Showing 30001 words to 33000 words out of 34129 words
mata wayar ganin mai kiranta a waya sai da taji wata faduwar gaba wacce bata taɓa jin kalar ta ba, tana ɗagawa yake faɗa mata ta sameshi a part ɗinsu, yana faɗin haka batareda ya jira me zatace ba ya sauke wayarsa yana jin yadda kafafunsa sukayi masa wani irin nauyi na ban mamaki, dakyar ya taka kafafunsa zuwa cikin part ɗinsu. Anan parlor ya zauna ko minti goma bai yi da zama ba Maimoon ta bayyana cikin falon, wani irin kamshinta ne ya fara bayyana masa cewa ta shigo cikin parlorn kafin yaji muryarta a kansa tana faɗin. "Yaayaah!" Muryar tata kuwa har wani shaking takeyi saboda yadda tayi kewarsa. Miƙewa tsaye yayi yana kallonta da wani irin shauƙi wanda ya fito tun daga cikin zuciyarsa. Rungumeshi tayi da sauri kamar wacce akaiwa baki, wani irin bugawa kirjinsa keyi, jinta ajikiinsa ba ƙaramin kokuwa yake da numfashinsa ba wajan dakewa. "I miss You so much Yaya, da gaske nayi kewarka." Ta faɗa muryata na karyewa. "Karki kadamu Moon bakijin wani kalar nauyi da kika yiba?" Ya faɗa da muryar da ya kwana biyu bai yi mata magana dashi ba. Maimoon ta zare jikinta daga cikin nasa ta shiga turo masa kyakkyawan bakinta, a shagwabe take faɗin. "Bani da nauyi fa Yaya sai kace wata ƙatuwa zakace zan kadamu." Dogon hancinta yaja gamida ware mata mayyan idonsa. Murmushi takeyi sosai rabon da yaga wannan murmushin a kyakkyawar fuskar nan an kwana biyu. Numfashi yaja tare da jan karan hancinsa yake faɗin."Kinata min ƙorafi ban miki komai na gudunmawa ba, bansan me zan yi miki ba dan nasan anriga an gama miki komai." Hannunsa ya tura cikin ajihun rigarsa ya fito da wani ɗan qaramin kit ya buɗe. Sarqa ce ta goal da ƴan kunne sai kuma zobe sai wani irin walwali takeyi. Zata yi magana ya juyata ya ɗauki sarqar yana saka mata jikin wuyanta. Hakama ƴan kunnen yaci sa'a ko ƴan kunne bata dashi a lokacin. Bakinta gabaki ɗaya yaki rufawa, hannunta ya kama ya saka mata zoben yana kallonta da wani farin ciki da yake shimfiɗe acikin fuskarta. "Wishing u Allah khair Noor with blessings in ur new home little sis." Ya faɗa yana danne wani mugun abu a cikin wuyansa. Lokaci ɗaya hawaye suka cika idon ta. Rungumesa tayi cikin rawar murya take faɗin. "I love You so much Yaya Rafeeq ɗina, Allah nasan zanyi kewarka sosai." Ɗagota yayi ya sumbaci goshinta yana faɗin. "Duk lokacin da kike bukata ta ina nan kirana kawai zaki yi, oya jeki gida Moon bana son hawayen nan karki karya min zuciya." Ya faɗa yana kallonta. Da wani yanayi akan fuskarsa. Girgiza kai ta shiga yi tana faɗin. "Nagode Yayana." Juyawa tayi tabar parlorn da ido ya bita tana barinsa da fitinannen kamshinta dake sakashi cikin wani yanayi. Maimoon kuwa duk da ba wannane kawai zinarinta ba, tana da wanda aka bata gado na mahaifiyarta, ga kuma wanda Daddy ya siya mata dana cikin kayan lefe, amma wannan da Rafeeq ya bada yafi kowanne muhimmanci a wajanta. Tana tafiya tana kallon zoben da ya saka mata wanda take jinsa har cikin tsokar kwakwalwalta. A parlor ta tarar dasu Haneefa su Yakumbo da Aunty da kuma sauran ƴan uwa da abokan arziƙi. Wajan Haneefa ta nufa cike da farin ciki wanda ake iya hangowa a kyakkyawar fuskarta. Zama tayi cike da zumuɗi take cewa. "Finally mun shirya da Yaya Rafeeq yau, kinga ma har ya bani gudunmawar Aurenah." Abinka da zuciya tuni ran Haneefa ya ɗan sosu, gani take wannan abun da Rafeeq yayi ba daidai bane ba, ita ya kamata ya fifita akan kowa saboda tana sanshi kuma ita zata zama matarsa uwar ƴaƴansa nan ba da jimawa ba. Kallan