Showing 3001 words to 6000 words out of 34129 words
jikinsa. "Yauwa Dr bari na saka masa riga sai ka duba shi." Ya faɗa yana buɗe wardrobe ɗin kayan Rafeeq ɗin. Riga da wando na bacci ya zaro masa suka sanya masa shida Shaheed, sannan suka taimaka masa ya bar kan gadon wanda bedsheet ɗin ya lalace da amai. Cikin soofa yake ƙoƙarin kwanciya suka hanashi, Daddy yace a maidashi room ɗin Shaheed kafin a gyara masa nashi. Sosai Dr Arham ya duddubashi kafin ya rubuta wata allura da magani sai kuma drip da za'a yi masa sakamakon rashin kuzarin da bashi dashi, sannan jikinsa yana buƙatar hakan saboda babu abinci a cikinsa. Kallansa kawai Alhaji Mustapha keyi yana faɗin. "Yanzu sabida Allah meyake shirin haifar maka da heart attack Rafeeq? Ko dai wani abin ake yi maka wanda ka kejin babu daɗi a cikin gidan nan? Ka sanar dani zanyi maganin abin da yardar Allah." Rafeeq yai shiru yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa, yasa hannunsa cike da dauriya ya kamo na Daddy yana kuma rintsa ido. "Alhaji ku tsagaita da yi masa yawan tambayoyi yanzu, duk wani abu da zai yi dogon bayani yanzu a ɗan barshi har mu samu zuciyarsa ta daidaita, yanzu bari naje a ɗakko allurar da sauran abubuwan da za'ayi masa, kafin na dawo a samu ya ɗan ci wani abun koyaya yake kafin na zo." Cike da sauraro Alhaji Mustapha ya amsawa Dr, yana fita ya kalli Shaheed yana cewa. "Shaheed kira mai kula da side ɗinku ya gyara room ɗin Rafeeq yanzun nan." Babu ɓata lokaci kuwa Shaheed ya fita ya sanar dashi kafin ya koma ɗakin ya zauna sukaci gaba da jiran Dr. Kai tsaye wajan dining room ta nufa inda aka gama shirya breakfast, kallan wormers ɗin ta shiga yi kafin ta fara buɗewa dan ganin abubuwan da suke ciki. Kujera taja tare da janyo flask ɗin kunun madara ta zuba cikin glass cup, jin an shigo cikin parlorn ne yasa ta ɗan waiga kaɗan, Yaya Shaheed ne ya haye stairs still idanunta suna kan hanyar taga ya shiga ɗakin Daddyn su. Cikin sauri taga ya sake fitowa zai fice ba tare da ya kulata ba tayi saurin cewa. "Yaya Shaheed Daddy bayanan nima naje mu gaisa na tarar babu kowa." Cikin yanayin sauri yake ce mata. "Yeah muna tare dashi a wajan Rafeeq za'a sanya masa drip." Da sauri ta miƙe ganin ko tsayawa beyi ba tabi bayansa. Maimoon tasha mamaki lokacin da taga yanayin da Rafeeq ke ciki, ta dinga zaro ido cike da tashin hankali take tambayar Alhaji Mustapha. "Daddy me ya samu Yaya haka?" Alhaji Mustapha Gwarzo ya kamo hannunta ya zaunar da ita a gefenshi yana cewa. "Muma bamu sani ba kiyi masa addu'a kinji ko?" Jikinta yayi sanyi ta shiga leƙen fuskarsa da take a lumshe yana jan numfashi kaɗan-kaɗan. Hannun mahaifinta ta kamo cike da tsantsar damuwa take cewa. "Ikon Allah sai kace jiya ba muna tare da shi ba. Daddy haka mutuwa fa takeyi ko? Kuna tare da mutum lafiya lau sai kaji ance ya mutu." Alhaji Mustapha ya sake damke hannunta yana kallanta yace. "Haka ne auta . shi yasa a kullum ake son mutum ya dinga yafiya dan kar a mutu ana jin haushin wani ko wata." Sosai jikinta