama mace mai hak'uri da kawaici, yaransu uku duk mata, Nafisa itace babba tayi aure harda yara biyu, dan daga aji uku na secondry aka cireta akai mata aure,, sai hauwa'u itamadai tayi aure kamar 'yar uwarta itama tana aji uku akai mata aure, yanzu tanada yarinya d'aya dan ko tafiyama bata farayiba; suduka suna aure anan cikin garin kano, sai auta safiyya wadda yanzu take (s,s,3) a wata secondary ta 'yammata, itamadai malam ibrahim yayi niyyar cireta yay mata aure amma sai uncle kabeer wani k'aninsa yahana, malam ibrahim yace" to shikam gsky bashida k'arfin rik'e ragamar karatunta, uncle kabeer yace" babu damuwa shizai d'auki nauyin karatunta dukda shima bawani k'arfine dashiba, amma yana aiki dan yayi karatu har zuwa degree.
Wanna nan shine dalilin cigaban karatun safiyya 'yar gatan uncle kabeer.
" gidan malam ibrahim ana cikin hali na talauci da fatara,amma wannan baisa 'ya'yansa sun lalaceba, saboda tarbiyyar dasuka samu a wajen inna da babansu, gasu ALLAH yabasu kwakwalwar karatu sunada k'ok'ari a makaranta, dan safiyya tuntana primary school take d'aukar na 1, har yanzu datake a secondary.
"" safiyya bak'ace saidai bak'inta mai k'yawune, irin wanda idan ka kalla saika sake kallo d'innan, tanada k'yau am ma bamai tsananiba, sai dai tanada manyan idanu dara dara wad'anda saudayawa susuke fara jan hankalin maza gareta,, gata tanada jiki mai k'yau irin wanda akecema karuwan jiki.
Fareeda 'yar anguwar su sopy ce dan gida biyarne tsakaninsu, itamadai iyayenta talawane dan babanta abokin malam ibrahim ne, su hud'u iyayensu suka haifa maza biyu mata biyu itama itace auta,, fareeda k'yak'yk'awace fara tas, dan tanada k'yau na d'aukar hankali,, fareeda k'awar safiyyace tun suna yara, dan ayanda najima rana d'aya aka haifesu,, k'awancensu yanada matuk'ar dank'o, dan tare yake da tsantsar so da k' auna dakuma yarda,, koda yaushe suna tare inbasa gidansu sopy to suna gidansu fareeda,, masu karatu amintakacefa mai tsantsar karfi ga wad'annan matasan 'yammata.
"Koda yaushe suna tare, tare a ka sakasu makaranta, ko d'inki tare ake musu iri d'aya kuma,, sai dai halin fareeda dana safiyya sun bambanta, safiyya tana da hak'uri da zuciya dan idan tayi fushi fareeda ce kawai ke iya shawo kanta kokuma uncle kabeer, Dan shine ma yasa mata suna sopy,, takan dad'e batayi fushiba dan sai ankaita mak'ura sannan.
Fareeda kam tanada tsiywa dan bata barin saita kwana,, soda yawa itace ke jawo musu fad'a gata batada k'arfi sai dai safiyya tashigar mata fad'an, kunsan masu zuciya akwai k'arfin tsiya,, fareeda tanada son nuna ita watace dan tanada kwad'ayi damma sopy tana sakata a hanya.
Tafiyarsu tafara samun gar gada ne alokacin da Abdul yashigo rayuwar safiyya,, shima d'an anguwarsu ne,, amma abayan layinsu yake,,babanshi yanada rufin asiri dan gsky yafi iyayensu safiyya kud'i.
"Gidan su Abdul gidane na mata uku, da tarin yara dasuka kai adadin ashirin zuwa sama, Abdul shine na 6 a gidansu,, yayi karatu har zuwa (N,C,E)Sai dai Abdul irin samarinnan ne 'yan k'arya dason nuna burga.
Sun had'u da safiyya awani yammacin ranar talata, lokacin sun dawo daga islamiyya itada fareeda,, tun aranar farko da fareeda taga Abdul takamu da sonsa,, sai dai kash daga baya sai ya nuna k'awarta yakeso safiyya,, dan danan kuma soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Abdul da safiyya, wannan yasa fareeda ta danne son Abdul azuciyarta, sai dai kuma yau da gobe sirrin nata yana nema fitowa fili.
"""" dan duk ranar da fareeda taga Abdul yazo wajen safiyya takanji wani bak'in ciki da kishi,, har yakansa ta nuna fushinta afili,, duk da tasan k'awarta tata tana tsananin son Abdul,, wanda a yanzun haka ankai kud'in auren Abdul gidansu safiyya, harda saka rana,, za ayi bikinsu bayan ta kammala secondry.