Maimoon tayi bayan ta lalibo murmushi da farin cikin yaƙe wanda yafi kuka ciwo tace. "Kai amma fa sunyi kyau, lallai Yaya yana ji dake irin wannan uban kuɗi da ya kashe miki." Murmushi Maimoon tayi tana sake shafa wuyanta inda sarƙartake manne, kallan Haneefa tayi bata ce komai ba ta wuce upstairs tana jin wani irin nishaɗi. Tana zuwa ta tarar Wahaab Bammali yana kiranta a waya, da sauri tayi daga, yadda yaji muryarta cikin farin ciki yafi komai yi masa daɗi, cikin zolaya yake cewa. "Duk murnar an saki a lalle ne ko? Irin wannan murna haka Hayati?" Bata san lokacin da wata dariya tazo mata ba, cikin basarwa dan idan ta gaya masa murnar sun shirya da Yaya Rafeeq ne tabbas ba zasu kwana suna walwala ba. "Toh kai kaga laifina a nan?" Wahaab dake kwance a saman lafiyayyan gadonshi na gidanshi wanda zasu zauna shida ita . yayi wani irin juyi yana rungume pillows, idanunsa ya lumshe yana jin ina ma ace a wannan lokacin suna manne da junansu tabbas da ya shayar da ita garɗin zumar daya tanadar mata. Cike da tsantsar soyayyarta dake sake huda kowacce ƙofa ta jikinsa yake faɗin. "No babu laifi sai ma jin daɗi. Hayati na gaji da gadin gidan nan ji nake kamar na janyo jibi ta dawo gobe kodai a matso da ɗaurin auran nan gobe?" Dariya ce ta sake kwace mata, lallai Wahaab a ƙagare yake ita har ta fara jin tsoro domin tunda satin bikin yazo taji yana Allah-Allah ranar auran su tayi. Cike da shagwaɓa take cewa. "Nifa ɗazu naje na cewa Daddy a ɗaga zuwa next month kuma yace zai je wajan Abban ku gobe suyi shawara." Kamar a gabansa take maganar domin yana daga kwance kawai ya ganshi a zaune yana ware idanuwa. Ji tayi yana cewa, "Amma dai Hayati mafarki kike yi ko? Wane irin next month ana zaune ƙalau. Please kidena min irin wannan wasan Bazan iya dauka ba wallahi." Sake turo baki tayi tana kuma karya murya take cewa. "Kaga fa lokacin mun gama exam yanzu fa ana ɗaura aure ran Saturday Monday zan koma school kaga babu wani isashen lokaci shi yasa na bada shawarar nan ta a ɗaga bikin." Wahaab ya shafa doguwar fuskarshi tare da jan numfashi yake cewa. "A'a a ɗaura ɗin zuwa exam kuma bazai gagara ba insha Allah. Hayati bazan iya jure har wani month ɗin ba bamu kasance a cikin gidan nan ni dake a matsayin mata da miji ba. Idan kuma ba haka ba ni a gobe ma zan iya sawa a ɗaura auran nan saboda naƙagu ki zama mallakina." Murmushin farin ciki ta saki, lallai Wahaab ba ƙaramin so yake mata ba ita kam dole ta sake godewa Allah da ya haɗata dashi. "Yaji tsoro abashi ruwan maɗaci." Yaji ta faɗa da salon tsokana. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sake kwanciya sukaci gaba da hirarsu irin da masoya masu tsantsar son juna.......
_#Shawarar Zeee Liman ta shiga dawo masa cikin kansa akan shawarar da take bashi. Girgiza kai ya shiga yi, a fili yake furta "No hakan bazata taɓa faruwa ba_.
_#Abu ɗaya ne ya rage masa wanda zai bashi damar mallakar Maimoon Gwarzo shine ya saceta kawai subar kan idanun duk wani wanda yake da alaka dasu._
_#Tunda ya baro gidansu Zainab Liman yaji alaqar rayuwarsa na juyewa da wani irin yanayi na ban mamaki wanda bai taɓa tsintar kansa a cikin wannan yanayin ba. Shine yanayin namene? A kuma kan meye yakejin sauyin?_
_#Shin Rafeeq Gwarzo zai yi nasarar lalatawa Maimoon Gwarzo rayuwa kamar yadda Zeee Liman ta bashi shawara? ko kuma dai zai bi shawarar zuciyarsa ta hanyar bin shawarar zuciyar na saceta? Toh wai zata so shine ko yaya?_
#Tsakanin Maimoon Gwarzo, Zeee Liman da kuma Haneefa wacece zata yi nasarar auren Rafeeq Gwarzo?
