Showing 1 words to 3000 words out of 34129 words

Chapter 1 - RAFEEQ COMPLETE HAUSA NOVEL

asmy   

08 Oct 2024

11290

[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*



*PAID BOOK....* #400

NA
*_ASMY B ALIYU_*
Da
*_HAJJA CE_*


1.

Wata shahararriyar mota ce ƙirar zamani ash color da ta gaji da haɗuwa tayi parking a gaban katafaran store ɗin nan wato Sahad store. Sai da aka kusan shafe mintuna biyar kafin a ɓalle murfin motar wacce take ciki ta fito gabaki ɗayanta waje. Tafe take cike da nishaɗi da walwala sanye cikin shigar wata doguwar rigar jallabiya ƙirar ƙasar (Oman) kalar sararin samaniya. Kallo ɗaya zakayi mata kasan da cewar tana taƙama da kuɗin da Allah ya baiwa mahaifinta. Cikin isa da wata irin izza ta shiga ciki tana ware idanunta a cikin store ɗin. Duka-duka minti talatin tayi a cikin shopping store ɗin ta ɗakko duk wasu abubuwan da take da buƙata ta biya aka kai mata cikin mota. Maimoon Gwarzo kenan kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance, farace tas irin farin nan na larabawan asali, haka kuma doguwa ce bata da jiki sosai, gabaki ɗaya dai zubinta irin wanda zaka kalleta ne ka kasa ɗauke idanunka a lokaci ɗaya. Ƴa ce ga Alhaji Mustapha Gwarzo wanda mutum ne shi mai kawaici da tawakkali, sannan shi mutum ne mai tausayin gaske, uwa uba kuma mai riƙo ne da addininsa. Yana da matuƙar mutunta jama'a da son maƙotansa fiye da tunanin mutane. Shi ɗin mai sakin fuska ne a wajan mutane, Allah ya bashi wani irin sihirtaccen kyau domin shi ɗin jinsin Fulani ne na asali. Matarsa ta farko ta rasu ne a wajen haihuwar ƴarsa Maimoonatu. Ɗansu na farko shine Abdul-Shaheed Gwarzo sai Moobarak Gwarzo sannan kuma Maimoonatu Gwarzo. Tun bayan rasuwar mahaifiyarsu da kusan shekaru goma sai lokacin Alhaji Mustapha Gwarzo ya ƙara yin wani auren yana da matarsa suna tare. Sai kuma yaron da yake riƙo a wajanshi wato ɗan ƙaninsa wanda tun yana ƙaraminsa iyayen sukayi haɗari suka rasu wato RAFEEQ Habeeb Gwarzo. Sosai Alhaji Mustapha Gwarzo yake riƙe dashi yana jinsa tamkar ɗan cikinsa da ya tsugunna ya haifa, haka kuma ya haɗeshi cikin yaransa baya taɓa nuna mishi wani banbanci a komai na rayuwarsu. Shekarun Maimoona huɗu a duniya ta fara zuwa makaranta, tana da shekaru goma sha ɗaya ta gama matakin primary school, a shekaru goma sha bakwai kuma ta kammala karatunta na secondary school. Babu yadda yayunta ba su yi ba akan mahaifinsu ya tura Maimoonatu karatu can ƙasar waje amma yaki, a cewarsa yana son yaga ƴan matan Nigeria suna kishin ƙasarsu. Dan haka ya samar mata gurbin karatunta a can (A.B.U Zaria). Suma kansu mazan dakyar yabarsu suka fita zuwa ƙasasashen waje karatun. Maimoonatu tun tana ss1 tayi saukarta ta karatun alkur'ani maigirma da kuma sauran wasu littattafai na addinin musulunci. Abdul-wahaab shine mutum na farko da ya fara shayar da ita zaƙi da kuma ɗanɗanon garɗi irin na soyayya. Wato Wahaab mutum ne mai matuƙar hakuri da sanin ya kamata. Abdul-Wahaab mutum ne da yake da ƙarancin haƙuri dan ya zamto ba komai Maimoonatu keyi masa ta ɓata masa rai ba. Gabaki ɗaya Wahaab ba kyakkyawa bane, sai dai kuma baya cikin layin da za'a