"Toko wannan aure zai yiwwu??ko fareeda zata hak'ura da k'udirinta kafin k'awar tata ta fargane??? kubiyoni dan tabba tarwa.........................โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
๐
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 3~October ~2016
๐ท๐นNI DA K'AWATA๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ3โฃ๐ธ๐ถ
............yau takama weekend babu school su sopy suna gida, sopy ce zaune tana wanke wanken kwanuka inna na gefenta tana tsintar shinkafa 'yar hausa.
"Safiyya! Wai bazakiyi sauri ki tashi awajennan ba ko?? Nafad'a mikifa yau kece zaki mana abinci, amma kin zauna wanke2 bawani mai yawaba sai lank'andi kikeyi, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Sopy ta turo baki gaba ALLAH inna ni bana son yin girkin nan mutum yayta fama da iccen nan, ga azabar hayak'i idonka yayta hawaye kamar kana kuka.
Inna ta girgiza kai tana murmushi, nima d'in danake dafa miki kullum kizo kici haka nake fama, dan haka yau har girkin dare kezakiyi shi.
Sopy tazaro ido ๐ณkai inna da gsk kikeyi??
Na tab'ayimiki k'aryane?? Inna tabad'a tana mik'ewa tsaye,, Sopy tace"A'a.
inna tace" to yimaza ki gama ki tashi rana tanayi kinsan babanki kuma yakusa dawowa.
Sopy tai shiru tana wanke2n ta can kuma saitace inna!! Inna ta amsa da na'am.
Inna mizai hana ahad'e abincin harna dare?? A'a baza a had'eba kinsan dai babanku bason cin shinkarnan yakeba koda yaushe balle wannan fara da mai d'in, yana cine kawai dan bashida yanda zaiyi,, ayi shinkafar yanzu da daddare sai ayi tuwo.
Tuwo kuma inna!!!! Jiyafa shi mukaci nikam nagaji da cin tuwonnan wlhy.
Inna ta d'auki wani murfin roba dake gefenta ta jefi safiyya dashi,, dan k'aniyarki in bakici tuwonba mizakici?? Ko kin ajiye mana wani abincinne bayan tuwon?? Kudai yaran yanzu bakusan ku godema ALLAH ba yayin dayay muku ni'ima, da basai ki wuni ki kwana bamuci abinci agidannan ba, amma yanzu ALLAH yarufa mana asiri shine zakiyima mutane iyayi,, kul nasake jin wannan furicin abakinki.
"" Sopy tai kwal2 da idanu tana shirin yin kuka dan ganin ran innarta ya b'aci, tace" dan ALLAH inna kiyi hak'uri bazan sakeba ki gafarceni???
Inna tai murmushi to shikenan ya wuce share hawayenki kinji,, barma girkin nizanyi.
A'a inna kibari zanyi tafad'a tana nufar kichin d'in da hayakin wuta ya maida bangon bak'ik'k'irin, tafara k'ok'arin had'a wutar icce.
Sopy tana aiki suna hira da inna, inna tace waini lfy yau banga fareeda ba agidannan kuma kema banga kinje gidansuba????
Sopy tace"wlhy babu komai inna, tacemin ne zataje gidan k'anuwar mama a hotoro, nikuma kinsan ba shiri muke da'itaba shiyyasa nace bazanjeba,, to inaga tana can bata dawoba.
Hummm kudai kaiwai shirmenku ne ya motsa amma in banda haka miye nawani rashin shiri kema aii sadiya innar kice.
"Taf inna ALLAH yakiyaye sadiya tazama inna ta,, dan tunda nalura batasan abotarmu da fareeda nai alk'awarin na daina zuwa gidanta,, idan tazo nan anguwar ma gaisa, shima idan mun had'u kenan.
Inna ta shige d'aki tana fad'in kudai kuka sani.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::โ
Fareeda tana gidan innarta sadiya, k'anwar mamace mahaifiyar fareeda, itamadai bawata babba bace dan kusan sa'ar hauwa'u ce yayar safiyya.
Suna zaune afalon sadiyar gabansu tiren taliyane da yaji damai,, kunsan dai mu 'yan kano mun iya k'wad'ayin mai da yaji, sadiya takalli fareeda 'yar uwa ina jinki jamuje labari.
Fareeda ta harareta oh dama matsalar tawa labarice?? Sadiya tace yi hak'uri ina tsokanarkine. """Fareeda taja ajiyar zuciya sannan takuma gyara zama tana fad'in wlhy anty da nayi niyyar bar mata Abdul amma yanzu bazan iyaba, idan nagansu tare jinake tamkar na had'iyi zuciya na mutu.