#Anya auren Maimoon Gwarzo da Abdul-wahab Bamalli zai tabbata? Shin Maimoon Gwarzo zata amince tabi Rafeeq Gwarzo zuwa wata duniyar ta daban dan suyi aure subar mahaifar su? Shin zatama amince da soyayyarsa?_
*Tabbas sai dai ku biyo alkamin HAJJA CE da ASMY B ALIYU acikin wannan doguwar tafiyar mai ɗauke da kalubalen rayuwa kala-kala. Muna tabbatar maku da bazakuyi da nasanin wannan tafiyar ba kamar yadda kuka karanta littafan mu a baya kamar Zo gareni, Nida Raheema, Waminal Hub, Albi (zuciya ta), Muhabbatil Qalb, ga kuma Tafiyar Rafeeq a gefe.....
#FAMILY
#LOVE
#REGRET AND PAIN....
ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)🔥
RAFEEQ🔥
MUNƊO🔥
ZAMANIN MU AYAU🔥
FATHIYYA.🔥
DOMIN SIYAN GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR ƊAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita da sunan
Asma'u Buhari Aliyu
08086207764
SAI KI/KA ISAR DA SHAIDAR BIYA TA ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
08086207764
07065283730
07051244211
07040402435
#ASMY B ALIYU
#HAJJA Ce
#Rafeeq Gwarzo
#Moobarak Gwarzo
#Team Tagwaye
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*
*PAID BOOK#400*
TEAM TAGWAYE NOVEL'S
NA
*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*
14
Addu'ar da yake yi ce kurum ta ƙarasa dashi cikin Mustapha Gwarzo mantion, ko parking motar bai yi da kyau ba drivern gidan yazo ya qarbi car key ɗin ganin yanayinsa aransa yake faɗin. "Shi dai wannan yaron abubuwansa kullum babu sauqi sai yayi ta abubuwa tamkar mai jinnu akansa." Rafeeq kam da gaske yana son ya bar Nigeria tsakanin gobe da jibi, kuma shirun daddy ya tabbatar masa da bai amince da wannan tafiyar tasa ba. Ganin yadda aka fara gyaran gidan nasu sannan mutane sun fara kai da kawo acikinsa yasa shi kuma shiga tashin hankali. Kai tsaye part ɗinsu ya nufa tun a hanya ya shiga cire botir ɗin shirt ɗin dake jikinsa yana jin yadda yake haɗa zufa ta ko'ina acikin jikinsa. Addu'a kawai yake Allah yasa Moobarak baya babban parlor dan bazai iya sauraren rigimarsa ba, yanzu yana bukatar zama shi ɗaya. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke ganin Shaheed ne kawai a parlorn da suits ajikinsa da alamar daga office ya dawo, bottle water ne a hannunsa har ya buɗe marfin zai kafa kai yasha Rafeeq ya shigo cikin parlon, kallonsa yake yana nazarin yanayinsa. Ɗaga masa hannu kawai Rafeeq yayi ya nufi stairs yana kin yadda su haɗa ido da Shaheed ɗin da ya bisa da kallo yana son Rafeeq ɗin ya kallesa. Kusan karo sukaci da Moobarak Gwarzo da ya ware ido yana kallonsa. Tsakiyya suka saka shi kowanne yayi folding hannunsa akan kirjinsa suna kallon Rafeeq Gwarzo. Da wata irin rigima da yake hangowa cikin fuskar kowanensu ya ɗan haɗe rai. "Da gaske yau muna so muji damuwarka Yah Rafeeq, wai shin menene ainahin abinda ke damunka? nasan dai ba matsalar kuɗi bane saboda daddy yana da kuɗi haka kuma kai ma kana dasu muna dasu, and ba matsalar rashin jin daɗi bane dan bakayi kalar wanda ke zama cikin wahala ba, ni nafi tunanin matsalarka kamar akan mace ne dan tun dazun da ka daukoni a Airport nake nazarin hakan a tattare