kirashi da munana ba. Kalar fatarsa mai duhu ce, amman da kaganshi kasan cewar yana cikin hutu da jin daɗin rayuwa. Yazo bautar ƙasa ne cikin makarantar A.B.U, wanda a nan ne alaƙarsu ta fara shida Maimoona. Shekarar su uku tare. Tana komawa gida toilet ta shiga, cikin jacuzzi ta shige tana sakarwa jikinta ruwa mai ɗan zafi. Tana zaune a cikin ɗakinta taji kamar hayaniyarsu Yayah Shaheed, ta duba agogon bangon ɗakin lokacin ƙarfe goma na safe. Ta runtse ido da sauri kafin ta ƙara buɗewa dan san tabbatar da cewar ba wai mafarki take yi ba. Da gudu ta fita daga ita sai kayan bacci a jikinta na riga da wando masu ɗan kauri, ko hula babu a kanta sai kananun kalabar dake ta faman reto a tsakiyyar bayanta. Sosai nayi matuƙar tsaye a wajan dan ganin Yayuna guda biyu a wajan, daman Moobarak Gwarzo ba ƙasa ɗaya suke karatu ba. Shi yana Germany su kuma suna ƙasar Cyprus. Da gudu ta ruga ta faɗa cikin jikin Yayah Shaheed tana ta faman dariyar farin ciki take faɗin. "Yaya kai ne kuwa? Anya kai ne Yah Shaheed?" Yana sake ɗago da fuskarta suna haɗa ido yake cewa. "Yeah ni ne nan mana autar Daddy me kika gani?" Ya faɗa yana ɗage mata gira ɗaya. Cikin murna take cewa. "Gaskiya Yaya ƙasar nan ta karɓeku kai da Yayah Rafeeq, Uhmmm kaga wani kalar haske da kuka yi kuwa?" Ta maida idanunta ta kalli gefen inda Yayah Rafeeq ɗin yake tsaye, ga mamakinta sai taga ya ɗauke kai daga kallanta. Ta marairaice fuska tare da kamo hannunsa cikin shagwaɓa take cewa. "I'm so sorry Yayana, kasan fa bama ƴar haka da kai, ko so kake Yayah Shaheed yayi mana dariya?"
Fisge hannunsa yayi wanda a dai-dai lokacin Daddy da Aunty suka fito. Da murmushi a fuskar Daddy yake faɗin. "Ku kuma haka ake zuwa babu wani sanarwa?" Dukansu suka juya tare da rungume Daddy. Rafeeq ne mai faɗin. "Mun gama komai Daddy har kwalayen karatun mu mun karɓa munyi bankwana da ƙasar Cyprus." Da farin ciki Daddy yake faɗin "Alhamdulillahi Allah yasawa karatun naku albarka." Duk suka haɗa baki. "Ameen." Suka amsawa Daddy. Haka Aunty ma ta tayasu murna. Tare suka shiga cikin kitchen da Aunty muka shirya masu abincin rana. Ƙarfe biyu suna gamawa Maimoona ta shige wanka, daman kuma tana son leƙawa gidan Aunty Amra wato ƙanwar Daddy. Har cikin parlor ta samu Daddy ta sanar dashi zataje yayi mata fatan sauka lafiya shi da Auntyn su. Harta shiga mota sai kuma ta fito da sauri ta nufi part ɗin su Yayah Shaheed, kai tsaye ɗakin Yah Rafeeq ta nufa, sai da taje sannan ta tsaya a bakin ƙofa tayi knocking kafin ta tura ƙofar ɗakin ta shiga. Ɗagowa yayi da sauri suka haɗa ido yayin da ya yiwa ruwan faron hannunshi wata irin kyakkyawar zuƙa. A hankali ta ƙarasa wajanshi ta karɓe jarkar ta wurgata ta window sannan ta dubeshi cikin muryar damuwa tana faɗin. "Meyasa hakan Yah Rafeeq? Ashe daman baka daina yiwa ruwa irin wannan shan ba tun a lokacin daka kace ka dai na?" Ranta ya ɓaci ta juya zata nufi ƙofa yayi saurin riƙo hannuta ya zaunar da ita a gefenshi. Ta harɗe hannunta akan kirjinta tana faman shan toka. Ganin yadda tayi ne yasa saura kaɗan Rafeeq ya fashe da dariya amman ya danne dan yasan idan har ya yi dariyar ya ƙara takalo wata