ya mutu da yanayin da taga ɗan uwan nata a ciki. Har aka gama masa allurar aka daura masa drip ɗin be motsa ba bare ya buɗe idanunsa. Yana jin duk wasu kalamai nata da suke fitowa daga cikin bakinta suna sauka a duka sashen jikinsa wanda har baya so yaji tayi shiru. "Shaheed kaci gaba da kula dashi bari naje sitting room zanyi baki." Cewar Alhaji Mustapha yana miƙewa tsaye ya fice daga cikin ɗakin. Maimoon ta koma wajan da Daddyn nasu ya tashi wato kusa da ƙafafuwan Rafeeq ta zauna har jikinta yana shafarsa yaji wani irin zirrr har cikin brain ɗinshi. "Kije kiyi breakfast ɗinki mana." Cewar Shaheed yana buɗe wardrobe ɗinshi. Da yanayin damuwa take cewa. "Wane irin breakfast zan iya yi Yaya Shaheed? Wallahi bazan iya ba yadda naga Yaya Rafeeq a cikin wannan yanayin." Rafeeq da idanunsa ke lumshe jin kalamanta ya sake jefa masa wata irin wutar soyayyarta a cikin ransa, ya dinga jin tamkar ya janyota zuwa cikin kirjinsa da yake jin tamkar zai rabe gida biyu. "Zaifi miki kyau dai kije kici karki janyowa kanki wata matsalar, kina gani dai shima harda ulcer da take damunsa." Girgiza kai tayi tana sake maida idanunta kan Rafeeq cike da tausayi take faɗin. "Jiya beci abinci ba ina kallansa." Rai a ɗan ɓace Shaheed yace. "Waike kin fimu damuwa da halin da yake ciki ne? Oya ki tashi ina san na kintsa a ɗakina kinzo kin zauna, sai kwana -kwana nake yi miki dan ki fita kin kasa ganewa." Maimoon ta juya tana kallan Rafeeq tana jin kamar idan har ta bar ɗakin wani abu marar daɗi zai iya samun shi, dan haka ta kawar da kai gefe tana cewa. "Yaya Shaheed ba wanka zakai ba? Taya za'a barshi shi kaɗai anan wajan, kawai kaje kayi ka barni na kula dashi." Baki wangale Shaheed yake kallanta, sai kuma ya juya ya shige bathroom bayan ya ɗauki ƙaton towel. A hankali ya shiga buɗe idanunsa ya ɗora su akan kyakkyawar fuskarta, bata san yana yi ba sakamakon wayarta da take faman dannawa suna chatting da Abdul-Wahaab. Kira ne ya shigo wayar ta ɗan saki murmushi tare da daga wayar ta kara jikin kunnenta tana cewa. "Wato chatting ɗin beyi maka ba dole sai munyi waya ko?" Rafeeq yaji kirjinsa ya sake yi masa wani irin nauyi, idanunsa suka sake ƙanƙancewa, zuciyarsa ta shiga yi masa zugi. Cikin wata irin murya Maimoon taji yana cewa. "Please get out." Jin yayi magana ne yasa tai saurin waigowa tana kallansa, sai dai idanunsa still a rufe suke. "Yaya Rafeeq magana kakeyi?" Yai mata banza sai lips da ya shiga cizawa da hakorinsa. "A'a bada kai nake ba nida Yaya Rafeeq ne bashi da lafiya." Cewar Maimoon tana sanarwa da Wahaab. Da yake bayajin abinda Wahaab ɗin ke cewa sai dai ita idan tayi magana yaji tace. "Eh shine bashida lafiya ka ganshi nan kwance ana masa ƙarin ruwa." Da salon muryar da yaji tana magana ne yasa shi kasa jurewa sauraranta, dan haka cikin azabar ciwo taji yace. "I said ki tashi ki fita." Tayi saurin kallansa da mamaki take faɗin. "Yaya Rafeeq wai dani kake ne?" Cikin tabbaci ya shiga ɗaga mata kai. Maimoon ta miƙe tsaye tare da ficewa tana turo baki.
