Showing 33001 words to 34129 words out of 34129 words

Chapter 12 - RAFEEQ COMPLETE HAUSA NOVEL

asmy   

08 Oct 2024

11291

abinda yake damunsa yakumbo kar muje mu shiga hakkinsa." Yakumbo ta ware idanuwa tana kallon Alhaji Mustapha take faɗin. "Magana ta kare ba sai an wani biye masa ba, rana da lokaci kawai za'a sanya." Daddy dan a zauna lafiya yasa, shi cewa. "Toh shikenan ai." Daga haka gurin ya kaure da surutu kowa da abinda yake cewa a game da wannan hadin na Rafeeq da Haneefa, duk sunji daɗi ba kamar Maimoon da ta san yadda Hanee ke mutuwar son shi. Koda Daddy ya tashi yayi ta kiran wayar Rafeeq akashe, sai kusan karfe biyu da rabi na rana sannan ya sake kira. Lokacin Rafeeq ya baro office yana jin wani zafi saboda saƙon da ya buɗe yaga Zee ta turo masa. "Daddy ina yini?" Alhaji Mustapha yace. "Kazo gida ina son ganinka yanzu." Tunda yaji yanayin Muryar Daddy yasan su Moobarak sun kai masa gulma. Tuƙi kawai yake yi zuciyarsa na sake tafasa, idan ya tuna saƙon da Zainab ta turo masa sai yaji me yasa ma bai yi mata tsinannan duka ba a lokacin da ta fara kawo mishi shawarar nan? Mai ta maidashi akan soyayyar da yake yiwa Maimoon? Haushin kansa yakeji da har ya bari Zee ɗin tasan asalin sirrin zuciyarsa gashi har ta fara bashi gurguwar shawara. Da wani irin tashin hankali ya isa Gwarzo mantion, shawarar da Zee ke sake bashi tana sake rugurguza shi harma ya rasa inda zai saka ranshi yaji daɗi. Side ɗinsu ya nufa idanunsa dake ganin dishi-dishi su yake ta rintsewa yana sake buɗewa a hankali. "Yaayaah " Yaji muryar Maimoon daga bayan shi, nan take kirjinsa ya buga yana jin yadda bugun zuciyarsa ya canza. Sake runtse idon yai har zai tsaya yaji me zata ce masa sai kuma ya cigaba da tafiya dan baiga abinda zai yi mata ba a yanzu. Itama Maimoon ganin yaki tsayawa yasa ta haɗe rai su Haneefa da Zee leeman da sauran matan dake cikin rumfar suna kallanta kamar zasuyi da dariya ganin yadda takeyi masa magana cike da rigima. Tafiya yaci gaba dayi har ya isa kofa, da sauri ta shige ganin yana shirin rufe ƙofar. Rintsa ido kawai Rafeeq yai jin kusancinsu da juna, ta tsaya a gabansa tana canza fuska. Buɗe idon yai yana wani haɗe rai da kalar da bata taɓa zaton yanayin irin hakan ba. "Yaya Rafeeq ko wani laifin nayi maka ne?" Tayi maganar tana kafe shi da manyan idanuwanta. "Idan wani abu nayi maka da ya sanya kaƙi shiga cikin harkar bikina dan Allah kayi hakuri kuma ka sanar dani ko menene sai na baka hakuri kuma na kiyaye gaba. Komai na bikina baka shiga ba Yaya, duk ka tsame hannunka babu wani abu da kake yi min, ni gaskiya bana jin daɗin hakan Yaya Rafeeq. Yanzu anyi ankon shadda na ƴan uwa maza da lace na mata ƴan uwa kowa yanayi kai banji kace komai ba. Yaya Shaheed da Yaya Moobarak duk sun min abubuwan gudunmawa kai shiru ko tsintsiya baka siyo kace Moon ga gudunmuwa ta , taya zanji daɗi Yaya Rafeeq?" Ta faɗa hawayen da take ta riƙewa suka fara zirarowa akan tattausan kuncinta da fatar take sheƙi saboda gyara, bata damu da gogewa ba saboda halin da take ciki na ɓacin ran watsi da Rafeeq yayi da lamarinta ba wanda yafi komai yi mata zafi. Zuciyarsa ce ta sake hargitsewa ganin yadda take kuka ya sake rintsa ido. Shin meke damunsa