rigima ne. "Okay na dai na but ina zakije hakan?" Kawar da fuska tayi gefe "Gidan Aunty Amra zanje." Ta faɗa still shaye da toka. Kallonta kawai yake with out blinking kallonta kawai yana sake faranta ranshi domin bashi da wani burin da ya wuce a duniyar nan Maimoonatu Gwarzo ta zama matarsa ta aure ba. "Me kake tunani haka?" Yaji sassanyar muryarta ta sake dukan cikin kunnanshi. Ya sake cijewa yace. "Babu komai, ina zaki hakan?" Sai da ta miqe tsaye sannan take faɗin. "Zanje gidan Aunty Amra ne." Numfashi yaja mai sanyi tare da faɗin. "Alright muje na rakaki toh." Ba tayi musu ba yabi bayanta su nufi motarta. Maimoona ke driving ɗin shi kuma yana gefenta da waya a hannunsa yana dannawa. Har ƙofar gidan Aunty Amra ta ajiye su sannan suka jera suka shiga cikin gidan. A falo Maimoona tayi sallama, da gudu Suhaila ta fito tana mata Oyo-yo-yo. Maimoona ta ɗagata sama tana zagaye parlorn da ita, wanda kuma hakan da tayi yasa Rafeeq Gwarzo ya harɗe hannayenshi akan kirji yana kallonsu yaji tankar a lokacin Maimoonatu matarsa ce da kuma ƴarsu. "Suhaila ina Mami take?" Cikin fara'a take faɗin. "Mami tana ɗakin Abba." Sake janyo hannunta tayi tana cewa. "Okay Suhal fa.?" Tace shima yana ɗaki yana buga game. Dai-dai lokacin Aunty Amra ta fito daga cikin wani ɗaki da fara'a take yi musu sannu da zuwa. Cike da mamaki kuma take tambayar Rafeeq yaushe a garin? Ya faɗa mata cewar ɗazu da safe. Da murna take faɗin. "Allah yasa wannan karon da matanku na aure a hannayenku kai da Shaheed? Dama ga auta nan Daddy na shirin yi mata aure banda ku. Da wani irin yanayi ya juya yana kallon Aunty Amra fuskarsa cike da tsantsar mamaki, kalmar auren da Maimoonatu zatayi yafi ko mai tsaya masa arai. Zai yi magana kuma aka kira Maimoonan a wayarta, dubawa tayi ganin yanayin yadda ta ɗora a jikin kunnan ta take wani amsa wayar ya tabbatar masa da cewa da namiji take wayar. Tashin hankalin da Rafeeq Gwarzon ya shiga a wannan lokacin ba zai faɗuba. Ya rinse ido yana lasar ƙasan lips ɗin shi da harshe yana cewa. "Aunty bari zanje na dawo zuwa anjima." Rafeeq ya faɗa yana ƙoƙarin barin cikin parlorn cike da tashin hankali yana kuma jin wani mugun sanyin na shigar masa duk wata ƙofa ta cikin jinin jikinsa. Tun daga tsakiyyar kansa har cikin tafin ƙafarsa haka yake jin sanyin. Sai da ya fita compound ya tuna baya tare da car key, juyawar da zaiyi ya hango Maimoona na fitowa da fara'a cikin fuskarta. Ganin yanayinsa yasa taji walwalar da take ciki na ɓacewa a hankali. Hannu kawai ya miƙa mata yana cewa. "Bani key ɗin." Kallonsa take ganin irin damuwar dake kwance a cikin fuskarsa yasa taji wata irin damuwa itama, dama kuma gashi duk cikin yayunta tafi jin Rafeeq Gwarzon har a ranta wanda batasan dalili ba. Jiki a sanyaye ta miƙa masa key ɗin tana faɗin. "Daman shi na fito na baka, but wai ina zaka haka kake ta sauri?" Batareda ya kalleta ba yake faɗin. "Yanzu zan dawo ba wani daɗewa zanyi ba." Daga haka ya shiga motar yai mata key yana yiwa mai gadi horn, tana kallon motar har tabar cikin compound ɗin sannan ta ɗan yi ajiyar zuciya ta juya ta koma cikin gidan tana jiran isowar Abdul-wahaab...