Shiru ya ziyarci cikin ɗakin sai kuma yaji duk babu daɗi, ashe har gwara tana wajan yana jin motsinta hankalinsa yafi kwanciya. Yanzu kuwa da ta tafi sai yaji wani irin kunci, tsanar Abdul-Wahaab ta shiga cikin zuciyarsa ta zauna, duk da bai taɓa ganinsa sai da ya hango yanayinsa a cikin idanunsa ya kuma ji cewa Maimoon bata dace dashi ɗin ba. Shaheed ne ya fito yana ware ido ko zai ga Maimoon a cikin ɗakin amma baiganta ba, yaje ya murzawa ƙofar key sannan ya fara shirya jikinsa. Sai da ya kammala komai sannan ya ɗakko wayarsa ya kirata, bugu ɗaya ta ɗauka tana faman ɓata rai yace ta shiryo masa breakfast ta kawo masa ɗaki. "Zansa Lami ta kawo maka." Cike da mamaki Shaheed ke cewa. "Ke mekike yi da bazaki kawo min da kanki ba?" Maimoon ta sake cuno baki kamar tana gabansa take faɗin. "Toh ba Yaya Rafeeq ya koroni ba." Kallon inda Rafeeq ke kwance yayi ganin yadda yake tun ɗazu haka yake yanzu yasa Shaheed cewa. "Shida yake bacci tun ɗazu shine zakice ya koreki? Kinga malama idan bazaki kawo min ba ki barshi idan na shigo naci." Yana kaiwa nan ya katse tare da dire wayar yana jan ɗan ƙaramin tsaki. Rafeeq yana jinsa babu abinda yai masa daɗi irin yadda zata dawo ɗakin, yasa a ransa idan har tazo kawo breakfast ɗin bazai barta ta kuma fita ba bare taje suyi waya da Wahaab. Bakinta da sallama ta turo ƙofar da kafarta hannunta ɗauke da tray idanunta akan gadon da Rafeeq ke kwance. Tunda yaji isowarta shi kuma ya buɗe idonsa, kallanta ya shiga yi sanye take cikin wasu riga da wando Pakistan pink da ratsin white ɗin fulawoyi a jiki, tayi kyau sosai kai kace ita tayi kanta . Wajan Shaheed ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin tana cewa. "Ni duk bansan abinda zakaci ba shi yasa kawai na zubo maka sinasir dan naga kamar shine ka daɗe bakaci ba." Shaheed na duba wasu book's yake cewa. "Kin kyauta kuwa sister dan a Cyprus ina mukaga wani sinasir." Ta juya zata fice Rafeeq ya buɗe baki a hankali ya kirata. "Moon." Tana jinsa amma tayi kamar bataji ba, sai da Shaheed ya kalleshi yana cewa. "Ah ashe ka farka? Maimoon Rafeeq na magana fa." Cak ta tsaya taki juyawa su haɗa ido saboda taji haushin korar da yai mata ɗazu. "Bakiji ba ne?" Shaheed ya faɗa da ɗan fushi ganin taki zuwa. A hankali ta juya ƙarasawa tayi wajanshi tana wani kifta idanuwa. "Zauna." Cewar Rafeeq idanunsa suna kanta. Gefen gadon ta zauna tana wasa da mayafin Pakistan ɗin jikinta. Idanunsa ya mayar ya lumshe, ta kalleshi cike da mamaki ganin bece komai. "Yaya Rafeeq gani fa." Ta faɗa cike da haushi a cikin muryarta, ya ɗan miƙa hannunsa da babu drip a jiki ya riƙo nata, ta kalli hannunwan nasu tana ware ido. "Kiyi zamanki naga kamar ɗazu kinji haushi right?" Cikin gaskiyarta tace dashi. "Sosai ma." Sakar mata hannun yayi yana sauke numfashi, kallosa take yana jinta har tsakiyar zuciyarsa yace. "Idan na mutu zaki damu?" Kafin tayi magana Shaheed yace. "Haba guy ya da wannan maganar kuma? Dan Allah ka dena maganar mutuwa sai munyi aure mun ajiye jikoki." Maganarsa tasa Maimoon tuntsirewa da dariya, yanayin yadda take dariyar cikin farin ciki shine ya haddasawa Rafeeq jin duk wani ciwo a jikinsa ya warke. "Wayaga Yaya Shaheed da jika ah." Ta faɗa tana sake fashewa da wata dariyar. Daga haka kuma sai duk ta manta da ɓacin ranta suka shiga hira duk da cewa Rafeeq baya sanya musu baki. Har ruwan ya ƙare Shaheed ya zare masa sannan ya maidashi ɗakinsa. Maimoon ce ta shiga bathroom ɗinshi ta haɗa masa ruwan wanka mai zafi, sai da ya shiga cikin bathroom ɗin sannan ita kuma ta fice zuwa sashen su...
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Maimoon Gwarzo
#Shaheed Gwarzo
#Dr Arham
#Haske writer's association...
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ....*
*PAID BOOK....* #400
NA
*_ASMY B ALIYU_*
Da
*_HAJJA CE_*
3..