ne? Yanzu me zai ce mata? Meye laifinta tunda bata san mugun son da yakeyi mata ba? Kallanta ya yi itama shi take kallo da sexy idanunta masu cike da rikici, itace ta fara ɗauke nata dan ba zata iya jure yi masa irin wannan kallon ba na cikin idanuwa. Gaba ɗaya magana sai tayi masa mugun wahala a gurin, bakinsa yaji yayi nauyi ya kasa ce mata komai. Room ɗinsa ya nufa da sauri yana sake jin zuciyarsa na san azalzalarsa, shaiɗan ya fara kwaɗaita masa bin shawarar da Zeee Liman ta bashi akan Maimoon ɗin, gashi yanzu da ya ganta sai yaga ta canza ta sake yi fresh sai walwali takeyi da wani ƙamshi na musamman. Kuka ta fashe da shi saboda a rayuwarta tana san taga ƴan uwanta maza suna bata muhimmanci a cikin lamarinta, wannan abubuwan na Rafeeq yana sanya ta tunani kala-kala, komai nashi ya canza cikin ƙanƙanin lokaci. Ta juya zata fita sukai karo da Moobarak, kallanta yai cike da mamaki kafin ya fara kallan cikin parlorn wai ko zaiga wanda ya sanya ta kukan. Ganin babu kowa yasa shi cewa. "Keda waye?" Maimoon ta cije baki. "Ba Yaya Rafeeq bane ba, wallahi ya canza duka Yaya Moobarak yadda kasan ba a cikin family ɗin Gwarzo yake ba." Ta faɗa tana share hawayen. "Ki rabu dashi ai mun gayawa Daddy insha Allah komai yazo karshe zai dena." Up stairs ɗin ta kalla tana sake turo baki, da kyar Moobarak ya lallaɓata ta hakura ta tafi wajan ƙawayenta. Yana shiga room ɗin ya rufe ƙofar tare da jingina bayansa a jiki yana sauke numfashi. Tunawa kawai yake sun kusa rabu sai kuma lokacin da tazo gidan shida ya ganta. Anya akwai abinda yafi ciwo irin na kana son mutum so irin wanda yake yiwa Moon ya kasa faɗa? Yana da tabbacin wannan ciwon yafi kowane ciwo a duniyar nan. Kenan Zeee ma tana cikin wani hali tunda tana sonshi yayin da shi kuma baya santa haka ake rayuwa ko kuwa dai sune aka tsarawa hakan? Tunawa da yai Daddy na jiransa yasa shi saurin rage kayan jikinsa. Wanka yayi ya sake kaya zuwa wani yadi ruwan zuma da akai masa ɗinki mai gajeran hannu, sosai yayi kyau abinka da dama shi ɗin mai kyau ne. Turarukansa dake jere wajan mirror ya fesa sannan ya fito zuwa side ɗin Daddy. Koda ya fito babu wanda ya kalla a cikin compound ɗin, kai tsaye babban parlor ya nufa nan kuma su Yakumbo ne da ƴan uwa dole yaje ya gaishe dasu suna ta yi masa tsiya amma ya share su ya nufi ɗakin Daddy. Knocking yayi kusan sau uku sannan aka buɗe masa, Daddy ne da kanshi wanda da alama daga toilet ya fito. "Shigo daga ciki." Daddy ya faɗa yana bashi hanya. Rafeeq ya shiga yana jin wani mugun tashin hankali dan besan me Daddyn zai ce masa ba.........


ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023

ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

IYALINA (A'ILATY)🔥
RAFEEQ🔥
MUNƊO🔥
ZAMANIN MU AYAU🔥
FATHIYYA.🔥

DOMIN SIYAN GUDA BIYAR N1500.

DOMIN SIYAR ƊAYA N400.

Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita da sunan

Asma'u Buhari Aliyu
08086207764

SAI KI/KA ISAR DA SHAIDAR BIYA TA ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.

08086207764
07065283730
07051244211
07040402435


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Rafeeq Gwarzo
#Moobarak Gwarzo
#Team Tagwaye

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login