****************
Har parlorn baki takai Abdul-wahaab, ya ɗaga kai ya kalleta yana faɗin. "Sai da aka gama shanyani ko?" Ta sakko da tray ɗin agabansa mai ɗauke da kayan motsa baki sannan ta zauna akan kujera mai fuskantarsa fuskarta kunshe da murmushi. Sake kallanta yai cike da soyayyarta yace. "Yanzu ke madam duk wannan abubuwan da, kika ajiye min su kike na cinye komai?" Maimoona ta sake yin wani sassanyan murmushi muryarta a sanyaye take cewa. "Idan har ka cinye zanfi kowa jin daɗin haka, ko babu komai nasan baka tafi da yunwa ba." Idanuwa suka haɗa tayi saurin ɗauke nata saboda kunyarsa da takeji. "Shikenan sakko muci tare." Ta buɗe ido tana kallansa. "Nifa kai kaɗai na kawowa kaci kabar ragowar." Yayi ƴar dariya kafin ya ɗauki juice ɗin yasha. Abdulwahab bai jima ba yayi mata sallama, anan kuma Aunty Amra ta roƙeta alfarma akan ta kai Suhail da Suhaila wajan shan ice cream ɗan tun jiya tayi masu alƙawarin zata kai su gashi bata samu lokaci ba, kuma yau Abbansu yana azumi zata tsaya ta haɗa masa abun buɗa baki. Daga haka Maimoona ta kwashesu a motar Aunty Amrah zuwa wajan shan ice cream. Tana gama yin parking ta hango motar ta a wajen, mamaki ya kamata, kenan Yah Rafeeq nan yazo? Aikuwa fitowar da Maimoona tayi daga cikin mota ta hangoshi cikin motar shi da wata budurwa zaune a gaban motar. Ƙarasawa sukayi gaban motar ita da yaran, kallo ɗaya tayiwa budurwar da irin shigar dake jikinta ta ɗauke kai tana taɓe baki kafin subar wajen da sauri. Budurwar ta kallonshi tana faɗin. "Ita kuma wannan wacece?" Sai da yaja numfashi mai ƙarfi kafin ya iya buɗe bakinsa. "Ƙanwata ce." Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba yana tada motar gamida barin wurin. Kusan awa biyu sukayi a wajen sannan suka dawo gidan. Ganin Rafeeq yaki dawowa ne yasa ta yiwa Aunty Amrah sallama tare yi mata ƙaryar cewa Rafeeq ɗin yana waje yana jiranta. Tana fitowa tayi tsaye a gefen hanya tana jiran abun hawa ranta duk a ɓace, sai ga Rafeeq ya tsaya ya sauke glass yana faɗin ta shigo. Ai kuwa ta wani haɗe rai tana faɗin. "Kawai ka tafi zan samu abun hawa na koma gida." Baki buɗe yake kallanta. "Kinsan Allah ranki zai ɓaci idan baki shigo ba." Ya faɗa da ɗan ɗaga murya. Ta buɗe ƙofar motar a fusace ta shiga tana jin wani irin takaici. Har suka hau babban titi babu mai kallon ɗan uwansa. Wayartace ta fara ringing sai dai tana ji taki ɗauka. Cike da mamaki Rafeeq ke faɗin. "Kina jin waya amma bazaki ɗauka ba.?" Tayi shiru tana faman cuno baki, sai kawai taga yayi parking a gefen hanya ya buɗe jakar ya ɗakko wayar yana dubawa, sunan da yaga yana yawo akan screen ɗin wayar ne ya karya masa duka wani kwarin gwiwarsa. Gani kawai tayi ya tada motar tare da harbata kan titi sun ci gaba da tafiya. Ita kam tana mamakin canjawar yanayin sa, ikon Allah kawai ya kaisu gida ba wai tuki cikin nutsuwa ba. Suna cikin cin abincin dare Daddy ya kalli