Ɗaure da milk ɗin towel ya fito a ƙugunsa yana sake sharce ruwan da yake kwance a saman fuskarshi, kai tsaye closet nashi ya nufa ya zuge murfin wardrobe ɗin yana san tantance waɗanda zai sanya. Waɗanda suka kwanta a cikin zuciyarsa ya ɗakko domin ya daɗe beyi irin shigar ba. Gefe bed ya ajiye kafin ya isa wajan mayukansa masu matuƙar kyau da gyara fata, jikinsa ya shafe dasu sannan ya miƙe yasa kayan. Shigar riga da wando yayi na farar shadda wacce aka yi masa ɗinkin zamani masu gajerun hannuwa, ya janyo hularsa zannah bukar baƙa ya ɗorata akansa tare da isa wajan madubi yana gyara botir ɗin gaban rigarsa. Tsayawa kawai ya yi yana zubawa tsari da kuma kamala irin wacce ubangiji Allah ya zuba masa, yasa hannu yanajan dogon karan hancinsa da ya ƙara ƙawata kyaun fuskarsa sai wani buɗe idanuwa yake kamar mai san gano wani abu a cikinsu. Rafeeq Habeeb Gwarzo kenan matashi mai ji da taƙama, uwa uba kuma kyawun da Allah subahanahu wa ta'ala ya zuba mishi. Sai dai abinda yake matuƙar bashi mamaki shine yadda yaga Maimoon Gwaro batayi masa irin soyayyar da yakeji a cikin zuciyarsa, kallansa takeyi tamkar yadda take kallan su Shaheed Gwarzo da suka fito ciki ɗaya. Juyawa ya yi a hankali ya zaro takalmi yasa ya ɗauki car key yafito. Kai tsaye wajan tsaleliyar motarsa ya nufa wacce Alhaji Mustapha Gwarzo ya sissiya musu, tashi black marsandi ta Shaheed kuma white sai ta Maimoon red color yayin da Mubarak sai ya dawo za'a bashi tashi. Yana ƙoƙarin shiga yaji zazzaƙar muryarta mai sauke masa duk wani noti dake ɗaure a jikinsa. Kallonta yake da dukkan nutsuwarsa har ta iso gabansa idanunshi suna zagaye jikinta. Sanye take cikin doguwar riga armless tayi matuƙar karɓar surar jikinta, kanta da hula kamar net ana hangen tarin gashin dake kanta. "Yaya sai ina kuma?" Ya riƙe murfin motar yana faɗin. "Unguwa." Wajansa taje itama ta riƙe murfin motar tana leƙa ciki, yadda kusancinsu yazo har yana jin ƙamshin turaren jikinta yana shigar masa cikin kai ne yasa shi faɗin. "Kina da saƙo ne?" Maimoon ta dago tare da kallansa da manyan idanunta farare tas tace. "Naga kasha kwalliya kamar wanda zashi taɗi, da alamar Auntyn tawa ƴar Nigeria ce, ko itace wacce naganku tare?" Cikin haɗe rai Rafeeq yake kallanta yana ƙoƙarin shiga cikin motar ya zauna yake faɗin. "Idan itace menene?" Maimoon ta samu kanta da haɗe rai, cikin yatsina fuska take faɗin. "Batai min ba tun lokacin da na ganku tare, haba Yaya duk macen da zaka aura karka bari idanunta su buɗe da zuwa irin wajajan nan indai ba matarka bace ta aure. Kawai ni yarinyar batai min tun kallan farko dana ganku." Kallanta ya yi sosai yaga dagaske take maganar, sai da ya murza key a jikin motar yake cewa. "Waye ya zaɓar miki Abdul-Wahaab?" Tambayar tazo mata a wani irin yanayi, ta turo baki tana wani kifta idanuwa take cewa. "Wahaab daban ne Yaya Rafeeq, ita kuma waccen daga gani bata da kamun kai." Cikin tsuke fuska ya kalleta zai yi masifa sai kuma yaji ya kasa, yasa hannu zai rufe motar Maimoon ta riƙe tana cewa. "Dan Allah karkaje wajan yarinyar nan baku dace da juna ba sam." Fizgo ƙofar yai ya kalleta yana cewa. "Kema ai baki dace da wanda zaki aura ba, so kowa yaje yaji da matsalarsa bye sai na dawo." Yaja motarsa da ɗan karfi har Maimoon tana saurin yin gefe guda ganin kamar zai mangareta. Har sai da ya fice daga cikin gidan sannan ta juya ta koma ciki tana jin takaici indai har wajan wannan yarinyar zashi, bedroom ta wuce ta ɗauki wayarta tana daddanawa. Rafeeq na fita kai tsaye wani