dakai. Maimoon Gwarzo tace ka daina damuwa da ita gabaki ɗaya kabi ka canja mata kamar ba favorite brother ɗinta ba why Rafeeq?." Shaheed Gwarzo ya ƙarasa maganar da wani yanayi tattare da muryarsa. Dafe kai yayi yana kallonsu da idanunsa da suka daɗe da canza kala. Yana jin yadda kirjinsa ke wani irin bugawa kansa ma wani irin ciwo yake yi masa, hayaniyarsu damunsa takeyi. "Kayi magana dan Allah Yaaya ko za'a samu solution." Moobarak Gwarzo ya faɗa yana kamo hannun Rafeeq Gwarzo yana damkewa cikin nasa hannun, kaunarsu mai girma ce , wacce basu farata cikin sauqi ba. Shaheed gani yayi idanun Rafeeq ɗin kamar suna juyewa lokaci ɗaya kamar so yake ya faɗi. Da sauri Shaheed ya taroshi jikiinsa yana kiransa a gigice. Kwantar dashi sukayi kan bed Moobarak na tallabe da kansa ya saka masa inhelar suna ƙoƙarin numfashinsa ya dawo daidai. "Ko dai mu kirawo daddy?" Moobarak Gwarzo ya faɗa cikin tashin hankali. Girgiza kai Shaheed Gwarzo ya shiga yi yana faɗin. "Karka kirashi ka ɗaga masa hankali. Ka duba cikin bedside akwai injection ɗin da ake yi masa." Da gudu Moobarak ya ƙarasa wajen, daukosu yayi daya bayan daya yana duba date din dake jikinsu sai da ya tabbatar da suna aiki sa'annan ya haɗa ya yiwa Rafeeq ɗin. Har lokacin suna tare dashi kusan minti goma suka fara jin saukar numfashinsa, Moobarak ya ɗora kansa akan pillow ya kalli Shaheed Gwarzo yana faɗin. "Ya samu bacci Yaya." Ɗaga kai kurum Shaheed yayi kusan tare suka baro cikin room ɗin gamida rufo masa ƙofar. "Wai mema zai kaishi yin soyayyar da zai riqa wahala har haka? nasan kuma wannan yarinyarce wacce kuka yi school tare mema sunanta? meyasa zata yi soyayya dashi idan tasan bazata iya kula dashi yadda ya kamata ba?." Moobarak Gwarzo ya faɗa cikin tsawa da ɓacin rai a muryarsa. "Kayi a hankali Moobarak kar ya tashi." A fusace ya sake cewa. "Akan me zanbi a hankali Yaya? yanzu idan ka bincika ma yaudararsa tayi shi yasa ya shiga cikin wannan yanayin, kasan mata ko kaɗan basu da amana basu da kirki idan suka ga wanda yafi ka, ni wallahi naga ma kokarinsa, bazan iya daukarwa kaina abunda zai hanani jin daɗin rayuwa ba." Ya ɗauki car key akan center table dake tsakiyar parlon ya wani sha toka yana kallon Shaheed Gwarzo dake tsaye yana kallonsa tamkar shine babba yake faɗin. "Muje gidansu Yaya, Idan har na bincika naga taci amanarsa ne, wallahi tallahi sai tayi da nasanin sanin Familyn Gwarzo, sai nasa an ɓatar da duka dangin su." Cikin sauri yace. "Kaifa wata rana baka da hankali, kusan halinku ɗaya da Rafeeq idan kuna ɓacin rai. Waya faɗa maka Zainab ce ta ɓata masa rai? waya faɗa maka Zeeee zata iya cin amanar Rafeeq?" Girgiza kai Shaheed gwarzo yayi cike da rashin yarda da tabbatarwa yake faɗin. "A yadda Zeeeee ke son Rafeeq zai yi wuya ta ɓata masa rai , sam ba matsalar Zeeee bace na faɗa maka haka, mubarshi zuwa dare sai mu lallaɓasa ya faɗa mana idan bai faɗaba muyi masa barazanar zamu haɗashi da daddy, kasan daddy shine babban weakpoint ɗinsa. Ba wai duka Moobarak Gwarzo ya yadda da maganganun Shaheed Gwarzo bane, a'a yayi shiru ne kurum dan yace su jira zuwa dare.