Shaheed da Rafeeq yake sanar dasu zancen auren ƴar uwarsu Maimoon nan da wani watan, sannan zata cigaba da karatunta a ɗakin mijinta. Rafeeq Gwarzo yafi kowa shiga cikin tashin hankali lokacin da yaji haka a bakin Daddy. Wata irin dariyar farin ciki Shaheed ya fashe da ita yana kallon Maimoon da takeji tamkar ta nutse cikin ƙasa saboda kunya. "Finally ƙanwata zatayi hankali very soon Inyeeee." Ya faɗa sounding so very happy a muryarsa. Da gudu Maimoon ta tashi ta nufi ɗakinta tana dariya. Shaheed Gwarzo na kwala mata kira amma bata ko kalleshi ba. Rafeeq kuwa gabaki ɗaya kasa cigaba da cin abincin yayi, ji yayi kalaman Daddy suna taɓa zuciyarsa, da murmushi yake faɗin. "Allah ya sanya alkhairi." Aunty ta karɓa da "Amin." Tana sake cewa. "Ya kamata kuma kuzo ku fito da matan aure duk ku shiga gidajenku dan abin kunya ne ace kaf cikin ku babu mai tsayayyar budurwa." Dariya kawai Shaheed yayi amma Rafeeq barin parlorn yayi yana jin kirjinsa nayi masa wani irin nauyi. Yanzu dagaske rasa Maimoon Gwarzo zai yi? Ya zai yi da soyayyar da yake mata shekaru kusan goma sha biyar zata tashi a banza? Ya dafe gefen kansa yana jin komai na cikin duniyar yana tsaya masa cak! Ko kafin wayewar gari jikinsa yayi mugun zafi haka ya tashi da wani irin zazzabi. Jin shirun yayi yawa Rafeeq bai fito ba yasa Shaheed ya leƙa cikin ɗakinsa a nan Rafeeq ɗin dunkule cikin duvert yana rawar sanyi. Hankalinsa yayi mugun ɗagawa, ya ƙarasa da sauri ya ɗagoshi duka zuwa cikin jikinsa yana tambayarsa meke damunsa, ganin duk yabi ya ruɗa ɗan uwansa kasancewar kaunarsu dabance a cikin gidan yasa Rafeeq sake rufe ido. Babu kalar tambayar da Shahed bai yi masa ba amman yaki buɗe baki yayi masa magana. Waya Shaheed ya ɗaga ya kira family doctor ɗin su. Kai tsaye cikin gidan ya tashi ya nufa, Aunty ya samu a kitchen tana shirya breakfast ita da ƴan aiki ya gaisheta yana tambayarta daddy fa? Ta faɗa masa cewar yana parlorn sa. "Lafiya dai ko?" Ta tambaya tana kallon yanayinsa. "Daman Rafeeq ne baya jin daɗi." Cikin sauri tace. "Meya samesa?" Cike da rashin sani yace. "Wallahi nima ban sani ba, amman jikinsa yayi zafi sosai." Aunty ta girgiza kai tana faɗin. "Toh Allah ya kara sauki, bara na haɗa tea akai masa ya samu ya sha sai ka kira family doctor ɗin." Daga haka Shaheed ya nufi parlorn mahaifinsu. Da sallama ya shiga duk da sun gaisa dan tare sukayi sallar asuba, amman sai da ya ƙara gaisheda Alhaji Mustapha Gwarzo. Cike da fara'a ya amsa yana kallon yaron nasa dake tare da damuwa cikin fuskarsa. "Lafiya dai koh?" Anan Shaheed ya faɗawa Daddy yadda ya tarar da Rafeeq. Dashi da Daddyn suka nufi part ɗin su wanda shine na farko a cikin gidan mai ɗauke da ƙaton falo da kuma ɗakunan barci dauke da karamin parlor a kowanne. Kai tsaye room ɗin Rafeeq suka nufa Shaheed na ɗauke da ƙaramin tray wanda Aunty ta haɗa masa tea da wainar kwai a cikin plate...