Dan ALLAH ki bani shawara miya kamata nayi???? Dan na mallaki Abdul.
"""Sadiya tayi murmushi aii wlhy koni ban goyi bayan ki bar mata shiba, Abdul k'yak'yk'awane dama dake yadace bawannan bak'ar yarin yarba,k'ilama asiri tai muku dan na lura tun farko ke yake so. Fareeda ta gir giza kai,, bana tunanin haka aunty sadiya nasan halin sopy nakuma san abinda zata iya,, inama tasan inda wasu malamai suke?? bare taje, kedai kawai bani shawara.
Sadiya ta tab'e baki dan ta lura fareeda bazata gane inda ta dosaba,, tace kawo kunnanki kiji!!!;!!
Fareeda ta mik'a kunnenta ga sadiya, can kuma sai suka tuntsire da dariya harda tafawa, fareeda tace"wlhy shawararki tayi auntyna ALLAH ya biyaki,, inada tabbacin samun ABDUL yanzu.
Tofa masu karatu wace irin shawar sadiya tabama fareeda ne??? dahar take murna haka, harma da tabbatar wa kanta samun ABDUL,, to kudai biyoni dan jin wannan bada k'ala.......... ..โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
๐
4~October ~2016
๐ท๐นNI DA K'AWATA ๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ4โฃ๐ธ๐ถ
..............koda yamma da fareeda tadawo bata shiga gidan su Sopy ba, Sopy tagama shirin islamiyya ta fito, inna bari nagani ko fareeda tadawo saimu wuce islamiyya idan kuma bata dawoba nisai na wuce.
"" to autar inna adawo lfy""
Tafita tana fad'in ALLAH yasa innata.
Da sallamarta tashiga gidan, mama dake zaune a k'ofar d'akinta tana linke kayan wanki, ta amsa da fara'arta,, Sopy ta tsugunna ta gaida mama.
"Mama tace" waini yau ina kika shiga safiyya?? Duk yau ban gankiba, ince dai lfy???
Sopy tayi murmushi wlhy lafiya lao mama ina gidane kawai.
Aii d'azu danaga fareeda ta shirya canake tare kuka tafi hotoron??
A'a mama batare mukajeba saboda zanyi wanki.
ALLAH sarki kishiga tana nan tun d'azu tadawo inagama barci takeyi;
Sopy tamik'e tana fad'in fareeda kasace aii,, amma barcin yamma.
Tad'aga labilen d'akin fareeda kwance d'ai d'ai akatifa tana kwasar barci, Sopy tak'arasa cikin d'akin tasa hannu ta daki bayan fareeda, ke uwar barci tashi.
"Fareeda ta taahi a firgice tana fad'in wayyo mama.......saitaga safiyya tsaye akanta,, Sopy tace sarkin tsoro kawai kin wani tashi afirgice kamar wadda aka firgita.
Fareeda ta harareta wlhy sopy ke 'yar iskace miye na tashina ina barci??
To badole natashekiba tunda ke bak'ya duba agogo, kullum kece kikeja mu makara a islamiyya.
Fareeda ta yatsine fuska aini inagama yau bazani islamiyyar nanaba.
" saboda me??? Sopy ta tanbaya.
Babu komai kainane kawai keyimin ciwo.
Sopy tace" kinsha maganine?? A'a ban shaba amma yanzu zani nasiyo tunda kin tasheni,, tamik'e barima mufita tare.
Tare suka fito fareeda ta amshi kud'in magani awajen mama suka tafi,, dai2 zasu fita kwanar layinsu suka gamu da ABDUL dawani abokinsa Adam,, adam yace" 'yan halak kunk'i ambato yanzu muke hirarku ashe kuna hanya.
"CIkin zolaya Sopy tace" kodai kuna gulmarmu???
Abdul yace" kajiko abokina shiyyasa nace kayi shiru karka fad'a,, wad'an nan baka iya musu.
Adam yay dariya gsky ne abokina,, wannan abotar mai k'arfice nadad'e banga k'awaye masu irin shak'uwarkuba, gaku nan tamkar 'yan biyu.
"" fareeda tace" lah bakada labarin mu 'yan biyune rana d'aya aka haifemu kaje ka tambaya.""
Adam ya jinjina kai aii bama saina tambayaba nayarda, dan abokina yatab'a fad'amin.
"Abdul yamatsa kusada sopy gimbiyata yayadai??
Tai murmushi lfy lao habibina saidai my sister ce kanta yake ciwo.
Ayya ALLAH yak'ara sauk'i shiyyasa naga d'aya da uniform d'aya babu???
Sopy tayi murmushi eh kusan hakane danni zanje islamiyya