Da yammah sosai Yakumbo ta iso da ƴan uwanta gidan sai qara ciki yake masha Allah kowa ka gani a cikin farin ciki yake. Gabaki ɗaya ranar Maimoon bata saka Rafeeq a idonta ba, ta kirasa kuma da safe bai ɗauka ba, tun safe tana tare da maigyaran jiki a ɓangaren Aunty, har Yaya Shaheed ta kira a waya dan ya haɗasu a wayar ya faɗa mata cewa shi yana office. Haka ta hakura sai bayan magrib da Moobarak ya shigo gaishe da Yakumbo taja hannunsa gefe ta riqe hannunsa tana kallonsa da idanunta tamkar zatayi kuka take faɗin. "Yaaya Rafeeq fa?" Ya ware mata ido yaja dogon hancina, bai faɗa mata gaskiyar abinda ya samu Rafeeq ɗin ba dan yasan zata iya ɗaga hankalinta. "Kin san halinsa baya son mutane ya fita tun da yamma." Da haka ya samu ya kwantar mata da hankali. Suna dawowa sallar isha'i ganin baiga Rafeeq a massalaci ba yasa ya nufi room ɗinsa kai tsaye, sai dai ga mamakinsa baya cikin room ɗin. Wayarsa ya fitar ya kirasa, ringing ɗaya ana biyun ya ɗauka. "Ina ka shiga?" Lokacin Rafeeq Gwarzo yana kwance a hotel room ɗin da ya kama yana jinyar zuciyarsa tamkar yasan abinda Moobarak ɗin ke shirin yi kayansa ya haɗa cikin qaramar bag ɗan idan ya cigaba da kallon Maimoon Gwarzo tana shirin zama matar wani bashi ba zurciyarsa zata iya bugawa shi yasa kawai ya yanke shawarar killace kansa a ɗakin hotel ko zai samu sauqin abunda yakeji aransa. "Kana ina ne Yaya zanzo na sameka?" Girgizawa Moobarak Gwarzo kai ya shiga yi tamkar yana ganinsa a zahiri yake faɗin. "Zan dawo zuwa anjima." Cike da kulawa yace "Amman kasan baka da lafiya koh?" Moobarak ya faɗa cike da ƙaraya a muryarsa. "Nasani zan kiyaye Baraak." Yana kiransa da hakan ne mafi yawancin lokuta. Ajiyar zuciya Moobarak ɗin ya sauke yana faɗin. "Ka kula dan Allah." Ɗaga kai kurum Rafeeq yayi batare da yayi magana ba. Yana sauke wayar kiran Zainab ya shigo wayarsa, har ta katse bai ɗaga ba, kiran da tayi masa ya kai goma amma babu wanda ya ɗaga aciki. Kiran na katsewa ya kashe wayar duka yana jin kansa na sarawa. Har washe gari da za'a saka Maimoon a lalle wayarsa a kashe take, wannan karon shirin zuwa office yayi cikin shigar italyn suite kalar ash wanda suka karɓi jikinsa sosai, aikin da ya fara tarawa kansa na kwana biyu a office ya fara ragewa dan kawai ya samu Maimoon Gwarzo dake cikin zuciyarsa ta fita daga ransa amman ko wane saukan numfashi da yake yi Maimoon Gwarzo ce manne a zuciyarsa. Karshe ma ture files ɗin dake gabansa yayi saboda ya kasa yin aikin, daura kansa yayi akan desk yana ƙoƙarin saita kansa.
Su Moobarak kuwa, ganin Rafeeq bai kwana a gidan ba yasa da safe suna breakfast Shaheed ya kalli Daddyn nasu cikin girmamawa ya kira sunansa. "Daddy." Alhaji Mustapha yana rike da fork yana cin ɗanwake ya kalli Shaheed ɗin alamar yana saurarensa. "Yaya Rafeeq kamar yana cikin damuwa fa, jiya ma ba a gidan nan ya kwana ba baya yiwa kowa magana yanzu sai dai ya keɓanta kansa bamu san menene ba." Shiru Alhaji Mustapha yai yana nazari a cikin zuciyarsa. Tabbas Rafeeq yana da damuwa to amma mecece? Tun randa yace yana son tafiya chaina bayan ya fita yai masa transfer kudi zuwa account ɗinsa duk ya ɗauka ko matsalar ta danganta da rashin kudi. Amma yanzu tunda aka ce bai kwana a gidan ba hankalinsa ya tashi ya fara tunanin meke faruwa? Ko kaɗan baya so yaga abu ya samu Rafeeq yanzun nan zai ce maraya ne ba'a so ana ɓatawa marayu rai. "Kinibabban yaro kawai, toh me aka yi masa? Ni wallahi da aure akai masa kowa ma ya huta, idan wacce zai aura ne babu zan iya taimakawa a haɗashi da Haneefa." Yakumbo tayi maganar sounding so very serious da sauri Maimoon da Haneefa suka kalli juna farin ciki a fuskar Haneefa ba'a cewa komai. Murmushi Maimoon tayi ganin mafarkinsu zai cika ko babu komai idan Haneefa ta auri Rafeeq kusancinsu ba zai yi nisa ba. "Abari dai aji
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book