#Hajja ce
#Asmy b Aliyu
#Rafeeq Gwarzo
#Maimoon Gwarzo
#Wahaab Bamalli
#Haske Writers Association......
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*


*PAID BOOK*


NA
_*ASMY B ALIYU*_
DA
*_HAJJA CE_*






2.


Tunda yaji muryar Daddy a cikin ɗakin sai kawai yaji duk gabaki ɗaya ana sake hargitsa masa ƙwaƙwalwarshi, ya sake curewa cikin duvert tare da rintsa idanuwa yana sauke wahalallan numfashi. Alhaji Mustapha ya ƙarasa wajan bed ɗin tare da sanya hannunsa ya yaye duvert ɗin jikinsa yana ƙarewa ɗan marayan yaran nashi kallo. "Rafeeq meke damunka haka?" Maimakon yayi magana kawai sai ya fara ƙoƙarin tashi zaune, Shaheed ya taimaka masa ya jingina bayansa jikin gadon yana furta. "Gajiya ce kawai Daddy kuma na kasa yin bacci." Cikin tsananin tausayawa Daddyn ya sake taɓa forehead ɗinshi, jin zafi sosai yasa shi cewa. "Wannan zazzabin na jikinka yafi ƙarfin ace na gajiya ne kaɗai, ka buɗe bakinka kasanar dani ainahin abinda yake damunka, ko kanada wanda ya fini ban sani ba?" Cikin sauri Rafeeq ya shiga girgiza masa kai yana cewa. "Haba Daddy har akwai wani da zaifika a gurina? Please kayi hakuri idan na ɓatamaka rai." Ganin yadda ya wani gigice ne yasa Daddy cewa. "Shikenan naji yanzu dai karɓi tea kasha Dr Arham yana hanyarsa ta zuwa gidan nan ya dubaka." Shaheed ya shiga miƙa masa tea cup ɗin ya karɓa tare da kaiwa bakinsa. Wani amai ne ya taho masa, kafin kace wani abu ya fara sakinshi a duka jikinsa. Alhaji Mustapha ya riƙeshi a jikinsa yana matse mishi shoulder yake faɗin. "Subahanallahi wannan wane irin ciwo ne yake damunka?" Hankali a tashe Shaheed ke cewa. "Da alama ba wai zazzabin bane kaɗai." Daddy ya jinjina kai. Wayar Shaheed ce ta fara ringing ya zarota daga cikin aljihu, Dr Arham ya gani ba tare da ya tsaya ba ya fice daga ɗakin yana amsawa. Tare suka shigo cikin ɗakin, a lokacin Alhaji Mustapha ya shiga gyarawa Rafeeq jikinsa wanda gabaki ɗaya ya rasa duk wani ƙwari na

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login