store ya shiga, kayan masarufi yasa aka jidar masa yasa a booth ɗin motarsa sannan ya nufi gidan marayu dake nan cikin ƙwaryar Kano. Daman tun ba yanzu ba Rafeeq yake zuwa kai taimako hakan yasa duk masu gadi da masu kula da gidan suka sanshi, ko baya cikin ƙasar yana turo da kuɗi ayiwa marayu abinda sukafi buƙata. Mutum ne shi da abin hannunshi baya rufe masa ido, yana matuƙar jin daɗi a duk lokacin da yayi irin wannan zuwan, yakan ji duk wata damuwa tashi Allah yana yayewa. Ɓangaren bebaye masu buƙata ta musamman aka fara rakashi, cike da tausayawa ya dinga shafa kawunansu yana sake godewa ubangiji da ya kaishi hannun Alhaji Mustapha Gwarzo, banda haka yasan shima da Allah zai iya kawo gidan nan yayi rayuwa makamanciyar da yaran nan keyi. Sai da aka rakashi ko'ina sannan ya fito ya bada umarnin sauke kayan dake cikin booth tare da yin alƙawarin kawowa yaran da suke under 6years suturar sakawa dan ya lura tayiwa yaran karanci a jikinsu. Yana cikin tuki yaji wayarsa na ringing, janyota yayi daga inda ya ajiye yana dubawa yaga mai kiran nashi, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya daure yai daga batare da yace komai ba. "Jan aji ma da yazo wajanka sai da ya sara maka, uhmm kana ina ne?" Ɗan yatsina fuska yayi kamar tana kallansa yake cewa. "Tuki nakeyi." Yanayin yadda taji yana maganar ne yasa ta gane baya cikin walwala, Zee Leeman ta kuma kashe murya cikin san janyo hankalinsa take cewa. "Ina Ado Bayero mall ko zaka ƙaraso?" Kalaman Maimoon ne ya faɗo masa inda take nuna masa cewar ba ajinshi bane yawan fita da mace zuwa wajan shaƙatawa wacce ba muharramarsa ba. Sai dai kuma shi mutum ne mai yawan san fita outing, yana so yaga yana zagawa cikin duniya dan ya dinga ganin yadda rayuwa take garawa. Karya kan motar yayi yana cewa. "Ganinan zuwa." Katsewa sukayi yana wani rintsa ido gani yake kamar bayajin shawarar ƴar uwar tashi, sai dai kuma in har beje wajan Zeee ɗin ba to babu wani waje da zashi, gida ne kuma ko yaje babu abinda zai yi a can ɗin. Tunda ta hangoshi takejin wani irin farin ciki yana cika mata zuwa, lokaci ɗaya kuma ta miƙe tare da nufowa inda yake. Kallan juna suka tsaya yi Rafeeq ya ɗage mata girarsa guda ɗaya alamar "Lafiya?" Handbag ɗin dake hannunta ta janyo tare da rungumeta a kirji. "Muje ko?" Ta faɗa tana nuna masa hanyar shiga wajan wasanni, shi yayi canji sannan suka biya suka shiga gurin.
Kai tsaye wajan zama suka nema suka zauna, Rafeeq yana karaɗe idanuwansa a wajan tamkar wani bako. Zee Leeman da takejin wata irin soyayyarsa tana taso mata takai hannunta tare da riƙo nashi, kallanta yayi sosai kafin ya janye idonsa acikin nata idon yaji tana faɗin. "Na ƙagu naji kace zaka fara zuwa gidan mu dan su san da matsayinka , amma kai sai naga kamar baka shirya aure na ba why?" Ya sauke wani irin numfashi yana zare hannunsa daga cikin nata yake cewa. "Zee har yanzu kin kasa gane inda zuciyata ta dosa, please mubar maganar auran nan yanzu." Cikin yanayin damuwa take sake kallansa, tana so ta gane sonta ne bayayi ko kuwa dai shirya yin aure yanzu ne baiyi ba? Gabaki ɗaya bata gane inda zuciyarsa ta nufa akan alaƙarsu, baya mata wulakanci haka kuma soyayya yake yi mata tamkar yadda saurayi da budurwa keyi. "Kasan ni macce ce Rafeeq, rayuwata kalilance zan so ace duk wannan zaman da mukeyi da kai ya zama mata da miji ne mu. Dan Allah baby ka shirya ka fara zuwa gidan mu su Abba su san da zamanka." Kallanta yake yi cike da
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book